Share this page
nan. To wai ma daga tambayar ki sai ki bi ki tashi hankalinki, idan ba haka ba ne ki bar zancen mana ko? Sai kiyi ta kuka?" Cikin kukan ta tashi ta zauna ta ce, "Da wata nawa kenan ina cikin wannan damuwar ta dameka ne? Kawai a kan wani zarginka maras tushe za ka jefa ni a masifa? Ka kalli ramar da nayi ka kalli wahalar da na sha, duk irin kiyayyar da nayi ma Suraj din har ka ke tunanin zan iya hada jikina da wannan kazamin? Haka ake rayuwa saboda Allah? Kuma wayar da ka bugo din ka ce ka ji maganar namiji waye? Ni da Badi'atu ne da 951Sha11 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Falalu a mota zai kai mu unguwa na ce ya yi shiru alamun ina waya. Kuma tun daga lokacin yau wata na shida bayan kai mu unguwa ba na yadda shiga motar kowa saboda bacin ranka. Ga su nan 'yan zoo road idan an zo daukar su a Makaranta ba muje da mota ba ba na bin su, saboda namiji ne yake tuka su. Ni kuwa na gwammace na shiga tukin Badi'atu da na shiga motar wani, kuma rabon da na sanya Suraj a idona tun ranar da ya sara maka adda, har gobe ban ganshi ba. Tunda saboda shi ne muka taso gidan nan amma har ka ke darsa wa zuciyarka zargin zan kebe da shi muyi me?" Sai kawai ta sake fashewa da kuka. Ba shiri ya janyota jikinsa ya rungume yana faman lallashi. Ya ce, "Ya isa don Allah, kiyi hakuri na yadda laifina ne, don Allah ki yafe mini kin ji ko?" Ta janye a jikinsa da ba za ta iya jurewa yadda take jinta a kirjinsa ba, ya ce "Kin hakura ne?" Ba ta kalle shi ba ta juyar da kanta 96|Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo can gefe guda, ya ce, "Ina jin ki ki bani amsa?" Ta ce, "Amsa? Amsa fa ka ce? Ai ka baiwa kanka amsa, ni kawai na hakura da wata soyayyarka ta azaba, da tunda ka dora mini nauyinta ka dora mini wahala." Ya tausasa murya ya ce, "Ki taimake ni zancen nan ya wuce kin ji ko?" Tayi kamar ba ta ji shi ba, ta kyale shi ya yi ta magiya ko tankawa bata yi ba. Bai bar dakin ba sai da Badi'atun ta bar dakin sannan ya fice. Da sassafe kuwa yana dawowa a Masallaci ya fado falon ya gaishe da Hajiya, ya ce "Wannan ba ta tashi ba?" Hajiya Maman ta ce, "Ba ta tashi ba, ko bata sallah ne? amma Badi'a ta fito." Kunya ta kama shi, ya dai daure ya wuce. Yana shiga dakin ta kudundune a bargo ya janye bargon sai ita kuma ta rike ta sake gyara rufarta sosai, ya ce, Ki tashi ko na janye. Kin yi sallah ne ki ke kwance?" Ta bata rai tare da turo gaba, don idan ta tuna akan abin da ya wahalar da ita haushi yake bata. 97 Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ta ce, "Ka biya sadakina ne da za ka janye mini bargo? Ko kuma dai don ka maida ni maras kamun kai?" Ya rike baki yana fadin, "Ni na isa? Allah Ya ba ki hakuri ni ba neman fitina ne ya shigo da ni ba, shigowa nayi naga ya ki ka tashi." Ta kyale shi ta rufe idonta kamar bacci take yi. Ya yi shiru yana kallonta. Ya ce, "Shi kenan za ki shigo anjima." Ta bude idonta ta ce, "Ina?" Ya dan langabar da kai ya ce, "Dakina mana, ai nasan za ki kawo break ko?" Ba ta tanka ba yai shiru kamar zai fice ya yi dan yi jim! Na tsawon lokaci sannan dai ya daure ya ce, "Dakin ma fa ba shara ki taimaka ki zo ki share mini, kin ji ko?" Ya jima a tsaye bata tanka ba, sannan ya ce, "Bari na fita dai a dakin nan kar ayi mini sharri, don naga kamar yau rigima ki ke ji." Ita dai bata tanka ba, ya juya ya fice. Tayi tsaki ta mike ta fita tsakar gida, su Talatuwa da Badi'a suna firar dankali da doya, taje ta dauko wuka da kujera ta fara. 981shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ganin ta fito yasa Talatuwa ta fara hada kayan wanke-wanke ita kuma Badi'a ta ci gaba da aikin suya, su Mama kuwa da Iya Kande suna kitchen aikin suke yi don dama kusan kullum haka suke yin aikin safe. Ita kam Goggon Maman tana cikin firar dankalin Ya Munir din ya fito yana faman kamshi. Ya ce, "Ba ki zo ba har na shirya, me yasa?" Bata yi magana ba, ya durkusa a gabanta. Sai yanzun ta kare masa kallo. Sanye yake cikin shirt da wando, wandon jeans ne baki shirt din kuma baka ce mai sarsar din fari. Yau ma a Munir dinsa yazo mata, don ya tsareta da manyan maganansa, don haka ta ki yadda ta hada ido da shi, zance yake mata cike da rada yake cewa. "Ki taimake ni dai kar wanda yasan shirmen kishi ne a gidan nan, don Allah ki rufa mini asiri kin ji ko?" Ta sake daure fuska tana ci gaba da abin da take yi. Ta ce, "Shirme? Shirme fa ka ce? Ka dauki makaman kashe ni ka ce shirme? Watana nawa....?" 99 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ya yi maza ya rufe mata baki ganin Hajiya ta fito a kitchen. Ya marairaice murya ya ce, "Ni ne fa my life, ni ne fa don Allah ki yafe mini kin ji ko?" Ba ta tanka ba, ta zuba dankalin hannunta a ruwa ta ci gaba da aikinta. Sai kuma hawaye ya 6allo mata, ganin hakan ya mike ya bar wurin. Hajiya Maman ta karaso wurin ta hauta da fada. Ta ce, Don rashin hankali ana ba ki hakuri kina bijirewa? Ko so ki ke ki zamo shaidan to koma meye ya hada ku ya gane kurensa ya ba ki hakuri ba za ki yafe masa ba? sai ki ringa wani kumburekumbure, maza dai ki zamo wanda ta fi shaidan." Ta share hawaye ta tashi ta wuce daki, Talatuwa ta ce, A'a Hajiya Mama, barta taja zarenta ai ya wahalar da ita shima. Duk gatansa kuwa sai ya dandani abin da ta dandana itama, ai namiji kyale shi ta rama abinda ya mata. Hajiya ba ta tanka ba ta wuce Talatuwa tana aikinta tana fadin, Ai ke Talatu ba kya son kashe wuta. 100 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ita kuwa idan har tasan ba ragowa tsakaninta da miji to tana girma ne ba biyayya tsakanin su ko me ya mata ai tilas tayi hakuri tunda ubanta hakuri ake yi da shi. Jin hakan yasa Talatuwa tayi shiru da magana. Da aka shirya break din Munir din Hajiya Maman ta ce, Badi'atu kirawo ta takai masa abinci. Taje ta kirawota, itama lokacin tayi wanke kayanta take sanyawa. Badi'atu tayi dariya ta ce, Kin samo kan mutumin ki naga gaba daya ya yi ladab bata mata magana ba ta shirya sosai cikin bakin les mai ratsin bakar fulawa tayi kyau sosai, kyau na mamaki sai kamshi take yi. Tasa hijabinta mai kalar da ta fito, ta dauki tiren abincinsa takai masa. Yana waya ta shiga, don haka ta ajiye zata fice. Da sauri yasha gabanta ya tura kofar ya yi mata key ya tsareta da ido yana magana wayar. a Jin kamar da mace yake wayar yasa ta natsu, take jiransa sai kuma taji yana cewa. 101, Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo "Ni ai an yanke bikina nan da wata daya ne don kwanakin da suka sanya ni sun yi mini nisa ma. Ya yi shiru alamun daga wancan sashen ana magana. Ya ce, "A'a da 'yar uwata ne, auren gata za a yi mini don haka ki daina jirana yanzun ba ni da lokacin aurenki, kiyi hakuri." Sai kuma ya kashe wayar. Yayin da Zainab ta sake shan mur! Ta bata fuska ta ce, "Ni aiki nake yi a cikin gida." Nan kuma ya ce, Hada mun tea idan na gama sai ki tafi ko?" Tana wani ciccin magani tana wani 6a66ata rai ta hade masa. Ya ce, Muci ko? Ta ce, Ni na Koshi." Ya ci gaba da abin da yake yi ya gama ya ce, Daman unguwa za ki raka ni, ta bata fuska ta ce, Unguwa fa ka ce? Ya ce, Eh! Ta ce, Ni ai bana fita unguwa da namiji. Ya ce, Ai yanzun dole muje tare don unguwar taki ce kuma ranar Litinin zann tafi kin ga ba ni da lokaci sai yau da gobe, ki shirya kawai muje. 102 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ta kalli agogo ta ce, Ai ni ban karya ba ne shi ne yasa kaga na ce ina zuwa. Ya kalli abincin gabanta ya ce, Gashi nan kiyi break a nan. Ta hada kayan ta ce, Ni dai ina zuwa. Ya ce, To shi kenan. Ta kwashi kayan tayi cikin gida, ya biyo ta da wasu a falon suka yi break da Badi'atu ta gama tana cewa, Badi'atun unguwa fa zamu je. Ta ce, Unguwa ina? Ta ce, Wallahi bai gaya mini ba, ya ce dai zan raka shi? Ko za ki je?" Ta ce, To bari na dauko gyalena. Ita da shi ke ma'abociyar gyale ce, tilas tasa sai da Goggon Maman ta sanya gyale har da wani gilas na manyan yara. Don ita Badi'atu da wahala tayi wanka ba gilas. Shi kansa da suka fito wurin mota dariya suka ba shi, ya dai kanne ya ce, Ke Badi'a wa ki ka biyo? Ta ce, Zainab ce ta ce na rako ta. Ya yi musu wani irin kallo ya ce, Ki bani wuri. To ke kuma shi ne ki ka je ki ka janyo ta, ni da ke ba za ki bi ni ba sai da mutum? Badi'atun kuwa tayi wnai kini-kini da fuskarta ta ce, Ni fa gaskiya Yaya ba wani 103|shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo gulma zanje ba, kawai zan rakata ne, nima ko Allah zai ba ni mijin a hanya. Takaici ya ishe shi, ya ce, au! Kin gaji da zaman gidan ne neman miji kuma za ki shiga? To ba dani ba, don Allah Ya ya ka bar ni na biku, ya ce, To ke Zainab koma tunda ke ce ki ka tsokano ta na fasa fitar. Ya bude mota ya zauna tare da danna kaset din (Doro buci). Goggon Maman ta harari Badi'atun ta ce, Ki koma kinga ransa ya 6aci, Badi'atun ta ce, "Da kin san ba zaki je da ni ba ki ka gayyato ni? Ni ban gilas dina." Goggon Maman tayi murmushi ta ce, "Ai aro ne, ki bar mini don Allah." Tayi kicin-kicin ta ce, "A'a wallahi a bani kayana." Zainab din ta mika mata ta ce, "Gashi nan za ki taba kayana nima, za ki ga wulakanci." Badi'atu ta ce. "Eh din! Da yaushe ki ka shirya da Ya Munir din har za ki wulakanta ni? Tunda ya ce ba zai je da ni ba ki fasa binsa mana, ba jan aji ba komai, shi yasa yake raina ki ai." Tayi tsaki ta wuce shi ta wuce cikin gida fusace tana fushi, a ranta Zainab ta Badi'atu. 104 Shafi a Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ba hankali mutumin da aka dinke shi yana yagewa shi ne abin da zan yi ma jan aji? Ta gewaye can gefensa ta shiga ta zauna. Ya juyo ya kalleta ya rage volume din CD ya ce, Kina son shigo mini da Badi'atu cikin harkokina, ita kuma hankali ya ki isarta, kar ki kara gayyato mini ita cikin harkokina. Ta ce, To. Ya dubeta ya yi murmushi yana tashin motar yana cewa, "Ina glass din? Ya yi miki kyau." Goggon Maman tayi dariya ta ce, "Ai daman Badin ce ta ara mini ta kwace abinta da ka ce ba za ta bi mu ba." Ya yi dariya yana girgiza kai. Ya ce, Badi'a rikicin duniya kenan, bata tsoro ko kaďan yarinyar nan, Allah ya shirya. Ta amsa "Amin." Tana fadin, Ai babbar yarinya ce, ita komai nata sai ta fitar shi daban. Ya yi dariya ya ce, Na gani. Shoprite ya nufa ya faka motarsa inda ake parking motoci, sama suka hau kai tsaye ofis din Manaja suka gaisa da Ya Munir din. Ya nemi wuri ya zauna "Ya dai Zainab Madam zauna mana." Ta zauna a three siter 105 Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo din da suke ofis din. Ya yi ma Manajan bayanin zuwansu, ya kira sakatariyarsa ya ce su rubuta duk abin da suke so a hado. Da sakatariyar aka lissafa kayan lefe tana rubutawa, sai da suka rubuta sannan aka kawo kaya akwayi mai shida ne set daya. Sai katuwar Jaka da aka loda takalma da Jakankuna super sha biyu les sha biyu shadda shida, kamfala shadda shida, Super English shida English shida Super aura shida, kaya dai an dankara kaya. Fannin kayan shafe-shafe komai na Dove aka zuba, sai tsadaddun turaruka da shi ya ringa fada mayafai da after dress, English sai kallo. Haka yasa sai da aka shirya komai yasa aka shirya a mota. Wurin sarkoki kuwa da fashion-fashion da awarwaro sune na karshe, har da gwal wuya biyu. Wurin biyan kudi kuwa sai ya bayas (ATM) suka ciri iyakar kudinsu, sannan suka fito. Can ya dire ma Umma kayan ya ce, Idan sun gani aje a kai lefen Zainab ne, a nan suka 1061Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo lalace wurin kallon kaya, tana faman sanya masa albarka. Itama ta dauko wata English gold ta kara sanyawa, sannan ta bayas kudi ta ce a karo atamfa classic da Diamond da Holland ba a sayo su ba shi dai a nan ya bar su yana fadın. "Mu Anty mu tafi." Ta ce, A'a Allah ya maka albarka, irin wannan dukiya! Aure ya yi goshi, ga aiki ga aure Allah ya kara budi. Nima bari na zuba gudunmawata, silifas zan aika a sayo guda shida naga toilet din gidan naka guda shida ne, kowanne a sanya daya ko ya ki ka ce Goggon Mama?" Ita dai bata cewa komai, sai 6oyewa idonta take yi, ita da Umma babu kunya sai yau. Umman ta ce, Ka barta sai dare zaku tafi ko taci abinci ta huta. Ya kalle ta ya ce, Wai haka Zainab? Ta girgiza kanta ya ce, "To taso mu tafi." A nan suka bar su da santin kayan a hanya ya lura duk tayi sanyi. Ya juya ya kalleta ya ce, Yaya ne Goggon Mama? Ko gajiya се?" 107 IShafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ta girgiza kanta ta ce, "Ban gaji ba, ina tunanin kudin da ka kashe ne." Ya ce, "Ki daina tunanin kudi, kin fi komai a wurina." Ta sake kallonsa taga har yanzun ita yake kallo. Ta ce, "Allah ya kara budi." Ya ce, "Yauwa, wannan shi ne fatan da za ayi." Ya ce, "Ni kuma duk tunanina ya kare na gobe kawai zan yini tare da ke jibi na tafi." Tа ce, "Ai dai yanzun za ka ringa yi mini waya ko?" Ya ce, "Dole ne ai na kira iyalina jai ya ki ke ko?" Tayi murmushi tana sake langabe kai ta ce, "Ni fa kaina har ya sara ciwo da gaske jibin za ka tafi? Don Allah ka bari sai wani satin." Ya ce, "Yi min adalci, ki ba ni izini na tafi jibin kin ji ko?" Bata yi magana ba, har ya iso kofar gida. Falalu ya bude masa get ya shigar da motar, yana faman tambayarta. "Ba ki ce komai ba, ko ba ki yadda ba?" Ta ce, "Na yadda, to ya zan yi? Ni kadai nasan irin rayuwar da nake yi idan ba ka nan. Rashinka yana takura min." 1081Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ya saki ajiyar zuciya ya ce, "Lallai rashina ba ya takura miki na yadda ni ne dai abin tausayi." Та се, "Мe yasa ka ce haka?" Ya ce, "Ai da rashina yana takura miki, za ki kira ni a waya ko text ba ki taba yi min ba. Ina fa kallonki, kuma don hakan na dawo miki da wayar amma dai na gode." Та се, "Вa ka yadda ba?" Ya ce, "Ya zan yadda Zainab? Kiga fa yadda Nuri tayi ma Hafiz soyayya, ki kalli yadda Ummi Farida take yi ma Sa'id soyayya. Yarinya karama amma ke sai wurin rashin kunya ki ka fi auki." Mayafinta ta yaye ta ce, "Kalli fa kashin wuyana, kalli ramata ka kalli yadda soyayyarka ta maida ni, ni me yasa ba ka tausayina?" Ya sanya hannu ya janyota jikinsa ya rungumeta, ita kam wasu irin hawaye take fitarwa ya rada mata a kunne "Wannan hawayen fa?" Ta janye jikinta daga gare shi ta ce, "Na kaunarka ne." Ya ce, "Kamar gaske." Ta ce, "Na me yasa baka gaskata ni akan so?" Ya cсе, 109 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo "Wata shida ba ka nemi masoyinka ba, ki gani fa ina janyo kina janyewa shi ne son?" Murmushi tayi ta bude murfin mota ta fice, ya jima bai fito ba, yana mota, da alamar ya shiga wata jihar. Ita kam! Bayan motar ta bude ta kwashi ledodin da ya zuba, kayan snacks ne da Ice cream da Kaji gasassu. Tana shiga gida Badi'a ta ce da Talatuwa, suna gyaran danyen kifi a gindin famfo. Talatuwa ta karbi ledar tana fadin, "Oyoyo uwar dakina mai sa'a." Takai mata falo ta dawo tana yi musu dariya da Badi'atu don da farko kin kulata tayi sai da Goggon Maman ta ce 'yar haka ce Badi'a? Ta watso mata harara ta ce, "Da ki ka tafi ki ka bar ni sai me? Ai sai da Hajiya Mama ta leka kun tafi, wallahi da ba ku isa kun tafi kun bar ni ba." Ta ce, "Ayi hakuri my sweat sister kuskure ne. Wucewar Munir ne yasa ta bishi da sauri tana gwalon Badi'atun, a dakinta ta iske shi ya ง 110 f Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo kishingida. Ta ce, "Malam wai gajiya ce?" Ya ce, "Na gaji sosai." Ita kam a kasa ta zauna bisa carpet tana masa murmushi. Ta ce, "Nayi zaton wanka zaka fara yi." Ya ce, "Sai anjima zan yi." Ta bude robar ice cream ta tura mas aya harareta ya ce, "Da kaina zan sha?" Tana hararar tasa itama ta ce, "To ya zan yi maka don Allah? Ban yi sallah ba kai kuma יי kayi La'asar dinka." Ya ce, "Ai na san ba ki da sallar." Ta ce, "Ina yi mana." Ya ce, "To na gani?" Ba shiri ta fice da gudu tana dariya. Abinci ta kawo masa da kyar ya ci abinci don rigima iri-iri ba irin wacce ba su yi ba, sai da ta sanya masa kuka ya kyale ta. Da ya fice ma bai jima ba ya dawo, lokacin an yi sallar Isha'i, ya matsa sai sunje dakinsa ta ce To yanzun Mallam me zan yi a dakinka? Ya ce, Wani abu zan nuna miki." Та се, "Kalli fa lokaci kana tuna awarka nawa a dakin nan?" Ya girgiza kansa ya ce, "To idan ba za ki je ba ki gaya mini." 111 Shaf Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ta ce, "Dare ya yi, don Allah ka bari sai da safe." Ya ce, "To shi kenan kina so na kwana a nan kenan?" Ta mike tana bata rai ta ce, "Muje." Ya mike ta biyo shi har sun zo kofar fita Hajiya Maman ta ce, "Zainab!" Ta amsa "Na'am." Ta ce, "Dawo ki kwnata, kai kuma tafi dakinka sai da safe." Gaba daya kunya ta kama shi. Zainab din ta wuce tabar shi shima da kyar ya iya tafiya dakin nasa, kunya ta lullube shi bai san Maman tana jin su ba. Zainab din tazo zata wuce Hajiya Maman ta ce, "Zo nan Zainab." Ta zo ta durkusa gefenta. Maman ta ce, "Ina ku ka je yau din?" Ta kalleta a sanyaye ta сe, "Mama gidan su abokinsa muka je." Maman ta harareta kallo mai cike da tuhuma ta ce, "To shi ne ba za ki je da Badi'atu ba?" Ta ce, "Shi ne ya ce ba za ta bishi ba, ni 99 na ce tazo muje. Badi'atun da take gefenta. Ta ce, "Wallahi ba ki ce ba, kina kallo ya kore ni ba kiyi יי magana ba." ব 1121 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Hajiya Maman ta ce, "Ya isa! Ya isa yi mini shiru ke ki sake fita dashi ki gani marasa kunya kawai. Kun yini tare to kwana ma idan an bar kи taren za ku yi ko?" Ta sunkuyar da kanta bata tanka ba. Ta ce, "Tashi ni ki bani wuri, in dai namiji ne ki biye masa ki sha kunya, don a bangaren son mace imaninsu ragagge ne.' Da safe har karfe tara ba ta fito ba, tana daki. Ya ringa kiran wayarta ta kasa dagawa, kusan missed call goma sha biyu, a na sha ukun ta daure ta daga. Ya ce, "Hello! Life kina jina?" Ta goge hawayen tausaya masa. Ya сe, "Ki kawo mini break mana, ina jiranki ko?" Ta mike jikinta ba kuzari. Ya ce, "Wai me ya faru ne?" Ta ce, "Ko za ka gaya ma Hajiya Maman, ka ce akai maka break din ni wallahi kunya nake ji ma a ganni ina hada maka break, wallahi don Allah ni..." Ya katse wayar yana fadin, "Kar ki kawo ki bar shi kawai." Ta mike ta janyo hijabinta ta sanya, ta feshe jikinta da turare. 113 Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Da shi ke yau da tayi wanka kwalliyar material tayi blue ne ya yi mata kyau sosai, tana kamshi irin dai kamshi na mamaki. Talatuwa ta sanya ta hada komai sannan ta fito, Maman ta bita da harara, ta ce "Saura kuma idan kin je ki zauna ki dade kar ki fito yanzu." Ita dai bata yi magana ba, tana ajiyewa ta dan koma gefe ta zauna ta ce masa, "Ina kwana?" Bai amsa ba ya ci gaba da danne-dannensa a Computer ta ce, "Zan koma ciki aiki zamu yi." Ya mike ya shige daki, kafin ya fito tayi niyyar fita ya ce, "Kar ki fita rike kofar." Ya karaso ya kwace hannunta a jikin kofar ya kulle ya ce, "Sai kin jira na gama ko?" Ta koma ta zauna sai hawaye ya 6alle mata, bai yi mata magana ta ci gaba da kukanta, tana zaune yana break din har ya kammala. Ya ce, "Kuka ko? Sai idonki ya tsiyaye zan bude miki kofa ki tafi, ni ne abun gudunki ko?" 3 1141Shais Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ya cilla mata mukulli ya ce, "Je ki ga key nan." Da sauri ta zauna ta bude ta fice. Yana tsakar gida ta wuce su daki. Badi'atu ta shigo tana mata habaici na dai bata kulata ba, tana fadin "Nima dai zan fitas da mijin nan na huta da wulakanci, donni ba zan iya wannan rainin hankalin ba, an wani ware ni ana ficewa tare da saurayi." Goggon Mama dai bata tanka mata ba, ita abin da ya isheta ya isheta. Tunanin wani irin fushi Malaminta yake yi, sai shiga take yi tana fita ta kasa zama. Tana jin shigowarsa biyu cikin gidan yana ficewa bai neme ta ba, kwanikan da ya ci abinci ma da kansa ya shigo da su. Shi kansa yasan bai kyauta ba, ya ya zata ketare umarnin Mama? To amma sai wata zuciyar ta ce, ai ta san ba zai iya shiga inda take ba, to ita tazo mana inda yake ai shi ne zata nuna ta damu da shi. Ya shigo ya dauki lemo a firjin falo yana yi ma Hajiya Maman hira. Ta ce, Ashe jiya gidan su abokinka kaje ko?" 1151Shafi Zumunci Dangin Ka Jamila M. Danfajo Ya ce, Eh! Suna gaishe ki, kin san ni gobe zan wuce." Ta ce, "KUma sai yaushe?" Ya ce, "Sai bikin ya rage sati zan dauki hutu." Та се, "Тo Allah ya maka albarka." Ya amsa da "Amin." Sallamar Falalu ce ta katse su, yana shigowa da akwatina biyu samarin kofar gidan sai shigo da kaya suke yi. Daga daki, Goggon Mama ta gane akwatinan lefenta ne, ba shiri ta fito ta fice shi din ma da sauri ya biyota. Jin hayaniyar 'yan kawo lefe yasa dole ta wuce dakin na Munir. Shi din ma da sauri ya bita sai kuma ga Badi'atu uwar tsegumi ta leko dakin ta ce, "Mе kuma ki ke yi a nan dakin? Ba Mama ta hana ki shigowa ba?" Munir din ne ya juyo ya ce mata, "Ke yi fa ki ka ce? Har aga mace a dakin mijinta a tambaye ta me take yi? To ciki zan yi mata." Ita kam Goggon Mama idonta ta rufe don gaba daya kunya lullubeta tayi, har Badi'atun ta juya. 116 Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Ya ce, "Zo nan." Ta zo ya sara mata warning ya ce, "Kin yi na karshe idan Zainab ta ce mini kina mata rashin kunya ko Allah dukanki zan yi, mahaukaciya kawai. Ke waye ma zai aure ki? A wannan haukan naki? Don Allah matsa ki bani wuri ni stupid kawai." Ta juya ta tafi suna mata dariya. Ta ce Fada tayi ranar da Sa'id ya zabi Ummi wai bai ce ita yake so ba. Ya yi dariya ya ce, "Wai ita maras mutunci idan ya ce ita yake so ma karshenta ta kunyata mutane. Baki yadda ta tuno baki ba yana cewa ita yake so zata yi rashin mutunci. Zainab din ta ce, "Allah ya sawwake da rashin mutunci." Ta ringa ba shi labarin Shafi'u. Ya ce, "To ban da Badi'a ce bata da hankali waye zai ce ba ya son Shafi'u, meye laifinsa?" Zainab ta ce, "Kai ne ba ka ga laifinsa ba, ai ita ta gani." Suka yi dariya. Hajiya Maimu ce ta leko dakin tana fadin, "Amarya da Ango ne ake hira a nan?" Ya yi 1171Shfi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo murmushi ya gaisheta yayin da Zainab din ta durkusa ta gaisheta, suka yi cikin gidan. Ita kam! Hajiya Mama, mamaki tayi na yawan kayan lefen da aka kawo, ita dai ido ta zuba a ranta tana zabgawa zumuncinsu addu'a. Yayin da makiya sai sharben hawaye da fatar hanci. Hajiya Maimu ta ce, "To shi kuwa Mai sunan mallam wace irin sana'a ya samu yake facaka da kudi haka?" Anty ta ce, "Kamfanin Taki fa? Duk buhun da zai fitas da ribarsa a jikinsa, ga shaya ya sanya duk karshen wata a fitar masa da ribarsa. Sannan ga albashinsa bayan cuku-cukun ofis da za a dan yi a ba su alawus." Ai kuwa Maman Ladifa sai ta yarfo guda aka dibi shewa. Tilas Hajiya Sa'a itama tayi gudar ta ce, "Yaro Allah ya ba shi duniya." Anty ta ce, "Duniyarsa mabudin lahira." Ita kam! Hajiya Mama shiga take tana fita tana fita tana fitas da ruwa da lemo, dambun nama ta yi ma Munir zai tafi da shi. 118 Shafi Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo Gaba daya ta ba su da dunot da kek ta fitas musu katan-katan da fantar gwangwani da maltina. A nan kuma kishiyoyi suka shaka don sun hakikance wannan hidimar Alhajin ba ya yi musu. Ita kam Munir ne ya mata sayayyar kayan drinks a dalilin yazo

Chapter 11 of 13