irin mazajen da kika haɗa min ya'ya da su.
AbdulHaleem mai martaba ya min bayani, kuje Allah ya muku albarka ya tsare mana ku, zan kula da komai fatima kada ki damu kin ji, maza ku je ku cigaba da shiri" ya karasa yana mai sallaman su fatima wacce ba haka ta so ba, ta so ta rungume mahaifinta ta bashi hakuri su yi nafila tare su roki Allah tare kamar yanda suka saba. Kawai sai ta fashe da kuka tare da fita, kowa ya tausaya musu don matan sun san kukan da take ba na rabuwa bane, na tafiya ta bar mahaifinta cikin kunci ne.
Add Vote
Haka su ka isa gida hawaye kwance a fuskarta, a tunanin ta za su isa Fada ne amma sai ta ga yayi hanyar gidansu.
"ya kamata mu je wajen Ummu ko" tace cikin kuka tana share hawaye, shi takaicin kukanta ya cika shi don bai ga abin kuka ba, sai kace wacce za'a yanka in aka tafi da ita.
"Nace miki an kore ni daga Fada, duk wanda ke son gani na shi zai biyo ni, in kuma za ki je sai ki aje min ɗa na ki je ke kaɗai" ya faɗi a fusace duk da ba hakan ya so ba. Bai kara ce mata komai ba sai figar motar da yayi har ta tsorata. Kallon sa tayi sai ta maida kallon ta ga tagar motar tana kallon titi. Ko da su ka isa gida basu ce da juna uffan ba. Ita wajen kayanta ta je ta haɗa, kayan jariran da su ka fara siya da gadon ta kalla sai hawaye.
' yanzu Shike nan duk shirin mutum
ba tabbas akai, lallai WA MAKARU WA
MAKRA ALLAH, WALLAHU KHAIRUL
MAKIREEN' tace a ranta tana tausayin kanta tana tausaya ma sauran yan Adam yanda mutum yake cike da kashi amma ya zauna yana tsara ma kansa ko wanda ke karkashin sa rayuwa cike da son rai alhali shi ɗin ba komai bane sai digon maniyyi da karshe zai zama abincin tsutsotsi. Ta gama shirya kayan kenan ta jiyo sallamar kuyangin da ke mata hidima nan su ka sanar mata da zuwan mahaifinta. Sam ta manta halin da take ciki na juna biyu ta fita da gudu. Tsaye ta isko shi da AbdulHaleem wani tsalle tayi ta rungume mahaifinta. Haba nan ta saki sabon kuka. Murna take mahaifinta ya shigo gidanta don bai taɓa zuwa ba sai wannan, bakin ciki take saura awanni kaɗan tayi masa nisa.
"Toh Aminiya zan koma tun da kuka za ki yi" yace yana share mata hawaye. "Na sha faɗa miki kuka bai miki kyau ki dena yi" ya kara faɗi yana dariya, itama dariya ta fara tare da jawo hannun sa zuwa kujera,
"Abbie kana lafiya? kayi hakuri kaji, addu'a ce magani, kayi nafilan? Me ke damun ka?" haka ta bi shi da tambayoyi tana rike gam da hannunsa kamar za'a kwace mata shi. Sai a lokacin AbdulHaleem ya fahimci shakuwar da ke tsakanin su nan kuma ya ji takaicin kansa na ihun da ya mata a lokacin da tafi bukatar ya lallashe ta.
" Fatimatuz Zahra! Duk nayi! Ni yanzu yanda zan kuɓuto da Ramla na ke tunani, sanda na so su fahimta sun ki, gani su ke aure ne bana so ta yi, yanzu ga inda gaggawa ya ke neman kaisu ko ince ya kaisu nan." Ya ce yana girgiza kai. Duk sun yi shiru kowa da abin da zuciyar sa ke kintsa masa.
Ganin shirun yai tsawo ne Abbie ya sake katse shirun
" AbdulHaleem ga amanar Fatima nan na baka a karo na biyu, tarbiyyanta, farincikinta, koshinta, suturarta, ilimin ta duk na wuyan ka. Kai ne miji Kaine aboki don ban yarda ka kwace min amintakan ba" Nan duk su ka dara gaba ɗaya.
"Abbie ni de na kwace mata gurbin ta, ka ga aminci tsakanin namiji da namiji yafi, nine amini itace matar amini dukkanmu kuma ya'ya in bata yarda ba ta zama matar ɗa" AbdulHaleem yace cikin dariya, ita kuma ta zumburo baki. Haka Abbie ya musu nasiha sosai akan rayuwar aure da kuma hakkokin da ke kasu. Ya musu addu'a sannan ya sallame su ya tafi su na kewa. Ya tafi ba da jimawa ba tawaga daga fada su ka zo, mai martaba ne da Ummu Maryam. Shimfidar jan kafet ne ya sanar musu da shigowar mai martaba. Cikin ɗaki su ka shige don Fatima ta sauya kayan ta shi kuma AbdulHaleem bai san irin tarbon da zai samu daga mai martaba ba.
Tare suka fito cikin shirin tafiya, sun mika gaisuwa ga iyayen da ke zaune a kan kujera, yayin da masu take musu baya da masu tsaronsu suka tsaya daga waje.
"Yanzu wane kasa kuka shirya tafiya?" mai martaba ya tambaya bayan sun gama gaisawa.
"Italiya" yace kai tsaye
"ina aka samo muku muhalli a Italiyan" ya sake tambaya
" lardin Milan (Milan province)" ya sake amsawa yana sunkuyar kai.
"Allah ya cigaba da tsare ku, ya baka ikon ɗaukan darasin da ya kamata ka ɗauka" ya ce yana zaune ba tare da ya sake cewa komai ba.
"Aameen ya rabbi" su ka ce suna godiya. Ummu kuwa ba abin da tace sai Fatima da ta ke ma nasiha akan hakuri da kuma kula da kai a matsayin mai juna biyu. Daga nan mai martaba ya cire kuɗi ya ba Fatima ya ce ta rike zai mata amfani. Da haka ya su ka tashi su ka juya, Fatima da AbdulHaleem na musu rakiya jikin kowannensu a sanyaye.
***
Tun da jirgi ya ɗaga daga Qahɗaanie bai tsaya ko ina ba sai Leonardo da Vinci international Airport Wanda aka fi sani da fiumicino Airport da ke birnin Rome, can kusa da kudanci Kasar.. Sun iske motoci na jiran su daga ofishin jakadancin Qahɗaanie, nan su ka isa su ka bada shedan isowarsu sannan nan ma aka basu kuɗi daga mai martaba sannan aka tura wa'inda zasu raka su lardin Milan.
Jirgin sojin Qahɗaanie ya sake ɗaga su daga fiumicino airport zuwa Malpensa airport da ke birnin Milan inda a nan su ka iske Stefano Angelo yana jiran su. Anan AbdulHaleem ya sallami duk wani ɗan rakiya don bai ma son a san inda za su sauka. Nan fa su ka so su yi gardama don mai martaba ya umurce su da su tabbata sun ga gidan da danshi zai sauka sannan a aje wasu daga cikin hukumomin tsaro a wajen don kula da shi. Amma AbdulHaleem ya tuɓure ya ce babu wanda zai bi shi, ya gode da karamci kuma ya bar Qahɗaanie kenan har abada.
Labarin nan ya girgiza mai martaba don kuwa ba su bar filin jirgin ba sai da su ka kira shi a waya su ka faɗa masu. Yaji takaicin bakin zuciya irin ta AbdulHaleem amma Ace ana nuna masa gabas yana shi kudu zai fuskanta. Bai ce komai ba sannan bai nuna a fuska ba sai ya cigaba da zancen da su ke da yan majalisa.
Faisal Musayyib, ɗaya daga cikin sojojin da su ka rako su AbdulHaleem, kuma idon Ummu Hafsa ne ya sa waya ya kira ta bayan ya ɓoye kan shi.
"Allah ja zamanin uwar sarkin gobe, ai kam dai zance ya tabbata, ya fusata ya aiko ma mai martaba zantuttuka marasa daɗi a cewarsa shi ba zai sake dawowa Qahɗaanie ba, ina ga lokacin dawo da AbdulHaseeb yayi don ya kasance kusa da mai martaba" ya faɗi cikin murna da farin ciki.
"faɗi abin da kake so Goron Albishir na aika ma iyalinka"
"Ummu duk abin da kika bada ina farin ciki, amma ina so a ba ni shugaban rundunar tsaro ta daular Qahɗaanie" yace don shi kanshi burin sa kenan. Don tun da ya taka mukamin manjo general yake Harin wannan mukamin.
"toh Faisal za'a kwatanta, na gode Allah ya muku albarka" tace tana murmusawa.
Faisal Musayyib jinin masarautar Qahɗaanie ne sannan kuma miji ga er Ummu Hafsa ta huɗu, wato Maimuna. Tun bayan aurensu ya shiga sojin Daular Qahɗaanie, kasancewar sa jinin masarauta bayan naɗa sarki Abdoul Jabbar ne ya maida shi karkashin masu kula da masarauta (Royal guards). Aminci da kuma kallon ɗa da sarki ke masa yasa mai martaba ya sa shi jagorantar tafiyar AbdulHaleem saboda hankalinsa bai bashi ba, ya san ana iya kashe masa ɗa yana ji yana gani.
***
Adjetey na zaune ranshi duk ba daɗi, yana ji da Aamir alhamzie, sannan wani banza na neman ya kassara masa, ko ba komai zaman sa a Masar ya koyi larabci, yanzu ya san ko bai karanta shari'a ba zai iya kwatar ma Alhamzie duk wani yanci ba tare da an cuce shi ba.
Wayar sa ya ɗauka ya sake kiran Aamir,
" Ubana da ya fi kowa" ya ce yana dariya
"ka na cike da albarka, naji sauki sosai, an cire harsashin don a kafa ya harbe ni" yace yana dariya
"MaashaAllah! Zan dawo nan kusa, ya kamata mu haɗa kai da ishmalie mu kwace Qahɗaanie, ko AbdulHaseeb ba zai yi sarautan ba" ya ce cikin kufula
"Ai ance ɗan iskan ya gudu, da ya jira mun gwada karfi da shi amma tun da uban sa na girmama ni kuma yana girmama zumunci za mu ɗaga musu kafa,, amma za mu buɗe namu daular a sannu sai mu ci su da yaki" yace yana so ya hana adjetey zuwa don ya san in ba su bari ya samu ilimin ba, ba za su wani samu nasara yanda su ke so ba.
"Abba ka bani dama in nuna kwanji na, ka yi hakuri in dawo. Sarauta ai ba sai da ilimin shari'a ba, mu karfi da yaji za mu kwata. Ka amince min kawai" ya ce yana mai magiya yana nuna masa yanzu da zafi zafi akan bugi karfe. Har sai da ya amince sannan ya aje wayar. Nan ne Zubaida ta shigo da cikin ta da ya tsufa, in akwai abin da adjetey ke so yana bayan matarsa da abin da ke cikin ta. Rungumo ta yayi ya zaunar a Saman cinyarsa. Sannan ya ce da ita
"kwana biyu na kasa gane kanki me ke damun ki" ya ce mata cikin rada.
"Ammie ce, sati biyu kenan ban ji daga gareta ba, kace su Fatima sun bar Qahɗaanie amma kuma ba ta kira ta bamu labari ba, sati biyu fa, ko dai mutuwa tayi" tace cikin hawaye. Hakan ya sa ya ji tausayinta don shi ya toshe lambar Ammie daga wayar ta. Ciro wayar sa yayi ya kira ta bugu uku ta ɗauka
"Ina kuma shige Zubaida" tace muryar ta na rawa
"Mun yi tafiya ne Ammie" ya faɗi, Zubaida ta sa ido tana kallon da ya sharara. Sai ya rufe mata baki ta hanyar sa mata wayar a baki.
"Ammie na yi kewar ki" Zubaida ta faɗi,
"kin san kuwa Ramlatie na hannun ɗan yan kan kai ne, mijinta shan jini yake yai arziki, Abbie kuma ya sake ni" tace tana sakin kuka, don da fari ta yi tunanin sharrin su fatima ne, sai da ta koma gida yayanta ya sa bincike nan duk hotunan Nasiruddeen ya fito a matsayin ɗan fashi. Sai kuma inda ya fito a matsayin ɗaya daga cikin member na wani club a Ghana wacce ake zargin masu shan jini. Nan dangin ta su ka sa ta gaba da sunan mai siyar da ya'ya saboda son abin duniya.
"ai ko ni ma ɗin ɗan fashi ne, don in kisa ne ba zan iya sanin adadin mutanen da na kashe ba, yanzu ya kenan" Adjetey ya faɗi yana mai katse wayar. Hajiya Amina kuwa suma tayi a wajen don Tsabagen tsorata da tayi.
Ashe ba yawa, da naji hannu na ya fara zafi se nayi tunanin ya kai 5k words ashe ko 2k bai yi ba. Anyway zan kokarta na muku gobe
Insha'Allah.
Ina jin daɗin comments ɗinku, kar ku
gaji, ku yi comment ku yi voting ku
gayyato ahlinku da aminanku.
Shin akwai wani gyara da kuka gani,
ku na iya gyara min ta safiyyahjibril@gmail.com ko kuma
sako ta nan.
Nagode
Ummu-Abdoul
Add Vote
Mahaifiyarta ce ta zo wucewa ta same ta kwance a sume, ruwa ta samu ta watsa mata nan ta farka a firgice. Sanin da tayi abin da ke damun ta ya sa ta cewa " Ai Amina ba ki ga komai ba, ai duk wanda yace bakar tukunya ɗiya ce toh ya goya ta da farar zani" mtswww ta karasa cikin jan tsaki. Kuka sosai Ammie ta saki, shike nan ta yi asarar ya'yanta dama su kenan Allah ya bata kuma ta aurar da su ido rufe. Sai da ta ci kukan ta ma ishi sannan ta mike ta fita da niyyar zuwa ta samu Alhaji Yahuza don ta roke shi ya taya ta neman ya'yanta. Haka ta ke zuba tafiya har ta iso ofishin sa, faɗi ma sakatarensa cewa ita ɗin matarsa ce ya sa ya barta ta shiga.
"Abbie don Allah ka taimaka min, ka maida auren mu wallahi ba zaka sake samu na da matsala ba" tace tana kamo kafarsa. Janye kafarsa yayi ya cigaba da rubutu ita kuwa kuka take ranta ɗaya. Ganin kukan yaki ci ya ki cinyewa ne ya tashi ya iso gareta
"Zan maida ki ɗakin ki in har za ki kwato min ya'ya na daga hannun miyagu. In kin yi haka a yanzu ma sai in maida ki don baki kammala idda ba" yace murmushi kwance a fuskarsa, wani murdawa da cikin ta yayi sai da ta zabura ta kalle shi a firgice.
"Kai ne karfi na Abbie, ka da ka min haka, wallahi ina cikin nadama da dana sani, ka yi min aikin gafara ka taimaka min" tace cikin kuka, kwarai ya so ya fara tausaya mata, amma sai ya basar ya nemi cilla zuciyar sa wani gun daban saboda kada ya tausaya mata.
"Haba Amina, ni ne nan shege mai hana aure mai haiqe ma ya'yansa" ya ce yana mai jin zafi a ransa. Bai kara uffan akai ba ya ɗaga hannu ya nuna mata hanyar kofa, ba ta Musa ba ta gyara fuskarta da hawaye ya kwanta mata ta fice jiki babu kwari. Zuciyar ta na aunowa kamar zata fashe sai ta fasa. Allah cikin ikon sa ne ya kaita gida lafiya don kuwa idon rufe ta ke tafiya.
***
A can Misra kuwa, mutuwar tsaye Zubaida ta yi a wajen, Jin kalaman Abdullahinta ga Ammienta. Shi kuma sai da ya furta sannan ya tuna ai tana zaune a wajen sannan duniya in da akwai abin da Allah ya jarabce shi da so toh Zubaida ce da abin da ke cikin ta, ganin irin daskarewan da tayi ya sa shi ɗan firgita. Ruwa ya ɗebo ya watsa mata, firgigit ta tashi tana zazzare idanu. Lumshe ido ta sake yi nan duk abin da ya faru minti biyar da su ka wuce su ka dawo mata, muryar mahaifiyarta da na mijinta ke mata tsuwa kowanne daga ciki na maimaita abinda kunnuwan ta su ka jiye mata.
'anya ba mafarki nake ba' zuciyar ta ya raya mata hakan amma ganin mijinta zaune da waya a hannu ya sa ta gaskata cewa anyi hakan.
"ke yanzu kin yarda anyi hakan kenan? Ai kawai na faɗa mata ne don na ga alamun an fara cin nasara a kanta, so ake a raba mu fa. Ban san me ya sa za ta yarda da" yace mata cikin rada bayan ya rungume ta tsam a jikin sa kamar yana tsoron rasa ta.
"Amma kuma ai ka san mahaifiyata ce ko" tace tana mai share hawaye da kuma samun zuciyar ta na washewa
"Ki yi hakuri, zan kira na bata hakuri" yace yana manne bakinsa akan nata hakan ya sa ta yin shiru. Cikin salonsa ya mantar da ita damuwar da ke tattare da ita su Lula duniyar da su kaɗai su ka san da shi.
Yinin ranar shi yayi komai na gidan tun daga girki har zuwa shara da komai, daidai da abinci shi ya ciyar da ita a baki yana yi yana kalamance ta, hakan ya sa ta kara so da kaunar mijinta sannan ta qara amincewa babu wacce ta kai ta dacen miji. Sai da ya tabbatar da ta yi barci sannan ya jawo kwamfutar sa ya shiga yanar gizo. Bincike yake akan dabarun da zai fishe shi don shi dai ya ɗauki alwashi ko zai sadaukar da rayuwar sa sau dubu ne sai ya ga bayan Qahɗaanie, don a ce wasa babu abin da zai taɓa Alhamzie ya sa ido ya barshi.
Am so sorry dear ones, wallahi na kasa typing ne, duk na ɗauko system don na yi typing se in kasa.
Akwai whatapp grp ga mai ra'ayin shiga, don zumunci. Mata zalla, WhatsApp me on 08157284163.
BAYAN SHEKARU HUDU
Matashiyar mata ce zaune, kallo ɗaya zaka mata ka san ta haura shekaru talatin da biyu a duniya, a fakaice zaka rantse babu wanda ya kaita farin ciki amma nace ma kallon kwayar idonta zai haska ma mai kallo damuwa a cikin idanunta.
A zahirance talabijin take kallo amma hankalinta gaba ɗaya ya tafi wata uwa duniya wanda hakan ba zai rasa alaka da damuwar da idanunta ke nunawa ba.
"Haba! Kashe kanki kike son yi? Nayi sallama yafi a kirga amma gaba daya baki doron duniyar nan, na gaji da wannan ɗabi'a fa" ya ce cikin faɗa, yana shirin barin wajen yaji an ambaci sunan da dole ya sa ya dawo ya maida kallo ga tashar Aljazira da ta bari kunne
"Daular Qahɗaanie na fama da gagarimin barazana don maganar da ake yi yanzu yan ta'addar Ishmalie sun yi nasarar kwace gwamnatin Daular, ita dai daular Qahɗaanie daula ce da Larabawa su ka kafa shi kusan shekaru dubu daya da su ka wuce, amma chuɗanya da su ka yi da mutanen yammacin Afirka musamman Hausawa ya sa Al'adun su ya gauraye ya zama ga dai shi nan. A yayin da ake ɗauko wannan rahoton ba'a san inda iyalan masarauta su ke ba bayan mutuwar uwargidan mai martaba da aka kashe yayin musayar wuta tsakanin yan ta'adda da sojojin Qahɗaanie..
Su dai ishmalie su na da'awar su kaɗai ke da ɗarikar musulunci na gaskiya yayin da sauran ke kan ɗarika mai cike da son rai da kwaskwarima, su na da littafin su na gaskiya wanda ba qur'ani ba sannan ba su yarda da ko wane hadisi ba don kuwa a cewarsu an sa son rai a ciki... " bai iya kai wa karshe ba ya kashe talebijin ɗin, da dinsa ɗaya yaran sun janye uwarsu da bai san ya zai yi da ita ba.
" Lokacin ɗaukan fansa yayi" ya faɗi a bayyane yana mai jawo na'urar sa mai kwakwalwa ya haɗa da yanar gizo ya shiga wani wajen da shekaru huɗu kenan rabon da ya garzaya cike da burin ba'a canza lambobin sirrin ba. Bai sha wuya ba sai ga shi yana hango masarauta. Mutanen da ke zagaye da ita ɗauke da manyan makamai, tun daga kan bindigogi da tankokin yaki wanda na sojojin Qahɗaanie ne amma kuma wa'inda ke sakaye da wajen wasu mutane ne daban.
"Yaa Mugithu Agithnie" ya faɗi yana furzar da iska. Wasu lambobi ya sake latsawa nan ya hango majalisa tare da wani baqin mutum zaune akan karaga, a shekaru ba za su wuce tsararraki ba amma kuma da gani gwani ne a ta'addanci. Waya aka miko masa nan ya amsa ya kara a kunne, sai ta abin yayi don ya ji yo maganganunsa amma bai ji sosai.
"Haba zuby, ki kula min da yara na, na faɗa miki jihadi mu ke yi, sannan na sa an fitar da Ammie Kasar waje, shi kuma Abbie ya na haɗe da tsohon sarki. Ni haɗin kanki nake nema Qahɗaanie nan da kwana goma za mu chanza masa suna da tuta. Ina sonki da yawa ki kula da yaran" yace yana jefa sumba a iska.
Zuciyar sa na bashi ko wanene wannan yana da alaka da matarsa amma ba ya son ya yarda, chan dabara ta faɗo masa, tashi yayi tsam ya nufi ɗaki wajen matar sa.
"Zan je Qahɗaanie, amma ni kaɗai, in mai martaba ya yafe min sai in dawo in ɗauke ku. Babu abin da nake so sama da farin cikin ki, ki kara hakuri, Abbie da kowa na cikin kwanciyar hankali kin ji. Ya ce yana shafo cikin ta da ya ɗan tasa. Bata ce komai ba sai murmushi don kuwa wata ɗaya kenan da ta fara mafarki da iyayensu da yan uwansu, tun lokacin ta sa rigima akan su koma Kasar su ta gado duk kuwa da cewa ta fi mijin nata amfana da birnin Milan ta Kasar Italiya.
***
Tun bayan rabuwan su da sojojin da su kai musu rakiya, da ɗaukan su da Stefano Angelo yayi bai tsaya da su ko ina ba sai Corso Venezia anguwa ce na manyan masu kuɗi wanda ya kunci abubuwa na ban girma da jin daɗin rayuwa. AbdulHaleem ya so ya gardama amma sai Stefano ya nuna masa zaman sa anan shine daidai, hakan kuma zai basshi ikon samun abin da yake burin samu saboda akwai wani shugaban mafia Fronteno clemenza da ke zaune a nan wajen kuma yana son ya maida shi ubangidan AbdulHaleem.
Sai da su ka dauki kwanaki su na zagaye gari inda duk su ka mace da son Kasar ba ma Milan city kaɗai ba. Gini ne na alfarma inda da gani anyi ɓarna dukiya wajen sarrafa wannan gine-ginen. Su na ganin wajajen su na qara godiya ga Allah AbdulHaleem na cike da burin son maida Qahɗaanie fiye da haka nan.
Ranar farko sun fara da manyan wajen kasuwanci ne inda su ka fara Via Montenapoleone Wani sashi na Quadrilatero d’Oro
Via Montenapoleone ba da mahimmanci sosai a fannin kasuwanci, don kuwa ana iya ce mata masaukin tsadaddun kaya kamar su Gucci, Prada da Valentino. Sannan ana samun kaya yan kanti da hadaddun kayan da aka yi su da fatu, za'a iya cewa nan ne ma mafi a'ala a wannan fannen, ana samun kayayyakin Bottega Veneta, Salvatore Ferragamo and Fendi hakan ya sa ake kallon wajen a kasuwa da ake samun kayan fatu masu lamba ɗaya (world class leather product)
Daga can sai su ka garzaya Corso di
Porta Ticinese
Tana zuwa wajen zuwa ta London ya faɗo mata a rai don kuwa gani yayi ya mata kama da Portobello Road saboda kayan data gani da su ke zarra (unique clothing) , daga nan sun je Corso Vittorio Emanuele
IIwanda ke kusa da Piazza del Duomo city square a tsakiyar Milan city, a nan ta ga shagunan Zara, H&M, Mango da Bershka .
Sun je Corso Buenos Aires, Nan sai da tayi kwalla don tunawa da tayi da Abbie, lokacin da su ka je Paris don wajen exactly Oxford Street da ke London da kuma avenue din des Champs-Élysées da ke birnin Paris.
Ranar a gajiye ya su ka isa gida bayan sun tabbatar da sun siya duk abin da zasu bukata da kuma wasu abubuwa da su ka san zai amfane su.
Washe gari su na fita su ka sake zagaye gari sun je wajajen kamar su : (hotuna yafi ko 😀)
Add Vote
Haka su ka cigaba da zagaye har su ka gama ganin gari sannan Stefano ya samu ya haɗa shi da Don clemenza.
***
Duk wani gata da mace za ta nema toh Fatimah ta samu wajen AbdulHaleem, don baya jira ta nema kafin ya bata duk kuwa da takan ji zafin raba ta da dangin ta da yayi da yanke duk wani hanyar zumunci da su.
Ko da cikin ta ya cika wata tara, daina fita ko ina yayi yana manne da ita don kada haihuwa ta zo musu yana nesa da ita. Allah cikin ikon sa kuwa ranar da naquda ta zo basu ɓata lokaci ba Allah ya sauke ta lafiya in da ta haifi yan uku duka mata.
Haihuwan da ta yi ya sa Don clemenza ya ce su dawo cikin gidan shi don matarsa Martina clemenza ta kula da Fatima. AbdulHaleem bai mu sa ba don ya yarda da amincin su duk da kasancewarsu maabota littafi yan ɗarikan katolika, ba su yarda su aikata wani abin da zai taɓa amincin da wani ya basu ba. Don clemenza ya yarda da amana ya yarda da abota sannan duk runtsi baya manta alkhairi.
Haɗuwar sa da AbdulHaleem ya gwada shi ya fi a kirga tun daga kan kuɗi har mata, kuma AbdulHaleem ɗin ya tsallake, a nan ya kara yarda da zancen wani ɗan uwanshi Solozo da ya ce masa babu mutanen da su ka kai musulmi Amana saboda su addinin su ta koyar da su hakan, toh duk
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 14