Share this page
shi ta ce, "Kaje ka tatso ta ko?" Ya yi murmushi ya ce, "Wallahi ban tatso ta ba, ita ce ta ban kudin da kanta." Ta daina abin da take yi ta ce, "Lallai Mai sunan Mallam da cuta ka ke, to bari na gaya maka, yadda ka karbo mata kudinta ka mayar mata. Idan kana son zaman lafiya, idan kuma ba haka ba kaga kudin da Abbanku ya baka, wallahi ba zan ba ka ba." Ya marairaice ya ce, "Haba don Allah Hajiya Umma, don Allah kin san fa kudin da Abba ya ke bayar wa ba isa suke yi ba wallahi." 47 |shafi a Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Ta harare shi ta ce, "Goben fa za ka je goben fa za ka dawo, amma don cuta sai ka karbo mata kudi?" Ya ce, "Wayyo! Hajiya Umma! Wayyo Allahna!! Ba za ki gane ba wallahi akwai kura wallahi. Kudin nan ba sa isa wallahi. Shi Abba kina gani ya sanya ma kudinsa kafiyo, 'yan kadan yake tsakurowa ya bayas, don Allah Umma ki bani." Ya fada yana dudduba inda take ajiye kudin, ya samu ya dauko yana tambayarta. "Wannan ne Umma? Nuri ina kudina?" Ta ce, "Su ne daman ni na ajiye maka." Ya fice da sauri. Umman takai masa duka da abin da ta saka na dan goyo tana fadin. "An dai huta da wannan karatun naka na damfara, tunda an gama, an huta." Ya fice yana dariya. Washegari da sassafe ya yi shiri ya kama hanyar tafiya Maiduguri. Tafiyar kwana biyu sai da ya yi sati guda, sannan ya dawo ba wanda ya yi bakin cikin dadewarss irin Goggon Mama. Don ko waya yake da Mamanta tana makale tana jin abin da yake fada. 48 |shafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Ranar da ya dawo da yamma ya zo gidan wannan karon tsarabar kurkur ya iyo musu da jaja amare kamar yadda 'yammatan suke tarbansa wannan zuwan ma yanyame shi suka yi da su da yaran suna oyoyo. Yaran ya mika musu alawoyi kala-kala, cakulat ya ce kuje maza a raba muku, ku kuma ledar ku tunda ba ku da aiki sai a cuci maza, fata وو ku shafa mata kurkur, gashi ku tuma tsumma. Gaba daya suka diba. "A'a wallahi, wallahi mun wuce a cuci wallahi ba ma yi." Ya ce, "To ku tsaya! Ku tsaya!! Ya isa. Ina Goggon Mama?" Suka yi shiru. Ya ce, "Ki kirawo mini ita." Sagira ce ta garzaya dakinsu na 'yammata ta ce, "Goggon Mama ki zo." Ta tashi tayi wata yatsina ta ce, "In ji wa?" Sagiran da daman suke jin haushinta, alamu sun nuna ita Ya Munir ya ke so. Ta ce, "In ji oho miki." Ta juya. Idonsa a kan Sagira ya ce, "Ina Goggon Maman?" Tа ce, "Tana zuwa." Bai 6ata lokaci ba ya ce, "Ta huta, daman hoton Yaghana zan 49 Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo nuna muku. Budurwata 'yar Maiduguri, ku zo ku koyi kwalliya." Gaba daya suka kwashi ihun murna, su Hajiya Mama suna General falour sai ihun yaran suke ji. Hajiya Mama ta leko taga me suke yi, tayi dariya kuma tana labartawa su Hajiya Maimu. Та се, "Wai hoton budurwarsa 'yar Maiduguri yake nuna musu, wata wai Yaghana." Gaba daya suka kwashi murna da shewa, itama tana taya su don ita gama da su duk shawarar da za su yanke da Kanwarta sun yanke sun gama lokaci suke jira. A can kuma su Khuzaimatu sun nutsa sai kallon hotunan Yaghana suke yi, sai da suka gama kallon sannan ya ce, "Tana da kyau ko ba ta da shi? Kun san fa mai tsada ce." Suka fara hayaniya. "Wallahi Yaya ba ta fi mu tsada ba." Goggon Mama ta zo ta wuce su bata tanka ba, ya bita da kallo. Shi kansa yasan daurewa yake yi da abin da yake damun shi a ransa game da ita. Ba a jma ba kuma sai ga ta ta dawo da Hollandia milk da robar Faro da kofuna a tire ta dire masa a sanyaye ta ce. 50shafi Zumunci Dangin Kauna "Ya Munir ina kwana?" Jamila M. Danfajo Ya bita da kallo, bai amsa ba. ya yi murmushi ya ce, "Ba zan sha ba, dauko abinki ki bani wuri, maras mutunci kawai." Ba ta dauko ba ta bar wurin, ya biyota da gudu ita a tsammaninta Hajiya Mama na daki, tana shiga ta iske bata nan. Don haka ya tare hanya ya ce, "Ba ki da mutunci ko? Ni ne nake kiranki ki ka ki zuwa ko?" Ta bata rai ba ta tanka ba, ya yi tsaki ya ce, "Ki sake ki gani, wallahi sai kin yi mamaki." Ya duddungure mata kai tare da bugunta a kafa, ya juya ya fice ya bar ta tana faman kuka. Ba ta san lokacin da ya fice ba ya bar gidan, amma dai tasan a duniya ba wanda ya takura mata rayuwarta irin Ya Munir, duk abin da tayi laifi ne a wurinsa. Hajiya Mama ta shigo ta ganta ta ce, "Ke kuma meye ki ke sana'ar taki ta kuka?" Ta goge hawayen ta ce, "Wallahi Hajiya Mama na daina shiga harkar Ya Munir, kalli fa abin da ya mini yau din don yaga ina hakura. Wallahi daga wannan na daina shiga harkasrsa, har ruwa fa na kai masa da lemo 51 Ishai 1 i i e a Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo amma sai da ya dake ni, sai ka ce wata jakarsa, wallahi dole nima na rama. "Ai na gaya miki kyale ni naja ajina nima, amma sai ki ringa cuccusa ni yana wani yankwana ni kamar wata kucaka." Hajiya Mama ta ce, "Ayi hakuri, ai shi komai na duniya dan hakuri ne, kin ji uwata?" Tun daga ranar ta 6oye ma ganinsa, sai ya shigo sau goma bai ce ina Goggon Mama ba, duk da ya san kawai daurewa yake yi da wani irin mahaukacin so da yake mata. Yana danne abin a ransa saboda kada ya kasa har dai ya daure ya ce, "Khuzaimat wai ina Goggon Mama? Kusan kwana nawa kenan ban ganta ba?" Zaimat din ta kalle shi ta basar ta ce, "Zai yi sati guda a lissafina dai." Ya girgiza kai ya ce, "Yau kwana goma, nemo mini ita." Ba irin neman da Khuzaimat bata yi mata ba, amma bata ganta ba. tilas ta hakura ta dawo ta ce, "Ban ganta ba fa Yaya Munir." Ya yi shiru alamun abin yana damunsa, ya ganta su yi fadan ma ai arziki ne, jikinsa a sanyaye ba kuzari. 521shafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Sallama ya yi da matan gidan zai tafi, sai kawai ya ganta a harabar gidan tana hira. Har ya wuce ya dawo ya mika ma abokin hirar tata hannu ya ce masa. "Barka da yamma." Ya ce, "Barka dai." Ya harareta ya ce, "Wuce ki tafi gida." Ya fada yana mata mayen kallonsa. To ta ladaftu ne da azabar sonsa gaba daya ji take yi yau din zata mutu idan bata ganshi ba, duk da ganin nasa ya yi mata dadi amma sai ta basar. Ta ce, "Na tafi gida fa ka ce?" Ya ce, "To shi kenan ko so ki ke na gaya masa halinki da ki ka yi mini a mota?" Ta juya da sauri ta wuce, ya ce masa "Kayi hakuri an yi mata miji ne ka ji ko?" Ya juya ya bar shi a nan çikin gidan ya bita. Ya isketa a dakin Hajiya Mama ya ce, "Wallahi duk ranar da na sake ganinki da saurayi ko? Zan gaya masa halinki ne kawai don ki sani ne. Sai na tona miki asiri." Cikin kuka ta ce, "Hajiya Mama ai kin ji shi ko? Ni dai wallahi kiyi mini tsakani da shi." 53 |shafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Hajiya Maman ta rike baki cike da mamaki ta ce, "Kin soma? Ni yanzun idan na raba ki da Yayanku ai na kaiki Kargo ban kai ki Sabara ba. Ai ba zai yiwu ba, kiyi hakuri don Allah." Ya ce, "Kyale יי ta Hajiya Mama, bata da hankali ne." Hajiya Maman tana fita ya fitar da wayarsa ya ce, "Abin da ba kya so ne bakin ciki ya hana ki gani, kin gani Yaghana mai sona." Ya dora mata wayar a kan cinyarta ya ce, "Ki dauka ki gani budurwata ta fiki komai. Ki kalli hotonta, kalli fuskarta." Ai ita kam ba ta san lokacin da tayi jifa da wayar ba ta daki bango ta baje. Ya kuwa faffala mata mari ya ce, "Kina cin kashi ne? ni za ki yi ma almubazzaranci da waya? Ko kina hauka ne?" Fada sosai suka yi. Hajiya Mama da ta shigo taji abinda ya hada su, bata yi magana ba sai ta dauki kayan dinki ta fice. Shima wayarsa ya dauka ya bar gidan, kwana biyu bai zo ba, don haka Hajiya Mama ta zazzaga wata atamfa. 54 Ishafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Umman su Nuri ta dinka mata da dinkin yafi wata biyar ta ce, "Ke Goggona ga dinki nan na dinka kije ki kai ma Umman su Nuri." Goggon Mama ta gane nufin Mamansu, don haka ta bata fuska ta ce, 'Dazun fa Maman su Khuzaimatu suka je Kofar Nassarawan, amma Mama da kin ba su mana su kai mata. Yanzun don kai dinki na tashi kafa da kafa naje har wannan uwar unguwar mai uban nisa?" Hajiya Maman ta tsaya tana kallonta cike da mamaki. Ta ce, "Tashi ki bani wuri, maza tun raina bai gama baci ba, ke yanzun tunda suke tafiya Nasarawa waye ya taba yi mini sallama ya се can zai je? Ko kuma ni nasan sirrin da yake kai su? Dakin kowa sirrinsu a boye amma ke sai kin nemi ki tona mini asiri don dai kawai kin raina ni?" Ta saki ajiyar zuciya ta ce, "To ai ni ba na son fita ne wallahi Mama, ga Ya Hafizu can a waje na kira shi ki aike shi. Don Allah Mama ki rufa mini asiri ki bar ni." Duk kwanarta da ta ke yi Hajiya Maman ta gano ta, don haka tayi watsi da ita ta ce "Minti 55 |shafi 1 i Π Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo talatin na ba ki ki shirya zan kira Hafizun a waya ya shirya yazo ya kai ki. Тaпa Ба6bata rai tayi wanka ta shirya cikin wani material blue mai tsadar gaske, sai daukar ido yake yі. Mayafi ta sanya sky blue din saboda shi ne hasken jikin material din. Tayi kyau sosai, ta yi kwalliya ta daukar hankali, material din siket tayi rigar fited ce sosai siket din ya yi kyau na ban mamaki. Daga Kasa an baje siket din daga sama ya yi ma kugunta cif, daurin dankwali dai tayi na zamani irin dai kalar acucin. YSai kamshi take yi, ta sanya takalmanta farare tas da post dinta itama kalar fari tas da golden a jiki. Zainabu Abu, Goggon Mama. Yarinya се danya sharaf da take kan kuruciyarta, da zamaninta LEWE Wankan tarwada ce kalarta tana da maganai manya farare tas, a tsaye doguwa ce sambal ta mike cikinta a shafe yake sosai tamkar bata cin komai. Daga baya akwai mazaunai wanda suke daukar hankalin mai kallonta, tana da cikakkun 56 1shaft Zumunci Dangin Kauna Jamila M Danfajo cinyoyi sune suka fitas da dirin ta don sun 6оуе tsawonta, saboda kugunta ya cika cif! Fuskarta a kewaye take tana da wushirya idan tayi dariya ko murmushi wushiryarta na birge mai kallonta. Idonta yana lumshewa idan tana cıkın Gacin rai bata iya bude shi, yanayinsa kamar na mai jin bacci, a lokacin 6acin ran nata. Idan kana son ganin gaba daya idonta ya bude to faranta mata don idan tana cikin farin cikin kyanta yakan bayyana ne komai na fuskarta tana bude shi. Kamar murmushinta, magananta, don idan Goggon Maman na cikin farin ciki har wani rausaya ta kan yi idan tana tafiya zata baka sha'awa idan ka ganta tana cikin walwala, idan ta tsaya kuma akwai rangwada. Yanzun kam ranta a 6ace yake, don haka idonta ma da kyar take bude shi, bata walwala saboda a kullum tana son ta nesanta kanta daga abin da zuciyarta take son kunyatata a kansa. Mai sunan Mallam ne soyayyarsa tana wahalar da ita, kalli yadda ya yi ma Khuzaimat da Ummanta akanta ce tana sonsa. 1 1 i r i i t e ان e a 57hati Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo To itama idan ta biyc karshe abinda zai yi mata kenan, don haka take rike mutuncin kanta. Amma Hajiya Mama sai wani sake cuso ta take yi, in da za a yi mata wulakanci. Hafizu ne ya shigo, ya sha boyil sai walkiya yake yi yana faman kamshi, yana wani haskawa. Hajiya Sa'a tana fitowa a kitchen din tsakar gidan ta ce, "Lah! Lah!! lyc! Kaga babban dana sai ina?" Hafizu ya yi murmushi yana gyara gilas din idonsa, ya ce "Ai Hajiya kin sani sai can mana." Dariya suka sake yi har Hajiya Mama, ta ce "Kaddai Nassarawan za ka je?" Ya ce, "Can ne wallahi." Hajiya Sa'a ta ce, "Yo ai ni ban sani ba ni wacce ce a ciki a cikin 'yammatan can din? Dakin Hajiya Binta ko kuma Hajiya Amina, fadi min?" Ya ce, "Ba ki canki dakin Hajiya Rabi'a ne 'yargida za a yi tuwona maina Hajiya Mama zata yi ba gara ba lefe, Nuriya ce." Ai kuwa Hajiya Sa'a ta zaburo ta yalyale guda. Ta ce, "Ahayye nanaye! Alkawarin Allah Ya cika, yaro kayi gadon ubanka, 58 Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Ba tsoro! 'yar gida ya dauko." Tа се, "Bari na zo babban dana ina zuwa." Ta wuce taje ta kawo masa sabbin 'yan dari biyu rafa guda. "Auren gata akwai gara, akwai lefe, ko ni zan yi duka biyun. Wannan kace ta ci cingam kafin nazo ni da kaina, Allah Ya bar kauna, a gaida Hajiya Rabi'a manyan mata a kofar Nasarawa, Allah yaja zamaninta." Hajiya Mama tayi murmushi ta ce, "An gode Hajiya, Allah Ya kara budi." Ta ce, "Amin, ai ni tunda mun kayar shi kenan burina ya cika." Hajiya Maimu da ke zaune a gefe guda tayi dariyan gatsetse wadda tafi kuka ciwo, ta ce "Don ma kudin Yayansu ne, idan an hana ya ba su a ba su ta hanyar kinibibi da tsigudidi da son tsegumi. Ni don Hafizu ya ki auran Kaltum diyar Binta ba komai ba ne, tunda aka yi murdiya aka hana Mai sunan Mallam ya auri Khuzaimatu. Nasan aikin banza ne, don an hana Hafizu ya auri Kaltum ba komai, rayuwa ce ai ke da aka auri diyar kin, kin raba su da dansu. Maji ma gani an binne tsohuwa da ranta. 59Ishafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Ayi mu gani idan tusa za ta hura wuta, ai kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba, in dai ni ce ayi mu gani. Hajiya Sa'a ta ce, "Kuma dai, ai mu nan an buga an bar mu." Ita dai Hajiya Mama addu'a tayi tare da fatan alheri, ai fa ganin irin kwalliyar da Goggon Mama tayi, yasa gaba daya hankalin Hajiya Maimu ya tashi. Ta bita da kallo cike da tsananin kishi, yadda take taku cikin Hill shoe din takalmi mai tsananin tsini kamar za su dina. Yayin da Hajiya Mama tabi su da addu'a, Hajiya Sa'a ma ba ta fasa ba, sai cacara take yi har wajen haraba ta rako su. Sai me? Motar da za su fitan K.B ya fice a ciki, dayar kuma Direba ya wuce dauko Alhaji a kasuwa (406) din kuma an kai Hajiya Adabiya unguwa, daya Jeep din kuma bata da lafiya. Hafiz ya kalli Mallam Ya'u Direba ya ce, "Ina K.B yaje?" Ya ce, "A'a, yanzun dai ya ce mini zai je ya dawo na ba shi mukullin motar na ba shi Hafizun ya kalle shi a fusace. Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Ya ce, "Ka gaya masa zan fita?" Ya ce, "Eh! To ka san shi ni ban fiya shiga harkar shi ba, yana da matsala." Hafizun ya kallo Goggon Mama ya ce, “Don Allah Malama kije ki ce Hajiya Mama ta ba mu mukullin waccan motar da ta sanya a lulluße da tamfal." Saboda ba mota, ta dan yi dum! Sannan ta ce, "Ba ta fa cika kudin motar ba saboda haka ma ta lullube ta a can ba a hawa ta ce sai ta cika." Ya Hafizun ya ce, "Tun yaushe ta cika kudin, ni na kai ma cikon kudin." Tayi dan tsaki a hankali ta juya don gaba daya ita an takura mata take ji, don haka ta iske Hajiya Maman ta gaya mata sakon Hafizu. Ta mike ta dauko mukullin motar da ta saya ta ce saboda irin wannan ranar na sayi motar nan, ga mukulli ai ni wulakancin gidan nan nayi sallama da shi, ga shi Allah Ya kiyaye." Hajiya Sa'a kam sai ta bita da kirari na birgewa tana fadin. mu, "Doguwa 'yar Mama, Uwar Mama, Doguwa kyau da kyau mun haife ki, kin haife 61 Zumunci Dangin Kauna Doguwa matar manya, Mijinki sai an duba." Jamila M. Danfajo Ita dai bata tanka ba, ta wuce tana takonta mai daukar hankali mai cike da rausaya. Hajiya Sa'a ta kalli Hajiya Maman ta ce, "Ai nima motar nan zan saya na huta da wulakancin fita unguwar nan. Sai ka shirya ka iske duk motocin an fita da su." Hajiya Mama ta ce, "Ai ni ba abinda yafi damuna irin sai na fito na iske wani ma ya ce unguwar zai je. Don haka motar zan sa a kawo mini nayi maganin su. Ita dai Hajiya Maimu shiga take tana fita, har K.B ya shigo ta ja shi dakinta ta ce "Bi su Nasarawan wai ka ji Hafizu ne yake son Nuri. Ka wargaza abin kaima ka ce kana sonta ka jima da abin a ranka ba ka fito ka fada ba ne.' Ya dan yi tsaki ya ce, "Kyale su Hajiya, zan yi maganinsu ni gobe naje na wargaza masa tsari." Ta ce, "Jeka ayi biyu babu wallahi, yadda aka yi na Zaimat, itama ayi ta wargaje ba jininsu 62 Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo zumunci ba wallahi sai na rama wannan auran zumuncin. Sai na 6ata shi, in dai ba za a yi da 'ya'yana ba to suma wallahi ba za a yi da su ba, mu zuba ni da su shege ka fasa." Ya ce, "Wai Hajiya duk me ya faru ne?" Tayi tsaki, duk yadda aka yi ta labarta mishi. K.B, Kabir shi ne babban dan Hajiya Maimu, gata da yadda ta dauki so ta dora masa, da son sai ya fi kowane da, ya maida shi dan iska. Shaye-shaye ba abin da ba ya sha a rayuwarsa, yawan mata kuwa kamar dan Karnuka. Hafizu kam! Shigar Magriba La'asar lis suka yi ma Kofar Nasarawa, wata majalisa ce a can gefe daga tsallaken gidan su Nuri. Duk in da karfe biyar tayi to wannan majalisa ta gama cika, don haka Hafizu bai shigar da motar harabar gidan ba. Ya nemi wuri ya yi parking din motar ganin su Mai sunan Mallam ne. Goggon Maman ta kalle shi ta ce, "Shigar da ni ciki mana saboda Allah za ka ajiye ni a nan?" 63 Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Ya yi tsakı ya ce, "Kina gani suna ta dago mini hannu sai na shiga ciki da ke kamar ina tsoronki? Ko ni Direbanki ne?" Ya yi tsaki yayin da zuciyarta take bugawa a kai- akai. Tun shigowar su unguwar fa zuciyarta ta hangi abin da take so, gaba daya ta nemi ta rikice, ta gigice da wani irin so da a kwana biyun ta fara mantawa. Amma a yanzun ganinsa ya tayar mata da tsohon mijin so da yake dankare a zuciyarta. Ji take yi tamkar hawaye zai zubo mata, amma da ta tuna da Yaghanar shi sai da idonta ya kawo hawaye, don tsabar tashin hankali. Don gaba daya sai tausayin kanta ya kama ta, kana son mutum ba ya sonka, to ya ya za ka yi? Hakuri! Tilas ta bude mota tayi cikin gidan, daya daga cikin samarin wurin ya kalli Hafizu ya cе, "Gidanku fa akwai 'yammata mutumina, ka bani wannan mana, irin su ne fita London, New York yin Honey moon." Mai sunan Mallam ya harare shi ya ce, "Wannan har an karbi sadakinta mutumina, an riga mu wallahi." 64 Ya yi tsaki yana fadın. Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo "Gidanku akwai 'yammata, ana haifar kyawawa. Kayi mini hanyar daya mana." Hafizu ya ce, "Ka shirya kaje zoo road har irin Larabawa muna da su." Suka yi dariya. Sannan Mai sunan Mallam ya kama hannun Hafizu ya ce, "Muje gidan akwai bayani, don naga kana waya da Nuri, da gaske ku ke ne?" Ya ce, "Wallahi da gaske muke yi, ai ni ban taba so irin wannan ba maras sassauci a rayuwa, yana wahalar da ni. Don aurenmu ni idan an ce wani satin baki zan yi ba." suka yi dariya suka tafa. A dakin Hajiya Rabi'a ya iske su, don Nuri ba wani kunya ta kallo Hafiz tana bude wayarta tana fadin. "Fantastic my love, what a wonderfull visit? Kar ka motsa bari nayi maka hoto." Hafiz din ya ce, "Mu fita haske can fulawoyi zai fi kyau." Ta mike ta bishi suka fice. Ummansu ta ce, "Oh! Rasa kunya beran tanka, ni ban san wace irin rashin kunya Nuri ta koyo ba." Mai sunan Mallam ya ce, "Ai ni tana birge ni, tasan mutuncin mai sonta." 65 |sha fi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Umman ta ce, "Oh! Kai kuma meye ya tsole maka ido?" Ya harari gefen da Goggon Mama take, Umman tayi murmushi. Ita dai Goggon Mama bata tanka ba, don wannan karon tafi karfin zuciyarta, ta ki kallon in da yake ma balle tayi masa gaisuwar da zai ki kulata. Ta durkusa ta gaishe da Umman ta cе, "Umma ina yini?" Umman ta amsa tana kallonta cike da sha'awa da kauna 'yar asali. Ta ce, "Lafiya lau uwata, ina Antin nawa?" A sanyaye ta ce, "Lafiya lau, tana gaishe ki. Ga shi ta ce na kawo miki, dinkin ki ne kuma da sako a ciki, ta ce zata yi miki waya.' Umman ta ware dinkin tana dariya tana sha'awa. Ta ce, "Sai Antina. Lallai Anti ta ce nayi kwalliyar Juma'a gobe." Wayar Goggon Mama tayi kara, ta bude post dinta ta dauki waya ta fice waje tana amsa wayar. Mai sunan Mallam ya biyo ta da kallo, wayar ta bata masa gaba daya farin cikin yininsa yau din nan ya yini lafiya lau, amma gaba daya ta 66 |shafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo rushe masa walwalarsa da farin cikinsa na yanzun. Ya mike ya biyota, ya jima tsaye a bayanta yana jin me take fada, ji ya yi zata fasa masa zuciya ya kwace wayar. Da sauri ta juyo tana cikin tsananin damuwa. Ta ce masa, "Bani wayata." Tayi shiru ta sake magana ta kakkashe idonta. Ta ce, "Ka bani wayata Ya Munir ba na son neman fitina da neman tashin hankali." Wucewa ya yi yana fadin "Ba ki da karfi? Ki zo ki kwata, idan kina da shi." Ya yi ficewarsa. A harabar gida ya iske su Hafiz ana faman hira. Ya ce, "Kai Mr love zo muje a sallaci Magriba ko?" Ya ce, "Shiga gida Nuri, ina zuwa akwai labari." A cikin gida ta iske har Goggon Mama tayi alwala ita kam! Umma ta wuce babban falo can inda suke bin Masallacin gidan. Su kam! 'Yammatan a nan dakin na Umman su Nuri suka yi sallah, sai da suka idar Nuri ta ce "Wai ya na ganki ne haka ba ki da kuzari?" Goggon Maman ta dan yi fari da idonta ta ce, "Ke dai 'yar uwa bari, ni kadai nasan irin 67 |shafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo damuwar da nake fuskanta, ko unguwar nan fa daurewa nayi nazo. Ki kalli fa irin wulakancin da Ya Munir yake yi mini, ki gani fa yanzun ma ya kwace mini 99 waya, ai wannan ma wulakanci ne. Nuri tayi dariya ta ce, "Ni kuwa gani nake yi kamar Ya Munir yana sonki." Tayi tsaki ta ce, "So? Ni ce zai so? Kina ganin mutum kowacce mace kusheta yake yi, kowacce bata isa ba?" Nuri ta ce, "Haba 'yar uwa! Za ki ce na gaya miki, yana sonki wallahi ba ki ga alamarsa ba?" Goggon Mama ta ce, "Ba ki da kai, ai ni ba ajinsa ba ce. Yaushe ma zai ce yana sona?" Nuri tayi tsaki ta ce, "To ajin zai aura? Duk wannan ajin nasa da wani jan ajinsa ai tilas aure zai yi. Kuma auren ne ya haife shi, bai isa ya ki yin auren ba." Goggon Mama tayi tsaki. Ta ce, "Kina hauka ke kin ji budurwarsa Yaghana?" Nuri ta ce, "Na ganta. Ya ce ai buga masa waya ki ka yi a bango don kin ganta, har screen din wayar ya tsage, sai sabuwa ya saya. 68 |shafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Goggon Maman tayi tsaki. Ta ce, "Ai shi wannan mutumin bai san hakkin dan Adam ba, shi bai san irin son da nake masa ba. Amma ki kalli yadda yake wulakanta ni?" Nuri tayi dariya ta ce, "Ai ya yi ma Umma zancen zai auri 'yar Maiduguri ta ce a'a. Goggon Maman ta saki ajiyar zuciya ta ce, "Ai kin san shi idan ma bai auri waccan ba ai sai sa'a ya aure ni. Kin ga kuwa yadda ya wulakanta Khuzaimat?" Nuri ta yi tsaki ta ce, "Ai haukan da suka yi kenan ita da uwar ta, ki rike ciwon son da ki ke masa a ranki ki ci gaba da addu'a. Insha Allahu zai dawo ya kaunace ki, ya so ki. Kin san fa yana nuna alamun sonki, miskilancinsa ne ya hana a gane amma dai ki ci gaba da addu'a." A sanyaye Goggon Mama ta saki ajiyar zuciya ta ce, "Uhum! Ni fa tunda nayi masa jifa da wayarsa ba ma magana. Yau ne ma ya dan kula ni, ya kwace mini waya muna waya da Yaya Suraj. Nuri ta ce, "Wane Yaya Suraj din?" Goggon Mama tayi fari da idonta cike da damuwa ta ce, "Yaya Suraj na gidan nan.' 69 Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Nuri ta rike baki cike da mamaki ta се, "Mе ya ce miki?" Ta dan yi fari da idonta cike da damuwa ta ce, "Wai haka ya ce yana sona, yaushe zai zo muyi magana (face to face). Bar rna ba shi amsa ba sai Yaya Munir din ya kwace mıni wayar, ba ki ji ma ni yadda na gama tsorata ba." Yaya Suraj dan gidan Hajiya Binta ne, shi ne yake bin Munir a gidan Alhaji Ahmad, shi dai Yaya Suraj asali irin mutanen nan ne wanda basa jin maganar iyayensu. Dukkan asalin gidan ba wanda zai kammala Sakandire bai fita kasuwa ba, amma Suraj ba ya fita, iyakarsa uwarsa ta ba shi kudi idan ba ya da su. Ranar kasuwa zai fita idan kuma yaje kasuwar ba komai zai yi ba, lokar da Alhaji Ahmad yake zuba kudi zai bude ya dauki yadda yai masa ya fice abinsa. Shaye-shaye ba irin wanda ba ya yi, haka nan harkar mata kuma duk yadda kayi da Suraj ba zaka gan shi da shiga ta mutunci ba. Wando ne Jeans (Earth down), iyakarsa jikin cinyoyi haka nan kuma sai wani katon takalmi kambas baki 70 Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo da riga (Body hug). Sumar kansa kamar ka yi masa kitso, duk lokacin da za ka gan shi, za ka gan shi ne a-kwale. Don a bayyane

Chapter 3 of 13