uku, tun kafin ya ƙarasa shigowa falo yake jiyo sautin kukan Noor da sauri ya ƙara sa shigowa bai ko yi wajen Noor ba ya nufi ɗakin Alesha yana tura ƙofar Mamma tayi saurin cewa " Dakata Jira a waje" jikinsa a sanyaye ya koma, koda Mamma ta fito sai faman zarya yake yi a bakin ƙofa ganinta yasa da sauri ya nufo ta yace"Ta haihu ne?" Mamma ta girgiza kai tare da faɗin"Har yanzu " Mamma mu je asibiti"Nima nayi tunanin haka amman naga haihuwar tayi kusa mu ɗan jira kaɗan "Kina ganin ba matsala kuwa Mamma?" In Sha Allah ba wata matsala " Allah yasa wallahi ina tsoron na rasa ta"Ya faɗa idanunsa sun ciko da k'wallah yana tuna lokacin da mahaifiyar Noor ita ma ta rasu wajen haihuwa
"Idan na rasata bazan iya rayuwa ba nima mutuwa zan yi wallahi Alesha ita ce rayuwa ta ita ce komai nawa " Mamma tayi murmushin jin daɗi ganin tsantsan son da yake ma Alesha a cikin idanunsa tace"Kar ka damu in Sha Allah ba abunda zai sameta zata haihu lafiya ku ci gaba da rayuwa "Allah yasa Mamma"Kai dai kawai kaci gaba da yi mata addu'a bara na koma "ta faɗa tare da komawa ɗakin
Cikin ƙank'anin lokaci Alesha duk ta fice hayyacinta har ta sadak'ar lokacin ta yayi mutuwa zata yi, nishi tayi da ƙarfi sai ga jaririya ta faɗo, cike da farin ciki da murna Mamma ta ɗauki jaririyar tana kuka daman tasan awon yadda ake yankar cibi ta auna ta yanke ta goge mata jikinta ta janyo zane ta sakata ciki tana ƙoƙarin miƙewa ta ga Alesha na wani irin nishi ko kafin kace me sai ga wata jaririyar ta faɗo murna da farin ciki duk suka mamaye Mamma ta aje jaririyar hannunta ta ɗauki wacce ta faɗo
'Bangaren Azaad kuwa yana cikin roƙon Allah yaji kukan jaririya, murna da farin ciki suka mamayesa amman duk wannan murnar da farin ciki sai tsoro da fargaba suka mamaye gurbin su tsoron kar a je ita ma ta rasu
Mamma ta gyara ma jarirran jikinsu ta ɗauki ɗaya ta nufo waje tana buɗe ƙofa Azaad yayo wajen ta yace "Zan iya shiga na ganta?"Saurin me ka ke yi ne zaka shiga ka ganta tana cikin ƙoshin lafiya "To" ya faɗa yana ƙoƙarin bi ta gefen Mamma ya wuce tayi saurin taresa tare da faɗin "Jira tukkunna sai an gyara mata jikinta amman yanzu ka fara ganin abunda ta haifa mana"Toh! Toh shikenan" ya faɗa tare da miƙa hannu ya kar'bi jaririyar duk ya dabulce da ka gansa zaka san a rud'e yake Mamma ta koma ciki don ɗauko ɗayar
Azaad yayi shuru yana kallan jaririyar, jajir da ita kamanninta kuwa duk na mahaifiyarta ne duk ita ta ɗauko gashin kanta har saman goshi ga yarinyar mulmul da ita ya kafeta da ido yana jin k'aunar yarinyar na ratsasa yana cikin mata wannan kallon Mamma ta fito da ɗayar ya kalleta ya kalli hannunsa cike da tsantsan farin ciki da wannan kyautar da Allah ya basu ya buɗe baki zai yi magana amman ya kasa sai ga hawayen farin ciki mamma na dariyar farin ciki tace "Yan biyu ta haifa duka mata"Allahu Akbar! Allahu Akbar! Allah Nagode ma"ya faɗa tare da miƙa ma Mamma jaririyar hannunsa ya faɗi yayi sujjada ta nuna godiya a wajen mahalaccin sammai da ƙassai ya jima a sujjadar sannan ya taso ya kar'bi yaran, ku zo kuga zallar farin ciki a wajensa ya ma rasa abunda zai yi ya wuce falo da su ya fara kiran sunan Noor wacce daga kuka bacci ya ɗauke ta,
Ta buɗe idanunta ta tashi zaune Azaad yace "See! See your sisters "tayi shuru tana kallan jarirran tayi murmushi ganin sun buɗe idanunsu sun sa hannunsu a baki suna tsutsa tace "Papah namu ne?" Azaad ya gyad'a mata kai yana murmushi yace "Eh namu ne mommynki ta haifa muna su" Mommy?" Eh mommynki" Papah ina son su, kallah ka ga ta buɗe ido " ta faɗa tare da matsowa kusa da su
Mamma ta fito ta d'aura ruwa sai da suka tafasa ta juye takai toilet ta zuba cikin wata sabuwar babba roba, ita ta gasama Alesha jikinta sannan ta fito ta bata waje don ta ida wankan ita kuma ta ƙara gyara ɗakin ta feshe sa da turaruka nan take ɗakin ya ɗauki daddad'an k'amshi ta ɗan rage gudun AC
kayan haihuwar da ta saka a roba ta fito ta je can bayan gida wajen wasu fulawoyi ta wanke kayan tsaff ta shanya a wajen ta dawo ta shiga kitchen............
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 45
Girki ta d'aura ta koma bedroom tana shiga Alesha na fitowa, ta sha ruwan zafi jikinta har suraci yake fitarwa "Sannu ga kayan da zaki saka nan" Mamma ta faɗa tare da nuna mata wata atamfa da ta fitar mata, Alesha tace "To" tayi shuru tana son ta tambeta ina abunda ta haifa amman tana jin nauyin Mamma gashi ko ganin fuskar abun da ta haifa bata yi ba
, kamar Mamma tasan abunda yake zuciyarta tace "Bara na haɗa ruwan wankan yaran can ayi musu wanka suma su ji daɗin jikinsu su san sun shigo duniya"
Mamma ta fita ita kuma ta wuce ta shafa mai ta shafa humra ta ɗauki kayanta ta saka ta hau gado ta kwanta
Kwanciyarta kenan aka turo k'ofa, ta ɗago kanta ta kalli ƙofar yana tsaye riƙe da yaran yana mata kallan love, murmushi ta sakar masa a hankali ya fara takowa har inda take, ta ɗago zata tashi ya girgiza mata kai alamun tayi zamanta ta koma ta kwanta ya zauna kusa gareta ya kai fuskarsa daff da tata ya sumbaci goshin ta yace " Hak'ik'a bazan taɓa iya misilta miki irin farin cikin da nake ciki ba kin bani abunda ban taɓa tsammani ba yan biyu babu abunda zan ce da ke sai Allah ya miki albarka Allah yasa ki gama da duniyar nan lafiya"Amin"Ohh ikon Allah wai ashe yan biyu ne kwance a wajen nan" ya faɗa yana kallan cikinta
"Ina Noor?" Zai bata amsa sai ga Mamma ta shigo ɗauke da ruwan wankan da zata yi ma twins Noor na bayanta a guje Noor tayi wajen su, Mamma tace "A kawo yaran a musu wanka"Azaad ya taso ya miƙa ɗaya Mamma tace "Ba wannan ba waccen zaka bani ita ta fara shak'ar iskan duniya"Mamma yanzu har kin gane wacce aka fara haihuwa "Zanen jikin su yasa na gane saboda ba iri ɗaya ne ba ko wacce daban daban na saka mata saboda na gane su "Ai ko hakan yayi amfani"ya faɗa tare da miƙa mata ita ya kar'bi wacce ke hannunta
Har ta gama mata wanka bata yi kuka ba sai da ta fara gasa mata jiki sannan ta fara kuka ta gama ta miƙata ta karb'i ɗaya ita kam tana fara yi mata ta fara kuka, ta gama musu wanka ta shafa musu baby oil ta shirya su cikin wasu kaya iri ɗaya amman kala daban daban, ta miƙa ma Alesha su don ta basu abinci taja Noor suka yi toilet tayi mata wanka ta shiryata, Azaad kuwa tun ana musu wanka ya fita wai bazai juri sauraran kukan su ba yaje d'akin sa ya ɗauki wayarsa ya fara kiran yan uwa da abokan arziki yana sanar musu kyautar da Allah ya basu
Tuwon shinkafa Mamma ta girka tayi kuma farfesun kaji ta kawo musu a tare suka ci da Alesha da Azaad da Noor leda uku suka cinye ta tuwo sannan suka ci farfesun suna gamawa suka wuce asibiti saboda a duba lafiyar yaran da ta uwarsu, sun fito kenan sai ga mai aikinta ta zo tayi musu barka
Mamma tace "Ta shiga zasu je asibiti su dawo"Ta wuce ciki su kuma suka wuce
Koda suka dawo asibiti mutane sun cika gidan su anzo ganin yan biyu
Suna dawowa Mamma ta shirya zata je gida ta dawo tana fitowa taga Azaad shima zai fita ta kirasa yazo tace "To kamar yadda ka sani a al'adarmu ta nan idan mace tayi haihuwar farko gida take zuwar har sai tayi arba'in sannan ta dawo wasu ma tun kafin su haihu suke zuwa gida amman akwai abunda nayi la'akari da shi wanda na yanke hukuncin Alesha zata yi zamanta d'akin ta" Tun da ta fara magana Azaad yaji zuciyarsa na harbawa jin ƙarshen maganarta yasa yaji wani sanyi don wallahi bai ji zai iya barin Alesha taje wani waje ba
Mamma tace "Akwai gwaggonta da zata zo nan ta zauna tare da ita ta kula da ita da yaran har Allah yasa ayi arba'in sai ta tafi " To Mamma nagode sosai" Shikenan yanzu zaka iya tafiya "okay ko akwai abunda ake buƙata" No bama buƙatar komai yanzu "To Mamma"ya faɗa tare da wucewa
Mommy najin haihuwar ita ma tazo, Ummie jin yan biyu Alesha ta haifa taji ita ma tana son taje ta gansu amman ta kasa yin hakan, Ammie da daddy kasa hak'ura suka yi su jira har a kawo musu yaran da dare suka shirya suka zo ganin yaran Ammie wallahi jin take kamar taje da su daddy ma yaran sun shiga ransa sosai sai kusan sha ɗaya da wani abu suka wuce
Alesha tana samun kulawa sosai a wajen gwaggo da Mamma, domin Mamma kusan kullum tana gidan musamman da biki ya kawo anata shirye shirye, Mommy ma tun da aka haihu kullum tana gidan
Biki ya ƙara to aka kira mai lalle tazo tayi musu lalle na ji da gani aka musu kitso,Lallen yayi bala'in yima Alesha kyau gashi ja ne ya fito a fatarta yadda ya dace ga matar ta iya lalle sosai kitso kuma masu ɗan girma girma aka yi mata saboda bata son ƙanana ko kitson ma sai da Mamma ta dage sannan ta bari aka yi mata, kuma ba laifi duk da manya ne yayi kyau sosai
Ana gobe suna Ummie da basmah suka shirya suka zo, gidan ya cika kamar yau ake suna wasu na aiki wasu na zaune Rukayya da k'awarta suna riƙe da yaran, Ummie ta nufo su Rukayya ta sakar mata murmushi tare da faɗin "Ki koma gaskiya mun yi fushi yaran ki suma sun yi fushi ace tun da aka haihu baki zo ba sai yau ki koma kawai bama so" ta faɗa tana dariya ita ma Ummie dariyar take tace "Ayi hak'uri tuba nake yi"Ba wani hak'uri da zamu yi sai kin kawo ƙwaƙwaran dalilin da ya hana ki zuwa " Bana da lafiya"Subhanallah ai ko kin kawo dalili to Ubangiji Allah ya ƙara sauk'i "Amin ya Allah ina aunty Alesha ne?" Tana ciki " ta faɗa tare da miƙa mata babyn dake hannunta, ta jima zaune a wajen sannan miƙa ma Rukayya babyn ta tashi tace zata je taga aunty Alesha ta nufi d'akin ta
K'irjinta na dukan uku uku har ta isa bakin k'ofar ta K'wank'wasa Alesha fitowar da bayi kenan taji an K'wank'wasa ta wuce taje ta buɗe cike da farin cikin ganin Ummie Alesha tace "Ummie ke ce? shigo mana" ta shigo ta mayar da ƙofar ta rufe tace "Ai na zata ba zaki zo ba" Ummie tayi murmushi tace "Noor bacci ake yi" Eh wallahi bata ma jima da yin baccin ba " Okay a she mun samu ƙaruwa Ubangiji Allah ya raya muna"Amin Ummie "Aunty Alesha don Allah ki yafe min duk abunda na miki nasan na miki abubuwa iri iri don Allah ki yafe min "Kar ki damu Ummie na yafe miki Allah ya yafe muna baki ɗaya"Amin ya Rabbi Nagode sosai "ta faɗa tana jin wani sanyi a zuciyarta
Alesha tace"Amman kina nan sai dare ko?" Eh zan tsaya muyi aiki"Yawwa to ko kuje keda Rukayya ku kar'bo donut 🍩 Saboda matar ta kira ni tace an gama "To Shikenan Rukayya tasan gida ne?" Eh tasan gida bara na kira a kai ku "ta faɗa tare da miƙa hannu ta ɗauko wayarta Ummie tace" Ba sai kin kira ba da mota nazo "Okay to Shikenan ma"Bara naje na sanar mata " ta faɗa tare da tashi taje ta sanarma Rukayya suka tafi
Ƙarfe biyu aka kawo kayan jego akwati dozin ɗaya aka yi ma yaran da maman su har Noor sai kayan yaji da sauran kayan da ake yi
Ana gama sallah magrib Azaad ya rufema Alesha ido yace "ta zo ya nuna mata wani abu "suka fito har harabar gidan sai da suka kawo daidai inda yake son su tsaya sannan ya koma bayanta ya buɗe mata ido, wata dalleliyar mota ta gani a gabanta mai masifar kyau da tsada cike da tsantsan mamaki da farin ciki ta juyo ta kalli Azaad ya sakar mata murmushi tare da miƙa mata mukullin motar, kasa magana ma tayi ta fashe da kukan farin ciki ta faɗa jikinsa suka rungume juna
Mutanen da suka fito ne suka ɗau tafi da ihu
Washe garin suna, aka yanka marak'i biyu rago biyu
Yaran suka ci sunan su da suka zo da su na Hassana da Hussaina wanda aka musu lak'ami da Aafreen da Aafreeda, an ci an sha an yi wadak'ala da kayakki, yaran sun samu kyautukka sosai har kyautar fili suka samu
bayan kwana biyu Alesha na d'akin Azaad tana gyaran d'akin ta buɗe wata wadurob sai ga hoton maman Noor ta ɗauko hoton tana kallo Noor ta taso ita ma tana kallan hoton tace "Mommy wacece wannan?" Alesha ta kalleta taja hannunta suka zauna saman gado tace "Wannan yayata ce"Yayarki?" Eh"Ban taɓa ganinta ba ai mommy " Bata tare da mu Allah ya karb'i abunsa"Ina" ina nufin ta rasu"Okay " Princess kin san abunda nake son kiyi min?"Noor ta girgiza kai Alesha tace "Ina son ki ɗaukar min alƙawarin duk sallar da kika yi zaki mata addu'a kinji? Zaki yi?" Noor ta gyad'a kai tare da faɗin "Eh mommy "Allah ya miki albarka "
Azaad na bayan su yana jin su juyawa kawai yayi ya fita
Alesha koda suka yi arba'in yaran sun yi wayo luk'a luk'a da su, Aafreen da Aafreeda na cika wata shidda suka koma sabon gidan su da Azaad ya gina wanda yaci uban wancan sau dubu aka yi walimar tarewarsu da kuma walimar cikar su Aafreen wata shidda a duniya
Bayan wani lokaci
Ummie ta samu miji har an sa ranar auren su, duk da har yanzu tana jin son Azaad ɗin sai dai ba kamar dah ba tana ci gaba da roƙon Allah da ya cire mata son sa gaba ɗaya a zuciyarta, zumuncin su da Alesha ya gyaru yanzu ba wata matsala a tsakanin su
Su Rukayya suma sun kammala karatun su an saka ranar auren su lokaci ɗaya za'a musu
'Bangaren su Alesha kuwa sai madallah zaman su lafiya k'alau ko wannensu yana ƙoƙarin yaga ya farantama ɗan uwansa ba wanda ya taɓa jin kan su koda ma kuwa sun ɗan samu sa'bani bazai wuce na yan awanni ba su shirya hankalin su kwance business ɗin su na tafiya yadda ya dace
End
ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH 🙏na gode Allah da ya bani ikon kammala wannan littafin abunda na rubuta ba daidai ba Allah ya yafe min my lovely fans i love U wujiga wujiga Allah ya barmu tare sai mun haɗu a sabon book love u all 💔❤️❤️🙏😊
An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 13