Noor ta shigo tace " Mommy papah yace na kira ki" To zo kije ki zauna kusa da aunty bata jin daɗi " To Mommy" Kiyi mata hannu kinji?" Noor ta gyad'a mata kai
Alesha ta fita Noor taje kusa da Ummie tayi tsaye
Alesha taja tayi tsaye bakin k'ofar d'akin Azaad, duk tsawon lokacin nan bata taɓa saka ƙafarta a d'akin sa ba, kamar wacce za'a yi ma wani abu sai da ta runtse ido sosai sannan ta ɗago hannu ta k'wank'wasa k'ofar ta kusa minti uku sannan taji yace shigo, bakinta ɗauke da sallama ta shiga yana zaune gefen gado yana duba wayarsa da alama wanka ya fito saboda ya sauya kaya yanzu daga shi sai gajeren wando fari da vest fara ga alamun ruwa nan a jikinsa ta fara kallan d'akin yayi kyau sosai kamar ma yafi nata kyau ta kalli gadon ta gansa duk a hargitse d'akin ma yana buƙatar shara ta mayar da idanunta kansa, Alesha ta kafesa da ido tana kallan k'irar jikinsa ya ɗago kansa yaga yadda take kallansa ya ɗauke kansa yayi kamar bai ganta ba ya mayar da kansa ƙasa dagowarda zai yi suka haɗa ido tayi saurin ɗauke kanta yayi murmushi yace " Ina abunda nasa ki dafa min?" Sorry wallahi na manta amman yanzu zan yi na kawo "Okay" ta wuce ta fita taje kitchen dan dafa masa tea ɗin da ya sakata
cikin yar' ƙaramar muryarta ta yara tace" Mommy ta ce na miki sannu bakya jin daɗi? " Ummie ta gyad'a mata kai" Uhm ni ma lokacin sai da papah ya bani magani na sha " Mtwwssssssssssssss naji dan Allah" Ummie ta faɗa cike da jin haushi dan gaba ɗaya haushin su take ji Noor tace " Aunty kema na je na ce ya baki" Ke!" Ta dakama Noor tsawa"dallah rufe min baki zabaya uwar surutu " ta faɗa tare da harararta, Noor sai da ta tsorata ta ja baya tana san yin kuka Ummie hankalinta na kan k'ofa tana Allah Allah Alesha ta dawo amman shuru shuru Noor ta juya ta kama hanya ta fita
Tana fita sai ga Mommynta zata je d'akin Azaad tace "Mommy ni bazan zauna tare da ita ba kuma ni bana son ta" ta faɗa tare da shigewa jikin Alesha " Be careful princess tea ne a hannu na da zafi, Meyasa bazaki zauna da ita ba?" Bata bata amsa ba ganin haka yasa tace"To mu je a kai ma papah tea yana jira "Suka wuce ta kai masa " Ummie jin tayi kamar ta tashi tabi su taje taga me suke yi sai addu'a take "Allah yasa ba wani abun suke yi ba na shiga uku " Wani tunani ya faɗo mata a rai tayi ihu da ƙarfi tace "Wallahi bazai yiwu ba nasan ba abunda zai yi da ita" ta dafe kanta tana jin yana mugun sara mata, ta ciro wayarta daga jaka ta lalubo wata number ta fara kira
Har kiran ya tsinke ba'a ɗaga ba ta sake kira sai da ya kusa katsewa aka ɗaga tace "Rufi na shiga uku Shikenan" ta faɗa tare da fashewa da kuka ta cikin wayar rufi tace " Ummie lafiya meyake faruwa? Waye baya da lafiya? " Ta tsagaita kukan tace "Wallahi dama a ce wani ne baya da lafiya zai fiye min sauk'i akan wannan abun" Topah meyake faruwa naji harda kuka big girl dake haba kar ki bada mu mana " Rufi ba zaki gane halin da nake ciki ba ne shiyasa baza ki gane damuwar da nake ciki ba wallahi ina cikin tashin hankali " To naji daina kukan faɗa min meyake faruwa?" Ummie ta share hawayenta tace" Rufi kin san wannan saurayin nawa wanda muke nema dai?" Eh wanda kike mutuwar so ɗin nan ko wanda muke yawon nema? Yes yes shi Rufi wai a she shi ne ya auri Alesha " What" Rufi ta faɗa da ƙarfi "Oh my God, wace Alesha dan ni Alesha ɗaya na sani yar' uwar ki" Hmmmmm Rufi ita ce ita ce wallahi ta aure sa " Kutumar uba taya aka yi haka ? Alesha fa "Rufi kin san na faɗa miki auren da Daddy yaso ya min naƙi amincewa to shi ne ya tunkari Alesha da maganar ta amince a she ban sani ba mutumen da nake ta nema nake mugun so shi ne aka tashi aura min naƙi amincewa "Ta faɗa tare da fashewa da matsanancin kuka
Rufi ta lallasheta ta daina kuka tace "Ki kwantar da hankalin ki in sha Allah na miki alƙawarin sai kin auresa sai ya so ki fiye da yadda kike son sa"Taya kenan Rufi?" Ohhh daɗina dake rashin hak'uri ki jira ki ji me zan faɗa ba kin ce auren na haɗi ne ba?" Eh " Kenan basa san junan su?" Eh" Ai ta kwana gidan sauk'i to ke da kika zo gidan kinga alamun ba su damu da juna ba?" Ummie tayi shuru can tace " Ni dai banga alamun so ba kuma banga alamun ƙiba " Kina ina ne yanzu?" Ina cikin gidan " okay su suna ina" Tun d'azu ya aiko yar'sa kiranta suna can tare "Topah wata sabuwa kinsan shawarar da zan baki yanzu?" Aah sai kin faɗa " Yawwa Ki kasan ce mai zama inda zai riƙa ganin ki a koda yaushe idan ya juya sannan ki riƙa yi masa kalamai masu taushi da jan hankali ta tafiya mai ɗaukar hankali kina jan wanka kina ɗan saka kaya masu kama jiki sannan idan yasa matarsa aiki kiyi maza ki karɓe aikin kije kiyi komai wahalar sa sannan kada ki riƙa barin su su biyu kawai a waje ki je ki zama ta ukun su komai za'a yi ayi a gaban idon ki sannan sai kin ɗan tsaya kin lura da abunda yake so saboda ki riƙa yi masa shi to in sha Allah muddin kika yi haka da kaɗan kaɗan zaki fara shiga ransa har yaji yana son ki ki mamaye zuciyarsa wannan plan A ne idan bai yi aiki ba zamu sake gwada wani " Allah k'awata kina ko ganin plan A ɗin nan zai yi aiki? "Sosai ma ke dai kiyi abubuwan da na ce kawai zaki sha mamaki "Wallahi shiyasa nake son ki har kin kwantar min da hankali"Kar ki damu Allah yasa kawai mu dace Mrs Azaad " Amin har kinsan naji wani sanyi sunan nan da kika kira ni da shi" Wannan sunan ai naki ne da ke kaɗai ya dace " Allah ko rufi?" Eh mana....................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 15
Rufi ta ƙara bata shawarar abunda zata yi suka yi sallama zuciyarta cike da farin ciki ta share hawayenta ta tashi ta shiga toilet ta wanke fuskarta ta fito, Alesha ta shigo riƙe da magani ta miƙa mata, bata yi mata wata gardama ba ta kar'ba ta sha dan har lokacin tana jin cikinta na murd'awa, sai da ciwon cikin ya lafa mata ta fito falo tun daga nesa ta hangosa zaune saman kujera ya miƙe ƙafafunsa yana kallan ƙwallo, sai da ta tsaya ta ƙara gyara rigarta ta gyara tafiyarta tana tako ɗai ɗai, ta ƙara so ta kwana kusa da kujerarsa Noor na kwance saman one siter tana buga game da wayar Mommynta Ummie ta gyara murya tace " Lahhh a she kai ma kana kallan ƙwallo kamar ni kenan" ta faɗa tana murmushi, Azaad juyowa kawai yayi ya kalleta ya ɗauke kai bai ko ji lokacin da ta iso falon ba ta sake cewa " Na lura kamar kana san ƙwallo sosai ko magana baka san yi" Uhmmmmmmmhhhhh" ya faɗa hankalin sa na kan tv
Ganin dai yaƙi kulata yasa duk taji wani iri Alesha ta fito daga kitchen ta jera abinci a dining, ta yo cikin falon tayi sallama ya juyo ya kalleta ya amsa sallamar
Ta ƙara sa wajen Azaad tace" Yaya abincin ya kammala " Okay kawo min shi a nan ban cika san hawa saman can ba" To Shikenan " Alesha yi zamanki kawai ki huta bara na kawo masa abincin kin yi girki kin gaji da yawa " Alesha ta kalleta Azaad ma haka sai dai shi kallan mamaki yake mata na jin ta kira sunan Alesha gatsai ba ko aunty wanda ko ba'a faɗa ba ka kalli fuskar Alesha ka kalli ta Ummie zaka san Alesha ta girmi Ummie but saboda rashin tarbiya ko karrama sunanta bata yi
Alesha ta buɗe baki zata yi magana Azaad ya yi saurin riganta yace"Madam je ki kawo min abinci da wani iyayin banza " Alesha ta wuce ta je ta haɗo masa abinci ta kawo masa harda lemon juice da ta haɗa yayi daɗi har ya gaji
Ta kalli Ummie tace "Bisimillah mu je mu ci abinci" Ummie ta ɗan yatsina fuska tace " Ku ci kawai bana jin yunwa" ta faɗi hakan ne kawai ba wai dan bata jin yunwa ba sai dan ta samu damar da zata yi magana da Azaad tun da ba waje ɗaya zasu zauna su ci abinci ba, Alesha kawai tace " okay" ta wuce wajen Noor ta karɓe waya ta aje tace " lokacin cin abinci yayi" Mommy sauran kaɗan a cinye ni " To ai ba'a cinye ba ko?" Noor ta gyad'a mata kai "Yawwa idan kika ci abinci sai ki ci gaba okay" Okay mommy " Yawwa good girl Allah ya miki albarka"Amin " Noor ta kalli filet ɗin Abbanta tace" Mommy zan ci a wajen Daddy "Aah muje mu ci namu kawai" Noor ta ɓata fuska Azaad dake kallan su yace " Zo mu ci " Tayi dariya tare da saurin sauka Alesha tace "Bara na kawo miki spoon" Ki ɗauko biyu " Azaad ya faɗa taje ta ɗauko yace ita ma ta zauna tare zasu ci, bata san yi masa musu ga shi kuma Ummie ta kasa ta tsare shiyasa kawai ta zauna suka fara ci
Ummie baƙin ciki kamar zai kasheta har wani abu take jin yana taso mata tayi danasanin cewar da tayi bata cin abinci da yanzu duk tare zasu ci waje ɗaya daga ƙarshe dai haushi ya isheta ta tashi tayi ɗaki, suna canyewa ta tashi ta ƙaro musu bata ƙoshi ba wallahi amman ta miƙe kawai tace ta k'oshi ta miƙe ita ma Noor ta tashi tace ta k'oshi shi kaɗai aka bari sai da yaci ya k'oshi ya miƙe ta kwashe kaya ta gyara wajen, ya koma saman kujera yaci gaba da kallo
Alesha ta sullace tayi d'akinsa ta gyara ko ina ta share ta sa turare ta wuce toilet ta haɗa ƙananun kayan sa ta wanke ta shanya su nan cin bayin ta wanke toilet yayi fesfess ta sa turaren toilet ta fito ta koma falo bayanan yayi masallaci Noor kuma tayi ɗaki ta wuce d'aki tun kafin ta ƙarasa take jiyo sautin kukan Noor da sauri ta ƙara sa tana shiga Noor ta rugo a guje wajenta ta rungume hankalin Alesha duk ya tashi tace "Lafiya meya faru? Wa ya taɓa ki?" Alesha ta jata suka zauna ta rarrasheta ta sake tambayar ta Noor tace " Mommy ban gan ki ba shi ne na tambi aunty tace wai kin ɓata " Jin abunda Noor ta ce yasa Alesha ta sauke ajiyar zuciya tace"Wannan abun ne yasa kika tada hankalin ki?aunty fa da wasa take miki ba gani ba bazan ɓata ba muje muyi sallah ko " Suka wuce bayi dan yin alwala duk wannan abun da ake Ummie na zaune tana latsar waya
Ummie ta kira Mommy ta sanar mata gidan zata kwana
Azaad yana dawowa masallaci ya wuce d'aki yana shiga sanyayyen k'amshi ya kaima hancinsa ziyara ya kalli d'akin yaga yadda ta gyara masa shi, Shi kansa wallahi d'akin ya burgesa ya wuce toilet dan yin wanka nan yaga aikin ta tasha ya ji bala'in daɗi cikin annashuwa da farin ciki yayi wanka ya fito ya shirya cikin wani yadi fari mai layi layi ya kafa hula sai baza k'amshi yake yi kamar inda aka yi 'barin turare ya fito nan falo ya same su Alesha na ta fama da Noor akan ta bata waya ta kira Mamma Noor taƙi, Azaad da ya daka mata tsawa sai da wayar ta faɗi jikinta ya fara rawa hatta Alesha sai da jikinta ya ɗau rawa Ummie ta mak'e cikin kujera yace " Wane irin siririn iskanci ne zata yi using da waya baza ki bata ba wallahi kika bari na sake ganin haka sai na saɓa miki" Noor ta lab'e bayan Alesha dan tasan ba ƙaramin aikin sa ba ne yanzu ya zane ta yace " Ɗauko wayar ki bata" Ta ɗuka ta ɗauko ta bata
Yace " Sai na dawo" Allah ya tsare " Ya kama hanya yayi ƙofa Alesha ta juyo ta ɗauki Noor idanunta cike da hawaye Azaad ya kusa kai bakin k'ofa ya tsaya ya juyo da niyar yi ma Alesha magana sai yaji tana faɗin" Yi hak'uri kar kiyi kuka kinji kyale papah baza mu basa waya yayi game ba ko?" Noor ta gyad'a mata kai, Azaad yayi murmushi juyawar da zai yi suka haɗa ido da Ummie da take jin kamar ta haɗesa tsabagen yadda take ji ya ɓalla mata harara ya buɗe ƙofa ya fice da dare taga Alesha tayi wanka tayi ma Noor tasa kayan bacci a tunaninta d'akin Azaad zata je amman sai taga sun haye gado sun kwanta taji wani irin daɗi sai da taga sun yi bacci sannan ita ma ta kwanta
Ummie kwanta huɗu a gidan duk abunda Rufi tace tayi tana yi amman mai makon ta samu yabo sai dai zagi, Azaad ko kallo bata isheshi ba Allah ya gani ya gaji da ganinta a gidan duk ya takura
Alesha na d'akin sa tana gyara ya shigo ya zauna bakin gado ya kalleta yace "Wai yaushe wannan zata tafi? Wallahi bazan ɓoye miki ba sai dai kiyi hak'uri Allah ya gani zamanta a nan yana takura ni mutum da gidan sa baya da ikon yin yadda yake so yanzu haka zama a falon sai naji duk na takura duk inda tayi sai naga tana kallo na wannan wace irin rayuwa ce fisabilillah mutum yayi magana kuma a ga laifinsa to ni wallahi ba ruwana faɗi na ke sai dai a ga laifi na " Alesha ta dakatar da abunda take tana sauraransa a zuci tace"A she dai bani kaɗai nake ganin irin wannan kallan da take maka ba " a zahiri kuma sai tayi murmushi tace" Yaya dan Allah ka ƙara hak'uri in sha Allah ina ganin ba zata wuce satin nan ba zata wuce " Shikenan amman dai wannan ba mamar ku ɗaya ba saboda naga gaba ɗaya kalar tarbiyar ku bama ɗaya ba" Alesha tayi murmushi tace " Iyayena sun rasu ɗiyar k'anen Abbanmu ce" ta faɗa muryarta tayi rauni
Azaad yaji gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi tayi bala'in basa tausayi yace "Allah sarki Allah ya gafarta musu"Amin ya Allah " taci gaba da aikinta
Ummie sai da ta kwana shida a gidan sannan ta koma gida dan sake sabon shiri ganin plan A bai yi aiki ba
kasan cewar yau Monday ce ba kowa a gidan ita kaɗai ce tana zaune a falo ta tuna bata gyara d'akin sa ba ta tashi taje ta gyara ta share tayi mopping tasa turare har zata fita taga hoton mahaifiyar Noor manne ta wuce gaban hoton tana kallo tayi mata addu'a, sai taga alamun kamar hoton yayi k'ura ta kai hannunta ta taɓa hoton kawai ya faɗo glass ɗin sa ya fashe "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta faɗa, k'amshi turarensa da taji yasa ta juyo kamar wani zaki haka ya tunkarota fuskarsa babu alamun sauk'i gareta yana isa ya ɗauke ta da wani gigitaccen mari sai da tayi tangal tangal wallahi kamar zata faɗi ya daka mata tsawa ta manne ga bangon d'akin jikinta na rawa yace "Wallahi daman nasan ba da zuciya ɗaya kike shigowa d'akin nan ba kina ganin saboda kin fasa hoton ta zaki iya fitar da ita daga cikin zuciyata ne munafukar banza munafukar wofi fitar min daga d'aki " ya faɗa cikin ɗaga murya jikinta na rawa ta fara takawa ta ɗaga ƙafarta wani ƙaton glass ya shigar mata ƙasan ƙafa sai da ta gantsara hawaye na zubo mata taci gaba da tafiya duk inda ta taka sai ka ga jini ta kusa isa bakin k'ofa ashe ruwan da tayi mopping basu ida bushewa ba jinta kawai kayi ƙasa ta faɗi glass ya shige mata tafin hannun ta fashe da wani irin kuka jini zuba kawai ya ke yi......................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
Dan Allah ku sanya ni cikin addu'ar ku masoya 🥹 🥹 🥹 🙏 Ƙaunar ku ta riga da ta kama sassan jikina 💔💔❤️❤️💘😵💫 masoyana abun alfaharina ina matuƙar yin ku kamar yadda ku ke yi na Allah ya bar tare ya bar zumunci Allah ya saka muku da mafificin alkhairinsa Ubangiji Allah ya biya muku bukatunku na alheri Allah ya yaye muku dukkan wata damuwa ko'bacin rai da suke damun ku Allah ya faranta mu ku Ubangiji Allah ya baku arziki mai yawa mai albarka Amin ya hayyu ya gayyum 🤲🤲🤲🤲😘😘😘😘 i love u wujiga wujiga 💔💔💔💔❤️❤️🥀🧡Dan Allah ku sani a addu'ar ku masoya 🥹🥹🥹🙏💔❤️
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 16 & 17
Dak'yar ta miƙe taci gaba da tafiya tana kuka ta nufi d'akin ta tana dafa bango ko da ta isa ɗakin kamar rayuwarta zata fita saboda azabar da take ji ta faɗa gado ta rushe da wani marayan kuka tana mai nadamar shiga d'akin sa da tayi, sai da taci kukanta ta k'oshi kanta har ya fara ciwo bacci ɓarawo yayi awon gaba da ita
'Bangaren Azaad kuwa idanunsa sun yi jajirrr tana fita ya duk'a ya ɗauki hoton ya aza saman mirror ya fice daga gidan baya jin daɗin komai
Noor da aka tada su school gidan Ammie aka wuce da ita, tun da Azaad ya je da ita gida rabonta da su Ammie, Lokacin da taje yan gidan sun yi farin cikin ganin ta sosai
Misalin ƙarfe uku Azaad ya koma gida, tun da ya shiga falo yaji gidan tsiff sa'banin yadda ya sake tarar da shi, ko ya iske su Noor na ta zuba mata surutu ko suna kallo ko ta goya Noor a bayanta suna zagaye falon, D'akin sa ya wuce har zai shiga ya tsaya kallan jinin da duk ya ɓata wajen har zuwa hanyar dakin ta jinin duk ya bushe, wani iri ya ji a zuciyarsa ya juya yayi hanyar dakin ta yana kai bakin k'ofa ya ja ya tsaya yana tunanin ya shiga ko yayi tafiyarsa wata zuciya na faɗa masa ya kamata ya shiga ko dan ya duba halin da take ji gashi ko motsinta bai ji ba tun da ya shigo, da haka dai ya tura k'ofar ya shiga sanyayyen k'amshi mai haɗe da k'amshin turare ya bugi hancinsa, sai da ya ƙara buɗe hancinsa ya shak'i k'amshin, hangota yayi kwance saman gado ya nufi wajen tun kafin ya ƙarasa ya hango k'aton glass ɗin da ya shigar mata tafin ƙafa jini duk ya lalata zanen gadon ƙafar har ta kumbura tafin hannun ta kuma tayi ƙasa da shi jini har ya bushe ga tayis
Duk sai yaji ta basa tausayi yaji yayi nadamar abunda yayi mata, zama yayi gefen gadon ya kai hannunsa tafin ƙafar wajen glass ɗin wata irin zabura tayi ta farka daga baccin da ya ɗauke ta ya sake kai hannunsa ta fashe da kuka tare da janye ƙafarta, kallanta yayi ba tare da ya ce komai ba ya tashi ya fito ya barta tana kuka
Wayarsa ya ciro ya kira likitar gidan su tare da tura mata address ɗin gidansa, ba da jimawa ba yaji wayarsa na ringing ya duba yaga mai gadi ne ya ɗaga kiran tun kafin mai gadi yayi magana ya basa umurni da a barta ta shigo yana gama faɗin haka ya cire wayar a kunnen sa ya je bakin k'ofa ya buɗe har ta iso suka gaisa ya wuce da ita d'akin Alesha
" Wai wai sannu ya aka yi haka? " Likitar ta faɗa tare da zama tana kallan ƙafar Alesha da ta kumbura tace "Tun yaushe wannan abun ya sameta?" Zai kai awa huɗu " What? Awa huɗu ba'a yi gaggawar cire mata wannan abun ba yanzu silar haka wata cutar zata iya shigar ta fa gaskiya kun yi sakaci ban ji daɗin wannan abun ba wallahi kunyi sakaci musamman ma kai Azaad da ilimin ka da hankali ba zaka ɗauke ta ka kai ta hospital ba zaka barta a gida da wannan k'aton glass cikin ƙafa duba ka ga yadda saman ƙafar yayi duk ya kumbura " Shi kansa ya ga yadda ƙafar ta kumbura, Alesha ko jin su bata yi azabar da take ji kaɗai ta ishe ta
Aka zo za'a cire glass ɗin taƙi tsayi kuka Himmhimmmhimm sai da Azaad ya riƙe ta aka samu aka cire glass ɗin aka yi treatment ɗin ƙafar da hannu ta rubuta maganin da za'a siyo ta riƙa sha wanda zai sa wajen yayi saurin haɗewa
Ya je ya raki likitar ya sallameta koda ya dawo wani nauyayyen bacci ya ɗauketa, ya kafeta da ido tayi bala'in basa tausayi tunawa yayi da marin da ya mata ya runtse idanunsa da sauri tare da girgiza kai ya buɗe ido ya ɗago hannunsa da ya mareta da shi yana kallo yana jin rashin kyautawar abun da yayi mata idanunsa na a kanta yana ƙaremata kallo bai taɓa yi mata irin wannan kallon ba in fact bai ma taɓa tsayawa ya mata irin wannan kallon ba yana san ya janye idanunsa a kanta amman ya kasa mai makon haka ma sai ƙarasawa da yayi wajen ta ya zauna kusa gareta, kan ta ba ɗankwali gashin ta duk ya bazu a wajen baƙi da shi ya sha gyara gaban goshinta gashi duk ya kwanta kamar abunda aka shafa jel ya kalli la'b'banta da suka ƙara yin pink saboda kukan da ta ci, ya kalli surar jikinta ta saman kayan da take sanye da su Wani abu zuciyarsa ta fara sak'a masa yana jin wani iri a jikinsa yayi saurin miƙewa tsaye ya fito daga d'akin ya wuce d'akinsa yayi alwala ya wuce masallaci lokacin ma har an kusa sallamewa
Bayan ya dawo ya lek'a ɗakinta ya ga har yanzu bacci take yi ya wuce d'akinsa ya ga d'akin duk ya hargitse ga jininta da ya zuba ga glass zube ya juyo ya fito ya koma falo ya zauna kamar yayi ihu haka yake ji ya rasa takamammen abunda zai yi, can wani tunani ya faɗo masa na ya kira ƙanwarsa Rukayya ta zo ko zata taimaka musu da wani abu, ya ɗauki wayarsa ya bincike kaff ba number Rukayya a ciki ya ja tsaki can ya yanke shawarar kiran Ammie sai ta haɗa sa da ita,haka kuwa a ka yi bayan ya kira Ammie suka gaisa ya nemi ta ba ma Rukayya wayar yana san magana da ita, Ammie na d'aki saboda haka sai ta kira wayar Rukayya ta faɗa mata ta kira Azaad zai yi magana da ita, Rukayya da taji haka sai da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 13