Share this page
taji yana bayar da kudin lefenta. Ya mike yana fadin, Sai Allah ya dawo da ni. Tabi shi da kallo kamar ta share shi, ta daure dai ta ce, Alaihi Tawakkaltu wa huwa Rabbul Arshil Azim. Ya juyo ya kalleta sai kuma ya yi murmushi ya ce, Amin. Ta ce, Allah ya kiyaye, Allah ya bada sa'a. Har ransa ya ji dadin addu'ar da tayi masa, ya sake amsawa "Amin Zainab, na gode." 701shati Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo A ransa yana ayyanawa yarinyar nan tayi hakuri da ni, to amma meye gaskiyar zargina? Kalli fa tsawon kwanakin da nayi, kowa na ganshi ban ga Suraj ba. Ko kunyar abin da ya mini ya hana shi zuwa? Ya fita su Mama rakiya har wurin motoci, su Talatuwa da Falalu tare da Alhaji suka fita yakai shi har Na'ibawa ya hau motar Kaduna. ** BAYAN TAFIYAR MUNIR Kullum sai Zainab ta share masa daki kamar Ibada tayi wankin toilet tayi turaren wuta ta fesa air freshner. Sannan tayi shirin Makaranta, sun riga sun fara Lecture can ta samu digree a (Caterring) harkar girke-girke. Ita kam Badi'atu (Law) take karantawa, kusan kullum tare suke dawowa, wani lokacin ma bata komawa gida Nassarawa sai ta samu dan sassaucin Lecture. A dakin Goggon Mama suke hidimar su duk Zainab din ta girma fa sosai, amma girman 71Shaf Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo jiki irin na Badi'a sai ka ce ma ita ce babba ga kazar-kazar ga aiki, ga abin dariya. Kullum tana manne da Goggo ana faman dinki, idan tana gidan idan ba haka ba tana kitchen. Dan abu kadan za ka ji fada ya kaure ita da Zainab, da Mama tayi magana zata ce ke dai bari Hajiya Mama, nayi maganin wannan masu felekan ita da Nuri sai su yi ta yi ma mutum manyance kamar sune uwata. Ita dai Mama dariya take yi, Tа сe, Ke Goggo ba na son son girman ki na tsiya. Cikin fushi zaka ji Zainab din ta ce, Wallahi Goggo ba ki san Badi'a ba. Yanzun fa sai bangaje ni take yi da wannan katon duwawun nata tabi ta babbake wuri inda mutum zai tsaya ma ya gagare shi duk ta tare. Yayin da Badi'a zata ce, "Wallahi tubarkalla da duwawuna, maye ya ci kansa ke da Nuri kun bi kun sanya ma duwawuna ido. Kuma ba zan matsa ba kiyi abin da za ki yi." Sai Hajiya Mama ta shiga kitchen din ta raba fadan sannan a zauna lafiya. 721sha: Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ranar Litinin da sassafe suka shiga kitchen din suna faman fadan su har suka gama break fast suka yi shirin fita Makaranta ana faman fada. Zainab ce dai da tsokana yau kuma rigima har Mama ta sanyo baki ta ce, Wai meye kuma?" Badi'atun ta ce, "Haka kawai wai Shafi'u ne a can Baffanku ya matsa min da aike, wai yana sona. Na ce bana sonsa ba na sonsa amma Falalu da Zainab sun takura mini, wallahi zan zage shi." Hajiya Maman ta ce, "Ba zagi. Ke Goggon Mama kar wanda ya kuma mata abin da bata وو So. Zainab din tayi dariya ta ce, "wallahi ba ruwana Hajiya, Falalu ne ya kawo fruit jiya ya ce wai kayan Azumin Litinin ne ba ruwana." Hajiya Maman tayi dariya "Oho! Ko shi ne na gani a firji?" Ta ce, "Eh!." Ta ce, "To kuje zan samu Shafi'un zan ce ya wuce kar na kuma ji." Sai kuma Hajiya Mama ta kira Shafi'u a lumana tayi masa ya kuwa hakura ya daina 73 Shaf Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo cewa yana sonta. To haka lamarin yake duk yadda ku ke da Hajiya Maman idan ka ce kana sonta to shi kenan an 6ata, ita dai bar ta a gayu da son kwalliya. Kamshi da matsa siket amma babu kula maza shi ita da maza suke so amma ba su ishe ta kallo ba. Yau ma sun yi shirin fita da yamma. Badi'a ce ta fara shiryawa, Zainab ta kalleta ta ce, wannan fa siket din ki ka sanya ta atamfa. Tayi tsaki ta cire tana fada tana gunguni. Zainab ta ce "Me ki ke?" Ta ce, "Yo gani nayi siket din ma sanyawa zaka yi amma sai an yi magana. Ku ke cewa nafi ku girma bayan ku din ma ba kananu ba ne." Zainab din ta ce, "Yo mu sa'anninki ne? yarinya kin girma da wuri ne mu ai mun jira girman ya zo mana ne. Hajiya Mama daga falo tana jiyo su. Ta ce, "Ai wanda ya girma shi ne babba Badi'atu, tunda sun fi ki kwanaki kin fi su girman jiki, ai kin zama yayarsu." Tayi dariya tana gwalon Goggon Maman. 741shaf Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Shiri suka yi za su je shoprite. Hajiyan ta ba su kudi za su sayo kayan shafa, Badi'a ce ta shiga falon Alhaji ta karo musu kudi. A hanya suna tafe Falalu yana tuKa su, wayar Zainab tayi ringing da sauri ta danna tayi sallama. Ta ce, "Salamu alaikum!" Taji shiru. Ta sake sallama, "Salamu alaikum." Taji an amsa muryar namiji ce da sauri ta kashe don ita bata san lambar ba. Aka sake bugowa ta daga a lokacin kuma sai magana ake yi da Badi'a da Falalu da taji sosai da kyar taji kamar anc e Munir ne ba kya ji?" Sai ta ce, "Don Allah kayi shiru ana waya ta zunguri Badi'a din ma suka yi shiru. Sai kuma taji an kashe wayar har suka fito a shoprite din bata ji an sake wayar ba don haka itama ta dore sabgar gabanta daga can ta gidan Anti Mairo suka biyo. Ba su dawo gida ba sai dare. Har suna shirin kwanciya kuma sai wayar ta sake yin ringing da sauri ta dauko ganin lambar dazu ce. 751Shafi Zumunci Dangin Kaur Jamila M. Danfajo Bai yi magana ba sai kawia taji ya ce, "Tambayarki nake yi, da wa ki ke magana ki - ya yi shiru?" Bata tanka ba ta yi kamar bata ji shi ba, ta ce ba magana nake yi miki ba?" Tayi shiru ta rasa me ma zata ce, sai kawai hawaye ne yake zuba a idonta wace irin rayuwa Munir yake so suyi ne? So yake ya takura rayuwarta ko me? Daga can taji ya yi tsaki ya kashe wayar. Ba a jima ba taji suna waya da Hajiya Mama, tana faman Allah ya sanya alheri ubana Allah ya kara daukaka." Yana amsawa tayi masa sallama ta kashe. Can a tsakar gida taji Maman tana gaya ma su Talatuwa da Kande ubana ne ya samu kasrin girma a wurin aikinsa can Lagos. Da a Port Harcourt yake wata daya aka maido shi Lagos kaji daukaka da Allah yake yi ma bawa, da albashinsa kawai ake biyansa yanzun kuma shi ne Director. Idan kaya zai fito an bashi shayarsa daban shima ya samu nasa. 76 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Talatuwa ce mai tambaya tana tambayar Maman ta ce, "To Hajiya wani irin aiki yake yi?" Hajiya Maman ta ce, "Aikin kamfani ne, kın san kamfanin tukin zamani na Manoma? To a can yake aiki. Don nima wannan fitarwar zai bani 'yar tirela uku na dora nawa." Talatuwa ta rike baki ta ce, "Hajiya a Tirela ukun nan fa sai ki samu ribar miliyan da rabi." Hajiya Mama ta ce, "Ko fi ba! Ai mu ba abin da zamu cewa haihuwa sai dai Allah ya masu albarka, bana ubana Allah ya yi dashi. Abokinsa ne suka yi karatu tare dan mutanen Katsina ne asalinsu, amma mazauna Kaduna da kamfanin Kaduna yake aikin yasa aka maida su Port Harcourt da daya abokin. Yanzun kuma da yaga gaskiyar uban nawa sai yasa aka ba shi Director General a kamfaninsu na takin zamani a Lagos. Ya ce kuma duk kayan da za a fitas ya dora nasa, kin ji fa baiwar da Allah ya yi masa." Shigowar Alhaji ne ya katse hirar sai a lokacin ne Zainab ta saki ajiyar zuciya taje ta 77151 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo dauki wayar Maman ta duba. Lambar taga iri daya da nambar da aka kira ta, ta Mama tayi saving mai sunan Mallam ta gani, don haka tayi saving din nambar itama a wayarta. Tun daga ranar tana sa ran kiran Mai sunan Mallam amma shiru bai sake kiranta ba, har ta dangana. Watansa uku da tafiya ya zama mai arziki abin nunawa saboda yadda ake fadar miliyoyin ribar da yake samu a rana daya nayan albashinsa. Bai zo gida ba sai da ya shiga wata na shida da tafiyarsa, ba shi da hutu ko kadan yanzun ma ya samu hutun rabin shekara ne yazo gida. Wannan an san da zuwansa, don haka Hajiya ta hana kowa sakat da zuwan ubanta, aiki ake yi sosai don da abokinsa za su tajo Sa'id. Wanda suke tare a kamfanin Babansa zai wuce Katsina daga nan. Don haka an yi girkegirke na mamaki. Dambun nama da soyayyun kaji ba magana, saboda yawan su. Shigar safe suka yi ma Kano, don karfe takwas ma suna babban falon 781shai1 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Alhajin suna break tare da shi, sai hirar kasuwa suke yi. Sa'id kam! Ya yaba da halin karamci irin na Kanawa, da ya tashi tafiya ya shiga suka gaisa da Hajiya, yaga 'yanmatan gidan Hajiya din ya kalli Mai sunan Mallam ya ce da shi. "Ni fa a gidan nan naku za a bani aure, don zuri'ar nan tilas mu hada ta da ku abokina." Dariyar yake ya yi ya ce, "To abokina ka ,, duba mana gasu nan." Ya fada gabansa yana bugawa kar ya nuna Zainab. Zainab ce ta fara gaishe shi ya amsa, sai Badi'atu da ta sha mur! Sai kuma ga Ummi Farida mai bin Badi'atu ce tazo a nan ta kwana tana taya su aiki. Kallo daya ya yi ma Ummi ta din ya ce, "Abokina wannan tayi." Ya Munir ya yi dariya ya ce, "Ba ka iya zabe ba abokina, wannan fa 'yar Secondary ce, yaushe z aka iya da reno zaka ji ko kuma da aikin gabanka?" Ya yi murmushi ya ce, "Ba ruwanka." Ya juyar da kallonsa ga Ummi ta din da take tsaye bakin kofa. Ya ce, "Beauty ba kya sona?" 791 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Dariya tayi tana rufe bakinta cike da mamaki ta ce, "Ina sonka mana." Ya juya yana hararar Munir din ya се, "Ка ji kunya abokina, tana sona ganin farko babu bata lokaci." Ya fada yana cewa, "Beauty zo ki ga muyi hoto ga wayata ina zuwa gida Mummy taga hotonki." Sai kuma a lokacin kunya ta kamata, ta ruga daki da gudu, yayin da suka fito da shi da Sa'id din suna dariya. Ba a jima ba ya dawo yana gaya ma Hajiya Mama, Sa'id fa da gaske yake yi yana son iri a gidan nan, ya yaba da karamci irin na kanawa." Hajiya Mama tayi murmushi ta ce, "Oh! Allah mai hikima! To yaga wadda tayi masa ne?" Ya ce, "Eh! Ya zabi Ummitan." Hajiya Maman ta ce, "Ga Badi'atu za ku ce ga Ummita? Da ko Seconary bata gama ba?" Ya yi dariya ya ce, "To Mama ita ya nuna." Ta ce, "Au! Har ya zaba ne?" Ya ce, "Ya zaba 99 mana." Ta ce, "To Allah yasa hakan shi ne yafi alheri." Ya amsa amin. 80ha: Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Lamarin kamar wasa, tun safen yake makale da Ummita, kaya kala-kala ta sanya wannan ta canza wancan sai faman kamshi da take yi. Shi kansa yasan Farida yarinya ce amma babbar garinya mai sa'a, yasan duk macen da ta same shi tayi sa'ar rayuwa a rayuwarta. Kwanansa biyu a Kano ranar da zai tafi ya shiga ya fita rike da hannun Farida ya rasa in da zai sanyata don so da soyayya. Bai taba tsammanin matar aurensa a nan Kano take ba, sun yi hotuna kala-kala da shi da ita. Ya ce, "Ummi Farida bana son na tafi na barki. Ummita kin yadda na tafi da ke?" Ummita yarinya ce amma ta shayar da shi mamaki. Ta ce, "Idan lokacin binka ya yi zan bika ai." Ya yi dariya ya ce, "Haka ne masoyiyata." Rakiya har air port su kansu 'yan uwan nata mamaki suka yi da yadda ta iya soyayya da wannan tsadadden mutum. Da za su rabu ya bar mata wayarsa guda daya ya ce "Zan kira ku gaisa da Mumyna kin 81 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M Danfajo ji ko?" Ta ce, "To, Allah ya sauke ka lafiya." Ya amsa "Amin." Lokacin da zai hau Jirgin ma sai da Munir ya kwala masa zagi ya ce, "Kai wannan ban san irinka ba wallahi, ka fiye jaraba wallahi, ka hana yarinya sakat haka ake rayuwa?" Ya yi dariya ya wuce. Ya ce, "Ai ni zarra zan yi maka, aure zan yi na barka ba zan iya gayyar gwauranci ba, don ni wannan ba da ni ba, mutum kullum a wahala." Suka rabu suna faman sheka dariya. Ita kam! Goggon Mama sai ido ta zuba tana kallon Ummita, tana ba ta sha'awa bata taba sanin dadın soyayya ba tana kallon wanda ya same ta a cikin sauki mai tsananin sa'a, don ita ko kallo bata ishi Mai sunan Mallam ba. Ranar da Sa'id ya tafi Hajiya Mama ta sanya Ummita a mota ta rakata gida da labarin alherin da ya same su, sun kulle kansu a daki suna tattaunawa. Maman va mika ma Hajiya Rabi'a makudan kudi dalar Amerika ba canji ta ce, "Kin ga dai aikin manya. 82 Zum in auna 2 Jamila M. Danfajo Hajiya Rabi'a ta kalli kudi a ambulan ta ce, "Ni har na tsorata, irin wannan kudi Anty?" Hajiya Rabi'a ta ce, "Haba Hajiya, ke ni ba nayi zaton ma Badi'atu zai zaba ba, ya zabi Ummita." Hajiya Rabi'a ta ce, "Nima wallahi nayi zaton hakan, sai aka ce wai Ummita." Ta се, "Wallahi ita ya ce yana son, don gani daya ya mata ya ce ita yake so. Kin san 'yaran zamani kana raina su, sai su ba ka mamaki ta haka ne kam." Ga Ummi da ta tafi taya ku aiki ni mamaki ma take bani kuma ya ku ka yi da ita? Da ta tafi daga ita sai kayan jikinta?" Hajiya Maman ta ce, "Can cikin dinkunan da nayi za a kai su Abuja na fitar mata shaddodi da lesis sai wasu atamfofi super na bata takalma da mayafai ta ringar alfarma, kin san su da son wannan kananun kaya, na hana ta sanyawa. Amma ranar da zai tafi ina kallon su sai da suka yi mata kwalliyar kananan kaya." Hajiya Rabi'a ta ce, "Hajiya Allah ya kara girma, 831Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo wannan دو kudi tafi dasu a san abin da za a yi da su. Та се, "То bari na bayar Hafizu yaje ya bude mata account" Ta ce, "To duk yadda ki ka yi daidai ne, ni tsakaninmu sai dai addu'a." Та сe, "Haka ne, yanzun muyi shiru da bakinmu, don ni wannan komawar ta ki gefe tayi mana dadi, dan a cikin gidanki suka hadu da mun ga hassada." Ta ce, "Ai Allah ya mana maganinsu." Kwana biyu ita dai Goggon Mama ta zuba ma Munir ido yana yadda yaga dama, don ko gaisuwa sai yaga dama yake amsawa. Don haka gaisuwar tata ma ba sosai yake amsawa ba, don haka itama ta dauki matakin gani da ido. Abu daya ne yake mata ciwo, taga soyayyar da ta kullu a stai daya tafi tata daraja. Lokacin da ba ya nan tana masa gyaran daki amma da ya dawo sai ta daina shiga, abincin ma sai ta daina kai masa. Ko an shirya abincin sashensa sai dai tasa Badi'atu takai masa ko Ummi Farida amma ita dai bata lekawa ko kwas! 841shafi 1 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ranar Juma'a da yamma da yamma duk suka shirya za su gaida Umma, Badi'atu ce ta shiga ta dauko mukullin mota, ta ce "Don Allah Hajiya Mama na tuka mu." Та се, "A'a Badi'a, je ki kirawo mini Yayanku yazo ya kai ku." Ita kam! Gaba daya ranta baci yayi. Goggon don tasan ko hanawa tayi ba yadda Maman za ta yi ba. Tunda Badi'atu ta tona musu asiri da sai dai su fice suyi tafiyar su ba wanda ya sani. Ya shigo yana muzurai don shima yanzun ya yi kwarin kai neman rigima yake yi da ita sosai, don haka take tsarewa mutuncin ta itama. Hajiya Maman ta ce, "Je ka kaisu unguwa daman Falalu ne yake kai su to ita wannan sarkin ikon ta ce Falalu ya daina kai su unguwa. Ya juya ya harareta ya ce, "wallahi Mama da hutawa zan yi." Ta ce, "To ya zan yi? Ta raina Falalu ranar nan kuka ta sanya mini da na ce Falalu ya kaita unguwa. Yanzu karfi da yaji sun koyi mota, don kar yana tuka su to ni tukin ne bana sonsa sai 85Sh Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo dole." Ya amshi mukullin ya yi gaba yana fadin, Sai mun dawo Mama. Ta ce, A dawo lafiya. Ya amsa "Amin." Suka bishi. A mota suna tafe ya danna karatu a motar ba magana kenan fa har suka je, Umman tayi musu oyoyo sosai, abin da ya kara tayar da hankalin Goggon Mama. Suna zama ko hutawa bata yi ba Anty ta ce, Oyoyo ga Amarya. Badi'a ta ce, Anty wacece Amaryar? Anty ta ce, Ah! Ke da wa ki ke tsammani ba Goggon Mama ba? yau da safen nan Alhaji ya yanke auren ku, ke da Mai sunan Mallam ya ce duk abin da za a yi bikinku wata uku ya dibar masa. Idonsa akan Zainab dın yaga ya zata yi? Ai kuwa mur! Tasha, ta bata fuska tamkar bata taba dariya ba. Shi ne ya yi dariya ya ce, Anty dole a ba ki goron albishiri. Ya dauko mata sabuwar Naira dubu, tayi dariya ta ce, wallahi nayi zaton ma 'yar dubu namsin din nan za ka ba ni." Yana dariya ya shiga dakin Ummansa yana fadin, Ina Hajiya Momy kuwa? Anty ta ce, 86 a Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M Danfajo Taje unguwa yau, mu ne da gidan." "Ya yi kyau." Ya fada yana shiga dakin. Umman sun kewaya ta kowa yana fadan matsalarsa, shi kam kallonta yake yana mamaki, ko murnar auransu bata yi. Ya dan basar da tunaninsa ya ce, Umma ina son ganinki, gashi kuma naga kin yi baki. Тa kalle shi ta ce, Nima ina da magana. Ya се kamar wacce fa? Ta ce, "A'a ba wata magana ba ce zancen lefenka ne daman. Ya girgiza kai yana kallon yadda Goggon Maman ta daure fuska, ya ce wannan maganar ta wuce ai. Hajiya Mama ta ce, Ba za ai lefe ba Maman? Ta girgiza kanta ta ce, Ba zai yiwu ba ai, ita Anty idan ka biye mata kyauta zata baka auren yanzun tayi maka komai da ta tsaya ka mallaki gida unguwar nan, kusan rabin kudin nata ne, ta baka diyarta kalli yadda muke artabu da makiya. Kana gani dai yadda ta kawas da idonta daga kowa sai ni da 'ya'yana take kallo. 87 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Kaga yadda take dawainiya da kai daga karatunka har zuwa yanzun ni kuma don lefen da za a yi ma diyarta ya gagare ni? Ai ko da kudina ma zan bayar a hado lefen. Ya yi dariya yana sosa kai, ya ce, Ni fa da wasa nake yi miki. Sai da ya gama zancensa ya fita sannan ta juyo kan Hajiya Maman ta ce, Uwata me yake damunki ki ke irin wannan ramar? Ba ta tanka ba ta ce, Ki kalli fa Badi'atu kin fi Badi'atu girma da komai amma a ce yanzun tayi kamar ita ce yayarki? Tayi shiru bata tanka ba ta ci gaba da lallashinta. Ta ce, Ki fada min ko wani abu ne yake damunki, don Allah ni zan yi miki maganinsa da karfina. Idan kuma daga Allah ne zan yi miki addu'a, Allah ya saukaka miki, ko me yake damunki. Bata yi magana ba har ya shigo ya ce, Ke Ummita ku fita a nan, ke Badi'a kuje falo, me yiwuwa idan ba kwa nan ta fadi abinda nake mata. Suna fita ya koma bakin gadon ya zauna. 881Shaf : Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ya ce ta fadi me nake mata, ni da bana gari, don tana ramewa sai a ce wani abu nake yi mata saboda Allah? Umman ta ce, Haba Mai sunan Mallam, tun farkon soyayyarka da Goggon wahala kawai ka ke gana mata, da wulakanci don dai tana sonka. Idan ka san kafi son 'yar Maidugurinka ka kyaleta ta zabi wanda take so a cikin masoyanta, ayi mata aurenta amma irin wannan takura da me tayi kama? Ko don kaga uwarta ta dauki son duniya ta dora maka? Idan ka kashe mata 'yarta ya ka ke so ta ganka? Sai a lokacin hawayen idon Zainab din suka zubo, ta kifar da kai da filo ta ci gaba da kuka mai shessheka. Tausayinta ya kama Umman, itama hawayen ta goge ta ce, Duk abin da ka yi ma yarinyar nan ba dan kadan ba ne tunda har tayi kuka irin wannan. In dai haka ne wallahi Mai sunan Mallam ka zalunci kanka wallahi, don ni ma ba zan yafe maka ba. 89 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Na lura ma so ka ke ka tona mana asiri a dangi, kalli yadda aka yi rigimar nan da kyar abubuwa suka gyaru, amma ka zo kana tona mana asiri kana yi ma yarinya wulakanci. Kai ni idan ka kai ni bango wallahi Allah sai na maka baki a kan kukan wannan yarinyar, don ba don mai zurfin ciki ba ce idan irin su Badi'atu marasa hakuri da yanzu kowa yasan abin da ake yi. Jikinsa ya yi sanyi, ya ce, Don Allah Umma kiyi hakuri kuskure aka samu, komai ya wuce don Allah ki yafe mini." Ta ce, "Ni laifin me kayi mini? Ni baka yi mini laifin komai ba, idan ka shirya da Goggona wallahi ko yanzun Allah Ya maka albarka." Ya yi murmushin dole ya ce, "Shi kenan ki kwantas da hankalinki, insha Allahu komai ya 99 wuce. Ta tashi ta fita, suka yi zaman shiru a dakin, yayin da Zainab din take faman shesshekar kuka. Ya yı gyaran murya. Ya ce, "Ya isa, ya isa haka nan kukan Zainab. 901shat Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Da za ki zo ki haďa ni da Umma, ni kin san laifin da ki ke mini ne? ya yi tsaki, tsawon lokaci sannan ya sake magana. Ya ce, "Wallahi idan ki ka hada ni da mahaifiyata ba zan yafe miki ba." Ta saki ajiyar zuciya, tana bude idonta tana kallonsa ido-cikin-ido, ta ce "Ni ce zan hada ka da mahaifiyarka? Ni? Ni ina ruwana da kai da zan kawo kararka? Wallahi ko za ka kashe ni ba zan kai kararka ba. Ka kashe ni ma mana, idan na mutu kai ma ai kayi asara bani kadai ce nayi asarar ba. Kai ma kayi asarar nan." Tana magana cikin sanyin murya, "Kuma wallahi-wallahi ban taba tunanin na gaya ma kowa abin da ka ke yi mini ba. Itama ganewa tayi, da ta tambaye ni kuma ba abin da na gaya mata wallahi, ka tambaye 99 ta." Suka yi shiru suna kallon juna. Idan tayi tunanin ko ba ya sonta ne, ko daman ba soyayya ba ce? Sai ta ringa tuna kuma yadda hankalinsa ya tashi lokacin da aka ce za a hada ta aure da Suraj. 91 Shaii Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Da yadda ya ringa rokonta alkawari ta rufa masa asiri ta ce shi take so. Amma kalli yadda ya watsar da ita, kamar ba ita ba. Ta goge hawayen da ya zubo mata ta ce, "Kuma maganar gaskiya ce da ta ce idan ba ka sona ka bari na fitar da wani cikin ma su sona ya aure ni. Tun ba ka sanya ni cikin bakin cikin da zai kashe ni ba, don yanzun ma ina gab da shiga wani hali, ni ban takura dole ka aure ni ba, amma idan ba ka yi ka fito ka gaya mini a ruwan sanyi mu rabu a girma da arziki da salama." Ta fada tana mikewa tsaye zata bar dakin. Ya sha gabanta, zuwa yanzu hankalinsa ya gama tashi gaba daya, ya rasa yadda zai yi. Bayan tausayin Goggon Maman har wani so ne ya lullube shi, idonsa ya kada ya yi jajir, damuwa tayi masa yawa, ya kamo hannunta ya zaunar da ita. Sun jima shiru ya rike kansa, sannan ya dago ya cire hular kansa yana kallon ta ya rasa kalmar da zai yi amfani da ita. 921ShaT Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Sannan ya daure ya yi 'yan mazanci ya ce, "Kiyi mini ahuwa Zainab, tun farko naso na hakura da auranki saboda damuwar da na tsinci kaina a ciki. Na rasa yadda zan yi ne, ba irin zargin da bai zo zuciyata ba a kan aurenki da Suraj, ban san wace irin mu'amala ku ka yi da shi ba lokacin kina da auransa. Haka kawai sai na tsinci kaina da mai kyamar matar da aka ce ya kusanceta, kishi da bahagon hasashe suka sanya gaba daya na tsani auranki. Kuma idan kin duba hakan kin san ba komai ba ne Zainab sonki ne ya yi mini yawa, yake neman ya jefa rayuwata cikin wani hali. Ki gaya mini gaskiya idan kin san da akwai boyayyar mu'ammala tsakaninki da shi kar ki gaya mini ki bar ni haka illa iyaka mu hakura da juna. Donni ba zan taba aurenki ba muddin wani ya riga ni mu'amala da ke, ko ya riga ni kusantarki, kuma da wa naji kina magana ranar da na miki waya?" 931Sha Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ta mike ta bar dakin da gudu, don ta rasa ma me zata ce masa, tsabar tashin hankali. Tana fita get din gidan ba kowa tuni ta tari adaidaita sahu ta bacewa unguwar. Lokacin da ya fito bai ganta ba, sai ya gewaya gidan Nuri ya ce mata Goggon Mama ta shigo? Ta ce, "A'a. Don haka yana zuwa gidan ya ce, Badi'a ku fito mu tafi, Ummita ta ce Ban da ni. Ya ce, Meye yasa? Ta ce, Mu fa muna (final exams) na kuma gobe karfe tara zamu zana (maths) ya ce, Allah Ya ba da sa'a." Ya juya da sauri ya fice. Ganin saurin da yake yasa Badi'atu ta dauki da za ta dauka ta wuce da sauri ta bishi wani irin gudu yake yi yana duba hanya amma bai ganta ba lokacin daya iso gida Magariba tayi. Ya iske Hajiya Maman da baki ya wuce dakin Zainab din tana kan gado kuka take yi. Ya zauna gefen gadon jikinsa ba kuzari, muryarsa ba karfi tamkar ba namiji ba. Ya ce, "Zainab! Zainab!! Zainab!!! Ba kya ji ne? 941shat Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Kiyi hakuri kin ji ko? Ki daina kukan nan don Allah, kiyi shiru." Ta saki shesshekar kuka da ajiyar zuciya mai karfi. Ta juya can take kallon bango. Ya ce, "Kiyi hakuri don Allah, ki taimake ni kar su Mama suji zancen da muka yi, kin ji ko? Ko ki tashi muje can dakina muyi maganar da zamu yi, don Allah kar ki bari suji ko me ki ke so zan yi Zainab, kiyi shiru da kukan

Chapter 10 of 13