Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels zu Bookshop ZUMUNCI DANGIN KAUNA JAMILA MUHAMMAD DANFAJO (Mrs Adam Dauda) Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo ZUMUNCI DANGIN KAUNA arabar gidan ta kacame da hayaniyar daukar Amarya, kowanne yana kokarin samun mota, don gaba daya lamarin a rikice yazo musu, motocin da gidan angon suka turo sunyi kadan saboda komai dai a cancana yazo ma angon. 'Yammatan gidan sun yi cirko-cirko a wurin kowacce ranta a bace, saboda ba su samu wuri ba motoci sun yi kadan. Hajiya Magajiya ta fito tana fadin. "Ina 'Yanmatan gidan? Ku koma daman ai kun je jere ba lallai sai an raka Amarya da ku ba, ku koma." Daya daga cikin 'yanmatan ta ce, "Gaskiya ni Hajiya Mama ban je jere ba, don Allah su dan matsa min a wannan Sieanna din na shiga kin ji Hajiya Mama." Ta fada tana kallon Hajiya, ta dan yi tsaki ta ce, "Wai me yasa ke jaraba tayi miki yawa ne ba kya jin magana? Uhum! Haba Goggona." Ita kam budurwar da aka kira Goggo sai ta kuma shagwabewa tana bata fuska ta cе, "Saboda Allah Goggona ina abin 6acin rai? Gobe zan sanya Yayanku Auwal ya kai ki kije 4shafi Zumunci Danglo Kauna Jamila M. Danfajo kiga gidan Amarya mu shiga gida, haba Goggon Mama." Ta sake shagwabewa cike da bata fuskа, Goggon ta fara lallabata sai kuma ga mota ta shigo harabar gidan da sauri Hajiya Mama ta се, "Shi kenan ma ga Yayanku Munir nan, bari ya kai ku na huta da jarabar nan taki." Gaba daya suka fara murna "Ga Ya Munir! Ga Ya Munir!! Oyoyo Ya Munir." Can gefe ya faka motar ya fito, da kyar ya samu hanyar shiga saboda jama'a, bai ma lura da in da suke ba sai da ya ji oyoyon ya yi yawa sannan ya karasa in da suke, kowacce sai fadin. "Ya Munir ina yini?" "Sannu da zuwa Ya Munir." Shi dai murmushi yake yi ya durkusa har kasa yana fadin "Hajiya Mama ina yini?" Ta yi murmushinta hakorin Makkanta guda biyu suka bayyana ta ce, "Sai yau? Yaya Munir." Ya ringa shafa kansa yana dariya, ya ce, "Wallahi Hajia Mama yanzun nan shigowata garin, Abbanmu ya ce nazo na dauko su Hajiya suna nan." Hajiya Maman ta ce, "To kafin su kintsa dan raka Amarya ka dawo zan shiga na 99 gaya musu ka zo.' 5shafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Ya ce, "Hajiya Mama ki manta da wannan da wannan 'yan hayaniyar taki kin ji ko?" Ta ce, "A'a mai sunan Mallam yi hakuri don Allah kuje ka kai su." Ta fada tana bude 'yar post dinta an kira wayarta. Ya ce, "Shi kenan kun ci darajar Hajiya Mama, amma wallahi da ki zan yi." Ita kam Goggon Mama tana can gefe daya ta cangala bata yi magana ba, saboda daman ba wani shiri take yi da shi ba, ta tsani ma yadda yake washe baki yana amsar gaisuwar 'yanmatan gidan nasu, su kuma sai faman shiga mota suke yi. 'Yanmatan gidan saboda daman kowacce a gidan so take a ce da ita yake yi, don duk ranar da ya ziyarci gidan yana shan shisshigi a wurin su. Yayin da iyayensu mata kowacce so take a се da diyarta Munir yake yi, sai faman cusa masa su ake yi, yayin da shi kuma zai yi ta zolayar su yana faman gurza musu magana. Don idan yaga kin matsa masa da shisshigi idan ya yaıko ba'a ya lafta miki sai kin raina kanki. Don haka Goggon Mama bata fiya cusa kanta a wurinsa ba, can yake lamarinsa da su 6h Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Khuzaiman da Ilham da Ladifa da Sagira, ita kam kishinta ba ya barinta ta sake. Balle da matan gidan abu kadan su goranta mata "Ke Goggon Mama idan mai sunan Mallam ya kawo guzuri sai ki tattare ki ce ke ce za ki raba, idan takamar ki da uwarki da uwarsa ciki daya suka fito to ai suma 'ya'yan gidan 'yan uwansa ne. Tunda da ubansu da ubanku ciki daya suka fito ba ki fi su komai a wurin sa ba, suma 'yan uwansa ne, don haka ki gaya masa idan ya tashi tsaraba ya yi ma kowa ledarsa, ai yasan yawan 'yanmatan gidan." Sau da yawa idan Makaranta Maiduguri (Unimaid) sai sun ba shi sako musamman idan ya biyo ta gidansu ya yi musu sallama sun ringa fadin. "Ya Munir ka kawo mana tsarabar Maiduguri." "To." Yake cewa don ya ringa fadin "Kar ku dame ni naji." ai idan daya ta sake magana zai ce "To na fasa." Sau da yawa ma tsarabar idan bai ga dama ba lalle yake sayo musu kusan kwano uku ya сe "Ke Goggon Mama raba musu." 7snati Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Idan yazo Zoo Road ya ce, Goggon Mama idan taje unguwarsu K/Nasarawa ya ce, Goggon Mama, don sunan Kakarsu ya ci. Sau da yawa suna wasansu na abokan wasa. Yafi tsokanarta ko lallan ne zai ce ke Goggon Mama ungo raba muku, yayin da matan gidan za su bude wuri da bala'i "Ke Goggon Hajiya, lallan ma ke za ki raba?" To fa ranar sai an yi rikici, don haka bata shiga harkarsa. Sau da yawa sai a rina a goge ba ta tanka musu ba, don haka yau ma dai an kuma. Ya Karasa gabanta ya tsaya yana fadin, "Ke kowa zai yi wanka ya yi kyau amma ban da ke? Kalle ki don Allah! Ashoben nan ya yi ma kowa amma ban da ke." Ba ta yi magana ba, sai kumbura da tayi ta cika fam! Ta batse, tana neman abin da zata tanka ta rasa. Don haka sai tayi wani irin fari da ido, ta watsa masa harara. Ai fa! Tamkar ta birge shi. Ya lumshe ido cike da zolaya ya bude yana kallonta cike da burgewa ya ce, "Ai ni ban san harara ba, sai ido ya fado dan Zakara ya dauke." Bata yi magana ba, sai abokan Ango daya daga cikinsu ya ce, "To ya abokina za ka rage 8 shafi Zumung Dangin Kauna Jamila M. Danfajo S mana ne? kaga saura a kasa." Ya fada yana kallonsa ya ce, "Yes! Zan dan rage muku amma ba zan dauki wannan a motana ba." Ya fada yana fadin "Kana 6atawa kanka lokaci ne, ni nasan wannan Gimbiyar duk wanda ya dauke ta وو a wurin nan zai gamu da fushinka ne. Ya yi dariya yana bude gaban mota, ya ce "Wallahi ba don halinta ba, ta shiga dai." Itama cike da kumburi ta fada motar, ya mayas ya rufe. Sagira ce sarkin tsokana ta ce mata, "Don dai bai yaba ba." Su Khuzaimat da sauran suka kwashe da dariya, ransu ya musu dadi ko ba komai dai sun san babu (soyayya) a tsakaninsu, tunda kullum a cikin kuhse ta yake. Goggon Mama tayi tsaki ta juyo tana ramawa. Та се, "То meye don ya ce ban yi kyau ba? wallahi yarinya kin san dai nafi karfin ajin Ya Munir, don shisshigi ba kwarjini yawa ne, ni ban ga saurayin da ya isa nayi masa shisshigi ba wallahi, never. Ya ce, "Haba yarinya, ni ne dai nafi karfin ajinki, kije University din mu kiga yadda 'yanmata suke ji da ni wallahi, don ke dai da 9Ishati Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo nake ganinki kwaila da ke ba ki isa ba balle na yaba." Ba ta sake magana ba saboda yanzun ba fuskar wasa a wurinsa. Ya daure sosai shi kuma duk iyakar kokarinka idan har ya daure fuska tilas ya saurara. Don haka Goggon Mama, cike da gunguni ta ce, "Ni ina ruwana da wani 'yammatanka can! Ai ni idan har nayi kwalliyata Mani ya yaba ai shi kenan." Ya dan rage sautin Radiyonsa yana fita a get din gidan, ya juyo yana kallonta ya ce, "Me ki ka се?" Ba ta yi magana ba, ya ce "Ki sake magana mana karamar maras kunya. Ta juyo ta watso masa kallon da ya fi so a rayuwarsa ta juya ta ci gaba da gunguninta ya ce, "Ai ni maganar ciki ba magana ba ce, ki fito fili ki fada din tsoro ya hana. Állah idan kin sake maimaita abinda da ki ka fada din ko? Za ki yi mamaki." Ta juyo ta kalle shi ta ce, "Mamakin me zan yi? Ai ba wani mamaki wallahi wane dare ne Jemage bai ba? ai sai na mutuwarsa." 10f Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Gaba daya sai dariya ta kama shi, ya yi dariya ya yi dariya ya ce, "Lallai kam! Za'ayita. Ke wannan 'yar yarinyar har ni za ki ce kin ga kowane dare? Wai ma wanne da wanne daren ki ka gani?" Takaici ya isheta da fassarar da yake so ya yi mata, ta ce "Wane kuwa daren wulakancinka mana bayan shi sai me?" Ya ce, "Eh! To ai ji nayi kina wani gunguni, don haka kina karawa zan bude motar nan ki fada kwalta nayi wucewata, tunda ke dai har kina jin kanki your matual ni za ki yi ma zancen wani kazamin saurayinki kucaki kawai." Ita dai bata sake magana ba, saboda gaba daya dariya su Sagira da Ladifa suke yi mata. Don haka taja bakinta tayi shiru har aka iso gidan Amarya suka shiga wurin Yaya Adama suna mata Allah sanya alkairi. Ango ya rako su har gaban mota, ya juya a hanya kam bai kula su ba, wakar Nura M. Inuwa yake saurare da ya yi a kan so, yana faman sauri. Sun yi kusa da gida sai mota ta dume da warin tusa gaba daya ya zuge gilasan yana kallon su yayin da ya tsayar da motar ya fice. 11 shafi 1 Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Yana fadin "Waye ya yi mini tusa a mota?" duk suka yi shiru, ya kare musu zagi ba wadda ta tanka, ya yi tsaki. Ya ce, "Tsiyar mota kenan, idan ba dealay suka yi ba to tusa a mota, ya juyo yana yi ma Goggon Mama tsiya, ganin ta sha mur! Tayi wani kicin-kicin da ita. Suna hada ido ya ce, "To ko ke ce ne ki ka yi tusar nan?" Ta sake watsa masa harara, sai dai wannan karon jikinta ya yi sanyi ta daure ta ce, "Duk motar nan ni ka raina?" 99 Ya ce, "Eh." Idonta ya cicciko da kwalla lokaci daya, hankalinta ya tashi duk da warin tusar ya bar motar amma sai ta ringa tunano warin tusar. Ace wannan tusarta ce ai an cuce ta, tuni ta 6alle murfin motar ta yi ficewar ta a motar. Da shi ke sun yi kusan isa gida, da kafarta ta karasa fuskar nan ba annuri, ta ci kuka ta koshi, kana ganinta ka san ba dan karamin kuka tayi ba. Na mota ya riga na kafa, don haka suna shiga gidan suka fara tambayar "Ina Goggon Mama?" Mama ta kalle su ta ce, "Ku fita tare ku zo kuna tambayata ita? Ina ku ka barta?" Ta fada tana 12 Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo kallonsu dukkansu su ka kwashe da dariya. Ta kalli Munir ta ce, "Mai sunan Mallam ya haka? Naga kana dariyar muguntar taka?" Ya ce, "Yanzun za ki ganta ki kwantar da hankalinki Mama zata shigo." Ana cikin wannan hira sai ga Goggon Maman ta shigo tana faman goge ido da mayafinta, ta shiga suka kwashe da dariya. Ta isa wurin Maman ta zauna a gefen Maman, Maman ta ce, "Wai menene ku ke dariya? Me aka yi Goggone?" Tayi shiru tana ba66ata rai, Maman ta се "Wai meye ne? kiyi magana mana?" Sai ta kwanta cinyar Maman ta fashe da kuka, yayin da Khuzaimatu suka ringa barin wurin Yaya Muni yana musu nuni su fice. Ummansa ta ce, "Wai ba za ku yi magana ba ne?" Ya dan kalli Goggon Mama don ita ma a lokacin sai faman goge fuska take yi. Ya ce, "Goggon Mama na fada?" Cikin kuka da fusata ta ce, "Ka fada din mana, idan ka fada ma meye?" Ya yi dariyar mugunta ya dauki 'yar gidan Anty Mairo ya fice yana fadin. 13 sha!i Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo "Umma kuyi sauri ku fito mu tafi dare ya fara. Ke kuma Goggon Mama na rufa asiri ba miki asiri ba don halinki ba." Ta sake fashewa da kuka ta ce, "Ka fada din mana sai me?" Maman ta dan bugeta a baki ta ce, "Ke ni bana son rashin kunya, kiyi mini shiru mai sunan Mallam din ne ki ke son ki zage shi?" Cikin kuka ta ce, "To Mama kina ganin yadda ya tsane ni? Ya takura mini ya hana ni sakat da rayuwata, ni kadai ce mutum a gidan nan da kullum sai ya nemi ya wulakanta ni?" A fusace Maman ta ce, "Ya wulakanta kin, maras mutunci. Ko kiyi mini shiru ko nayi maganinki yanzun nan.” Ta ci gaba da kukanta sosai, Maman na zaginta. Ta matsa kusan Ummansa ta ce, "Umma kin gani ko? Kiyi mini tsakani da Yaya Munir." Umman ta ce, "Ni? Haba Goggona, wane irin tsakani? Idan nayi muku tsakani kuma waye mai rike min ke wata rana idan bana duniyar? Yi hakuri da dan uwanki kin ji ko?" Cikin kuka ta ce, "To ni Umma wani irin hakuri, kina kallo fa sai ya kalli idonna ya yi mini dariyar mugunta ya ce mini wai na fada?" 14 hafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Umman ta fusata tana kallonsa ta ce, "Wai me za ka fada? To fadi man ko ma meye?" Ya ce, "Kyaleta dai Umma, kyale ta don Allah, na rufa mata asiri ko na fadi Goggon su? Don mu ba Goggonmu ba ce, Goggon su ce ko na fada?" Та се, "Eh! Ka fada din." Ya wuce yana fadin "A dai rufa miki asiri ba don halinki ba." ta shiga daki da gudu, tana ganin tana ji suka fice suka tafi. Da safe ita da 'yan uwan shi kenan ba a magana gashi ya gargade su kar wanda ya fada. Sai ya zamto ya samu lagonta, kullum suka hadu sai ya tsokane ta, tayi ta fadin na fada Goggo? Ta ce, "Eh! Fadi din ko tayi masa banza. Sau da yawa din ma idan ya matsa banza take yi masa, ko kuma ya yi ta yi mata. To wane dare ne Jemage bai gani ba? tilas ta gudu ta bar shi, don bai dauki abin wasa ba sosai, ya samu ya takura mata don idan tana tsakar gida sai ya san yadda ya yi ya tsokaneta. Yayin da ita kuma daga ya fara irin hakan sai ta fada dakin Maman ta 6uya abinta sai ya tafi ta fito. 15 |shafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo TUSHEN LABARIN Gidan Alhaji Usman Osese Soron Dinki, yana nan a (Zoo Road), gida ne katon gida mai kunshe da mata hudu na aure, don haka gidan yake cike da Jama'a kala daban-daban. Matarsa ta farko Hajiya Magajiya, wadda suka fi kira da Hajiya Mama, ita ce uwargida. Kusan manyan 'ya'yanta duk mata ne su hudu, an yi musu aure kusan ma jikokinta yanzun ake aure don babbar mace ce. Danta babban bai dade da aure ba Nabil, yaransa uku, shi ne na biyu, Yayarsa Nabila sai Mairo, sai Nafisa 'ya'yanta kusan su tara ne amma wannan su ne ma su aure sai 'yan bayansu autar dai Goggo ce. Ita ce aka sanya sunan uwarta, uwar goyon mijinta Hajiya Goggon Soron dinki, don haka suka fi kiran ta da Goggon Maman. Goggon Soron dinki ita ce Yayar uban su Alhaji Osese da kaninsa Alhaji Ahmad, ita ce ta aurar da su kuma duk 'ya'yanta ta aurawa Alhaji Usman. Ta aura masa Magajiya mai sunan uwarsa, sai kuma Alhaji Ahmad ta aura masa Rabi'a. Dalilin 16snafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo rikonta da wannan Alhazai mutuwar uwar su matar kaninta, don haka ta rike su amana. Goggo mace ce mai zumunci sosai, tana son 'ya'yan 'yan uwanta so maras misali, lokacin a ta karbi rikonsu uwarsu ta mutu kuma ita kadai ce Alhaji Yakubu yake da ita (dan uwanta kenan). Lokacin yana bin mahaifinsu yawon fatauci kawo goro daga Shagamyu zuwa Kurmi, a lokacin manyan runfuna gare su. Bayan mutuwar mahaifinsu tayi masa aure, matarsa daya rak! Ta haifa masa yara biyu maza da Usman da Ahmad ta mutu ta bar masa su. Ba shi da mai rikewa, tilas Yayarsa ta amsa ta rike masa, suka hada kansu, wanda daman ba a ganin tsakaninsu tun asali. Hatta da gadonta a hannunsa ba ta amsa ba ta ce ya ci gaba da juya musu, da ta haifi diyarta ma Khadija ta sanya sunan matar dan uwanta, suke kiranta (Magajiya). Bayan mutuwar dan uwanta, ta shiga halin tashin hankali da juyayi na rashin sa, a lokacin bai sake aure ba tun bayan mutuwar matarsa Khadija. Ya ci gaba da kula da yaransa, daga Makaranta sai kasuwa, don suna kammala 17 |shafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Sakandire da wuri suka dora da Difiloma, Goggonsu na kula da su sosai. Ita a lokacin da Alhaji Yakubu ya mutu, as lokacin itama Goggon yaranta biyu da Magajiya mai sunan matar kaninta sai kanwarta Rabi'a. Don haka da lokacin auren Magajiya ya taso sai ta hadata da Usman, ya yi gini a (Zoo Road) ya koma. Bayan shekara takwas shima Ahmad ta hada shi da Rabi'a, aka yi bikinsu, Alhaji Usman din ya yi masa gini a Kofar Nassarawa ya tare da matarsa cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Yaran Magajiya shida, Alhaji Usman ya kara aure ya auro Hajiya Maimuna mace mai iya kisisina, mutuniyar Gwarzo. Da kanwasrta tazo ta ganin kanwar Magajiya ke auren kanin mijinta Alhaji Ahmad, sai da ta shiga ta fita tayi munafuncin da ya auri kanwarta Binta. Don haka zaman ya ki dadi, kishi ya yi tsanani a family din, don ma Hajiya Magajiya na kawar da kai, kuma ta nuna halin dattako a cikin gidan. Ba ta yadda rigima ta fito, ko sun kullota tasan yadda zata yi ta maida abin wasa, ba tare 18 |shafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo da an yi tashin hankali ba (to Bakanuwa ce ta asali fa). Sau da yawa idan rikici ya balle ita ce take hana komai, daga na gidan kanwarta har na gidan kaninta. Shi kam Alhaji Usman ya dauki girma ya bata, ba ya yadda a raina Hajiya (Magajiya), ko menene ita ce ta ke tsarawa. Ko 'yan tafiya Makka ya ce ta fitar tilas zata sanya Goggonsu ta sanya uban Hajiya Maimuna, ko uwarsu amma bata fita arzikin mijinta ne ya tsole musu ido. Wanda a ka tara shi da gadon uwarsu, amma bata taba nuna masa ba, balle ta nuna a bai wa Goggo gadonta. Komai ta kauda kai, shekarar da arzikin ya bunkasa sosai shekarar ya kara aure, wannan karon Balarabiya ya auro a kasar Egypt birnin Misira. Ita ma kuma tazo da sa'a, haihuwar farko ma tagwaye a lokacin 'ya'yan Hajiya Maimuna biyu, a nan fa kishi ya koma kan Balarabiya, ake faman bugawa, tun bata iya ba sai da aka kure ta. Rayuwa kenan, a kwana a tashi lamari ya bunkasa, shi ma Alhaji Ahmad ya kara aure matansa uku, a shekarar Goggon ta rasu. 19 |shafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Don tuni babban dan Rabi'a mai sunan Mallam ya girma sosai yana Sakandire. Yayin da a lokacin Yaya Nabil ya gama Jami'a a fannin kasuwanci, yana shirin tafiya bautar kasa Goggon ta mutu. Tilas aka fitar da dukiyar Goggo a ka bai wa yaranta, Rabi'a da Magajiya ba bata lokaci suka danka dukiyar a hannun Nabil. Yana gama bautar kasa ya fada kasuwanci, sai kuma al'amari ya mike, sosai ya ke fita waje yake musu business don ita ma Hajiya Rabi'a din bata karbi ko sisi a ciki ba. Gaba daya ta bayar ta juya musu, lokacin a Nabil ya yi shirin auren farko al'amasrin yazo da sauyi kala-kala. A lokacin Babansa ya karo mace ta hudu, Hajiya Sa'ade wadda diya ce ga Hajiya sa'ade da ubanta ya mutu ya barta da dukiya mai tarin yawa, abokin su Alhaji Usman din ne. Da farko Hajiya Sa'ade ta shige sukut karkashin Hajiya Magajiya, sai da aka yi auren diyarta da babban dan gidan Nabil gaba daya suka janye shi da shi da dukiyarsa, tilas Hajiya ta zamo 'yar kallo. 20shafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Can Alhaji Ahmad din ma hakan take, ya yi Amaryar sai dai shi kanwar abokinsa ce matan gidansa hudu ne cif! Don haka gidajen ya cika da 'ya'ya maza da mata, kowanne yana ban wuri a harkar ilimi da kasuwanci. BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYAR Tuni Munir ya gama Masters digree a wannan lokacin, Alhaji Usman yara uku ya sanya lalle ya yi musu aure 'yammata. Don babban Yayansu Nabil tuni yaransa biyu, a ranar Munir ya iso daga Maiduguri don samun daurin aure. Bai iske ba sai ya 6ige da kai 'yammata rakiyar amarya. Kusan kowacce budurwa a gidan Alhaji Usman din, so take yi ace ita ce Munir yake yi da ita, don idan ya iso gidan kowacce sai ta canza kwalliya a iske shi falon baki a yi ta faman kwarkwasa. Ita kam Goggon Mama ba ta kula su, kullum tsakaninsu da tsakuwa sau da yawa zai tsare ta da ido yasha mur ya ce mata. "Ke Goggon su Umma ba ki da kirki ko? Kowa yazo ya gaishe ni ban da ke ko?" 21 Ishafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Kallonsa take ta watsar ta ce, "To gaisuwar nawa ce? Ba na gaishe ka ba ne tun dadewa?" Ya ce, "Yaushe ne tun dadewar?" Sai ta kuma kallonshi ta watsar ta ce, "Tun shigowar ka mana, ko kai kurma ne?" Duk da kallon dadi yake yi masa amma sai ya doke ta ko ya kai mata hari, idan ta dan fara gudu yasa mata kafa ta fadi a yi ta rikici. Goggo ta ce, "Bangane me ka ke nufi ba mai sunan Mallam? Kullum ka zo gidan nan sai ka ci zalin uwar nan tawa, don dai zalinci kawai. To ba ta sonka a kai kasuwa." Dariya yake ya ce, "Haba Hajiya Mama, duk 'yammatan gidan nan? Ki kalli fa har da Larabawa, me zan yi da ita?" Goggon ta ce, "Ai ko kana yi da ita ba na baka tun yanzun ana yin irin wannan cutar, idan an kwana biyu na baka ita ai zubar mini ita zaka yi a bola bayan ka karairayata ka watsar." Dariya yake yi sosai, ya ce "Wallahi Hajiya Mama kin gano, ke dai bari." Itama dariya Hajiya Maman take yi, ta ce "To ai dai ga irinta nan, ka fada za ka auri Indiya ma amma ban da uwar nan tawa da sai mai Jirgin وو sama. 22 |shafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo Idan ta fadi hada dariya ake yi sosai a gidan. Irin wannan yana yi ma su Hajiya Maimuna Jadi da Hajiya Sa'ade, su miko baki ayi tayi don Balarabiyar bata shiga shirginsu. "Lalle mai sunan Mallam da gaske ka ke, yo kai da gida duk 'yammata ka zabi ka darje ga kasuwar farare na ci yaushe za ka bata lokacinka a kasuwar ma su kalasr duhu. Farin wankan tarwada ai an daina yayınsa, an fari tas! Shi ne magana." Munir ya ce, "Wannan kuma haka ne, 'Ummansu Khuzaimat bari dai nayi screening. Ina 'yammatan gidan suke? Duk ku fito, kuna karbe mini lalle ban ga kuna kwalliyar lallen ba, duk ku fito na gani wacce ta fito zan zaba." Abin kamar zuga, kowacce zata ci kwalliya ta fito su hudu, ya kalli wannan ya ce ta gabza hoda, ya kalli wancan ya kwashe mata da dariya, ya ce (Tunkiya ta dumbuji gari), janbaki ya yi yawa. Ya ce wannan ta fiya gajarta tun a nan yake nuna ba ya so. Sagira da Ladifa ya ce sun yi siririya da yawa, Khuzai ce mai gabza hoda, ya ce ban da mai hoda ban da siririya sosai ban da 23 |shafi Zumunci Dangin Kauna Jamila M. Danfajo gajera, ban da mai yawan dariya, ga wannan halin naku da ku ka yi min a mota. Gaba daya su kwashi ihu. "A'a Yaya wane irin abu? Wane irin abu ba а yin haka, ba a haka." Ya ce, "Halinkun nan? Wannan halin da

Chapter 1 of 13