ba zai iya magana ba.
Allah ya jikan mamatanmu ya kai Rahma ga makwancin su ya sa su kasance cikin Raudha min riyaadil Janna. Mu kuma ya sa mu is ko su a sa'a.
Ummu-Abdoul
24th February 2018
5:11pm Nigeria
Add Vote
shamuSYY accept my condolence please, Allah jikan ummah ya sada ta da rahma. Sisters pls pray for her mum.
Ku kara hakuri da er boko, kuma zance na Allah am a lazy type, ga abubuwa da dama a gaba na. Ur prayers needed.
😍😘😘😘😘😘
Ganin yanda ɗakin ke tsare ya so ya ba shi tsoro, jikin wani lungu ya maqale a tsorace.
'Kasan ba'a banza na ɗora ka akan
karati da tokwando ba sai don ka san
yanda zaka kwaci kanka, kuma
musamman daga Kasar China na
hayo su toh kar ka bani kunya ko a
bayan ido na, ko bayan kasa ya rufe
ido na' kalaman don Clemenza ya faɗo masa a rai take wasu kwarin guiwa da bai san da su ba suka taso masa tun daga tafin kafarsa. Hakan ya sa ya tuna da ajiyar da ke jikin wondonsa na ciki. Rabuwarsa da direban taxi ya saka ta a wandon kafin ya ajiye sauran kayansu a wani kogon bishiya.
Bindiga ce, Don ya masa kyautar sa da zai baro, tana iya harbin abin da ke da tsawon mile ɗari in dai an seta shi da kyau. Sannan ba ta da kara, tana ɗaukan harsashi sannan tana ɗaukan nakiya duka biyu Don ya cika masa shi ya ce iya taimakon da zai iya masa yanzu kenan.
'Ka san mafi yawan yan ta'adda bindiga kawai ce karfin su, ba su da karfin yin faɗa da jikkunan su, saboda haka a duk sanda ka haɗu da su nema hanyar raba su da bindigogin su Shike nan ka ci nasara matakin farko a kansu' cewar yogn Chen mai koyar da shi karate. Yana tuna hakan ya daidaita bindigar sa ga mutanen da ke zaune a bakin kofar kowannensu ya sakar musu harsashi, kafin su ankare da zuwan halsashin kowannensu ya samu isowar nashi cikin kirji. Tim su ka faɗi nan sauran da ke tsaye a gefe su ka yi sauri don barin wajen domin kuwa labarin shocking din Adjetey ya is ko su, a wata majiyar ma cewa ake ya suma an fice da shi daga fada don samun magani.
"Aljanu ne a fadan, ka san mu a kasarmu aljanu na taimakawa masarauta" cewar ɗaya daga cikinsu da ya fito daga yankin arewacin Nijeriya, ta yana gizo ya hadu da wani dan ismaalie a hankali daga abota su ka janye shi zuwa ga ta'addanci.
Kalamansa ya sa da yawansu tsorata, har su ka juya sai wasu karfafa daga yankin Kasar ibo sa su ka ɗauki aniyar ganin wannan aljani. AbdulHaleem na ganin tahowarsu ya sake sakin harsashi wanda bai sauka a ko ina ba sai cikin cikin ɗaya da ga ciki, take ya sheme a kasa. Dayan na ganin haka ya tsaya cak, ya gudu ko ya tsaya. Hakan ya sa AbdulHaleem fitowa ya dunkare shi ba tare da tsoro ko shakka ba.
Daga idon da yayi ya ga AbdulHaleem take zawo ya nemi kucce masa, don kuwa tabbas wannan ne hoton da ke zagaye da falon Alhamzie da sunan ɗan sarki da su ka kashe, kenan Aljanun ma Fatalwa ne, bai dawo daga duniyar tunani ba yaji saukar naushi a fuskar sa don sai da kumatun ya lotse, wani sabon naushin ne ya sauka nan ya fara kuka wiwiwiw faɗi yake
"ka yi min rai in fita, ba zan sake dawowa ba" karamar wukar da Mr Chen ya bashi ya zaro daga in da ya aje ya so ka ma mutumin a cinya. Wukar na shiga cinyar sa yana sakin ihu, hakan ya sa AbdulHaleem ya sakar masa kuma. Faɗin da yayi yana gurnanin azaba, AbdulHaleem ya dunfari ɗakin, buɗewa ke da wuya ya iske yan ta'adda uku suna mashaa da wasu tsofaffi, ma'aikata a fada. Take ya tsorata kada Ace mutanen nan sun yi da iyayensa.
"Kai ma dauki ɗaya, yanzu muka fara don mu sha romon dukkansu kafin a tada mu" daya ya faɗi ba tare da ya juyo ba ganin irin tsorata da matan su ka yi ganin AbdulHaleem.
Bindigogin da su ka ajiye ya kwashe ya damka ma mahaifiyarsa kana ya jawo mai maganar cikinsu ya daɓa masa wuka a mazakutarsa, ya yasar da shi gefe.
Sauran ba su ankara ba sai da yayi ma na biyun wanda shi sakin ihu yayi da ya ji azaban. Ba kamar na farko ba da ya kasa motsi saboda tsananin azaba. Ihun na biyun ya sa na uku tashi a firgice yana lalubo bindigar sa ganin babu ya Mike yana mazurai.
"wanene kai, don kazan kazan ka har zaka shigo nan, ka kawo kanka ajalinka" yace yana fiffiga kamar zai iya wani abin. Isa gareshi AbdulHaleem yayi bai masa wani gargadi ba ya soka masa wukar a cinya, azaban da ya ji ya sa ya nemi guduwa amma kafan ya hana hakan ya sa ya janye jiki gefe. Bin sa yayi ya masa abin da yayi ma sauran nan shi ma ya bi saura wajen jin azaba da zubar jini.
Sake waya yayi zuwa hedkwatar sojin Qahɗaanie inda aka tabbatar masa da zuwan jirgi mai saukar angulu a inda ya bada umurni. Nan ya jagora ci matan da ke ɗakin zuwa kofar yamma in da jirgi ke jiran su. Sai da ya tabbatar da tashin su sannan yayi yunkurin komawa don ya fuskanci sauran da ke gaban gidan.
'malam ga matar ka ga ya'ya kada ka yi yunkurin raba su da gatansu' wani sashi na zuciyar sa ya ankarar da shi amma ya cije ya dage. Saman gini ya nufa, yana tafe yana Hasbunallahu wa ni'imal wakeel don ya san bai da wani gata sai na mai duka. Ko da ya isa nan ya samu an ajiye na'urar harsashi da in aka saki zai yi kaca-kaca da wanda aka harbawa.
"Duk wanda baya fatan mahaifiyarsa ta yi sabon naquda ya sallama kansa, masarauta za ta yanta shi cike da kyatuttuka da aikin yi" ya faɗi ta lasifika din da ke makale da wannan tankin. Wasu maballai ya latsa take harsashi ya sauka a kan wasu yan ta'adda ya na kallon yanda su ka tarwatse. Babu shiri su ka fara gudu don tsira da ransu suna hayewa kan hillux hillux din da ke harabar wajen suna guduwa. Ganin haka ya sa AbdulHaleem ya sake sakin harsashi nan wasu suka kara zubewa, don burin sa ya rage yawan yan ta'addan.
'ina mai martaba' shine tambayar da ta hana masa latsa botirin a karo na bakwai nan ya juya da sauri zuwa ga hanyar da zai sada shi ga cikin majalisa
Add Vote
Faɗin wahalan da Adjetey ya ji a dalilin shocking ɗin nan ma ɓata lokaci ne, umurni ya bayar aka miko masa jallabiyarsa ya sanya ta ya nemi ta shi. Nan ya ji kafafunsa na maido masa da shocking ɗin da ya ji. Kwanciya yayi warwas a wajen yana mike kafafunsa ko zai samu sa'ida.
Bai gama mai da karfinsa ba sai jin ihun wasu ya yi, sai ga wasu a guje suna haki
"Yaa Naqib, wallahi aljanu sun bayyana da ga can gefen, sakin harsashi su ke, mutanenmu na chan kwance a mace" haka su ke faɗi wani na faɗi wani na caɓewa. Wani tsoro ne ya ziyarci Adjetey don bai taɓa tunanin haka ba da ya shiryo ma zuwan su.
"Ai yanzu ma suka illa ta Naqib, yanzu haka ga shi nan magashiyan, ai gara na mutu da na haukace" mai sai ta bindiga ga mai martaba ya faɗi yana ajiye bindiga ya ari ta kare, nan wasu su ka biyo sawu sun fito kenan su ka shige jirgin su mai tashin angulu da ya ke a harabar fada. Adjetey na fitowa shima ya faɗa, tare da ba da umurnin tashi nan su ka tashi suka bar masu gadin fada a cikinsu.
***
Bayan fitar su mai martaba ya kalli waziri ya ce " AbdulHaleem ne ya iso, babu wani aljani a fadan nan don a kafa daular nan akan ɗarikan sunnar annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi, ka ga kenan babu yanda za'a ayi shirka ta shigo daular nan" nan fa su ka fara faɗin albarkacin bakunansu duk da cewa da yawa a cikin su a tsorace su ke.
alkyabba mai martaba ya cire don ya rufe yarinyar da su ka ma tsiraici. Su na haka su ka jiyou muryar AbdulHaleem yana ba da shela, hamdala mai martaba yayi ta yi, zuciyar sa na haske da farin cikin samun nasara.
Tun daga bakin kofa ya tari AbdulHaleem, dudduba shi yake don ya tabbatar da lafiyar sa., sai da ya Kalle shi tsaf sannan ya rungume shi yana mai shi masa albarka. Bin iyayen yayi daya bayan daya suna dafa kansa su na shi masa albarka. Sannan su ka dunguma zuwa kewaye fada bayan AbdulHaleem ya bada sanarwan a turo musu dakarun sojojin Qahɗaanie.
"Hakika na yarda duk ta'addancin da ya zarce awa ashirin da huɗu to gwamnati na da ra'ayi akai ko kuma gwamnati ta gaza" cewan mai martaba yana kara rungume AbdulHaleem a karo na ba adadi.
"Baka da ra'ayi kuma baka Gaza ba, kawai de tunanin ka ne irin na bayin Allah wa'inda a lokacin su ta'addancin bai hayayyafa ba. Amma a zamanin nan yanda aka fitar da na'urorin tsaro haka ake bayyana mutane zuwa ga ta'addanci.Shi yasa lokacin nan na sauya tsarin fada" ya faɗi yana kyafta ma mai martaba ido, nan su ka sa dariya.
***
Yini uku aka ɗauka wajen gyara fada tare da yi masa sabon fenti. Sauran na'urorin da aka illata kuma AbdulHaleem ya hana a taɓa su don bai yarda wani ɗan Qahɗaanie ya san da zaman su ba. Sai a sannan aka dawo da matan gida sannan a lokacin ne mai martaba ya samu labarin Ummu Hafsa na kwance ne a gadon asibiti ba ta mutu a kamar yanda suka faɗa masa.
Anyi jana'iza duk wa'inda su ka rasu, fili guda mai martaba ya ware ya zama makabartan duk wanda ya rasu a dalilin Ismaalie. Sannan aka fara gina gidajen da su ka salwanta a kwanakin firgici sannan mai martaba ya koma fada. A lokacin ne ya bada daman zama da yan jarida kamar su BBC, aljazeera da sauransu in da ya faɗa ma duniya cigaban da aka samu.
"an ce yan kungiyar Ismaalie sun koma dajin Asad, shin wani yunkuri kake don fitar da su daga daular na ka gaba daya" ɗan jarida ya tambaya wanda hakan ya sa mai martaba tunawa da su.
Shi tun da aka samu nasara sai yake gani kamar gaba ɗaya babu su a daular. Gudun ɓata ma kansa suna da martaba ya sa shi yin murmushi ya ce
" wannan ba wani babban matsala bane don kuwa muna shiri ne don so muke mu kauda burbushin su gaba ɗaya daga Qahɗaanie, sun samu mafaka ne daga wasu yan daulan, mun san da su kuma za mu fara yanke musu hukunci nan ba da jimawa ba" ya bada amsa, haka su ka cigaba da tambaya yana basu amsa, yayin da ake nuna su kai tsaye a manyan tashoshin talebijin na duniya.
Ya samu sakonnin taya murna da sambarka daga shugabanni kasashe zuwa ga sarakunan daulolin Larabawa da sauran su.
***
Sai da aka yi sati sannan AbdulHaleem ya kai ziyara gidan Abbie, sai a lokacin ya tuna bai kira Fatimansa ba. Karkada kai yayi don ya san a cike take da shi.
Ya kira Don de tun a kwanakin nasara, in da yayi masa godiya haɗe da bayani kana ya nemi alfarma Don ya sama ma masa wa'inda za su gyara musu fada da ma ita kanta daula don ta danyi shigen kasashe ma su cigaba.
Bayan sun gaisa da Abbie nan ya masa faɗa sosai, ya nuna masa kuskuren da su ka ɗauka na rashin kira ko waiwayen gida. Din mutuwa ba ta zuwa da shela in ta tashi se bayan ta ɗauki wanda yake rabon ta kafin a san da ziyarar ta. Bai kasa da guiwa ba ya nemi gafaran Abbie sannan ya latsa lambobin Fatima ya kira. Ringing biyu ta ɗauka bata amsa sallaman sa ba ta hau masifa
"ni wallahi ban san mijin da na ce na aura ba, shi de ko yaushe burin sa ne a gaban sa da ya sa gaba baya ko waiwaye. Toh malam dusar ka ta bushe ka bada himma zuwa kwashewa, tom" ta ce tana murguda baki, shi kuma dariya yake don ya sa ta a murya ne (handsfree) ne ga iyayenta duka zaune.
"Hala firgicin bai sake ka bane kake ta dariya don anya na lafiya ne" tace a kufule.
"wai rayuwar da kuke yi kenan miji ba abakin komai ba, wani irin iya shege ne faɗin ma miji magana" cewa Ummie don ita abin bai bata dariya ba kamar yanda sauran su ka tiqe su na yi. Muryar Ummie da taji yasa ta kiran sunan da karfin ta cikin murna. Sai duk su ka sa dariya. Gaisawa tayi da kowa da aka kawo wajen Abbie cewa tayi sai dai video call, nan su ka jona Skype su ka fara. Murna a wajen su ba'a magana. Ya'yan ta zaunar da su tana nuna musu dangin su.
"Abbie tun da an samu lafiya za mu zo ko, don ni na gaji da rashin ku" tace cikin shagwaba. Ya'yan duk sai suka maimaita hakan ya ba Abbie dariya. Haka de su ka yi sallama ba tare da ya bata a sa.
***
Tafe yake cikin nishadi don magana da ya yi da iyalin sa. Tafe yake mutane na jinjina masa don yabawa da su ka yi da kokarin sa wajen dawo masu da zaman lafiya.
A kofar shiga majalisa ya ci karo da AbdulHaseeb da Abdul Baar, rungume su yayi cikin farin ciki don tun da ya dawo bai sa su a Ido ba don duk su biyun na cikin dakarun sojin Qahɗaanie.
"ka yafe min AbdulHaleem, in ba haka ba rayuwa ta zata zama matsala. Na cuce ka sau ba adadi don kawai na gaji mai martaba, yanzu na kara tabbatar da cewa kafi ni cancantar sarauta, ka fi ni a komi ni ba komai bane sai mai cike da son kanshi" ya karasa yana mai rushewa da kuka. ha'an Nisfie kuka ba na jarumai ba ne, an halicce mu ne don mu yi kuskure shi ya sa baa yi mu mala'iku ko annabawa ba, kada ka damu zo mu karasa cikin gida.
Sun fara da sashin Umma Hafsa in da ta ke jinya tun bayan dawowarta daga asibiti, kwance su ka iske ta idanunta a rufe amma kuma hawaye na zuba daga idanunta. Zuciyarta yayi baki kirin kamar wanda aka babbaka saboda haushi, takaici da kiyayyar Abdulhaleem da ya mamaye ta. Ranta ya qara 6aci jin shigowar su. Ta ya za’a yi tana ji tana gani nasara ya hau kan Abdulhaleem duk shirin da su ka yi masa, sannan don cin Amana kuma kawunta Saifullahi ya shirya hanyar da za’a kasha ta. Wasu zafafan hawaye su ka gangaro mata don tana ganin in ba hakan ta yi ba ba za ta ji salama ba a ranta.
AbdulHaseeb da ya san dalilin hawayenta ji yayi ina kasa za ta bud’e duk su shige ko sa huta, a da yayi abu cikin son raid a kuma zuga irin na mahaifiyarsa amma tun day a fahimci Alhamzie amfani da su kawai ya ke don ya cimma wata manufa ta sat a daban ya sallama ma bakin nufinsu na son yayi mulki ko ana ha maza ha mata amma lokacin ya qure masa a sannan. Ko a jiya da ya shigo d’akin mahaifiyar ta sa , ya so ta fahimce shi amma inaa gani take tuba a yanzu kamar mutum ne ya na ganin nasara sannan ya janye nema.
“Ko bayan raina ban yarda ka bar ma AbdulHaleem kujeran Mulki ba, duk fitinar da ke tattare da kujeran kar ka damu ko da kuwa kowa zai mutu ne a bar ka a raye” tace masa bilhakki har cikin ranta hakan ne. shi ya sa da ya ga hawayenta zuciyar sat a bashi ganin Abdulhaleem da tayi ne duk da kuwa cewa idanunta a rufe yake hakan bai hana ta fahimtar kasancewarsa a wajen ba.
Hannu Abdulhaleem ya sa ya yana share mata hawayen,amma ji ta ke kamar an d’aura mata gawayi saboda tsananin kiyayyarsa da take ji a ranta. “LAA BA’ASA DUHURAN INSHA’ALLAH" y ace mata yana share mata hawayen, tausayinta yake ji don ba zai manta labarin da Don ya bas hi ba na irin azaban da ke tattare da harsashi kasancewar an taba masa shi ya sa ko makiyinsa ne ya fi so ya kasha shit a guba bat a harsashi ba tun da aka ta6a harba masa ita.
“Ka bar Ummu ka zo mu karasa ciki, harda tausayinmu ya sa Ummu hawaye, tana bukatar kadaici” Abdulhaseeb ya ce don ya samu su fita kafin ta kwafsa masa. Ba musu suka fita bas u tsaya ko ina ba sai d’akin Ummu Maryam. Zaune take tana tilawar Al-Qur’ani, tayi farinciki ainun da ganin d’anta don tun day a dawo bas u ke6e ba, bata so ganin sa da AbdulHaseeb ba don in akwai wanda ba ta yarda da shi ba yanzu Abdulhaseeb ne don kuwa ta sha kama shi yana fad’in kalaman 6atanci akanta ko akan Abdulhaleem duk kuwa bai ta6a sauya mata ta fannin biyayya ko kyautatawa ba. Hakan ya sa ita ma ba ta ta6a nuna masa ta ji ko sau d’aya ba.
Anti A’azu Naasi alaiyya,
Anti Ahabbu naasi ilayya
Ummi anti hayatie
Anti Noorie
Anti Qalbie
Uhubbuki bi killo diqqatin min qalbie
Abdulhaleem yace yana rerawa kamar wak’a , kusa da ita ya zauna yana mai kwanciya a gefen kafad’unta. Dariya tayi tana mintsilinsa nan take yayi tsalle yana mai ja da baya.
“Qalbie ba ki ma yi kewata ba, hmm ni kam nayi wallahi kullum sai mun yi hiranki da yara” yace yaka rungume ta. Ajiye Qur’ani tayi ta kale shi ta ce
“Ai kai ka auru kawai mallam, tun da nab aka d’iyata shike nan kamanta alkhairi, haba mallam a dinga tuna alkhairi” nan duk su ka sa dariya. AbdulBaar ne ya shigo hakan ya hana Abdulhaleem fadin zancen da ya yi niyya don bai ga alamun nadama daga AbdulBaar ba sai ma kwantaccen bak’inciki da idanunsa ke fitarwa. Hira su ka cigaba da yin a kan rayuwa ba tare da sun firta wani abu dangane da inda Abdulhaleem yake ba ko kuma abin day a faru a masaruta bayan ba shi. Can dai ya jawo kwamfutar d’akin ya bud’e shafin Skype ya kira Fatima, fatansa dai tana kusa don su gaisa da Ummu.
Yaran ne su ka fito a akwatin kwamfutar, Humaira wato Aisha itace mai maganar bayan ganin mahaifinsu das u kayi “Papa quando torni” Tace cikin halshen italiya wato Papa Yaushe zaka dawo.
“Gadan inshaAllah” ya ce hakan da yayi na musu nufi da larabci za su yi Magana. Abdulbaar kuwa burinsa ya san garin da su ke hakan ya sa shi haddace torni don ya fita ya tambayi yaren wani gari ne hakan.
“wannan ne maman Papa ?” cewar Hanan wato Hafsah kenan tana nuna Ummu da ke zaune tana murmushi
“Laa ke ce kika haifi Papa, kina da kyau sosai ina sonki “ inji Hibbatullah wato Maryam. Nan farin ciki ya cika Ummu Maryam, wai ita aka Haifa ma ya’ya har uku. Hawayen farinciki ne ya zubo mata don kuwa Allah kenan mai baiwa, ya bata d’aya sai ya bata nafila har uku .
“Ba ku fada mata sunayenku ba” Abdulhaleem ya ce, “kunga Ammou Abdulhaseeb da Ammou AbdulBaar da ke hotunan nan kun tuna” yace yana jawo su don su gansu
“Laa papa wannan ne mai cin abin yan Nijeriya d’innan a hoto” su ka fad’I suna nuna AbdulBaar saboda wani hoto day a zauna ya na shan Faten da makocinsu a amerika ya basu san das u ke can.
Fitowar Fatima ya sa Abdulbaar mutuwar zaune, duk da tana cikin mayafi hakan ba zai hana mutum gane cikin da ta ke d’auke dashi ba, gaida ummu ta yi kana ta gaida sauran , kokallon mijinta ba tayi ba don cike ta ke dashi, yanzu ma ihun yaran ya sa ta tasowa don ta gaida uwar mijinta.
“wainnan anya zan bari Mai Martaba ya gansu kuwa, wannan fi’ili da su keda shi ai sai su kwace min miji na” tace ma Fatima cikin dariya
“Ai fa Ummu kin ga kin tashi a amarya kenan kuma fa, don yara na kyawawa ne” cewar Abdulhaseeb.
“Haba Ummu wainnan munanan ne kike fad’uwan gaba akansu, ai uwata ce Amarya har gaban Abada” Fatima tace tana murmushi
“Ummu kinji ko, Allah yi mata wa’azi matar da ke kiran mijinta mummuna, da ni fa take don ta san jinni na ya fi karfi akan su” dariya duk su kayi, su ka danyi hira kadan sannan su ka yi sallama. Anan d’akin Ummu maryam su ka cigaba har aka yi kiran sallah, sannan su ka sauka don bada farali, daga nan su ka shiga majalisa wajen mai martaba.
Sun iske sun a karanta wasikar shugaban Kasan Ghana ne, hakan ya tuna ma Abdulhaleem ajiyar da yayi a Ghana. Bayan sun gaisa da mai martaba ne ya nemi izinin zuwa Ghana don akwai wacce ke can da zai taho da ita Qahd’aanie.
‘ai ko in Fatima ce sai dai ayi biyu babu don ba zan hakura ba, wannan mace mai cike da kayan dad’i ne zan bar ma wani, hmmn’ AbdulBaar ya fadi a cikin ransa bayan ya saurari Mai martaba ya shirya yanda tafiyar Abdulhaleem zai kasnce cike da tsaro.
DA YAU AKA ‘DAURA AUREN ZAINAB MUHAMMAD (XIESOBA) AMMA ALLAH BAI SO HAKAN BA, YA ‘DAUKE RAYUWARTA A LOKACIN DA TAKE TSAKA DA CIKA BURIKANTA..
UBANGIJI ALLAH YA JADDADA RAHMA A GARETA YA SANYA TANA CIKIN DAUSAYIN ALJANNA .
SISTERS KU KARA HAKURI DA NI PLEASE, NAYI ALMOST 6K WORDS ASHE BAI SAVING BA, HAKAN YA SA NA JI KAMAR NA AJE BGGB. NONE THE LESS WILL TRY AND UPDATE SOON INSHA’ALLAH.
LOVE YOU ALL…
Karfe bakwai na safe jirgin su ya tashi daga babban filin jirgin Qahɗaanie, AbdulHaleem ne kawai sai wasu amintattun sojoji da mai martaba da kansa ya zaɓo su ne su ka tafi. Tafiyar awa uku su ka sauka birnin Accra in da sojoji da jami'an tsaro daga ofishin jakadancin Qahɗaanie su ka nemi gwamnati ta basu ne su ka iske su na jiran su da motoci. Bayan sun gaisa ne AbdulHaleem ya nemi su karasa wajen da yan tasi ke zama don ya duba wani. Ya kai nan ya na shirin tambayar Sufyan Marwan kawai ya ji an rungumo shi ta baya. Cike da farin ciki Sufyan ya ce
"Kaga ikon Allah ko, da ma na san nasara ba na su bane" ya karasa yana mai kara rungume shi.
"Alhamdulillah! Abu ya zo da sauki fiye da yanda mu ka zata. Ka san tun rabuwan mu nake ambatar HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL kuma na ga ijaba don ba yi na bane yin Allah ne ne" AbdulHaleem ya faɗi cike da murna. Kallon yan rakiyan yayi yace su biyo bayan su don shi a motar Sufyan zai karasa. Ba su yi masa musu ba sai ma qara shirya kansu da su ka yi wasu na gaba wasu na baya su ka bar filin jirgin inda ba su zame ko ina ba sai gidan Sufyan.
"Mai girma sarkin gobe ko rundunar nan za su tsaya daga nan ne kai mu shiga ciki?" Sufyan ya tambaya, hakan ya sa AbdulHaleem ya tsaya ya yi masu magana take su ka Kewaye gidan don kowanne daga cikin su na mamakin haɗin yarima mai jiran gado da dan tasi.
Bayan sun shiga ciki ne, falonsa dan madaidaici sannan su ka kara gaisawa, ya shiga cikin gida ya zo masa da abin motsa baki sannan Iyalinsa su ka fito su ka gaida shi. Kwarai AbdulHaleem ya ji daɗin wannan karamcin da kauna da Sufyan ke masa.
"ina ajiyata" ya faɗi yana murmushi.
"Ajiyar ka na nan ta ji sauki kwarai amma tana cikin hatsari, bakinta ba ya iya furta komai tun da lafiya ya samu take zubar kwalla, abu ɗaya ta ke rubuta min Wanda na ke tunanin in ba mahaifi ba toh tabbas makusanci ne a gareta, ka ganshi nan" ya ce yana mai mika ma sa takardan.
"Nemi Alhaji Yahuza Bello Qahɗaanie" ya Karanta a bayyane. Wani Yahuza Bello ba dai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 14