take harkokin
6ata maza da mata ba wacce ba ya yi.
Don da shi da K.B sun yi kaurin suna a
family din su. Dan Yaya da kanwa.
Domin idan za ka tambayi iyayensu maza to
wannan yaran sune matsala a families dinsu.
Don bai yi sati ba aka kashe rigimarsa da
yarinya 'yar shekara shida da ya Gatata, sai da
ubansa ya biya tara ta makudan kudade masu
yawa.
Labari daya ne Yayar Babansa ta kira shi a
waya ta ce duk in da Goggon Mama take ka
neme ta ka ce kana sonta, don itama nan Nuri
din K.B yana zuwa.
Ba su isa ba, Hajiya Rabi'a da Yayarta wai
auran gida za su yi ma 'ya'yansu, ni kuma idan
ba a aura maku yaran ba sai dai ba na numfashi a
duniya, za su gani tuggu kala-kala ni da su mu
buga."
Don haka yana kashe waya ya nemi lambar
Goggon Maman ya buga mata, ko amsa bata ba
shi ba Munir ya kwace ma wayar.
71 Ishafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Don haka dawowar su Munir din daga Sallar
Isha'i sai kuma gasu nan sun shigo.
Hannu kawai Hafiz ya dagowa Nuri ta tashi
ta bishi suka fice, Munir din bai iya magana ba
don gaba daya a cikin damuwa yake.
Ya zauna gefen Goggon Maman cike da
tausasa murya, "Zainab waye ya kira ki a waya?"
Tayi shiru, ya sake tausasa murya. Ya се,
"Magana fa nake yi da ke, ko ba kya jina?"
Ta kasa kallonsa, don daman ita bata iya daga
idonta ta kalli nasa idon, balle yadda ya zo mata
a sanyinsa, ga wani irin kamshinsa da
kwarjininsa ya cika dakin.
Duk wani tsaurin ido da rashin kunya da take
yi masa a lokacin yana mata wasa ne, a yanzun
ba wasan a fuskarsa.
Wani sonsa da kaunarsa ne ya lulluбе
zuciyarta, ta kasa magana sai ma kirjinta da yake
dakan tara-tara.
Wayarsa da tata ya mika masa ya ce, "Ungo
ki kira lambar a wayata.
Ta kalle shi a sanyaye ta ce, "Ni ban san
waye ya kira ni ba." Ya ce, "Eh! Naji ki kira
lambar." Tayi shiru, ya daka mata tsawa jikinsa
yana bari ya ce, "Ki kira na ce." A sanyaye ta
72 1
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
bude wayoyin ta ringa shigar da lambar a
wayarta, sai da ta gama sannan ta kira wayar.
Abin mamaki sai ga suna ya bayyana a
wayar, alamun kira ne ya bayyana a wayar fayar
tana faman (Ringing).
Yayin da sunan Bro Suraj ya bayyana a
wayar, gabanta ya buga.
Ya ce, "Ai kin gani ko?" A sanyaye ta amsa
"Eh!" Ya ce, "Waye?" Sai da ta kashe waya
sannan ta kalle shi ta ce, "Brother Suraj na gidan 99
nan.
Ya ce, "To ni ban ma san lambar waye ba, na
kira ne na tambaya waye don ko za a aurar da ku
bai kamata mu bari kowane kwashe-kwashe
yazo a aura muku shi ba.
Shi ne yasa ki ka gani ina damuwa idan na
gan ku da samari barkatai ina hanawa, amma
tunda shi wannan ki ke so ai shi kenan bani
wayata."
Gaba daya ma jikin Goggon Mama rawa yake yi, duk wata tsiwa da ta shigo da ita gidan ta kawas da ita gefe daya.
Don gaba daya a cikin damuwa take. Ta kalle shi muryarta na rawa alamun kuka.
73 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Ta ce, "Wallahi ba na sonsa, ni bai ma taba
kirana ba sai yau, ba wani abu a tsakanina da
shi."
Fuskarsa ba annuri ya ce, "Ba ni wayata na се
miki, maras mutunci kawai.
Daman ai naga kina mini wata irin rashin
kunya, ashe dai daman da saninki ko? To wallahi
ki shirya, in dai ni ne...'
Ragowar maganganun suka makale a
bakinsa, ya fisge wayarsa ya fice, yayin da ita
kuma Goggon Maman ta fashe da kuka.
Ta fada gado bata taba ganin tashin hankali
irin wannan ba, tunda take a rayuwarta. Ta jima
tana kuka.
Har Ummansu ta shigo ta ce, "Uwata meye
ya faru? Tashi ki gaya mini." Ta mike tana
faman kuka.
Ta tashi ta zauna cike da shesshekar kuka ta
zayyane ma Umman komai.
Hajiya Rabi'a tayi tsaki ta ce, "Aniyarsa ta
bishi, insha Allahu ke ba matarsa ba ce. Goge
hawayenki, duk mugun halinsu insha Allahu ba
za su yi galaba a kanmu ba."
Hafiz suka shigo suna faman nishadi da shi
da Nuri, a kofar dakin ya tsaya yana fadin.
74.1shafi
Zumunci Dangin Kauna
"Umma sai da safe."
Jamila M. Danfajo
Та се, "Тo ka gaishe min da Antin nawa,
goben ka taho mini da kayan uwata ko set goma
zamu dan kwana biyu tunda suka yi candy bata
zo mun huta ba."
Yaya Hafiz din ya harareta ya ce, "Mun huta
wallahi Umma, kwana biyun nan daman ta hana
mutane sakat! A dakin Mama tayi zamanta a nan
munafuka."
Umman tayi dariya ta ce, "Kyale min uwar
nan tawa a cikin matsala take."
Sai a sannan ta zayyane ma Hafiz halin da
ake ciki, ya yi murmushi ya ce, "Ah haba!" Ya
ce, "Wallahi kuwa." Ya ce, "To ai ba su isa ba
wallahi.
Komai zai faru sai dai ya faru, mutum yana
so a ba shi auran kintsattsiyar mace me ya hana
shi ya zamo nutsattse?
Wannan ma ai zance ne, idan don wannan ma
ki daina kuka, ba zai yiwu ba."
Ita kam ba wannan ne damuwarta ba,
damuwarta daya da yadda ran Yaya Munir ya
baci.
Kusan kwananta uku bata sanya shi a idonta
ba, ko cikin gida ba ya shigowa, ko abu yake so
75 |shaf!
E
1
S
I
1
1
t
1
i
t
ر
f
2
t
1
2
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
sai dai ya yi waya a kai masa, duk da Umman ta
gano fushin da yake yi amma ba ta tanka musu.
Ranar Juma'a an sauko daga Masallaci, sai
kawai ga Suraj ya shigo, da alama ranar ma a
kwale yake.
Yana faman tangadi yana layi ya shiga falon
Umman, a lokacin suna zaune da Nuri, suna
faman koyon dinki, don ita Nuri bata iya dinki
ba, yayin da Goggon Mama ta iya, tana koya
mata suna yanka.
Suraj din ya shigo hannunsa da fulawar
(Rose) irin dai wanda ake yin (gift) din soyayya,
yana fadin.
"Goggon su, don mu ba Goggonmu ba ce
Goggon su ce, kina sona?"
Ita dai sai ta kuma matsawa a kusan sa yana
miko mata tana matsawa, ganin ba zai fasa ba
yasa ta amsa a tsammaninta idan ta amsa zai
kyale ta.
Tana amsawa shi kuma Yaya Munir yana
sako kai a falon, ganin hakan ya yi saurin
juyawa.
Ita kam Goggon Mama ba ta ma san ana yi
ba, da kyar dai ta samu ta lallaba shi ya fice.
76 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M Danfajo
Amma da Nuri ta ce "Yaya Munir ya shigo
yanzun ya fita." Sai tayi watsi da fulawa (Rose)
din ta fashe da kuka.
Nuri ta ce, "Daman fa na gaya miki kishi ne
ya kama Ya Munir, yana sonki wallahi, don
yanzun ma ba ki gani ba yadda ransa ya бaci ya
juya ya fice a falon."
Cikin kuka ta ce, "To ni Nuri ya zan yi da
raina? Ya ake so nayi'? Ni gara ma na bar gidan
nan ko na samu kwanciyar hankali a rayuwata."
Ya ce, "Eh lallai kam! Wannan abun Ya Suraj
ya yi yawa, ko Umma tayi masa magana, ko
kuma ki tafi din."
Dalilin shigowar Umman suka yi shiru.
Ta kalli Goggon Mama ta ce, "Wai ke uwa
ban da kuka ba ki da aiki?"
Nuri ta ce, "A'a Umma dole tayi kuka, ba ki
gani ba fa abin da Ya Suraj yake shigowa yake
yi mata."
Umman jikinta da sanyi ta ce, "Zan yi
maganin abin, kwantar da hankalinki."
Kusan sati guda kenan da yin rigimarta da
Suraj, amma kullum sai ya shigo an yi fada zai
fice. Haka nan tsawon kwanakin da Ya Munir
bai shigo cikin gidan ba, don ko ganin cikin
77
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
gidan ba ya yi, balle ya shiga. Yayin da wannan
abun ya damu Goggon Mama, gaba daya cikin kwanakin ta rame tayi wani fiyat.
Umman ta ringa fada ta ce, "Wai uwata duk
maganar Suraj din ce ta maida ke hakan?"
Tayi shiru, sai dai hawaye ya yi ta zubo mata
saf-saf! Umma ta ce, "Allah Ya sawwake, bari
Alhajin ya shigo ai ba zai yiwu ba.
Jiya ma Alhaji Babba ya samu Alhajin gidan,
wai Kabir yana son Nuri, yana son a ba shi izini
ya fara neman aure.
Ban san ya suka yi ba, amma na gaya masa
Nuri Hafizu ke sonta tun tana J.S 3.
Don haka ya hakura amma ban san ya suka yi
ba, ya ce zai kira (meeting) yau Asabar anjima,
mai yiwuwa a shiga (meeting) din, don haka
kuyi hakuri komai zai wuce."
Ita kam Goggon Mama kamar ta ce, Ni
damuwata da Ya Munir ba ya mini magana da
daina shigowa gidan nan, don kar ya ganni,
iyakarsa harabar gidan.
Amma dai sai tayi shiru, don wata maganar ta
kuma tasowa. Nuri ta cc, "Ban gane ba Umma,
daman K.B din sona yake yi da yake faman bugo
mini waya?"
78
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Umma ta ce, "Can! Suka kulla
maganganunsu, sun bar Antin nawa da faman
rikici, tunda dai za a shiga meeting ai shi ke
nan.
Cikinn awa daya sai ga matan gidan Alhaji
Babba gaba daya an kawo su. Hafizu ne ya shigo
ya ce, "Duka kowa da kowa ya shiga dakin
meeting saboda an kawo kowa har 'yammatan
zoo road din da samarinsu da matan gidan.
Bayan bude taro da addu'a da Alhaji Babba
ya yi, ya ce, "Hajiya Magajiya da ke zan fara, ki
gaya mini maganar da ki ka gaya mini
shekaranjiya."
Cikin daure fuska tayi shiru.
Ya ce, "Magana nake yi da ke."
"To Alhaji wace magana ce?"
Ya ce, "Maganar auran Surajo da Goggon
Mama." Ta ce, "To ai haka na ce ban amince ba."
Ya ce, "Meye hujjarki na cewa ba ki amince
ba?" Ta ce, "Saboda 'Yata ce, ni na haife ta. Ina
da hakki wajen zabar miji, don haka ba za ta
aure shi ba.
Saboda na farko ba shi da kamalar da zan
dauki 'yata nutsattsiya na ba shi aurenta.
79|shafi
Zumunci Dangin Kanne Jamila M. Danfajo
Na biyu kuma, kowa ya sani ba shi da
kamala. Na uku kuma kowane mutum da abokin
aurensa, don haka da ya nutsu ba abin da zai
hana na ba shi auren Zainab ba. Don haka ya
sake tsari na fada aure ba zai yiwu ba."
Ita kam Hajiya Maimu kuka take yi tana
fadin "Ban taba ganin in da ake raba zumunci
ba, sai a gidan nan. Idan an yi wani abun ki ji
kowa cewa ko ba ki auri Alhaji Osese ba.
Kina da iko da 'ya'yansa don Alhaji Ahmadu
amma idan an zo maganar aure ki ce ba kya son
'ya'yanmu, haka ake rayuwa?
Kalli fa yadda ki ka hana auren Khuzaimatu
da Mai sunan Mallam aka hakura."
Can ita Hajiya Rabi'a ta hana auren Kabir da
Nuri, mune dai ba kwa so a cikin gidan nan da ni
da 'yar uwata da 'ya'yanta."
Falon ya yi shiru kowa yana sauraronta,
Alhaji Usman ne ya raba rigimar ya ce, "Wannan
duk ba maganar ku ke ba ce kuyi mini shiru.
Shi Hafizu da kansa ya same ni da maganar
Nuri, a take a wurin na ce na ba shi, amma ita
Goggon Mama ai bata da saurayi a family.
Kuma lalacewar Surajo ba zai hana aurensu
ba, ni na haifi Goggon Mama, don haka na baiwa
80 Ishat!
ご
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Suraj aurenta, kar wanda ya kuma kawo mini
99
wata magana sabanin wannan.
Hajiya Magajiya tayi karaf! Ta ce, "Wallahi
Alhaji ba zai yiwu ba, ni ban haifawa dan ganye,
dan kwaya, dan giya diyata ba.
Don haka duk wanda ya ce sai an yi auren
Zainab din da Suraj, to sai ya daura damarar
korata ni da ita a gidan nan, wallahi ba zan taba
yadda ba."
Alhaji Usman ya ce, "To kada ki yadda kin ji
Magajiya, idan ma don kin ga ina bin maganar
ki, wallahi ki janye ni nafi karfinki.
Ki sake rayuwa wallahi a kan ki raba mini
zumuncin 'ya'yana da na dan uwana komai zai
faru sai dai ya faru, amma wallahi na daina kyale
ki.
Sai an dauko maganar auren zumunci ku
ringa rusheta ke da Rabi'a, to a yanzun a shirye
nake."
Alhaji Ahmad ya ce, "Ba za a yi haka ba, shi
yana son nutsattsiyar matar aure me yasa bai
zama nutsattsen ba, ai tana da gaskiya."
Alhaji Babban ya ce, "Ai maganar banza take
yi, idan na biye ta aure uku kenan ta hana a
81 ha
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
zuri'ar nan, don haka auren Suraj da Goggon
Mama ba zan fasa ba."
Alhaji Ahmad ya ce, "A tambaye ta idan tana
da wanda take so ko?"
Alhaji Usman ya ce, "Idan ma da wanda take
so ai ni bata gaya mini ba, kuma bai zo ya gaya
mini ba.
Don haka kuma ragowar 'yammatan da
samarin kowa ya fitar da matar da yake so,
aurenku saba'ar watan gobe ne ba zan fasa ba."
Hajiya Magajiya ce ta fara barin wurin cike
da fusata, Alhajin ya ce, "Ina Zainab din?"
Fuskar nan tata sharkaf! Da hawaye ya ce,
"To meye abin kuka? Insha Allahu auren Suraj
alheri ne a gare ki, kin ji ko?
Da izinin Ubangiji Allah zai kawo masa
shiriya, duk wannan munanan halayen insha
Allahu, Allah zai canza masa su izuwa kyawawa.
Dan uwanki ne, ke ma ki ringa yi masa
addu'a kin ji ko?" cikin muryasr kuka ta ce,
"To."
Aka rufe ero da addu'a, Munir ne a bakin
kofa, don haka shi ne ya fara fita.
Bai taba jin tashin hankali irin na yau ba
tunda yake, a ransa ya yi tsammanin zai iya
82|shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
hakura da Zainab din, amma gaba daya ji yake
yi zai mutu.
Ciwon son Goggon Mama gaba daya ya
maida shi tamkar zai yi hauka.
Ya kwana ya yini yana sintiri a tsakar
dakinsa, damuwa ta yi masa yawa. Cikin 'yan
mintuna ya fede ya yi wata irin rama, gaba daya
ya zama abin tausayi.
Yayin da itama Hajiya Magajiya din ta shiga
damuwa, ita da Zainab din, don ita Goggon
Maman kwana take yi kuka da sallah, ta rasa me
zata yi ban da addu'a.
Itama ramar tayi, ta yi siririyar fuska. Bа
auren Suraj ne ya dame ta ba, auran mutumin da
idan ta aure shi, auren Munir ya haramta a gareta shi ne kawai damuwarta.
So, so masifa ne, cin abinci ma bata iyawa,
ban da kuka ba abin da take yi, ga habaici na
rashiń mutunci da Hajiya Maimu take faman yi
musu.
Wai ace ba a son dan ganye to ai me cikin
haihuwa ba ya kin dan ganye, dan kwaya, don Kaddara ba wanda bata samu.
Yo ma shi aure idan Allah ya baka ya za ayi? Ai sai dai mai ficewa ya fice auren nufin Allah
83shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
ne, idan zaman zama, idan tafiya tafiya, karyar
banza. Ai ni Alhaji ya yi mini maganin isar
banza.
Kwana biyu tana faman habaici, yayin da
Hajiya Magajiya ta ce, "Ni kuma idan ina
numfashi wallahi wannan auren ba za a yi shi ba.
Kina gidan nan ina gidan nan wallahi ba gudu
ba ja da baya mu zuba ni da ku shege ka fasa,
wallahi ba za a yi ba."
Duk wannan maganganu da suke yi a kunnen
Alhaji Usman.
Ya fito zai wuce kasuwa ya tsaya shima ya
katse wulakancin sa ya ce, "In dai 'ya tawa ce,
wallahi ba zan fasa bai wa Suraj ba.
Don duk duniya ba ni da wanda ya kai
ubansa, ba ni da wanda zai taimake ni ya
taimaka mini sai ubansa sai Allah da ya halicce
ni.
Mu biyu rak! Iyayenmu suka haifa, don haka
ba ni da wanda yafi 'ya'yansa a duniyar nan.
Idan kuma Zainab 'yar halas ce ba shegiya ba
ina son ta nuna mini, idan kuma shegiya ce kafin
bikin nan ta nun. mini ita din shegiya ce.
Don haka ni da ku ina jiran mai fasawa, don
99 mutuwa ta ce kawai zata hana auren nan.'
84 1shafl
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Itama kuwa Hajiya Magajiya din haka ta ce
masa, ta daga labulen dakinta ta ce, "Lallai kam!
Nima sai dai idan mutuwa nayi.
Wannan kuwa ka dauki Zainabu Abu ka
sanya a dakin Surajo na yadda, amma muddin
ina numfashi wannan auren ko ka daura shi sai
ka warware shi, mu zuba ni da kai.
Ai biyayya ba hauka ba ce, ni ina maka
biyayya kai kana yi ma Maimu da kanwarta, to a
kan na hada zuri'a da wadannan mutanen
wallahi gara ko me zamu yi muyi ni da kai.
Amma auren mugunta babu shi don ba don
Allah za a yi auren ba, mugunta ce kawai.
Don haka na fada da kai da Maimu da Binta
karanku bai kai sille ba."
Shigowar Munir ne ya raba fadan manya, ya
raka Alhaji mota ya dawo ya ringa lallashin
Hajiya Mama.
Shima Hafizun lallashin Hajiya Mama ya
shigo ya yi, ita kam Goggon Mama tana jin shigowar Munir din ta fada Toilet din cikin daki
ta kulle kanta tayi ta kuka sosai kamar ranta zai
fita. Saboda ganin Munir wani fami take kara yi
ma kanta, shima kuma ya daure ne kawai amina
ba don ya hakura ba.
851
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Sai da kura ta lafa sannan da yamma ya yi shirin barin gidan. Ya ce, "Daman fa zuwa nayi
na gaya miki Hajiya Mama, gobe Yaghana da Yayarta za su zo Kano aure, ta ce za ta zo ku gaisa."
Tayi murmushi ta ce, "Allah Ya kai mu." Ya
ce, "Amin Ya Allah."
Hajiya Sa'a itama irin nata habaicin da take
yi a tsakar gidan daban.
Wani lokacin ta ce, "Duk fa don a kan auren
Nabil da Jidda ne ake kin auren dan kishiya da
'yar kishiya a gidannan, mu kuwa mun ci dubu
sai ceto."
Hajiya Maimu ta ce, "Uhum! Ai ni na sani ko
kyauta aka yi musu ai a kudin dansu ne, ba don
Allah ba ne ni ai na gane."
Ita dai Hajiya Magajiya bata shiga harkarsu,
don ta kanta take yi da 6acin ranta, balle da gari
ya waye ta tashi da hidimar tarban Yaghana.
Yayin da Goggon Mama ta tashi da wata irin
kasala da faduwar gaba maras adadi, ko wanka
sai da Hajiya Mama ta zazzageta sannan ta tashi tayi. Ba ir ifi tayi kwalliya cikin wani material
mai dan karan kyau, jar kala ne kuma cotton ne
da fulawoyi kala-kala.
86 1
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Tayı kyau tana kwance a gadon Mama duk da
ta rame amma dai idan ka ganta ka san
kyakkyawa ce.
Ta gyara gashinta sosai ta daure da jan ribon,
idan ka ganta zaka yi tsammanin tayi jinyar
shekara, ga wanda ya santa.
Misalin karfe biyu gidan ya kaure da murnar
zuwan Yaghana, gaba daya 'yammatan gidan
suka tarbo ta dooо!!
Yara suka direta falon Hajiya Mama, tana
faman jin kunya.
Ba laifi Yaghana a fili bata da kyau kamar a
waya da suka ga hotonta, Yayarta har da
'ya'yanta guda biyu.
Shima uban tafiya a rame yake ba sosai yake
fara'a ba, bakin gilashin da ya sanya a idonsa shi
ne ya kara masa kyau, ya kuma 6oye yanayin da
yake ciki.
Hajiya Mama kam sai nan-nan take da
surukarta, ta cika musu carfet da kuloli kala-kala,
da kayan sha nau'i-nau'i, sai da za su ci abinci
sannan falon ya ragu.
Shima fita ya yi ya ba su wuri, sai da suka
gama cin abinci suka sha sannan Hajiya Maman
ta kwalawa Goggon Mama kira ta ce, "Fito ki
87 shuti
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
gyara wurin nan." Yayin da Yaghanar ta се, "A'a Mama zan gyara." Ta fito suka gyara wurin
tare duk dai tana yi tana taya ta.
Sai da ta gyara ta sanya Room freshner na
(Aroosa) sannan ta gaishe su. Suka yi zaman
kurame.
Sai da maman ta shigo suke hira sama-sama
cike da kunya take bata amsa.
Ita kuwa Yayar tata tasha mur! Bata magana,
a haka matan gidan suka leko aka gaisa.
Shigowar Ya Munir ne yasa Maman ta shiga
daki, suna ganinsa suka yi haramar tafiya, yasa
hannu ya dauki 'yar karamar diyar Yayar tata ya
leka ya ce, "Hajiya Mama za su tafi."
Та се, "То, ina zuwa." Ta dauko ledar da ta
zuba abin da zata bata, ta mika wa Goggon
Mama ta ce, "Ungo raka su mota sai ki ba su.
Tilas ta ware mayafinta jar kala, kanta ba
dankwali ta lullußa shi, sannan suka yi sallama
da Maman da matan gidan.
'Yammatan suka raka su mota, ana faman
raha kowace daga dakinsu ta fito da alheri, don
Hajiya Sa'a kući ta bayas dubu goma.
Yayin da Hajiya Maimu ta bayar da kayan
shafa, da turmin atamfa Holland ta ce, "Ai ni
88 |shafi
Zumunci Dangin auna Jamila M. Danfajo
wannan yarinyar tayi min daidai, dole na
kambamata.
Don ita ce ta hana wannan mai gurza-gurzan
idanun ya ce yana son Goggon Mama, Allah dai
shi raka taki gona."
Ya bude ma Yaghana mota ta shiga mazaunin
direba, ya rufe yana fadin.
"Kiyi tuki a hankali fa."
Wani irin kallo take yi masa mai cike da
soyayya. Ta ce, "Insha Allahu Hubbyna, sai ka
وو shigo." Ya се, "То."
Ya gewaya ya maki ma Yayar tata diyarta,
sannan ya bude gidan baya suka ringa sanya
ledodin hannunsu.
Sai a lokacin Yayar tata tayi magana. Ta ce,
"Har da wahala?" Ya ce, "Ba wahala ba ce,
alheri ne irin namu na 'yan asalin Kanawa."
Suka yi dariya.
Su Khuzaimat suna ta faman zolayarta, suna
shiga gida, shima ya kashe wayarsa ya shiga a
harabar dan wani fili da zai sadaka da kofar
shiga cikin gidan.
A nan ya iske Goggon Mama tana faman
kuka. Gaba daya jikinsa ya yi sanyi, ya rasa abin
da yake masa dadi. Shi kansa yasan suna shan
89 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
wahala, saboda soyayyar junansu da take faman wahalar da su.
Ya yi shiru yana kallonta, ya jima yana tsaye bata san yana wurin ba, sai da ya yi gyaran
murya sannan ta dago idonta suka hada ido.
Ta zabura zata shiga gidan, da sauri ya sha
gabanta. Tilas ta sunkuyar da kanta, idonta yana
zubar da hawaye ita kadai tasan ya take jin dafin
sonsa a ranta.
Kamar ta fito titi ta yi ta kuka, tayi ta ihu tana
gaya ma mutane abin da yake damunta. Tilas ta
hakura ta danne saboda idan tayi hakan tabbas za
a ce ta haukace.
Wata zuciyar ta ce mata 'To a ce na haukace
din mana, ba ma gara nayi hauka da wannan
halin da nake ciki ba, mutum ba ya tausayin mai
sonsa...'
Ya yi gyaran murya. Ya ce, "Muje dakin
Hafiz ki gaya min abin da yake damunki, muje."
Ta juya a sanyaye ta shiga dakin na Hafiz,
saboda bata da mafita idan ba hakan ba.
Ya maide kofar ya kulle ya zauna a bisa
carpet a gab unta da shi ke a kujera take zaune.
Ya ce, "Me yake damunki Zainab?" Tayi shiru.
Ya cire gilas din da yake a idonsa ya ce, "Me
901shafl
3
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
yake damunki? Kiyi magana mana ko?"" Ta
sanya mayafinta ta lulluße idonta ta ci gaba da
kukanta.
Ya ce, "Okey! Ba za ki fadi abin da yake
damunki ba ko?"
Ta sake fashewa da kuka. Ya ce, "Haba
Zainab! Kina son ki fasa mini zuciya ne?" Yana
magana a sanyaye. "Ya ki ke so nayi da raina?
Ni kin san halin da ki ka jefa rayuwata? Ko
so ki ke na fadi na mutu? Ki bar ni da abin da ki
יי ka yi mini mana."
Cikin muryar kuka ta ce, "Me nayi maka?"
Ya girgiza kansa sannan ya mike a tsaye yana
juya mata baya.
Ya ce, "Ai kin san ina sonki ko?" Itama a
tsayen ta mike cike da mamakin kalmar da ta fita
a bakinsa. Ta ce, "So? So fa ka ce? Kana sona ka
bar ni na shiga wannan halin?
Kana sona ka bar rayuwata tana garari?
Haka ake so?
Ban taba ganin irin wannan son ba.
So ko mugunta?
Kana sona ka bar ni rayuwata ta fada garari?
Kana kallo za a aura min dan giya? Duk ba
ka ce kana sona ba sai yanzu bikina sauran sati
91 Ishafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
daya? Ka hada iyayena fada? Da ka ce kana
sona yaushe iyayena za su yi fada?
Wannan ba so ba ne, yaudara ce. Ba zan taba
yadda so ka ke yi mini ba, yaudara ce shi ne ka
kulle ni a daki za ka cuce ni?
Haka ake so...?" Sai kuma kawai ta fashe da
kuka irin kukann nan mai nuna tsananin damuwa
da tashin hankali.
Shima idonsa ya kada ya yi jajir, kwalla ta
ringa fita, ya kamo ta ya rungume ta bisa
kirjinsa, tilas ta saki ajiyar zuciya.
Cikin muryarsa mai taushi ya ringa
lallashinta, ya zaunar da ita a kujera mai zaman
mutum uku, ya zauna a gefenta har numfashinsa
na bugun fuskarta.
Ya ce, "Ina sonki Zainab! Ina sonki Zainab!!
Son da ban san yawansa ba. na danne shi a raina
ya ki dannuwa, ki kalli kwayar idona so ne da ba
zai taba gushewa ba.
So ne da ba zai taba canzuwa ba, Goggon
Ummata! Ba mugunta ba ne so ne maras surki,
taimaka ki karbe shi, so ne na gaskiya, sai dai
idan ke ba kya sona.'
Sai ta fashe da kuka, duk da daman hawayen
bai tsaya a idonta ba.
92shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Tа сe, "Kar ka tambaye ni maganar so, ta
fada tana yaye lullubin kanta. Та се, "Kalli
yadda sonka ya maida ni tamkar ba ni ba, so ka
ke na mutu ka huta ai. Kalli yadda sonka ya
canza mini kamanni."
Ya ringa girgiza kansa ya ce, "Ya zan so ki
mutu? Idan kin mutu da wa zan yi rayuwa?"
Ta mike tsaye tana kara goge idonta, ta ce
"Magana ce mai girma ka gyarata, sannan kayi
tunanin muyi rayuwa tare."
Ya ce, "To tsaya kiji mana." Bata tsaya ba ta
wuce cikin gida da sauri. Dakin Mama ta wuce tayi kuka mai isarta.
Shi kansa a ranar tausayin kansa ne ya kama shi, da tausayin Zainab. Bai san tana yi masa
wannan son ba da babu mai hana shi bayyana
mata son.
Duk da Babansa ya ce ba za a ba shi mata a
families dinsu ba.
Ranar kwana ya yi cikin damuwa, don haka
ko shirin fita kasuwa bai yi ba, balle ya motsa.
Sai wajan karfe goma ya yi wanka, da ya yi wankan ma sai ya sanya jallabiya kawai ya sanya
turare ya fita. Cikin gidan ya nufa kusan kullum
rayuwarsa a gidan take, don haka idan ya shigo
93shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
sai ya gaida kowa sannan ya shiga dakin Hajiya Mama.
Yau ma hakan aka yi, sai da ya gaisa da kowa
sannan ya yi ma dakin na Hajiya Mama tsinke.
Tana can a kitchen tana ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 13