ne? Mu je ciki" ya juya Ammie ta ƙara sa shigowa suka yi ciki, su Rukayya suka gaidasa ko alamun amsawa bai yi ba Ammie tace "Please ku ɗan bamu waje" Duk suka tashi har aunty suwaiba, ya wuce ya kwanta saman gado sai yanzu ya lura da Noor dake kwance saman gadon tana bacci
"Wai taron me ake ne a gidan? Me yake faruwa?" Ya faɗa yana lumshe idanu " Hidimar auren ka muke yi" Kamar wanda bai ji abunda tace ba can ya zabura ya miƙe ya kalli Ammie yace " Me kika ce Ammie ?Kamar kunne na ya jimin ba daidai ba" Ammie tayi murmushi tace" Hidimar auren ka yau aka ɗaura ma aure " ta faɗa tare da wucewa wajen fridge
Azaad ya nuna k'irjinsa da hannu yace " Ni aka ɗaura ma aure" Yayi wani murmushi wanda yafi kuka ciwo, Ammie ta miƙa masa lemon da ta ɗauko masa yace " Ammie wai gaske kike ko wasa?" Mun taɓa irin wannan da kai Azaad baka ji ba yadda daddynku bai yi ba akan ka fito da mata har lokaci ya sa maka amman kayi bulus nima ban so hakan ta kasance ba amman ka kai sa ƙarshe naso ka fitar da wacce ka ke so yanzu komai ya ƙare dan har an ɗaura aure nan da sati uku zata tare ya ma ce na sanar maka kasa a gyara gidan nan a zuba duk abunda babu kayan abinci a kai komai da ake buƙata wajen girki saboda ya sanar da iyayen yarinyar ba'a buƙatar komai " Azaad kasa magana ma yayi idanunsa sun yi jajirrr tashi kawai yayi ya fita
Kwana biyar da aure aka kawo lefe akwati dozin biyu komai an saka mata cikin lefe babu ne kawai babu a ciki, Mommy da ka kalleta zaga ka baƙin ciki ƙarara a fuskarta bata taɓa tunanin arzikin su yakai haka ba sai yanzu da aka kawo lefe da kayan sa ruwa kuka zahiri ne kawai bata yi ba amman tayi na zuci dan tayi nadamar k'in amincer da tayi tun farko da yanzu y'arta ce da wannan kayan sai yadda suka so amman yanzu Mamma ta hakimce komai sai yadda tace ayi haka ake yi, tsawon sati biyu Mamma na bama Alesha maganin sanyi sannan ana mata dilka ta gyara jiki sai da akayi sati biyu ciff sannan ta fara bata wani hatsabibin maganin mata mai kyau da inganci tsumi mai kyau ga gumba kala kala ko wace da lokacin da zata sha ta
'Bangaren ango ba wani shiri da ake yi ango auren nan ko a jikinsa walima kawai za'a yi ranar da amarya zata tare, An yi ma amarya lalle mai kyau ya zanu a fatarta washe gari aka yi kitso k'ananu sosai Alesha tayi kyau haskenta ya ƙara fitowa fatar ta tayi clear tun da aka ɗaura aure har zuwa yau da amarya zata tare ango bai taɓa zuwa ba bata san sa ba shima bai san ta ba babban abunda ya ƙara tayar ma da Alesha hankali kenan ƙarfe goma na safe aka fara walima saboda ƙarfe biyu gidan miji zasu turo a ɗauke ta za'a je da ita ƙarfe huɗu suma suyi walima ƙarshe shida akai amarya ɗakin ta
Sha biyu daidai aka gama walima Mamma ta ja ta suka wuce ɗaki sai kuka take, Mamma ta sa ta rage kayan jikinta ta shiga toilet tayi wanka koda ta fito daga wanka ta fitar mata da kayan da zata saka, ta shirya cikin wani material mai shegen kyau da tsada ga awarwaron hannunta masu kyau tasa sark'a mai haɗe da yan kunne da abun hannu ta yafa mayafi Mamma ta miƙa mata jakarda sai gashi an faɗa musu gidan miji sun turo motoci Alesha kawai ta fashe da kuka mai ban tausayi ta rirrik'e Mamma.....................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
Wannan shafin sadaukarwa ne a gareku masoyana masoyan asali 🥀❤️❤️❤️ina matuƙar k'aunar ku Ubangiji Allah ya faranta muku ya shiga lamuran ku Allah ya barmu tare, ina son ku matuƙa🧡🧡🧡💛🩶♠️❤️❤️❤️❤️🥀🌷
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 11 & 12
Mamma ta daure zuciyarta ta hana kanta kuka ta kama Alesha ita da kanta ta saka ta mota suka wuce, har suka isa gidan Alesha na kuka sai dai yanzu kukan nata ba mai sauti ba ne, gidan an cika har anyi shirin walima an kafa baranda ga kujerun zama duk an aza, mutane a ka yi taro suna san suga fuskar amarya Aunty binta 'yar uwar su mamman taƙi yadda da a buɗe mata fuska suka yi cikin gida
Ammie ta tarbesu hannu biyu biyu ta kai Alesha har ɗakin su Rukayya dan ta samu ta zauna ta huta, Ammie ta hana kowa shigowa ɗakin daga ita sai Aunty binta sai amaryar, Ammie ta zauna kusa da Alesha tasa hannu ta yaye mayafin da ke kanta fuskarta ɗauke da murmushi lokacin da tayi arba da face ɗin Alesha ita kanta bata san lokacin da kalmar "Ma sha Allah tabarakallah" ta fito mata ba saboda ko kaɗan bata yi tunanin Alesha ta kai kyawon haka ba bugu da k'ari amincewa da tayi da wannan auren duk da bata taɓa ganin yaron ba wannan ya tabbatar ma da Ammie yarinyar na da tarbiya ta samu raino mai kyau ga kuma alamun kunya a tare da ita ko kallan Ammie ta kasa kanta na ƙasa lokaci ɗaya Ammie taji Alesha ta shiga ranta tana farin ciki na ganin ɗanta ya samu matar kirki
"Daughter ki saki jikin ki daga yau kema kin zama y'arta kamar yadda na haifi Azaad yake kira na da Ammie kema yanzu duk matsayin ku ɗaya a waje na Ina rok'on Ubangiji Allah yasa wannan auren ya zama sanadiyar farin cikin mu baki daya" Amin ya Allah "Aunty binta ta faɗa
Ammie tace" Bara na baki ɗan tak'aitaccen bayani y'ar yan mu huɗu maza biyu mata biyu Aminu Azaad Rukayya Husnah, Azaad shi ne yaron mu na biyu a gidan nan ban sani ba ko an faɗa miki ya taɓa aure matarsa ta rasu wajen haihuwa yana da yarinya ɗaya sunanta Amina ana kiranta da Noor yayansa kuma yana da mata ɗaya da yara biyu sai k'annensa Rukayya da husnah dake karatu yanzu ma sun fita ne suna tare da k'awayensu zasu haɗa dan biki a gidan gwaggwan su na kin gan su, abunda zan faɗa miki nasan kafin ki zo gidan nan an faɗa miki shi zan dai ƙara tunasar da ke ne kawai Daughter Shi aure da kike gani ɗan hak'uri ne yau da daɗi gobe ba daɗi sannan duk wanda yace zo mu zauna to yace zo mu saɓa saboda dole wata rana sai an samu rashin fahimta a tsakani daughter bazan 'boye miki ba wallahi sai kin yi hak'uri sosai da Azaad ni na haifesa cikin halayyarsa ba wanda ban sani ba sai kin jure kin zage damtse kafin ku fahimci juna mutum ne shi mai wuyar sha'ani amman idan kin fahimce shi kuma mutum ne mai sauƙin kai muddin kika fahimci abubuwan da yake so da wanda baya so kika fahimce su kuma kika kiyaye wallahi zaki ji daɗin zama da shi abu ɗaya nake muku fata Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyaba Allah ya kwauda duk wata fitina da tashin hankali a zamantakewar ku kar na cika ki da surutu bara na baki waje ki huta nan da awa ɗaya dan Allah ki samu ki shirya dan a fara da wuri a gama" Alesha ta gyad'a kai Aunty binta ta yaba sosai da Ammie
Ammie ta fito ta basu waje ta koma wajen baƙi, da wuri ko aka fara walima biyar da rabi aka gama Amarya ta sake wanka aka jera motoci ta shiga suka wuce gidan ta
Ba k'arya wallahi gidan ya haɗu over, tun daga bakin gate zuwa harabar cikin gidan sai gaf da ƙofar shiga ciki motar amarya ta tsaya suka fito, kana tura kanta cikin falon wani sanyayyen sanyi mai haɗe da ni'imantaccen k'amshi zai kai ma hancinka ziyara, wasu dangararrun kujeru ne masu kyau aka zuba a falon ga k'atuwar tv bango mai tsawo da faɗi duk da ba'a wani sa kayan kyale k'yale sosai ɗin nan ba amman falon yayi mugun kyau kai abun sai wanda ya gani
Direct bedroom aka wuce da ita nan ma an gyara mata shi sosai, mutane suka musu fatan alheri suka wuce gidan ya rage daga ita sai Aunty binta, sai da aka yi sallahr isha'i Aunty binta ta wuce aiko Alesha taci kuka kamar ranta zai fita idanunta sun yi jajirrr ta dawo falo ta zauna saman kujera tayi tagumi har goma ta buga tana wajen ta ƙara gyara zamanta daga haka bacci yayi awon gaba da ita ba ita ta farka ba sai ƙarfe huɗu na dare ta miƙe ta wuce bedroom kai tsaye toilet ta wuce tayi alwala ta fito tayi tsaye tana dubin inda zata ga sallaya ganin bata gansa ba ta wuce wajen wardrobe ta buɗe nan ta hangota sama ta ɗauko tare da hijab ɗin da ke wajen ta shimfida sallaya ta saka hijab ta kabarta sallah, sai da aka fara sallar asuba sannan ta dakata tayi sallahr asuba ta cire hijab ta nad'e sallaya ta mayar ta faɗa toilet tayi wanka ta fito ɗaure da towel ta shafa mai ta fesa turare ta buɗe akwati ta fito da wata riga marar nauyi ta saka ta faɗa gado ta kwanta ta janyo wayarta ta lalubo number Mamma kiranta taso yi sai kuma ta fasa ganin safiya bata ko ida wayewa ba ta aje wayar ta kwanta bacci ya sake ɗaukarta
Ammie tun da ta tashi sallah bata koma bacci ba ta sauko ta shiga haɗa ma amarya breakfast da kanta koda takwas tayi ta haɗa komai har su yau ita tayi musu breakfast ta shirya na amarya ta haɗa komai ta saka cikin basket, ta wuce ɗaki dan ta shirya
Zuwa ƙarfe goma kowa ya shirya ya fito dan yin break, har sun fara cin abinci sai kawai suka ga Azaad yana saukowa Ammie da Dad suka kalli juna kusan gaba ki ɗayan su abun ya basu mamaki ganinsa gida kuma ga dukkan alamu gidan ya kwana, hankalin sa kwance ya ƙara so wajen su ya ja kujera zai zauna Dad ya haɗe rai yace " Kai kuma daga ina? Me ka ke min a gida da wannan sanyin safiyar Azaad? Kar dai abunda nake tunani haka ne? A gidan nan ka kwana?" Azaad yayi shuru alamun rashin gaskiya ya bayyana a fuskarsa
"Azaad kana nufin yarinyar nan ita kaɗai ta kwana a gidan nan? Innalillahi wa inna ilaihiraji'un wai dan Allah wane irin mutum ne kai" Ammie ta faɗa tare da dafe kanta tana jin wani irin k'una a cikin zuciyarta "Yanzu a ganin ka kayi ma yarinyar nan adalci? muma iyayenka ka muna adalci kenan? " Bar ni da shi kawai wallahi yanzun nan tun kafin raina ya ƙara 'baci ka fice min a gida ka wuce gidan ka kai bari ma kaji yau yau nake san ka kwashe duk wani tarkace da ya zamo naka a gidan nan ka kai gidan ka ai kaji ni?" Azaad bai ce uffanba Dad ransa ya 'baci yace"Zaka fice min a gida ko sai na taso?" Sumi sumi ya kama hanya Ammie tace"Dakata " ta tashi ta shiga kitchen ta ɗauko basket ta wuce gabansa ta aje tace"Abinci ne ka ɗauke sa kaje ka kai mata " abincin ya kalla da sauri ya kalli Ammie yace" Haba Ammie kina nufin ni zan kai mata abinci?" Ko kafi ƙarfin ka kai ne? Eh idan kafi ƙarfin kaje aikin da nayi ma ne sai na ji" ba dan ransa yaso ba ya ɗauka har ya kama hanya Noor dake zaune a wajen tace" Papah zan bika " wani mugun kallo ya yi mata zai ɗauke kai suka haɗa ido da Dad yace " Sai kaje da ita wallahi sai ta bika tashi ki bisa ki je kiga mommyn ki" Noor ta miƙe da sauri tana farin ciki
"Yaro sai taurin kai da bak'ar zuciya sai dai ka mutu sai ta bika" Dad ya faɗa
Azaad yayi gaba abusa Noor ta bi bayansa da sauri har ya fita, ya buɗe mata gaba ta shiga ya saka kwando ya shiga ya ja motar tsiyace
Alesha sai goma saura ta tashi ta shiga tayi wanka ta fito ta shirya cikin wani material maroon mai haɗe da mayafinsa sai k'amshi take zubawa ta fito falo ta zauna sai kallon falon take yi ya mata kyau sosai, ko kaɗan bata ji alamun buɗe gate ba saboda daga wajen gate ɗin su zuwa nan akwai yar tazara kuma gate ɗin ba mai ƙara ba ne bare idan aka buɗe ka sani sai kawai jin tayi ana faɗin " Mommy! Mommy" ta juya ta kalli ƙofar daidai ita ma Noor na kallan wajen da take cike da farin ciki tace " Mommyyyyyy" ta shek'a a guje wajenta Alesha farin ciki ya mamayeta sosai ta buɗe ma Noor hannu tana zuwa ta ɗagata sama ta rungume........................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 13
Dukan su suka shiga cikin wani irin farin ciki marar misaltuwa musamman Alesha da take jin kanta cikin kad'ai ci sai ga shi Allah ya kawo mata Noor, sun yi minti uku rungume da juna sannan ta sauketa ta zauna saman kujera ta ɗauketa ta ɗaura saman ƙafafunta " Mommy ba za ki sake tafi ki barni ba ko?" Alesha ta gyad'a mata kai tace " Daga yanzu duk inda zan je muna tare" Yeeeeeeeeeeee mommyna ba zata sake tafiya ta barni ba " Noor ta faɗa tana jin daɗi yan ƙananun hak'oranta suka bayyana
Azaad dake tsaye yana kallan su ganin kamar daman can sun san juna dan daga ganin irin wannan shak'uwar ta su zaka san ba ta lokaci ɗaya ba ce, taɓe baki yayi ya ƙara so cikin falon ya aje basket ɗin hannunsa yayi hanyar bedroom, Alesha ta ɗago ta kallesa ta ɗauke idanunta a kansa ta mayar ga Noor dake ta zuba mata surutu
Ɗakin sa ya wuce daman ya kawo fiye da rabin kayansa a gidan yana shiga ya wuce gurin wani hoto dake manne a ɗakin yayi tsaye gaban hoton yayi murmushi ya shafi hoton ya wuce toilet ya sake wanka ya fito ya shirya cikin wasu k'ananun kaya da suka yi bala'in yi masa kyau, suna nan zaune a falo inda ya barsu tun da ya kallesu sau ɗaya bai sake kallan wajen da suke ba ya fice ya bar gidan
Kusan sati ɗaya da zuwanta gidan amman gaisuwar kirki ma ba haɗa su take yi ba daga ina kwana sai ina wuni, Tana zaune a falo tana waya da Mamma sai zuba mata shagwa'ba take yi Noor na kwance saman jikinta tayi bacci, ya shigo gidan ya sameta tana waya wallahi ba dan ta sa wayar speaker ba a yadda take wayar zaka iya ransuwa kace da namiji take waya saboda yadda take zubama Mamma shagwa'ba tana narke murya ita a dole sai Mamma ta zo ita kuma tace bazata zo ba, Azaad tsintar kansa yayi da tsayuwa yana kallanta duniya yana bala'in san shagwa'ba bare ma yadda yaga Alesha na yi ga shi tana magana dimple ɗin ta na lotsawa ba k'arya ta tafi da imaninsa
Alesha tayi tayi akan Mamma ta zo ita ko ta kafe bazata zo ba hakan yasa Alesha ta kashe wayar harda yan guntayen hawayenta tasa hannu ta goge, tana kashewa Mamma ta sake kira tak'i ɗagawa har sau biyu sai a na uku ta ɗauka ta kai wayar a kunne Mamma tace "Kinga har kinsa na manta abunda zan sanar miki sai yanzu ɗazu yar uwarki Ummie ta kira ni tace na tura mata da a direshin gidan ki zata zo " Okay"Alesha " Uhm" Fushi kike da Mamma?" Uhh.....uhmm...ni.......ni ban ce ba" a yadda tayi maganar wallahi dole ta baka dariya Azaad sai da ya murmusa, bansan me Mamma tace mata ba tayi dariya ta aje wayar ta ƙara gyara ma Noor kwanciyarta ta ɗan juya taga Azaad, sai da ta ji kunya dan bata san shigowarsa ba, Fuskarsa yau sake har da murmushi kamar taga yana yi
Yunk'urawa tayi ta taso ta zame Noor daga jikinta a hankali ta kwantar da ita saman kujera ta sauka ta duk'a ta gaidasa ya amsa faram faram ya ƙara so wajen ya samu waje ya zauna, ta wuce ta ɗauko masa ruwa ya kar'ba ya sha, ita kanta abun har mamaki ya bata ganin yadda yau ya sakar mata fuska har ya zauna wajen da suke ta kawo masa ruwa ya sha wanda sai dai ya je ya ɗauko da kansa ko da ko ta kawo masa
Noor ya kalla yace "Bacci take yi?" Eh " ta faɗa tare da komawa wajen da Noor take ta zauna, tashi ya yi ya wuce ɗakinsa yayi wanka ya sanya gajeren wando da vest ya fito riƙe da wayarsa yana latsa
Kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kanta ya zo ya zauna ta tashi taje kitchen ta zubo masa abinci ta kawo fried rice ce ta zuba dafaffen wake a gefe ta kawo onion source ta zuba ga rabin soyayyar kaza a gefe k'amshin abincin kawai ya bugi hancin sa yaji yana san cin abincin ta koma ta dauko masa abun sha koda ta dawo sauka ya zauna saman kafet ɗin tsakiyar falon yasa abinci a gaba ga waya a kunnensa da alama waya yake yi, tana ajewa ta ɗauki Noor suka yi ɗaki ta kai Noor toilet tasa tayi fitsari suka fito ta kwantar da ita saman gado taci gaba da bacci
Yana gama waya ya aje ta a gefe bai ko yi amfani da spoon 🥄 ba yasa hannunsa lomar farko da ya kai baki sai da ya lumshe ido a kan daɗin da abincin ya masa wallahi zama yayi ya buɗe ciki yaci sai da ya k'oshi kaɗan kawai ya rage, Alesha ta fito ta ɗauke kayan ta kawo masa ruwa da waje ya wanke hannunsa ta yi zaune a falo duk da tana jin nauyin kallansa a haka ya kunna musu kallo
Kusan watan su biyu da kwanaki da aure yanzu sun ɗan fara sabawa dan har zama suke yi suyi fira ko suyi kallo tare idan ya dawo aiki baya zuwa ko ina yana gida kasancewar yau weekend ce baya zuwa aiki yana gida, kwance yake saman Three siter yana dannar waya sai ga kiran gate man ɗin su ya shigo ya ɗaga tare da faɗin " Ya aka yi ne?" Wata ce tazo wajen Hajiya " Wata! Wata to wace?" Yana jin lokacin da mai gadi ya tambayi sunanta ya sanar masa yace " Okay bara na bincika idan nan ne" Okay sir " Ya katse kiran ya dallama Noor kira dake cikin kitchen tare da Alesha, sai ga Noor tazo yace" Je ki kiran Mommynki " To" taje ta faɗa ma Mommynta tazo, yaji zuwanta amman sai yayi kamar bai ganta ba yaci gaba da latsar wayarsa tace " Abban Noor kana nema na?" Kin san wata Ummie?" Sai da gabanta ya faɗi jin tambayar da ya mata
Bakinta na ɗan karkarwa tace " E....eh na santa" Miye haɗin ki da ita?" Ya faɗa tare da ɗagowa ya kalleta tace" Kanwa ta ce " Okay" ya faɗa ya zata yaji tace k'awarta ce da wallahi ba zai bari ta shigo ba dan shi bai san gayyar tsiyar nan, Ya kira mai gadi taji yace " A barta ta shigo " ta juya zata koma kitchen ta tsinkayo muryarsa yana faɗin " Idan ta iso wa zai buɗe mata ƙofa?" Ko ida rufe bakinsa bai yi ba Ummie ta fara buga ƙofar kamar zata 'ballata
Ta wuce taje ta buɗe mata, Kamar ta bangaje Alesha tayo cikin falon ta riƙe k'ugu " Wannan wane irin iskanci ne da rainin wayo zaki sa a tsare ni bakin gate ana min tambayoyin rainin wayo dan kin samu an zo gidan ki wallahi ba dan sak'on da Mamma ta bayar ba tace na kawo miki ba da wallahi nayi tafiyata rainin wayon banza wallahi ai wulak'anci ne" Yi hak'uri dan Allah wallahi ba laifi na ba ne "
Azaad dake kwance yana jin yadda Ummie ke ta yi ma Alesha bala'i kamar zata doketa abunda ma ya basa mamaki Alesha ta ce masa k'anwarta ce amman yadda take yi mata bala'i kamar ita ta haifeta, "Noor! Noor " Yes Papah" come " Ummie dake bala'i bata san lokacin da ta juya tana kallan wajen da taji sautin muryarsa ba ko cikin magagin bacci take ba zata taɓa manta wannan muryar ba ɗaga kanta tayi idanunta suka sauka akan hotonsa dake manne a falon idanu ta buɗe tana kallan hoton, kusan suman tsaye tayi lokacin da tayi arba da kyakkyawar fuskarsa ya miƙe......................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 14
Wani wulak'antaccen kallo yayi ma Ummie tun daga sama har ƙasa ya zubar ya ɗauki cup ɗin shayinsa yayi gaba Noor ta bi sa a baya, Ummie ta bi sa da kallo har sai da ta daina ganinsa, ta juyo ta kalli Alesha muryarta ta ɗan yi sanyi tace " Waye wannan?" Ta faɗa tare da kafeta da ido
"Abban Noor ne" ta bata amsa " Kina nufin shi ne wanda aka aura miki?" Ta faɗa k'irjinta na dukan uku uku " Eh shi ne meya faru?" Alesha na faɗin haka cikin Ummie ya wani irin murd'awa yayi ƙara har Alesha sai da taji ƙarar cikin ai ko nan take gudanawa ya kamata a wahalce tace " Ina ne d'aki ?" Alesha ta nuna mata da hannu a guje tayi bedroom tana shiga ta faɗa toilet jin ka ke fatattattattatttttttttt fattttttttttttttt hutttttttttt fattttttttttttttt
Alesha ta duk'a ta ɗauki kayan da ta shigo da su ta wuce bedroom, akan ƙarar zawon har Alesha sai da ta ji tace "Subhanallah to me yake damunta? Me taci ya 'bata mata ciki haka " Ta aje kayan tayi tsaye, sai ga Ummie ta fito a wahalce kamar zata yi kuka ta wuce gado ta zauna Alesha tace"Sannu bakya jin daɗi daman?" Ummie ta ɗago ta kalleta ta 'balla mata harara ta buɗe baki da zummar magana cikin ya sake murd'a mata ta miƙe ba shiri ta koma toilet, ko da ta fito kamar mai koyon tafiya a hankali take takawa ta zo ta zauna " Sannu kin san bakya jin daɗi ai da kinyi zaman ki" Dallah ni ki min shuru ki barni da abun da nake ji wannan wane irin bala'i ne da masifa abar mutum ma ya huta baza'a yi ba " Allah ya baki hak'uri" Alesha ta faɗa tare da kama bakinta tayi shuru sai ga
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 13