da babban bako, don haka
a but ta sanya musu suka tafi da shi.
Suna faman kunsar bakin ciki, duk yadda
suka yi tsammanin rayuwar Hajiya zata koma
baya sai ya zamto sune suka raina kansu.
Don Allah ya mata nasibi ba dan kadan ba,
ta kowacce fuska. Rayuwa kenan.
Ranar gidan a cike ya yini da Jama'a,
wannan ya shigo ya fita, wannan ya shigo ya
fita ana faman kallon irin dukiyar da aka zuba
a cikin lefen kowa labari yake yi.
Ita kam Hajiya Mama, mamaki ne ya hana
ta magana, sai washe baki take, yawan
shigowar Jama'a ne ya sanyaya zuciyarta akan
fushinta da Mai sunan Mallam da Zainab din
suka samu damar yini tare suna amayar da
abinda yake zuciyarsu.
119
Zumunci Dangin Kauna 2
Jamila M. Danfajo
Sai da suka yi sallar Isha'i, sannan suka
shigo cikin gida, ba yadda zata yi da su ta ce,
wai daman ka san yau din za a kawo lefe ka ki
gaya mini?
Ya yi murmushi ya ce, "Hanawa za ki yi to
Hajiya Mama ni kuma bana son ki hana."
Tayi murmushi tana ai da ka gaya mini ba
za ka yi lefe ba, sai dai ka sayi mota ka tsole
idon makiya."
Badi'atu ta ce, "Ai kuwa lefen ma ya tsole
musu idon, don duk family ba wanda ya samu
lefe kamar na Goggon Mama, ba ki gani ba
duk jikinsu ya yi sanyi." Ta ce, "Lallai kam!"
To Allah ya sanya alheri. Ta amsa "Amin."
Zamansu a falon gaban lefen yasa tilas ta bar
wurin.
Suka shiga gwada warwaro da takalma, ana
fesa turare don aji kamshin kowanne.
Ita kam! Badi'atu ficewa tayi a falon tana
fadin "Nima dai Allah ya kawo mini mijin nan
mai sona na huta da kafafar masoyi." Suka
kalli juna suka yi dariya.
Sai sha daya saura suka rabu, a ranar shima
da kyar ta lallaßa shi, yaje ya kwanta.
120
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Yana kwanciya ya kirata, ta ce ba ka
tausayina ne Yaya Mallam ka bar ni nayi bacci
mana ko? Kuma fa kai ma goben karfe takwas
יי ka bar Kano."
Ya yi dariya ya ce, "Haba yarinya, so nake
na sabar miki da rashin bacci, don kin san ba
barin ki zan yi kiyi baccin ba idan muna tare,
kin gane ko?"
Shiru tayi don ta rasa bakin magana, ta kasa
ce masa komai. Ya ce, "Ko ba kya jin gwarzon
mazaje yana magana?"
Ta saki ajiyar zuciya ta ce, "Ni dai sai da
safe." Ya ce, "Kin san Allah kar ki kashe mini
waya. Wallahi kina kashewa zan shigo."
Murmushi tayi ta ce, "Wallahi ka shigo
mana, kai da Hajiya Mama. Ka san abin da
zaka ce mata idan ta tsare kа."
Yana dariya cike da nishadi ya ce, "Zan ce
mata ke ce ki ka kirawo ni, ki ka ce nazo ba ki
da lafiya kina cutar son ganina."
Tayi dariya ta ce, "To Allah Ya baka
hakuri, ai ni wannan maganar tafi karfina, sai
da safe.
121Sh&s
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Don yanzun zan yi sallah ne na roka maka
sa'ar tafiya wurin aiki." Ya ce, "To na gode,
sai da safe."
Washegari kuwa kafin ya tafi sai da ya
canza mata waya, suka raka shi har air port,
sannan suka dawo.
Sabon rikici kuma ya 6alle ita a Badi'atu,
don ko wuri daya ba sa zama balle kwanciya,
da ta matsa sai taji me ya hada su.
Sai kawai ta ce, "Ke da Ya Munir ya ce zai
miki ciki! Na sani ko ya miki?"
Ita Zainab takaici ma hanata magana ya yi,
take kallon Badi'atu da idan tayi wani abun
tamkar bata santa ba.
Ko wata maras hankali ta tashi ta bar mata
wurin don idan ta biye mata sai tayi mata tonon
asiri, har Hajiya Maman taji da abinda kenan.
Kwanaki na tafiya, yayin da watanni suke
juya su kamarin su Zainab yana kara karfi har
bikinsu ya matso, bikin sauran sati daya rak!
'Yan Katsina suka kawo lefen Ummi
Farida, abin sai wanda ya gani, don zuwa
yanzun Ummi din ta gama Secondary.
122shafi
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Don haka aka yanke hukuncin aurenta da na
su Zainab za a hada, Alhaji kuma ya ce da Badi'atu.
"Badi'atu ki fitar da miji mana a hada ki da
'yan uwanki, kin san ba za a aurar da su a bar
ki ba."
Da shi ke maganar a tsakar gida ya mata, a
gaban mutane ta ce, "Ni fa Alhaji bani da
wanda yake sona, kowane saurayi nayi sai
Ummi ta raba ni da shi.
Wancan ma ni ya fara gani daga karshe ta
janye shi."
Abban ya yi dariya don yana son shirmen
Badi'atu, ya ce, "To tunda ba ki da saurayi ba
kya samun samari bari na zabo miki mijin da kaina."
Tayi dan dum! Sannan ta će, "Amma Alhaji wanda zai so ni irin na Zainab da Ya Munir?"
Ya ce, "Har ma yafi. Ina nan ina addu'a
Allah ya tabbatar da alheri." Ta ce, "Amin Alhajinmu, na gode. Allah ya kara girma."
Sai da daddare har tayi shimfidarta ta kwanta, sai ta tsokano hira tsakaninta da
Zainab, lokacin tayi waya da Munir ta kashe.
123Safi
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Badi'atu din ta ce, "Ni Goggon Mama ban
san irin mijin da Alhaji Babba zai zaba mini
ba."
Ta ce mata, "Ke dai kiyi addu'a, idan da
rabonki sai ki ga kin samu irin wanda ki ke
So.
Tayi tsaki ta gyara kwanciyarta.
Ta ce, "Ina tsoron mai kishiya ne, donni
idan mai kishiya ne wallahi bana so, wallahi
tun wuri ki gaya ma Maman. Don ni ba kalar
gidan kishiya ba ce.
Zainab ta ce, "Ke dai kiyi fata ya so ki mijin
irin yadda Munir din yake sona, ina ruwanki da
wata kishiyarsa?"
Suka yi shiru tsawon lokaci, ta ce "Ai ni ban
san meye soyayyar nan ba, ku ne dai 'yan
jarabar soyayya har saurayi ya ce zai maka
ciki, kana manne da shi."
Ita dai bata sake magana ba don so take ta
tona mata asiri. Ta ce, "Ke ai ba ki samu mai
cewa zai miki cikin ba, sai faman an kwace
miki saurayi.
Ke kullum korafi ne aikinki. Idan gidan
kishiyar aka kai ki ba iyawa za ki yi ba."
1241shai
Zumyr Dain auna 2 Jamila M. Danfajo
Tana kwance ta tashi a zaune ta ce, "Cab!
To wallahi ni ko kishiya goma ce zan yi
maganinta, balle wata guda daya don dai bana
so ne.
Amma idan ina son mijin sai dai ta hakura,
amma ba ni ba."
**
NABIL
Misalin karfe uku na daren Litinin, Hafiz
yake buga gida da wani irin karfinsa.
Shi kansa Alhaji ya tsorata da buga gidan,
don haka ba wanda ya tashi ya bude gidan.
Ganin ba a bude masa ba ya ringa kiran
lambobinsu duk a rufe, yana kiran ta Goggon
Mama ta dauka a tsorace ta ce, "Lafiya Ya Hafizu?"
A fusace ya ce, "Lafiya lau, ki ce a bude
mini gida gani a get."
Ta mike a sanyaye taje ta tashi Hajiya
Mama, sai ma ta iske idonta biyu. Ta ce,
"Hajiya kin ji bugun gida?" Ta ce, "Naji, ai
abinda Alhaji ya yi shiru yana gida ni me zan
ce?"
125d
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Ta ce, "A'a Yaya Hafiz ne fa yanzun ya kira
wayata ya ce yana kofar gida."
Hajiya Maman ta ce, "To lafiya?" Та се,
"Bari na kira miki shi a waya."
Sai da taji muryarsa sannan taje ta kai ma
Alhaji wayar suka yi magana, sannan aka bude
masa gida.
Ya ce, "Ba shigowa zan yi ba, mukullin
mota za a bani, air port zan je yanzun nan Yaya
Nabil ya ce mini yazo shi suna jirana."
Alhajin ya ce, "To barkansa da zuwa, kaima
mai dauko shin barkan ka da zuwa." Ya се,
"Yauwa Alhaji."
Mukullin ya mika masa ya juya. Hajiya
Maman ta ce, "Alhajin ba zai je taryan Ya
Nabil ba?" Alhajin ya ce, "Ni da nasan ma
Nabil ne yazo shi ba zan bude gidana ba."
Hafizu kam! Dariya yake yi sosai, Hajiya ta
ce, "Don zuwan Nabil kam ka sani shi yasa ma
ina ce maka Nabil ne naga kayi hanzari ka
tashi."
Ya koma dakinsa ba tare da ya juyo ba.
Shi kam Hafizu mota ya dauka, Hajiya
Mama ta ce, "Bari muje mu."." Hafizun ya yi
126hafs
Zurnunci Dangin Kauna 2
Jamila M. Danfajo
dariya ya ce, "A'a Hajiya yi zamanki, bani
minti talatin yanzun za ki ganni kin ji ko?" Ta
ce, "To Allah ya kiyaye." Ya amsa "Amin.”
Nabil din yana sanye cikin suit da shi da
'ya'yansa 'yammata su biyu kowacce cikin suit
din samfarin kayan mata da takalma kafa ciki.
Mutanen kasar Turai, da shi da matarsa abin
kallo a kasar Hausa.
Ita kam Jalilar sanye take cikin doguwar
riga mai kalar baki, da jajayen fulawoyi.
Hannu da kasanta da gefen dankwalin, sai
kamshi suke yi. Da sauri Hafizun ya rungume~ Yayansa yana tambayarsa.
"Ina ka samu lambata?" Ya ce, "Ba wahala
Brother in dai ina son abu daga Nigeria ina
samu da wuri." Ya ce, "Kai amma nayi murna da zuwanka Yaya Nabil."
Ya fada yana daukar jakarsa ya kalli mai jin
sai shan kamshi take yi, ya ce, "A'a Anty mai jin ya kasar sanyi fine." Ta ce ta dauki diyarta
yayin da Nabil din ya dauki dayar suka nufi.
Ita da yaranta a baya, yayin da shi da Nabil
a gaba Hafizun yana tuka su. Hira suka yi sosai
na bayan rabuwa.
127 |Shafi
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Ya ce, "Yanzun ina muka nufa?" Hafizun
ya ce, "In da ka ce mana." Ya ce, "Muje Soron
Dinki."
Ya yi dariya ya ce, "Ya kayi ka san Hajiya
Mama na Soron Dinki?" Ya ce, "Ka daina
mamakina ina da labarin komai na gidanmu."
Ya yi dariya.
Ya ce, "Ai auta ce ta maida ta can, auranmu
yazo da rudani kala-kala." Ya ce, "Kowa ka
gani a duniyar nan da kaddararsa, muna fatan
mu tsinci kanmu a kaddara mai kyau. Hafizu
ya ce, "Amin."
Ita kam mai jin din sai faman cika da
batsewar rashin mutunci take yi ya ce ya
saukake, ni ya kai ni zoo road din.
Nabil din ya kalle ta ya ce, "A'a sai dai mu
sauke ki ki tari tasi ni da 'ya'yana gidan uwata
zamu je, ko ya ka ke gani?" Ya fada yana
kallon Hafizun.
Ya ce, "A'a ba komai bari akai ku sai na
mika ta ko?" Ya ce, "Idan ba za ta bari da safe
taje zoo road din ba, ta sauka a nan ta tari
Taxi."
1281Shafi
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Daga haka ba ta sake magana ba, har suka
iso gida.
Su kam su Zainab ba su koma bacci ba da
su da Goggon ma, da Hajiya Maman suna
faman kaiwa da kawowa a tsakar gida.
Don Hajiya Mama sai ta bude (Deep Freezer) ta soma fito da kaji da kifi, kowanne
ta wanke ta kunna gas ta dora.
Sannan tasa ruwa a kettle ta zuba kamunfari
da lipton sosai take girke-girke ta zuba wake a
ruwa shirin kosan safe ta kwaso dankali ta fara
ferewa.
Farin ciki ya cika mata ciki sai hamda take yi.
Suna shigowa kuwa su Goggon Mama suka barke da oyoyon Yaya, ba a jin na wani ita da Badi'atu.
Ba wanda bai rungume Yaya Nabil ba, Hajiya Mama kam! Wuka ta yadda ta sunkuci baby tana fadin "Oyoyo da zuwan Amaryar Alhaji."
Suka wuce falo ya nemi wuri ya zauna yana fadin "Oyoyon ya ishe ni." Goggon Mama don Allah ku bar ni na huta.
1291Shafi.
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Badi'a ta ce, "A'a Yaya wallahi bai isheka
ba bari ma ka gani ta zauna a gabansa ta cire
masa takalmi ta cire masa safa ta mike tana
cire masa suit din shi tana fadin.
"Ka gaji ya ya bari ka ma Antinmu a cire
miki kin gaji." Ta girgiza kai alamun bata so.
Ita kam! Goggon Mama firji ta wuce taje ta
dauko ruwa da lemuna da kofuna ta kawo ta
koma ta kawo dambun nama.
Hajiya Maman ta shigo tana fadin,
"Sannunku da hanya ya gajiya?" Ya sauko ya
durkusa ya gaishe da Hajiya Maman sosai yana
fadin "Mun same ku lafiya?" Ta ce, "Lafiya
lau ubana, ka same mu.
Ita kam Maijin sai da Hajiya Maman ta ce,
"Maijidda ya hanya?" Sannan ta yatsina fuska
ta ce, "Da gajiya."
Badi'atu da Goggon Maman suka kyalkyale
da dariya suka fada da yin wata irin shewa
suka tafa.
Hajiya Maman ta kore su ta ce, "Ashe ku ba
mutanen arziki ba ne, zaku yi mana shewa a
wannan daren?"
1301Shafi
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
13 Badi'a ta ce, "Ai duk a cikin happy ne.
Hajiya Mama ta ce, "To maza aje a yi ma יי
yaran nan wanka, a canza musu pampers."
Kowacce ta kama daya, suka tafi yayin da
Hazif ya ringa shigo da kayansu yana jibgewa
a dakin Hajiya. Ta ce, "Maijidda shiga kiyi
wanka ki huta kin ji?"
Dakin su Badi'a ta shiga, ta ce Hafizu
wannan Jakar bakake guda uku nawa ne,
ragowar kuma nasa ne.
Don Allah mayar su mota ka kawo mini
dayar. Ya ce, "To ba matsala." Ya mayar ya
kawo wadda za su canza kaya ita da 'ya'yanta.
Idan ka gansu abin sha'awa, amma rashin
sakin fuska yasa sun zamo wasu abin kyama,
don ki suka yi a wanke su sai ita ce tayi musu
komai da kanta.
Ita kam! Hajiya zan ce suke yi ita da danta,
irin na bayan rabuwa, su tona dadi su tona
wuya.
Ta ce, Muna nan muna hakuri da rayuwa.
Nabil ya ce, Ai fa na gani kam! Har jikin Asuba.
1311 Shfi
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
A nan kuma da ya dawo bai shigo ba can
sashen Alhaji suka yi sai da ya masa fada
kamar zai doke shi sannan kuma suka dore da
zance irin na da da mahaifi.
Ya ce, Yanzun kuma yaushe za ka koma?
Ya ce, Hutun karshen shekara kenan tsawon
wata biyu, ya ce to akwai gidana a Na'ibawa
an gama komai ya za a yi?
Yaya Nabil din ya ringa sosa kai yana
dariya ya ce, "To Alhaji ayi ciniki kawai."
Alhajin ya ce, "Daman cinikin ya kamata ayi
(up stiar) ne sashe uku ne a cikin gidan yana
kyau sosai.
Wurin parking ma sai ka faka mota biyar,
shida. Ya ce, To na gode Allah ya kara girma
Alhaji ya ce Amin Ya Allah.
Kwana biyu ana shirye-shiryen biki,
angwaye sun iso. Hidima sai wanda ya gani,
ranar kamu za a yi party (sisters day).
Badi'atu kwalliyar da tayi sai ka ce ita ce
amaryar, sai kamshi take yi duk shirye-shiryen
da aka yi ma Amare.
Tana wurin saida aka yi mata itama, dilka
da halawa, da lalle. Ummi Farida kam tunda
132 1Shafi
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
aka shirya ta sai ya zamto can sa'id ya rasa
sukuni ya tare ta da hirar soyayyarsa wani irin
tattali da kauna.
Shi kam Ya Munir bai shigo gida ba sai
karfe biyar ya gaji lis don tun ranar da suka iso
bai huta ba yana shirye-shiryen biki yadda za
su kayata shi.
Lokacin da zai shigo kuma Gimbiyar tayi
bacci ga kunyar Hajiya Mama da ta kama shi a
kwanakin nan gaba daya jin kunyarta yake yi.
Ba ya iya hada hanya da ita, balle ya yadda
su hada ido.
Don haka yana shiryawa cikin less wani irin
mai kyau da tsada (pink colour) yana takunsa
na kasaita, sai kamshi yake yi.
Ya duba agogo ya yi tsaki. Bashir abokinsa
ya iso inda ya tsaya ya ce, "Ummi Farida da
Sa'id fa sun wuce tuntuni."
Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ai ka san ita
Madam din tawa yangar tsiya." Suka yi dariya
ya ce, "Kar dai ta 6ata mana lokaci."
,Ya ciro wayarsa yana nemanta ya ji wayarta
a kashe ya yi tsaki ya ce "Ina zuwa.
133Shafi
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Duk da gidan akwai taron mata sai da ya
shiga har dakinta sai a lokacin ta fito a wanka,
shafe-shafe take yi.
Tayi kyau sosai ganinsa yasa ta dauki
kayanta ta shiryo tsaf a toilet din sannan ta fito
irin kayansa itama ta sanya kallo daya ya mata
ya kawas da kansa don tun shigowarsa ya ganta
yasan lalle ya mallaki mace mai kyau.
Ya mika mata hannu ta kama amma sai ta
kauce ma hakan, ta dauki jakarta 'yar post
mahadin takalminta fari.
Ta wuce gaba ya biyo ta kamar. ya ce ya
fasa fita party din saboda kawai zai gane masa
matarsa.
Ya karaso ya rike hannunta tana son
kwacewa ya rike da karfinsa har suka fito
wurin motoci.
Yaya Nabil ya gan su a kofar fita, sai kunya
take ji tana son kwacewa. Ya ce, "Goggon
meye haka? Ai kauyanci kenan." Ya Munir din
ya ce, "Ai ita a nan tafi auki."
Ta bude musu mota suka shiga, don shi
Munir maganar ma da kyar yake yi, shi kadai
yasan halin da yake ciki.
1341al
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Don wata irin muguwar sha'awa da ta rafke
shi ya ce, "Wai kin san na dawo?" Ya fada
cikin muryar rada.
Ta daga ido ta kalle shi ta sunkuyar da
kanta ta ce, "Nasan ka dawo mana, ka neme ni ne?"
Ya sunkuya yana leken idonta, ya ce "Na
neme ki mana, kin kashe mini waya kanwata
ba ki san halin da nake ciki ba ne da na ba ki
tausayi."
Murmushi ta yi ta ce, "Ai kai ba abin tausayi ba ne." Ya girgiza kai ya ce, "Kе се baki san ni abin tausayi ba ne, amma ni nasan
ni abin tausayi ne.
Ina azabtuwa amma shi ne ki ka boye ma
ganina ko?" Ta girgiza kanta ta ce, "To kai ma Yaya wallahi." Ya ce, "Wallahi me?" Ta се,
"To garin da za ka maye ka ke aike?"
Ya ce, "Eh! Lalle haka ne mai sona, ba sai
nayi aike ba, Allah ya bar kauna, ya kai ni
wannan gari da aka hana ni aike."
Suna isowa wurin party har wurin zamansu
bai saki hannunta ba, suna high table don
Farida da Sa'id tuni sun kame a kujera abinsu.
135 Shafi
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Sa'id din tun daga shigowar su ya zuba
musu ido sosai, Amaryar Munir din ta dauke
hankalinsa da wata irin sha'awa.
Bai taba ganin Zainab din babu hijabi ba,
sai yau da ya kare mata kallo tun daga nesa.
Gaba daya sai ya raina amaryarsa, ya ji shi
daman tun farko Zainab din ya zaba idonsa
akan hips dinta har ta zauna bai saurara ba.
Sai da Munir din ya dungure shi ya ce,
"Wai ga ka ga amaryar taka me ka ke kallo?"
Ya saki ajiyar zuciya ya ce, "Kai dai bari
abokina, ina tunanin abu ne wallahi." Ya се,
"Nima Zainab ce ta bata min lokaci, tana can
tana yi mini yanga.'
Sa'id din ya dubeta ya ce, "Barka da
yamma Yayarmu."
Murmushi tayi daya daga cikin tsadaddan
murmushinta, sai ma ya sake shagala.
Ta ce, "Lafiya lau kanina." A nan kuma sai
da Munir din ya dungure shi ya ce, "Badi'atu
ce da rikicinta wai itama a nan zata zauna gefe
can isowa.
1361Shafi
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Tana zuwa kuwa ta zauna a kujerar kusa da
Ya Nabil, don dama da shi da matarsa za su
zauna bata zo ba.
Shi ma Yaya sai ya zauna to baya son
zaman shi kadai don haka bai hana Badi'atu
zama ba, suka dore da hirarsu.
Lokacin da Maijidda tazo babu wurin zama,
Badi'atun kuwa ta samo yaga Nabil da hira
yana tambayarta.
"Ni Badi'a banga saurayinki ba?" Tayi
murmushi ta kallo Zainab ta ce, "Ko Zainab ta
yi maka gulmata ne?" i
Ya yi dariya ya ce, "Gulmar me? Ko ba ki
da gaskiya ne?"
Ta sake dariya cike da shagwaba ta ce, "A'a
ni wallahi Yaya yarinya ce ban fara kula maza ba."
Ya yi dariya ta ishe shi ya ce, "Ba kya
kallon kanki a madubi shi yasa ki ke kiran
kanki yarinya.
Amma ni kam ina ganin girmanki, kalli kirjinki fa amma ki ce ke yarinya сe.
137 Shafi
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Kanta lullube ta da sauri ta mike zata bar
wurin. Ya riko ta har gwaggwaronta yana faduwa.
Ya dauko ya dora mata abunta akan ta ya
ce, "Dole ki zauna mu karasa hirarmu, jiyama
tun bayan sallar azahar ina ganinki ba ki yi
sallah ba, amma ki ce duk ba ki girma ba? Na
nawa kuma girman?"
Cikin jin kunya ta ce, "Don Allah Yaya
sakar mini hannu kaga Anty Maijidda can tana
kallona."
Ya kalli inda take nuna masan, ya yi
murmushi ya ce, "To meye don tana kallona?
Ke kina tsoronta ne?"
Ta langabe kai ta ce, "Don kaga ni ma
amare da angwaye suna faman rawa bari naje
nayi musu kari nima na D.J ta a can din."
Yace, "A'a ba za ki yi rawa ba, ai filin yara
ne ke kuwa ai na gane kin girma." Tilas ta
sunkuyar da kanta ta ci gaba da rokonsa.
9% Ya ce, "Muje kiyi kari, amma ban da rawa.
Ta mike yana fadin "Ban ga amfanin irin
wannan dinkunan da ku ke yi ba.
138 Shaf
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Wallahi tun suna birge ni sun fara ba ni
haushi, yanzun idan mun je wurin likin nan
kallonki za a ringa yi." Ya fada yana mata
wani irin kallo da sai da kunya ta kama ta.
Ta mike ya dora a bayanta, syuka je yin liki. Sosai ya lika kudi, babban Yaya ya fitar
da su kunya.
Badi'atu kam Yayan ta yi ma likin yayin da
shima ya juyo ya mata nasa likin biki ya koma kansu.
Don gaba daya Hall din ihu aka kwasa,
kowa sai farin ciki yake yi a families din su don shi Ya Nabil din rike hannun Badi'atun ya yi, yana rawa cikin wani irin salo.
Ita kam bata rawa sai wata irin rausaya da ta
ringa yi mai birge shi, ai fa gaba daya
angwayen suka juyo suke masa liki da su da amarcinsu.
Yayin da gaba daya families din kowa ransa
ya masa dadi, don yadda matarsa ta dauki girman kai, da wani rashin mutunci da wulakanta mutane.
Ta dawo a Turai abin sai wanda ya gani.
139 Shari
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Don kowa yake farin ciki da wannan
mu'amala ta Badi'atu da Ya Nabil, don su
Nabila da Anty Mairo sai faman 6aras da kudi
suke yi a liki da take rawa.
Biki bai tashi ba sai sha biyu da rabi na
dare, don Badi'atu ranar a zoo road suka cashe.
A can suka kwana ita da Amare, washegari
Asabar daurin aure. Tunda sanyin Asuba ake shirye-shiryen tafiya Soron Dinki daurin aure.
Don yau wani irin go slow ake a Kano,
kowa ya san families din Osese ana biki sai
motocinsu ne ke faman kaiwa da kawowa.
Hajiya Sa'ade idonta a kan Ya Nabil, yana
shiga yana fita yana kiran Badi'atu, yana mata
zance yayin da Hajiuya Sa'a ta kalli Hajiya
Maimu ta ce, "Yaron nan ban san abin da yake
nufi ba.
Hajiya Maimu ta ce, "Wa ya san abinda
yake nufi? Ke ni fa bana damuwa maza dai ya
mata ciki naga karyar zumunci."
Wannan zance karaf! A kunnen Badi'atu.
Ta juyo ta kalle su ba ta tanka ba.
Hajiya Sa'aden ta ce, "Oh! Su Badi'atu an
yi girman doya.
140shass
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Yau auran kanwarki amma ke ko kunya ba
kya ji ko?" Tayi tsaki ta ce, "An yi girman
banza, har kanwarki ta riga ki aure." Ta се,
"A'a ba komai wallahi don ta riga ni aure ba
matsala.
Ai na samu mai yi mini ciki a gidan ma ba
sai da aure ba." Ta wuce su kowanne yana rike
da baki cike da mamaki.
Hajiya Maimu ta bi ta da kallo. Ta ce, "Kin
ga balagaggiyar yarinya?" Hajiya Sa'ade ta ce,
"Za ta ga balaga, ganin idonta wallahi, donni
ba a taba ni a zauna lafiya.
Shirin da na musu gaba daya sai na tarwatsa
su a kan wannan diyar tawa guda daya, wallahi
nafi karfinsu da shekarar su nawa ba su ga Nabil din ba?"
Hajiya Sa'ade ta fada cikin zolaya ta ce,
"Za ki kashe kudinki ne kawai, don wannan
mutanen asiri ba ya kama su.
Kina kallo yadda Hajiya Mama ta gagare
mu a rayuwarta, matar nan kin san kuwa akwai
karya tambaya iri-iri, shegiyar muna tufka tana 99
warwarewa.
141Shafi
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Suna cikin wannan hira ta kace-nace,
Marokiya ta shigo bakinta dauke da bututun
gaa tana fadin.
"Aure ya dauru, alherin Allah! Na shigo
naci arziki na bar arziki a mazauninsa.
Allah ya yadda auren BADI'ATU DA
YAYANTA NABILU.
AUREN
SA'IDU.
FARIDA UMMITA da OGA
Alherin Allah Ya sauka, MAI SUNAN
MALLAM DA GOGGON MAMA, aure ya
tabbata na shigo naci arzikin yara ma su sunan
iyayensu.
Zuri'ar Soron Dinki tun daga can na taho na
gangaro na taho naci arziki.
Allah Ya jikan Goggon Soron Dinki,
arzikin gado ba taka-haye ba, gidan tsohon
kudi na bakin Kurmi, ku ne Kano, Kanawan
asali a bani domin 'ya'ya 'yan albarka.
Ita dai Hajiya Sa'ade kujera ce ta zame mata
ta zauna dagwash! Cikin shirgin wanke-wanke
tana faman salati.
Ita kam Hajiya Maimu haka ta ce, Sai kiyi
da gaske, don kin san matar nan da gaske take
142
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
yi ba da wasa take yi dammara ta daura zata
yake mu."
Nima Jamila birona na ajiye zan yi sallah
naji ya zata kare?
Don haka mu hadu a cikin littafi na uku da
yardar Allah.
Taku;
'Yar Mutan Gumel Matar Bahadeje.
07032987315
143 IShafi
Zumunci Dangin Kauna 2
Jamila M. Danfajo
MAHARAZU
BOOKSHOP
SANARWA! SANARWAII SANARWA!!!
Albishirinku Makaranta Littattafan Hausa, ma
su sayen daya ko sari. Domin samun littattafan
Hausa kowanne iri, da na Turanci da na Koyon
Girke-girke kala-kala, da na lemuka kala-kala,
da kuma MUJALLU na fina-finan Hausa a cikin
farashi mai sauki, to maza ku garzaya zuwa
shagon MAHARAZU BOOKSHOP, wanda ke
GIDAN UMMA BAYERO, da ke kusa da
STANBIC IBTC BANK, tashar kasuwar RIMI
kusa da ASIBITIN MURTALA.
Bayan haka kuma, muna buga littafi a kan
farashi mai sauki, kuma a cikin kankanin lokaci
tare da yin aiki mai inganci.
Domin neman karin bayani, za ku iya
tuntubarmu a wadannan lambobi kamar haka:
08036175492, 08099199121, 08092828378
SAI KUN ZO!
144 ShaÍi
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 13