ku
ka yi mini a mota ku ka sanya nayi ashar ranar
daukar amaryar su Safiyya?"
Kowacce sai tayi shiru nuna alamun rashin
gakiya. Khuzai ce ta ce, "Ai kai ma ka san
wadda tayi, har ka fada mata."
Ya dan kallo inda Goggon Mama take tana ta
faman linke kaya.
Ta ce, "Wallahi ni ba ni ba ce, ku ku ka san
ma wace се."
Suka kwashi hayaniya. Ya ce, "A'a ku tsaya,
kar ku cika mini kunne, ba na son hayaniya kun
jawo gashi nan Goggon Mama sai fushi take yi
da ni. Ai wannan ma wulakanci ne wallahi."
Ita kam! Ko kallonsu bata yi ba, Hajiya
Mama ta ce, "Oh! Mai sunan Mallam da rigima
ka ke, yanzun duk cikin 'ya'yan nawa ka rasa
mata? Sai kushe su ka ke faman yi, haka ake yin
rayuwa?"
24 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Ya ce, "Kyale su Mama, yaran nan ba su da kirki, idan na tona musu asiri sai kin dake su abin da suka yi mini a mota."
Hajiya Maman ta ce, "Yaushe ne?" Ya dan girgiza kansa ya ce, "Uhum! Za ki sha mamaki idan ki ka ji ranar daukar amarya da muka kai Safiyya gidanta ranar nan...bari kawai na rufa muku asiri kar na tona." Ya fada yana ficewa a
dakin.
Suka kaure da hayaniya, Hajiya Maman ta ce, "Allah mai iko! Daman wani abun ku ka yi masa?"
Khuzaimat ta ce, "Don Allah kyale shi Mama, da dinta mu haka yake cewa ban da mu Goggon Mama ce, kuma yanzun kin ga ya ce mu ne.
Don yaga tun lokacin ba ta masa magana
fushi take yi, shi ne fa ya dora mana don wulakanci har da cewa shi ba zai auri ko daya a
cikinmu ba."
Hajiya Sa'a tana daga tsakar gida a gindin famfo ta ce, "Oh! Kuma dai da cusa kai ku ke, ni ban taba ganin irin wannan iyaka da karfafa ba. Sai ka ce mai sunan Mallam ne autan maza a
duniyar nan? Duk fa wannan abun da yake
25 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
muku, alama ce yake nuna muku matarsa bata
cikinku.
Sai ku sama masa lafiya, ku kyale shi, tun
yana kora da hali kafin ya fara muku kora da
kara."
Hajiya Maimuna ta ce, "Ai kuwa ba zai yiwu
ba, saboda Alhaji ma haka ya ce ya zo gidan nan
ya zaba ba zai fita waje ba."
Hajiya Sa'a ta ce, "Yo ke idan ma zabar ce ai
ban da dakin ki Hajiya Maimuna, da ta dora
ranta sai sun mallake Alhaji Ahmad da dan
uwansa da dansa."
Abin ya fusatata. Ta ce, "Bangane ba abinda
ki ke nufi da ki ke cewa ban da 'yandakina?"
Hajiya Sa'a tayi dariya ta ce, "Allah Ya ba ki
hakuri idan zafi ya miki, daman gani nayi irin
rashin mutuncin da Hajiya Binta take tsulawa
uwarsa yaushe za su yadda ya auri diyarki.
Tunda gashi can abin da ku ka shuka sai fita
yake yi a gidan Alhaji Ahmad, ai gaskiya се
amma tunda naga kin ji haushi, kiyi hakuri." Та
fada tana barin wurin cike da kwarewa da iya
zaman duniya. Bakin ciki ya lullube Hajiya
Maimuna, gaba daya zufa ta lullubeta, ta ma rasa
amsar da za ta bayar a rayuwarta ta huce.
26 Ishaf:
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
A fusace ta bi Hajiya Sa'ade kofar dakinta ta
ce, "Amma Hajiya kin bani mamaki, yanzun
ashe idan mai sunan Mallam ya ce yana son
Zaimat ba za ki bari ba, kema 'yar kawo sukan
ra'ayi ce kar ya auri zuri'ata?
To ba yadda za ku yi, kannansa ubansu daya
da shi, 'ya'yan kanwata ne kuma, kuma kanwar
tawa matar ubanshi ce.
Haka nan kuma ubansa kanin uban Zaimat
ne, naga mai hana auren nan idan Allah ya yi, ai
daman duk gidan nan ba wanda yake shiri da ita
sai Khuzaimat din.
Don haka ba yadda za ku yi dani, idan ya ce
yana sonta sai dan bakin ciki ya mutu wallahik."
Ta wuce tana faman balbalin-bala'i, ita dai
Hajiya Mama ba ta tanka ba saboda daman
bakinsu daya, tare suke munafuncinsu daman ita
da Maman su Sagira ne kansu a hade.
Hajiya Adabiyya saboda bata da kowa a
Kano, daga kasar Sudan aka aurota aka kawo ta
Najeriya.
Alhajin ya danka ta a hannun Hajiya Magajiya ya ce bata san kowa ba sai ke, ki rike
ta amana ba kishi a tsakaninku.
27 Ishafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Don haka ana aurowa Hajiya Sa'a itama
Hajiya Maimuna ta shige wurinta suke
munafuncinsu tare, yayin da Hajiya Magajiya ta
zuba musu ido.
Lokacin da Ya Nabil babban dan Hajiya
Magajiya din ma ya auri diyar Hajiya Sa'a, ido
ta zuba musu ake faman kulle-kulle da
munafunce-munafunce.
Su Aminan kishiyoyi yanzun kuma dubu ta
cika, ana kyashin juna, don haka da suna
fadansu ma ko lekowa ma bata yi ba, balle ta се
me ake yi?
Da daddare shigowar Alhaji Usman daga
kasuwa ko hutawa bai yi ba, Hajiya Maimuna ta
tarye shi da maganar abin da Hajiya Sa'a tayi
mata.
Ya ce, "To duka gidan su zo yana son
ganinsu." Sai da kowa yazo Hajiya Magajiya ba
ta zo ba, Alhajin ya yi wanka ya fito sanye da
jallabiya.
Yana zama suka ringa gaishe shi yana
amsawa sama-sama, ya ce, "Ina Hajiya Magajiya
din?"
Hajiya Sa'a tayi dariya ta ce, "To ai manyan
mata ne ka san su manya ai sai a hankali."
28 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Ita kam Hajiya Maimu sai ta ce, "Ai tasan me
ta kulla shi ne yasa ta ki zuwa, ai daman tun dadewa akan mai sunan Mallam ta dade tana mini gadara.
Kawai ban gaya maka ba ne, komai nunawa
take yi ta fi mu kusa da shi, ko tsaraba ya kawo
sai ta hana, ta ce sai Goggon Mama ce zata raba. Ita kuma Goggon Maman ta kafa gadara tana rabawa a wulakance, yanzun wannan zuwan kayan shafa ya kawo da sabulai, ina kallonta da kyar ta ba su dai-dai.
Ai wannan raba zumunci ne, idan bata gyara ba da girmanta ai kuma ba za ta 6ata ba."
Ya yi gyaran murya tare da daga hannu alamun ya ishe shi haka.
Hajiya Sa'a dai sai ta ce, "Allah shi sawwake,
son kai!" Hajiya Maimu ta ce, "Wane irin son kai? Ke yanzun ba ga nan Nabil ba tunda ya auri Jidda ta raba shi da uwarshi ba, ta ma janye shi ko kasar ba ya zuwa.
Alhajin ya daka tsawa, suka yi shiru. Ya dauki wayarshi ya kira layin Hajiya Magajiya din, har ta tsinke ba ta daga ba. ya sake kira na biyu, na uku, na hudu sai yaronta ne Hafiz ya daga.
29 shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Alhajin ya ce, "Hafiz ina Hajiya din?"
Ya ce, "Ga ta nan a kan keken dinki, tana
dinki ne.'"Ya ce, "Ka bata wayar."
Hafizu ya mika mata, amma sai ta harare shi
alamun ba za ta amshi wayar ba.
Alhajin ya bar taron matan ya taso har dakin
nata, ya tsaya yana kallonta tana ta dinkinta ko
inda yake kallo bata kalla ba.
Shi kansa yasan yau ranta a bace yake, ita
kuma zata dade bata yi fushi ba, amma idan tayi
fushin abin ba shi da kyau, a gidan sai kowa ya
san ranta ya бaci.
Alhajin ya yi murmushi ya matsa in da take
dinkin ya dafa hannunta, da kafarta yasa
almakashi wurin allurar keken ya taka kafar
keken allurar ta karye.
Ya sake fadin "Muje ko kuma na fita waje
yanzun nayi kyautar keken dinkin naga ya za ki
yi?"
Tayi har! Da idonta, alamun damuwa ta
wuce. Yabi bayanta da fada yana fadin.
"Ni banga me ki ke samu a wata sana'ar dinki
ba, ban da wahalar da kanki da ki ke yi, ke kenan
kullum ba ki da hutu, komai dare dinki, kowanne
lokaci dinki.
301shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Ai ni wannan ban san ya za ki yi ba wallahi, idan na kyautar da keken dinkin nan.
Ba ta tanka ba har sai dai da suka shiga falon
ya ci gaba da fada da maganganu, sannan ta ce "Ni ban iya zama hannu goma baki na sha daya ba, dole dai kowa ya sani Kanawan asali akwai maida taro sisi, ba zama wuri daya.
Yaushe zan jira samun 'ya'yana ko na miji? Ai ni na wuce da wannan matsayin wallahi."
Ya yi dariya ya ce, "Haka ne! muna alfahari ni da 'ya'yana da samunki cikin rayuwarmu, sai
kuma bayani na gaba.
Ki taimaka don Allah ki taimake ni, zan yanke wani umarni irin wanda na saba yankewa
da yardarki."
Ta kalle shi ta ce, "Kamar wanne fa?" Ya ce, "Ina so zan hada auren Khuzaimatu da mai
sunan Mallam, ina fatan ya zamo al'amarin ya birge ki. Ki kuma sanya albarka tun da dai yaran sun hada kansu ko?"
Tayi dan murmushi ta ce, "Madallah, Allah
ya sanya alheri, ai don wannan ka isa ba sai ka
gaya mini ba."
Ya kira wayar Alhaji Ahmad ya gaya masa Alhajin kamar su yana tare da gaba daya
31 Ishafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
matansa, ya bayyana abin da dan uwansa ya fada
a wayar, gaba daya wannan ta kalli wannan,
waccan ta kalli waccan.
Hajiya Rabi'a ta ce, "Anya anyi wannan
zancen Alhaji? A dai tambayi mai sunan Mallam
din kar a yanke hukunci ba daidai ba.
Donni ji nayi ya ce mini abokinsa ya ba shi
budurwa a can Maiduguri, suna nan mazauna
دو Abuja ne.
Alhajin ya yi tsaki ya ce, "Kuna shirme da ke
da shi, ni har na isa na daga umarnin Yaya
Usman? Abin da ya ce ai shi ne ko ba ya so tilas
ya amince, saboda nima shi ne yake iko da ni,
balle abin da yake karkashin ikona.
Kinga dole ne ya yi biyayya da abin da aka ce
وو
masa.
Shigowar Munir din ne yasa duk suka juyo,
Hajiya Binta cike da gadara ta ce.
"To ai ba aman ba lashewar, tunda ga mai
sunan Mallam din ya fada da kansa muji, ai ni
wulakancin da ake mana families din ya fara
isata.
Don tun asali Allah Ya yi aurena da Alhaji
Ahmad ake, kinmu ni da Yayata, ni kuma ba
321shfi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
yadda mutum zai yi damu, don yana takamar mijin yayansa ne."
Ita dai Hajiya Rabi'a bata tanka ba, don ba sosai take daukar raini ba.
Ta sake daure fuska cikin sanyin murya ta kalli Mai sunan Mallam din.
Та се, "Kai yaushe ku ka kulla alakar
soyayya da Khuzaimatu 'yar gidan Alhaji Babba?"
Ya yi murmushi tare da durkusawa a gaban
Baban nasu, shima tambayr ya kuma yi masa.
Ya ce, "Da gaske ne?" Ya girgiza kansa ya
ce, "A'a Alhaji ba da gaske ba ne, ai ni dukkan
su yaran nan ban taßa musu maganar soyayya ba wallahi."
Alhaji Ahmad ya daga masa hannu yana fadin "Ya isa haka, to idan ma ba ka so an baka
Khuzaimatu, ai ita 'yar Maidugurin da abokinka
ya ba ka bai kai ubanka ba Yayana ko?"
Ya yi shiru, Alhajin ya sake magana ya ce, "Ai bai kai Alhajin zoo road ba don abokinka ma
ya baka ka karba balle kuma ubanka, tashi kaje Allah Ya maka albarka."
Ya mike bai iya tankawa ba, Hajiya Rabi'a ta
ce, "Akwai sauran gyara dannan tsaya, idan kana
33 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
son Khuzaima ka gaya mini tun a nan, idan ba ka
sonta ka fada kowa ya ji.
Ya dan rusuna ya ce, "Umma ki kwantar da
hankalinki, ba a maganar so idan ana maganar
biyayya, ba komai can gaba son ya zo.
Ta mike a tsaye ta goya 'yar diyarta da take
goyo, watanta goma. Ta janyo zanin goyon a
fusace ta daure goyon gam!
Ta ce, "Fita ka tafi." Ya tsaya zai yi magana
ta ce, "Fita na ce! Fita!! Fita ka ba ni wuri." Ta
sake maimaitawa a fusace.
Da sauri Munir ya fice.
Ta kalli Alhaji tayi murmushi, ta ce "Sorry!
Na ce sorry!! Wallahi sorinka!!!
To a kan wannan auren ne da aka kullo don a
ci mana zarafi ni da 'yar uwata ko? Wallahi sai
dai aurena ya mutu ka hada ni da ni da Munir ka
sallame mu, amma ba zai taba auran 'yar Maimu
ba.
Saboda bai ce yana so ba, lakawa a ka yi a ci
mutuncin 'yar uwata, to albishirinka! Yadda
suka auro maka Binta suka gani ba su kwace ka
ba, shi ne yanzun suka kullo wannan don su
kwace mini da?
34
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Kalli auran Nabil da Jidda, me ya kara mana
ban da rashin ci gaba? Wallahi ba zai yiwu ba,
kowa ya nemo matarsa a waje."
Alhaji Ahmad ba ya son fitina sosai, ya ya
yana kallon Hajiya Rabi'a tana wanka ruwan
bala'i.
Ya yi dariya ya daga mata hannu alamun ya
19
isa "Koma ki zauna ya isa haka zauna."
Ta sake gyara goyon diyarta, ta zunkudata ta
zauna a fusace. Ya yi dariya ya ce, "Ke idan ban
da abinki ki kyale ayi auren mana?
Ita Bintar da aka auro ta kinga ta raba ni da
ke? Balle wata Khuzaimatu? Me za ta dauka? Ki
gagari ita Bintan ma da Maimun diyarsu ce zata
gagare ki?"
Suka yi dariya ragowar matan.
Ta ce, "Ni fa na gaya maka tun wuri, kawai
auren munafuncin nan ba za a yi shi ba."
Ya girgiza kansa.
"Auren zumunci ne, kuma insha Allahu ba
zamu fasa ba."
Ta mike ta fice daga falon don garin saukowa
step ına sai da ta yi rauni a babban dan yatsanta
ta yi targade.
35
17
Zumunci Dangin Kauna Jemila M. Danfajo
Da kanta ta kira wayar Alhaji usıman ta ce,
"Auran nan fa munafunci ne Alhaji.
Ya ce. "Bangane ba?" Ta zayyane ma Alhajin
yadda suka yi da Munir din, ya fahimce ta sosai.
To amma ganin Hajiya Maimu sun sanya shi a
gaba sai kawai ya ce mata.
"Kiyi hakuri Rabi'a, zan yi dan wani bincike
nan da kwana biyu."
Tayi godiya ta kashe wayar tana faman zubar
da ruwan bala'i a tsakasr gidan, tana fadin.
"Ai ni wannan cin kashin da ake yi ma Yaya
Magajiya tana hakuri wallahi ni ba zan hakura
ba, mutum yana shigo mini cikin sabgogina zan
fitar da shi, munafuncin banza kawai."
Ba wanda ya tanka mata, don dama ita tsakar
gidanta idan ta yar da karanta ba wanda ya isa ya
Ketare mata.
Sau da yawa kuwa idan lamura suka tsananta
na rigima ita da Maigidan sai Yayan su Alhaji
Usman din ya sako baki sannan wutar rigimar ta
mutu.
Da safe kuwa fada ta lullube Munir da shi
sosai, ta ce sai ya taka da kafarsa gaban Alhaji
Babba ya ce masa ba ya son auran Khuzaimatu.
36 1
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Idan ba haka ba kuma ba ita ba shi, don jikinsa a sanyaye ya nufi zoo road din. To ai mutumin ne mai girma da daraja,
mutum ne da ya musu gata ko bukatar meye ta
taso musu kafin ma ubansa ya yi masa Alhaji Babba din tuni ya yi masa.
Ya canza masa mota ya fi a kidaya, ya masa gata fiye da yadda yake tsammani.
Yana zuwa kasuwa idan ya dawo a
Makaranta, kusan duk harkokinshi shi ne yake kula da su.
Sau da yawa sai yazo kasuwa zai miko masa boyil da shadda a leda, ya ce bari na kirawo Tela ya gwadaka.
Da Telolin ma suka gane gwajinsa sai dai ya gani a dinke, takalma da turaruka kuwa ba a
magana, gata na karshe yake yi masa.
To ya zai iya duban tsabar idonsa ya ce ba ya
son jininsa? Shi dai yasan yana cikin jarabawar Ubangiji.
Bayan kwana biyu shigar yamma ya yi ma gidan, a harabar gidan wani babban al'amari ya bugi zuciyarsa.
Goggon Mama ya gani tana hira da wani
babban mutum, da ganin mutumin Magidanci ne.
37 shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Zuciyarsa wani irin bugu ta karba mai karfin
gaske, da sauri take bugawa, bai tsaya karbar
gaisuwar da mutumin yake yi masa ba.
Yana zaune cikin mota (E.O.D) Dark blue ce
kamar yadda shaddar jikinsa ma haka kalarta,
bugaggiyar Ghalila. Haka hular kansa kirar
(Damanga) ita ma blue ce kalar fari tas!
Ya cika harabar wurin da Kamshin turaren
jikinsa, kalafunsa a wajen motarsa, yayin da
Goggon Mama take zaune a bisa farar kujera, a
gabansu tire ne da kofuna da lemo da ruwa.
Ya wuce ba tare da ya karbi gaisuwar da ake
yi masa ba daga cikin motar, ya wuce cikin
gidan.
'Yammatan a gindin famfo suna aikin gyaran
kaji, kowacce bakinta har kunne.
"Yaya sannu. da zuwa, Yaya oyoyo. Yaya
sannu da zuwa."
Fuskarshin nan mai wasa da dariya a yau a
daure take gam! Ba walwala.
Suna ganinsa sun san yau ba sauki, don haka
kowacce ta kame kanta.
Ya nuna Khuzaimat da dan yatsansa ya се,
"Ke zo.." jikinta yana rawa ta taso tazo.
38|shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Ya kashe murya sosai yadda bt mai jiyo shi, ya ce "Yaushe na ce ina sonki?" Tayi shiru, ya
kuma daka tsawa ya ce, "Tambayarki nake yi, yaushe na ce ina sonki? Ba ki da mutunci ko? Sai ku ringa hada fitina.
Da Allah gafara ki ba ni wuri stupid girl kawai, idan don ina yi muku wasa ne ma ki ka
יי kala mini karya ni da ke ne.'
Ta wuce sumi-sumi alamun rashin gaskiya, taje ta gaya ma Ummanta tana faman kuka.
A lokacin ya shiga dakin Hajiya Mama, ya
wuce har dakin nata ya zauna, ita a lokacin tana
sashin Alhaji saboda bai riga ya fita ba, da shi ke dai ba ya jin dadi.
Yana zaune abin duniya ya dame shi,
tunaninsa daya saurayin da ya gani wurin Goggon Mama, zuciyarsa don bugu tamkar ta 6allo ta fito.
Bai taba sanin akwai son Goggon Mama а
ransa ba sai yau. Ya nutsa cikin tunani, sai kawai
ya ji sallama a fusace.
Yana daga ido yaga Hajiya Maimu da Zaimat, a nan ta 6alle kwandon bala'i. "Idan ba ka sonta sai me? Na ce sai me? Wallahi ka ba ni mamaki Mai sunan Mallam!
39 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Ka ba ni mamaki! Khuzaimat ce ba ka so ko?
Na gode! Ai daman Hajiya Rabi'a ta ce a'a, ta се
ba za ka taba auren 'yata ba idan kayi mini
godiya Allah yana nan.
Makiyan Khuzaimat za su yi mamaki sai ta
auri wanda ya fi ka."
Maganganu ta ringa yi cikin fusata, cikin
daga harshe. Shigowar Alhaji Ahmad ne yasa ta
saurara.
A falonsa ya kira meeting jin Munir yana
gidan ya ce a kirawo shi.
A ranar ya kashe maganar ya сe, "Ke
Khuzaimatu kar na kuma jin abin da ba shi an zo
an kawo mini shi nan.
Duk abin da mutum zai fada ya tabbatar ya
fada min gaskiya, saboda dai ni ba karamin
mutum ba ce.
Alhaji Ahmad ya ce, "To Alhaji meye idan
shi ba ya sonta ai ita tana son shi, ai wannan
auren ba fashi.
Sai dai ya yi abin da zai yi, amma ba fasawa.
Ai daga ji ka san akwai wata a kasa, suna son
6ata abin, ka san su mata ba hankali ne da su ba.
Bata zumunci ba su maida shi a bakin komai
ba."
40 |shafi
Zumunci Pangin Kauna Jamila M. Danfajo
Alhaji Usman ya girgiza kai ya ce, "Ba zai
yiwu ba ayi abin da za ayi da na saninsa.
Ai namiji idan yana son mace ba ya iya
6oyewa, tashi jeka ai tunda ya ce ba ya so, ba ya
so to ba ya so din."
Alhaji Ahmad ya fusata ya ce, "To tunda abin
naka iskanci ne, ba za a taba baka aure a families
dinmu ba, jeka 'yar Maidugurin ta isheka."
Shi dai bai damu ba saboda yasan ya kubuta
daga fushin Mahaifiyarsa, wanda idan tana
fushin ba ya iya cin abinci ba ya iya karatu balle
bacci.
Ya jima yana jiran Hajiya Mama a falonta ba
ta shigo ba, itama Goggon Mama ta jima a
wajen.
Ya kalli agogo ya tuna tsawon lokacin da ta
bata a wajen, kafin zuwansa gidan ma balle
kuma zuwansa yanzun.
Mikewa ya yi kamar wanda ake tsikara ya yi
wajen, kansa tsaye wurinta ya nufa. Na cikin
motar ya miko masa hannu ya ce masa.
"Dazun ina maka magana ai ba ka ji ba." Ya
sake bata fuska ya ce, "Eh! Ya yi kyau. Ke
Goggon Mama koma gida."
41 1shati
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Yadda ya yi maganar da yadda yaga fuskarsa
ta nuna, tilas ta mike ta wuce.
Ya murza 'yan yatsunsa ya ce, "Wannan
yarinyar an yi mata miji." Shima a tsayen ya
mike yana muzurai.
Ya ce, "Bangane ba? Ai Alhajin yasan da
zuwana, shagona yana nan bayan nasa a kasuwa
tun ranar da na gano ita diyarsa ce nace ina so ya
ce ya bani."
Gaban Munir ya buga da karfi, lalle ana
kashe shi da ransa. Ya ce, "To idan ya fito
kasuwa ka gaya masa sakon da ya bayar an gaya
maka, ka gane ko? Zai yi maka karin bayani."
Yana fada ya yi kwallo da tiren kayan lemon da
kujerar.
Goggon Mama da ta ke rakabe, da gudu ta
karasa cikin gida don daman ita ba wani sonsa
take yi ba, saboda har fa mata biyu gare shi an
raba ta da rakai.
Yana jan motarsa yana tafiya yaran gidan
suka kwashi kayan lemon suka yi cikin gida da
shi suna bada labari.
Dukkaısu a gaban Hajiya Maimuna suke
zancen, suka ajiye farantin, tayi tsaki tana fadin.
?
42 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
"Ai karyar banza ce, kishin banza yake yi ai
shi Alhajin nasa ai da kansa ya ce idan bai auri
Khuzaimatu ba, ba 'yar da zai aura a dangi a ba
shi, don ni nasan uwarsa ce ta zuga shi kar ya
auri diyata, to tasun ma ba zai aura ba, da izinin
Ubangiji.
Mu za a yi wa karyar auren zumunci! Kalli
yanzun yadda Alhaji Ahmad ya shigo falon duka
aka fito damu amma ita Hajiya Magajiya tana
ciki.
Duk shawarar duniya da ita ake yi, idan an yi
magana sai su ce wai ai ita kanwarsu ce, irin
hakan ne mu ba ta so, ai dama da 'ya'yan a auren
dangi.
Sai dai su'i'su, ai kuwa na gani ace ba a son
diyata a auri wata a gidan nan, naga yadda za ayi
in dai ina raye a duniya."
Ita kam Goggon Mama bata fito tsakar gida
ba, yayin da shi Munir din yake zaune a falo ya
tsareta da idonsa ma su ba ta tsoro.
Ita kallon ya maida ita tamkar auduga, don
wani irin laushi da tayi ta kasa dagowa su hada
idon, to ma duk lokacin da ta dago idon shi yana kallonta cike da nuna tsantsar so maras surki.
43
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Ta daburce ta rasa sukuni, ita kanta tasan tana
son Ya Munir, kishi ne yake sanyawa taji
haushinsa, yadda a gidan yake sakar ma
'yammatan gidan fuska.
Kalli fa har wata a cikinsu ta ce shi take so,
ba shi ne ya janyo ba? wannan dalilin yasa
kullum suke rigima ita da shi.
Duk bata san ya rigimar ta kwashe ba, sai
zuciyarta ta rada mata ai wannan ma zalunci ne
ya fitar da matar aurensa yazo ya hana ta zance
da samarinta.
Ina laifi ko kati suke sanya mata za a kore
mata samari.
Munir din ya ce, "Tashi ki ba ni ruwa." Yi
tayi kamar bata ji ba, ya ce "Ba magana nake yi
miki ba?"
Shiru ta yi a ranta kuwa ji take duk abin da
tayi zata bayar da kanta, don a salon magana ma
ya kashe mata jiki balle mugum kallonsa.
Don haka ta ki magana, ta ki motsi, yayin da
ya zare belt yake tafka mata.
Rikici har tsakar gidan, don waje tayi da gudu
tana fan an kuka.
Hajiya Sa'a ce ta ce "Haba Mai sunan
Mallam! Me tayi maka?" Bai tanka ba ya juya
44
Zumunçi Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
don ranar ransa a bace yake ba alamun wasa a
fuskarsa.
Ta wuce kitchen ta dauko tire ta shirya ruwa
da lemo a kan tire da kofuna a kai, ta wuce ta kai
masa.
Hajiya Sa'a ta ce, "Taurin kanki har a ba ni
ruwa na sha ina abin Kiwa don dai kun raina
mutane?"
Ita dai bata tanka ba, ta wuce shi taje ta ajiye
ta fito. Ya ce, "Zo ki bude ki zuba mini." Ta
ringa kallonsa cike da harara.
Tazo ta zuba masa tana faman gunguni da
goge hawaye.
Shigowar Hajiya Mama ne yasa ya dan saki fuskarsa ya ce, "Hajiya jiranki nake yi." Ta cе,
"Ai ni nayi zaton.ka tafi, sai da naji hayaniyarku
na ce ashe kana nan."
Ya duba agogon hannunsa ya dauko kofin lemon da ta zuba masa yasha ya ce, "So nake zan
wuce Maiduguri yau takarduna zan kar6o."
Та се, "То yaushe ne za ka dawo?"
Ya ce, "Yau fa zan dawo komai dare, so nake
na kai takarduna Kaduna, jibi kuma nake so zan
kai wurin Sa'id, Babansa zai sa ni aiki a
kamfaninsa."
45 |shaf1
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Hajiya Maman ta ce, "Allah yasa a dace, can
wurin Baban abokin nan naka da ka ke bani
labari ko?"
Ya ce, "Eh! Wallahi." Ta ce, "Allah Ya
taimaka." Ya ce, "Amin Ya Allah."
Ta ce, "Ai kai kam ka tsallake rijiya da baya,
kaga nufin mutanan nan akan mu ko?"
Ya ce, Na gani Hajiya Mama, insha Allahu
ba za su yi nasara ba." ta ce, "To ku ringa
kiyayewa, yanzun kai da Hafizu ne suke hari, kai
ka ketare insha Allahu Hafizun ma ba za su yi
nasara ba."
Ya ce, "Haka ne Hajiya Mama, Allah Ya
dora mu a kan su." Ta ce, "Amin."
Ya jima suna hira sanda ya yi shiri zai tafi ta
dauko kudi ta ce, "Ga su to Mai sunan Mallam
wancan adashen ina kwasa Hafizu ya karba.
Don ya raina mini wayo ya ce zai karbo mini
wurin Babansu kaga shiru kai ma ungo wannan
din."
Ya dan sosa kansa ya amsa ya ce, "Kuma
wallahi Mama kamar kin san ba ni da kudi, don
Umma haka ta ce kudinta na sayo kwalaben nan
na (Passion) nasu Nuri ne zata fara taro."
46 |shafi
۴
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Hajiya Mama ta ce, "Ban sayo mata ba
wancan zuwan." Ya harari Goggon Mama ya cе,
יי
"Haka ta ce wai tana jin Goggon Mama ne.
Hajiya Maman tayi dariya ta ce, "Oh! Lallai
da kallo ran auren uwata da Nuri."
Yasa kai ya fita yana yi ma matan gidan
sallama ya tafi.
A gidansu ya iske Ummansa a daki ta sanya
injin saka a gaba ita da Nuri sai faman saka suke
yi, suna faman hirarsu.
Ya shigo ya zauna ya ce "Umma Hajiya
Mama na gaishe ki." Ta harare
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 13