su ke yi don tun da ta gano soyayyar da ke tsakanin Fatima da mahaifinta ta daura mata ninkin sa. Hakan ya sa Alhaji Bello ke girmama ta haka za lika Hafsa.
***
Amina na jin labarin kuɗin da Alhaji Bello ya tara nan ta kasa ta tsare har sai da ta shigo gidan, lokacin ne zaman lafiya ya fara karanci a tsakanin su don Amina bata kyashin karta ma kowa rashin mutunci a gidan sannan ta yi amfani da kissa ta rufe ba tare da Alhaji ya san anyi ba.
Fatima na da shekaru goma sha shida ta kammala karatunta na kwaleji, cikin nasara da hazaka nan Hajiya sadiya ta bada shawaran tura ta jami'ar Ahmadu Bello don yin karatun digiri amma Sam Alh Bello ya ki.
Fatima ta taso shiru-shiru mara hayaniya, ba ta da abin da ta sa a gaba sama da littafanta na boko da islamiyya. Ta taso ba ta da kawa ko ɗaya sai dai a haɗu a aji a rabu cikin aminci. Mahaifinta ne kawai ya san sirrin ta, shi kaɗai ta ke isa ga don neman shawara sannan shi kadai ke iya fassara maganar ta ko bata furta ba.
"Ni a zan tura ya ta gari garara har wata kasa ba, ki sake shawara ko zan iya dauka wannan dai kiyi hakuri" Ya ce da ita lokacin da ta masa maganar.
"Aure dai za'a mata, wani irin jami'a ko yawon karuwanci" hajiya Amina ta faɗi son ita babu wacce ta tsana sama da fatima don ganin yan matan ta uku ba wani kulawa suke daga mahaifinsu ba.
"Ke dai baki da magana sai na namiji, kada ki maida min ya'ya jarababbu don Allah. Fatima ko za tayi aure sai ta fara karatu. Zan nema mata a Safiyyah jibril, ta fara in miji ya zo in aurar da ita" da haka ya rufe taron da yake da matansa akan Fatima.
Add Vote
Afuwan Afuwan pls, da kyar na iya yin wannan, ku min addu'a. Manage this pls.
Cikin ikon Allah ya sama mata gurbin karatu a jami'ar kimiyya da fasaha wato Safiyyah jibril University of science and technology a sashin kere-keren magudanar ruwa ( water resources engineering adepartment). Sannan ya siya mata mota kirar civic don zirga-zirgan ta na makaranta. Siyan motar da yayi ya kara tayar da hankalin Hajiya Amina don ko su matansa da a tunanin ta yake karuwa da su bai siya musu ba. Nan kishin Fatima da tsanar ta ya cika mata kirji har take ganin ai kawai ta kawar da ita shi ne mafita.
Ranar da Fatima za ta fara zuwa makaranta, ta shirya cike da ɗoki kamar kowane sabon ɗalibi. Bayan ta bi iyayenta mata ta yi musu sallama ne ta karasa wajen Abbie.
" Fatimatu-zahra an shirya kenan, ubangiji Allah ya sa kin fara kenan a sa'a, ya miki albarka. Ina so ki sani cewa jami'a waje ne na koyon darasi. Ko in ce duniya ce mai zaman kanta, wasu kan shiga a tambade su fita a shirye, haka wasu kan shiga a shirye su tambade kafin su gama wasu su kan shiga a shirye su fita a hakan wasu a tambade su fita a hakan. Saboda haka ina so ki kasance mai tunawa da inda kika fito a duk wani mataki na rayuwa. Ki tuna ke ɗin musulma ce wane dokoki ne Allah ya sharɗanta miki.
Ban rage ki da komai ba, duk abin da kike bukata ki same ni zan miki, sannan ki sani kina da babban Aboki kuma amini wanda ba kunya ko tsoro tsakanin ku, sannan wanda duk duniya babu wanda zai kai shi ɓoye miki sirri don kuwa ba zai so a ce ga yar sa tayi kaza ba " ya faɗi yana nuna kansa. Hawayen da ta gani a idon ta ya sa shi yin dariya da faɗin
" oooo Yar jami'a da kuka? Ba ki san kin zama yan mata ba, maza share hawayenki Allah ya miki albarka" ya karasa yana mika mata hankici. A karshe ma tashi yayi don ya kaita makarantar suna tafe yana kara mata kwarin gwuiwa tare da nuna mata ai zata iya kwas din da aka bata kuma za ta yi nasara. Hakan ya sa ta isa makaranta da karfinta, ta shiga Darussan da aka ce tana da su a ranar kuma ta fahimce su duka.
A ajin ne ta haɗu da wata wacce ta zauna kusa da ita mai suna Salma, a tsakanin darussan ne su ka gaisa har suka gabatar da junansu.
Salma yar asalin Qahɗaanie ce don balarabiya ce da ma ba su watsar da al'adan su ba. Amma tana jin hausa kamar kowane ɗan Qahɗaanie.
Bayan an tashi makaranta ne yayan salma ya zo ya ɗauke ta, ita kuma Abbie ya zo ya ɗauke ta. Tun a cikin mota ta ke bashi labarin darussan da aka musu da maluman su har da sabuwar kawarta salma.
"Aahh MaashaAllah, kada ki yi saurin sake mata jiki sai kin tabbatar da cewa tarbiyyan ku ya zo ɗaya, kin san masu iya magana na cewa gwada min abokinka ya ishe ni
sanin ko kai w aye. Banda rashin karatu banda rashin tarbiyya in dai ba shi ba kina iya kawncen aji da ita in kuma hali ya zo ɗaya sai ku zama kawayen har abada"
"Abbie har wani kawar aji ne akwai?" Ta tambaya cikin dariya
"Sosai ma kuwa, kawar da a aji zaku gaisa a ɗan yi hiran duniya amma in za'a sa mata wuka bata san komai game da ke ba" ya faɗi shima yana dariya. A haka su ka isa gida, ta gaida iyayen ta mata sannan ta karasa ɗakin ta don chanza kaya.
***
A wata ɗaya da yan kwanaki da Fatima ta yi a jami'a ta saba da karatun sannan sun shaqu da kawarta Salma Babikir saboda yarda da tayi da tarbiyyan ta. Sai ya zama in Fatima ta fito gida take biyawa Salma su wuce a motar ta. A ɗan wannan lokacin duk yan gidan su fatima sun san Salma haka yan gidan su salma sun san Fatima.
A nan cikin ajin nasu kuma akwai saudah, ita ma balarabiya ce amma b su daɗe da tarewa a Qahɗaanie ba. Ta kan zauna a cikinsu amma ba kasafai ba, amma in ba'a ganta ba akan tambaye su ina Saudah.
Tun da kanin mahaifin saudah mai suna Sufyan ya kyalla ido ya ga Fatima ya ce da wa Allah ya haɗa shi. Nan ya shiga mata aike ta waya da wasika, katukan gaisuwa na bege (greeting card) da wasu ababen.
Kafin a ankara ta faɗa tarkon soyayyar sa, saboda kirkin da ya ke mata da kulawarsa gareta. Bata ɓoye ma Abbie ba shi kuma yana bata shawara don baya so yayi gaggawa ya fi so ya ga gudun ruwansu.
***
"Habibty kin san irin son da na ke miki kuwa, don Allah ki so ni kuma kada ki yarda wani ya shiga tsakanin mu" su ne kalaman sufyan kullum har Fatima ta haddace. Hakan ya sa ta tabbatar da lallai ta sa mu miji, kuma zata ji daɗin aurenta don gwani ne wajen tsara kalamai na soyayya da kulawa.
Shekaransu ɗaya tare kenan kasancewa tana aji biyu, soyayyar sufyan bai taɓa hana mata karatu ba don ita ke jagoranci a ajin nasu.
Zaune su ke ita da Salma suna karatu, wayarta tayi kara nan ta ɗaga cike da shauqi ta ce
"Habibie Sufyan, na yi kewan ka wallahi ba ko kaɗan ba, kana ina" Ta ce cikin shagwaba
"Gani na shigo makarantarku, ki fito mu yi hira daga nan mu karasa lambun fada" yace mata yana kwantar da murya
"Gani nan tafe, Insha'Allah" tace tana sauke waya haɗe da ajiye littafan da take karantawa a gefe. Fauda ta dauko ta shafa ta kara gyara fuskanta nan ta fito fes abin ta.
"Kin san Allah babu inda zaki, in yana so ku yi hira ya je gida mana" salma ta ce a fusace
"Toh wakikiyar Abbie ai ko shi ya san da shi" Ta ce tana murguda baki, bata ankara ba Salma ta ɗauke takalmanta da wayarta ta zauna akai
"ba zan san kina cikin majununai ba sai kin tafi a haka, kin bari soyayya na neman rufe miki ido wallahi ba aurenki zai yi ba. Dalilin me ya baki na rashin zuwan sa gida? Kullum shi kenan sai dai ku haɗu a wani waje ba dai ya je gidanku ba kuma kina laqe da shi" Ta ce mata kai tsaye duk da sanin da tayi ranta zai ɓace.
"Alo tace ka yi hakuri kazo gida anjima karfe uku za mu kammala" salma ta faɗi bayan ta ansa wayar da ya kira.
Duk inda ran Fatima ya kai ya ɓaci don gani take kamar bakin ciki Salma take mata, hakan ya sa ta quduri cema sufyan ya turo ayi aurensu ta huta da masu faɗi mata ba aurenta zai yi ba. A haka su ka tashi kowannensu ya isa gida a gajiye saboda karatun da su ka sha.
Na Kanji ana cewa makaranta ke son
marubuta, amma gare ni ba haka bane don ni ina son makaranta
littafai na don jin su nake kamar
wasu jinina. Allah ya bar zumunci har
gaban abada. Keep on voting, keep on commenting, and I will keep you updated
Tun da ta isa gida ta ke tsumayen kiran Sufyan amma shiru take ji, haka ta zauna sukuku kamar wacce kwai ya fashe mawa a ciki. Tsaki take tana zagin salma a ranta don ta san duk ita ta ja mata fushi masoyi.
Ganin anyi sallan isha'i bai kira ba ya sa ta danna masa kira, bugu biyu ya ɗaga
"idan na ce miki Salmah ba kawar arziki ba ce ki ce na cika kishi, gashi nan ta zuga ki yau kin ki gani na" ya ce bayan ya ɗaga kiran. Take zuciyar Fatima ta kara cika da jin haushin Salmah
"Kawai a zo a sa mana rana mu wuce wajen don Allah,ka ga masu bakin ciki sai cikin su ya kara baki" Ta ce cikin shagwaɓe murya
"Ayi aure mutum bai san kalan matar da ai aura ba, ɗan zancen kwantar da zuciya da mace za ta yi mutum ya san aurensa zai cika da romansiyya kawarki ta hana, yanzu haɗuwar ma tana neman ta hana balle mu ji ɗumin juna. In kina so ayi auren nan ki bani dama sau ɗaya Kawai habibty" ya faɗi yana mai sumbatar iska zuwa ga kunnenta.
"toh" Ta ce a sanyaye zuciyar ta na karyata bakinta
" kuma ki sani wannan sirri ne tsakanin mata da miji, saura ki je ki faɗi ma kunne na uku" ya faɗi da muryar umurni.
"wai har yanzu baka hakura bane, wallahi kwace wayar tayi a hannu na ban ma sani ba, sannan ta ɗauke takalma na ka san ba zan iya tafiya haka ba, kai ma ba za ka so ba aiko" tace masa cikin muryar kuka don duk in da hankalin ta yake ya tashi saboda fushi da ya nuna mata yana yi da ita.
"ai ba abin da so baya sawa se ki taho a hakan, nan zan tabbatar da son da kike ikirarin kina min" ya ce yana mai katse wayar. Nan ta zauna tana kallon wayar a hannunta, zuciyar ta na faɗi ma ta " ai da yana son ki da ya zo gidan yanda kika ce " amma mayaudariyar zuciyar ta cewa take " ya za ki ce haka, bayan kin san yana
makaranta ta wulakanta shi" haka ta yi ta sakawa da warwarewa har barci ɓarawo ya sace ta.
***
Washe gari da matsanancin ciwon kai ta tashi da shi, sannan ga karuwan son Sufyan da ya kara mamaye mata Zuci, haka dai ta cigaba da abu kamar mai cuta.
"Fatima me ke damunki ne tun jiya na lura kina wani shiru shiru" mahaifiyarta tace lokacin da ta shiga gaida ta
" Ummie kaina ke ciwo, ki mun addu'a" Ta ce tana mai hawaye
"ciwon kai sai ki kama kuka Fatima se kace wata karamar yarinya, sa'o'inki nawa ke dakunan mazajensu haka za su zauna su na ma ciwon kai kuka, kar ki nemi magani ki sha ki tsaya kina wauta" Ta ce tana juyawa tana ma kanwar fatima surayya tana mata bayanin wani kaya da ta siyo mata don an sa ranar aurenta daga ta kammala shekarar farko na jami'a inda take karanta Technical education.
Sumsum Fatima ta fita ta isa ga hajiya Sadiya, nan ma bayan gaisuwa tambayar ta tayi me ke damun ta, amsa ɗaya ta bayar,
"Kar ki ce don an sa ranar surayya za ki tada hankali, kowa da lokacin sa, shi wannan mai kiran ki a waya ba zai fito bane? Ni ban san mai sa Abbie ke yin shiru bane, nan ya matsa ma Anisa kwatakwata guda nawa ta ke, daga ya kamata tana waya yace ya zo. Kin ga tun wuri kiyi ma kanki karatun ta natsu, in son ki dagaske yaron yake ya fito a wuce wurin in kuma ba dagaske yake ba ya baki wuri masu son ki su fito" Ta ce cikin faɗa, haka ta cigaba da faɗan ta kai tsaye wanda Fatima a zuciyar ta faɗi take " don an takura yar ki sai ki
takura ni"
Add Vote
Haka ta baro ɗakin ranta a ɓace, san inda ta yi kila zuciyar ta ya buga matukar ta kai kanta ɗakin hajiya Amina ya sa ta wuce wajen Abbie, nan ta take sa'a yana barci ta juya ta yi shirin makaranta.
A makaranta ba ta ko bi takan Salmah ba, waje daya su ka zauna amma ba wanda ya ce da wani kanzil. Bayan darasin da su kayi karfe 12 zuwa 2 ne Saudah ta Kalle su tace
" Ni kuwa Ammie Fatima kun rabu da ammou nane? Naji ana za'a je tambayar sa Anjima, momma take ce min ba kawata na ce yana so ba nace eh, sai ta yi shiru" ba Fatima ba hatta Salmah sai da ta ji karayar zuciya. Nan Fatima ta tattaro duk wani Karfin hali ta ce
"Ya faɗa min, dama abokantaka kawai mu ke yi" Ta faɗi tana dariya
"Haba wallahi na yi mamaki da yace ma su momma haka, wai shi fa dama can ba budurwar sa bane kawarsa ce, ai ko gidanku bai taɓa zuwa ba, ni ko na ce ammou aji tsoron Allah, ya biyo ni zai kwade, amma Ammie kin yi babban wauta, saboda aboki ki kori wa'inda ke son ki da aure" Ta ce tana karkada kai
"Sai kiyi, Allah ya sanya Alkhairi ya ba su zama lafiya" Fatima ta ce tana murmushi. Salma bata ce kala ba sai wayarta da tayi ta latsawa, sunyi shiru duka kafin su ga ta kara wayar a kunne
"Ubangiji Allah ya azurta ka da ya mace a farko, ya sa a mata abin da kayi ma yar wasu nan zaka ji in da Daɗi" salma tace tana mai katse wayar.
"Haba Salmah Ido da kunya fa, ko mai zai yi ai yaci albarkaci na, ita wacce kika shigar mawa ma cewa tayi su abokai ne, kin ga kenan babu abin da ya'yansa za su gani sai alkhairi" Ta ce tana mai mikewa da barin wajen. Sai a lokacin Fatima ta samu damar yin kuka, tana mai gode ma Allah da bata kai ga amincewa ba, niyyarta yau in ta tashi ta neme shi duk abin abin da zai faru ya faru su yi aurensu su huta.
"Share hawayenki, ba karamin asara yayi ba, ke kuma Allah na sonki shi ya sa har kika ga hakan ya faru, miji nagari na nan zuwa miki. Ki cigaba da addu'a da tsare mutuncinki kamar yanda Abbie ke faɗa mana" Ta ce tana share mata hawaye tana mai matse nata hawayen. Nan Fatima ta ɓata labarin yanda su kayi da kuma niyyarta a da.
"Alhamdulillah, Kinga yana cikin rahman Allah dabaran dauke miki waya da takalma, don na tabbatar da kun haɗu jiya da kin zama fanko. Ai duk namijin da ya ce zai aure ka bayan ya sanka ɗiya mace to dama ba aurenka zai yi ba" haka ta cigaba da ba ta baki har su ka isa gida. Tare su ka isa har ga Abbie, Salmah ta ba shi labarin abin da saudah ta ce musu.
" Kun ga kenan ya zama maku darasi ku duka, namijin da ke son ku gidan Mahaifin ku zai biyo ku amma duk wani mai haɗa wajen haɗuwa toh ba aurenku zai yi ba. Sannan duk wani disappointment alkhairi ne, abin da ake bukatar mumini da shi a wannan lokacin shine hakuri.
Akwai wani sarki yana da amintaccen
bawa, duk abin da ya faru sai bawan nan ya ce "alkhairi ne daga rahman Allah" hakan da ya ke faɗi sai yayi ta
ba sarki haushi don gani yake kawai
rainin wayau ne. Wata rana sarki sai ya rasa yatsa ɗaya, sai bawan nan
yace "Alkhairi ne daga rahaman Allah" Sai sarki ya ji haushi ya sa aka
kulle shi a gidan yari. Bayan shekaru
sarki ya ma manta da wannan bawa
na sa, sai wata rana yana rangadi se
yayi sha'awar yin farauta, a cikin daji ya ci karo da masu cin mutane. Nan
suka ɗaure shi suka hura wutan da za su gasa shi sannan su ka kamo shi don su yanka. Nan su ka lura da
rashin yatsan nan na shi su ka sake shi a matsayin shi ba cikakken
mutum bane.
Add Vote
Yana dawowa sai ya tuna da
amintaccen bawansa da kalamansa
na cewa rashin yatsan sa alkhairi ne
daga Rahman Allah, sai ya sa aka
kawo masa shi, nan ya bashi labari ya kuma kara ba shi hakuri. Bawan nan ya sake gurfanawa ya ce "Kulle
ni ai alkhairi ne daga rahman Allah"
Sai sarki ya ce masa "Ta ya zaka kira
zaman gidan yari alkhairi bayan ba akan laifin ka aka kulle ka ba"
Sai bawa ya ce "Da ace baka kulle ni
ba, babu yanda za'a yi in barka ka je
farauta kai kaɗai, Kaga kenan da tare
zasu kama mu, kai za'a sake ka ni
kuma da nake cikakken mutum a
wajensu tsaf zasu cinye ni.
Kun ga labarin nan kaɗai ya ishe ku gode ma Allah a duk wani abin da ka so kuma Allah bai ba ku ba.
Kin san kanwar sarki Safiyyah, ita ma
lokacin nan akwai wani da ta so
kamar ranta zai fita, bata da abokan
shawara daga ni sai marigayi
Abdoulgaffar, shi ya sa kika ga har
gobe zumuncinmu da ita bai yanke
ba.
Taso bawan Allah ɗin nan amma
kwatsam yace shi Sam ba zai aureta
ba wayonta yayi yawa kuma ta fito
gidan sarauta. Tayi kuka tayi karamar
hauka in faɗa muku amma ba'a yi
wata ba take ce min "ashe gara da ban aure wane ba, Allah ya tanadar min wannan ne" , saboda shi wanda ya ki ta ɗin nan zina abin ado ne a
wajen sa, ya nemi matan aure,
zaurawa har ma da yan mata. Ga
caca sannan matarsa wuya take ji.
Anan na kara gaskata kissar sama"
Shiru yayi yana kallon su yanda jikin su yayi sanyi, ruwa ya dauko ya ba su daga firij ɗinsa sannan ya cigaba da faɗin
"Saboda haka, ku kwantar da hankali, banda gaggawa banda wulakanci duk wanda ya zo kuma dagaske yake sai ku faɗi a binciki halinsa da asalinsa, ku natsu ku yi karatun ku yanda ya kamata saboda shine ginshikin zama mai nasara" haka ya cigaba da mu su nasiha har zuwa la'asar sannan su ka je yin sallah su ka maida Salmah gida.
***
Duk yanda Fatima ta so ta kwantar da hankali damuwa bai gagara ziyartar ta ba lokaci zuwa lokaci, haka ta dage da karatu har suka kammala aji uku na jami'a, a shekaran ne aka yi auren Surayya kanwar ta da ke bi mata da Anisa babban yar hajiya sadiya.
Biki aka yi na yan gata, Fatima ta shiga ta fita ta tabbatar da bikin ya tafi yanda ake so, Salmah ma ba'a barta a baya ba don zama tayi yar gida aka shagale da ita duk da ita ma bikin ta saura watanni ne.
Add Vote
Tribute to Zainab Muhammad @xiesobamention a user
Safiyyah Ummu-Abdoul
Safiyyahjibril@gmail.com
Some hours ago I called Sharhabil Yahaya Musa to confirm something concerning my soil physical measurement report, from the background I heard a frnd of ours saying "kace mata taji mutuwar zee soba" I freezed upon hearing that, even though death has no notice but Urs is one of the least expected death.
I asked him more than 3x "zee soba fa" coz my mind was busy telling he is just joking even though I knw he don't joke on serious issues like death.
I knew zainab since my 200lvl at abu but we became close during AMSA's (Association of Muslim students Agriculturalist) Agro-trip to Sokoto cement, from then onwards we became sisters. I so much respect her because of her straightforwardness and kind heart.
Earlier this year we met at faculty of Agric ABU, her words were "Sophie zamu dawo masters dinnan next year Insha'Allah, tunda kun wuce mu" not knowing u will only sit for the aptitude test before leaving us for ever..
U messaged me everytime u r coming to zaria but the meetings we r destined to have ended April 2017.
Zee I wish u d best of best of the hereafter, may ur grave be part of Raudha min riyaadil Janna, may we meet in jannatul firdaus, may Allah make ur pains a purification for ur sins and may he bless us the fortitude to bear the pain of ur loss coz My heart is seriously aching as am writing this.
Allah amshi bakoncin ki zainab😭😭😭😭
Add Vote
Assalamu Alaikum warahmatullah
Dafatan na same ku lafiya, Nagode
kwarai da addu'o'inku akan yar uwa
zainab @xiesoba, faɗin irin kaɗuwar da nayi ma ɓata lokaci ne, har yau na
kasa dawowa daidai, practical report
ɗin da na ke yi labarin mutuwar ta ya
iske ni wallahi se yau na iya
karasawa kuma last experiment ya rage min.
Kullum da zainab nake kwana nake
farkawa, d moments we had together, da na san zaman mu
kalilan ne da zumuncin da zamu yi se ya fi wanda aka yi a baya.
Rasuwar zainab ya kara tabbatar min da ɗan Adam zai mutu da burikansa. Allah bai yi zainab ta cika mafi yawan
burikanta ba. Muna fatan Allah ya
musanya mata su da lada mai girma
don burikanta mafi yawa akan neman
yardan Allah ne.
Last time da muka haɗu ta iske ni a
skul, duk yanda tayi mu haɗu
washegari mu je bikin wata a Kaduna
na ki akan bata gayyace ni ba, faɗi take ai zaman tare ya wuce a yi
gayyata ina ma lokaci zai dawo baya da kafata kafarki zainab 😢😢😢.
Add Vote.
A ranar nake mata tsiya "xiesoba bani kaso na na Npower" Ta siya min
eggrol da team tana ai wani jin daɗi
se aikin federal government ya fito. Mun rabu muna kewan juna da
alkawuran zamu haɗu akai akai not knowing it was our last.
Ta ci burin dawowa msc, muna kara
zuga ta akan ta dawo ashe ba ta da
rabo, ta so tayi entrance exams not knowing sauran ta kwana goma sha
uku a duniya.
Ta ci burin tayi aure ta nemi Aljanna ta nan, disappointments kala-kala ta
samu sai da bikin ta ya rage saura
wata biyu Allah ya amshi abarsa , a
iya sani na xiesoba ba ta taɓa Zina
ba, ina sa ran tana cikin wa'inda
annabi SAW ya kira da shahidai.
Duk na ɗauko Wattpad msgs ɗin xiesoba ke fin karfi na,
in na tashi typing tunawa da ita ma some weeks ago Haka take typing se
na ji rubutu ya fice min a rai. Amma ya muka iya, haka Allah ya tsara, haka yaso kuma haka ne daidai. Allah ya rahamshe ta ya sa jinyar da ta yi kaffara ne agareta , ya sa tana
cikin dausayin aljanna. Mu kuma in
tamu ta zo ya sa mu cika da imani.
***
Anyi bikin su surayya cikin kwanciyar hankali kowaccensu an mika ta ɗakunan mazajensu, a nan kewa ya cika Fatima don Ahlam da ya ke abokin hiranta ya cilla Kasar Masar don karanta shari'ar musulunci a jami'ar Al'azhar.
A haka ta shiga aji huɗu nan kuma aka sanya ranar auren Salmah da masoyinta Muhammad Suraj. A wajen shirye-shirye ne ta haɗu da amininsa Muhammad Khuder, tun da ya ga Fatima ya fara bibiyar ta, tun ba ta amince masa ba har dai ta bashi fuska. Murna wajen aminan biyu ba'a magana saboda ganin amintansu zai kai ga ba yanda miji zai shiga tsakani.
Sun yi soyayya mai tsafta har ya fara shirin turo iyayensa ayi tambaya, murna a wajen Fatima ba'a magana burin ta ya kusa cika itama tayi auren nan, kullum zancen su da Salmah bai wuce "aure daɗi gareshi" hakan ya sa ta matsu tayi auren ta ji daɗin da Salmah ke kira mata.
Yau ma kamar kullum Khuder ya zo gidansu su na
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 14