An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
Alhamdulillah Alhamdulillah, yadda na fara littafin nan lafiya Ubangiji Allah ya nuna min na kammalasa lafiya Allah ya bani ikon rubuta daidai a cikin sa ya hayyu ya qayyum🤲
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
Page 1
Kyakkyawar budurwa ce ajin farko fara doguwa farin ta irin mai kyaun nan ne sannan tsayinta daidai a k'allah dai shekarun ta zasu yi twenty something, tana ɗaure da towel a jikinta, Allah ya mata diri mai kyau, tana tsaye gaban mirror ta janyo wata kwalbar mai wanda kwalbar ce kawai ke saman mirror sai wani dan ƙaramin turare da ya kusa ƙarewa
Dubanta ta kai ga agogon dake manne a d'akin taga 7:48 "Ya Allah na kusa makara" ta faɗa wanda yasa dimple ɗin ta suka bayyana, da sauri ta shiga shafa mai ta gama ta ɗauki turare ta shafa a jikinta, ta wuce wajen gado ta ɗauki tufafin ta da ta fitar, cikin sauri take yin komai har ta gama sa kayan ta ɗauki hijabin ta Nut brown dogo ta saka ta kawo nik'ab ta saka ta ɗauki jakarta ta saka takalmi tayi hanyar fita
Tana ƙoƙarin isa bakin k'ofar aka turo k'ofar, Wata matashiyar budurwa ce shekarun ta ba zasu gaza 13 to 14 years ba wani k'ask'antaccen kallo ta tsaya tana yi mata tun daga samanta har ƙasa take mata wannan kallon, Ganin haka yasa ta raɓa ta gefenta zata wuce "Wallahi ki ka kuskura ki ka fita gidan nan yau sai azabar Allah ta same ki " Ta ji Muryar yarinyar ta sauka ta tsaya tare da jiyowa ta zuba mata idanu ta cikin nik'af Yarinyar ta ce "Mommy na kiran ki kuma tace kiyi sauri ki sameta falo yanzun nan " Kai Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta faɗa cikin damuwa yarinyar tace " Ohh mahaifiyar mu ce shad'an kenan wallahi sai na sanar mata" Ba tare da tace da ita komai ba ta juya ta fito ta nufi falon gabanta na dukan uku uku tana addu'a Allah yasa ba wani aikin ne zata saka ta ba dan tama makara sosai wallahi
Bakinta ɗauke da sallama ta isa falon kusan sau uku tana sallama duk da mutanen dake falon hakan bai an samu koda mutum ɗaya daga cikin su ya amsa sallamar ba, wanda inda sabo ta saba, tasa hannu ta ɗage nik'af ɗin ta sama ta nufi wajen da matar take zaune ta gurfana murya na rawa tace "Mommy ga ni" ta faɗa yafi sau uku sannan ta juyo da fuskarta wajen ta tace " Kinga dama kin zo?" Wallahi yanzun nan Basmah ta sanar min kina nema na"Lahh lahh lalahh sharri zaki min Allah Mommy na jima da faɗa mata sai da ta tsaya ta gama abunda take yi sannan tazo kuma ma da na sanar mata kin san abunda tace?" Basmah ta faɗa Mommy ta girgiza mata kai alamun aah sai kin faɗa tace" Neman tsarin Ubangiji take daga gareki " Alesha Shaid'an ce ni?"Mommy ta faɗa tare da nuna k'irjinta
Muryar Alesha na rawa tace"Wallahi Mommy ba hakan nake nufi ba " To me kike nufi?" Ba komai " Kina nufin kenan Basmah sharri zata miki?"
"Wallahi Mommy duk ke ki ke k'yale ta shiyasa ta raina ki da yawa " Cewar wani saurayi dake wajen, Mommy ta buɗe baki zata yi magana budurwar da ke wajen ta riga ta faɗin" Ai bro sakin fuskar da take mata ne yasa ta rainata haka " Mommy ta yi murmushi tace"Naji yanzu duk ba wannan ba ina indomie da Ummie tace ki dafa mata kin gama ne?" Alesha tayi shuru kanta a ƙasa sai da Mommy ta daka mata tsawa ta ɗago kanta tace" Uhm mmmn daman da naga na kusa makara ne shi ne na barma uwani mai aiki ta dafa mata naje na shirya " Uwani! " Ummie ta faɗa tare da ɗagowa ta aje wayar da ke hannunta tace " Ki ka barma uwani? Uwani nasa ta dafa min ko ke? Ai naga uwanir amman nace ki dafa min wallahi idan ta dafa ta bazan ci ta ba Mommy kina jin ta fa ai wannan rainin wayo ne da wulak'anci" Kwantar da hankalin ki miye na tada jijiyoyin wuya indomie kamar kin canye " Mommy ta faɗa
"Alesha zo nan " Mommy ta faɗa tare da yi mata alamun da ta wajenta, ba musu taja k'uiwoyinta sai gaban Mommy, saukar mari kawai taji saman face ɗin ta " Dis na makarar da kikayi wajen kiran da na miki" kan ta ankara ta sake jin wani" Dis na aikin da ta saka ki ne kika k'iyi " Alesha hawaye kamar an buɗe famfo "That's good " Saurayin ya faɗa
"Tashi min a nan ko yanzu na sake baki wasu banza kuma ki wuce kitchen yanzun nan ki dafa mata abunda ta saka ki mansur idan bata tashi ba kazo ka 'ba'b'ballah min ita a nan" Da sauri Alesha ta miƙe ta ɗauki jakarta " Shegiya tana fama da hijabi har ƙasa kamar mai takaba" Mommy ta fada
Alesha hanyar ɗaki tayi ta cire hijab ta wuce kitchen har lokacin kuka take koda ta shiga ta tarar da uwani har ta dafa indomie tana juyewa a filet,
Tun da uwani ta ɗora idanunta a fuskarta ta san wani abu ya faru saboda fuskarta tayi ja ga kuma kukan da take yi, Uwani cikin tausayin shugabar tata ta matso wajen ta tace "Hajiya ƙarama meya faru? Me ya samu fuskarki kuma me aka miki kike kuka? Kin fasa zuwa makarantar ne?" Uwani ta jero mata waɗan nan tambayoyin lokaci ɗaya, ba tare da tace da ita komai ba ta wuce wajen pampon dake wajen ta wanke fuskart ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa masu sanyi ta sha ta mayar ta ƙara goge fuskarta ta juyo wajen uwani tace " Har kin kammala? " Eh yanzun nan zan kai mata " Aah ba sai kin kai ba ki ɗauki wannan kawai ki canye" Amman meyasa? Duk fa abunda kika ce a saka na saka " Uwani ki ɗauka kawai" To Hajiya ƙarama amman meya sameki nagan ki cikin wani iri?" Bakomai kiyi aikin ki kawai "Hajiya ƙarama Ubangiji Allah ya sassauta miki ya kawo miki mafita " Alesha tayi murmushi a zuci kuma sai amin take faɗi.......................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*GA MAI BUƘATAR A TALLATA MATA SANA'AR TA KO GROUP ƊIN TA NA KASUWANCI YOU CAN CHAT ME ON 09046495943*
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
Page 2
Cikin k'ank'anin lokaci Allah ya taimaketa ta kammala ta juye indomie saman filet da ɗauka ta nufo falo, har yanzu duk suna nan zaune kowa da abunda yake yi banda Mansur da ya tashi ya fita
Har gaban Ummie ta isa ta aje indomie, tace "Gashi nan" Wani yatsina fuska Ummie tayi tace "Ya banga egg 🥚ba bayan kin san idan ba shi bana iya cin indomie" Na manta ne wallahi dan Allah kiyi hak'uri kinga na makara idan yaso anjima idan zan dafa miki sai na saka " Wallahi baki isa ba dole ne kije ki dafomin k'wai ki kawo yanzun nan" Amm.........." Alesha" Mommy ta kira sunanta kana tace " Ba na hanaki yin jayayya da ita ba ne? Wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da kunnuwana zasu ƙara jiye min ina fatan kin jini?" Eh" Good kuma ki wuce kije ki kawo mata abunda take buƙata" To Mommy "
Ta juya ta koma kitchen jiki ba k'wari sai da ta dafa k'wain ta kai mata sannan ta fara cin indomie, Bayan ta gama da sauri ta ɗauki hijabin ta ta saka ta mayar da nik'af ɗin ta a fuska ta ɗauki jaka ta fito taje ta sanar musu ta tafi, tana ƙoƙarin fita sai ga daddy ya fito da shirinsa da alama fita zai yi shima tayi masa ina kwana ta wuce, Da sauri ta fito, motoci uku ne a compound ɗin gidan amman ga mamaki na sai naga ta nufi bakin gate ƙasa bata yi wajen motocin ba buɗe k'ofar gate ɗin tayi ta fita, mai gadi dake cikin daki jin an buɗe k'ofar yasa ya fito ya lek'a yaga ita ce ya juyo sai ga daddy ya fito ya gaida sa ya buɗe masa gate ya fice, Tafiya take a ƙafa sai sauri take yi ta buɗe jakarta taga Naira 60 saba'in ce gareta kuma ba zasu kaita school ba dan haka ta ƙara sauri tana cikin tafiya motar Daddy ta biyo ta wuce ko alamun tsayi bai yi ba bare ya kalli gefenta ita kam ba abunda ya dameta dan ta saba gata ga su zata fita suma zasu fita amman ba mai rage mata hanya ko ya bama kuɗi yace ta hau abun hawa
Tayi tafiya mai ɗan nisa, sannan ta tsaya wani shago ta shiga ta siyo biscuit na hamsin sweet guda ɗaya na Ten Naira ya rage mata saura naira goma, ta fito taci gaba da tafiya bata ƙara wata tafiya mai nisa ba ta iso Wata private school, cikin mutumci suka gaida da baba mai gadi ta wuce tana shiga ana tashi breakfast, kai tsaye office ɗin shugabar makaranta ta wuce dan sa hannu koda ta je shugaba baya nan ɗan aikensa ne kawai tasa hannu ta fito ta wuce staff ɗin su na malamai
Tana shiga yan uwanta malamai suka sanar mata Noor tayi ta zuwa bata nan tace "Allah sarki princess nima ina can gida amman tunanin ta ya dameni " Zata zauna sai ga Noor ta shigo da gudu sai wajen ta tana dariya ta ɗauke ta sama tana juyawa suna ci gaba da dariya, Noor yarinya ce yar' kimanin shekaru shida tunda aka kawota makaranta kullum cikin kuka take bata zama school amman zuwan Alesha ya sauya komai Jinin Noor da Alesha ya haɗu waje ɗaya daman Allah yayi ma Alesha san yara bare kuma da taji ance mahaifiyar Noor ta rasu tana haihuwarta idan ka ga abunda suke zaka iya rantsuwa kace uwa da yar' ne saboda shak'uwarsu sauran malamai ma farko sun zata Ita ce mahaifiyar Noor waɗan da basu sani ba, sometimes idan aka tashi school sai anyi drama tsakaninsu Noor tace sai ta bita gida, dak'yar ta ke lalla'bata driver ya wuce da ita, wannan kenan
Sai da suka gama juyin su sannan ta sauke ta ta zauna ta ɗaura ta saman ƙafafunta Noor tace "Mommy tun d'azu nake ta neman ki" ta faɗa cikin muryarta ta yara Alesha tace "Ohh Sorry princess yau Mommy ta makara sosai ko amman bazata sake ba kinji?" Noor ta gyad'a kai tana murmushi
"Kin ci abinci?" Alesha ta tambeta ta girgiza mata kai alamun aah tace"Ina abincin?" In bag " Alesha ta shiga cire jakar da ke bayan ta ta ciro wata had'ad'd'iyar ƙaramar kula ta yan makaranta ta buɗe ta riƙa bata a baki har sai da ta k'oshi ta bata ruwa ta sha, ta ciro biscuit ɗin da ta siyo mata ta buɗe ta bata ta ɗauke ta suka yi class ɗin su saboda an gama break har an koma class ajinsu ma take da yanzu
Bayan an tashi Noor harda kuka sai ta bita ga driver tsaye ya na jiran su yana kallan su yana murmushi dan rigimar su na burgeshi dak'yar ta hak'ura Alesha ta sata mota suka wuce ta kama hanya ita kaɗai tana tafiya ga zafi ga kuma zafin rana koda ta isa gida kamar zata kama da wuta, tayi wanka ta yi sallah sannan ta fito duk da a gajiye take tana buƙatar ta kwanta ta huta amman tasan hakan ba mai samuwa ba ne
, gidan yayi shuru da alama yaran duk basa nan Mommy kaɗai ce a falo daga kallo bacci ya ɗauke ta a zaune sallamar Alesha ta tayar da ita
Mommy tace "Sai yanzu kika dawo?" Eh" ta faɗa kanta a ƙasa Mommy taja tsaki tace" Kije kitchen kaji na nan guda shida cikin fridge ki ɗauke su a gyara sannan gida biyu za'a raba rabi ayi farfesu rabi a soya irin jar suyan nan sannan da kin soya sai ki barbad'a yaji a kai ai kingane yadda nake nufi ko?" Eh" Okay maza wuce ki fara saboda bana san babanku ya dawo ba tare da an gama ba tun d'azu ya aiko su uwani kuma bazata iya yin yadda nake so ba idan kin gama gugar kayan Basmah na nan "To" ta wuce kitchen taje ta fara aiki tana cikin aiki su Ummie suka dawo kowa nen su riƙe da leda sun siyo kayan mak'ulashe
Ita kaɗai tayi ta bulek'en aikin kajin har ta gama, zuwa lokacin har biyar tayi, har ta gama ko tsinke ɗaya bata sa a baki ba ta ɗauke sa gaba ɗaya ta kaima Mommy
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Wani katafaren gida ne mai masifar kyau, gidan ya haɗu sosai ga shi da girma kai da ganin gidan kasan na masu shegunan ne ( Kuɗi kenan 😅) buɗe gate aka yi motarsa ta danno kai ciki ya nufi wajen aje motoci yayi parking ya fito, kyakkyawa ne ajin farko fatarsa baƙa ce sai dai ba irin baƙin nan ba dan ba zaka ce masa fari ba kuma ba zaka kirasa baƙi ba irin dai tsaka tsakar nan ne gashi da hanci sa Allah ya basa gira kamar mace idanuwansa basa da wani girma amman farare ne tasss bakinsa shi ba ƙarami ba kuma shi ba babba ba yana da ɗan gashin gemunsa ɗan daidai yana sanye cikin ƙananun kaya riga da wando, fuskar nan tasa a haɗe take kamar ko yaushe ko alamun murmushi babu a kanta, Ɗaya ɗaya yake takawa irin cikin izzar nan, Ma'aikatan dake gaidasa ko kallo basu ishesa ba bare ya samu damar amsa musu har ya isa bakin falo ya tura k'ofar ya shiga, sallamar da yayi ko wanda yake kusa da shi sai idan ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya a bakinsa sannan zai ga alamun yayi sallama dan ko sautin maganar baza ka ji ba bakinsa kawai da yayi motsi shi zai nuna ma alamun yayi sallama
Matar da take zaune a falo tare da baƙi kallo ɗaya zaka mata ka gane ita ce mahaifiyarsa saboda suna da kama sosai amman sai dai ita fara ce, juyowar da zata yi ta gansa tafe saboda ko sautin tafiyarsa baka ji tayi murmushi har ya ƙaraso yana ƙoƙarin wuce su tace "AZAAD.....................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*GA MAI BUƘATAR A TALLATA MATA SANA'AR TA KO GROUP ƊIN TA NA KASUWANCI YOU CAN CHAT ME ON 09046495943*
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
Page 3
Tsayawa yayi ya juyo yana kallan mahaifiyar tasa ba tare da yace komai ba Ammie tace " Baka ga baƙi ba ne?" Ɗan juyawa yayi 'bangaren da mutanen suke zaune dan shi bai ma lura da mutane a wajen ba, Baƙin su biyu ne sai wata budurwa wacce ta kafesa da ido tana kallansa kamar ta had'iyesa
"Sannu ko " Ya faɗa da k'yar dan maganarma kamar wanda aka sa dole Ammie tace " Ka gane su kuwa?" Kai ya girgiza mata dan ya fara gundura "Maman Aliya ce fa da ƙanwarta da kuma Aliya" Ɗan juyawa yayi ya kalle su yaji ransa yayi mugun 'baci, su kuma sai wasar baki suke yi Maman Aliya tace "Ai tun d'azu muka zo Hajiya tace ka fita ashe da rabon zamu gana ga Aliya nan ko duk ta damu da ta ganka "Kallanta kawai yake ba tare da yace da ita komai ba ganin haka yasa ta taɓa Aliya tace"Tashi ki je ku gaisa "Da sauri Aliya ta miƙe zuciyarta cike da farin ciki ganin abunda take so zata samu,
Aliya ta taso tana yanga ko kallon kirki bata isheshi ba tana ƙoƙarin isowa wajensa ya ɗaga mata hannu tare da faɗin "Stop here " taja burki ta tsaya tana ƙare masa kallo yace "Mun gaisa zan shiga ciki ina da aikin yi" ita kaɗai taji abunda ya faɗa duk da hankalin mamanta na kansu amman bata gane abunda ya faɗa ba, Wucewarsa yayi ya haye sama yayi d'akin sa ya barta nan tsaye
Ammie duk da bata san abunda ya faɗa ba amman tana da yaƙi nin dakatar da ita ne yayi saboda tasan ko waye ɗan nata bare kuma yadda taga fuskar Aliya, murmushi kawai tayi ta kalli Aliya dake tsaye a wajen har yanzu tace"Daughter dawo ki zauna " Aliya ta k'ak'alo murmushi ta wuce ta zauna
Ƙanwarta maman Aliya tace "Wai har yanzu bai sake yin Aure ba ne ? ko an tsayar masa da wata " Har yanzu kuma ba wacce aka tsayar masa na sha taya masa yaran Aminai duk wacce na nuna masa yace Aah ni abun na damuna wallahi dan nafi san yayi auren ko zai manta da komai" Allah sarki yarinyar tana ina?" Tana sama tana bacci" Okay " To Hajiya idan ba damuwa nace mezai hana mu haɗa sa da Aliya kinga yarinya ce mai kirki kuma na tabbata zata riƙe yarinyar kamar ita ta haifeta " Ba Aliya kaɗai ba harta mahaifiyarta taji bala'in daɗin wannan maganar da ƙanwarta tayi, Aliya tayi murmushi tayi ƙasa da kai
Ammie tace " To bazan ce eh ba bakuma zan ce aah ba saboda Azaad ba'a masa gwazan gori domin na sha zuwa masa da irin waɗan nan maganganun yana kushewa amman dai zan jaraba Allah yasa a dace domin nima na yaba da hankalin yarinyar da gani zata yi kirki"Yawwa Hajiya to Allah yasa a dace ina taya mu murna mun kusa k'ullah alak'a mai ƙarfi a tsakanin mu "Allah ya tabbatar muna da alkhairi"Ammie ta faɗa duk suka amsa da Amin, Maman Aliya ta kalli Aliya tare da faɗin "To fa Hajiya kinga mutuniyar taki an nok'e kai ƙasa kunya" Ai kuwa "Ammie ta faɗa tana dariya
Azaad yana isa ɗakin sa ya tura k'ofar da ƙarfi ya shiga ransa duk a 'bace yake jinsa duk an dagula masa lissafi ya shigo da yar' fara'arsa, wani irin dogon tsaki ya ja da ya tuna irin kallan da Aliya ke masa time ɗin da yake mata magana abun ya basa haushi sosai har sai da ya furta "Stupid girl "
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Zaune suke a falo Alesha ta ɗauko filet Mommy ta amsa ita ta zubama kowa Daddy, Mansur, Mamie, Basmah, duk sai da ta cika musu filet da naman kaji ga nata kuma a gefe, ta kalli Alesha dake durk'ushe a ƙasa tace "Baƙar mayya ta zo ta sani gaba dallah miƙo min filet gashi nan na saka miki kar na fara ci ya tsayamin a mak'ogaro" Daddy ya ɗago ya kalle su ba tare da yace komai ba yaci gaba da cin kazar sa, Alesha ta matso ta ɗauki filet da miƙa mata
Kai da k'afafu ta riƙa tsinta tana sa mata gaba ɗaya ta tsince su ta zuba mata sannan ta saka mata cinya ɗaya ta miƙa mata "Karb'i nasan zaki fi jin daɗin waɗan nan kin ma fi mu cin albarkar naman" Alesha tasa hannu biyu ta kar'ba tare da faɗin " Nagode" ta miƙe tsaye har ta kama hanya Mommy ta kirata ta miƙa mata tsoka biyu tace "Wannan ki miƙa ma Uwani"Ta amsa ta wuce
Ɗakin da uwani ke kwana taje ta zauna suka gaisa ta miƙa mata naman har nata tace ta cinye
Ta jima a d'akin uwani suna fira sannan ta tashi taje ta ɗauki kayan Basmah ta fara guga kiran sallah magrib ne ya tadata taje tayi sallah, tashin da tayi ashe ta manta bata kashe soket ba tashi kawai tayi tana dawowa sai kawai ta danna soket ta zata a kashe yake ta ɗauki stone ta danna ga wata riga nan take rigar ta cinye sai ga Basmah ganin rigarta ta k'one ta tsala wata irin ƙara nan take sai ga Mommy da Daddy uwani ma dake kitchen tana aiki sai da ta fito,
Wani salati Mommy ta rafka tare da nufar wajen ta ɗauki rigar tana nuna ma Daddy tace "Yanzu Alhaji dubi aikin da yarinyar nan tayi tun da ba ta so ba na saka ta shine tayi mata wannan aikin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 13