Share this page
sai da suka shiga yada magana. 201Shaf Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Can dakunanta biyu da falo na tsakar gida da suke gefe guda, suma an gyare su ta zuba kekunan dinkinta a cikinsu. Kusan keke biyar ne har da na wuta, ba abin da ba a dinkawa a ciki, yara ne suke dinkin da matasa kusan dukansu 'ya'yanta ne. Zannuwan gado da labulaye (Ready made) sai dinkunan su shadda da ake yi ma aikin cinku, ko aikin sama. A dinke su a fita da su cikin leda sinkesinke, don sitayil iri-iri ba irin wanda ba sa yi, yayin da Alhaji ya daure mata baya. Kaya direct daga China ake kawo wa, sai dai ta kwance a nan don shadda da lesis da material daki guda ne a jibge da kayan sayarwa, atamfofi da takalma. Dogayen riguna da hijabai komai idan an shigo da shi daga waje sarinta daban ne, ta bayar da sari ta sayar dai-dai. Shi kansa Alhajin dawowar Hajiya Magajiya cikin garin dadi ya yi masa don ya zamo kullum zai shigo da safe ya gaisa da 'yan tsofaffin da suka zamo dole daman a ce shi ne 191Sh411 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo maganar sayen furnitures na ce taje da Hafizu ya rakata ta zaba na bata kyauta." Hajiya Sa'ade ta ce, "Lalle madalla an gode ni dai a sa da ni a wannan business din tunda har shagunan furnitures aka bude." Hajiya Mama ta ce, "Za a daga miki hannu, sai idan mijinki ya yarda." Ta ce, "Yo kema ya yadda ki ke yi balle ni." Hajiya Mama ta ce, "Kuma fa haka ne, na manta." Suka kwashe da dariya. Ta ce, "Ashe dai kin tuna." To haka rayuwa tazo ma Hajiya Magajiya cike da cin nasarar mahassada, kudaden da a da ake hana su yanzun sun dawo an ba su. Hatta kudinta da ta kashe a wajen ginin gidan tun farko ya maida mata, rayuwa tazo mata cike da ci gaba iri-iri, addu'arta kullum Allah Ya kawo mata Mai sunan Mallam. Amma shiru ba labarinsa, tafiya ta tafi tsawon wata biyar kenan balle Munir da ya zamto mata tamkar dan gudun hijira. Ya tafi kasashen Turai gida ya zame masa kamar ba shi da kowa, kullum addu'a take yi 23S Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Allah Ya kawo shi duk inda ya shiga a fadin duniyar nan. Don ita Hajiya Sa'a tana da labarinsa, amma ko lambar wayar diyarta bata bari a samo balle har ayi maganar ina Nabil? Sai dai ta aiko mata dukiya makis da kudade ayi ta facaka da ita. Ita dai Hajiya Mama bata magana, ta bar wa Allah ån raßa da zumunci an cuce ta. Ka ji rayuwa. Munir kam tun ranar da Zainab ta kira shi a waya, tun ranar ya rasa sukunin shi. Ranar wata Juma'a kamar kullum, bai je office ba saboda canjin da aka yi mishi na aiki zuwa Port Harcourt can kamfanin Alhaji Lurwan din, in da dansa yake aiki. Jikinsa ba dadi ya wayi Juma'ar zuwa Port Harcourt din, ya janyo ya tsani aikin ma, don haka ya duba account dinsa ya iske kudi da dama da yadda yake so, don haka ya kwaso yadda zai ishe shi ya yi shirin gida. Abdulbasi ya ringa masa dariya yana fadin "Yau Kano ta kira ka, gurasa tayi kira ko?" Suka yi dariya. Ya ce, "A'a ya kosan Hajiya Mama ne ya kira ni, tafiya zan yi." Ya ringa 241 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo dariya yana fadin. "Ko dai Zainab ce tayi kiran?" Ya girgiza kai ya ce, "Kyaleta kawai Abdul, Zainab haushi take bani." Ya ce, "A'a me tayi maka?" Munir din ya rike kansa tsawon lokaci. Ya ce, "Ni ai ka san maganar auren nan ne gaba daya bani da tabbas a kanta. Kai ni fa tunda aka yi auren Zainab din da Suraj, ba ita Zainab din ba shi kansa Suraj din na tsane shi. Itama Zainab din na tsaneta. Kai ni fa Kanon ma ba son zuwa nake yi ba, zan dai daure naje ni saboda iyayena ne, amma idan don Zainab ne wallahi na bar Kano har abada." Abdulbasi ya ringa tausaya masa yana kallonsa cike da alhini ya ce, "Kayi hakuri haka mata suke, duk kiyayyar su da namiji sai dai bai kai su shimfida ba, yanzun za su manta da wata kiyayya." Ya ringa ba shi labarin wata kanwarsa da aka yi ma auren dole, ya ce, "Za ka yi mamaki idan ka ganta yanzun har da ‘ya'ya biyu. Sabanin lokacin auren har fetur ta zubawa kanta zata sanya ashana aka kwace. 251Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Wallahi alkawarin mata ragagge ne a kan soyayya. Kayi hakuri wallahi wata rana sai ka ce na gaya maka, sai ka samu wadda ka ke so fiye da ita wallahi. Balle kai ga Yaganarka nan mai sonka." Ya yi tsaki ya ce, "Maganar Yagana ya wuce wallahi, ko na rasa Zainab ba zan iya aurenta ba, sai dai kawai ayi addu'a." Sai yamma ya tafi saboda sai da ya yi tsaraba sannan ya nufi Kanon Dabo, garin da yake so fiye da kowani gari a duniya. Amma soyayyar mace yasa ta tsani gari a da ko hutu zai taho daga Maiduguri, farin çiki yake ya shigo garin Kano yana walwala yana farin ciki. Zai nufi zoo road ba abinda yake son gani irin ya yi ido biyu da Zainab din, don yanayin da yake ciki. Tabbas idan ya kalli kyawawan idanuwanta, sai sanyi ya sauko a zuciyarsa. Yanzun kam! Ya tsani unguwar zoo road din saboda duk masifar da ya tsinci kansa а ciki ya san ba kowa ba ne ya yi masa sanadinta 261Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo matan gidan ne. Don haka ya ke ji a ransa baya son gidan. Gidan Mahaifinsa kuma, ba ya son zuwa kar yaga Suraj, don haka kansa tsaye Soron Dinki ya yi ma tsinke, tara da rabi na dare. Ranasr Alhaji ba a gidan yake ba, a harabar gidan ya jibge kayan da ya zo da shi. Falalu ne yake faman taya shi. Falalu wani yaro ne shima dinki yake yi ma Hajiya Mama. Sallamar Munir ne ta katse musu zancen da suke yi da Hajiya Maman da Zainab. Da sauri ta dago ido ta kalle shi, shima idonsa akan Zainab din, zuciya taga abincinta, don haka dole ido ya bayyana sakon zuciyar. Hajiya Maman ta ce, "Amin wa'alaikas salam. Mai sunan Malam! Oyoyo ubana yazo shi, oyoyo." Yayin da Munir din ya ringa murmushi, har gabanta ya isa ya durkusa. Farin ciki a wurin Hajiya Mama kamar tayi ya ya? Ta kai hannu ta cire masa hula ta се, "Oyoyo ubana, ya hanya?" Ya ringa murmushi ya ce, "Hanya sai godiyar Ubangiji." Hajiya ta ce, "Falalu bude 27 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo sashen bakin ka shigar masa da kayan nan, shigo ubana." Ita kam Zainab kallonsa take yi, suka shiga falon na Hajiyan ya shiga yana cike da gajiya, ya zauna a bisa carpet. Hajiya Maman ta ce, "Ubana hau sama ka zauna mana." Ya yi murmushi ya ce, "Na gaji יי ne Hajiya, bari na huta anan din ma. Hajiya Maman ta juya ta kalli Zainab din ta ce, "Ke kuma sai bin mutane ki ke yi kamar mai tallan makilin, kina wage hakora. Haka ake saukar bako? Ki kawo masa ruwa mana. Shima Munir kallon Zainab din ya yi ta wuce kitchen din falon ta dauko robar Faro da Exotic ta doro bisa tire da kofuna, ta kawo ta ajiye masa. Suna ta hira da Hajiya din suna ta labarin tasowar Maman gidan taga ta kawo tuwo, don daman sakwara suka yi da agushi miyar naman kaji ta shiryo ta ajiye masa a lokacin ma sai da tayi dabara suka hada ido da shi. Ji tayi kamar ta suma don farin ciki, da wani irin dadi da ya rufeta. Dakinta ta shige tana jiran su gama hirarsu da Hajiya Maman, 28 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo amman shiru kamar ana kara zuge su. Labarin auren nan kakaf! Sai da ta sa shi, ba magana da ta dago masa hankali irin da ta ce an raba auren da Allah ya tona musu asiri. Da kansa Suraj din ya fallashe su abin kunya dai sun gama yinsa." Har Hajiya Maman ta tashi a wurin hankalinsa ba ya jikinsa, ta ce bari naje ubana nayi baki. Ya ce, To nima so nake na watsa ruwa nayi sallah sannan naci abinci. Ya fada yana tsiya ya lemo ya sha. Zuciyarsa fal! da tunani iri-iri, to kafin a raba auren ma Suraj ya yi ma Zainab? Ko kallonta kawai ya yi? Aure kusan wata guda fa? Ko to ba shi kanta ne ya tona asirin iyayensa? Anya zai tona kyauta? Ya aka yi aka rabu cikin sauki? Idan Zainab ta kusanci Suraj ta cuce ni. Shaidan ya ringa kitsa masa maganganu iriiri, tilas ya dauki daya ya watsa da sauran tunanin. A daidai lokacin Zainab din ta shigo 29 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo ta caba ado cikin atamfa, dinkin ya mata kyau sosai. Sai kamshi take yi duk yadda kishinta ya mamaye ta birge tabbas ya yadda yana sonta. Ya tsaya ya kare mata kallo Zainab mai kyau ce sai dai tayi muguwar rama. Ta zauna a gefansa, amma ta kasa magana, sai murmushin take yi, shi kam! Gaba daya so ya mamaye zuciyarsa sai san yana son Zainab haka ba sa yau din shi take kallo. Idanuwan sun kafe, sun kasa hakura da junansu zuciya ta isar da sakon abin da yake cikin ta, ta hanyar kallon. Shi ne ya yi 'yan mazanci ya dauka idonsa itama sai a lokacin ta hankalta ta ce mishi. "Sannu da zuwa ya hanya?" Bai amsa ba sai murmushi da ya yi, sanna ya ce mata. "Hanya Alhamdulillahi Zainab." Ta tsiyaya masa lemo ta ce, "Ba ka sha komai ba fa." Ya kalli lemon ya ce, "A gajiye nake Zainab, da wanka zan yi da sallah." Ta се, "A'a don Allah kasha lemon." 301a Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ta fada cike da shagwaba. Ya yi murmushi ya ce, "To bari nasha." Itama murmushin tayi. Sai da ya sha kuma ya mike yana kallon aogo ya ce, "Dare ma fa ya yi." Ta ce, "To a biyo ka da kayan abincin?" Ya dan kalleta ya yi jim! Sannan ya ce, "Bari zan dauko. Da wannan kwalliyar za ki fito gaban su Falalu?" Tayi murmushi ta ce, "To na jira ka a nan din za ka dawo." Ya kare mata kallo, zarginsa yana kara karfi a zuciyarsa, an ce idan mace tasan namiji ba ta da kunya, bata tsoron maza. Ya ce, "A'a kije ki kwanta sai da safe." Sai kuma ta langabe kai ta ce, "Ni dai don Allah Yayana ina jiranka." Ya yi murmushi ya ce, "To shi kenan, in dai ba za ki gaji da jiran ba ki zauna." Ya fada yana daukar kayan abincinsa. Sha daya da rabi ta gaji da kallon Arewa ta koma Tauraruwa, wani fim suka sanya ya dauke hankalinta sosai. Kallo take yi sai kuma ta gan shi ya shigo sanye da jallabiya fara kal! Sai kamshi yake yi. 31 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Suna hada ido ya sakar mata murmushi, shi mamaki ma take ba shi ya ce, "Kije ki kwanta dare fa ya yi. Ta ringa kallonsa ta ce, "Kuma yaushe ne zan sha labarin Kaduna?" Ya ce, "Sai da safe, yanzun zamu zo muyi ta hirar hana Hajiya bacci ne?" Ta ce, "Cab! Ita ina ruwanta da kai, tana can fa sashen ma lissafi ita da Talatuwa mai kai mata kaya." 99 Ya ce, "A'a ni to ai na gaji zan so na huta. Ta bi shi da kallo yana fita a falon ta mike ta bishi cike da tsananin kewarsa. Та се, "Тo sai da safe ko?" Ya juyo yana kallonta, ashe biyo shi tayi. Ya yi murmushi tare da girgiza kai ya wuce ba tare da ya juyo ba. Itama sai zuciyarta ta darsa mata wani abu, amma kuma sai ta basar. Lokacin da taje kwanciya sai taci gaba da tunani, mutumin da ba ya son rabuwa idan suka fara hira, sai dai ita ta gaji ta ce masa dare ya yi, amma kalli shi yake gudunta. 321 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Fuskarta har ta nuna wani abu, amma sai wata zuciyar ta ce mata gajiya ce ya gaji ne. Tayi addu'a kawai ta kwanta. Da Asuba suna yin sallar Asuba ta shiga kitchen ta shirya masa break ita Hajiya Mama dama can babban kitchen ta nufa don daman kullum sai tayi abincin sadaka don kyauta, yan tsofaffi Baffaninsu ta ce ai ka ma break. Wani lokaci tayi kunun gyada da funkķasu, wani lokaci tayi koko da kosai ko tayi dan wake, fanke da kunun gyada idan tayi wainar masa. Tabbas da miyan kaji ko naman kai haka ranar funkaso miyar kayan ciki take yi don haka kullum sabon budi yake fito musu ita da mijinta. Yayin da tsofaffin kullum suke shi mata albarka. Haka nan duk wanda ya shigo gidan zai yi break mai kyau, don haka can a karamin kitchen Zainab din dankali ta fere ta hada masa kayan Sa, hanta da koda, tayi masa tea mai kayan kamshi sosai ta kai masa. 33 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Lokacin da taje ya shiga wanka, don haka sai ta ajiye komai a falo ta juyo itama tayi wankan ta shirya cikin wando da riga na shadda dinkin ya yi kyau sosai. Shaddar Sky blue ce tayi daurin dankwalinta saukake ta maida shi baya ta hada shi da parking din gashinta (acuci) ya yi mata kyau sosai, sai kamshi take yi. Lokacin tana shirin tafiya wurinsa, sai kuma gashi falon har kasa ya durkusa ya gaishe da Hajiya Mama, murmushi tayi ta ce, "Ubana an fito?" Ya ce, "Eh! Na fito Hajiya." Та сe, "Тo Allah ya maka albarka." Ya ce, "Amin." Hajiya ganin Zainab yasa ta bar wurin. Shima juyawa ya yi zai koma sashensa. Zainab din ta ce, "Yaya ina kwana?" Ya yi kamar ban ganta ba, yana tafe yana amsawa, don haka ta bishi falon nasa. A gefensa ta zauna ta hada masa filet, ta hada masa tea ya dauka yasha yana kallon yadda ta zauna a kusa dashi wanda a da din ba ta iyawa ko kadan. 34 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Kuma sai yanzun ta ringa shige masa? Tuni wani irin kishi ya taso masa, ya rasa yadda zai yi. Haka ya ringa cin abincin kamar ba ya so. Ta yi ta masa shagwaba, ba ya son cin abincin yana cewa ya koshi, ta tare shi da shagwaba. "Wai Yayana meye ya sameka?" Ya kalleta cike da shan mur ya ce, "Me ki ka gani?" Sai kuma jikinta ya yi sanyi. Ta ce, "Ba komai." Ta kwashe komai ta dawo, ya се "Ki janyo waccan jakar na sallame ki, tsarabarki ko?" Ta mika a sanyaye tana son yin magana amma ganin ba fuska yasa tayi shiru. Ta janyo masa jakar ya fitar da abinda zai fitar ya tura mata jakar gaba daya. Ya ce, "Ki zabi abinda ya miki, raguwar ki sallami su Khuzaimatu da Nuri ko?" Ta ringa kallonsa tana so su hada ido amma ya ki. Ta ce, "Ni fa ba wata tsaraba ce ta dame ni ba." Ya ce, "To me ya dame ki? Kin ji muryar Alhaji a falonsa ya shigo zan je mu gaisa, kuma ina son zuwa kofar Nasarawa. Ki bari 35IShaf Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo idan na dawo sai mu zauna ko?" Ya fada yana ficewa a dakin. Ta ringa kallon tsarabar kamar tayi kuka don tashin hankali, wani irin wulakanci ne wannan a wurin Ya Munir? Tunda yazo shi wani shasshareta yake yi? Bata samo amsa ba tilas ta hakura ta tafi. Hajiya Mama ce ta tayata ware tsarabar ta ce, "Bari na shirya ma yau yawo za ayi naje na kai ma Amare tsarabarsu." A falon Alhajin ma sun fi awa suna faman hira, shima Alhaji Karami a nan ya iske su aka yi murnar da shi, suka yi break sannan ya wuce kasuwa. Shi kam! Munir da ya yi wankan ma sai ya yi zamansa a falo, yana kallon tashar Aljazeera. Ita kam! Kayan tsarabarsu ta zuba a leda, har na 'yan zoo road tayi shirin tafiya (after dress) ta sanya ta fito. A kofar dakinsa ta tsaya tayi masa sallama, kallonta ya yi daga sama har kasa, ita kanta kallon sai da ya fadar mata da gaba. 361hafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo A gabansa ta zauna cike da mutuwar jiki, tana rangwadar da kai ta ce, "Yayana zan tafi. Idonsa ya lumshe yana jingine da kujera, shi kansa yasan ba ya kyautawa. Ya yi shiru bai tanka mata ba, ita din ma sai jikinta ya yi sanyi, ta ce "Yaya ko gajiyar ce?" Ya yi shiru bai tanka ba. A ransa kalma daya ce take masa yawo, ba shi da wanda zai tambaya sai ita, kuma ji yake idan ya tambayetga ya gama zubewa. Don haka abin nukurkusarsa yake yi, wace irin mu'amala tayi da Suraj kafin a raba aurensu? An raba auransu in ji Hajiya, sauran bincike sirrin zuciyarsa ne. Ya rasa yadda zai yi da ransa, da wannan al'amari mai rikitarwa ya kalleta cike da kishi a lokacin ma kamar ta shige jikinsa don tsananin nuna masa kulawa. Cike da kasala da wata irin shagwaba ta langaße tana tambayarsa abinda yake damunsa, Ta ce, "Yayana meye yake damunka ne?" Kallo daya ya mata zuciyarsa tana raya masa. "Ka ga ni ko? Bazawara sak! 371shat1 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ba ta tsoron maza ita din da a da take tsoronka kalli yadda take shige maka? Ya mike a tsaye yana daura agogon hannunsa, ya dauki hularsa yana murzawa ya се, "Кагбo mini mukullin mota a wurin Hajiya, unguwa zan je." Ta ceе, "То." Da hanzarinta taje ta karbo har durkusawa take yi wajen ba shi mukullin, jikinta yana rawa. Ya sake daure fuska yana wani shan mur! Jikinta ba kuzari ko kadan, muryarta har rawa take yi tana kallonsa ta ce, "To Yayana sauke ni gidan Khuzaiman, tunda fita za ka yi. Ya wuce ta yana goge takalmi, ya yi shiru kamar bai ji ta ba, ya fice ta bishi da kallo. Falalu ya kirawo tare suka shigo ya ce, "Falalu kai mini kayan nan mota. Falalu ya sunkuci Jaka, shi kuma ya juya ya kalleta ya ce, "A hakan za ki bi ni? Wannan rigar kina nufin hijab cсе?" Ta kalli kanta ta kalle shi, tayi murmushi ta ce, "Ban yi kyau ba ne Yaya?" Bai yi magana ba yana fesa turare sai da ya ajiye ya juyo ya kalleta. 381Saf P Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ya ce, "Kyau ake miki magana ne? sai kuma ta sake yin sanyi. Cike da dariyar yake ta ce, "Bari to nazo." Ta koma cikin gida aba daya ta canza kaya. Kwalliyar atamfa ta iyo, har kala da shi ke super ce sai tayi amfani da hijabi jar kala, irin dai hijabin robar nan. Bai kalleta ba suka fita, amma a hakan ma gani yake ta kure akwati ne, don tayi masa wani kyau na birgewa. Suna tafe a motar ba ya magana, sai ma ya danna karatun Alkur'ani mai girma, idonsa cikin bakin gilas. Munir yana da kyau ne ajin farko a cikin kyawawa, kalar wankan tarwada ne, sai dai yana kalar haske sosai. Don idan a cikin su Zainab ne to fari za a kira shi, yana da tsayi sosai, dogo ne, har kamar yana da jiki mai kyau. Idan ana maganar ilimi da wayewa idan ka samu Munir karshen zance kenan, dangayu ne mai tsafta, tsafta irin wacce ake cewa mutum yana da Aljannun tsafta. 39 Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Don ba abincin kowa yake iya ci ba, haka nan fuskarsa doguwa ce amma cikakkiya mai hasken annuri, yana da dogon hanci irin hancin nan mai karan hanci. Ya fito da manyan maganai duk tsaurinka idan ya kalleka sai ka saurara, don mutum ne mai kwarjini. Ba ka yi masa laifi ba ma shi kansa abin shakka ne, balle kayi masa laifi, ba kowane lokaci yake dariya ba, don haka idan ya yi maka fara'a za ka ji tamkar ya yi maka kyauta ne. Don haka a ko'ina yake da farin jinin 'yammata don sumar kansa kadai abin so се, balle ya yi dariya ka kalli hakorinsa za ka san Allah ya masa kyauta ta fararen hakora, da idan ya yi maka dariya tilas ka san yana da kyau. Kalarsa da tsarinsa, da yanayin karfin jikinsa, za ka yi tsammanin ya hada jinsi da Indiyawa. A mota suna tafe ba ya magana, bayan ma daure fuska da ya yi har gilas yasa (dark space) ya boye ganinsa. 40 21 Zumunci Dangin Kauņa 2 Jamila M. Danfajo Sanye yake cikin shadda mai kalar (Bournvita), sosai ya dauki dinki dogon riga ce har kasa tazarce ta asali, hularsa damanga ta bugu sosai kalar shaddar kamshi yake yi kamshin da gaba daya ya cika motar. Rashin walwalarsa da yadda yake shan mur din yasa itama ta kama kanta. Sai da ya dauki hanyar zoo road din ta ce "Fara kai ni gidan Khuzaima idan na gama sai na taho zoo road din." Bai yi magana ba ya ci gaba da tukinsa cike da izza da nuna iko. Ita dai bata yi masa magana ba, sai zoo road din ya nufa da ita. A gidan yara sun yi murnar ganinsu, ita kam! Sosai take walwalar ganin 'yan kannenta, musamman 'yan tagwayen Hajiya Sa'a da Kausar din Maman Ladifa, sun hana ta sakat. Inda kaga dariya a nan ka ke falon Maman Ladifan ta sauka itama kuma farin cikin zuwansu take yi. A nan Hajiya Sa'a ta same ta amma don Hajiya Maimu kin fitowa tayi sai da ta ji shigowar Munir, taji kuma yana rabon kudi 41 shati Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo (Aminin nata) ta fito suka gaggaisa da mutanen gidan. Ya juya ya fice a gidan yana faman shan mur! Su kansu mamakin yanayinsa suka yi. Ta basu tsarabar su suna faman murna. Itama a nan ta bar su da godiya fal! bakinsu, ta fice a ranta tana fadin, gidanmu gidan dadi, hali na nan. Da sauri ta iske shi a mota, sai da ta zauna ya ce, Ina ne gidan Khuzaimat din? A sanyaye ta ce, Ita Sagira nan ne fa sharada, ita kuma Khuzai din Na'ibawa din. Bai yi magana ba ya ci gaba da tuki yana fadin, "To Ladifa fa?" Ta ce, "Ita Ladin Ja'in ne." Ya ce, "To sai ki ringa kwatantawa, don sauri nake yi." Ita dai a ranta tayi farin cikin rakiyarsa, amma bata nuna ba. Gidan kowa aka je zai shiga ya yi musu murna, tare da ba su gudunmawarsa. Ita kuma ta ba su tsaraba har gidan Anti Mairo an je san ıan aka je gidan Khuzaimat. Ita da Khuzaimat din rungume juna aka yi ana faman dariya, duk 'yan uwanta sun fi shiri 421Sha Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo S da Khuzaimatu. Kuma sun fi yin fada, don sosai ake tafka rigima har a dambace amma idan ana maganar a sanya kaya iri daya su biyu ne. Don duk kayan da Goggon Maman ta sanya lokacin suna gida s ai ta koma ta gaya ma Ummanta ta ce Umma kin ga dai Goggon Mama ta sanya less, ko atamfa kaza, ko ta ce kinga dai Goggon Mama yau an canza mata sarka ta zirari ko kirar Dubai ce. Ga shi nan dai adawa ake yi ta kirki, kuma idan kowa ce Goggon Maman tayi tilas ta shige karkashin kowar nan ta raba su don haka ma bata kawa. Ke ko rigar bacci Goggon Maman ta sanyo sai ta sayi irinta, don sai an aiki Goggon kasuwa ta ishishshire ta ce sai sun je tare. Idan kuma an tafin ba komai zata sanyo ba kudi. Hajiya Maman zata bata ta ce ta ki duk abin da ta sanya kema ki sayo mana shegu iyayen mugun abu, komai su 6oye. Don haka ko saurayi Goggon Maman tayi sai tayi yadda tayi ta kore shi ko ta zuga ta ta kore shi. 431Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Gado karfin Allah, Khuzai duk halin uwarta ta debe shi, don duk yadda za a yi sai dai ayi, sai ta janye saurayin idan bai janyu ba to za ta zuga Zainab din a kore shi. Ko mijin da ta aura da farko Goggon Mama ya gani amma da ya zo aka kirata sai ita ta fito dan aiken ita ya gayawa. Don haka sai da ta san yadda tayi ta janye shi ta ce, ita an yi miji tuni sa dai na baka wata a kannen nawa. Yawan zuwan da yake ya gane an yi ma Zainab din miji, yana yawan ganinta da Munir din, don ta kure shi ma kirawo Ya Munir tayi ta ce, Don Allah Ya Munir ba anyi ma Goggon Mama miji ba?" Ya ce, Eh! Wani abu?" Ta ce, Ah! Abokin Tahir ne yake sonta." Ya yi dariya ya ce, "Ka ba shi hakuri tuni ni ne mijinta, to ta wannan silar ta janye Tahir ta masa waya 'yar ta masa gobe da haka ya zama dan gidan ta janye shi, Allah ya yi mijinta ne aka yi aurenta da shi. Don haka yana jin zuwan Zainab din ya fito yana murna ya ce, Sai yau aka zo gidan 441 Zumunci Dangn Kauna 2 Jamila M. Danfajo namu?" Ta ce, wani angon? Zainab ta ce, Mai sunan Mallam mana. Tahir din ne ya fita ya shigo da shi da Khuzai ta kawo musu ruwa da lemo da cin-cin tana fadin. "Ya Munir yaushe ne bikinku da Zainab?" Ya yi dariya yana ture hularsa baya ya kalli Zainab don da tayi bakam tana kallonsa. Ya ce, "Me ku ka tanadar mana ranar bikin namu?" Ta langabe tana kallon tahir din ta cе, "Ka ji fa sweety, wai me muka tanadar musu?" Tahir ya yi dasriya ya ce, "Ni party na shirya muku, ka zaba dinner ko kuma walima." Khuzai tayi ta ce, "A'a sisters day zamu yi ka san mu da 'yan uwa kowa yazo da mijinsa." Duka suka yi dariya. Ya ce, "Sha kurumin ki, ke dai Khuzaimat kiyi addu'a ni ina jin daurin aurena a Saudia za a yi." Suka sake yin wata dariyar. Ta ce, "Lallai Yaya ka ce mu shirya da wuri." Ya ce, "Ku shirya, ko ba haka ba Zainab?" Ya fada yana kallonta. 45 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Sai a lokacin ta saki ranta. Ta ce, "Haka ne kam!" Ta mike ta isa inda lemon yake kan center table ta zuba masa cup ta durkusa ta mika masa. Yana fadin "Na gode." Tayi murmushi ta zubo a kofinta ta dauka ta koma gefensa ta zauna, yana gamawa ta ce, "A zuba ruwa?" Ya girgiza kansa. Tahir ya kalli Khuzai ya ce, "Kinga yadda ake yi." Tayi murmushi tana harararsa. Ta ce, "Ni bana yi maka?" Ya ce, "Ba irin wannan ba." Ta ce, "Ka manta?" Ta fada tana harararsa. Ya ce, "Oh! Sorry ban manta ba." Та се, "To ita ta isa tayi masa wancan din?" Ya ce, "A'a ba ta isa ba, bata isa ba ayi hakuri kar a hana ni." Ta ce, "A to, za

Chapter 8 of 13