ce, auta kashe aure
kenan. Mu duk rikicin aure da 6acin ransa ba mu
san shi ba sai yanzun a kan auranki.
Kina neman raba iyayenki ko?" ta tashi tana
soshe-soshe, tare da turo baki gaba alamun
baccinta ya mata dadi an tashe ta.
Та се, "Нajiya Mama kin ganta ko? Kin ga
tana dukana."
Hajiya Mama ta ce, "Ina ruwanki da ita?"
Tayi dariya ta ce, "Alhaji Babba ne ya ce mu
taho da ita gidanta za a kaita."
Hajiya Maman ta ce, "Ku aka turo?" Anti
Mairo ta ce, "Wallahi Hajiya wannan nauyin ya
dora mana, don haka ya ce, "Idan ba mu kaita
gidan Suraj ba, ba shi ba mu.
Ta yi dariya ta ce, "Lalle kam ba shi ba ku.
Sai kuje ku mutu, shegu ba uba in dai sai an kai
Goggo gidan Suraj.”
Nabila da take gefe guda bata magana tunda
suka shigo ta ce, "Kiyi hakuri Hajiya Mama a
kaita, saboda da tsauraran matakan da ya dauka.
Ya ce, wallahi idan kin hana mu kaita gidanta
ya ce mu gaya miki fa wai..."
"Wai me? Wai din ta wuce saki? Idan ma
sakin ne na huta da masifar gidansa.
139l
1
Zumunci Dangin Kauna Jamila M, Danfajo
Kalli yadda na rasa Yayanku Nabil, saboda
kawaici nayi hakuri aka masa auran da gaba
daya na rasa shi don yana takamar zumunci.
Ni? Ke wallahi ba da ni ba, ko bai sake ni ba
lumana ba zan kai shi kotu ya sake ni, don ni
wannan auren da yake cutata ya ishe ni.
a
Yanzun dukiyarmu ma da take hannunsu mun
kyale su ne wata ko zancenta ba a yi, suna tsoron
matansu sun hana mu hakkinmu.
Kuma da ku ke wannan zancen kun san in da
Mai sunan Mallam yake tun shekaran jiya nake
neman wayarsa a kashe.
An ce Alhaji Ahmad din ya kore shi a gidan,
ya kyauta kenan? Ko kuma an ce musu don su
kadai aka halicce mu?
Mun zama bayin su ayi ta zuge su ana sanya
su suna cin zarafin mu, muna zaune a wurin su
don zumunci ana kallon mu ma su naci ne."
Jikinsu ya yi sanyi. Anti Mairo ta ce,
"Gaskiya ba a kyauta ba, in dai haka ne yanzun
ina ya tafi?"
Hajiya Maman ta sanya zani ta goge hawaye
ta ce, Oho! Hafizun ne yana cikin hidima, shi
nake jira yazo naji in da Munir din ya shiga а
duniya.
140
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Ai mutanen nan sun cuce mu, kuma duk abin
da suke nufi damu sai Allah Ya maida musu,
aure kuma insha Allahu na hakura da shi in dai
don ina auren ake yi mini kama-karуа.
Ku kanku da kun yi tunani kun san a gidan
nan ana zaluntata, komai zai danka shi a
hannuna amma idan an tashi sai ya yi abin da zai
ci mutuncina.
Haka ake yin rayuwa? ki kalli a aurenki irin
wulakancin da aka yi mini, kuma ki duba ki gani
duk shekara uban Maimu sai na sanya shi a cikin
masu zuwa aikin Hajji.
Uwa ce da ni da zai mata ko uba? Amma duk
jumullar ku ya taba biya muku? Idan ma na
sanya ku ciki zai ce a'a, yana sane da ku.
Ki kalli auren Yayanku yadda aka kulla shi!
Me na ce? Ga shi an hada auren ban ki ba amma
ai an raba ni da dan.
Sai aike ya ke yi ma uwarta, kin ji ni na shiga
harkar su? Shiru nayi na bar wa Allah, don haka
na gaji da takaicinsa."
Nafisa ta numfasa, su kansu yaran sun san
hakuri suke yi da uban nasu a fannin komai, mahaifiyar tasu zaman hakuri take yi.
141 Ishafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Ana zaluntarta ana cewa ita ce take yin
zalunci, don haka a komai sai an yi yadda aka yi
a ka cuce ta.
Ta ce, "Allah Yasa hakan shi ne yafi alkairi."
Itama Anti Mairo addu'ar tayi, sai kuma aka
6alle da hirar hakuri da iyayen nasu suke yi da
iyayensu, ciwon 'ya mace na 'ya mace ne.
A nan suka yini, shima Hafizu sai yamma
yazo aka hadu aka yi ta hirar duniya da jajen hakuri da iyayen nasu maza.
Hajiya Maman ta ce, "Yanzun ina Mai sunan
Mallam din?" Hafiz ya yi shiru tsawon lokaci.
Ta ce, "Tambayarka fa nake yi?" Ya numfasa
وو
ya ce, "Yna nan." Ta ce, "Ban gane yana nan ba!
ina ya tafi?"
Hafiz din ya ce, "Ya tafi Kaduna, kin san
akwai wannan abokin nasa da suka yi karatu
tare, to shi ne ai yake neman aiki a kamfanin
Babansa.
To Allah da ikonsa aikin ya samu, ya ce mini
zai zo sai karshen watan nan, ba ya son ayi wasu
rigingimun yana nan ba, ya ce kansa ba zai iya dauka ba."
142 shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Hajiya Maman ta ce, "To ba an ce Baban
naku ya kore shi ba?" Hafiz din ya ce, "Habahaba dai! Hajiya duk zance ne.
Sun yi waya ai dazun ma muna tare da
Baban, ya bugo waya sun jima suna waya, ku
daina kama zancen 'yan jita-jita suna tayar muku
da hankali, yanzun yaushe za ki koma gidanku?"
Ta kare masa kallo ta ce, "Sai ranar da
ubanka ya canza hali."
Gaba daya tsorata suka yi, ba wanda ya sake
magana.
Nima dai na ajiye birona zan yi sallah, kafin
canza halin.
Mu hadu cikin littafi na biyu don jin yadda za
a kwashe.
'Yar Mutan Gumel,
Matar Bahadeje,
Jamila Muhammad Danfajo
(Matar Adamu Dauda Haďejia)
07032987315
143 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
MAHARAZU
BOOKSHOP
SANARWA! SANARWAI| SANARWA!!!
Albishirinku Makaranta Littattafan Hausa, ma
su sayen daya ko sari. Domin samun littattafan
Hausa kowanne iri, da na Turanci da na Koyon
Girke-girke kala-kala, da na lemuka kala-kala,
da kuma MUJALLU na fina-finan Hausa a cikin
farashi mai sauki, to maza ku garzaya zuwa
shagon MAHARAZU BOOKSHOP, wanda ke
GIDAN UMMA BAYERO, da ke kusa da
STANBIC ІВTС BANK, tashar kasuwar RIMI
kusa da ASIBITIN MURTALA.
Bayan haka kuma, muna buga littafi a kan
farashi mai sauki, kuma a cikin kankanin lokaci
tare da yin aiki mai inganci.
Domin neman karin bayani, za ku iya
tuntubarmu a wadannan lambobi kamar haka:
08036175492, 08099199121, 08092828378
144 |shafi
SAI KUN ZO!
1
Maharazu Bookshop
ZUMUNCI
DANGIN KAUNA
2
JALaMHINiлнат
JAMILA MUHAMMAD DANFAJO
(Mrs Adam Dauda)
Zumunci Dangin Kauna 2
Jamila M. Danfajo
ZUMUNCI DANGIN KAUNA 2
afizun bai sake magana ba saboda Hafizrigimar ce ya ji tafi karfinsa.
Ya mike yana kallon Goggon Maman. Ya yi
dariya ya ce, "Nuri na gaishe ki." Ba ta amsa
ba, ta kyale shi don tasan ya yi nufin zolayarta
ne.
Ya ji bata yi magana ba. Ya ce, "To Ango
dai yana can an shirya masa gida, kina nan sai
faman kunatar kanki ki ke yi.
Ni ban ga abin kin yadda da kaddara ba, da
Surajo da Munir din duk ba daya ba ne? kamar
su daya wata biyar ne fa tsiransu."
Nabila ta ce, "To ai hali ake dubawa, shima
ai ba a ki shi ba, halinsa aka ki." Ya yi
יי murmushi ya ce, "Hum! Ya canza fa."
Ya fada yana kallon fuskar Hajiyarsu. Ya
ce, "Wallahi Suraj ya canza, ba ki ga yadda ya
yi ladabi ba, za ki yi mamaki idan ki ka gan
shi, jikinsa ya yi sanyi sosai.
Shi kansa yasan bai kyauta ba a kan abin da
ya yi, wallahi mun jima muna magana da shi.
Ya ce tsautsayi ne, kuma duk komai sharrin
abokansa ne.
31S
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Wallahi bai ga Munir da Zainab suna aikata
wani abu ba, kawai shaidan ya kintsa masa
komai ya ce a bai wa Munir din hakuri, na
kuma hada su a waya na ce ya ba shi hakuri."
Hajiya Maman ta ce, "Ai a banza, tunda ya
hada shi da iyayensa suna ganinsa da bakin fenti, sharrin zina ai dafi ne, kuma sharrin zina
zunubi ne mai girma a wurin Allah."
Hafiz din ya ce, "Ai ya yafe masa." Hajiya
Maman ta ce, "Cabdi! Wallahi ba zai yafe
masa ba, da su da munafukan iyayensu, idan
kuma shi ya yafe ai Goggona ba za ta yafe ba."
Anti Mairo ta ce, "Ayi dai komai a sannu,
wannan ba abin damuwa ba ne, komai ai dan a
hankali ne.
Ni wallahi wannan tahowar ta Hajiya Mama
tafi damuna, ita kaddara ai yadda ake yi da ita,
ba ki san rabon da yake cikin auren nan na
Suraj da Zainab ba, don dai kina daure mata
gindi ne."
Bata yi magana ba, sai ta fice ta ce, "To dai
duk abin bai kai ba, ayi komai a hankali nafi
son komai ya daidaita a kaita gidan Suraj din,
meye duniya?
4
Zumunci Dangi Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Mu duk ba zabar mana mijin aka yi ba, aka
kai mu gidansa? Mutuwa muka yi? Da za a се
ita dole sai wanda take so zata aura?"
Hajiya Maman ta ce, "Ai ba ku da hankali
ne shi yasa. Wannan auren ai ba kaddara ba cсе,
idan kaddara ce ba zan taba ja da ita ba.
Kulle-kulle ne kawai aka yi shi don a cusa
mini bakin ciki, kuma an yi insha Allahu kuma
sai Allah Ya tona asirinsu.
Duk wanda yake da hannu a cikin wannan
tashin hankalin da aka sanya mu, insha Allahu
sai Allah ya tona asirinsu.
Ko don yaron da aka kora ba hakkinsa aka
saukar masa jinya. Kalli yadda aka kore shi ko
warkewa bai yi ba saboda an yi munafunci.
Ai ni ina nan, wallahi ko uwata ba za tà auri
Munir ba sai an saketa ta auri wani, amma ba
zabin Hajiya Maimu da Binta ba.
Saki kuwa da ya ce zai sake ni wallahi ina
jiransa, ai komai daman ya yi farko zai yi
karshe. Rayuwa kuma mutum ma yake mutuwa
balle aure?
Yanzu ina iyayenmu? Tuni sun kaura. Kalli
girman gidan nan, gidan da ya kunshi mutum
51hafi
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
kusan goma, yanzun ina suke? Duk sai tarihi
balle wani aure karamin alhaki."
Hafizun ya duba agogonsa ya ce, "Allah Ya sauwake, ni zan tafi to tunda dai abin yafi
Karfina." Ta ce, "Yafi karfinka, kuma ku dukanku na lura kun goyi bayan banku, kar wanda ya kuma zuwa mini da zance irin wannan.
Idan kuma mutum ya sake tayar mini da maganar auren nan ban yafe ba, in dai ba
goyon bayana zai yi ba, wallahi mutum ya fita
a idona."
Dukkan su tsit! Suka yi tsawon lokaci ba
wanda ya tanka, sai Hafiz din da ya mike zai
tafi.
Ya ce, "To Hajiya Mama, Allah Ya huci
zuciyarki." Та се, "Amin." Ya ce, "Ni zan
tafi."
Ta ce, "Jeka mana, ko da kirawo ka nayi?"
Ya rike baki yana jinjina girman lamarin. Ya
ce, "Allah Ya sawwaka." Ta sake cewa,
"Amin." St kam! Sun Anti Mairo duk sun yi
tsuru-tsuru, ba wanda ya sake magana. Ya juya
zai tafi.
6Sha
e
Zumunci Dngin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Goggon Maman tayi karaf ta ce, "Mama zai
tafi bai ba ki lambar Mai sunan mallam ba." Та
ce, "Kar ya bani, ya tafi ai ba ya bakin ciki da
korar da aka yi masa, yana ji ina neman
wayarsa yau kwana uku ba a ganshi ba, ba a yi
waya da shi ba.
Yaje ya hada su da Surajon suka yi wayar,
ni ce ba zai hada ni da shi ba. yaje kar ya bayar
meye duniya?"
Jikin Hafizun ya yi sanyi.
Ya juyo yana hararar Goggon Maman. Su
Anti Mairo dai dariya suke yi.
Ya ce, "Kawo wayar a sanya muku, idan
,י kuma da (MTN) dinsa mai (070) to shi ne.'
Та се, "А'a babu shi a nan a wayata ne
daman kuma tana wurinshi." Ya ringa fada
mata tana shigarwa a wayar Maman, suma su
Anti Mairon duk sun dauka.
Nabila ta ce, "To ni fa Hajiya Mama gobe
zan tafi (da shi ke a Legas ta ke).
Ta ce, "Me zan yi miki don gobe za ki tafi?"
Та се, "A'a ba komai daman ina son daddawa
ne da yajinta." Bata yi magana ba tsawon
7
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
lokaci ta ce, "Kije man uban naki ya saya miki,
99 ba kun fi sonsa da ni ba? ai da karuwa.
Ta ce, "A'a Hajiya Mama nafi sonki." Gaba
daya suka yi dariya, tsawon lokaci suna hira,
sannan suka tafi.
Alhaji Usman kam! Tun yana daukar al'amarin wasa har wankin hula ya kai neman kai shi dare.
Duk yadda ya dauki al'amarin ya wuce saninsa, ya kafe akan idan har Surajo ya saki
auren Zainab to a bakin auren Hajiya Maman. Yayin da nadama ta lullube Suraj din. Sau
da yawa ya ringa zuwa gidan Hajiya Maman ya
yi ta bata hakuri. Ita dai bata magana, haka nan
Zainab din sai ta 6oye ta ki yadda ya ganta har
ya gaji da zama ya yi tafiyarsa.
'Yan aiken ayi hakuri a ba shi matarsa uwa
har sun gaji da aikowa sun hakura.
Hajiya Rabi'a kam! Bata cewa komai, don
har aka gama hidimar bikin nan ba mai cewa
ya ji ta bakinta, don ita ba su ma isheta kallo
ba, balle akai ga ta tanka musu. Shi kansa
Alhaji Ahmad din ya rasa gane kanta, har gara
81
Zumunci DanKauna 2 Jamila M. Danfajo
shi Alhaji Usman yake gani da Hajiya Maman
ta bar masa gidan yasan bata nan amma Hajiya
Rabi'a tayi mirsisi ba ta shiga harkarsa.
Don ranar da Suraj ya karyata sharrinsu da
kansa ya shiga yake gaya mata Ahmad din sai
da ya gama ta ce, "Allah Ya sawwake." Ba ta
sake tankawa ba.
Yayin da Suraj ya bude bakin bayar da
hakuri, kullum sai ya shigo da kansa ya bata
hakuri ta ce ba komai Suraj tunda dan uwanka
ya yafe maka wallahi na yafe maka har ga
Allah.
Sai dai ya rusuna ya ce, "Hajiya ki bai wa
Hajiya Mama hakuri, wallahi da farko sharrin
su Hajiya Maimu ne, su suka sanya na nemi
auren Zainab.
Duk da nasan ita din ba ajin aurena ba ce,
wallahi sune suka tilasta ni, duk wasu
sharrance-sharrance su ne suka kulla shi,
wallahi ni ba ruwana." A nan ya zayyane
farkon kulla neman aurensa da Zainab din. Ya
zayyane mata komai.
Ta ce, "Don Allah Surajo kayi mini arziki
daya." Ya ce, "Arzikin me?" Ta ce, "Yadda ka
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
zo nan kayi mini bayanin komai, ka taimake ni
kayi mini bayanin a gaban su Alhaji Babba."
Ya yi murmushi ya ce, "Nayi miki duk alkawari, duk ranar da ki ke son magana da ni
kiyi magana, don Allah." Ta ce, "Shi kenan, na gode."
Kafa da kafa ta tafi zoo road har falon Alhajin ta iske shi, sai da suka gaisa. Tayi
masa bayanin abin da take so ayi.
Da farko shiru ya yi, sai kuma ya ce, "Shi
kenan kije soron dinkin muna zuwa da
Amadun." Ta mike tayi masa sallama ta tafi, don matan gidan ba wanda ya amsa mata, tana fadin "Matan gidan nan sai da safe."
A Soron Dinki kuwa an yi ta ta kare,
Alhajin ya jima yana mamakin jin gaskiya daga bakin Suraj din. To mutum ne dama
marar jin magana, maras shakka.
Don haka bai ji tsoron komai ba ya zayyane
musu yadda lamarin ya faru. Alhaji Usman ya jima shiru bai iya magana ba.
Alhaji Ahmad din ne ma ya ce, "To sakar
masa diyarsa, aurenka da ita na haramta shi,
10
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
tunda na auri uwarka ba ta bar mu mun zauna
lafiya ba.
Don haka ba zan taba yafe mata ba ita da
יי Maimu, suje kuma duniya ce." A sanyaye
Suraj din ya ce, "Na sawwake mata, ni dai
burina daya ne, ku yafe min laifukan da ku ke
kallona da shi.
Akwai yarinyar da nake so a nema mini
aurenta, insha Allahu zan zamo yadda ku ke
so."
Alhaji Usman ya ce, "Ka fada yarinyar ko
'yar ina ce zan nema maka aurenta insha
Allahu.
Yadda ka bude mini abin da yake lullube
insha Allahu ba abin da ba zan yi maka ba.
Tashi kaje zan neme ka, Allah Ya yi maka albarka." Ya amsa "Amin Ya Allah." Ya mike
ya fita.
Alhaji Babba kam da Alhaji Karami sun jima suna bai wa Hajiya Mama hakuri ta huce
ta koma dakinta.
Ta ce, "Daki? Wanne irin daki kuma? Ai ni
wannan auran na bar shi sai dai kuma zumunci
in Allah Yasa za ayi sai ayi.”
111Sha
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Alhaji Karami ya ce, "Kar ki cika baki,
wallahi ni ba na son cika baki." Ya ce "Eh! Da
aka ce za a sake kin an sake kin bare ki ce za ki
yi iko da kanki?"
Ta saki ajiyar zuciya ta ce, "Ko da auren
idan na ce ba zan koma wannan gidan ba me za
ka yi mini?"
Alhaji Ahmad ya yi dariya. Ya ce, "Ni me
zan yi miki?" Ya fada yana kallon Alhaji
Osesen. Ya ce, "Ga wanda zai dauki mataki
.nan יי
Alhajin ya girgiza kai ya ce, "Ai ni da nan
da can ni duk daya ne a wurina, in dai ana yi
da ni."
Alhaji Ahmad ya ce, "Rabi'a ta ce mu tafi
ba zai yiwu ba al'amarin muna nan wannan
tsoronta yake yi."
Alhaji Osesen ya yi dariya yana kallon
agogo. Ya ce, "Ai dole naji tsoronta, ba ka gani
itama tsoron wadancan ne ya koro ta nan ba?
nan din ya yi ai.'
Sai a lokacin Hajiya Maman ta ce, "Ai nan
din da kudina na gina, don haka ba wanda zai
shigo mini."
121shaf
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Sai a lokacin Alhajin ya kalleta a tsakiyar
idonta ya ce, "A'a Hajiya Dije, ba ma haka da
ke. Fadi nawa ki ka kashe a ginin naki a biya
ki?"
Sai kuma tayi shiru bata tanka ba. Hajiya
Rabi'a ce ta ce, "A'a Alhaji mu tafi haka nan
kar girma ya fadi a gabanmu."
Suka fice suna dariya.
Wannan dai ta kare.
e
**
MUNIR FA?
Shi kam Munir a Kaduna ya yada zango,
gidan su abokinsa Abdulbasi.
Iyayen Abdulbasi talakawa ne, ba su da
karfi sosai, tuni suna neman aiki amma ba su
samu ba, a kamfanin Baban abokinsu.
Tare suka yi Makaranta a Maiduguri har
suka kammala Digree suka yi masters ba su
taba gudun juna ba gidansu Abdul na nan
(Festac) a Kaduna.
Da daddare misalin karfe goma da rabi
mashin ya ajiye Munir kofar gidan su
Abdulbasi, ya sallami mai mashin din.
13S
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Kofar shagon Abdul ya kwankwasa kofar
da sauri Abdul ya bude saboda yanayi ne na
damuna, ranar an tafka ruwa.
Don haka Abdul har ya kwanta, jin ana
buga masa kofa ya taso ya bude. Ganin Munir
suka kwashe da dariya har da tafawa.
Ya ce, "Mutumina daga ina haka?" Munir
bai yi magana ba sai dariya. Yaja Troly dinsa
suka shiga ciki. Ya ce, "Lallai yau ina da
manyan baki, to ko kamfani sun kira
(interview) ne?"
Ya girgiza kai ya ce, "Ba wannan ne ya
kawo ni ba, wallahi Abdul akwai matsaloli ne,
na dan guje wa Kanon nan."
Abdul ya ce, "Kamar wanne irin matsaloli?"
Ya ce, "Suna da yawa sosai, akan dai wannan
yarinyar ta gidanmu ne." Ya ce, "Wai Zainab?"
Ya ce, "Yes! Ka gane ashe."
A nan ya kwashe labari kakaf ya gaya masa,
ya jajanta masa ya ce, "Haka fa aure yake,
yana da matsaloli sosai, sai a hankali.
Bari na shiga gida na samo maka abinda za
ka ci." Bai jima ba ya dawo. Ya ce, "Zo muje
14
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
mutumina wurin mai shayi ya yi mana indomie
da kwai."
A can suka ci abinci sannan Abdul ya nemo
masa ruwa a bokiti ya yi wanka ya samu
nutsuwa.
Kwana biyu Munir ya rasa natsuwarsa, da
kyar Abdulyake dan kwantar masa da hankali.
Sai da suka yi waya da Suraj da Alhajinsu
sannan ya dan rage damuwa, amma duk da
haka ba ya bude wayarsa. Sau da yawa idan ya
bude wayar yana gaisawa da Hafizu, daga
karshe ma sai ya daina daga wayar 'yan gidansu, sau daya ya gaisa da Hajiya Mama.
Ranar wata Juma'a ya dawo daga Masallaci,
kiran Hajiya Maman ya shigo wayarsa, ya daga
sai ya ji muryar Zainab din.
Suma ne kawia bai yi ba don dadi, ya yi
bakam ya kasa magana yana jin ta tana fadin.
"Hello!
"Hello!!
"Hello!!!
"Ya Munir kana ji na?" Ya yi shiru yana
sauraronta, sai kuma ya kashe wayar. A ransa
15 Shafi
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
yana ayyana to me zance mata? Matar aure ce fa?"
Kishi da wani irin duhu ya ziyarce shi, gaba
daya ya tsani rayuwar duniyar, cikin tunanin sa
ya sake jin ringing din wayar.
Ya dauka yana dubawa, me zai ce mata? Sai
kawai ya kashe wayar ya bude ta ya cire batir
din ya watsa karkashin filo.
A duniya ba abin da yake so irin Goggon
Mama, ko ina yaje sai ya nemo ta a waya. Tun
tana 'yar yarinyar ta, idan kuma yana gari ba
shi da wurin zuwa sama da gidanta.
Don komai yake hankalinta yana kanta
sanyinta da miskilancinta, shi ne ya kara saka
su suna shakuwa, bai san lokacin da suka shige
shi ba.
Yana jin a rayuwarsa bai taba son mace
yadda yake son Goggon Mama ba.
Kwanaki sun tura tsawon wata uku kenan
yana Kaduna, sun samu aiki sai dai ba wani
aiki ne na ku zo mu gani ba.
Kawai dai ana lallabawa ne Karshen wata a
kwashi albashi duk da ba su fi kudin bukatun
yau da kullum ba.
16Shat1
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Abu daya ne ya karu dashi ya murje ya yi
kyau sosai, duk wani bacin rai da yake nunawa
a jikinsa da ne, don yanzun jikinsa bai nuna ba.
Sai dai a zuci dafin yana murzarsa, don dai
mutum ne shi mai hakuri, yasa jikinsa bai nuna
ba, ya dangana da ya rasa Zainab din har abada
to dan uwa ciki daya fa.
Yayin da Abdulbasi ya ringa matsa masa ka
taimaki kan ka muje Kano mu gaida su Hajiya
ko?
Shi dai ba ya magana idan yana masa irin
wannan maganar, abu daya yasan ya yi a
rayuwarsa tunda yazo Kaduna yana gaishe da
iyayensa.
Alhaji Babba kullum zancensa yaushe za ka
dawo? Bai iya cewa komai da kyar ya gaya ma
Alhajin "Na samu aiki ne a nan." Alhajin ya
sanya albarka.
Yana son gaya masa an raba auren Zainab
da Suraj tuni har an yi masa aure, amma kuma
ya kyale shi saboda yana tunanin ko ya sani
wata zuciyar ma ta ce to ai warhaka iyayensa
mata sun gaya masa don haka yaja girmansa
bai tanka masa ba.
171
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Bai san al'amarin hoto ba ne, don shi Munir
ba ya iya yin waya da iyayensa mata saboda
raunin su.
Idan ya ji yadda abubuwa suke tafiya a
wurin Hafiz sai ya kasa kiran su don tunda ya
tabbatar da Hajiya Maman ta bar gidan su
yasan tabbas akwai wata baya.
Don da Alhaji Babban ma da kyar yake
gaisawa a gaggauce yana tsoron kar ya ji wata
magana da za ta rusa masa lissafi a rayuwar sa.
Wannan ita ce rayuwar da Munir ya ke yi a
Kaduna, amma dai damuwarsa ta tafi kakaf a
kan ya zai iya yinta a haka ba hasken
rayuwarsa?
**
ZAINAВ
Rayuwarsu suke yi a gidansu na gado Soron
Dinki, sosai Hajiyan take yin walwala da
Jama'arsu.
Don daman kusan rabin lungunsu 'yan
uwanta ne, don haka Hajiya Mama sana'arta
take yi ba abin da bata sayarwa na harkokin
rayuwa.
18
Zumunci Dangin Kauna 2
Jamila M. Danfajo
Hajiya Maimu ta ce, "Lalle bana Hajiya
Sa'ade, Alhaji zaim yi nadama, don duk yadda
za a yi sai dai ayi sai kowacce ta mallaki gida.
Hajiya Sa'ade ta ce, "To ai kamar da kasa in
ji mai ciwon ido, waye zai yadda da wulakanci
irin wannan?"
Ita kam Hajiya Mama dariya tayі. Та се,
"To ai Alhaji ya ce ba zai raba gida ba, ko kin
manta?" Ya ce, "Zumuncin 'ya'yansa rabuwa
zai yi idan ya raba gida."
Hajiya Sa'ade ta ce, "Yo ai daga na gaba
ake gane zurfin ruwa. Ai tunda ya ware miki
gida wallahi shiri zai yi sosai, tsarin ya yi
kyau." Ta ce, "Nima ba ni da kowane sai auta,
itama yanzun idan na aurar da ita ai shi kenan
ba ni da kowa, ko kuwa masu bataliya?
Idan kun raba gida ai zumuncin balbalcewa
zai yi, ko da ku ke son zumunci kamar kuyi ya
ya?"
To da wannan ta rufe bakinsu ba wanda ta
sake magana sai da aka leka sashen Alhajin
kowacce bakinta ya shiga motsi a sashen kayan
sana'a kuma habaici a ke yi ma Goggon Mama
da 'yan aiki.
21Sha
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
Hajiya Sa'ade ce tayi magana, ta ce "Lallai Goggon Mama, nan ne sashenki? A raba miki
aure kin dafe dinki sai kin gamu da basir?"
Ita dai bata tanka ba, sukai ta bakin cikin su
suka fice, don kayan kasuwar ta da Hajiya Maimu ta gani haka ta ce, Lalle Alhaji ya kauro nan, da shi da dukiyar sa mu muna can a
unguwar gidan zoo abin tausayi. Hajiya Mama kam dariya tayi sosai ta ce, "Wallahi idan namun daji sun fito a zoo ta kan ku za su fara a nan kuma sai aka yi dariya.
Ta shigo ta debo kayan sayarwa a wani kit gaba daya gwalagwalai ne ta ringa ba su zobe
su gwada kyautar su tayi musu ta ce kun zo
dan kunne ya kare, amma ga zobe."
Hajiya Maimu ta ce, "A'a wallahi ni bana
saka zoben gwal, fariya ma kenan. Ni ba 'yar kowa ba nake wanke-wanke da zinare a hannu.
Don mu yanzun Aljanna muke nema ba
wata duniya ba." Hajiya Sa'a kam sanyawa tayi tana fadin "An gode Allah ya kara arziki.
A kawo na Maman Ladifa tana gida bata zo
ba." Hajiya Mama ta ce, "Ai na bata nata tun
ranar da suka zo da Alhaji, kin san tazo ta
221Sha11
Zumunci Dangin Kauna 2 Jamila M. Danfajo
yake daukar nauyin su sabon zumuncin da ya
zamto yanzun a ka gyara.
Rayuwa ta dawo ma Hajiya Mama sabuwa, ba ruwanta da wasu matsaloli ta gyara rayuwarta da 'yan uwanta tana sana'arta kuma
abin da kishiyoyin suke so sun rasa tun suna fushi har sun hakura.
Alhajin kam gaban gidan yasa aka rushe,
wasu manyan shaguna guda uku ginin kasa da
rufin su yaso ya rufta bai ru fta din ba.
Sai manyan zaure guda biyu, da dakin baki
da wani store irin dai ginin mutanen da, yasa aka dora masa gini na zamani don sashensa aka yi da sahshen baki.
Sai wani wawakeken fili da aka fitas don parking din motoci. Gida sosai ya tsa ru don a
cikin wata ukun idan ka shigo unguwar zaka cе kayi batan kai ne.
Matan gidansa ba su san sun yi rashin hankali ba, sai da aka ce Hajiya Maman bata da lafiya suka zo gaisheta suka gani.
Daular duniyha sashenta kawai ya firgita su, don wasu irin kujeru da kayan gado da aka zuba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 13