Share this page
surikinsa ba, take ya firgita ya d'ago kai da sauri yana kallon Sufyan. "ka fito min da ita in ganta mana" yace masa a ɗan firgice "BA fitowar ne matsala ba, gwamnati na neman ta wanted, ban san laifin da ta yi ba amma an saka makudan dukiya ga wanda ya bayyana ta a cewarsu yar shugaban majalisar wakilai ne, abin da ya sa ban mika ta ba, bambancin addini da ke tsakanin su biyun" Sufyan ya faɗi kamar yana raɗa. "toh ko cikin gidan zan shiga nima ne dai, ka san de ba zan yi zuwan banza ba ko" AbdulHaleem ya fadi yana mai kokarin Saita kanshi kar ya kwafsa don ranshi ya ɗan fara ɓaci. " zan so haka don ban yarda da jami'an da gwamnati ta turo maka ba, kada su zama Silar Ajali" yace yana masa Jagora, a kofar shiga wani ɗaki ne ya iske yaro kamar humaira, nan gaban saya kara faɗi kada hasashensa ya zama gaskiya. "Ya sunanka" ya ce da shi yana mai shafa masa kai, "Ahmad, za ka sa mommy na ta min magana ta dena kuka?" yace yana kallon AbdulHaleem. "ba ka gane shi ba ko, shine yaron D kukansa ya ja hankalinmu, ashe yunwa ce ta sa yayi kama da karamin yaro, inaga zai yi shekaru hudu fa" Sufyan ya ce, sama sama AbdulHaleem ke jinsa don ya cike da rudani. Ganin bai amsa ba ya sashi yin sallama da shiga dakin, AbdulHaleem ma ya bi shi, wacce ya gani tabbas ita ya ke zato. "Ramlat" ya fadi muryar sa na rawa. Mikewa tayi da sauri ta nufe shi kamar za ta rungume sai kuma ta tsaya, tsugunawa tayi ta saki sabon kuka, babu abin da take bukata sama da taji an rungume ta ana bata hakuri, so take ta faɗi matsalan ta ga wanda zai fahimce ta, so take a ce mata tayi gagganci ayi mata fada sosai, sai gashi Allah ya kawo mata wanda bakin ciki da cigaban sa ya kaita ga fadawa halin da take ciki a matsayin wanda shi ne kawai zai taimaka mata. "Zan samu niqabi anan kusa, ko da kuwa a fita a siyo ne?" AbdulHaleem yace yana mai tambayar Sufyan wanda kallon su yake cike da mamaki. "kanwata tace, aure ya kawo ta garin nan, aka aiko mana da sakon rasuwan ta" yace ganin kallon da Sufyan ke bin su da shi. "Maman zahra kan yi amfani da shi zuwa islamiyya, toh sai ta yi amfani da shi" ya ce yana mai mik'ewa. Ɗauko niqab din yayi ya ba ta, har a lokacin kuka ta ke yi mai tsuma zuciya. Mik'a mata yayi ta amsa ta sanya, AbdulHaleem bai ce komai ba ya juya ya fita, Sufyan ya biyo shi rike da Ahmad ita kuma ta shiga ta yi musu Sallama aka rabu ana kewa. "Ka nemi gidan siyarwa ka siya ka koma cikin sirri, zaman ka a nan akwai hatsari" AbdulHaleem yace yana mai mik'a Masa wasu dolloli da bai san yawansu ba. Sufyan bai so ya amsa ba amma kallon da AbdulHaleem ya masa na rokon ya amsa ne ya amsa sannan su ka fita. Wa'inda ke waje sun yi mamakin ganin AbdulHaleem da yaro da kuma mace sanye da niqabi. Nan yan gulma a cikinsu su ka fara kallon kallo yayin da wasu su ka basar. Bai ce musu komai ba ya isa ga motar sa nan ne aka bude masa, Ramlat ta fara shiga sai Ahmad kafin shi ya shiga. Babu wanda ya maganta cikinsu har su ka isa filin jirgi, nan su ka shiga jirgi sai daular Musulunci Qahɗaanie. Sai da la'asar jirgin su ya sauka a Qahɗaanie nan din ma mota ce ke jiranye s wajen don Tafiya masarauta. *** Labari ya riga su isa don jakadan Qahɗaanie ya kira mai martaba ya fadi masa aure AbdulHaleem fa yayi a Ghana kuma har da rabo, don dai shi kam shaida ne a yaya mata Fatima ta haifa masa. Ko da mai martaba ya ji shiru yayi bayan ya sallami jakada. A sanina AbdulHaleem ba zai taɓa aure ba da izinin sa ba duk kuwa rashin tabbas na ɗan yau amma ya hakura ya jira zuwan sa. Haka wajen Ummu Maryam da gidan su Fatima duk tsegumin ya is ko su amma sai su ka fi Ta'allaka da cewa Fatima ce dama Ghana ya ajiye ta kenan. Daga kallon da ake jifan shi da ya san wani magana ta shigo masarauta hakan ya sa ya wuce da zubaida ɗakin Ummu Maryam ya kuma umurce ta da kar ta yarda a ga fuskanta. Sannan ya wuce majalisa inda ya iske wajen makil da mutane kamar jira ake a ji daga gare shi, ga yan jarida da ma'aikatan gidan jarida kamar su aljazeera da sai sauran su. Hankalinsa ya tashi don Kuwa ya san bayyana Ramlat yanzu kamar zuba fetir ne a wutan da ke ci balbal. Bayan ya kai gaisuwa ya samu wajen Zama kamar kullum ba tare da ya furta komai ba kamar yanda mutane su ka so yayi. "mai martaba an samu ɓarkewan gobara a Hilaalu Qamar, mutane fiye da 100 sun rasa rayukansu kuma har gobe ba'a san Silar ta ba" cewar wani ɗan sanda da ya shigo yana haki. Karkade kai AbdulHaleem yayi don ya san ba kowa ke da alhakin wannan abin ba sai ISMAALIE, ya san shirun sa su ka yi wani shiri ne na daban. "A shirya mana tafiya zuwa wajen yanzu, sannan a haska komi ga mutanen gari" AbdulHaleem ya faɗi yana mai cijewa. Sarki ya girgiza kai alamun nuna jinjina, hakan ya sa su ka fita zuwa wajen. Tafiyar minti talatin su ka yi zuwa wajen. Cincirindo mutane ne ana tsamo gawawaki da wa'inda ke da sauran ransu amma sun jikkata sosai. "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun" kawai AbdulHaleem ke fadi don bai taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba. Tare ya shiga cikin yan kwana kwana ana kauda gawawaki ana saka wa'inda ke d rai cikin motar asibiti. Suna yi suna duba fuskokin gawawakin da ba su qone kurmus ba, don gane mamatan. Anan su ka tsinci wasu gawawaki guda biyu a kusa da juna kafafun su ne kawai ya ƙone, AbdulHaleem ya kalle su ya kara nan kawai zuciyar sa bata bashi ba, nan ya sa aka ɗauke su hotuna sannan ya sa aka haɗa su da sauran. Sai da su ka sallace su sannan su ka birne su gaba daya, sheikh Yusuf ya musu wa'azi mai shiga zuciya duk ana mai nunawa live a dukkan tashoshin talebijin, hakan ya kara ma AbdulHaleem daraja da Martaba a idon duniya Manage this.. Love u all 💞💕😘😍 Add Vote Happy birthday, sweetie. May you always believe in yourself and follow your bliss, wherever it takes you! Wishing you a birthday as beautiful and bright as you, dearest daughter! Have an incredibly wonderful birthday, our sweet little angel Hafsa (Haneefa) Sai da aka kwana uku ana makoki, da su AbdulHaleem da sauran manyan masarauta, a cikin kwana ukun nan AbdulHaleem baya ko runtsawa, kokari yake ya gano su waye mamallakin wannan fuskan ta wata na'ura da ya samo daga Amerika wanda aikinsa tantance sassan jikin dan adam ne, wannan na'ura in aka sanya ko da hoton Yatsa ne zata aika hoton yana gizo in da zata dauko hoton da yatsan nan ke ciki da inda hoton yake. Sai da yayi kwana uku kafin ya samu aka samo masa hotuna guda goma na mutanen nan biyu kusan duk hotunan a tare su ke ɗauka. Har ya cire rai ya fara tunanin zargin su kawai yake kila kasuwanci ya kawo su kasancewa Hilaalu Qamar na da babban kasuwa da ake zuwa cin ta da ga fadin duniya. Sai ya ga an sa masa next, wato da sauran bincike kenan, bai yi qasa a guiwa ba ya latsa nan ya samu abin da yake so. Wato wasu hotuna ne nasu tare da manyan yan ta'adda, majalisar ɗinkin duniya ta sanya binciken su. Buɗewa yayi da kyau nan ya karanta takaitaccen tarihin su. Daya daga cikinsu Joseph Jones dan asalin Nairobi ne, a kasa sai aka ambace shi da zama dan bindiga, shi kuma na biyu Yasser Musa dan Kasar Somaliya ne, shi aka ambace shi da laifin ta'addanci, nan takaici ya cika AbdulHaleem wato in musulmi zai fitar da sanda ya daki wani toh ta'addanci me amma in wanda ba musulmi ba zai yi wani aiki da ya shafi kisa toh tabbas shi din ko dan bindiga ne ko kuma mashayi. Cigaba da bincike yayi har ya samo wani hoto na su da ya fito sosai a nan ya adana hoton ya ajiye kwamfutar. Daga nan ya aika ma jami'an tsaro da kuma yan jarida don a fada ma duniya wa'inda su ka aikata wannan ta'asan sannan ya yi kira ga saura da su guji fadawa tarkon su. Hakan ya kawo cecekuce, yan siyasa na duniya da manazarta suna kara jinjina ma masarautar Qahɗaanie na amfani da hanyoyin zamani wajen magance ta'addanci. Yan kungiyar ISMAALIE kuma hakan ya sanya masu tsoro da dan firgici don jin kalaman masarauta akan tsatsauran hukuncin da za'a masu in an kama su, sannan ga kyauta ta musamman ga wa'inda su kayi saranda. Wannan ya sanya su shirya taron gaggawa a gidan Amir Alhamzie Wanda ya dawo Zangon Qahɗaanie ba tare da sanin kowa ba sai su yan kungiya. "Wai ni ban gane ba, mun dawo Qahɗaanie baka barni na je ga Ammie ba, kullum kana hanyar fita, kai ba soja ba amma duk wani nau'i na bindiga kawo maka ake, me kake yi da su" zubaida ta tambaya cikin fushi, ta rasa gane sana'ar mijinta sannan an kawo ta wani gida an garkame. "Kinga yanzu ina da taro, kar ki ɓata min lokaci. Kar ki damu ba abin da ya sami dangankinki, Ramlat ce ma de ake kan nema wata shida kenan ita da yaron ta su ka gudu. Wacce ba ta iya hakuri m Ibadan aure ba ta ya za ta yi nasara gobe kiyama" yace yana ratsewa ta gefen ta ya na mai ficewa haɗe da garkame qofa kamar yanda yake mata. Zama tayi daɓas a wajen tana tunani in har Ramlat za ta gudu toh cikin biyu akwai ɗaya, walau su na magana da Fatima ta yaudare ta ko kuma da gaske mijin nata na da wani dodo a kwabat. Shiru tayi tana tunani itama ga ta nan dai, kwanaki an ce Qahɗaanie na cike da hatsari da karancin tsaro, amma ita gidanta babu wani abu makamancin haka. Sai dai kuma kalaman mijinta a ko da yaushe na 'mun kusa mulkan Qahɗaanie, na kusa zama sarkin Qahɗaanie' ya faɗi mata hakan ya fi sau a kirga amma bata taɓa yin ma kalaman fashin baqi ba se yanzu. Tashi ta yi zuwa dakin sa, tana mai addu'ar bai kulle ba, don ba kasafai ya ke kullewa ba tun bayan da ya sa Allah ya isa in ta shiga ba tare da izininsa ba. Ajiye yaron da ta ke goye da shi tayi gefen yayansa dan shekara huɗu sa rabi sannan ta je. Durowowi ta fara bincika anan ta ga abin mamaki, bindiga, kwaroron roba, guru, layu, wayoyin cable da dai sauran abubuwan ta'addanci kamar su wukake girma girma. Haka ta cigaba da bincike nan ta ci karo da jaridan da aka manna manyan yan ta'addan Afirka, sai ga hoton mijinta a matsayin Adjetey ba Abdallah da ta sani ba, kuma a matsayin mataccen ɗan fashi D gwamnatin Kasar Ghana tace ta hallaka saboda laifin fashi. Ko da ta ga kwanan watan nan ta Shiga tashin hankali Saboda tserar wata daya ne da lokacin bikin su. Tunawa tayi da zancen Fatima da take faɗi mata aibun auren wanda ba ta sani ba, bata san inda ya fito ba kawai don ta matsu ta yi aure. Kuka ta fara kamar ranta zai fita amma sai tunanin hakan ba shine mafita ba, ya sa ta samun kwarin guiwa don samun cin ma nasara. *** Ramlat tun bayan isarta dakin Ummu maryam ta ke cikin dar-dar, amma kuma ganin yanda Ummu ta amshe ta ya sa ta sakin jiki, gobaran da aka yi ya sa ba'a bi ta kanta ba, sai da aka gama makoki. AbdulHaleem neman Mahaifin ta da mahaifiyar ta yayi sannan mai martaba da kuma Ummu nan su ka hadu a dakin sirri na masarauta kafin ya aika ma zuwan ta da na yaron. "Ramlatie!" Hajiya Amina tace tana rungume er ta cike da hawaye. "Na san kai alkhairi ne, mun gode Allah ya saka da alkhairi" ta faɗi tana shasshafa er ta. Maganar sai ya ba Alhaji Yahuza dariya, wato sharrin da take kira ne yau ta kira da alkhairi. Isa ga Mahaifin ta tayi shima rungume ta yayi sannan ya sumbaci goshinta . Sai da su ka gama murna AbdulHaleem ya faɗa masu inda ya haɗu da ita, da kuma amanar ta da ya bari a hannun Sufyan. "Zan wuce da ita wajen Fatima saboda tana cikin hatsari" ya kammala da faɗin haka. "ban yi shekara ba na fahimci sana'ar miji na ba komi bane sai shan jini da kungiyar asiri, duk yanda na so na tuntuɓe ku na kasa sai daga baya na aika ma ukhty Fatima sakon text daga wayar wata matar shugaban sa. Ni dai na san na goge text din amma ba'a yi sati biyu ba ya dawo ya min dukan kawo wuka wai na faɗi a gidanmu yana shan jini, wacce na tura mawa sun bar Qahɗaanie kuma a satin za'a je a kashe mijinta. Tun da ga ranar sau 1 ake bani abinci, sannan in ya tashi nema na baya min ta inda aka halatta, haka zai qulle ni ya gama abin da yake da shirin yi. Haihuwan Ahmad ya sa nayi tunanin zai raga min amma maimakon haka sai abun ma ya karu. Ana cikin haka mijin zubaida ya zo gidan mu, anan ya ke fada min da hannun sa ya kashe mijin ukhty Fatima, inyi ladabi irin na zubaida in ci moriyar rayuwar duniya. Nan fa na nemi yafiyan miji na muka zauna lafiya, a lokacin na samu saida har ya ke ganin na miqa wuya ya fara bari na zuwa kasuwa da asibiti amma shi ma da masu tsaro na. Bayan shekaru hudu ne wata rana na samu maganin barci na zuba musu a lemun abarba da kwakwa, nan su ka sha su ka fara barci. A haka na gudu na bar gidan ba tare da sun sani ba. Rashin sanin wajen zuwa ya sa mu ka isa dajin da aka tsinto mu, ina ga mun yi kusan wata shida a wajen ko fiye don kuwa tun abin da na qullo mana ya kare muna samun kayan marmari har mu ka kai ga cin ciyayi har mu ka koma shan rawu" ta faɗi tana zubar da kwalla. Haka duk wanda ya ke zaune sai da zuciyar sa ta motsa don tausayin ta. "ina ga zuwa Anjima da maraice za mu wuce, na bar iyali na da juna biyu duk da na san Don zai kula da ita amma tana bukatata" ya ce yana kwanto ma mai martaba. " malam ba za ka tafi da ya'ya na biyu garin da ba mu sani ba" cewan Ummu Maryam "Italiya fa nace zani, ban bar wajen ba, ina can duk da ina tunanin komawa Mauritius" ya faɗi yana dariya. *** Jirgin su na tashi Ammie ta daga waya ta kira Adjetey, da murna take ce masa yanzu jirgin su Ramlatie ya tashi da mijin Fatima ai shine ya tsinto ta, ai yace daga Italiya zasu koma Mauritius. "Mauritania dai ko, ni ban taɓa jin kasa haka ba, ai ko haska yace kila ya faɗi ne don ya shashantar da mu ne" ta bada amsa. "ai gara da ya ta fi da ita, shegen mijinta ya je ya ci kanshi, wallahi ya ci amana since shi yasa nace miki da farko na sha sharri ce kawai" ya fadi yana nuna farin ciki. Zubaida da ke zaune a wajen ji tayi kamar ta shiga cikin wayar ta nakaɗa ma Ammie duka. Add Vote double update Is an angel's birthday. .. Ko da ya gama wayar ya fara bata labari ji kawai tayi ta kara tsanar sa, wanda zai iya nuna farin ciki akan abin da ta yi imani zuciyar sa na cike da bakin ciki toh ta tabbatar abubuwa da ya kasance yana ɓoye mata yana cutar da shi da yawa su ke. Bata dawo daga duniyar mamaki ba sai taji yana faɗin "Banza an baka amanar yarinya ka cinye, Allah ya kubutar da ita ga ta anan AbdulHaleem ya dawo da ita, ya kuma..." bai kai aya ba ta fisge wayar ta buga a kasa, firgigit yayi yana kallon ta " a matsayin adjetey kake magana ko Abdullah?" Ta ce tana mai tsallakewa ta wuce ta barshi baki a hangame. Tunani yake ya akayi ta san wannan sunan ko kuma dai ta samu mai kawo mata tsegumi ne, amma kuma ko da yaushe rufe ya ke barinta. Tashi yayi don neman hanyar yin waya don kuwa dole yayi ma tufkar hanci. *** A gajiya su ka isa Milan city, Ramla sai Kalle Kalle take don Tsabagen kyau da ta iske, a da tayi tunanin kyau na Qahɗaanie saboda ganin yanda ya ninka Ghana a kyau se yanzu take ganin Afirka ba komai bane cikin ta sai dauɗa. Tun tashin duniya uffan bai ce mata ba, har su ka isa Milan city, anan ne su ka iske su Fatima a wajen jiran passenger. Turus Fatima ta tsaya tana kallon mijin ta rike da yaro mai kama da Yaranta, sai dai shi baqi ne, a daga bayansa kuma mace cikin niqabi. Daurewa tayi ta isa gareshi, bayan ya ɗaga yaran yana sumbatar su. "Papa wanene wannan handsome din" humaira tace tana shafa fuskar sa. "ɗan uwanku ne sunan sa Ahmad. Ahmad ga yayyin ka" yace yana haɗa hannuwansu. "muna da tafiyar mintuna kafin isar mu gida fa" fatima tace zuciyar ta na kuna, ko ta ina zata fara ne ma wai itace da kishiya. Bai ce mata komai ba har su ka isa mota, ya shiga mazaunin direba ya zauna hakan ya sa zama baya tana kumbure kumbure. Kallon ta yayi ya girgiza kai, bai ce komai ba su ka. Cigaba da tafiya, ita dai Ramla bata dage niqab ba saboda umurnin da ya bata kenan. Suna isa gida ya d'auki kayan Ramlat ya shiga da shi gida, su kuma su ka biyo sawunsa, yaran ko kula da su ba su yi ba sai wasan su su ke. Sai da su ka shiga cikin gida sannan ya ce ma Ramla ta daga niqab ɗin. "Ramlatie" tace tana mai ja da baya, "Amma kun ɗauki alhaki don kila jini na ya kai 300" ta ce tana rungume ta. "Ai Kiris in fashe da dariya, nace Ukhty da kishi take" nan su ka sa dariya su duka. Shi kuma AbdulHaleem ya haɗe rai kamar bai san suna yi ba. Tashi yayi ya shige dakinsa har da sa makulli. "kamar fa yayi fushi ne" Ramla ta ce tana kallon er uwarta. "manta da shi, zo muje ki yi wanka kinji" Fatima ta faɗi tana mai mikewa. *** Kwana su kayi suna hira, sun sha kukansu yayin da Ramlat ke ɓata labarin rayuwar aurenta, "Ai Ukhty na ɗauki darasi, gaggawa a aure ba shi ne jin daɗin auren ba, Hmmmn na ga rayuwa ni yanzu ban ma san makoman aure na ba" ta ce tana share hawaye. Add Vote "ai kin san kowa da kalar kaddaran sa, mutum kan zama sanadi ne kawai. Ba don kiji haushi ba, sai da na kusa talatin amma kuma wallahi se dai irin faɗan nan, amma kam ban san bakin cikin aure ba" fatima tace tana tausaya ma kanwarta "ai Ukhty zubaida ce abin tausayi, mijinta ashe ɗan fashi ne, wai a Ghana an san an kashe shi ashe fitar da shi aka yi sai ya samu masauki a Zangon Qahɗaanie" tace tana karkada kai. "toh Allah sa baya cikin ISMAALIE don ni tsoron su nake. Oh ni 'ya su, Ammie kuma na, zaune hankalin ta kwance" cewa Fatima "Ukhty wallahi tunani na kenan, iyaye na da aiki a gabansu, son abin duniya na sawa ba sa wani maida hankali wajen sauke hakkin su. Allah dai ya bamu sa'a" "Aameen Ramlatie kina jin kiran sallah kuwa, Taɓ lallai mun raba dare, bari in je in lallaɓa sarkin gobe" Fatima tace suna dariya. *** Ko da ta isa ta iske shi zaune saman darduma yana karatun alkurani. Zama tayi gefen sa har ya kai karshen suratul Maryam, yana shirin fara basmala na suratul ɗaha ta amshi qur'anin. Banza yai mata ya cigaba da istigfari, a bayyane tana jinsa. Kamo hanunsa tayi ta daura asaman cikinta hakan ya sa ya kallo ta yana mai kara haɗe rai "kin san lokacin ibada ne yanzu ko, don an kira sallan farko" ya ce cikin dakewa. "wani Ibadan na ke sonka da shi, kira'arka da na ji ya tayar min da kwadayin ka" ta rada masa cikin kunne. Duniya in akwai abin da ya ke so ta nuna tana muradinsa hakan na kara masa son ta da begenta a cikin ransa.. Amma duk da haka ya dake bai dai motsa ba sannan bai taimaka mata ba ita kuma bata kyale shi ba. Bata wani sha wahala ba ya kasa jurewa ba shiri ya bada kai.. *** Tun da suka koma AbdulHaleem ke shirye shirye komawar su Mauritius saboda ya san rayuwar sa da na iyalinsa na cikin hatsari, hakan ya sa ya nemi Don da ya bashi jirgin sa mai tashin angulu su ka isa Republic of Mauritius (French: République de Maurice) , sun fara sauka a babban birnin Kasar wato Port Louis, da Niyyar yin sati ɗaya don su ga garin da ake kira da Aljannar duniya. Mauritius kamar kasa ce a cikin Afirka sannan itace Kasar da ta raba Afirka da Asia, zagaye take da ruwa (island) fiye da kashi hamsin da ahlin Kasar yan addinin hindu ne, kashi 13 ne kawai musulmi amma hakan bai hana musu daraja musulunci ba. Bayan sun share mako suna ganin gari sannan su kayi kaura zuwa THE ST REGIS MAURITIUS Resort , wanda ya ke Kewaye da ruwa, ga wajajen shakatawa. Anan su ka kara gode ma Allah da ni'imar da yayi musu don kuwa hatta shi AbdulHaleem bai taɓa sanin da wani kasa Mauritius ba balle abin da ta kunsa sai da yake Qahɗaanie yana bincike ya gano ta cikin map din duniya. Add Vote Suna zaune a cikin resort amma Tunaninsa na Qahɗaanie, tun bayan da labari ya iso shi akan an sace matar Galadima da Ummu Hafsat wacce ba ta daɗe da warwarewa ba, an sace su ne a cikin asibiti Ummu Hafsa ta je don kara duba lafiyan ta, sannan ga wasu yara kanana da aka sace ana sakin ma masarauta gawawaki ɗaya bayan ɗaya. Latso tauraron dan adam ɗin da aka jefa Qahɗaanie ya yi, Ya sanya lambobin sirri take ta haska masa daular. A hankali ya ke bin sawun da yake tunanin nan ne mabuyar yan ta'adda yana yi yana aika ma sojin Qahɗaanie da sako (signals) su kuma a can suna amfani da shi wajen bincike. Hankalinsa ya dauku ya tuna da ai suna fitar da fayafayen video, bai wahala ba sheikh Google ya samar masa wanda aka turo karshe. Nan ya shiga ciki ya fara lalube yana dubo lambobin internet da aka sa wajen shigar da bidiyon. *** Tun bayan warkewan Ummu Hafsa ta ke karɓan magani daga likitan masarauta. Tayi kyau abin ta amma ko da yaushe burin ta fita, hakan ya sa ta haɗa baki da likita akan za ta je asibiti don wasu gwajin. Hakan ya sa mai martaba ya haɗa ta da matar Galadima don kula da ita. Sun kammala da likita sun fito ofishin kenan ta ji bindiga a kunnen ta. "wuce mu tafi" suka daka mudu tsawa hakan yasa su ka bi su ba tare da gardama ba, ba ta kofar da su ka shigo aka bi da su wani wajen. Bakin mota mai rufaffen Baya (van) aka shigar da su. Shigar mutan Kasar ke yi kenan Tafiya ake da su kamar za su bar gari, ihu da kabbara kawai su ke yi suna harba bindiga sama, hakan ya kara ruda cikin Ummu hafsa, gani take kawai mutuwa zata yi. Ta ina zata fara, me ya sa sai ita ne ko da yaushe a saninta ko a jiya Ummu Maryam ta je unguwa kuma ta koma

Chapter 13 of 14