hira a falon Abbie sai wayar ta tayi kara, ganin bakon lamba ne ya sa ta dagawa tana mai cika sallama.
"Waalaikumus salam warahmatullah, Hajiya Fatima kin kusa haɗa digiri shi ya sa ba'a ko ta kanmu ko?" aka ce daga ɗayan ɓangaren
" Allah sarki ban ma gane mai magana ba" tace tana dariya
"Sufyan ne, lallai Fatima kin koshi da yawa" yace daga jin sautin muryarsa ta san ya ji haushi
"Allah sarki, Ammou Sufyan ai ko ka kira a sa'a, ga surikinka ku gaisa, ai nayi aure ne" tace sanin da tayi saudah ta yi aure tana Kuwait, kuma ba waya su ke ba balle ta san abin da ke faruwa tsakanin su. Ta mika ma Khuder wayar su ka gaisa ya kashe wayar.
"Wane Sufyan ne kuma wannan har da Kalen Ammou"
"Allahus Samad Rafeeq, wallahi baffa kawata ne, kwanaki ya so ni amma Allah bai nufa ba" tace saboda ta san babu ɓoye ɓoye tsakanin su.
"Ai na sanshi, aboki na ne tare mukai karatu lokacin ba su dawo Qahɗaanie ba, ba wani abu zamu yi waya" yace yana mikewa. Ita mamaki ya cika ta mai Sufyan ya faɗi da ya ke kumbure-kumbure.
Khuder na fita bai tsaya ko ina ba se gidan Salmah. Bayan sun gaisa ne ya kalli idonta ya ce "yanzu kin san kawarki ba ta da kamun kai kika rufa min, ni ban taɓa zina ba kuma soyayya ba zai sa na samar ma yayana mazinaciyar uwa ba." takaici ya cika Salmah don ji take da ma ita ya zaga akan ya aibata baiwar Allah Fatimah
"Au wai baka da labari, yara uku ta haifa gaban Fatiha fa, ai soyayya ba ruwan shi da aibu in kana son mutum yanda yake za'a so shi, Allah kaɗai ya san yawan kwan da kayi asarar su gara ita ta haife" Ta na kaiwa aya ta wuce ɗaki ta barshi nan tsaye. Muhammad na masa magana amma inaa duhu kawai yake gani haka ya juya a fusace ya bar gidan. A ranar ya yanke shawarar auren Aisha budurwar da ta mace a son sa yayin da su ke jami'a.
***
Ganin anyi sati babu labarin Khuder ne ta tuntuɓe Salmah, nan ta fishe mata abin da ya haɗa su da ce ma Muhammad da yayi "Ai duk wanda ya san Sufyan ya san kura ne a kan mace, akan me zai sa in auri raguwarsa" Nan Bakin ciki ya mamaye zuciyar ta, hawaye ke zuba daga idonta zuciyar ta na quna
"ki gode ma Allah da yanzu ya miki hakan, da sai da aka yi auren ne ya sake ki fa? Ko kuma a ce se bayan an saka rana ne ya miki wannan tijarar, ai ki kwanta ki more Allah ne ya kwace ki daga mugun miji" haka salma ta cigaba da bata baki har ta samu kanta.
***
A kwana a tashi ba wuya su ka kammala karatunsu cikin nasara sannan aka ɗauke ta aiki kasancewar ita ta buɗe ajinsu a maki. Anan ne kuma sabon tashin hankali ya zo mata saboda damuwa da mahaifiyarta tayi akan rashin aurenta da kuma sauran matan mahaifinta, tun bata damuwa har ta kai ga damuwa. Samari da mazan aure ma su zuwa mata su kan zo ne da sunan za su aure ta amma da magana ya dan kwana biyu sai su fara neman jikinta.
Wasu kuma tun a zuwan farko da neman biyan bukata su ke zuwa ciki kuwa har da AbdoulBaar da farfesa Jabir da wasu da duk su ka ɗauki aniyar sai sun bi hanyar da ta tanadar ma mijin aurenta kawai.
***
Hawayen da ya zubo mata ta goge bayan ta gama tuna rayuwar ta.
"Ya Allah don rahamanka da tausayinka, kai ne sarki, buwayi gagara misali wanda in ya so aukuwar abu ya kwance kun fa ya kun. Ya rabbi kai kaɗai nake bautawa kuma gareka kaɗai nake neman Taimako ka gafarta min, ka yafe min ka zaɓa min abokin zama zaɓin ka ba nawa ba. Yaa hayyu ya qayyum bi rahmatika astagithu" Ta maimaita ya fi a kirga kana ta rufe da salatin annabi.
"tab in ba don bawan Allahn nan da ya zo ba da yanzu an min tsirara a bainar jama'a" Ta faɗi a bayyane tana kara hamdala tana mai mike wa. Salmah ta kira a waya ta bata labari
"Amma ke ma Fatima abin duka kike, yanzu har kina da zuciyar kula khuder, ni wallahi ba ni ya mawa ba amma tsakanin mu sallama" Ta ce tana tsaki.
"Salmah auren nan nake so na yi in huta da rigiman su Mamie" tace tana hawaye
"Toh za ki yi ma kanki abin da Allah bai miki ba? Ko kuwa don kina son ki yi aure shike nan kowane kare da doki za ki aura, ki cigaba da hakuri ki yi imani da Allah ki yarda dashi zai baki mijin da kullum sai kin gode ma Allah" Salmah ta faɗi cikin rarrashi.
A haka su ka rabu Fatima ta isa gida zuciyar ta na sanyi saboda kalaman Salmah a gareta.
Ku yi hakuri gobe Insha'Allah zan
turo wani mai yawa. Gaba daya komi ya tsaya min ne chak daz y nai saurin summarizing fb ɗin. Thank you ol
Love
Ummu-Abdoul
Adjetey Tetteh ne zaune a filin jirgin Kasar Habasha in da jirgin su ya tsaya shi kuma yana jiran cikan lokacin da jirgin su zai ɗaga Kasar Masar in da ya samu gurbin karatu a jami'ar Ain Shams University in da zai karanci Shari'a. Karfe huɗu jirgin su ya tashi daga Habasha, ya zauna jigum yana nazari, tunano babban aikin da ke gaban shi da auren da Ubangidansa ke shirin k'ak'aba masa, ga labarin kashe yan uwansa na fashi da ya ji sifeto janar ɗin ya jagoranci yi da wasu ababen su ka dinga masa yawo a kwakwalwa.
" Ina so ka dawo da shiri, in mulkin
Qahɗaanie ya dawo gefenmu tabbas babu yanda za'a yi a ce wani bare ne
zai zama babban Alkalin Kasar nan, shi ya sa na maida maka suna
Abdullah Saifullahi, in ka zama akwai
wa'inda za mu tura gidan yari kawai
mu manta da lamarin su " ya tuno maganganun Aamir a daren da zai baro Zangon Qahɗaanie.
" Kaga hakan na nufin kila wata rana
kayi sarki ko kuma ka zama fiye da
Aamir a mulki" zuciyar sa mai son qawa ta ayyana masa, bai san lokacin da ya saki murmushi ba wanda yayi daidai da isar su Kasar Masar.
***
Ko da Fatima ta isa gida da niyyar ba Abbie labari, hatsaniyar da ta iske a gidan ne ya sa ta jan bakin ta tayi shiru.
"Ai wallahi se dai ka sake ni, aure za'a yi shi nan da sati biyu babu fashi, akan wani dalili za'a bar min 'ya ta yi kwantai, miji ya fito ka ce baka yarda da shi ba, ohhh ruwan idon er gaban goshi kake son rufe wa da ya ta, sanda kannenta da sa'o'inta ke aure uban wa ya hana mata yi, sai an taɓo ku yanzu ku fara tauhidin karya lokacin ta ne bai yi ba" faɗin Ammi Hajiya Amina cikin ɗaga murya, hawaye na zuba mata
zai mare ta Fatima tayi sauri tarewa, cilla ta yayi gefe ya nuna ta da yatsa
"Ke don baki da hankali kaifin halshenki bai tsaya a kaina ba sai ya kai ga Mahalicci, in ma ruwan idon ne ta yi ina ruwanki, kenan akwai tauhidin karya da gaskiya, musulunci dama in ka so yai na karya in kaso kayi na gaskiya ne da kike ba da wannan fatawa.
Mutun kan zama sanadi ne, naji tayi ruwan ido ya zama mata sanadin rashin aure da wuri ko? Amma dai Allah babu mai sa shi babu mai hana shi, ashe zubar da madara da kika yi kika ce min qaddara ce ashe tauhidin karya ne ko yanzu aka baki dama yi zaki yi.
Na gode Allah Fatima tayi ruwan ido amma kuma ba'a kama ta da badala ba, kuma ina da yakini kamun kan da tayi Zai sa Allah ya bata mijin da ya fi na dubu, aure ne nace ba zan ba da ya ta ga wanda ban sani ba" ya ce yana shirin barin wajen don hawayen da ya zubo masa, faɗi yake a ransa "ashe ba Yan matan da su ka daɗe ba aure kaɗai ke jin jiki da damuwa har iyayensu" don tun da ta fara babu abin da ɓata masa rai sama da wannan. Karaf se ya ji tace
"in dai zancen Yan Hilaalu ba gaskiya bane na zaman ka shege toh ka aurar da ita ga masoyinta, amma in Kaki Kaga ka tabbatar da zancen su don shege ne kawai bai son raya sunna." tace tana shigewa ɗaki da rufe kofa.
Duk wani mai hankali yaro da babba ya ji zancen kamar dirar aradu. Hajiya sadiya da kan biyeta tafi kowa shiga damuwa don faɗi take
" Haba Amina wannan diban albarka har ina? Wai baki san tausasa halshe ga makiyi ma aikin lada ne balle kuma ga wanda yake wajibi a gare ki, Abbie don Allah kayi musu yanda su ke so, ni ban son fitina" ko kallon su bi ba ya juya, babu wanda yayi yunkurin bisa sai fatima da ke kuka kamar ranta zai fita. Hawayen da ta gani a idonsa ta fara sharewa, cewa take
Add Vote
"Abbie ka aura min duk wanda ka so, zan zauna zan yi biyayya ba zan jure ganinka cikin damuwa ba" shafa mata kai yayi ya Mike ya faɗa makewayi, nan ma alwala yayi ya tada sallah duk da kasancewar maraice ne lis ba'a nafila amma abin da yake bukata kawai shine ya samu ganawa da Mahaliccinsa cikin soyayyar da babu kamarta (sujjada). Ya fi minti talatin a sujjada yana kuka yana mai fadawa Allah damuwar sa, Fatima nana zaune tausayin mahaifinta na kara mamaye zuciyarta, tana mai kara gode Allah da mahaifin da ya azurta ta da shi.
"Abbie ka yafe min, na bar maka. Zaɓi ka zaɓa min duk wanda ka so ka aurar da ni ka huta da gori, kayi min rai" Ta ce sanda ya kammala addu'a ya shafa. Murmushi yayi ya ce
"Allah ne mai azurtawa walau arziki na kuɗi, ya'ya ko abokin zama. Duk wanda aka ma gorin arziki sai Allah ya azurta shi da wanda yafi na mai Gorin albarka. Za ki yi aure Fatima kuma kowa sai ya so ace shi ya samu mijin da zaki samu. Zubaida kuma ranar Juma'a zan ɗaura mata aure kuma a ranar za ta tare a gidanta " ya ce yana murmushi, ganin hawayen ta yaki tsayawa ne ya fara tsokanar ta har su ka dara, nan su ka fito dakinsa suna dariya abin da ya ba mutanen gida mamaki.
" Zubaida " ya kira ta yana mai ɗaga murya, jiki na rawa ta fito ita ma idanunta sun bayyana alamun ta sha kuka ba ko kaɗan ba.
"shi Abdullahin yana ina kika ce?" Ya tambaye ta murya a sanyaye kamar ba shi ya tashi dukanta ba
"Abbie ya je karatu ne Kasar Masar toh shine ake so in je chan dan na cigaba da karatu nima" Ta maimaita cikin tsoro.
"in kun yi waya toh ki ce ranar Jumma'a za'a ɗaura aurenku a fada, gobe zan je in sami mai martaba" ya ce yana ficewa daga gidan zuwa masallaci.
"Aaa lallai mun yarda Fatima er Abbie ce, wato kun Shige ɗaka kun kimtsa tsakanin ku, Allah sa hakan ne Alkhairi" cewar Mamie haj sadiya. Nan duk suka sa dariya haɗe da fara shirya ma bikin.
Ko da ya dawo bayan sallar isha'i ba abin da ya nuna na ɓacin rai, tare da matan su duka ya ci abinci daga nan su kayi hirar duniya.
***
A fada kuwa bayan sarki ya shiga ɗaki ya nemi ganawa da iyalinsa a karo na biyu duk a dalilin Wasikar Ansari. Bayan sun zauna da matansa da yarana maza da ya mallaka ne ya buɗe taron da addu'a sannan yace
" Nayi tunanin fitowa in bayyana AbdulHaleem a matsayin yarima mai jiran gado. Dalili na kuwa shine tsoro ba namu bane, kuma shi saifullahi ya kamata ya san matsayin sa ba zai ci gaba da zama barazana a garemu ba. Kuma na baku sati ku samo matan aure" ya yi shiru yana kallon su duka da kuma yanda su ke tafiyar da fuskokin su a dalilin waswasin da su ke a zukatansu.
"Allah qara girma Zaki, ka bani izini in kawar maka da shi daga doron kasa, ba zai cigaba da zama barazana ga masarauta ba" AbdulHaleem ya faɗi yana mai tsanar Ansari
"Hakan bashi a cikin tsarin mulki, in kace da an maka abu ka yi kisa wata rana zaka nemi wanda za ka so ka kashe baka samu ba, wanda ya kashe barci kuma ai ya gama barci" sarki ya faɗi yana dariya
"Kaga kenan bai cika zama sarki ba, ɗazu yake ce dani in da hali a nema masa auren yarinyar nan da ya taimaka amma bai sani ba ko za ka yarda ya aureta don kamar Fulani ce, Kaga kenan ba jinin masarauta bace" Ummu Maryam ta faɗi. Bakin ciki ya taso ma AbdulHaleem, akan me zata sa shi yin abin da bai iyawa, auren baiwa, duk karatunta ya kamata Ace jinin sarauta na yawo a jikinta ko yaya ne. Hawayen da ya ji ne yasa yayi saurin sauke kansa qasa hakan ya sa mai martaba tunanin kunya ce tasa shi hakan.
"MaashaAllahu Barakallah, zan aika a bincika min asalin ta gobe, kuma za'a yi nan ba da jimawa ba. .
AbdulHaseeb da Ummu Hafsa na zaune takaicin duniya ya cika su, yanzu duk abin su zai tashi a banza kenan.
" Allah taimaki zaki, abu na gaba don Allah a AbdulHaseeb sarautan, Allah barshi kar a faɗi, ka gina min katon gida can waje da fada don zama da matata" AbdulHaleem ya faɗi bayan tunanin irin horon da zai mata don kuwa itace sanadin rashin samun sarautar.
Sarki dariya kawai yayi ya sallame su sai Ummu Maryam da ke da kwana ta tsaya. Suna fita AbdulHaseeb ya mata nuni da su kebe. Anan su ka shawarta zuwa wajen Ansari a wannan daren.
****
Satar hanya su ka yi cikin daren nan suka samu Ansari, sun feshe masa duk abin da ya faru, nan shi kuma ya shiga nazari.
"yauwa, abu ya zo cikin sauki ma. Kin gane Abdoulgaffar ai kanin mijinki, toh akwai amininsa in za ki gane shi Yahuza Bello kuma matarsa abokiyar tagwaitar matar Abdoulgaffar ɗin, sarki na son mutumin nan saboda dan uwansa, yana da ɗiya Fatima abin da za'a yi ka ce da mai martaba Fatima kake so, ina mai tabbatar maka babu yanda za'a ayi sarki ya hana ya ba jinin Yahuza zama matar sarki " dariya duk su ka yi nan su Abdoul haseeb su ka koma.
Asubahin fari Ummu Hafsa ta sami sarki ta faɗa masa wacce Abdoul haseeb ke so, sai da yayi Jim sannan ya ce
"tun yaushe su ka haɗu, bana son aikin gaggawa fa" ya ce yana kallonta, take ya karanci firgicin da ta shiga amma ya basar yana jiran amsar da zata bashi.
"eh! Toh gaskiya bai riga ya mata magana ba, amma dai ya san ba za ta ki shi ba" tace ta na yake.
"Toh zan bincika in ji in har ba ta da wani, don ba zan yi nema akan nema ba. Allah ya tabbatar da Alkhairi" ya ce yana mai kauda kai alamun ya gama da ita don shi jikin shi ya gagara yarda da ita duk da bai son ya yanke hukunci akan zato. Ta fita tana roqon Allah ya sa yanda baffanta ya shaida mata cewa babu wani a tare da ita ya tabbata a hakan. Nan dai ta isa ɗaki ta iske mai kula da kayan sawarta ta fito mata da shi, masu hidimar wankanta suna haɗa mata ruwan wanka, nan ta shiga ta yi wanka ta fito, aka shafe ta da mai kana ta sa kaya. Sannan ta kwanta don komawa barci kamar yadda ta saba.
***
Sarki na isa fada ya fara sa a binciko masa wacece AbdulHaleem ya taimakawa sannan a binciko shin tana da wani in babu ya bada izini a nemi mahaifinta a ce ana neman iri ya basu lokacin da za su zo bikin tambaya.
Dan sako wanda ya kasance babban ɗan yayan mai martaba. Shi kuma yana fita daga fada AbdulBaar ya nema ya tambaye shi wacece yarinyar shi kuma sanin da yayi Alhaji Muhammad yafi kowa tsanar talaka ko wanda yake ba jinin sarauta ba ya sa shi faɗa masa wacece a tunaninsa rashin mutunci zai karta mata don shi yaya yake a wajen mahaifiyarsu. Duk da yaya yake a wajensu in aka bi gefen mahaifinsu ne.
Jin sunan wanda aka kira ya sa shi dariya, tare duk su ka taso da Alhaji Yahuza a fada sai dai tun bayan rasuwan Abdoulgaffar zumuncinsu yayi nisa don shi bai faye harka da wanda ba jinin sarauta ba duk kuɗin sa, kuma shi ya sa ma AbdulHaleem wannan ɗabi'a don rayuwar da su kayi da shi a kasar America.
Bai qara ce da AbdulBaar komai ba ya ja mota ya fice, hakan ya kara faranta ran sa don ya san daga ita har ubanta a gidan yari za su kwana in kuwa hakan ya faru ko fyade ne sai ya mata a cikin sel dinnan abu ne da ya ba gandirobobin kuɗi ya samu shiga. Da wannan farin cikin ya shiga cikin gidansu ko ya samu ya kwanta don ya sha alwashin raya daren yana horar da Fatima ta hanyar da har abada ba zata taɓa mantawa ba.
***
Ko da Alhaji Muhammadu ya isa gidan su Fatima ya iske Alhaji Yahuza ya fito zai shiga motarsa da aka fitar wajen gate.
"wa nake gani ne haka amma dai ɗan nan namu ɓatan hanya yayi ko" yace da shi bayan ya ɗan rungume shi.
"Kai Ammou, ka san dai bana zama ne shi ya sa" yace yana dariya, duk izzarsa yana girmama Alhaji Yahuza duk da ya ɗan girme su kaɗan amma kasancewa Abdoulgaffar kanen mahaifinsa ne ya sa yake kiran su da Ammou
"Ko da yake saraki ake bi amma ka san dai shi ke bin iyayensa, ai ina shirin isa fada ne akwai auren da nake so ayi ranar Jumma'a ne, toh abin ya zo ba notice ne shi yasa" ya ce yayin da suka karasa cikin falon tarbon bakin sa. Kayan shayi aka kawo masa bayan ya yi waya cikin gida mahaifiyar fatima ta shigo da su.
"Hajiya Hafsa kuna lafiya, ya muka kara ji da hakuri" ya faɗi yana share kwallan da ya zo masa, yana daga cikin abin da ya sa baya neman Alhaji Yahuza don duk ya gansa sai mutuwar amininsa kuma baffansa ya dawo masa sabo, haka duk suka haɗu sai ya sake musu ta'aziyya shekaru talatin da huɗu kenan amma kamar minti talatin da huɗu.
"Sai hakuri Alhaji, muna musu kyakkyawar fata, in da suke yafi nan da su ka bari. Allah ya mu dace" tace tana mai jin zugi ita ma.
"Mai martaba ya aiko ni, AbdulHaleem ya ga Fatima yana so, shi ne aka ce in zo ka ba mu lokacin bikin tambaya"
Add Vote
Sujjadan godiya kawai Alhaji Yahuza ya yi don bai taɓa ganin ijaba cikin gaggawa kamar wannan ba. Yana dagowa ya rungume Alhaji Muhammadu sannan ya ce
"Fatima ta yi hakuri, Fatima ta ga jarabawa iri-iri, na san Allah ba ya barci kuma maji roko ne, Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!"
"Ai na san ba wanda zai kai mai martaba murna, ba shi kaɗai ba duk wani ahli na gidan nan zai farin ciki don kuwa kamar an dawo da Ammou Abdoulgaffar ne" ya ce shima cike da farin ciki. Ganin Alhaji Yahuza bai kawo zancen abin da ya faru ba ya sa shi ma bai dago maganar ba. Anan su ka tsaida sati uku masu zuwa a matsayin ranar bikin tambaya.
***
Bayan tafiyar Alhaji Muhammadu, tafiya wajen aiki alhaji Yahuza yayi ba tare da ya koma cikin gida ba balle ya faɗa musu abin da ya faru. Nan ya kula a rana ba zai faɗi ba sai ana gobe bikin, duk wani shirye-shirye zai bada kwangilar yi ne don kuwa a Hilaalu Sambo za'a yi ko don bakin cikin masu bakin ciki ya kashe su.
Shi kuma Alhaji Muhammadu ko da ya isa fada nan ya faɗa ma Mai martaba wanene Mahaifin Fatima da kuma yanda su ka kwashe. Take ya ciko Nutud dubu ɗari uku da zinari dirhami arba'in ya ce ga sadakin AbdulHaleem nan ya bada gudunmuwa. Nan yan majalisa su ka masa godiya da jinjina akan kokarin da yayi.
Sarki dai ya shiga ruɗani don baya son abin da zai kawo masa matsala a cikin gida, da Ace Muhammad bai furta ma su AbdulHaleem ba da babu abin da zai hana ya juya shi ga AbdulHaseeb don ya san ya fi nagarta sannan AbdulHaleem ya fi hakuri da juriya yayin da ya rasa abu.
Haka ya zauna shiru yana neman taimakon mai duka, ba zai ɓoye musu ba amma ba zai faɗi ma su wa za'a ba ma wa ba.
"ina so zancen kada ya fita bangon majalisan nan, in Allah ya kaimu sati uku ma su zuwa Daula za ta san wanene mijin Fatima. Allah ya nuna mana, Muhammadu ka san ana babban wa uba, toh ka jagoranci komai na neman auren nan. Allah ya maka albarka" ya ce yana mai rufe zama.
***
Duk yanda Alhaji Yahuza ya so ya ɓoye murnarsa ya gagara don haka ya dinga sadaka da kyaututtuka yana gode ma Mai duka.
Ko a gida sai da aka fahimci farin cikin sa, duk yanda aka so a ji dalilin ya ki ya faɗi sai cewa yake
"Addu'a nayi jiya kuma Allah ya amsa min ita nagani a yau" nan dai su ka dinga masa tsiya ba tare da sun hasaso komai ba.
Sarki kuwa sai da dare ya sake ganawa da iyalinsa. Tare su ka ci abincin dare su duka sannan su ka taba hira.
"wai kun san wani abin mamaki, Fatima Yahuza Bello ita ce yarinyar da AbdulHaleem ya ke so, haka itace yarinyar da kanensa AbdulHaseeb ya gani yace yana so. Toh abin da ban sani ba shine yaushe kuka fara ɓoye ma junanku sirri da har aka samu wannan akasin, ko kuma duk ku biyun wani abin kuke nema da kuka ɗauko min ta hanyar da yake rauni a gare ni" ya ce yana karantar dukkansu, so yake ya fahimci mai gaskiya a tare da su.
" Ni dai na san sunanta Fatima, AbdulBaar ne ma ya nuna min ya Santa, kuma ni in bacin Qalbi da na ce ma ina sonta har ta faɗi maka ba wanda ya san ina sonta, amma in shi yana sonta da gaske ne na hakura" AbdulHaleem ya faɗi yana ciccijewa don kuwa shi dama ba kalarsa bace duk da ya yini tana masa gizo amma zai yi ne don farin cikin ummansa
"Ni dai ina sonta kuma ba zan taɓa hakura da ita ba, haka kawai don na ce ina sonta saboda wani buri da ake son a cika a ce shima yana sonta" AbdulHaseeb ya faɗi har da hawayensa don burinsa ya zama sarki kuma duk hanyar da ya dauko sai ta rushe
"Ni kuwa mamaki kuke bani, tun kuna shekara goma a duniya mu ka tafi Kasar Amerika tare, nice uwar ku nice makwafin ubanku, na rike ku tamkar AbdulHaleem da AbdulHaseeb ɗin da na haifa AbdulHaseeb ya rasu. Na baku tarbiyya ba tarbiyyan son mulki ba, ban dawo ga miji na ba sai da kuka kammala jami'a kuka mallaki hankula.
Add Vote
Dawowarku bayan kun yi digirgir na fahimci AbdulHaseeb ya fi hankali da daraja dan adam, na fahimci cewa kun watsar da kusan rabin abin da na ɗaura ku akai ban furta muku ba ban damu ba amma yau kun tabbatar min da cewa na faɗi a matsayin uwa, tun da zaku kalli idon Zaki ku yi rashin kunya.
In ma wani abin kuke sha toh ku dawo da hankalin ku waje ɗaya, Fatima ba rabon ko guda bace a cikin ku. Don mace ba za ta shiga tsakanin ku, ba zata rusa ginin da na sadaukar da son mijina wajen gina shi ba" Ummu Maryam tace hankali a tashe. Don ta na iya hango kiyayyar da ke kwance a idanunsu.
"wai duk za ku barni in ji sanyi ko kuwa za ku karasa ni da tsufa na" mai martaba yace yana mai ɗaga murya. Nan duk suka yi shiru suna sauraronshi.
"Fatima dai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 14