tana school dawowarta ta samu labarin suna asibiti
Sallama tayi duk suka juyo suka kalleta har da Ummie, Mommy tace " Har kin iso" Eh " ta faɗa tare da nufar gadon ta aje ledar hannunta ta kalli Ummie tace"Sannu Ummie ya jikin?" Da sauƙi " Allah ya ƙara sauƙi " Mommy tace "Amin Alesha Mommy sai kallan Alesha take tun da ta shigo taga ta ƙara kyau ta cika ga wani yanayi da ta gani a tare da ita wanda ta kasa fahimtar mene ne
Alesha ta tausayama Ummie ganin duk ta rame tayi baƙi
Ummie ta kalli Mommy tace " Mommy dan Allah ku bamu waje ina son muyi magana da ita"Ummie Mu fita fa kika ce? har da ni mahaifiyarki na fita " Please Mommy magana zamu yi" To Shikenan zamu fita kinji karki damu basmah mu je waje ko " Ta faɗa tare da tashi suka fito ganin su yasa Daddy yace" Lafiya?" Cewa tayi mu basu waje zasu yi magana"Okay "
Alesha ta zauna inda Mommy ta tashi tace "Ummie wace irin magana ce ki ke son mu yi da baza ki yi a gaban Mommy ba "Aunty Alesha wallahi ina cikin matsanan cin damuwa da takaici wanda ni na ja ma kai na aunty Alesha duniyar nan zaune ne kawai nake a cikinta amman wallahi ban jin daɗin ta duniya ta daina min daɗi aunty Alesha duk wannan damuwar tawa ke kaɗai ce ke da maganinta " Ummie ni kuma? Taya nake da maganin damuwar da take damun ki?" Yanzu zan sanar miki amman sai kin min alƙawarin zaki amince da abunda zan faɗa miki 'Ummie taya zan ɗau alƙawarin abunda ban sani ba "Aunty Alesha kin taɓa cewa muddin kina da maganin damuwata zaki yi min don Allah ki ɗaukar min alƙawari zaki yi min maganin damuwata wallahi ke kaɗai ce zaki iya yi min maganinta don Allah aunty ki taimaka min wallahi zan iya rasa rayuwata " Kar ki sake faɗin haka Ummie in sha Allah baza ki rasa rayuwarki ba ki faɗi kawai in sha Allahu muddin ina da maganin matsalar ki zan miki" Aunty Alesha ina matuƙar son yaya Azaad Alesha ta buɗe ido tana kallanta.................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 36
Tamkar saukar aradu haka taji maganar tayi shuru tana kallanta tace "Bangane ba wane yaya Azaad ɗin? " Wanda ki ka sani " Ummie Kimin gwari gwari yadda zan fahimce ki" Ummie ta riƙo hannunta tace "Aunty Alesha wallahi tun kafin ki auri yaya Azaad na san shi zuciyata ta kamu da son sa sanadiyar hakan yasa lokacin da Daddy yazo min da maganar yayi min miji ya bada aure na ga wani naƙi amincewa a she ban sani ba wanda nake mutuwar so da k'auna ne ya biyo ni har gida amman na murje ido na watsa ma mahaifinmu ƙasa a ido naƙi amincewa da zaɓi da ya kawo min Mommy ta goya min baya ke kuma ki ka masa biyayya ki ka amince " ta ƙarashe faɗa tare da fashewa da matsanancin kuka
Alesha tace"Please stop cry kinga halin da ki ke ciki please ki daina kuka okay " Ta share hawayenta tace"Aunty Alesha nasan duk duniyar nan ke kaɗai ce zaki iya taimakona ki sa yaya Azaad ya aure ni wallahi aunty Alesha idan ban auresa ba zan iya mutuwa wutar son sa ta ruru a zuciyata ƙiriss take jira ta kama ki taimaka min kar in rasa rayuwata ki tausaya min son da nake masa ne ya kawo ni saman wannan gadon" Alesha tayi shuru can tace"Ummie ki share hawayenki in sha Allahu na miki alƙawari bazaki rasa rayuwarki ba "Zaki sa ya aure ni ne?" Alesha ta runtse idanunta tace " Eh" ta faɗa tare da gyad'a mata kai" Ummie in har auren yaya zai sa ki samu lafiya da kwanciyar hankali to in sha Allah zaki auresa ko da kuwa hakan zai sa ni na fita ke ki shigo ne " Nagode Nagode sosai aunty Alesha wallahi kin min abunda ba ko wace mace zata iya yin haka ba Nagode aunty"Kar ki damu Ummie Allah ya baki lafiya ya kuma bamu zaman lafiya da hak'uri da juna "Amin"
Duk abunda suka faɗa a kunnen Mommy tana tsaye bakin k'ofa ganin ba wanda ya ganta ta juya ta koma jiki a sanyaye
Alesha tace "Kin ci abinci kuwa?" Aah bazan iya ci ba " Ki daure ki ci ko kaɗan ne"Ko da na ci bazai wuce ba " To ga fruit ki ci ko kaɗan ne "Aah"Yaya fa ya siyo miki shi ne baza ki sha ba "Dagaske shi ya siyo?" Eh "Alesha ta faɗa tare da ciro banana 🍌 ta ɓare ta miƙa mata ta kar'ba ta fara ci, tana canyewa ta sake miƙa mata wata sai da taci guda uku sannan ta tashi tace "zata wuce yaya na jiranta zasu je wani wajen" Suka yi sallama ta fito
Mommy ta taso tace" Har kin fito "Eh Mommy z......." Ta kasa ƙarasawa saboda kanta da yayi wani irin mugun sarawa jiri ya ɗauke ta tayi baya da sauri Azaad ya tareta ta faɗo jikinsa Daddy shi ma ya taso yace "Subhanallah daughter lafiya kuwa meyake damunta?" Kwanan nan ne wallahi take fama da ciwon kai yau ma muke da k'udirin zuwa ganin likita sai ga kiran Mommy " Allah sarki to me zai hana ku tsaya nan ku ga likita" To Shikenan Daddy" Sannu Allah ya sauwaka bara na shiga ciki na ganta "Mommy ta faɗa tare da shiga d'akin da Ummie take
Azaad da Alesha kuma suka wuce don ganin likita, Daddy ya biyo bayan su
Koda suka je kuwa ba mutane aka shiga yi mata gwaje gwaje da aune aune tashi ɗaya aka gano tana da ciki na tsawon wata biyu, murna da farin ciki wajen Azaad basa 'boyuwa a gaban Daddy ya rungume matarsa ya sumbaceta a goshi, Alesha taji kamar ƙasa ta buɗe ta shige saboda kunya amman shi ko a jikinsa, Daddy shi ma yayi farin ciki sosai zai samu jika kuma ya ji daɗin ganin yadda Azaad yake nuna kula gareta hakan ya tabbatar masa da zaman su lafiya k'alau yake kuma suna son junan su
Basu koma ta wajen su Ummie ba suka yi sallama da Daddy suka wuce, Daddy da ya je yake sanar musu ashe ciki ne da Alesha fuskarta Mommy ba farin ciki ba baƙin ciki tace "Allah ya raba lafiya"
Saman hanyar su Azaad sai tambayarta yake yi me take so me zata ci duk abunda ya faɗa tare aah bata son komai ganin dai ya nace yasa tace " Zan sha yoghurt" Suka tsaya wata plaza ya shiga ya siyo mata suka wuce gidan Ammie, da shigar su gidan Azaad ya sanar ma Ammie Alesha na da ciki, Alesha kunya kamar za ta kasheta ammie kuwa tayi farin ciki sosai da sosai
Sai da suka yi sallahr magrib a gidan sannan suka wuce gidan su,
Har sun yi shirin kwanciya Alesha tace " Yaya ina son muyi wata magana mai muhimmanci"Okay ina jin ki " ya faɗa tare da mayar da hankalinsa a kanta " Uhm yaya don Allah daman wata alfarma nake nema a wajen ka" Ta faɗa tare da yin shuru yace "Ki faɗi ko mene ne babu wata alfarmar da zaki nema a waje na ba tare da na miki ita ba in Sha Allah " Ya faɗa tare da kai hannu ya sha cikin ta
"Daman ina son uhm daman i...in......a.....son kaaa.......... ƙara aure" what?" Ya faɗa tare da ɗan ja baya ya tsare ta da ido, ita kanta da ta faɗi kalmar sai da taji wani iri................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 37&38
"Eh yaya ina son ka ƙara aure don Allah" Alesha kina cikin hankalin kan ki kuwa? ko wani abu ke damun ki ne? kin ko san abunda ki ke gaya min ?" Yaya na san abunda nake faɗa"Aah Alesha akwai abunda yake damun ki "Wallahi ba abunda yake damuna yaya"Azaad yayi shuru yana kallanta can yace "Okay na fahimta ai ba ta haka zaki fito min ba fitowa fili zaki yi ki ce bakya so na ina takura miki ba sai kin yi kwauna kwauna ba " Haba yaya taya zaka faɗi irin wannan maganar"Taya kuwa bazan faɗi irin wannan maganar ba maganganun ki sun nuna bakya so na bakya kishi na saboda duk matar da take son mijinta take kishinsa bazata so ya ƙara aure ba amman ke da bakin ki kike faɗin na ƙara aure alamun me kenan? " Alesha ta langoɓe kai idanunta sun ciko da hawaye tace"Yaya ka fahimce ni wallahi duk duniyar nan ba wanda nake ma irin son da nake maka kuma baza'a yi shi ba wallahi ina son ka ina kishin ka fiye da yadda baka tunani "
"Ban yarda ba da kina sona kamar yadda kika faɗa da bazaki tunkare ni da wannan maganar ba" Yaya ka fahimce ni"A kan me zan fahimce ki? saboda wane dalili? ki kawo min ƙauƙaurar hujjarki ɗaya ta cewa nayi aure " Banada! banada wata hujja da zan ce ka ƙara aure yaya Ummie ce nake son ka aura wallahi tana son ka sosai ta kamu da ciwon zuciya ne sanadiyyar son da take maka yaya wannan alfarmar ce nake nema a wajen ka ka taimaka ka auri Ummie wallahi zata iya rasa rayuwarta kuma nas................................."Tayi shuru ne na hannun da Azaad ya ɗaga mata cikin zallar 'bacin rai ya ce "Ya ishe ki haka Alesha bana so bana son ji tun da muke da ke baki taɓa ɓata min rai ba amman yau gashi kina gasa min maganganu waɗan da zasu iya hanani bacci don haka ya ishe ki " Ya faɗa tare da tashi ya sauka saman gadon ya fita, ita kuma ta shiga tunanin yadda za'a yi ta shawo kansa ya amince da auren nan
Ruwa ya je ya sha ya dawo ya rage hasken ɗakin ya haye gado ya kwanta nesa da ita tana zaune saman gadon tana kallansa ganin ya kwanta ita ma ta kwanta ta rufe idanunta tana son tayi bacci amman ta kasa saboda ya riga da ya sabar mata da bacci a jikinsa shiyasa ko da rana bata iya yin bacci sai idan yana nan ta kwanta a jikinsa su yi bacci idan kuma kaga tayi baccin ranar to baccin ya ci ƙarfin ta ne, ga tsigar jikinta da take tashi ta sha wani magani da Mamma ta bata, sai juye juye take yi ta juya ta kalli Azaad da ya bata baya idanunta suka ciko da hawaye ita ma ta juya ta basa baya ta rufe idanu duk yadda taso bacci ya ɗauketa yaƙi ɗaukar ta, duk motsin da take yi yana jinta shima bai yi bacci ba
Ya juyo ya kalleta yace "Come here " ya faɗa tare da buɗe hannunsa
Da mugun sauri ta ƙara so wajen sa ta faɗa jikinsa har tana sauke ajiyar zuciya ta shiga goga masa dukiyar fulaninta yaƙi tanka mata ta fara yi masa tafiyar tsutsa tayi ƙasa da hannunta da sauri ya riƙe hannun ya buɗe idanunsa ta ɗago ta kallesa yace "Sleeping" ya faɗa tare da mayar da idanunsa ya rufe ta turo baki ta mayar da kanta ta kwantar a k'irjinsa ya fahimci duk abunda take buƙata shima yana buƙatar ta amman dole ya daure ya kaurace mata yau ya nuna mata kuskurenta
" Uhm uhm Honey! Honey" Uhmm" ya faɗa alamun bacci ya fara ɗaukar sa tayi masa irin dukan wasan nan a k'irji yace "Me na miki?" Ta turo baki tare da faɗin "Uhm ba kai ba ne"Me nayi?" Uhhmm uhm husbyyyyyyyyy " Mene ne " ta wani ƙanƙamesa sosai tana sauke numfashi jin numfashinta ya sauya ya kalleta yaga tayi bacci ya shafi kanta tare da faɗin"Sorry "ya manna mata kiss a haka bacci yayi awon gaba da shi
Washe gari bayan sun yi break ya shirya zai aje Noor a makaranta shi kuma sai ya wuce wajen aiki daga can saboda driver Noor baya nan
Alesha ta ɗauko masa agogonsa ya miƙa hannu ta daura masa tace " Yaya sai ka dawo ne zamu ƙarasa maganar " Wace maganar?" Ya tambaya tace "Maganar da muka fara jiya" Cikinta ya shafa yace " Ki kula da kanki da kuma abunda ke cikin ki sai na dawo muje Noor " Noor ta taso ya kama hannunta ya kar'bi basket ɗin ta suka wuce tace"A dawo lafiya Allah ya tsare "Amin"
Suna fita ta shiga kitchen ta fara shirin d'aura dinner, dak'yar taga ta kammala girkin saboda tashin zuciya da take fama da shi ga kuma ciwon kan da ya dawo mata, abincin da zata je da shi asibiti ta saka a basket ta haɗa komai sannan ta wuce tayi bedroom ta faɗa toilet tayi wanka ta dauro alwala ta fito ta kwanta tana kwance har ɗaya tayi sannan ta tashi tasa kaya ta ɗauko wayarta ta fara neman Azaad a waya ga wayar na ringing ba'a ɗaga ba har kusan kira biyar 5 ta masa bai ɗaga ba yasa ta aje wayar tasan dai duk inda yake yanzu yana kan hanyar zuwa gida saboda lokacin tashi daga makarantar su Noor yayi kuma shi zai ɗaukota ta tashi ta fito falo tana fitowa ko aka fara k'wank'wasa ƙofa ta je ta buɗe Noor ce tare da yaron sa ya gaidata yace "Aiki yayi ma oga yawa a office shi ne yace na ɗauko ta" Alesha ta masa godiya ta kama Noor suka wuce
Direct ɗaki ta wuce da ita ta cire mata kaya suka wuce toilet tayi mata wanka ta shiryata ta bata abinci, wayarta ta fara ringing Noor ta miƙo mata sunan da ta gani ne yasa tayi murmushi tare ɗagawa ta kafa wayar a kunne sun jima suna waya sannan ta bama Noor ya tambeta me take so ya biyo mata da shi tace "Sweet" yace "To shikenan ta bama Mommynta waya" ta miƙa mata suka yi magana ya kashe
Misalin ƙarfe biyar ya dawo a gajiye yayi wanka yaci abinci suka zube a falo kallon da Alesha ke masa ya fahimci akwai abunda take son faɗa yace "Mene ne?" Tace "Yaya zuwa asibiti?" Da sauri ya miƙe daga kwancen da yake yace" Bakya jin daɗi ne? Me yake damun ki? Wani abun ki ke ji?" Ya jero mata waɗan nan tambayoyin a tare tace "Aah bana jin komai"Alhamdulillah to me zamu yi a asibiti?" Wajen su mommy " Sai da ta faɗi haka ya tuna da Ummie bata da lafiya yace " Gaskiya ba zamu samu zuwa ba yanzu kinga marece yayi a bari kawai sai next time " Okay to shikenan" ta faɗa tare da ɗaukar wayarta ta kira musa mai gadi yazo bakin ƙofa ta ɗauki abincin da ta saka ma su mommy ta basa ta kalli Noor tace " Baby ba kin ce an baku homework ba?" Eh mommy " Okay je ki ɗauko jakan ki" ta je ta ɗauko tayi mata homework
Bayan sallahr magrib ya dawo da masallaci ya ɗauki key ɗin mota ya fita yaje yayi siyayyar kayan jarirrai har da su duk ya siyo musu kaya ya kawo mata tayi farin ciki sosai tayi masa godiya tare da addu'a
Suna zaune suna firar su mai daɗi Noor tayi bacci Alesha ta sake ɗauko masa da maganar auren Ummie ya kalleta ya kira sunanta yace "Bazan ƙara aure ba bana da sha'awar zama da mata biyu sannan bara ki ji koda ma ace ina da sha'awar ƙara aure Ummie bata cikin jerin tsarin zubin matar da nake so wallahi Bazan iya aurenta ba Alesha ke kaɗai kin ishe ni duk abunda nake so kina yi min baki rage ni da komai ba muna zaman lafiya to mezai sa na ƙara aure? A kan me ? Saboda wane dalili?" Na mata alƙawarin zaka aure ta yaya don Allah ka taimaka mata"Look Alesha na roƙeki daga yanzu kar ki sake min wannan maganar ina tunanin mun kawo ƙarshe, wallahi bazan 'boye miki ba har mamaki ki ke bani tausayin ki yayi yawa mutanen da ba k'aunar ki suke yi ba amman har ki ke tunanin sadaukar da farin cikin ki gare su " Bata tanka masa ba ta tashi ta ɗauki Noor tayi bedroom ta kwantar da ita
Tun daga lokacin yaga ta canza masa saboda yaƙi amincewa da auren Ummie kusan kwana uku duk yadda zai mata bayani ya shawo kanta yayi amman taƙi fahimtarsa don haka ya je ya sami Mamma ya sanar mata duk abunda yake faruwa, tayi mamaki sosai don ko a tarihi bata taɓa jin irin wannan sakarci da ganganci da Alesha take son aikatawa ba ta bama Azaad hak'uri tare da yi masa alƙawarin zata sameta tayi mata magana...................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 39
Mamma sai da ta cika masa tumbinsa sannan ya baro gidan direct kuma daga can ya wuce gidan Ammie sai bayan sallahr la'asar sannan ya dawo
Falo ya tarar da su tana zaune miƙe da ƙafa tana dannar waya Noor kuma na zane a takarda, Noor tayi masa oyoyo ya ɗaga ta sama ya aje yace "Zanen me ake haka?" Gida ne " Waya gaya miki haka ake zana gida je ɗauko na nuna miki yadda ake yi" ta je ta ɗauko, Alesha ta aje waya ta miƙe tayi masa sannu da zuwa ya amsa ta wuce taje ta kawo masa ruwa masu sanyi ya sha ta ɗauko kulolin abinci ta aje ta ɗauko filet da spoon ta buɗe abincin zata fara zuba masa yace" Idan ni zaki sakama kar ki wahalar da kan ki domin kuwa bana jin yunwa " ta ɗago ta kallesa tace"Bakya jin yunwa to me ka ci?" Eh naci abinci" A ina " Gidan su Ummie" da mugun sauri ta kallesa tace" Wace Ummie? " Ummie dai wacce ki ka sani Ummie amarya ta " Gabanta yayi mugun faɗuwa zuciyarta na harbawa da sauri sauri ta kafesa da ido
Tace"ka ci abinci a gidan su Ummie?" Ta faɗa cike da zallar mamaki " Eh ko ba hakan ki ke so ba?" Uhmmm amaryata, ta riƙa nanata maganar a zuci ta miƙe ta kwashe kulolin ta dawo falon ta zauna ta ɗauki wayarta taji ma ta kasa dannar wayar tana jin abu ya tokare mata zuciya ta tashi tayi bedroom Azaad ya bi bayanta da kallo yayi murmushi shi yasan wallahi Alesha ba ƙaramin kishi ne da ita ba tausayin Ummie ne kawai ya rufe mata ido take ƙoƙarin jefa kanta a rame ita kuma ta fito da ita
Tana shiga bedroom ta faɗa gado ta fashe da kuka sai tayi shuru tace "Kukan me nake yi? Wajen Ummie fa ya je" ta faɗa tare da share hawayen fuskarta ta janyo wayarta ta kunna karatun Alkur'ani mai girma tana saurara ta fara jin zuciyarta ta ɗan yi sauk'i
Washe gari
Yana fita Mamma na shigowa a guje Noor ta yi wajenta cike da farin cikin ganinta tana faɗin " Mama kaka" Mamma ta rungumeta ita ma Allah ya sa mata k'aunar Noor tace "Baby baby yau ba school ana gida ana hutawa ko?" Eh amman anjima akwai islamiyya " Okay ina mommynki ne?" Tana ɗaki "Okay" Ta nemi waje ta zauna sai ga Alesha ta fito cike da farin cikin ganin Mamma ta ƙaraso tace "Mamma ke ce haka sannu da zuwa" Yawwa " ta faɗa fuskarta a ɗaure ga wani kallo da take ma Alesha, ta wuce taje ta kawo mata lemon juice Mamma tace " Aje kayan ki bana buƙata ba shi ya kawo ni ba" Alesha tayi zuru zuru gabanta na faɗuwa ta kasa cewa komai
Mamma ta kalli Noor tace "Noor ki zauna kiyi kallo kinji zamu yi magana da mamanki "To " ta miƙe tace "Mu je ɗakin ki" Alesha ta wuce jiki a sanyaye suka yi ɗakin ta
Mamma ta bita da wani irin kallo tace "Wallahi Alesha jin nake kamar na wanka miki mari a she sakarya ce ke marar wayau wacce bata san kanta ba kin ko san illar abunda ki ke ƙoƙarin aikatawa kan ki ?" Mamma me nayi?" Gidan ku ki ka yi kinji nace gidan ku ki ka yi "Dan Allah kiyi hak'uri" Wallahi Alesha da na samu labarin abunda kike ƙoƙarin aikatawa ba ƙaramin mamaki nayi ba ina hankalin ki da tunanin ki suka je ne ina miki kallon mai hankali da tunani ashe ba haka ba ne kishiya kin ko san me ake cema kishiya? Kin san kishi? To wallahi ko ni da na kwana biyu yanzu da ace baban ku yana da rai yace zai ƙaro min kishiya sai inda ƙarfi na ya tsaya bare ke da baki tauna ba bare ki haɗe ki ke ƙoƙarin jajuboma kan ku masifa eh mana masifa don wallahi kishiya gareni masifa ce ta shigo ta hana ka kwanciyar hankali kishiyar ma ki rasa wacce zaki jajubo sai wacce ba k'aunar ki take yi ba idan ta shigo ta kashe ki kenan to wallahi ki buɗe kunnen ki da kyau ki saurare ni muddin ki ka tilasta masa yayi auren nan ba ni ba ke "Mamma don Allah kiyi hak'uri"ta faɗa tana kuka
Mamma tace "Ai kinjini bani ba ke sai ki je ki rungumi waɗan da ba k'aunar ki suke yi ba shashashar banza da wofi har yaushe zaki tilasta mijinki akan ya ƙara aure ke gaki uwar tausayi ko wallahi ki gode Allah ya baki miji mai son ki don da wani ne da wallahi ba wannan zancen ake yi ba amman ke da yake shashasha ce Allah ya baki miji ki ke ƙoƙarin salwantarwa wata shi, ya faɗa miki baya da sha'awar zama da mata biyu amman ke da yake mai taurin kai ce har ki ɗau fushi da shi ya je ya kai ƙarar ki, Mamaki ma ki ke bani wallahi ban san ki da wannan halin ba na kafiya har da zaki tsaya kina jayayya da mijinki, Alesha idan na tuna da maganar nan k'irji na har tafasa yake yi ki ci gaba da tilasta masa yayi aure ni kuma bani ba ke " ta faɗa tare da wucewa tayi gaba Alesha ta sha gabanta tana kuka tace"Mamma don Allah kiyi hak'uri na tuba bazan sake ba "Bani zaki bama hak'uri ba mijinki zaki bama hak'uri don shi kika ɓata ma rai ki samesa ki basa hak'uri" ta faɗa tare da raɓawa gefenta ta wuce.................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️(
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 13