Share this page
kajanyo ma kanka." Suna Kus-kus dinsu amma duk da hakan tana jin su. Shi kam daman Munir yana waya ne, sai Zainab din ce ta ce, "Mu ma ai muna bisa hanya in dai auren nan ne a daina yi mini gori. Shi kam Munir dariya ya yi yana kallon agogon hannunsa yana fadin "Su aure manya, 461hafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo 3 tashi mu tafi ko?" Ta mike tana cewa, "Ga tsarabarki can a leda in yi Ya Munir." Sai a lokacin Khuzai din ta tashi da sauri ta dauko leda ta bude tana fadin. "Shi ne ba ki gaya mini ba sai da za ku tafi?" Ta bude ledar tana fadin "Yanzun haka sai da ki ka zabe sannan ki ka kawo mana, wallahi zan zo naga naki idan yafi nawa kyau wallahi sai na canza. Zainab tayi dariya ta ce, "Lalle yarinyar nan mijina ya kawo mini abu ki ce sai kin canza mini, ke nasan me mijinki yake miki?" Tahir ya ce, "Rigimarta dai, siket da riga ya kawo musu da turare." Har motar ta biyo su tana mita kudin da Ya Munir din ya bata ne yasa tayi shiru da mitar, tana kallonsu suka je mota suka tafi, kowane ya koma zamansu na da zaman kurame. Wannan sabon al'amari yana damunta, gaba daya ta rasa abin da yake mata dadi, rayuwa kenan mutumin da ta ke ja masa aji ta wulakanta shi, tayi masa fushi ya yi ta binta yana son ganinta. 47 Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Amma kalli yadda yanzun ta zama banza a wurinsa, take faman wulakanta shi yana neman soyayyarta yanzun ita ce haka a wurinsa ba ta ishe shi kallo ba. Tafiya suke yi ba magana, idonta ya kada ya yi jajir gaba daya ta fita hayyacinta da wannan shan mur din ai gara ya doke ta ko ya zageta da wannan sharetan da yake yi. Ta kalle shi tga kawar da kai tana son tayi masa tambaya amma gaba daya ya cika motar take gani saboda kwarjininsa. Ta saki ajiyar zuciya ta ce masa, "Yanzun ina zamu ne?" Ya ce, "Gidan Ummanmu." Ta saki ajiyar zuciya har ya lura da hakan. Zuciyarsa tana son ba shi hakuri saboda tausayinta da ya ji, sai kuma ya basar. Shi kam ai shi ne abin tausayi, da ta bari wani ya taba ta, sai kawai sabon fushi da yake yin ba zai bari ba har ya gano bakin zaren. A kofasr Nasarawa gida ya kacame da oyoyon zuwansa, su Hajiya Binta an ji kunya a da Malaminsu ya ce Munir da Kano har abada. 481Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ya yi irin na Nabil sai kuma ga Munir din da wani irin sauri ta fito tare da dafe kirji cike da mamakin ganinsa. Та се, "Munir! Munir dai!! Mai sunan Mallam?" Ya iso gabanta yana dariya. Ya ce, "Ni ne Momy, ga Munir." "Ina ka shiga Munir?" Ya ce, "Alhaji bai gaya muku in da nake ba? ai muna waya dashi." Ya fada yana wasa da sabuwar jaririyar da Anti ta haifa. Ya ce, "Kai Anti kin haifi katuwar jaririya, ya sunanta?" Tayi dariya ta ce, "Goggon Mama sunanta, sunan Goggon aka sanya mata amma fa ba waccan ba, autar Mama." Ta fada tana kallon Zainab din da take tsaye tana dariya. Ya ce, "Kowa an kawo masa tsaraba amma ban da ita, ban san kin haihu ba." Та се, "Ваa ka da laifi, laifin Alhaji ne ya ki ya gaya ma mutane an samu karuwa ko na samu kayan barka sosai. Ke ma Zainab muna jiran kayan barkanki, tunda dai sunanki aka sanya.' 491Shat Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Munir ya yi dariya ya ce, "Bari a sallami Mai sunan Zainab." Kudi ya kwaso ya bata shi kansa bai san nawa ba ne. Ya ce, a sai mata riga ya fanshi Zainab din. Anty ta ce, ba ruwanka Mai sunan Mallam, ni da Goggon Mama a gidan nan idan bata kawo rigar mai sunanta da hannunta ba. Ya ce, "A'a Anti ai ni na kawo tunda na kawo ai kamar ta kawo ne." Ta ce, "Ban yadda ba, kyale ni da ita." Ta ce, "Ai ni na kawo tun ranar da muka zo barka da Mama, wallahi na יי fita." Antin ta ce, "Ba wani nan. Ai wannan na Hajiya Mama ki ka karu a jikin wanda rigarki idan ba ki kawo kayan mai sunanki ba, ranar bikinki da goyo zamu dinner sai kin sanya goggwaro kiyi goyo." Aka kwashe da dariya, gidan nan ana cin dariya amma ban da Hajiya Binta da bakin cikinta bai boyu ba. Hajiya Rabi'a kam! Farin ciki kamar tayi yaya. Don suna shiga dakin da ta gaishe ta sai ta ce, "Bari na kewaya gidan Nuri." Da shi ke gidansa a nan kofar Nasarawa ne, ya yi gininsa ire-iren filayen da Alhaji Usman 5015ha1 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo ya saya ya gina masa gida a nan. Da sauri Nuri ta tarbe ta tana fadin "Amaryar danko." Suka yi dariya har da rungume juna. Hafiz din ya fito a daki ya ce, "Kar ki karbi gaisuwarta, sai yau tazo miki gia?" Tayi dariya ta ce, "Wayyo Nuri! Kar ki bari ya hada mu, ba na fita ko ina yanzun ma Ya Munir ne yazo na fito." Nuri ta kalle ta ta ce, "Don Allah?" Ta ce, "Wallahi kuwa." "Yanzun yana ina?" Ta ce, "Wayyo Nuri yana can yana tare da Umma na sanya su a gaba? Wuri na ba su su zanta dadi su zanta wuya. Jiya ba ki ga abin da Mama ta yi ba, hana ni ma shi tayi muyi zance, ta tattare shi da labari." Suka yi dariya. Nuri ta ce, "Hajiya Mama tamu kenan, ke kuwa ai da gaskiyarta." Hafizun ya ce, "Bari na shiga cikin gidan." Ya fada yana fita, ta tashi ta bishi suka yi 'yar radarsu, ko me suka ce? Oho! Suna ta faman kyalkyata dariya, Nurin ta dawo ta zauna a gefen Zainab din ta ce, "Me ki ka ce?" suka kyalkyale da dariya. 51 Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Nuri ta ce, "Sai kin ji?" suka yi dariya ta ce, "Ga tsarabarki nan." Nurin ta bude tana fadin "Mu ma muka sha tsaraba balle ke?" Та се, "Ke dai bari Nuri, ina ganin ikon Allah wurin Ya Munir, jiyan dai da ya zo lafiya lau ba wata damuwa. Amma yanzun yau da safe zuwa yanzun sai share ni yake, ban san me yake damunsa ba. Nuri ta ce, "Ko wani abun aka yi masa? Ko su Alhaji sun Gata masa rai." Ta girgiza kai ta ce, "Ba ruwan Alhaji wallahi sune ba zance suke fita. Kin san ya samu aikinsa na Kaduna yanzun haka har an maida shi Port Harcourt da shi ke kamfani suke yi ma aiki yana samun harka sosai. Ni dai na rasa abin da yake damunsa." Ta ce, "To shi kenan Allah ya sauwake, muyi sallah muci abinci." Suka mike gaba daya Zainab tana fadin "Wai me ya dawo gida ya yi Ya Hafiz din? Ко yau bai fita kasuwa ba?" Nurin tayi kwafa! Ta ce, "Ni da mara mutuncin nan mana Badi'a, ba ni da lafiya amma ta ki shigowa ta 521sha Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo dan taya ni aiki, kin san su Alhaji ya bari su ci gaba da karatu. Wai ta samu admission a (BUK) karya ta karu tazo tayi mini dan aikin bana kirki ba, amma ta ki. Sai da kansa yazo ya rage wasu ayyukan." Zainab tayi murmushi. Ta ce, "Badi'a kenan. Taje shekaran jiya ta karbo dinkuna ai shiga Jami'ar nan tana masa shiri sosai." Suka yi dariya. Nuri ta ce, "Jiya ma sai da na zazzageta 99 shegiyar rawar kanta ya yi yawa. Badi'atu kanwar Nuri ce, sai dai tafi Nuri girman jiki, idan ta ganta ma ba ka sani ba sai ka ce Yayar Nurin ce, dukan su diyan Hajiya Rabi'a ne. Sune yanzun sabbin 'yanmatan families din da Alhaji Usman ya ce an daina hana 'yammata karatu su fita suyi ilimi, ya daina ajiyar su ba su fitas da miji da wuri da wuri ba. Don haka su Badi'a din ake rawar kan tafiya Jami'a, tafi Nuri fitina da rashin hakuri duk families din nan an san Nuri a rashin mutunci. 53 Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Idan ka tabo ta yanzun za'a rikito ba tsoro take yi ba, don sau da yawa ita ce take kwace ma Hajiyar su fada idan an yi wani abun, sai dai aji ta kwace fadan har ta tsokano wani fadan. Don haka tunda aka yi bikin su Nuri ya zamto a nan take yini, idan Hafizun ya tafi kasuwa. Ranar da Nuri tayi mata fadan Jami'a sai a hankali yasa ta dauke kafarta a gidan saboda gudun wulakancin Nurin tayi mata. Suka yi dariya ta ce, "Wai don daga fadan tayi miki fushi?" Ta ce, "Wallahi." Suka yi sallama suka ci abinci har La'asar tana gidan Nuri, sai da Ya Munir din suka shigo da Hafiz. Ya ce, "Ke tashi mu tafi dare fa ya yi." Ta mike tana kallonsa, ya canza kaya zuwa farare. Wani yadi ya sanya fari mai sassaukan nauyi shara-shara, don ana ganin singilet din shi fara kal. A sanyaye ta kalle shi ta ce, "Yayana kayi kyau." Bai amsa ba, yana fadin "Ke Nuri ki gaya ma Badi'atu kar na dawo gobe na iske 541shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Hafiz ya yi miki aiki ko me zata yi kafin tayi ta tabbatar ta miki aikin gida." A sanyaye ta amsa "To Yaya, ka gaya mata?" Ya girgiza kai ya ce, "Ban gaya mata ba, amma na gaya ma Umman idan kuma ta isa maras jin magana, to kar tazo ta taimaka miki na gaya miki ai." Та се, "То." Ya mika mata kudı yadda ya bai wa 'yan uwantan. Hafiz din ya ce, "To ai da ni ka bai wa kudin nan me zata yi da kudi ita wannan ban da asusu?" Ya Munir din ya yi murmushi ya mika masa ya ce "Na amare ne, ka rike wannan." Suka yi dariya ya amsa yana fadin, "Allah ya kara girma." Ya raka su mota. Nuri tana fadin, "Sai yaushe Amarya?" Tayi dariya ta ce, "Kafin mu fara fita Lecture za ki ganni." Ya juya ya kalleta yana yi ma mota key. Ya ce, "Lecture za ki fara, ta me?" Ba ta yi magana ba ta ce, "Alhaji ne ya siya mana forт muka cike, kuma ma ina ganin mun samu admission" 55 Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ya ce, "Zaman dai haka ba dadi." Ya ce, "Ya yi kyau." Har suka je gida bai tanka mata ba, itama ba ta tanka ba, don abin ya daina bata mamaki ya shiga bata tsoro. Kwana daya, biyu, uku tana yi mata gaba, daga gaisuwa ba kari, gaba daya cikin kwanakin zuwan sa duk ta canza kuma tayi wata irin rama duk ta fada ko abinci ta sanyo a gabanta sai ta ture. Sai ta yini a daki daga sallah sai dai tasha lemo ko tasha fresh milk, idan yunwa ta tsananta zata sha fura da dambun nama, Idan ba haka ba zata zauna da yunwa ido ya sake firfito mata. Ita dai Hajiya Mama tana kallonsu ba ta ce komai ba, don a cikinsu ba wanda ya same ta ya gaya mata, don haka take kallonsu da ido. A da aiki a wurin Zainab sai Hajiya Maman ta tausaya mata ta ce bari ki huta uwata, haka nan dinki idan ta fara sai ta ce tashi ki huta haka nan. To balle ta shiga kitchen shi kenan kuma ai ranar ciki lafiya baka lafiya. To yanzun kuma 56 11 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo ta rasa meye ya canza mata ita ta koma hakan? Da sassafe ta fito, yau din bayan ta idar da sallah tayi wuridinta suna aiki a tsakar gida ta nemi wuri ta zauna tana kallonsu. Har suka hattama aikin suka baiwa Laure, ita kuma Talatuwa ta shiga sharar falon na Hajiya, ta ce Talan ki shiga ki gyara mini daki." Talan din ta ce, "Wai ni ina kuzarinki ya tafi ne? ko kuma Badi'atu ce ta kwace miki? Naga tunda Badi'a tazo ba ki da hanzari." Suka yi dariya ita da Iya Laure. Hajiya Mama da take juya miya a cikin kitchen din itama ta sako baki ta ce, "Gane mini hanya dai Talan, bincika ki taimake ni." Zainab ta ce, "Yo ni ina ruwana da wata Badi'a da zata hana ni kuzari? Kawai na ce muku ba na jin dadi ne, shi yasa ki ka ganni haka. Amma duk ku bi kusa mini ido ku takura mini, me na tare muku a gidan nan? Allah ku fita a harkata." 571Snafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Hajiya Mama ta ce, "Wannan shi ne borin kunya, daga tambaya sai cibi ya zama kari, Allah ya ba ki hakuri." Tunani ya yi ma zuciyar Zainab yawa, ta rasa a wace duniya take don tashin hankali. Don kaskanci da wulakancin da Ya Munir yake nuna mata ya mata yawa. Har 'yan aiki sun gane suna mata gugar zana, wannan ma ai wulakanci ne. Sai kawai ta fashe da kuka, take faman kuka. Hajiya Maman ta ce, "Tashi ki dauko abinci break din Munir ki kai masa, ba na son shirme, me aka yi miki na kuka? Haka kurum za ki farke mana da kuka?" Cikin kuka ta ce, "Ba Talatuwa ba ce, harkarta nake shiga zata shiga kayana? ko ina ruwanta da ni zata ringa yi mini Gugar Zana?" Hajiya Mama ta rike baki cike da mamaki tana dariya, itama Talan din dariyar take yi, tare da rufe baki kar Zainab din ta jiyo dariyarta. Hajiya Maman ta ce, "Allah ya ba ki hakuri uwata, ai wannan kuskure ne ma, ayi hakuri ba za a kara ba."Ta mike tana goge hawayenta. 581Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ta dauki tiren abincinsa ta shiga da niyyar kai masa idan tayi sallama bai amsa ba zata juyo don daman sai ta hana idonta bacci tayi masa abinci ta kai ya ki ci ko kuma tayi sallama ya ki amsa mata. To tunda abin wulakanci ne wallahi ta gaji, yau sai ya gaya mata abin da tayi masa yake tozartata. To ina laifin ma mai kulawa da kai da rayuwarka? Ita ce sharar dakinsa, goge-goge, komai tana yi masa amma bai maida ta mutum ba, sai wani shasshareta yake yi kamar wata baiwarsa. Don haka itama yau ta hau tsini. Tana shiga ta iske shi a falo yana kallo a kwance yake a carpet, sanye da jallabiya. Ba ta kalle shi ba, a tsaye take bayan ta ajiye abincin kamar zata juya sai ta nemi kujera ta zauna ta dauki Remote din ta rage muryar TV din sosai ta ce, "Ni kuwa ina da tambaya Ya Munir." Bai juyo ba haka nan bai kalleta ba ya ce, "Ina jin ki." 591Sha Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ta ce, "Ni wani laifi nayi maka ne? na gani tunda ka dawo sai faman fushi ka ke yi da ni, idan laifi nayi maka ka gaya mini don Allah." Tana magana cike da ladabi da tausasa murya, bai tanka ba haka nan bai motsa ba. Nazari yake yi wai yarinyar nan haka ta raina shi? Ya tambayi kansa. Ya mike a zaune ya ce, "Вa ni Remote dina, marar mutunci kawai."Ya kwace Remote din ya ce, "Har kin isa kizo kina wani tambayata? Matsalar da ki ka sanya ni ma ai ta ishe ni, tashi ki bani wuri yanzun nan ko ranki ya 6aci." Ya fada yana kwace Remote din a hannunta. Ya juya ya ci gaba da kallonsa ya kara murya. Yayin da ita kuma taci gaba da kuka, sosai take yin kuka, yana jinta ya kasa tanka mata. Tayi mai isarta ta tashi ta fice ya bita da kallo cike da tausayi. Shi kansa tausayinta yake ji, Ya girgiza kansa yana yin tsaki a ransa ya baiwa kansa da tuni ya zan yi? To taje ma tayi fushin mana. 601a. Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ranar yini tayi tana kuka, daman tana dan boyewa ne don ta samu ta sanyaya zuciyarta, to abu ya riga ya fito ba wani boye-6oye yanzun. Don haka ta yini kuka ko abincin safe bata ci ba, har Magariba. Shi din ma abinci kashi biyu ba wanda ya ci, da yamma ne da abin ya ishe shi ya yi wanka ya dauki mota ya fice, sai bayan sallar isha'i ya shigo. A lokacin ta fito Goggon Maman tayi wanka ta ci abinci, ita dai Hajiya Mama tana kallonsu ta zura musu ido, bata cewa komai. Yana shigowa falon da Zainab din ya yi ido biyu, idonta ya kumbura sosai ya shiga ciki alamun kuka tayi ya isheta. Kallo daya ya yi mata sai da gabanta ya buga don tsoron kar wani abu ya same ta. Can gefen Hajiya Maman ya zauna, yayin da Goggon Maman ta mike ta fice ta bar falon, sabanin da da za ta shiga hidima da shi. Abinci, ruwa, lemo da fura ta kawo wannan ta kawo wancan tana lallaminsa. "Yayana me zaka ci? Ko tea za ka sha?" Ta yanko fruit ta kawo masa. Amma yana shareta. 611Sha1 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ya bita da kallo, ba ta dawo ba suna maganar filaye da Hajiya Mama. Saboda kudinsa da ya bayar a sayi gida a sayar da filaye guda biyu. Filayan kuma nasa ne guda uku ne, ya ce a sayar da su. Don haka Hajiya Maman ta ce ko barin filin nan za a yi na Na'ibawa? Naga ba su taya shi da daraja kuma gidan wurin Alhaji Karami din nan kar ka saye shi. Ya ce, "Mama me yasa?" Ta ce, "Ita uwarka ce bata da hankali, na gaya mata kar ayi aikin nan tana neman janyo maka bala'i, ba zai yiwu ba. Kai ne babba a ce ka fara da sayen kadarorin ubanka, duk dadin bakin ubanka ta rabu da shi, fili kuma biyu halak dinka ne da ya baka. Don haka an samo mini gida mai kyau a can Nasarawa, kuma gidan ya yi kyau idan kana so sai ka saya ko? Ya ce, Ni fa Hajiya duk yadda ki ka yi daidai ne, ni dai kawai gida nake so ya ki ka gani?" Ta ce, "Shi kenan idan ka yadda sai aje a gani." 62 Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ya ce, "Ba matsala. Ni fa Hajiya duk yadda ki ka yi wallahi daidai ne ba damuwa." Zainab din ta shigo ta fita. Hajiya Maman ta ce, "Ita wannan me ya hada ku ne?" Ya yi murmushi ya ce, "Ba abin da ya hada mu." Hajiya Maman ta ce, "Ya za ka ce haka Mai sunan Mallam? Akwai abin da ya hada ku mana ubana, ayi fushi haka ace ba komai? Ai idan ka ji gudu da labari ni ai dole ce, dole ka gaya mini. Mu ai namu sasantawa ne ko? Idan kuma kun san auren ba zai yiwu ba kar ku bari a hada daga baya a samu matsala. Don fushin nan naku ya tsorata ni. Ya ka gani? Kar ka rufe ni ko ka gani mahaifiyarta ce ba wani abu kayi mini bayani." Ya yi gyaran murya ya ce, "Ba komai wallahi Hajiya Mama, ki daina ma kawo irin wannan zancen, ba abin da zai hana auranmu yiwuwa. Kar ma irin wannan tunanin ya ringa zuwa miki, duk abin da ki ka ga tana yi ki kyale ta ni da ita zamu daidaita." Та се, "Тo shi kenan, Allah ya sawwaka." Ya amsa "Amin." 63 Shati Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ita kam! Goggon Mama tana can tana dinki. Hajiya Maman ta ce, Talatuwa kirawo ta.Та shigo tana faman shan kunu. Hajiya Maman ta ce, "Wai ni Zainab sa'aninki ki ka maida mu?" Zainab din ta nemi wuri ta zauna tana faman cika da batsewa. Ta ce, "Wai Goggona meye ki ke shiga ki ke fita kina kumbura kije ki kawo ma Munir abinci ni zan je na hada kayan Hajiya Maryo, gobe zata wuce mini Katsina da su. Та се, "Тo." Ta mike ta wuce abinta ta bar su a nan. Ita kam Zainab yi tayi kamar ba za ta tashi ba tsawon lokaci. Sannan dai taje ta zubo abincin a wulakance ta kawo masa ta ajiye a wani kodaddan fulas da murfinsa ya bare, bata kuma kawo ruwa ba abincin yake ajiye ya ki ci da ya tashi tafiya sai ya bude firji ya dauki fura ya wuce. Da safe Hajiya Mama take masa zancen makarantar Zainab, ya ce yana da kyau ayi hakan don zaman ba dadi. Ta ce, "Eh, Alhajin ma hakan ya duba ka san ba ya son ta tashi da son sana'ar dinki." 64 Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ya yi dariya ya ce, "Me yasa?" Ta cе, "Ai shi ka san haka yake cewa da wahala, nima ban huta ba zan hana ta hutawa." Ya ce, To ai daman ita wannan me son jiki ce ai Hajiya Mama ba na jin zata yi dinki irin naki." Tayi dariya ta ce, "Uwata kenan." Tsawon wata guda kenan ana 'yar tsama tsakanin Mai sunan Mallam da Goggon Mama, sai ita ce take shan wahala don gaba daya ta fada ta rame tayi wata irin rama. Da rana su yini rikici ta rame ta lalace, daddare tayi kwanan kuka da sallah. Kullum addu'ar ta Allah ya cire mata son mai sunan Mallam din a ranta amma kullum abu karuwa yake yi kamar bata addu'a. Don zamanin gaba daya ya lalace, wani lokacin sai ta kashe kunne tana sauraronsa, jin muryarsa kawai yana sanyaya ranta. Duk hirar da yake da zancen da yake yi idan dai tazo wurin zai yi shiru. Haka nan ya bi ta da kallon banza, ita kam bata cewa komai sai dai ta bishi da kallo tun tana kokarin ramawa, har abin ya fi karfinta. 651 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ranar Juma'a da sassafe ya shigo ya zauna a falon Hajiya Maman tana tattare kayan dinki da aka kawo mata. Ta gaisheta ya ce, "Mama ga kudin nan, ni yau zan wuce. Tayi sakware tana kallonsa. Ta ce, "Ina za ka ubana?" Ya ringa murmushi yana sosa kai. Ya ce, "Mama Port Harcourt din zamu je yau din nake so na shiga Kaduna mu wuce da Abdul Basi bayan sallar Juma'a." Tayi shiru tana kallonsa, mamaki ya hana ta magana. Ta ce, "Ba za ka bari mu dan kwana biyu ba ubana? Ni yaushe ma ka zo garin?" Ya ringa dariya. Ya ce, "Sati shida kenan da zuwana Mama. Ita Umma sai fada ma take yi wai na zo na zauna naki tafiya wurin aiki sai sun kore ni." Hajiya Maman tayi tsaki ta ce, "Ita wannan ban da fada me ta ajiye?" Tayi shiru ta ce, "Ai shi kenan. To wannan kudaden fa?" Ya ce, "Wannan kudin lefen Zainab ne, ki bayar a hada mata. Sai kuma kudin gaisuwa da hidimar su ta 'yammata, shi ne na ce idan ba zai isa ba ki ranta mini kafin na juyo." 66|Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Hajiya Maman ta ce, "Haba ubana! Yaushe muka fara 'yar rance da kai? Ni wani lefe ma za ka yi mata? Ko ba lefe ma ai aurenku za a muku. Wannan kudin ka bar su zan bai wa Hafizu aje a gyara wancan gidan da aka saya. Ya sunkuyar da kansa yana murmushi ya ce, "Umma fada zata yi yanzun ma fadan take yi, kin cike kusan kudin rabin gidan sai fada take yi." Hajiya Maman ta ce, "Tayi fadan mana ai za ta daina ni tunda na ganka a gida aurenka а gida ai na gode Allah, yanzun ina Yayanku? Idan zan ganshin ma na wahala masa da kudina ma ai murna zan yi. Munir ya ce, "Insha Allahu zan dawo gida kamar kowa ya yi rayuwa." ta ce, "Allah yasa." Ya amsa "Amin." Ta canza zancen ta ce, Kaje kaga gidan ko?" Ya ce, Eh! Ashe ba wancan ba ne." Ta ce, Fasawa nayi da naga ina da ciko, gida ba wurin mota ai ba gida ba ne, ko ya ya kadan faka motarka. 67 Shaf Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ya yi dariya ya ce, "To Hajiya Mama ni dai ba ni da mota." Ta ce, "Mai rai ba ya fidda rai da arziki ubana." Ya sunkuyar da kansa cike da ladabi ya ce, "Allah ya kara girma Hajiya, na gode." Ta ce, "Ba komai ubana, idan ba mu yi muku ba waye zamu yi wa? Allah ya hada kanku." Ya amsa "Amin." Ta mike ta fice ta ce, "Ka shiga wurin Alhaji ne?" Ya ce, "Eh! Na shiga, tunda muka dawo a Masallaci da Asuba ai muna tare. Та се, То nima bari na shiga kitchen din tsakar gida, ban shirya komai ba." Tana fita ya shiga dakin Hajiya Mama tun daga bakin kofa yake sallama tana jinsa ba ta amsa ba. Sai kamshinsa da ya cika mata hanci. Ya ce, "Ba kya ji ana sallama ko ba ki tashi ba?" Tayi shiru, ya zauna a gefen gadon tsawon lokaci ba ta motsa ba. Ya ce, "Ni zan tafi ba kya ji?" Tayi shiru. Ba ya son kallonta. Saboda rigar bacci ce a jikinta, yana kallonta ya kauda kai. Ta tashi ta sanya hijabi, ta sanya tana mikewa ta shige bandaki, yayin da ya 681Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo kishingida a gadon nata abin mamaki sai ya ji ya kasa ficewa daga dakin. Don kamshinta ma gaba daya ya kashe masa jiki. Tunani iri-iri a ransa ba irin wanda bai yi ba, yana jinta ta fito a wanka ta dauki abin da zata dauka ta fice, ta kuma dakin gefenta ta shirya tsaf! Abinda ta dawo daki ta ajiye kayan kwalliyarta. Ya bita da kallo riga da siket ta sanya ireiren dai wanda ya kawo mata, turaren ne ya gane kamshinsa irin da ya saya mata ne. Tayi kyau ba laifi, sai dai ramar da tayi ne ta ba shi tsoro don rabon da ya ganta ba hijabi tun tana masa kwalliya. Ta nemi wuri ta zauna ta ce masa. "Ina kwana?" Ya kare mata kallo, tausayinta ya kama shi ya ce, "Lafiya lau! Zainab zan tafi." Ta dago ido tana kallonsa, shima idon ya kyaro mata, tilas ita ta sunkuyar da kanta. Ya suma yana kallonta, ta daure ta ce "Daman zancen wayata ne, na gaya ma Hajiya Mama ta ce na gaya maka." 69Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ya ce "Me za ki yi da waya?" Ta ce, "Ai yanzun zan fara zuwa Makaranta ne, kaga kenan tilas ina bukatar waya." Ya ringa kallonta a sanyaye, ya tanka. Ya ce, "Wayar kin ma tana nan cikin kayana da aka kwaso a zoo road, sai ki samu lokaci kije ki dubata." Ya fada yana mika mata mukullin. Ya ce, "Ki ringa kula da dakin don Allah." Ta amsa a sanyaye. To a ranta tana son tambayarsa me tayi masa yake shareta? Amma yanzu da ta riga ta gane shi, kallonsa kawai take yi. Auren da take kokonton ko ba zai yiwu ba, sai

Chapter 9 of 13