hidima da ‘yan
karin safe, sai Goggon Mama a dakin. Ya zauna
a gefen gadon da take kwance muryarsa a
sanyaye. Ya ce, "Ya dai Zainab? Ba ki tashi ba
ne?"
Ta ture bargo ta tashi ta janyo hijabinta ta
sanya a kan rigar baccinta, ta mike a tsaye tana
gyara gadon.
Ta ce masa, "Ina kwana?" Kallonta yake yi
bai amsa ba. Ta kuma cewa, "Yaya ina kwana?"
Ya ce, "Lafiya Goggon Mama. Ya naga idonki
alamar kin yi kuka? Zancen bai wuce ba? Ai ina
ganin kuka ya kare ko?"
Maganar tayi mata dadi a ranta, ta kalle shi a
sanyaye muryarta ba karfi ta ce masa, "Ni kam!
Ai ina tsoron Abban gidan nan, ka san shi fa?"
Ya ce, "Kar ki damu, in dai kina sona ai
komai zai zo mini da sauki, rashin samun hadin
kanki shi ne babbar matsalata. Ki kalli idona fa
ban yi bacci ba jiya ma." Ta сe, "To уyanzun kaje
kayi baccin mana ko?"
94shafi
:
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Ya girgiza kansa ya ce, "Akwai maganar da
nake son ji daga bakinki, tafi baccin a wurina."
Ganin yadda ya shigar da idonsa yake
kallonta yasa kunya ta kama ta, ta juya masa baya ta ce, "Ka fada me ka ke so?"
Ya ce, "Ni yanzun a duniyar nan ki ce kina
sona ai yafi mini samun komai a duniyar nan."
Ta ce, "Ina sonka Yaya Munir, ni kaina ban
san yawan son da nake yi maka ba. Ina sonka Yaya Munir, sai dai a yanzun son ba shi da wani amfani a tare da mu."
Ya ce, "Yana da amfani. Kiyi mini alkawarin
za ki kasance da wannan son nawa har karshen
rayuwarki, kiyi mini alkawari ba mai raba mu up
to the end with our life.".
Ta ce, "Nayi maka, amma akwai aiki a
gabanka."
Maganar Hajiya Mama ce ta katse su. Ta ce, "Ba wani aiki a gabansa."
Gaba daya suka yi cirko-cirko da su. Hajiya Maman ta ce, "Ina jin ku ai tun shigowar ka."
Kansa a sunkuye bai iya magana ba.
Та се, "Каyi kuruciya idan ana son mace ba a
yin shiru, me yasa tun farko ba ka gaya mini ba?
95h
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
ko ita me yasa ba ka gaya mata ba?" Ya sake
rusunawa ya ce, "Ai ni kam! Mama ban san ya
zan kwatanta miki ba, ina son na gama da
Yaghana ne, su ba sa son a fitas da ita a garinsu.
Sun ce idan har ba zan zaunar da ita a
Maiduguri ba to tabbas na hakura na ce musu
zan yi shawara su bani sati daya.
Lokacin zuwansu idan kin lura ai ita Yayarta
ba ta fara'a, basa son aurena da ita shi yasa da
nayi ma Umma bayani ta ce a'a kar ma na fara
kai mata ita gidansu. Shi yasa ma na kawo ta
nan.
Maman ta ce, "To ai shi Alhaji har yana
maganar sun yi magana da mahaifinta a waya za
su je Maidugurin."
Ya ce, "Eh! Na dakatar da su ai ni gani nayi
tafiyarmu ba za ta zo daya da su ba, don suna da
وو matsala sosai a cikin al'amuran rayuwa."
Maman ta ce, "To ai shi kenan, Allah Ya
zaba maka wacce tafi alheri." A sanyaye ya се,
"Amin." Tа се, "Кajе kayi ma Alhajin to bayanin da na ji kuna yi, don idan ni nayi masa
ban san ya zai dauki maganar ba." Ya yi shiru ya
ce, "To Mama bari ya dawo daga China sai a san
yadda za a yi, ina ganin yau da yamma zai tafi."
96
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Та се, "Тo Allah Ya dawo da shi lafiya." Suka
amsa "Amin."
Ta ajiye filas din da ta dauko cike da kunun
gyada, ta ce "Ai da ka gaya mini tun farko da ba
a kai ga wannan tashin hankalin ba.
Tun farko ma ido muka zuba muku mu gani
ko za ku hada kanku, sai ku ka tsaya ku ke
shiririta, ku ke neman fitina da junanku.
Amma ke Zainab ki tabbatar duk maganar da
ki ka fada tamkar alkawari ki ka dauka, ki
kiyaye karya alkawari kin ji na gaya miki."
A sanyaye ta ce, "To." Maman ta koma
kitchen ta kawo tire ta ajiye ta fice.
Ita kam! Goggon Mama wanka ta shiga,
bayan ta dauki duk abin da zata yi amfani da shi,
don haka a shirye ta fito fes da ita.
Cikin wasu irin Pakistan masu tsananin kyau,
kalar fari tas! Sai surkin silba zare da aka yi
kwalliya da shi, gashinta ta gyara shi sosai
tamkar wata 'yar Indiya, sai faman kamshi take
yi.
Ya bita da kallo yana murmushi. Ya ce, "Kin
yi kyau." Ta saki ajiyar zuciya. Ya ce, "Gama ki
raka ni Kofar Nasarawa."
97 |shati
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Ta ce, "Ni fa ba na son zuwa unguwar nan."
Ya girgiza kansa ya ce, "Kar ki kuma fadin
haka." Kanta ta karkace ta ce, "Ya Suraj fa yana
دو
nan.
Ya ce, "Kiyi yadda za ki yi ki manta da shi,
ya zama na karshe, kuma kar ki kuma ambatar
sunansa a gabana." Ta sunkuyar da kanta bata yi
magana ba.
Kofin gabansa ta janyo ta zuba masa kunun
gyada ta bude filas din kosai ta tura masa
gabansa ya fara break din.
Yana yi yana kallonta ya ce, "Ba za ki ci ba?"
Ta ce, "To ai akwai matsala ne, idan nayi break
fast da wuri."
Bai sake magana ba ya mike ya fita ya ce,
"To ni na gama ki zama cikin shiri."
Yana fita itama tayi break din daman tana kin
yi ne saboda shi. Ya shigo ya sameta a wurin da
ya tashi tana shan farfesu. Ya harareta ya се,
"Magulmaciya! Har da wai ba kya ci da wuri ne,
to kawo cokalin na baki a baki."
Ba shiri ta mike a tsaye tana fadin, "Wallahi
ni na koshi." Ya ce, "Wannan kuma shi ne
wasa." Hajiya Maimu ce ta soko kai dakin, ganin
Munir din yana bai wa Zainab din farfesu a baki
98Ishaf
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
tayi salati. Abin da ta shigo dauka sai ta fasa.
Nan ta shiga magana a tsakar gida tana fadin.
"Wannan ai cin amana ne, matar da dan
uwanka zai aura har ubanta ya ba shi shi ne ka
sanya ta a daki ka ke faman latseta? Ai ni idona
ya yi mugun gani yau.
Ai Hajiya Magajiya tana cutar Alhaji a gidan
nan, sai ya kafa doka ta karya masa. Kalli yadda
ta sanya Mai sunan Mallam a daki yana batawa
Zainab tarbiyyarta, ai daman kowa ya hana
mugun abu bai yi kallo ba, rayuwa ce ai kowa ya
yi da kyau zai gani."
Ita dai Hajiya Maman ba ta tanka ba, taci
gaba da hidimominta. Hajiya Sa'a ta ce, "Ai lalle
kam! Kowa ya hana mugun abu bai yi kallo ba.
Daman ai isar banza ce take yi a gidan nan,
ko ma meye laifin Alhaji ne da ya ce ya bai wa
Suraj Zainab din, meye ya hana bai daura aure
ba?"
Hajiya Maimu ta ce, "Yana tsoronta ne, ai da
ya ce ta bar masa gidansa ai kin ga bai sake
magana ba, itama kuma ba inda taje ta, sai ma
sake samun wuri da tayi ta mike kafa.
Sai an yi maganar tarbiyya ta ce ita 'yar
Malaman soro ce, sai dai a koyi tarbiyya a
99 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
wurinta. Kalli yadda ta hada balagaggu a daki
suke fasikanci. Ai kam! Allah wadaran naka ya
lalace."
Duk wannan rigima da fadace-fadace a
kunnen Alhaji ake yinsa, bai gane me ake nufi
ba, don haka bai tanka ba ya zo ya fice a gidan
ya nufi kasuwa.
Yayin da Hafizu ya rike masa Jaka ya bishi
kasuwar, ko kudin cefane bai bayas ba.
Abu daya ne yake damunsa, ana ambaton
Munir da Zainab ya ce, "Hafizu me yake
faruwa?" Shi ne ya zayyane ya fede masa biri
har bindinsa.
Ya yi murmushi ya ce, "Ai zancen banza Mai
sunan Mallam yake yi, bai ce yana son Zainab ba
sai yanzun da aka bayas da ita?
Kuma ma ina aurensa na Maidugurin? Kо
don sun raina mutane da shi da uwarsa?" Daga
wannan bai sake yin magana ba.
Ita kam! Goggon Mama jikinta sanyi ya yi,
sai ga Munir din ya shigo ya daura agogo ya
gama shiryawa, sai kamshi yake yi. Ya dauki
mukullin mota yana fadın.
"Mama mun je kofar Nasarawa." Ya kalli
Zainab din ya ce, "Tashi muje." Ta muke a
1005dl:
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
sanyaye ya riga ta fita, don haka ta tsaya neman
Sagira ta rakata, ita ma Sagiran ki tayi.
Lokacin da ta fito a dakin 'yammatan Hajiya
Mama ta ce, "Ina ki ka je yana jiranki tun
dazun?"
Ta dan yi diri-diri alamun tsoron Maman, ta
ce "A'a Mama daman Sagira na kirawo ta raka
mu, ni bana son zargi."
Maman ta daka mata tsawa ta ce, "Wuce ku
tafi, bana son shirmen banza.
Wanda zai yi zargin ba ya kaunar Allah, don
ubansa! Wuce ki tafi idan ma ciki zai yi miki ya
yi miki, ni naji na gani isar kuma da aka ce
Alhajin bai isa ba, bai isan ba.
Kuma ba zai taba isa ba in dai Maimun ce to
shi dai a gidan nan ba zai isa ba, donni sai na
kawo karshen munafuncin kowa a gidan nan.”
Da gudu Zainab din ta wuce ta nufi waje,
yana mota yana jiranta. Ta iso ya bude mata ta
shiga. Sai da ta zauna ta rufe motar sannan ya се,
"Ina ki ka tsaya?"
Tayi shiru. Aka jima ya tsare ta da idonsa da
ba sa saurarawa. Ya ce, "Ki gaya mini ina ki ka
tsaya?" Ta ce, "Daman Sagira naje zan kirawo
sai kuma Mama ta koro ni."
101 | shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Ya ce, "Me yasa za ki kira Sagiran?"
"To ai ni Yaya ba na son zargi ne, ka kalli fa
yadda ake zarginmu?"Ya ware idonsa a kanta ya
ce, "Ba na son shirme, me zargin zai yi?
To bari na gaya miki, duk wanda ya dogara
ga Allah ba ya tsoron sharrin mutum, ke dai ki
rika addu'a musamman Azkar."
Yaja motar suka fita a hanya ba ya magana
sosai, abin tausayi da shi saboda gaba daya
damuwa tayi masa yawa. Ya juyo yana kallon
Goggon Mama ya ce, "Jiya fa saboda rashina ki
ke kukan nan?"
Ta kalle shi ta ce, "To ni kuka nawa nayi
saboda wannan yarinyar? Ko waya kayi mata ko
tayi maka ai sai na yi kuka. Ai ni kam na sha
bakin cikin wannan Yaghanar." Ya yi dariya.
Karo na farko da zuciyarsa tayi fari a safiyar
yau din, ya ringa kallon Zainab din yana
mamakin kuruciyarta.
Ya ce, "To da Khuzaimat ta ce tana sona fa?"
Murmushi tayi sai kuma ta bata rai ta ce, "Ai
wallahi kyaleka nayi. Da ka yarda kana sonta da
kayi mamaki. Don daman ni haka na ce ba ni ba
kai har abada, kuma wallahi yanzun ma ka bari
aka aura mini wannan Suraj din mamakin za ka
102 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
yi." Ya yi dariya ya ce, "Ah! Haba?" Та сe,
"Wallahi kuwa." Ya ce, "To ai kin gani dai ba
laifina ba ne idan bamu yi aure ba daga Allah ne
ko?" Sai kuma tayi shiru bata tanka ba, ya се
"Insha Allahu zamu yi yadda zan yi naga mun yi
aure ko ban fara aiki ba."
Suka yi shiru gaba dayansu suna tafe a mota,
karatun Alkur'ani Mai girma suke saurare, sai
kuma wayar shi tayi kara.
Ya kalli kiran, itama kuma kiran ta kalla.
Yaghana ce. Da sauri ya dauka ya ce, "Hello!" Daga can sashen itama ta ce, "Hello!" Ya се, "Honey ya garin?"
Itama ta ce, "Honey jiranka fa nake yi." Ya
dan kalli Zainab din yaga yadda tasha mur! Ya
ce, "To Yaghana ga wani uzuri ya taso mini.
Ba zan samu zuwa ba, Alhajinmu ya aike ni K.D, sai dai ian na dawo za ki ji ni." Ta ce, "Shi ke nan Allah Ya kiyaye, a dawo lafiya."
Ya sanyaya murya ya ce, "Bye miss you!" alamun ya yi kissing wayar ya kashe ya na kallon Zainab din.
Ya ce, "Ya ya dai Goggon Mama?" Ba ta kalle shi ba ya ce, "Ba kya ji ne?” Ta dago ido ta kalle shi ta ce, "Ai ni daman tun farko ba abinda
103 shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
yake damuna. Da kai ka gani muna fada sai don
wannan Yaghanar."
Ya ce, "To ai idan kin kwantar da hankalinki
ke auranki zan yi, ita fa? Sai sa'a idan ta sake
ganina a rayuwarta, ai kin sani ko?" Ta ce, "Ni
ban sani ba."
A haka suka iso gida suna faman rikici а
harabar gidan ya faka motar.
Daman labarin zuwansu tuni ya iso kunnen
Suraj, don tuni ya gayyato abokansa marasa jin
magana, don haka Munir yana yin parking suna
kewaye motar.
Bai ankara da su ba, don haka ya fito. Yana
fitowa Suraj din yana shan gabansa, hannunsa da
wata sharbebiyar adda.
Ya ce, "Kai wannan gayan zamu kaddamar
maka fa! Don rainin hankali kawai."
Daya a cikinsu ya ce, "Wannan baby din ba
matar Yayanka ba ce z aka nemi ka haike mata,
kana da hankali kuwa?"
Suraj ya ce, "Ya raina mutane ne kawai, zai
kawo mana yawa ya yake so ne ayi? Kawai a
sassara shi ya gane kuransa, gobe ma idan ya ga
matar da zan aura zai kiyayeta."
104 shdfi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Goggon Mama jikinta ya dauki rawa. Та се, "Don Allah kuyi hakuri kar ku taba shi don Allah."
Tsawa Suraj ya daka mata. Ya ce, "Ki баcе
mini da gani kin ji Malama, tun ban kaddamar
miki ba." Ya kai mata saran adda, tayi cikin gida
da gudu.
Yayin da Munir ya yi hanzarin rike shi yana fadin. "Ai ni ni ne mai laifi, ita ina ruwanta...?"
Bai rufe bakinsa ba, kwatsam! Sai jin saran
adda ya yi ta ko'ina ya lullube shi, cike da tashin hankali Goggon Mama ta rusa wani irin ihu.
"Wayyo Umma! Wayyo Allahna!! Wayyo za
su kashe mana Yaya Munir!!! Taimako Jama'a.
Kafin ta ankara sun yi waje da gudu cike da
wani irin zafin nama. Tayi hanzarin tarbo Yaya
Munir din kafin ya kai kasa ta rungume shi tana fadin, "Ya Suraj ne.'
Jama'ar gidan suka yi waje da gudu don ganin su waye? Umman ta tarbo dan nata, gaba daya hankalinta a tashe tana fadin.
"Munir! Munir!! Munir!!!"
Shiru ba amsa. Ta ce, "Innalillahi wa'inna
ilaihir raji'un! La haula wala kuwwata illa
105
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
billah! Subahanallahi! Munir! Mai sunan Mallam!!"
Tana kiransa tana jijjiga shi, yayin da jini ke
ta zuba daga saman kansa da wasu gurare a
jikinsa, itama kuma jinin ya 6ata mata jiki amma
duk bata damu ba, so take kawai taga ya motsa.
Umman ta ce, "Maza je ki kawo mini ruwan Kankara."
Anti ce tayi sauri saboda duk suna wurin ta
sanya dankwalinta ta daure wurin ta ce, "Kawai
muje asibiti ina zuwa.
Hijabi kawai ta dauko da mukullin mota, nan
baya suka gewaya wani asibitin kudi (MAI
GAFAZ CLINIC).
Da sauri aka kar6e shi sai da aka aske wurin
sannan aka yi dinki, a kafarsa ma akwai rauni,
sai na tsakiyar kansa, sai kuma wasu raunika
filla-flla da aka yi masa a jikinsa, duk aka gyara
masa.
Goggon Mama kam! Gaba daya hawaye ne
yake zubowa a idonta, ita din ma kamar ta shide,
sai da Umman ta kama ta ta ce, "Kwanta ga gado
nan ki huta, Allah Ya bi mana hakkinmu, Allah
Ya saka masa." Hajiya Binta kam! Ko leken
asibitin, haka nan 'ya'yanta ba wanda ya zo.
106
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Alhaji Ahmad kam! Bai zo ba sai Magriba, duk
da an yi masa waya tare da Hajiya Bintan ya zo
ta gama zuga shi.
Lokacin da ya zo ma a lokacin bacci Munir
din yake yi, ya amsa gaisuwar kowa amma ban
da ta Umman.
Ita ce ta daure ta ce masa, "Kaga yadda jiki
ya yi ko?" Ya kalli Munir din ya tabe baki ya ce,
"Ai hakan ya yi masa kyau, ai ni Allah shi kara
na ce gobe ma ya nemi matar da ba tasa ba.
Ba jiya matar da zai aura tazo ba? ai ina da
labarin komai, kyashi ne ko hassada ce zai ce shi
Goggon Mama yake so?"
Ita dai Umman bata yi magana ba. Ta ce, "Ai
kowa yasan Mai sunan Mallam a family yasan
yana son Goggon Mama, kuma kwauron baki ya yi bai riga ya ce ita yake so bá ko?
Kuma ma ai mu mun riga mun ce auren Zainab ba zai yiwu ba da Suraj, daga baya idan
sun daidaita da Munir ayi bikinsu.
Amma ina dalilin kazafi? Yau ne Goggon Maman take gabansa bai bata mata rayuwa ba
sai yanzu?
Aure ne Zainabu ta ce ita ba ta son Suraj ko
sai an yi? Mata dole?"
107 shati
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Hajiya Binta ta ce, "A'a shi Suraj ya hakura
ba ya so, idan ma ya aura karshenta a hana shi
zaman lafiya da matar, suje suyi auren ai ga
gurin nan.
Alhaji Ahmad ya ce, "Aure ba fashi, sai an yi shi wallahi, sai dai idan mutuwa nayi to wannan
kuwa na yadda amma ban ga wanda ya isa ya
hana auren nan ba sai ikon Allah."
Hajiya Bintan cike da duniyanci take fadin,
"A'a to ai ni ba don Alhaji Babba ba da an ga
abin da zan yi."
Shigowar Hajiya Magajiya da jama'ar gidan
ne ya sa kowa ya yi shiru saboda daman shirun
ake tafe a dalilin Alhaji Usman ya hana kowa
magana a mota.
Hajiya Magajiya kam! Tana shigowa taga
yadda jikin na Munir yake, sai ta fashe da kuka
ta ce, "Cin amana? Cin amana? A mutu a bar
muku amanarmu amma kuyi watsi da mu don
cin amana? Saboda matanku da 'ya'yanku?
Wallahi ba zai yiwu ba.
Ke Hajiya Rabi'a an kama Surajo ne?" Ta ce,
"A'a ya za a kama shi, shi dangata? Ya daki
banza ne kawai." Ta kama kofa zata fice ta ce,
108afi
Zumunci Dangin Jamila M. Danfajo
"Wallahi kara zan shigar ba zan yadda da irin
יי
wannan kama-karyar da ake yi mana ba."
Alhaji Usman ne ya rike kofar ya ce, "Kiyi
hakuri, ai dole a dauki mataki, ba zai yiwu ba.
tilas ayi masa hukunci, ai dukan ya yi yawa."
Alhaji Ahmad ya ce, "Ai ba wani hukunci
dan uwansa to idan ma shari'a ce da wa za ayi?"
Shi kam Munir yana kwance magashiyan rai
a hannun Allah, ga Zainab din a gefensa ta ci
kuka ta gode Allah." Alhaji ya yi ta musu nasiha.
Alhaji Usman ya ce, bakwa daukar rayuwa da
sauki tun farko sai da na gaya miki idan Allah ya
kaddaro aure aje ayi shi ki ka ki ki ka koma ki
ka zuga Mai sunan Mallam.
Ki ka ce yaje ya nemi auran Zainab za ki ba
shi ai kin ga yadda ta kasan ce ko? Ta ce, ai ba
zuga shi nayi ba daman yana sonta.
Alhajin ya juya yana magana da Nurse bai yi
wani yunkurin ba tuni Hajiya Magajiya ta fice a
dakin tana fita ta ce, "Hafizu kai ni Police
Station."
Ya ce, "To." Hajiya Mama ta ce, "Ai ka san
in da Suraj yake zama ko?" Ya ce, "Har dabarsu
zan kai ki ta ce muje." Cikin minti goma ta
109 Ishafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
shigar da kara tayi komai duk wanda za su gani
sun gani duk yadda za'ayi anyi.
Black Maria aka ba su cike da 'yan sanda can
gidan kwanansu inda yake tara abokansa a can
aka iske su ba tare da shan wahala ba.
Aka yi musu kamun ka ji a gidan abokinsa inda suke hada dabarsu.
D.P.O din da case din yake hannunsa ya nemi
a sasanta amma Hajiya Magajiya ta ce, "Wallahi
ba sasantawa sai an yi shari'a.
To da farko Alhaji Ahmad yaso ya hana
amma abu ya faskara, tilas aka saka Suraj a
(Cell) kafin fita kotu.
Duk da ragowar iyayensu sun yi belinsu
amma shi kam a fangarensa ba beli sai maras
lafiyan ya ji sauki za a yi shari'a.
Hajiya Binta kam! Hankalinsu ya tashi, 'sun
shiga gari yawon Malamai, addu'ar samun
nasara a shari'a.
To ai haka abin yake, a rayuwa duk yadda ka
dauki duniya haka take zuwar maka.
Munir kam! Kwanansa uku a asibiti, bai san
wanda yake kansa ba. sai faman bacci saboda
saran da aka yi masa a kansa.
110safi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Har ana tsoron kada ya taba kwakwalwarsa,
amma da shi ke ana addu'a cikin ikon Allah sai
ya dawo cikin nutsuwarsa lafiya lau.
A da komai Hafizu ne yake yi masa, amna
yanzun yana iya komai da kansa.
Ranar Juma'a da ya cika sati guda, ranar aka
warware masa wasu daga cikin dressing din da
aka yi masa, kuma a ranar duk wani kumburi na
fuskarsa ya sabe, sauki ya samu sosai.
Ya kalli Hafizu ya ce, "Wai Hafizu ina
Goggon Mama?" Ya yi murmushi ya ce, "Tа
fiya koke-koke, shi yasa Umma ta tafi da ita gida
ta hana ta zama, wai kar ta gamu da ciwon zuciya."
Ya yi murmushi ya ce, "Sosai take yin kukan?" Ya ce, "Ba ta cin komai fa a gidan ma
ban da kuka ba abin da take yi."
Ya ce, "Ina wayata?" Hafizu ya ce, "Suna wurin Umma." Ya ce, "To idan kaje gida ka taho
mini da ita, kuma itama Goggon Maman ku taho min da ita ai na samu sauki."
Ya yi dariya ya ce, "Ba ka tambayi kowa ba
sai Goggon Mama?" Ya ce, "To kai wa ka ke so
na tambaya? Ba kowa yana zuwa ina ganinsa ba?"
111|shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Ya ce, "To amma Nuri fa?" Ya harare shi ya
ce, "Nurin ba da safe tazo ba? idan anjima da
yamma ma zata zo.
Ina ganin ku fa kyale ku nake yi, ba wurina
take zuwa ba soyayya ta ke zuwa kuyi, ku bar ni
ina fama da ciwo ko ba ku ne a bayan nan ba
ne?"
Hafiz ya yi dariya ya ce, "Yes! Yes!! Haka ne
mune ka gane mu."
Shigowar su Hajiya Mama ne ya hana su
magana, ita da Umman su Munir.
Ya ce, "Shi kenan ga su Umman bari naje
gida nayi wanka na dawo."
Umma ta ce, "A'a bari mu gama tattaunawa
tukun, don Babanku ya ce, Jibi zai daura auren
yaran nan bana son a samu matsala shi yasa ban
tsaya tambayar sa maganar su Zainab ba kuma
ina ganin.har auran ku za'a dauri bikin ne naji
yana cewa, sai December.
Sannan kura ta lafa, ban gane ba? abin da
suke nufi, amma kaje ka same shi yana nan a
gida ka jiyo mini yadda za a yi.
Idan auran Munir da Zainab ba zai yiwu ba ka
wuce gidan Goggona kasa a gyara mini sashenta
112 |shafi
소
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
ayi fenti duk abinda yake muhimmi kaje ka
kwashe mini a gidanku.
Wallahi zamana ya kare da ubanku, in dai ya
biye Hajiya Maimu da Binta ya tozarta mu,
wallahi zai yi mamakina, irin wanda bai taba yi
ba."
Jikin Hajiya Binta ya yi sanyi.
Ta сe, "Ah! Aure kam! Da Surajo yake burin
daura shi, ya ce ko shekara nawa zai yi sai dai ya
yi ana jiran fitowarsa.
Amma sai ya fito ayi bikin, yanzun aure zai daura musu.
Hafizu ya ce, "Lamarin fa sai dai mu ci gaba
da addu'a. Hajiya Mama wane ficewa za ki yi?
Idan kin fice kin bar gidan kuma ai lamari ya
sake lalacewa, ayi komai dai kina gidan kar ki
matsa a gidan.
Idan kin hana Amarya tarewa ai dole za su gaji su sakar miki 'yarki ko?"
Tayi tsaki ta ce, "Ba ka da hankali. Lokacin
da Alhajin zai zo ya sanya ta a gaba a kaita gidan mijin zan iya ja da shi ne? kaje kayi mini abin da
na ce maka ka ji ko?"
Ya shuri takalminsa ya fita suka ci gaba da
tattauna matsalar da ta shafe su.
113 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Umman Munir din ta ce, "Amma ni Anti ba
na so ki fice a gidan nan, bana son sanadin Mai
sunan Mallam a samu matsala.
Ya hakura mana shi da Zainab din tunda dai
yana da yarinyar da ya ke so?"
Hajiya Maman ta ce, "To yanzun kauna ki ke
nuna mini ko kiyayya? Ko kuma so ki ke ya
hakura ya auri waccan ita Zainab a aura mata
dan iska?
To wannan maganar ma kar ki sake yin irinta
ba na so. Idan kinga na bari Zainab ta auri Surajo
sai dai bana numfashi a duniya.
Amma dai muddin ina rayen wallahi bata da
miji sai Munir, wallahi ni da Alhaji mu zuba.
Shi yasa na sanya gyaran gidanmu na Soron
dinki, ke yanzun don wannan dan karamin
hargitsin har ya isa ya fara tsorata ki?
Ai hargitsi yana gaba, wallahi mu zuba ni da
su shege ka fasa, wallahi dan halas sai ya yi."
Shi kam Mai sunan Mallam din ya yi shiru ya
Kasa magana, don shi tashin hankalin da yake
ciki yafi na ciwon jikinsa.
Don haka idonsa ya lumshe tamkar mai bacci,
tunani da nazari sun yi masa yawa, ya rasa bakin
zaren.
114shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M Danfajo
Na farko abinda yafi damunsa daya ne, yasan halin iyayensa mazan nan idan sun kafe a kan abu ba sa fasawa.
Tunda aka riga aka furta auran Surajo da Zainab mawuyaci ne a fasa auran nan.
Don haka tunaninsa yafi tafiya a kan Hajiya Mama ta bar gidan, don idan ta zauna ma in har
an daura auren koda duka sai an kai Zainab gidan Suraj.
Da ganin wannan ranar gara ace ga ranar mutuwarsa, don haka yafi yadda da shawarar Hajiya Mama, barin gidan shi ne yafi masa kwanciyar hankali.
Ko zai yi dako ya nemo ya ciyar da su yafi
masa sauki da ganin wannan ranar.
Sai Magriba Hafizu ya iso da Nuri da Zainab, shi da Nurin farin ciki suke yi kamar me?
Kowanne sai faman walwala yake yi, fuskar
nan kamar wata daran sha hudu.
Hajiya Rabi'a ta mike tana goya diyarta da take goyo. Ta ce, "Ni Anti zan je gida." Hafizun ya mika mata katunan bikin. Ya ce, "Umma kin gani fa."
Kallo daya tayi ma katin ta kawas da kanta.
Ta ce, "Ya yi kyau." Ta fice a dakin.
115
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Ita kam Hajiya Mama tsawa ta daka ma
Hafizun cike da firgici ta ce, "Wai kaje kayi mini
abin da na sanya ka? Ko kuma yawon karbar
katin ka tafi?"
Ya ce, "A'a wallahi yanzun zan je Hajiya
Mama, kiyi hakuri." Ya juya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 13