Share this page
ya rufe kwamfutar ya koma ya zauna. Daɗi ya ma sarki yawa yana qara jinjina ma AbdulHaleem don bai taba tunanin zai kawo wannan tunanin ba. "Akwai mai qalubalantar wannan shiri da hujja" sarki ya tambaya don ya ba kowa hakkinsa, ganin sun yi na'am da shirin ya ce a fara aikin a lokacin da AbdulHaleem ya shirya. Tun daga majalisa babu inda maganar ta fita har se bayan sati da ma'aikata su ka zo su ka yi duk wani haɗe-haɗe na kayan mafi yawa a bango su ke birnewa sai su saka kofa da ta haɗe da sauran fentin, sai kuma wasu a kasa aka yi, daga gefe kuma ginin fada na karkashin kasa aka sanya abubuwan tsaro da ya yi daidai da zamani. *** "Wai baffa haka za ka sa mu ido? Ka ga yanzu duk wani shiri na mu an tarwatsa shi, ni dai bana son yaron nan ya sha balle har sarautar ta zo kan shi" Ummu Hafsa ce ta faɗi gaban Alhamzie bayan ta faɗa masa matakan tsaron da aka sa fada. "Ki barni da su, fadan zan zo da kaina in masa tijara cikin mabiyansa, in shi bai da kunya toh zan nuna masa shi qaramin mara kunya ne" yace yana mai sallamanta don kuwa ranshi ya riga ya ɓaci. Ashe tun bai shekara da zama yarima mai jiran gado ba yana neman ya zama masu matsala. "Baffa kuma an ce matarsa ciki ne da ita, satin da ya wuce ta zo inaga zai kai wata huɗu kenan. Ka san wata su takwas da aure kenan" Ta faɗi cikin ɓacin rai tana mai mikewa don ta san ba zai saurare ta ba kenan. Tun bayan da aka kafa matakan tsaro a fada Ummu Hafsa ba ta samu fita ba saboda ciwon hawan jini da ya kwantar da ita, AbdulHaseeb kuma da gangan AbdulHaleem ya sanya sunansa a cikin sunayen ma su zuwa kwas don ya tsiratar da shi daga sharrin da ya ke shirin jefa kansa. Hakan ya qara dafa Ummu Hafsa don Sam an rusa mata duk wani shirin ta. A ɓangaren sa da Fatima kuwa zama lafiya sai san barka, mafi yawan lokutta shi ya ke kaita makaranta wajen aiki kuma ya je ya ɗauke ta, don ba ya son a tura da masu gadin masarauta wa'inda sojoji ne maza da mata. Sanda su ka gane ciki ne da ita kuwa shi da kansa ya rubuta mata ɗaukan hutu na shekara ba tare da a biyan albashi ba (leave without pay) ya kai tun daga nan ya ke kara shagwaba shi don burinsa ta hayayyafa da yawa zuri'ar Ummu Maryam su yi yawa su ma. *** Tun bayan da Ummu Hafsa ta bar zango, Alhamzie ya rasa in da zai sa kansa, bakin ciki ya masa yawa, can dai ya figi mota bai tsaya ko ina ba sai majalisar sarki inda su ke ganawa da yan majalisa. "Kai Abdul-Jabbar! Tsohon banza wanda bai cika ɗa ba. Wai me kake nufi da mutane ne" ya faɗi ya na nuna sarki da ɗan yatsa, nan yan sanda da sojojin da ke wajen su ka tashi ɗauke shi, amma sarki ya dakatar da su. AbdulHaleem ne ya Mike ba tare da ya ji umurnin sarki ba ya same shi gaba da gaba. Kallon sa Yayi tun daga kasa har sama sannan ya ce "Duk cikin dangin ubanka babu wani tsohon da zai tunkare ni ne sai kai karamin Alhaki?" Ya ce yana harararsa bai ankare ba ya ji an kwashe shi da mari, wanda ya gigita shi har ya tsuguna. Yana tasowa ya sake dauke shi da mari anan ne sarki ya daka ma AbdulHaleem tsawa. Hakan ya sa ya ɗauke rawanin Alhamzie ya fita da shi. Bai zame ko ina ba sai madafa nan ya nemi a bashi bussashen kifi ya nade ya ce a kai ma Alhamzie gidansa kafin ya isa. "Ina umurtan AbdulHaleem da ya sauke rawaninsa, sannan na bashi kwana uku ya fita daga daular Qahɗaanie, wannan hukunci ne akan duk wani wanda aka kama da laifin ɗaga mukami sama da na sarki, wanda hakan ne abin da AbdulHaleem yayi yanzu" ya faɗi bayan yan sanda sun janye Alhamzie zuwa wajen fada kamar yanda nai martaba ya ba da umurni. Daga kitchen ɗakin da shi kaɗai ke da hurumin shiga ya isa cikin sauri, na'urar kwamfutar da ke maqale jikin bango ya kunna nan take fuskar kwamfutar ta hasko masa kofar fadan Qahɗaanie, yana kallon yanda komai ya ke tafiya har fito da Alhamzie da yan sanda su ka yi har ya shiga motarsa, sannan ya kashe ya fice daga gidan. Motarsa ya shiga ya fige ta kamar zai tashi sama, hanyar gidan sa yayi don ya san lallai da akwai yan gulma, sai da ya fice ma idon mutan fada sannan ya juya kan motar ya nufi hanyar Zangon Qahɗaanie. Yana cikin tafiyar Fatima ta faɗo masa a rai, kamar zai juya amma dai yana so ya ida nufin sa. Ya kai inda ba zai kai mile goma zuwa ga zango ya hango motar Alhamzie tafe, take ya ja burki ya tsaya a tsakiyar titin yanda babu yanda za'a yi Alhamzie ya iya wucewa. Shima ɗin tsayawa yayi ya na kallon sa rai a ɓace "Kaga karamin kwaro, bani waje in wuce tun kafin Yar bayin nan ta sake naquda" ya faɗi yana hura hanci Bai yi aune ba ya ji saukan harsashi a jikin sa, bai yi tsammanin haka ba, take ya zube a wajen yana zubar jini. AbdulHaleem na gama sakin harsashin ya ɓalla bindigar ya aje kusa da Alhamzie sannan ya juya. Tashin motarsa yayi daidai da isowar mutane zuwa wajen don sun ji karar saukar bindiga wanda abu ne da aka daɗe ba'a ji shi ba. *** Wasikar kora daga Fada ya iske a gidan, bai yi mamaki ba amma kuma abin ya taɓa shi. Wanka yayi ya wanke kayan jikin sa son ya ga alamun jini a hannun rigar sa, sannan ya fito ya sami Fatimah da ta shiga damuwa saboda Yanayin da ya zo mata da shi. "Azeezatie ki yi hakuri, muna cikin wani jarabawa wanda sai da taimakon ki kawai za mu iya ci. Mai martaba ya kore ni daga daular qahdaanie saboda laifin yin hukunci sama da nashi a fada, haka dokar take, za ki bini ko kuma za ki zauna ki haifi ya'yanki a cikin dangin su. Ban san in da zamu nufa ba, saboda haka na bar ki zuwa gobe ki yi shawara da zuciyar ki" ya faɗi kai tsaye yana mai mikewa. Sai a lokacin ta fara tsanar kasancewar sa mai abu kai tsaye ba tare da ɓoye-ɓoye ba ko lallashi ba, takaicin ta ya karu duk ta tuna da faɗin sa na wai zata bi shi ne? Tunanin sa za ta bar shi ya tafi ba tare da ta kasance makale da shi ba. "toh aikin ki fa" wata sashi ta zuciyar ta ta tuna mata da kasancewar ta mai aiki. Nan ta kara shiga ruɗu don har ga Allah tana son aikinta burinta da mahaifinta shine ta taka matakin farfesa. Kuma bata ga dalilin da zai sa ta rusa musu wannan buri na su ba. Haka zuciyar ta taci gaba da raya mata abubuwa, nan ta gama rudewa kawai sai ta ja jiki zuwa ɗaki. *** Tun da AbdulHaleem ya shiga ɗki ya ke tunanin ina zai nufa, ga matarsa ga ciki ga kuma kewan gida, ya san barin sa Qahɗaanie kamar bayyana mahaifinsa ga abin da zai cutar da shi ne. Yana cikin wannan tunanin ya tuna da abokin sa da su ka yi karatu tare mai suna Stefano Angelo wanda yake ɗan yankin romaniyawa ne wato Kasar Italiya. Stefano abokin AbdulHaleem ne kuma ya sha faɗa masa irin dabarun mulki da su ke da shi a yankin su da kuma yanda Kasar Italiya ta zama cikin kasashe da su ka samu nasara lokacin yaqin duniya na ɗaya. Hakan ya sa ya tura masa sako ta akwatin email akan ya na so ya zo Kasar su ya yi shekara saboda koyon dabarun mulki da yaki, yana so ya sama masa gida a kusa da yan tawaye matukar hakan ba zai cutar da shi ba. Daga nan ya masa godiya bayan Stefano ya tabbatar masa da samun duk wani abin da ya bukata, daga nan ya fara neman hanyar fita saboda fasfo da bisa ɗinsa na masarauta ce ta bashi damar shiga dukkan Kasar da ta ke da jakadanci da a Qahɗaanie ciki kuwa har da Italiya. *** Mutanen wajen na qarasowa su ka tsinci Alhamzie kwance cikin jini. Ganin ya ɗaga hannunsa ya sa ya tabbatar masu cewa yana da sauran rai a jikinsa. Cikin azama wani ya ɗaga shi sai a lokacin su ka kula da Aamir Al Ansari ne. Ba su ɓata lokaci ba su ka ɗauke shi sai babban asibitin Zangon Qahɗaanie inda likitocin su ka tare shi cikin gaggawa. "Aamir Al Ansari ya rasu a sanadiyar harbin bindiga" ya kasance taken Labaran gidajen radiyon Qahɗaanie, haka gidajen talabijin ga hotonsa da kuma hotunan da aka ɗauka bayan fitowarsa daga fadan mai martaba. Nan mutane su ka fara samun bambancin ra'ayi, wasu gani su ke hukumomin tsaro ke da alhakin kisan yayin da wasu ke ganin cikin yan tawayen da ya hana musu wajen zama ne a zango aka samu wanda ya masa wannan kisan gillar. "Majiya ta musamman ta sanar mana da yan tawaye yan aqidar ISMAAALIE ke da alhakin mutuwar Alhamzie, su dai Wa'innan sun zo ne daga yankin gabas in da su ka nemi da ya basu matsuguni don yaɗa aqidar su tare da yaqar duk wata aqida da ba tasu ba, amma Alhamzie ya kasa ya tsare ya hana, kakakin wannan akidar ya sanar a wani faifai na bidiyo da su ka saki akan sun kashe shi ne saboda ganin sa ya fito daga fadar daular Qahɗaanie, sun yi amanna akan yana so ya haɗa kai da sarki ne don yakar su" kashe talabijin ɗin AbdulHaleem yayi don ya san karya ce kawai, duk da yana sane da ISMAALIE ya san ba su da makamai a hannun shi kuma ya sani sarai Alhamzie na da hannu a cikin kafuwar qungiyar. Tashi yayi ya shirya kayansu don ba zai kara awa 24 a cikin Qahɗaanie ba, in Fatima za ta bi shi toh in kuma ta fi son zaman Qahɗaanie toh ruwan ta don shi a shirye yake da ya ya qi Alhamzie don yana da yaqini bai mutu ba yana nan da rana. Manage this Love u all A Zangon Qahɗaanie kuwa tun da aka kai Alhamzie asibiti labari ya iske iyalinsa akan ya rasu. Nan yan uwansa da yake zumunci da suna kusa suka hallara a gidansa don tarbon gawar sa yayin da yan maza su ka isa asibiti don tahowa da shi. Da isar su ne suka iske labarin yana Raye sai dai ya jikkata sosai saboda asarar jini da yayi. "A cinya aka harbe shi" faɗin mijin er sa ta fari. Don ya riga isa wajen kasancewar yana cikin wa'inda su ka fara isa inda abin ya faru. "Wai waye wannan ya aikata wannan aika-aika" wani matashi ya tambaya, kallo ɗaya zaka masa ka san malami ne zaahidi. Don kuwa yakan jikin sa kaɗai ya isa ya nuna tsantsan talaucin da yake fama dashi. "ga dai abin da aka kawo ma matansa cikin rawani sa, ganin kifin a bushe yana nufin Aamir na cikin hatsari, in bai niyyar kashe shi ba yanzu toh ana rantsar da shi sarki zai gama da Aamir" Yusuf kanen Aamir ya faɗi wanda shi matan su ka mika ma sakon ganin ai rawanin da yayi amfani da shi a ranar kenan. "Ai yanzu lokacin bayyana kanmu ne yayi, zamu ce mu muka harbi Alhamzie don mushen can da ke mulkin zalunci ya saki jiki da shi, daga haka sai mu ba ɗaukacin al'umman qahɗaanie shiriya su tuba su bi hanyar gaskiya" wannan zaahidin ya faɗi yana zazzare idanu. "Amma kuma ai bamu san shirin da ya ke ba, kada mu yi sauri mu ga abin da ba hakan ba" Yusuf ya faɗi yana mai jin tsoro. Amma shi zaahidin nan ya tsaya kai da fata akan gara a nuna musu akwai shiri na musamman, sannan a yi ma fada shigo shigo ba zurfi. Hakan ya sa su bada sanarwan su suka harbi Amir al Ansari. *** Tun da Zubaida ta isa Kasar Masar ta haɗu da wanda ya kira kansa Abdullah ta mace masa, baki ne mai tsawo da kyan sura, sannan yana da wani irin zaiba a idanunsa da ke tafiya da zukatan yan mata. Ta iske shi a namiji da ya iya sarrafa mace, ita kuma karatun da ta taso da shi kenan a aure, hakan ya sa gaba ɗaya ta ke ganin ta a Aljanna. Tun da ta isa bata taba jin haushi ba sai da mahaifiyarsu take faɗa mata wa Fatima ta aura sannan auren ramla bai yiwu ba nan ta zauna da mahaifiyar nata su na tsine ma Fatima da mahaifinsu don Zubaida faɗi tayi "Ammie kin tabbata da ba so yake ya dinga haura mata ba kamar fatima shi ya sa yake cewa shi ba zai ɗaura mata aure ba" tace kanta tsaye ba tare da da la'akari da girman ɓatancin da take faɗi akan mahaifinta ba. Nan uwar ta shiga waswasi don sheɗan ya sha raya mata wannan shakuwa da ke tsakanin Fatima da Alhaji yahuza babu Allah a ciki. "ke dai ki iya bakinki, ita Ramla yanzu zan san yanda za'a yi na turo miki ita ko kuma in shi Abdullah na da wani a kasa da zai aureta ya taimaka ya zo a ɗaura" haka su ka tsaida magana akan haka su ka yi sallama suna cike da begen juna. Abdullah na dawowa kuwa ta zauna ta feshe masa komi tana karfafa mahaifinta ba ya so Ramla ta yi aure ne don ya samu ya dinga haure mata kamar yanda yake yi da Fatima. Nan su ka haɗu suna tsine ma Fatima da fatan dukkan wani bala'i ya sauka a gareta da mijinta, shi yana yi ne saboda ubangidan sa mafi ma uba a wajen sa Aamir Al Ansari, sannan yana yi don ya kara samun yardanta yayin da su ka tashi shuka ma su Fatima wani bala'in. "Yauwa akwai ɗan uwa na, yaron kawu na ne, kin san na ce miki mahaifiyata er Ghana ce toh shi yana chan amma mutumin Allah ne, don kuwa zan iya rantsuwa akan shi waliyyi ne, zan masa magana sai ya je su daidaita da Ramla ayi auren a wuce wajen" yace bayan ya lissafa ya ga hakan ne zai kara ba su damar mallakar fada in su biyu suna auren mafi soyuwa a wajen sarki. Ba su tashi a wajen ba sai da suka kira Hajiya Amina a daular Qahɗaanie suka mata albishir sannan ya kira wanda ya laqa ma Nasiruddeen ya faɗa masa ya masa mata yana so ya shirya ya je Qahɗaanie ayi komai cikin wata biyu zuwa uku. A bangaren Nasiruddeen bai ko Musa ba don Abdullah ya bashi labarin dace da yayi da mata ruwan Fulani da Larabawa. Add Nkrumah Kojo ɗan asalin qasar Ghana ne gaba da baya, shine yaro na ta a wajen malam Kojo malike da ya ke zaune a Zango ghana, hakan ya sa aka faɗa masa Nkrumah. Ya taso a sake babu kwabo babu tarbiyya har Allah ya sa ya girma Hak ya taso sagagaga. Bayan kammala karatun sa na sakandire ne jinin su ya haɗu da Adjetey har su ka zama aminai kum shugabanni ga kungiyoyin yan fashi guda biyu da su ke gagarumin ɓarna a qasar Ghana baki ɗaya. Bayan tarwatsewar kungiyar adjetey da tafiyarsa Kasar Masar ne Nkrumah ya ɗan ja baya da fashi don shi burin sa ya samfe daga Kasar kafin ya haɗu da bakar rana, shi dai bai da ubangida mai harkoki kamar adjetey saboda haka kawai ya dira ta kai ya shiga wata kungiyar asiri wanda ta kunshi manya daga cikin kusoshi a kasashen da ke kewaye da Ghana da ita kanta Ghana ɗin. *** Cikin wata biyu Nkrumah ya shirya kamar yanda su ka tsara da amininsa Adjetey ya je a matsayin Nasiruddeen tubashin Abdullah ya amso matarsa wacce ba musu aka bashi. Bayan ya kira adjetey ya faɗa masa abin ya tabbata ne su ka kira ammie "Maman Amarya" Zubaida ta faɗi bayan ammie ta ɗaga ita kuma ta bayyana sautin yanda Abdullah zai iya jiyo abin da Ammie ke faɗi. "Ai kam dai fa uwar Amarya, Ramlatie na can uwa duniya ɗazu muka gama waya, ai in faɗa miki ranar da Nasiruddeen ya zo ranar na saka borin ya kira shaidu a waje a ɗaura auren, Allah cikin ikonsa sai ya sa er ayin na gidan ta zo. Budan bakin ta wai a ɗaura aure ba bincike ko ba don komai ba wai ai ba'a daula za ta yi aure ba, in gaya miki mijinta na zaune na gwaɓe mata baki, wai se cewa yayi Nisfie taso mu je, ban iya masa tijara ba don na san yana iya sa wa a kulle ni don ba mutunci ne da shi ba. Amma naji daɗi don duk basu so abin da nai mata ba" du suka sa dariya suna mai ganin Ammie ta burge. Haka su ka cigaba da hiran su har su ka mata sallama. *** A bangaren Ramlat kuwa sun sha amarci na sati biyu ba tare da ya fita ba, amma daga sati biyun nan ba ta sake gane mijin da take aure ba, ya amshe wayar hannunta sannan su kan yini tun safe har ayi sallar isha'i tare ba tare da taga ya yi alwala ba, zai yi sallah duka don shi ke jan su limanci kuma Allah ya ɗaura mata son kira'arsa. Amma tana bin sa jam'i ne cikin waswasi don bata ganin sa yana alwala. Sannan da ance karfe tara ta yi zai shiga wanka ya sauya kaya zuwa ja da ruwan bula da baki, ya fice ta kofar baya ba tare da yace mata uffan ba. Duk ta yunkura za ta masa korafi sai ya chanza akalar labarin ya fara shayar da ita kalan na shi salon hakan ke rufe mata baki don jin ta take a wata duniya ta musamman. A cikin watanni biyu da su ka yi tare, ta tabbatar ma kanta lallai ko menene hanyar samun kuɗin Abdullah toh ba hanya ce mai tsafta ba, don ta sha kama shi da jini a hannu ko kuma ya dawo idon ta biyu ta ga jikin sa duk shatin jini kamar ya feso masa. Anan ta shiga damuwa da danasani fiye da akirga don kuwa ta sha gani finafinan da ake cewa ana kuɗi ta shan jini sannan uwa da mata ake mikawa ko ya'ya. Tsoro da firgici ya shige ta sosai nan duk ta lalace ta yi baki ta shiga damuwa. Tana cikin wannan damuwar ne Nasiruddeen ya dauke ta zuwa gaida ubangidanshi. Nan ta ke fadama matar damuwar ta don tun da aka yi aure itace mace ta farko da ta fara haɗuwa da ita, shi ya sa tana ganinta bata ɓata lokaci ba ta fara gaya mata matsalar ta. "Ai kam tun da anyi gara ki yi hakuri, kina so a fara kiran ki bazawara ne? Ai komai munin halin namiji zama ake da shi a rufa masa asiri don hakan ne zai sada mutum ga Aljanna. Yanzu ki yi shiru kuma duk ranar da ya neme ki ta baya ki amince, Aljanna kike nema sai an sha wuya, don in kin hana zai koma kunnama ne yayi ta harbin ki" tace mata kai tsaye, haka ta cigaba da lallashin ta tana faɗa mata abin data ke yi hanyar neman Aljanna ne kuma sai an dage. Ba musu ta amince amma zuciyar ta taqi amincewa don ba laifi Mahaifin su ya yi kokari wajen inganta musu ilimin addini kuma ta san babu biyayya ga miji wa wajen saɓon Allah. Nan ta tuna da iyayenta da yan uwanta, nan ta fara zargin mahaifiyarta da yayarta wajen jefa ta wannan bala'i. Gashi addu'a kanta gagarar ta yake yi. Tunanin da ya faɗo mata ya sa ta washewa ta saki jiki tana ta gode ma matar don kawai ta cinma burinta. Ko da aka tashi sallan la'asar nan ta ga duk sun Mike sun tada sallah ba tare da sabonta alwala ba, itace dai ta sake sannan su ka shiga yin sallah. Bayan sun idar ne ta samu ta sace wayar matar gidan ta aika ma Fatima da sako. Sannan ta goge shi da lambar gaba ɗaya. *** Harbin da aka ma Alhamzie ya ɗaga hankalin adjetey ba ko kaɗan ba, don a ranar zubaida ta ga sabon Abdullah ba iri ɗaya da nata da ta sani ba. Masifa yake yana sakin ashar akan masarauta yana ɗauka alwashi. Hankalin sa bai kwanta ba don so yake ya ga Aamir din shi ya ji ya kalan cutar da aka masa duk da rahoto ya zo masa kan cewa a cinya ne aka masa sai dai jini da ya zubar. "Baba kar ka damu, sai mun gama da daular nan, ni ɗin nan zan jagoranci wannan shiri, sai na zo in Allah ya kaimu sati mai zuwa zan diro. Da kaina zan taho maka kanshi" alwashin da Adjetey ke ma Alhamzie kenan da su ka yi waya safiyar washegarin ranar da aka harbe shi. *** A qahɗaanie kuwa tun da garin Allah ya waye aka baza jami'an tsaro a lunguna da sakon Qahɗaanie. AbdulHaleem kuma ya tashi cikin shiri don jirgin sama na sojojin sama ne za su wuce da su. Wanda duk cikin dare ya gama shirya wa, ba tare da ya nemi ra'ayin Fatima ba. "Haba tawan, farin cikin zuciya ta, matar sarkin gobe uwargida na a Aljanna" ya ce yana shafo cikin ta, kamar abin da ke ciki ya sani kuwa ya motsa, da sauri ya janye hannu yana kallonta, dariya ta sa masa kawai. "ki shirya mu je kiyi ma Abbie sallama, don karfe goma sha biyu zamu wuce" yace kai tsaye "Aiki na fa? Karatu na fa? Saura kaɗan in haɗa doktora na fa amma ka ce mu tafi?" tace tana mai jin haushi don ita gaba ɗaya ta tsara zata koma gaban iyayenta ne har ya dawo. "kiyi hakuri, aikin ki za mu dau hutu, karatun ki za ki dinga turo musu ta akwatin sako, azizatie an samu cigaba, ranar gabatar da aikin kuma zaki zo kiyi alkawari ne, kiyi hakuri kece karfi na, ina son ki sosai kinji" ya karasa yana marairaice mata. "muje amma in Abbie ya ce a'a se kayi hakuri, don mun riga mun tsara zan zama farfesa ne kafin na cika 35" tace tana juya idsnu "WA MAKARU WAMAKRAL ALLAH, WALLAHU KHAIRUL MAAKIREEN" yace mata cikin kira'arsa mai laushi. Mintsilin shi tayi, shi kuma ya sa mata dariya. Dauko wayar ta tayi nan ta ga sako na yawo buɗewar da tayi se ta ga lambar wata kasa ce don ya fara da +233, buɗewa tayi ta karanta shi kuma ya tsare ta da ido ganin firgicin da ta shiga. Jin tayi shiru yasa ya share suka fita zuwa gidansu. Tafiyar mintuna goma ya sada su da gidan Abbie, sun iske shi suna hira da matansa alamun sun gama cin abinci. Wayar ta ta mika masa ya karanta sakon bai ce uffan ba ya mika ma Ammie ' Assalamu Alaikum warahmatullah, yaya Fatima Ramla ce ki taimaka min, miji na ɗan luwaɗi ne kuma yana kisa sosai, kusan kullum da jini yake dawowa. Ya kwace wayata, bana fita, banda ko sisi yau ne ya kaini gidan ubangidanshi shine na sace wayar matar na miki text, kar ki kira, ki taimaka min ne don Allah, kar ki faɗi ma Abbie zai shiga tashin hankali, kice ma Ammie ita ta ja min' ta karanta tana zare idanu. 'oh ni Aminatu, bakin ciki har ya kai ga haka, ni za ki ma haka Fatima, yata na cikin kwanciyar hankali kuma da yardan Allah Kinga ɗn luwaɗin nan gefenki" tace cikin borin kunya amma kan cikin ta ya duri ruwa don wata biyu kenan bata ji daga ramla ba. Bata dawo daga duniyar tunanin da ta shiga ba Abbie ya mika mata farar embilob, yace "takardar nan tun da kika sheganta ni na rubuta ta amma na aje se kina cikin kwanciyar hankali, ba'a kai ga haka ba na gano

Chapter 9 of 14