Share this page
sannan kada ka sanar da kowa ga abin da aka yanke, hakan zai sa shi Ansari yayi ta tunane tunane. Sannan ya da wasikar take na kai da iyali kada majalisa su san da shi don makashin ka na tare da kai" Ummou Maryam ta faɗi hankalinta kwance, babu ko damuwa a tattare da ita. "Ba Za ayi haka ba, shi Haleem shi ne babba, kuma ko da yaushe babban ɗa shi ne ke gadon mulki, ban ga abin razana a cikin wasikar da har za'a yi saurin mika wuya ba" Ummou Hafsa ta ce tana mai yamutsa fuska. "Ka bani izini in je in sami Baffa, ya kamata a ajiye duk wani adawa a haɗa kai. Ni dai a bari mai rabo ya dauka, banga abin karaya da wuri ba kamar yanda Ummou ta ce" AbdulHaseeb ya faɗi har da hawayensa. Sarki dai bai ce uffan ba, har su ka gama gardamansu sannan ya ce "idan ɗan uwanka ya dawo ka ce ya kawo min hujjan da zai hana in hukunta shi na sa a ɗauke mana network" "Ranka shi daɗe ka yarda bai cancanta ba ko" faɗin Ummou Maryam. Murmushi kawai yayi sannan ya sallame su. *** Sai bayan la'asar sannan ya gurfana a gaban majalisa, bayan ya mika gaisuwa ga sarki ya sunkuye da kansa yana jiran abin da zai ce. "Kai mu ke jira, saraki" faɗin waziri ganin yayi shiru "Cin zarafin wata baiwar Allah na iske a nayi a lambun fada, wacce na iske tana yi kuma takama da karfin mulkin mahaifinta take da kuma kusancinta da masarauta, gudun kada a hana min yanke hukunci ya sa na sa a janye network, yanzu haka tana tare da yan da ayi min afuwa ranka shi daɗe" Ya faɗi cike da biyayya. "Wacece ita, wajibi a hukunta ta matukar ta tabbata mai laifi" jin waziri ya faɗi haka ya sa ya zauna ya feshe musu duk abin da ya faru da hukuncin da ya ɗauka. Nan su ka sanya salati tare da Allah wadai da kishi irin na wasu matan don kuwa ba kishi bane rashin hankali ne. Bayan sarki ya sallame shi ya karasa cikin gida don duba lafiyar Ummou Hafsa, nan ya same ta kwance ana mata tausa, da fara'a ta amsa gaisuwar sa sannan ya karasa wajen mahaifiyarsa. Nan ya bata labarin abin da aka ma fatima ya karkare da faɗin "wallahi na tausaya mata, haka nake jin kukanta har cikin raina, karantarwa take a jami'a, sannan da gani ba tayi aure ba. Ta birge ni ta kuma bani tausayi" Ya ce yana mai nuna alhini. "Allah sarki, har ka sa min sha'awarta, ko za mu cusa masu haushi ne mu aure ta kawai, dama ni bana son ka yi aure gidan sarauta" Ta ce masa ganin yana ta nanata maganar cikin tausayawa da jin haushi "Kai Ummou har yanzu kin kasa fara tunanin masu sarauta, mijin ki fa shi ne mutum mafi ɗaukaka a duk faɗin Qahdaanie ki sa na auri baiwa. Duk wanda ba jinin sarauta ba bawa ne a waje na kin sani" Ya ce yana kara kwanciya akan shimfiɗar da ta ke zaune. "haka fa, karshen duniya dama baiwa zata haifi uwargijiyarta ko"ta ce tana murmushin jin haushi " Yaa salam, wallahi ba nufi na kenan ba, Ummou kin kasa fahimtar inda na dosa, ni fa yanda nake ɗan fari kujerar nan fa ba zai wuce ni ba" Ya ce yana wasa da hannunta suna er tafawa "Toh ina so ka zaɓa ko ni ko sarauta, kuma ba zan taɓa janye ɗaya ba, dole ka zaɓa kowanne ka ɗauka zan mara maka baya har ka kai ga nasara" "Toh Ummou in dai haka ne, ba zan sake maganar ba, Allah sa haka ne Alkhairi" Ya ce yana mai share kwallan da ya zo masa. Take ta tausaya masa amma tana son sa da alkhairi ne shi ya sa. "ka san kafin na auri mai martaba wa na so?" tace tana son ta dauke hankalinsa. A hankali y girgiza mata kai hakan ya sa ta cigaba "mus'ab bn Abbas na so kamar rai, duk aka ce min Allah tabbatar da Alkhairi sai in ce ai shine alkhairi saboda ido na sun rufe akan lallai sai shi. Addu'a ta kullum Allah sa ni ce mace ta farko da zai aura amma inaa kullum kamar kara nesanta mu ake, har dai na hakura. Wata rana ina zaune a shago sai ga yan gidansu sun shigo suna hiransa, anan na gano a she ɗan karya ne, ba abin da ya sa a gaba sai cin bashi. Albashin sa kusan nutud dubu ɗari huɗu ne don wajen karɓan haraji ya ke amma bai da gida, bai da ko keken hawa sai abokantaka da manyan masu kuɗi. Ana haka sai na ga ai soyayyar asali shine in gyara shi y shiryu sai kawai na koma ruwa a sonshi, in faɗa maka na ji jiki sosai wallahi kuma ba nasara. Kwatsam rannan na hango shi, sai na fara auno wahalar da zan sha in har na amince na aure shi, kawai sai na koma da dukkan lamurana zuwa ga Allah, ba'a yi wata uku ba sai ga mijin da dukkan mata ke Mafarkin samu, shekara biyu da aurenmu ya hau karagan mulki. Kenan abin da Allah ya tanada maka yafi alkhairi akan abin da ka so ma kanka. Yi tunani akan Fatima, ban ce ka nemi shawara ba. Duk abin da ka yanke shike nan" Ta karasa tana ɗaga masa gira. Nan ya sa dariya. Cikin barkwanci ta bashi lbrn wasikar da k aiko ma mai martaba. Dariya kawai yayi ya ce "Ai ke na zaɓa, kuma ke zan zaɓa ko menene kuwa aka haɗa zaɓin sa da ke" Ya ce yana mai kara Mike kafa. A haka su ka cigaba da hira har aka kira magriba. *** Fatima tun bayan fitan AbdulHaleem ta zauna akan kujera ta shiga rera kuka har sai da ta gaji don kanta. A duk lokacin da aka ɓata mata rai ba ta da abin da ke saukar mata shine ta zauna mahaifinta ya karanto mata tarihin su, tun daga tushe su. Hakan ya sa ta yi tunanin yin abin da ba ta taɓa yi ba ita kaɗai watau to. Stop being angry at your mom just because she says stuff that no one else does. Remember that she does things for you that no one else ever will. That’s what I’ve learnt when I’ve looked back at my childhood. Thanks ma, happy birthday. A shekarar da aka kafa makarantar koyor da boko na farko wato shekara ashirin da tara bayan an kafa daular Qahɗaanie, a shekaran ne aka samu wasu baki yan Hijira daga yankin Adamawa. Mai gida ne da zuri'arsa nan suka nemi iso wajen sarki imam Abdulhamid. "Marhabanbikum" Ya faɗi ganin su farare kirar Larabawa "Shukran Yaa Aamir" dattijon cikinsu ya faɗi "Sunana Muhammad Sambo, Mun taso daga yankin Gongola ne, na kasance limami ga tsohon Lamido ya rasu wata bakwai da suka wuce sai aka naɗa ɗan shi, yana hawa ya sauke ni a matsayin liman kuma alkali ya naɗa wani, hakan ne dalilin da ya sa na yo kaura, na yaɗa zango wurare da dama kafin mu ka iso nan, ina rokon sarki da ya bamu wajen zama ni da iyali na har ma da dabbobinmu da su ka mana saura" Ya faɗi cikin ladabi duk da kallo ɗaya za ka masa ka san zai haifi sarkin. "mu na muku barka da zuwa Qahɗaanie, mun ba ku yankin arewa da fada ka tare da zuri'arka da dukiyar ka sannan na sanya ma wajen Hilaalu Sambo. Gobe za ku fara gini kafin nan zan baku wajen zama na wucin gadi, da fatan za ku kammala wajen zaman ku kafin wata biyu ma su zuwa" da haka sarki ya sallame su, washe gari da sassafe maza daga cikinsu tare da wasu mazauna Qahɗaanie su ka taru wajen gini. Cikin ikon Allah sati daya bai shige ba aka kamala gidan, babban gida mai dakuna da sassa daban daban na shi da iyalinsa har da yaransa maza da iyalinsu. A haka rayuwar mutanen Hilaalu Sambo ke ta tafiya ana mutuwa ana haihuwa, duk wani Fulani da zai yaɗa zango a Qahɗaanie toh a Hilaal yake sauka. A mutu a haihu ayi aure a rabu haka dai har duk wa'inda aka kafa Hilaal da su suka rasu, ya'yansu ma haka har dai aka ai ga zuri'arsu ta ashirin da takwas a nan ne aka haifi Muhammad Yahuza, ya taso cikin gata da yan uwansa mata bakwai cur. Dalilin haka ya sa ya taso cikin gata duk da rasuwan iyayensa hakan bai sa ya san maraici saboda rashi ba. Yana da shekara takwas a duniya ya yi saukan alkur'ani hakan ya sa su kayi tunanin tura shi makarantar koyon kimiyya. Ganin shi ke ci a Qahɗaanie kowa na son zama kwaro a kimiyya. Muhammad Yahuza bai ba Yan uwansa kunya ba yayi karatu cikin nasara, bayan ya kammala kwaleji suka tura sa Kasar Turai ya karo ilimi, dawowarsa ya sa babu wanda ya kai shi ilimi a bangangaren kimiyya. A shekaran ne aka kafa jami'ar kimiyya da fasaha na tunawa da Safiyyah bnt Jibril, kuma take aka bashi mukamin shugaban jami'ar. Duk da zaman sa shugaba hakan bai hana masa shiga aji sai kafin shekara ya zagayo an samu nasara sosai a jami'ar amma kuma cecekuce ya fara yawo akan shugaban da ya kasa ajiye iyali ta ina zai shugabanci al'umma. Hankalin sa da na yan uwansa ya tashi don shi bai da abin so sama da littafan sa da yan uwansa, hakan ya sa bai taba soyayya ba. Bayan sun yi zama ne suka yanke shawaran haɗa shi aure da kanwar mijin yayarsa marikiyarsa Surayya. Ba'a ɗauki lokaci ba yayi aure ya tare da amaryar sa a cikin makaranta. Shekara daya da aurensa su ka wayi gari da tashin hankali, don kuwa mahaya suka shigo har cikin jami'a suka iske shi a gida su ka raba gida biyu. Daukacin al'ummar Qahɗaanie sun shiga tashin hankali don wannan shine taaddanci na farko da aka fara tun bayan kafa daular shekaru aru-aru da su ka wuce. Bayan rasuwan sa da wata uku matarsa ta haifi da namiji nan aka sa masa Muhammad Bello, wasu sun so a maida masa da Yahuza amma Surayya ta kasa ta tsare tace "kafin kanina ya rasu ya sha faɗa min Bello zai haifa" Bello na da shekara ɗaya Allah yayi ma mahaifiyarsa rasuwa anan kula da shi ya koma hannun Hajiya Surayya, bai rasa komai ba haka ta haɗa shi da nata ya'yan ta raina ba tare da nuna gajiyawa ko bambanci ba. Bello na da shekara biyar Allah yayi ma Hajiya Surayya rasuwa, anan rikon sa ya koma gun mabi da ita Aisha, nan ma shekara biyu kawai yayi hannunta ta rasa ranta a dalilin haihuwa. Tun daga nan Bello ya san me ake kira da maraici don sauran yan uwa da su ka rage mazajensu na kallon dukiyar da Bello ya gada ne, nan su ka yi kasafi a tsakaninsu kowannensu ya kwashi rabon sa. Shi kuma su ka barshi da gallafiri a tsakanin su yau yana gidan wannan gobe yana gidan wancan har dai ya samfe ya koma fadan sarki da zama. Nan ɗin ma ba wani abin arziki yake samu ba sai dai yakan ci ya sha sannan yana zama cikin ya'yan sarki da su ke sa'oinsa. Da rarrafe ya kammala kwaleji anan ya fara siyar da dabino da riɗi, sannu a hankali ya koma safaran fata daga Nijeriya zuwa Qahɗaanie. In zai tafi sai ya kai musu man riɗi da riɗi da dabino. Tun yan tsallakawa ya dawo babu wani riba har ya kai ga ribansa kan ninka kuɗin da yaje da shi. Daga haka ya buɗe masanaartan sarrafa riɗi zuwa biskit da wasu ababen kwalama. Hakan Allah ya ɗaukaka shi yana da shekaru ashirin da takwas a duniya. "Bello ya kamata ka yi karatu mai nisa,ka bar min amanar kamfanin ka zan kula muka da shi ka je Kasar waje ka you ilimi ka dawo" faɗin amininsa AbdoulGaffar ɗan sarki mai ci a lokacin. Bai Musa masa ba ya nema kuma ya samu tare da taimakon AbdoulGaffar ɗin. Kasar Spain ya je yayo ilimi akan kasuwanci, shekara uku ya ɗauka ya dawo ya iske ya samu riba fiye da tunani. Bayan ya dawo ne ya haɗu da Amina, budurwar da ke tashe a Qahɗaanie don duk samarin ta dafa sarakai sai ya'yan su amma Bello ya kasa ya tsare shi sonta ya ke. "Ba fa za ta aure ka ba, yarinyar da su saifullahi su ka gama kwakwala za ka aura, sannan ai kai ba ajinta bane" faɗin AbdoulGaffar cikin jin haushi bayan sun je gidan su Amina zance sun iske maza na layi. "ina sonta ne Amini" Bello ya ce yana jin zafi "In rabon ka ce zaka aure ta a gaba, yanzu ka je ka nemi Abokiyar tagwaitar matata ka aura, samun abokiyar zama ta gari kuma uwargida ta gari zai sa duk Fitinar wa'inda zaka auro daga baya ba zai taɓa damunka ba, je ka neme ta" a ranar da haka su ka rabu kowannensu da abin da yake sakawa a ransa. A daren ranar kuma Allah yayi ma adalin sarki rasuwa. Sarki Abdoulwahabb ya rasu sanadiyar ciwon cikin da ta turknuke shi. Haka aka yi kwanan jimami Bello na faman rarrashin amininsa AbdoulGaffar saboda Shakuwar da ke tsakanin sa da mahaifinsa ya fi na kowanne don sarkin ya sha faɗin bashi da Magaji sai AbdoulGaffar duk da kasancewarsa ƙkarami cikin ya'yan sa maza uku. Washe gari aka sallaci marigayi aka kai shi gidan sa na gaskiya, da yamma lis sai ga labarin rasuwan AbdoulGaffar da matarsa ta sanadiyar ruwan da su ka sha. Hankali ya tashi a fada nan aka fara bincike don ganin wa zai ba su ruwan guba da har za su rasu. Ana cikin bincike kuma aka sake samun labarin rasuwan amintaccen hadimin sarki wanda shi ke bashi abinci, kuma mutane da dama sun ganshi da AbdoulGaffar bayan sallan la'asar. Nan bincike ya sauya salo don take aka gano cewa sarki da AbdoulGaffar duk Alu amintaccen hadimin sarki ne ya kashe su. Amma abin tambaya a zuciyar kowa Shine wanene ya sa shi kashe su? *** An ɗauki kwana bakwai ana makokinsu uku da aka birne a jere, sannan an kafa kwamitin bincike da ke bincike akan wanda ya sa ayi kisan. Sannan an ba da Daman fitar da masu takara saboda wanda ke jiran gado ma babu shi. Nan duk wasu masu kwaɗayin sarauta kuma su ke tunanin sun cancanta su ka fito. Da fari babu ɗa ko guda daga cikin ya'yan sarki mai rasuwa da ya fito, sannan duk. Kannensa da su ke Raye sun yafe sarautan ya sa aka saka sunan Abdoulajabbar ba tare da ya sani ba. Bayan bincike da duba cancanta sai kwamitin suka tsaida Abdoulajabbar a matsayin sarki kuma Alkali mai iko na karshe a Daular Qahɗaanie. Tsaida Abdoulajabbar ya kawo cecekuce a masarauta ganin in ba'a yi wasa b sarautan zai fita daga gidansu ganin bai da ɗa namiji ko ɗaya sai mata biyar da uwargida Ummou Hafsa ta haifa masa. A cikin bayin sarki akwai wanda jinin su ya haɗu da Abdoulajabbar, dattijo ne shi yake kula da shanayen masarauta hakan yasa da yawa basu san Ammou Yusuf a matsayin bawa ba. Yana da ya'ya goma sha huɗu da matarsa Zainab wanda sha uku daga ciki maza ne sai mace ɗaya tilo. Not much sha Vote share and share after commenting evry line Thnx 4ur love Ummu-Abdoul Add Vote Do you know that...? BGGB was sopos to b the title for Silar Ajali.. I only know two things about BGGB that is the disguised blessings in delay of marriage when one is patient and decent and the problem of desperation. I only know what to write when I pick up my system to type😂 or sometimes some thin will come to my mind and I will quickly type It so that I won't forget.. Qahɗaanie doesn't exist its just an Arabic name for some clans of Arabs But the culture of the Qahɗaanies is nt Arab its theirs 😂😂😂 so don't compare them with any body. Nutud is from nuqud Hilaalu Sambo meaning Sambo'quarters or crescent Qahɗaanie's settings is from my imagination and that of Ghana or Nigeria are 80% real. If u realize any kwafsi pls quickly draw my attention, but pls the words should be💞💕 ﺃﺣﺒﻜﻢ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻞ ﺍﻟﻠﻪ 😍😘💞💕 ﺻﻔﻴﻴﺔ ﺑﻨﺖ ﺟﺒﺮﻳﻞ ‏( ﺃﻡ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ) 💞💞💞 Musamman Mai martaba ya iske Ammou Yusuf a gidansa da ya sama masa a can wajen gari, a cewarsa shi mahaifi ne kuma mahaifa ba sa zama cikin fada don kuwa ya'ya ke bin iyaye ba iyaye ke bin Ya'yan su masarauta ba. "Ranka shi daɗe da aikowa ka yi aka kira ni" faɗin Ammou Yusuf yana mai gurfanawa kamar zai masa sujjada "Ai kai uba ne, na tuna lokutan da mukan kebe mu yi sirri a cikin shanaye ne nayi sha'awar yin hakan. Ko za mu je ran gadi ne Ammou" sarki ya faɗi yana zama kusa da Ammou Yusuf. Dukkansu tunawa su ka yi da lokutan sirrin su, in Abdouljabbar na da wata damuwa Ammou Yusuf ne kaɗai wanda ya kan iske kai tsaye ya faɗa masa sannan shi ne kaɗai ya ke fahimtar sa ya bashi shawaran da amfani da shi cin riba ne. Shiryawa Ammou yayi ya fito su ka gangara, su na tafe su na hira, har su ka shiga gonar masarauta da ke daga bayan gari, cikin shanaye inda su ka saba zama nan suka zauna, take sarki ya umurci ma'aikatan wajen da su basu waje. Sun fita suna mamakin ganin sarki shi ɗaya kamar yanda dukkan wa'inda su ka wuce ke mamakin ganin shi da tafiya a kasa kuma shi kaɗai. "Ammou ina son ɗa namiji, in ka yi la'akari da mu huɗu ne kawai maza cikin ya'ya arba'in da huɗu da marigayi ya haifa, sai in ce kila nine nayi gado. Bani shawara me ya kamata inyi kada sarauta ya fita daga gidanmu" sarki ya faɗi cike da damuwa "Abdouljabbar haihuwan mace, namiji, ko rashin sa ma gaba daya ba yin mutum bane. Allah da kansa ya faɗi yana azurta wasu da da wasu da maza wasu da duka biyu sannan yakan hana ma wasu amma dai ka kara aure, in rabon na jikinta ne sai ta haifa maka" Ya ce yana mai tausaya masa. "Ammou ka bani auren Maryam, ka yanke min sadaki ko nawa ne zan biya" Ya ce cikin hawaye, don damar da yake so Ammou ya bashi kenan kuma ya bashi. "Maryam baiwa ce a masarautarku, ka manta ni bawa ne? Ya'ya na ma duka bayi ne don ɗaya daga ciki ma a wajen bauta ya iske ajalinsa" Ya faɗi kai tsaye. Add Vot "in dai haka ne, daga yau na yanta ka, sannan duk wani jini naka ya tashi da ga bawa, kai ba ma ku ba na soke bauta a daular Qahɗaanie." Ya faɗi cikin isa da mulki, rungume sa yayi yana kuka nan tausayin tsohon ya kara kama shi. Basu bar gona ba sai da aka tara shaidu aka ɗaura auren Sarki Abdouljabbar da Maryam. Sannan a wajen sarki yayi shelar yanta duk wani bawa da ke Qahɗaanie sannan aka sa haddin zaman shekara ashirin ga duk wanda aka kama da bautar da ɗan Adam. Duk wani hadimanci na gida aka sanya albashin da za'a sa musu saboda ba bauta su ke ba aiki ne kamar ya'ya. Labarin na isa fada tsofaffin bayi su ka shiga murna suna roka ma sarki Aljanna da kuma biyan bukatun duniya da lahira. *** Sai da aka yi kwana bakwai ana bikin Sarki wanda ya haɗa har da bikin Yanci da kuma naɗa Ammou a matsayin uban masarauta. Anan ne kura ya tashi sosai amma masu hankali sun yarda ya cancanci a bashi wannan sarautan. Sati ɗaya bayan biki amarya ta tare a sashinta, a ranar ne Bello ya kai ziyarar sa ta farko wajen Hafsa, abokiyar tagwaitar Abdoulgaffar. Sanin da ta masa ta hannun marigayi ya sa ba ta wani ja zancen da tsawo ba. Ta amince masa nan su ka kulla alkawarin hana komai shiga tsakaninsu. Bai bar gidansu ba sai da son ta ya samu waje ya zauna a zuciyar sa, sannan ya yi na'am da ɗan ɗabi'un da ta nuna masa. Bai yi kasa a guiwa ba ya iske mijin yayar mahaifinsa ya nema masa auren Hafsat "Ka taɓa ganin wani cikin zuri'ar Sambo ya auri bare? Toh ka zo ga ikilima ka aura an riga an gama magana kai kaɗai muke jira" Ya ce da shi bayan ya gama saurarensa. "Ni fa ba izini na zo nema wajenka ba baffa, alfarma nake nema ka jagoranci neman aure na don kada ku ji a gari ku ga ban muku adalci ba" Bello ya faɗi kansa tsaye. "Au! Au!! Au!!! Toh an ki a je, in kana da wa'inda su ka fi mu sai su je maka, shashshasha wanda bai iya rike maraicinsa ba" Ya faɗi yana shura takalmansa da yin gaba. Haka ya bi yan uwansa duk wanda ya je sai ya iske inda ya fito ya fi na gaba sassauci, don gori kala-kala da cin mutunci sun sauke masa a cewarsu yayi kuɗi ya manta da su. Ganin haka ya sa ya bi ta fada, nan sarki Abdul-Jabbar ya sa aka je aka yi komai na auren, haɗe da sanya rana wata goma sha biyar. *** Kwanci tashi ba wuya, wata goma da auren sarki da Maryam ta haifa masa yan biyu duka maza, anyi shagali sosai sarki ya yanta yan kurkuku sannan ya bada Sadaka na kuɗi da abinci ga mabukata. Wannan murna da ya nuna ya kara dasa ma uwargida ummou Hafsa tsanar Ummou Maryam da yaranta. Nan ta bazama neman magani duk inda ta ji ana bada maganin haihuwa ta ke zuwa don a bata na haihuwar ɗa namiji. Cikin ikon Allah yaran na da wata uku ta samu ciki, kuma a watan babban AbdoulHaseeb ya ce ga garinku ya bar husaininsa AbdoulHaleem, Sarki da duk wani masoyin fada yayi bakin cikin wannan rashi da aka yi. *** Anyi bikin Bello da Hafsa cikin kwanciyar hankali ta tare a gidanta da ke bayan fada. Gini ne wanda zai ci mace daya da ya'ya don dakuna uku ne sai falon a tsakiya. Yan uwa sun mata murna suna masu roka mata zaman lafiya da zuri'a dayyaba. Cikin Ummou Hafsa na cika ta haifi ɗan ta mai kama da marigayi AbdoulHaseeb hakan ya sa sarki ya maimaita masa sunan. *** Tun bayan haihuwan AbdoulHaseeb ba'a sake haihuwa a fada ba, duk yanda sarki ya so Ummou maryam da ta nemi taimako ta ki don a cewarta "Haihuwa, mutuwa da aure duk na Allah ne, in lokacin yi bai zo ba duk wayon mutum da dabaransa ba zai yi ba" da kalaman da take kwantar ma sarki rai kenan ya hakura duk da yana ji a jikin sa asiri aka mata akan haihuwa. Bello da Hafsa na zaune cikin zaman lafiya amma ganin shekara takwas ya wuce ba tare da ta yi ko ɓatan wata ba, ya sa suka dukufa addu'a, azumi da sadaka. In suna zaune ko tafiye ba abin da suke ambata daga istigfari sai RABBI LAA TAZARNI FARDAN WA ANTA KHAIRUL WAARITHEEN saboda addu'ar da annabi zakariyya ya yi kenan Allah azurta shi da Yahya. A shekaran su na tara ne ciki ya ɓullo a jikin and murna a wajensu ba'a magana, sun yi godiya ga Allah sannan sun maida hankali wajen ci gaba da rokon sa akan ya sauke ta lafiya sannan ya albarkaci abin da za ta haifa. "Kin san buri na Hafsa, in haifi ya mace mai kama da ke, in ba ta daɗin da babu wanda zai taɓa ba ta a duniya" Ya zama wakan da Hafsa ta hardace daga bakin mijinta. "Allah dai ya bamu masu albarka" kan zama amsar ta. Cikin ikon Allah lokacin haihuwarta na isa ta haife ya mace mai matukar kama da mahaifinta. Farin ciki a wajen sa ba'a magana nan ya saka mata suna Fatima. Tun bayan dawowarsu daga gida wankan jego ya maida shi jiki yi ma Fatima wanka. Wani lokaci har goyata yake har barci ya kwashe ta. Hakan ya jawo Shakuwa mai karfi da soyayya tsakaninsu. Fatima na da shekaru uku aka haifi Surayya, daga ita sai Aahil. Bayan haihuwan Aahil ne Alhaji Bello ya auro sadiya, ita yar asalin Kasar Nijeriya ce karatu ya kawo ta Qahɗaanie su ka haɗu su ka yi aure. Zaman lafiya sosai

Chapter 4 of 14