Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 40
"Mamma ka da ki barni wallahi na tuba bazan sake ba ki yafemin" Alesha ta faɗa tana bin Mamma a baya, Mamma ta wuce wajen Noor ta buɗe jakarta ta ɗauko ledar sweet ɗin da ta kawo ma Noor ta miƙa mata cike da jin daɗi Noor ta kar'ba tare da faɗin " Nagode mama kaka" kar ki damu " ta faɗa tare da shafa kanta tana murmushi, Alesha ta share hawayen fuskarta, Mamma ta ɗauki jakarta ta wuce
Alesha tayi zaune tana tunanin maganganun da Mamma tayi mata
Misalin ƙarfe huɗu da rabi ya dawo gida ko da ya dawo a gajiye ga kuma yunwa, bai tarar da su a falo ba ya wuce d'akin sa yayi wanka ya fito sanye da gajeren wando da vest d'akinta ya wuce kwance ta tarar da ita idanunta a rufe kamar mai bacci Noor na kusa gareta tana kallo ya ƙara so yace "Bacci ki ke a wannan lokacin?" Ta buɗe idanunta da suka yi ja- ja- ja alamun zazzaɓi Noor tace "Papah" Baby kallo ake yi?" Eh" To ai zaki takurama Mommynki da wannan kallon je ki falo kiyi kallon gamu nan tafe "Okay papah" ta faɗa tare da sauka saman gadon ta wuce falo
Hannunsa ya kai jikinta yaji jikinta da zafi sosai yace" Bakya jin daɗi? Meyasa baki sanar min ba?"Bana jin komai yaya kawai ƙarfin jikina ne bana ji shiyasa ban sanar maka ba kuma na sha magani amman kayi hak'uri " Ta faɗa tare da tashi zaune ta jingina bayan ta ga kan gado yace "Sannu yanzu ba abunda ki ke ji ko?" Ya faɗa tare da ɗaga rigarta ya ɗora hannunsa a cikinta yana shafawa, sai da taji wani iri a jikinta a hankali tace " Eh babu ba abunda nake ji" Okay kin ci abinci kuwa?" Eh "Yawwa to yanzu me ki ke son ci?" Girgiza masa kai tayi alamun bata son komai yace " Ki kwanta ki huta Bara na je naci abinci yunwa nake ji"Ya miƙe ta riƙo hannunsa tace ita ma zata bisa falo, suka fito falon tare
Yayi yayi akan tayi zamanta ya saka abincin da kansa taƙi amincewa dole ya barta ta saka masa yaci sai da ya k'oshi ta kwashe kaya ta kai kitchen ta dawo ta kwanta tare da ɗora kanta saman ƙafafunsa
Misalin sha ɗaya na dare ta shigo d'akin sa fitowarsa wanka kenan yana tsaye ɗaure da towel a k'ugunsa yana duba sakon da aka turo masa a waya ta nufi wajen da yake ta rungumesa ta baya yayi murmushi ya aje wayar hannunsa ya juyo da ita gabansa ta kasa ɗago kai ta kallesa muryarta na rawa tace "Yaya don Allah ka yafe min" ta faɗa tana ƙoƙarin durk'usawa yayi saurin riƙo ta tare da girgiza kai yace "Miye haka?" Yaya ka yafe min nasan kwanakin nan na yi ta ɓata kama rai a bisa wani dalilina na banza wallahi bazan sake ba ka yafe min nasan na aikata babban kuskure " Alesha kin min babban laifi"Yaya girman laifin da nayi ma yafiyarka ta zarce shi na tuba " ta faɗa tana kuka
"Ki daina wannan kukan bana so " Ka yafe min?" Murmushi yayi ya shafi gefen fuskarta yace "Ban taɓa riƙe ki a rai ba na ɗauki abunda ki ke yi kawai a matsayin tausayin da ki ke ma yarinyar nan shiyasa nayi ta ƙoƙarin na fahimtar da ke amman kin kasa fahimta ta shiyasa naje kawai na samu Mamma na sanar mata komai Alesha nafi kowa sanin ki nasan tsananin zafin kishin da gareki kawai tausayin ta ne ya rufe miki ido ki ke ƙoƙarin salwantar da farin cikin mu amman yanzu tun da kin gane Shikenan komai ya wuce "Yaya dagaske baza ka min kishiya ba?" Ta faɗa tana masa wani shu'umin kallo
"Har abada kuwa in sha Allah " ya faɗa tare da janyota jikinsa ya cire hijabin jikinta, Wata rigar bacci ce a jikinta wacce da ita da babu duk ɗaya saboda rigar bata ɓoye komai ba raga raga take ai kuwa nan take gogan naku ya rikice ya shiga kissing ɗinta ta ko ina yana matsa na shanunta da suka ƙara cikowa irin na mai sabon ciki ita ma ta biye masa suka shiga faranta ran juna har suka samar ma kansu natsuwa
Washe gari sha biyu na rana ya kai su gidan Mamma ƙarfe biyu ya ɗauke su ya kai su gidan abokinsa Abbas da ya dawo ƙasar daga can suka wuce wata plaza suka yi siyayya suka kamo hanyar gida
Tun a wajen plazar da suka tsaya yaga wasu motoci uku na bin bayan su har yanzu kuma da suka doshi hanyar gida motocin na bin su a baya, tuk'insa ya ci gaba da yi har ya iso mai gadi ya buɗe masa ya wuce motarsa na shiga da sauri motocin dake bin su a baya suka danno kai cikin gidan.................................
*Ina mai matuƙar baku hak'uri na jin shuru ba update sakamakon rashin jin daɗin da bana yi* i know kuna hak'uri dani don Allah ku ƙara thank you 🙏😊💕 Love u all💔❤️❤️
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 41
Parking yayi duk suka fito da mamaki Alesha ke kallon motocin shima haka Azaad yana tunanin to waye haka, motar da ke ƙarshe aka buɗe ƙofa wasu zaratan sojoji suka fito suka nufi motar da ke gabansu ɗaya daga cikin su ya buɗe murfin motar, wani attajirin dattijo mai ji da naira ne ya fito yana sanye cikin manyan kaya fuskarsa ɗauke da murmushi sojojin suka basa hanya
Alesha ta kama hannun Noor ta kalli Azaad tace "Zamu shiga ciki" ya gyad'a mata kai ta juya kenan har tayi tako biyu dattijon yace " Wait Please " ta tsaya tare da juyowa ta kallesa sai taga kamar tasan fuskarsa amman ta kasa tuno inda tasan fuskar takowa yayi har wajen su ya miƙa ma Azaad hannu suka gaisa yace " Sunana Alhaji Aminu balarabe" Alhaji Aminu balarabe?" Azaad ya faɗa cike da tsantsan mamaki domin kuwa Alhaji Aminu balarabe ba ƙara min mutum ba ne a ƙasar nan koda baka san sa ba ka san sunansa duk da ba a ƙasar yake zaune ba,
ya kalli Alesha yace "Alesha ko?" Ya faɗa tare da nunata ta gyad'a masa kai yace "Kin gane ni kuwa?" Kai ta girgiza tare da faɗin "Aah"Yayi murmushi yace "Daman nasan da wuya ki gane ni kai ne mijinta?" Ya tambayi Azaad yace "Eh"Idan ba matsala don Allah ko zamu iya shiga ciki"Okay bisimillah " ya faɗa tare da nuna masa hanya suka yi ciki sojojin suka tsaya waje, suna shiga Alesha ta wuce d'aki ta cire mayafin jikinta ta saka hijab ta fito ta shiga kitchen ta kawo masa lemo mai sanyi ta buɗe zata zuba masa yace "No barshi kawai zan zuba da kai na" Ya faɗa tare da ɗaukar lemon ya zuba ya ɗauka ya sha yayi hamdala ya gyara zaman sa ya kalli Alesha yace "Zaki iya tuna wani aminin mahaifinki wanda baban ki ya ɗauki dukiyarsa ya basa"Alesha tayi shuru can tace "Eh na tuna wanda Daddy yayi ta nemansa amman bai samesa ba" Alhaji Aminu yayi murmushi yace "To ni ne wannan aminin nasa"Kai ne?" Eh ni ne "ya faɗa tare da miƙewa ya mayar da hannayensa a baya yace"A lokacin da na bar ƙasar nan lokacin na rasa wayata a cikin mota wanda hakan yasa na rasa number mahaifin ki,
tun daga lokacin sai na fara kawai kasuwancin da ya kai ni ina sayen motoci da golagolai daga can ina ba suwa ana kawo wa nan gida ana siyarwa da kaɗan kaɗan Allah ya sama kasuwancin albarka cikin shekara ɗaya sai ga riba ta ru'banya sosai har ta fi jarin da muka zuba hakan yasa na fara process ɗin buɗe kamfanin shinkafa a nan ƙasar bayan komai ya kankama shi ne na shirya zan je ma mahaifinki da daddad'an labari mummunan labarin da na tarar ya girgiza ni shi ne mahaifinki baya tare da mu Allah ya karb'i abunsa washe gari da na koma unguwar ku ta tambayi ko ansan inda ki ke aka ce k'anen mahaifinki ya ɗauke ki amman ba wanda yasan in da yake zaune nayi ta yawo a gari ko Allah zai sa na ganki tsawon wata biyu amman ko mai kama da ke ban gani ba dole na hak'ura da neman ki na mayar da hankali akan kasuwancin mu, mun buɗe gidan mai a ƙasar nan wanda a ƙallah zasu kai goma mun buɗe kamfanin hamdala na fulawa flower shagunan da aka buɗe kuwa suna da yawa sosai akwai na kayan abinci akwai na clothes tufafi akwai na Jewellery ado shagunan nada yawa mun gina masallatai da makarantunne sadaka
Jiya na shigo ƙasar nan na fito kamar a mafarki zamu wuce naga kun shiga wata plaza har mun wuce nace su dawo baya ina ta roƙon Allah yasa ke ce na gani don na sauke nauyin da ke kai na sai gashi kun fito duk da kin canza amman bazan taɓa mance kamannin ki ba hakan yasa motar ku na tashi muka biku a baya " ya ƙarashe faɗa tare da juyowa ya kalleta yace"Alesha duk wannan matsayin nawa da girma da dukiya duk na mahaifin ki ne wanda a yanzu mallakin ki ne ke keda mallakin komai wallahi cikin dukiyar nan banada ko sisi domin kuwa dukiyar da mahaifin ki ya bani ita ce ake ta juyawa har yanzu Allah ya sa mata albarka duk cikin arzikin sa ne muke ci mu ci mu sha mu yi sutura har muba wasu muyi sadaka nagode Allah da ya haɗa ni da ke a wannan lokacin yanzu zan hallanta komai a gare ki" ya koma ya zauna, yace idan Allah ya kai su gobe su shirya zai zo suje ya nuna musu duk wuraren da suke mallakin su ya ɗan jima a gidan sannan suka yi sallama ya wuce bayan sun yi musayan numbobin waya Azaad ya jinjina masa matuƙa saboda a wannan lokacin abu ne mai wuya a samu mai ƙarfin imanin da riƙon amana wanda zai iya yin abunda Alhaji Aminu balarabe yayi
Alesha ta kira Mamma ta sanar mata duk abunda yake faru ita kuma ta kira Daddy ta sanar masa Daddy yayi mamaki sosai su har sun manta shi saboda sun yi zaton yaudarar mahaifin Alesha ne kawai yayi ya gudu da dukiyarsa ashe ba haka ba ne
Washe gari tun da safe Alhaji Aminu balarabe yazo domin su je ya nuna musu ko ina Alesha tace ita ba sai taje ba Azaad kawai yaje don haka aka je da Daddy da Azaad suka je,
Basu dawo ba sai bayan sallahr la'asar gidan Daddy suka tsaya Alhaji Aminu balarabe ya wuce Azaad ya shiga ciki, koda suka shigo Ummie na kwance a falo ta murmuje ba ƙarya ta rame gaskiya kamar a mafarki taji muryar Azaad tayi sallama da sauri ta ɗago kanta ganin tabbas shi ne bata san lokacin da ta miƙe daga kwance ba ta zauna cike da farin cikin ganinsa ta miƙe tsaye ta gaida su....................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 42&43
Fuskarta ɗauke da murmushi Daddy yace "Ummie ana falo?" Eh Daddy "Okay sannu" Uhm Yaya Azaad ina wuni" ya ɗago ya kalleta yace"Lafiya kalau Ummie ya gida " Alhamdulillah ya su aunty Alesha?" Lafiya suke"Ma sha Allah "
Daddy yace" je ki kiran mommynku"Toh " ta faɗa ta kama hanyar zuwa kiranta zuciyarta cike da farin ciki don ita a tunaninta Azaad wajenta ya zo bare kuma da Daddy yace ta kira mommy sai tayi tunanin maganar auren su ce za'a yi
Azaad yace"To Daddy ni zan wuce "Aah ka tsaya mana ka ci abinci" Aah wallahi Daddy nagode "Abincin? To ka tsaya ka sha ruwa" Idan na sake dawowa zan sha Daddy "ya faɗa tare da kama hanya daddy yace"Wai da gaske ka ke kuwa bazaka tsaya ba to ka jira ni nazo na mai daka tun da ba mota a hannun ka "Nayi ma direba na magana yanzu haka yana waje yana jira na" ya faɗa ba tare da ya tsaya ba ko ya juyo ba ya buɗe ƙofa ya wuce
Mommy ta fito tace "Alhaji kun dawo? Sannu da zuwa wai ina kuka je ne?" To yanzu wanne ki ke son na amsa miki?" Duka nake san ka bani amsa" Daddy yayi murmushi sai ga Ummie ta fito ashe da ta kira mommy sai ta wuce ɗakinta ta shafa jambaki ta fesa turare ta fito, tun da ta fito take lek'e amman ko mai kama da shi bata gani ba a falon har ta ƙara so, mommy ta kalleta tace "Ummie ina zaki je yanzu?" Ni fa mommy ba inda zan je " Naga kin shafa wannan uban jambakin" Ba ta bata amsa ba sai ma tambayar Daddy da tayi tace"Daddy yana ina?" Wa kenan" ya tambeta " Yaya Azaad" Ohh ya wuce ina ganin kamar sauri yake yi " Ya tafi?" Eh lafiya dai ko naga fuskar ki ta sauya " Ba komai daman uhm daman ina ta sauri ne nazo na basa sak'o ya kai ma aunty Alesha"Ayyah gashi kuwa ya tafi to sai ki shirya gobe ki je da kanki ki kai mata tun da kin ji sauk'i "Toh"ta faɗa idanunta sun ɗan ciko da hawaye,
Mommy tun da taji ta ambaci sunan Azaad ta fahimci saboda shi taje ta shafa jambaki cike da tausayi take kallon y'ar tata ganin ta ɗauko dala ba gamo saboda a yadda take kallon Azaad duk da ba wani zama tayi da shi sosai ba amman wallahi ta fahimci yana matuƙar kaunar matarsa kuma ba abunda zai sa ya ƙara mata kishiya abu ɗaya kawai zata iya yima Ummie shi ne ta taya ta addu'a Allah ya cire mata son sa a zuciyarta
Juyawa tayi jiki a sanyaye tayi ɗakin ta Daddy yace "Ki saurare ni"To ina jinka "Mommy ta faɗa tare da mayar da attention ɗin ta garesa Daddy ya shiga koro mata bayanin duk abunda yake faruwa tun daga farko har ƙarshe "Allahu Akbar kabiran Allah mai girma da ɗaukaka yanzu duk tarin wannan dukiyar da ka faɗa min na Alesha ne ita kaɗai Allahu Akbar Allah Sarki marainiyar Allah har na tuna lokacin da take gidan nan Allah mai iko don Allah alhaji kayi min izini gobe ina son naje na duba ta kwanaki naji ance bata da lafiya duk da nasan ciwon bazai wuce na laulayin da take yi ba ne kuma ina son ma naje na nemi yafiyarta akan abubuwan da na riƙa yi mata lokacin tana gidan nan "Daddy kallon ta kawai yake auren Alesha yanzu kusan wata nawa amman dai dai da rana ɗaya bata taɓa zuwa gidan ta ba ko taga matsuguninta ba amman yanzu tun da taji maganar dukiya neman sulhu take da ita wannan wace irin rayuwa ce
Daddy yayi murmushi yace "Na miki izini ki je "To shikenan Allah ya kai muna rai gobe "Amin"
'Bangaren Azaad kuwa yana fita ya tarar da direbansa ya shiga suka wuce gida bayan yayi wanka yaci abinci ya huta ya sanar ma Alesha duk wuraren da suka je, washe gari wajajen sha biyu na rana sai ga mommy a gidan Alesha bata ko san gida ba sai da Daddy ya kwatanta ma direban da zai kawo ta waje sannan tun a harabar gidan ta yaba da kyawon gidan da tsaruwarsa lokacin da Alesha ta ganta ba ƙaramin mamaki da tsoro ba ne suka kamata ba na ganin mommy a gidanta, amman ganin yadda take wani faram faram da ita sai tsoron ya gushe ya bar mamaki saboda rabon da mommy ta tayi mata magana cikin tausasawa da murmushi tun iyayenta na raye amman yau abun mamaki mommy ke mata magana cikin tausasawa harda murmushi sannan ta durk'usa ta bata hak'uri na abubuwan da tayi mata tare da neman yafiyarta har da kukan ta, Alesha tace "Ta yafe mata ita daman bata taɓa riƙe ta a rai ba Allah ya yafe musu gaba ɗaya" Duk yadda mommy taso noor tazo wajen ta k'iyawa tayi ta lak'ema Mommynta
Mommy har kusan ƙarfe uku tana gidan da ta tashi Alesha ta haɗota da kaya kala kala tayi ta mata godiya ta wuce
Tafiyarta ba da jimawa ba Azaad ya dawo ta sanar masa mommy ta zo shima yayi matuƙar mamaki ya sanar mata ta lura kawai
A kwana a tashi cikin Alesha ya fara girma tana samun kulawa sosai a wajen Azaad fiye da yadda bakwa tunani yana faranta mata ita ma tana kula da shi tana faranta masa hankalin ta kwance ba abunda ya ke damunta
Yau zata fara zuwa awo daga wajen awo sai ta wuce gidan Ammie,da shi da Noor ne zaune a falo suna jiran ta fito su wuce K'amshin turarenta ya kawo ma hancinsa farmaki sai da ya lumshe ido ya ɗago ya kalli hanyar da take zuwa, tana sanye cikin wani tsadadden material marron an masa ado da golden stone ɗinkin riga da siket rigar bubu ce ɗinkin ya mata kyau sosai musamman cikin nan nata da ya fito sosai ga haɗad'd'iyar sarƙarta da ta saka mai haɗe da yan hannu da zobe fuskarta ba makeup lipgloss ne kawai sai kwalli da ta shafama idanunta mayafinta da handbag da takalmi duk golden ne wallahi ba ƙaramin kyau tayi ba ga wani ni'imantaccen k'amshin da yake tashi a jikinta, Azaad ya saki baki da hanci yana kallanta tana sakar masa tsadadden murmushin ta mai narkar da zuciyarsa
"Wowwwww tabarakallah ma sha Allah kinga yadda ki ka yi kyau kuwa wowwwww"ya faɗa tare da tashi ya riƙo hannunta tana murmushi yace "Allah na gode maka da ka azurta ni da samun wannan zankad'ed'iyar kyakkyawar matar a matsayin matata sarauniyar gidana gimbiya a waje na mai kyau da kyawon halayya Allah ya ƙara kare mu da sharrin duk wani mai sharri mutum ko aljan Allah ya barmu tare ya barmin ke Allah ya azurtamu da samun kyawawan yara masu kyawon hali kamar ke " ya faɗa yana ƙoƙarin sumbatar ta tayi saurin ja baya tace"Me kake ƙoƙarin yi " Kamar ya?"shima ya tambeta saboda ya ma manta da Noor dake wajen, Ta nuna masa Noor da ido ya juya ya kalli Noor yace "I forget " Alesha tayi murmushi Noor ta taso ta shiga tsakiyar su tace "Mommy kin yi kyau" Ohhh really ?" Ta faɗa tare da ɗaukar Noor" Eh mommy " To ai ban kai kyaun ki ba " Ki daina ɗaukanta yanzu saboda ba ke kaɗai ba ce" ya faɗa tare da kai hannu ya shafi cikinta, suka wuce
Basu jima a asibiti sosai ba ya kai su gidan Mamma a can suka wuni sai dare suka dawo, bayan kwana biyu sai ga mommy ta sake zuwa wannan karon koda tazo Azaad na nan bata wani jima sosai ba ta wuce, tun daga lokacin mommy ta samu wajen zuwa
cikin Alesha tun da yayi wata bakwai aka nemo mata mai aiki wacce zata riƙa yi musu share share da goge goge saboda cikinta yayi girma sosai kamar ba cikin fari ba ga yawan bacci amman duk da haka ita ke yi musu girki mai aikin da ta gama abunda take yi zata wuce a kwana a tashi ba wuya cikin Alesha ya shigo watan haihuwa tafiya ma dak'yar take yinta saboda nauyin da cikin yayi ga kuma girma ga ciwon marar da take fama da shi, har ta shanye watan haihuwarta ta shigo wani shuru
Tana kwance mararta na suka mata sama sama har aka fara kiran sallahr asuba Azaad ya farka ya kalleta duk tayi wani iri cike da tausayinta yace"Sannu Allah ya sauke ki lafiya" Kai kawai ta ɗaga masa ya tambeta akwai abunda take ji ne? Ta girgiza masa kai, ya tashi yaje toilet yayi alwala ya fito ya zura jallabiya ya wuce masallaci tashi tayi ta lalla'ba tayi ɗakin ta toilet ta shiga tayi alwala ta fito ta shimfid'a sallaya da dabara ta zauna ta kabarta sallah har tayi raka'a ɗaya mararta da bayanta suka riƙe wani azababben ciwon da tun da uwarta ta haifota bata taɓa jin irinsa ba bata san lokacin da ta yi wurgi da hijabin jikinta ba ta fashe da matsanancin kuka tana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Innalillahi wa inna ilaihiraji'un mutuwa zan yi wayyoo marata bayana uhmmmmmm"ta faɗa tana yin wani irin nishi zufa karyo mata kawai yake ta ko ina, kamar an tsakari Noor a bacci ta tashi da gudu ta sauko saman gado tayo wajen Mommynta ganin halin da take ciki ta fashe da kuka tare da rungumeta "Ɗauko wayata"ta faɗa daidai kunnen Noor ta saketa taje ta ɗauko wayar ta miƙo mata ta kar'ba ta aje ƙasa Allah yasa number Mamma a sama take ta danna kiran tasa speaker
Mamma na zaune saman sallaya tana lazumi taji wayarta na ƙara alamun kira na shigowa sai da gabanta ya faɗi tayi sauri ta miƙe number Alesha ta gani tana ganin number tasan haihuwa ce ta ɗaga jin muryar Mamma yasa Noor tace "Mama kaka ki zo mommy na kuka" Ina daddyn ki ne?" Ban gansa ba" sai mamma ta tuna by dis time yana masallaci tace "Gani nan tafe"ita ma duk ta rud'e koda ta kashe wayar har ta kawo ƙofar falo ta ɗauko key ɗin mota ta buɗe ta fito ta shiga mota taja a guje
Cikin minti goma ta iso bakin gate ta aje motar saboda tayi hn mai gadi na sallah ta fito ta buɗe ƙofar gate ta shiga...........
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 44
Sauri take yi sosai kamar wacce zata tashi sama koda ta isa falon ta matsu kai tsaye ta wuce bedroom ɗin Alesha durk'ushe ta tarar da ita tana faman nishi mai haɗe da gurnani Noor na rungume da ita tana kuka da sauri ta isa wajen su ta janyo Noor dake kuka suka fito waje ta kaita falo ta zaunar da ita tace "Ta daina kuka ta jira su yanzu zasu fito" ta wuce ta koma, Noor ta sake fashewa da kuka
Mamma na zuwa ta cire hijab ɗin ta tayi kan Alesha
Azaad yana fitowa masallaci ya ga mota bakin gate yabi motar da kallo nan take ya gano motar Mamma ce, da sauri ya wuce ciki zuciyarsa na har'bin uku
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 13