An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
zu Bookshop
ZUMUNCI
DANGIN KAUNA
JAMILA MUHAMMAD DANFAJO
(Mrs Adam Dauda)
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
ZUMUNCI DANGIN KAUNA
arabar gidan ta kacame da hayaniyar
daukar Amarya, kowanne yana kokarin samun mota, don gaba daya lamarin a
rikice yazo musu, motocin da gidan angon suka
turo sunyi kadan saboda komai dai a cancana
yazo ma angon.
'Yammatan gidan sun yi cirko-cirko a wurin
kowacce ranta a bace, saboda ba su samu wuri
ba motoci sun yi kadan. Hajiya Magajiya ta fito
tana fadin.
"Ina 'Yanmatan gidan? Ku koma daman ai
kun je jere ba lallai sai an raka Amarya da ku ba,
ku koma."
Daya daga cikin 'yanmatan ta ce, "Gaskiya ni
Hajiya Mama ban je jere ba, don Allah su dan
matsa min a wannan Sieanna din na shiga kin ji
Hajiya Mama."
Ta fada tana kallon Hajiya, ta dan yi tsaki ta
ce, "Wai me yasa ke jaraba tayi miki yawa ne ba
kya jin magana? Uhum! Haba Goggona."
Ita kam budurwar da aka kira Goggo sai ta
kuma shagwabewa tana bata fuska ta cе,
"Saboda Allah Goggona ina abin 6acin rai?
Gobe zan sanya Yayanku Auwal ya kai ki kije
4shafi
Zumunci Danglo Kauna Jamila M. Danfajo
kiga gidan Amarya mu shiga gida, haba Goggon
Mama."
Ta sake shagwabewa cike da bata fuskа,
Goggon ta fara lallabata sai kuma ga mota ta
shigo harabar gidan da sauri Hajiya Mama ta се,
"Shi kenan ma ga Yayanku Munir nan, bari ya
kai ku na huta da jarabar nan taki."
Gaba daya suka fara murna "Ga Ya Munir!
Ga Ya Munir!! Oyoyo Ya Munir."
Can gefe ya faka motar ya fito, da kyar ya
samu hanyar shiga saboda jama'a, bai ma lura da
in da suke ba sai da ya ji oyoyon ya yi yawa
sannan ya karasa in da suke, kowacce sai fadin.
"Ya Munir ina yini?"
"Sannu da zuwa Ya Munir."
Shi dai murmushi yake yi ya durkusa har
kasa yana fadin "Hajiya Mama ina yini?" Ta yi
murmushinta hakorin Makkanta guda biyu suka
bayyana ta ce, "Sai yau? Yaya Munir."
Ya ringa shafa kansa yana dariya, ya ce,
"Wallahi Hajia Mama yanzun nan shigowata
garin, Abbanmu ya ce nazo na dauko su Hajiya
suna nan." Hajiya Maman ta ce, "To kafin su
kintsa dan raka Amarya ka dawo zan shiga na
99
gaya musu ka zo.'
5shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Ya ce, "Hajiya Mama ki manta da wannan da
wannan 'yan hayaniyar taki kin ji ko?"
Ta ce, "A'a mai sunan Mallam yi hakuri don
Allah kuje ka kai su." Ta fada tana bude 'yar
post dinta an kira wayarta.
Ya ce, "Shi kenan kun ci darajar Hajiya
Mama, amma wallahi da ki zan yi."
Ita kam Goggon Mama tana can gefe daya ta
cangala bata yi magana ba, saboda daman ba
wani shiri take yi da shi ba, ta tsani ma yadda
yake washe baki yana amsar gaisuwar 'yanmatan
gidan nasu, su kuma sai faman shiga mota suke
yi.
'Yanmatan gidan saboda daman kowacce a
gidan so take a ce da ita yake yi, don duk ranar
da ya ziyarci gidan yana shan shisshigi a wurin
su.
Yayin da iyayensu mata kowacce so take a се
da diyarta Munir yake yi, sai faman cusa masa
su ake yi, yayin da shi kuma zai yi ta zolayar su
yana faman gurza musu magana.
Don idan yaga kin matsa masa da shisshigi
idan ya yaıko ba'a ya lafta miki sai kin raina
kanki. Don haka Goggon Mama bata fiya cusa
kanta a wurinsa ba, can yake lamarinsa da su
6h
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Khuzaiman da Ilham da Ladifa da Sagira, ita
kam kishinta ba ya barinta ta sake.
Balle da matan gidan abu kadan su goranta
mata "Ke Goggon Mama idan mai sunan Mallam
ya kawo guzuri sai ki tattare ki ce ke ce za ki
raba, idan takamar ki da uwarki da uwarsa ciki
daya suka fito to ai suma 'ya'yan gidan 'yan
uwansa ne.
Tunda da ubansu da ubanku ciki daya suka
fito ba ki fi su komai a wurin sa ba, suma 'yan
uwansa ne, don haka ki gaya masa idan ya tashi
tsaraba ya yi ma kowa ledarsa, ai yasan yawan
'yanmatan gidan."
Sau da yawa idan Makaranta Maiduguri
(Unimaid) sai sun ba shi sako musamman idan
ya biyo ta gidansu ya yi musu sallama sun ringa
fadin.
"Ya Munir ka kawo mana tsarabar
Maiduguri."
"To." Yake cewa don ya ringa fadin "Kar ku
dame ni naji." ai idan daya ta sake magana zai ce
"To na fasa."
Sau da yawa ma tsarabar idan bai ga dama ba
lalle yake sayo musu kusan kwano uku ya сe
"Ke Goggon Mama raba musu."
7snati
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Idan yazo Zoo Road ya ce, Goggon Mama
idan taje unguwarsu K/Nasarawa ya ce, Goggon
Mama, don sunan Kakarsu ya ci. Sau da yawa
suna wasansu na abokan wasa.
Yafi tsokanarta ko lallan ne zai ce ke Goggon
Mama ungo raba muku, yayin da matan gidan za
su bude wuri da bala'i "Ke Goggon Hajiya,
lallan ma ke za ki raba?"
To fa ranar sai an yi rikici, don haka bata
shiga harkarsa. Sau da yawa sai a rina a goge ba
ta tanka musu ba, don haka yau ma dai an kuma.
Ya Karasa gabanta ya tsaya yana fadin, "Ke
kowa zai yi wanka ya yi kyau amma ban da ke?
Kalle ki don Allah! Ashoben nan ya yi ma kowa
amma ban da ke."
Ba ta yi magana ba, sai kumbura da tayi ta
cika fam! Ta batse, tana neman abin da zata
tanka ta rasa. Don haka sai tayi wani irin fari da
ido, ta watsa masa harara.
Ai fa! Tamkar ta birge shi. Ya lumshe ido
cike da zolaya ya bude yana kallonta cike da
burgewa ya ce, "Ai ni ban san harara ba, sai ido
ya fado dan Zakara ya dauke."
Bata yi magana ba, sai abokan Ango daya
daga cikinsu ya ce, "To ya abokina za ka rage
8 shafi
Zumung Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
S
mana ne? kaga saura a kasa." Ya fada yana
kallonsa ya ce, "Yes! Zan dan rage muku amma
ba zan dauki wannan a motana ba." Ya fada
yana fadin "Kana 6atawa kanka lokaci ne, ni
nasan wannan Gimbiyar duk wanda ya dauke ta
وو
a wurin nan zai gamu da fushinka ne.
Ya yi dariya yana bude gaban mota, ya ce
"Wallahi ba don halinta ba, ta shiga dai."
Itama cike da kumburi ta fada motar, ya
mayas ya rufe. Sagira ce sarkin tsokana ta ce
mata, "Don dai bai yaba ba."
Su Khuzaimat da sauran suka kwashe da
dariya, ransu ya musu dadi ko ba komai dai sun
san babu (soyayya) a tsakaninsu, tunda kullum a
cikin kuhse ta yake.
Goggon Mama tayi tsaki ta juyo tana
ramawa.
Та се, "То meye don ya ce ban yi kyau ba?
wallahi yarinya kin san dai nafi karfin ajin Ya Munir, don shisshigi ba kwarjini yawa ne, ni ban
ga saurayin da ya isa nayi masa shisshigi ba wallahi, never.
Ya ce, "Haba yarinya, ni ne dai nafi karfin ajinki, kije University din mu kiga yadda 'yanmata suke ji da ni wallahi, don ke dai da
9Ishati
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
nake ganinki kwaila da ke ba ki isa ba balle na
yaba."
Ba ta sake magana ba saboda yanzun ba
fuskar wasa a wurinsa. Ya daure sosai shi kuma
duk iyakar kokarinka idan har ya daure fuska
tilas ya saurara.
Don haka Goggon Mama, cike da gunguni ta
ce, "Ni ina ruwana da wani 'yammatanka can!
Ai ni idan har nayi kwalliyata Mani ya yaba ai
shi kenan."
Ya dan rage sautin Radiyonsa yana fita a get
din gidan, ya juyo yana kallonta ya ce, "Me ki ka
се?"
Ba ta yi magana ba, ya ce "Ki sake magana
mana karamar maras kunya.
Ta juyo ta watso masa kallon da ya fi so a
rayuwarsa ta juya ta ci gaba da gunguninta ya ce,
"Ai ni maganar ciki ba magana ba ce, ki fito fili
ki fada din tsoro ya hana.
Állah idan kin sake maimaita abinda da ki ka
fada din ko? Za ki yi mamaki."
Ta juyo ta kalle shi ta ce, "Mamakin me zan
yi? Ai ba wani mamaki wallahi wane dare ne
Jemage bai ba? ai sai na mutuwarsa."
10f
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Gaba daya sai dariya ta kama shi, ya yi dariya
ya yi dariya ya ce, "Lallai kam! Za'ayita.
Ke wannan 'yar yarinyar har ni za ki ce kin
ga kowane dare? Wai ma wanne da wanne daren
ki ka gani?"
Takaici ya isheta da fassarar da yake so ya yi
mata, ta ce "Wane kuwa daren wulakancinka
mana bayan shi sai me?"
Ya ce, "Eh! To ai ji nayi kina wani gunguni,
don haka kina karawa zan bude motar nan ki
fada kwalta nayi wucewata, tunda ke dai har
kina jin kanki your matual ni za ki yi ma zancen
wani kazamin saurayinki kucaki kawai."
Ita dai bata sake magana ba, saboda gaba
daya dariya su Sagira da Ladifa suke yi mata.
Don haka taja bakinta tayi shiru har aka iso
gidan Amarya suka shiga wurin Yaya Adama
suna mata Allah sanya alkairi.
Ango ya rako su har gaban mota, ya juya a
hanya kam bai kula su ba, wakar Nura M. Inuwa
yake saurare da ya yi a kan so, yana faman sauri.
Sun yi kusa da gida sai mota ta dume da
warin tusa gaba daya ya zuge gilasan yana
kallon su yayin da ya tsayar da motar ya fice.
11 shafi
1
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Yana fadin "Waye ya yi mini tusa a mota?"
duk suka yi shiru, ya kare musu zagi ba wadda ta
tanka, ya yi tsaki.
Ya ce, "Tsiyar mota kenan, idan ba dealay
suka yi ba to tusa a mota, ya juyo yana yi ma
Goggon Mama tsiya, ganin ta sha mur! Tayi
wani kicin-kicin da ita.
Suna hada ido ya ce, "To ko ke ce ne ki ka yi
tusar nan?" Ta sake watsa masa harara, sai dai
wannan karon jikinta ya yi sanyi ta daure ta ce,
"Duk motar nan ni ka raina?"
99 Ya ce, "Eh."
Idonta ya cicciko da kwalla lokaci daya,
hankalinta ya tashi duk da warin tusar ya bar
motar amma sai ta ringa tunano warin tusar.
Ace wannan tusarta ce ai an cuce ta, tuni ta
6alle murfin motar ta yi ficewar ta a motar.
Da shi ke sun yi kusan isa gida, da kafarta ta
karasa fuskar nan ba annuri, ta ci kuka ta koshi,
kana ganinta ka san ba dan karamin kuka tayi
ba.
Na mota ya riga na kafa, don haka suna shiga
gidan suka fara tambayar "Ina Goggon Mama?"
Mama ta kalle su ta ce, "Ku fita tare ku zo kuna
tambayata ita? Ina ku ka barta?" Ta fada tana
12
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
kallonsu dukkansu su ka kwashe da dariya. Ta
kalli Munir ta ce, "Mai sunan Mallam ya haka?
Naga kana dariyar muguntar taka?"
Ya ce, "Yanzun za ki ganta ki kwantar da
hankalinki Mama zata shigo."
Ana cikin wannan hira sai ga Goggon Maman
ta shigo tana faman goge ido da mayafinta, ta shiga suka kwashe da dariya.
Ta isa wurin Maman ta zauna a gefen
Maman, Maman ta ce, "Wai menene ku ke
dariya? Me aka yi Goggone?"
Tayi shiru tana ba66ata rai, Maman ta се
"Wai meye ne? kiyi magana mana?"
Sai ta kwanta cinyar Maman ta fashe da kuka,
yayin da Khuzaimatu suka ringa barin wurin
Yaya Muni yana musu nuni su fice.
Ummansa ta ce, "Wai ba za ku yi magana ba
ne?"
Ya dan kalli Goggon Mama don ita ma a
lokacin sai faman goge fuska take yi.
Ya ce, "Goggon Mama na fada?"
Cikin kuka da fusata ta ce, "Ka fada din
mana, idan ka fada ma meye?"
Ya yi dariyar mugunta ya dauki 'yar gidan
Anty Mairo ya fice yana fadin.
13 sha!i
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
"Umma kuyi sauri ku fito mu tafi dare ya
fara. Ke kuma Goggon Mama na rufa asiri ba
miki asiri ba don halinki ba."
Ta sake fashewa da kuka ta ce, "Ka fada din
mana sai me?"
Maman ta dan bugeta a baki ta ce, "Ke ni
bana son rashin kunya, kiyi mini shiru mai sunan
Mallam din ne ki ke son ki zage shi?"
Cikin kuka ta ce, "To Mama kina ganin yadda
ya tsane ni? Ya takura mini ya hana ni sakat da
rayuwata, ni kadai ce mutum a gidan nan da
kullum sai ya nemi ya wulakanta ni?"
A fusace Maman ta ce, "Ya wulakanta kin,
maras mutunci. Ko kiyi mini shiru ko nayi
maganinki yanzun nan.” Ta ci gaba da kukanta
sosai, Maman na zaginta.
Ta matsa kusan Ummansa ta ce, "Umma kin
gani ko? Kiyi mini tsakani da Yaya Munir."
Umman ta ce, "Ni? Haba Goggona, wane irin
tsakani? Idan nayi muku tsakani kuma waye mai
rike min ke wata rana idan bana duniyar? Yi
hakuri da dan uwanki kin ji ko?"
Cikin kuka ta ce, "To ni Umma wani irin
hakuri, kina kallo fa sai ya kalli idonna ya yi
mini dariyar mugunta ya ce mini wai na fada?"
14 hafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Umman ta fusata tana kallonsa ta ce, "Wai
me za ka fada? To fadi man ko ma meye?"
Ya ce, "Kyaleta dai Umma, kyale ta don
Allah, na rufa mata asiri ko na fadi Goggon su?
Don mu ba Goggonmu ba ce, Goggon su ce ko
na fada?"
Та се, "Eh! Ka fada din." Ya wuce yana
fadin "A dai rufa miki asiri ba don halinki ba." ta
shiga daki da gudu, tana ganin tana ji suka fice
suka tafi.
Da safe ita da 'yan uwan shi kenan ba a
magana gashi ya gargade su kar wanda ya fada.
Sai ya zamto ya samu lagonta, kullum suka
hadu sai ya tsokane ta, tayi ta fadin na fada
Goggo? Ta ce, "Eh! Fadi din ko tayi masa
banza.
Sau da yawa din ma idan ya matsa banza take
yi masa, ko kuma ya yi ta yi mata.
To wane dare ne Jemage bai gani ba? tilas ta
gudu ta bar shi, don bai dauki abin wasa ba
sosai, ya samu ya takura mata don idan tana
tsakar gida sai ya san yadda ya yi ya tsokaneta.
Yayin da ita kuma daga ya fara irin hakan sai
ta fada dakin Maman ta 6uya abinta sai ya tafi ta
fito.
15 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
TUSHEN LABARIN
Gidan Alhaji Usman Osese Soron Dinki,
yana nan a (Zoo Road), gida ne katon gida mai
kunshe da mata hudu na aure, don haka gidan
yake cike da Jama'a kala daban-daban.
Matarsa ta farko Hajiya Magajiya, wadda
suka fi kira da Hajiya Mama, ita ce uwargida.
Kusan manyan 'ya'yanta duk mata ne su
hudu, an yi musu aure kusan ma jikokinta
yanzun ake aure don babbar mace ce.
Danta babban bai dade da aure ba Nabil,
yaransa uku, shi ne na biyu, Yayarsa Nabila sai
Mairo, sai Nafisa 'ya'yanta kusan su tara ne
amma wannan su ne ma su aure sai 'yan bayansu
autar dai Goggo ce.
Ita ce aka sanya sunan uwarta, uwar goyon
mijinta Hajiya Goggon Soron dinki, don haka
suka fi kiran ta da Goggon Maman.
Goggon Soron dinki ita ce Yayar uban su
Alhaji Osese da kaninsa Alhaji Ahmad, ita ce ta
aurar da su kuma duk 'ya'yanta ta aurawa Alhaji
Usman.
Ta aura masa Magajiya mai sunan uwarsa, sai
kuma Alhaji Ahmad ta aura masa Rabi'a. Dalilin
16snafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
rikonta da wannan Alhazai mutuwar uwar su
matar kaninta, don haka ta rike su amana.
Goggo mace ce mai zumunci sosai, tana son
'ya'yan 'yan uwanta so maras misali, lokacin a
ta karbi rikonsu uwarsu ta mutu kuma ita kadai
ce Alhaji Yakubu yake da ita (dan uwanta kenan).
Lokacin yana bin mahaifinsu yawon fatauci
kawo goro daga Shagamyu zuwa Kurmi, a
lokacin manyan runfuna gare su. Bayan mutuwar mahaifinsu tayi masa aure,
matarsa daya rak! Ta haifa masa yara biyu maza da Usman da Ahmad ta mutu ta bar masa su.
Ba shi da mai rikewa, tilas Yayarsa ta amsa ta rike masa, suka hada kansu, wanda daman ba a
ganin tsakaninsu tun asali.
Hatta da gadonta a hannunsa ba ta amsa ba ta
ce ya ci gaba da juya musu, da ta haifi diyarta
ma Khadija ta sanya sunan matar dan uwanta,
suke kiranta (Magajiya).
Bayan mutuwar dan uwanta, ta shiga halin
tashin hankali da juyayi na rashin sa, a lokacin
bai sake aure ba tun bayan mutuwar matarsa Khadija. Ya ci gaba da kula da yaransa, daga
Makaranta sai kasuwa, don suna kammala
17 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Sakandire da wuri suka dora da Difiloma,
Goggonsu na kula da su sosai.
Ita a lokacin da Alhaji Yakubu ya mutu, as
lokacin itama Goggon yaranta biyu da Magajiya
mai sunan matar kaninta sai kanwarta Rabi'a.
Don haka da lokacin auren Magajiya ya taso
sai ta hadata da Usman, ya yi gini a (Zoo Road)
ya koma.
Bayan shekara takwas shima Ahmad ta hada
shi da Rabi'a, aka yi bikinsu, Alhaji Usman din
ya yi masa gini a Kofar Nassarawa ya tare da
matarsa cikin zaman lafiya da kwanciyar
hankali.
Yaran Magajiya shida, Alhaji Usman ya kara
aure ya auro Hajiya Maimuna mace mai iya
kisisina, mutuniyar Gwarzo.
Da kanwasrta tazo ta ganin kanwar Magajiya
ke auren kanin mijinta Alhaji Ahmad, sai da ta
shiga ta fita tayi munafuncin da ya auri kanwarta
Binta.
Don haka zaman ya ki dadi, kishi ya yi
tsanani a family din, don ma Hajiya Magajiya na
kawar da kai, kuma ta nuna halin dattako a cikin
gidan. Ba ta yadda rigima ta fito, ko sun kullota
tasan yadda zata yi ta maida abin wasa, ba tare
18 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
da an yi tashin hankali ba (to Bakanuwa ce ta asali fa). Sau da yawa idan rikici ya balle ita ce
take hana komai, daga na gidan kanwarta har na gidan kaninta.
Shi kam Alhaji Usman ya dauki girma ya bata, ba ya yadda a raina Hajiya (Magajiya), ko menene ita ce ta ke tsarawa.
Ko 'yan tafiya Makka ya ce ta fitar tilas zata
sanya Goggonsu ta sanya uban Hajiya Maimuna, ko uwarsu amma bata fita arzikin mijinta ne ya tsole musu ido.
Wanda a ka tara shi da gadon uwarsu, amma bata taba nuna masa ba, balle ta nuna a bai wa Goggo gadonta.
Komai ta kauda kai, shekarar da arzikin ya bunkasa sosai shekarar ya kara aure, wannan karon Balarabiya ya auro a kasar Egypt birnin Misira.
Ita ma kuma tazo da sa'a, haihuwar farko ma tagwaye a lokacin 'ya'yan Hajiya Maimuna biyu, a nan fa kishi ya koma kan Balarabiya, ake faman bugawa, tun bata iya ba sai da aka kure ta. Rayuwa kenan, a kwana a tashi lamari ya bunkasa, shi ma Alhaji Ahmad ya kara aure
matansa uku, a shekarar Goggon ta rasu.
19 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Don tuni babban dan Rabi'a mai sunan
Mallam ya girma sosai yana Sakandire.
Yayin da a lokacin Yaya Nabil ya gama
Jami'a a fannin kasuwanci, yana shirin tafiya
bautar kasa Goggon ta mutu.
Tilas aka fitar da dukiyar Goggo a ka bai wa
yaranta, Rabi'a da Magajiya ba bata lokaci suka
danka dukiyar a hannun Nabil.
Yana gama bautar kasa ya fada kasuwanci,
sai kuma al'amari ya mike, sosai ya ke fita waje
yake musu business don ita ma Hajiya Rabi'a
din bata karbi ko sisi a ciki ba.
Gaba daya ta bayar ta juya musu, lokacin a
Nabil ya yi shirin auren farko al'amasrin yazo da
sauyi kala-kala.
A lokacin Babansa ya karo mace ta hudu,
Hajiya Sa'ade wadda diya ce ga Hajiya sa'ade
da ubanta ya mutu ya barta da dukiya mai tarin
yawa, abokin su Alhaji Usman din ne.
Da farko Hajiya Sa'ade ta shige sukut
karkashin Hajiya Magajiya, sai da aka yi auren
diyarta da babban dan gidan Nabil gaba daya
suka janye shi da shi da dukiyarsa, tilas Hajiya ta
zamo 'yar kallo.
20shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Can Alhaji Ahmad din ma hakan take, ya yi Amaryar sai dai shi kanwar abokinsa ce matan gidansa hudu ne cif!
Don haka gidajen ya cika da 'ya'ya maza da
mata, kowanne yana ban wuri a harkar ilimi da kasuwanci.
BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYAR
Tuni Munir ya gama Masters digree a wannan lokacin, Alhaji Usman yara uku ya sanya lalle ya yi musu aure 'yammata.
Don babban Yayansu Nabil tuni yaransa biyu,
a ranar Munir ya iso daga Maiduguri don samun daurin aure. Bai iske ba sai ya 6ige da kai 'yammata rakiyar amarya.
Kusan kowacce budurwa a gidan Alhaji
Usman din, so take yi ace ita ce Munir yake yi
da ita, don idan ya iso gidan kowacce sai ta
canza kwalliya a iske shi falon baki a yi ta faman kwarkwasa.
Ita kam Goggon Mama ba ta kula su, kullum
tsakaninsu da tsakuwa sau da yawa zai tsare ta
da ido yasha mur ya ce mata.
"Ke Goggon su Umma ba ki da kirki ko?
Kowa yazo ya gaishe ni ban da ke ko?"
21 Ishafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Kallonsa take ta watsar ta ce, "To gaisuwar
nawa ce? Ba na gaishe ka ba ne tun dadewa?"
Ya ce, "Yaushe ne tun dadewar?" Sai ta
kuma kallonshi ta watsar ta ce, "Tun shigowar ka
mana, ko kai kurma ne?"
Duk da kallon dadi yake yi masa amma sai ya
doke ta ko ya kai mata hari, idan ta dan fara
gudu yasa mata kafa ta fadi a yi ta rikici.
Goggo ta ce, "Bangane me ka ke nufi ba mai
sunan Mallam? Kullum ka zo gidan nan sai ka ci
zalin uwar nan tawa, don dai zalinci kawai. To
ba ta sonka a kai kasuwa."
Dariya yake ya ce, "Haba Hajiya Mama, duk
'yammatan gidan nan? Ki kalli fa har da
Larabawa, me zan yi da ita?"
Goggon ta ce, "Ai ko kana yi da ita ba na
baka tun yanzun ana yin irin wannan cutar, idan
an kwana biyu na baka ita ai zubar mini ita zaka
yi a bola bayan ka karairayata ka watsar."
Dariya yake yi sosai, ya ce "Wallahi Hajiya
Mama kin gano, ke dai bari."
Itama dariya Hajiya Maman take yi, ta ce "To
ai dai ga irinta nan, ka fada za ka auri Indiya ma
amma ban da uwar nan tawa da sai mai Jirgin
وو
sama.
22 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
Idan ta fadi hada dariya ake yi sosai a gidan.
Irin wannan yana yi ma su Hajiya Maimuna
Jadi da Hajiya Sa'ade, su miko baki ayi tayi don
Balarabiyar bata shiga shirginsu.
"Lalle mai sunan Mallam da gaske ka ke, yo
kai da gida duk 'yammata ka zabi ka darje ga kasuwar farare na ci yaushe za ka bata lokacinka
a kasuwar ma su kalasr duhu.
Farin wankan tarwada ai an daina yayınsa, an
fari tas! Shi ne magana."
Munir ya ce, "Wannan kuma haka ne, 'Ummansu Khuzaimat bari dai nayi screening.
Ina 'yammatan gidan suke? Duk ku fito, kuna
karbe mini lalle ban ga kuna kwalliyar lallen ba, duk ku fito na gani wacce ta fito zan zaba."
Abin kamar zuga, kowacce zata ci kwalliya ta fito su hudu, ya kalli wannan ya ce ta gabza hoda, ya kalli wancan ya kwashe mata da dariya,
ya ce (Tunkiya ta dumbuji gari), janbaki ya yi yawa.
Ya ce wannan ta fiya gajarta tun a nan yake
nuna ba ya so. Sagira da Ladifa ya ce sun yi siririya da yawa, Khuzai ce mai gabza hoda, ya ce ban da mai hoda ban da siririya sosai ban da
23 |shafi
Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo
gajera, ban da mai yawan dariya, ga wannan
halin naku da ku ka yi min a mota.
Gaba daya su kwashi ihu.
"A'a Yaya wane irin abu? Wane irin abu ba а
yin haka, ba a haka."
Ya ce, "Halinkun nan? Wannan halin da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 13