Share this page
takaicin rashin ba ta wani abin yayi, ko ba komai za ta ji daɗi kila hakan zai sa ta so shi. "Kar ka damu, mutane kan ɗauka ana soyayya kafin aure a dena son juna bayan aure, wannan duk ba haka bane, mutane ma su hankali kan faɗa soyayya kafin aure sai aurensu ya tayar da son da suka faɗa ya ginu a jikin su, sai su zama masoya, aminai kuma jinin da ke gudana a jikin su. Kar ka damu wai don ba ku yi soyayya ba za ku yi aure, ku natsu ku fahimci junanku sannan ku kyautata ma junanku hakan zai sa ku fara son juna cikin mutuntawa ba tare da kun sani ba" tace ganin ya yi nisa a tunani. "Ko ba ta maka bane?" Ta qara jifansa da tambaya "Wallahi ta yi, na gode ma Allah da ya bani ke a matsayin uwa, ina ganin ta fa na fara sonta, har kamanin Abbie yayi ina shauki ina kallon hoton nan" yace yana murmushi. Dariya tayi cikin jin daɗi da gode ma Allah. **** Ana shiga sabuwar wata aka fara shirye-shiryen bikin Yarima AbdulHaleem da Fatima, sai Ramlat da Suraj wanda har yanzu Alhaji Yahuza bai gama tantance za'a yi ko ba za'a yi ba don babu Suraj ba danginsa. "Ina ga za'a ɗaga auren Ramla har zuwa lokacin da da shi ma nemin nata zai turo mutanen ta, kuma kwatakwata guda nawa ta ke da za'a yi gaggawa akan zancen aurenta" Alhaji Yahuza ya faɗi suna zaune da iyalinsa "Abbie ya ce ranar daurin auren za su zo ayi komai a ranar shi ya sa bai zo ba, amma ko ɗazu ya kira ni a waya" Ramlat ta katse shi don ba ta son ya samu goyon bayan kowa. "Wai ni Alhaji mai na tsare maka ne, bakin cikin auren ya'ya na kawai ka keyi. Ita Fatima ba sai a filin bikin tambaya aka san da zancen bikin ta ba? Ka ce a'a ko kayi masa gurguwan tunani. Ga zubaida can hankali kwance a Masar duk da bakin fatan da kuka bi ta da shi, ni ko ba su zo ba a ɗaura kawai, Allah barshi na bada sadakin in ya zo ya biya ni" hajiya Amina tace hankalinta a tashe. Add Vo "Ba sai kin biya ba, ana bada aure a bashi duk ranar da ya samu sai ya biya, shike nan ko" Alhaji Yahuza ya ce yana karkada kai. "Ban numbar sa in masa magana" ya ce yana kallon Ramla, ta karanto masa ya kira, bugu biyu ya ɗaga "Yaa" ya ce daga ɗayan ɓarin wanda hakan saransa ne akan in an kira shi ya amsa da Yaa. "Yahuza ne Mahaifin Ramla" Alhaji ya amsa kai tsaye "Au toh ya aka yi? Ina Yini" Suraj ya amsa daga ɗaya gefen. "Kana da ra'ayin auren ko yanzu ka fasa?" Ya sake tambaya duk da kokarin sa na son ya kwantar da kansa da fushin da ya ji yana taso masa. "ina son baby amma gaskiya kuɗin sadaki na bai cika ba" ya amsa masa yana layi kamar wanda ya sha wani abin kawar da hankali. "Ba matsala ka zo za'a baka bashi in ka samu ka biya, ranar Jumma'a fa biki don Allah kada ku saɓa alkawari" ya sake faɗi, ba tare da godiya ba kawai ya katse daga ɗayan gefe. Nan ya bar su duka da sakin baki don duk suna jin sa don a sifika Alhaji yasa. "Alhaji ni kuwa sai in ga kamar kada ka biye ma su, Son zuciya kullum fa ga ɓacin zuciya ya ke kai mutum. Aure ba'a masa gaggawa in aka yi hakuri sai a kai ga auren mijin da zaa ce gara da aka jira" inji Hajiya Hafsa tace "kwarai kuwa, za ki ce haka da yar ki ta kusa ga rashin iya haihuwa sannan aka iya kiranyo mata miji dole ki ce haka. Yanzu wannan tsohuwar wani soyayya za ta samu wajen miji duk lokacin da ya ci tayi shagwaba ta shanye shi a gidan uba. Ni dai yata za ta yi aure ba gudu ba ja da baya" tace tana karasawa da tsaki. Nan ta cigaba da jefa magana a cewarta na suna masu hassada. Tun daga ranar aka cigaba da shirin bikin mutum biyu a gidan Alhaji Yahuza Bello da kuma fadar sarkin Qahɗaanie. Ana sauran kwana biyar daurin aure aka kawo lehe kamar yanda yan Hilaalu Sambo ke yi don ba su watsar Al'adun su na Yola ba. Babu abin da ya dauki hankalin mutane kamar zinarin da aka zuba wanda musamman masarauta ta yi odar sa daga wajen ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻣﺤﻤﺪ ﺭﺟﺐ Wato Abdullah M. R gold aka siya jaka guda aka sa mata, hakan ya sa mutane ba su maida hankali a sauran kayan ba sai a gwalagwalen. STORY CONTINUES BELOW "MaashaAllah! Fatima ta yi goshi, Allah ya sa a miki fiye da hakan bayan aure" kawai yan fatan alkhairi ke faɗi. Yayin da yan ciki baki ke faɗin "BA GIRIN-GIRIN BA ta yi mai" a zukatan su kuma suna bi da mugun addu'a. *** Faɗin yawan mutanen da su ka halarci ɗaurin auren ɓata lokaci ne ma. Sarakuna daga sassan duniya, yan siyasa da kuma manyan masu kuɗi duk sun halarta. Bayan an ɗaura ne aka shirya gagarimin Walima, amarya tayi kyau sosai lallen ta kaɗai abin a kalla ne yayi jaa yayi kyau sosai. STORY CONTINUES BE Wasu na ganin ai ta fi kyau duk da ba wani kwaliya ta yi a bikin da aka yi jiya ba, nan ɗin ɗan karamin liyafa ne ango da amarya da abokan su su ka yi a filin gidan su Fatima. Ramla ma ta yi kyau sosai, sai a wajen walima labari ke zuwa cewa ba'a ɗaura auren Ramla ba saboda angwayen ba su zo ba sannan babu wakilansa ko ɗaya. Nan Hajiya Amina ta rufe bakin mutane da faɗin in sun zo ba sai an yi wani biki ba, kawai a ɗaura aure ne a kaita ɗakinta. Nan fa surutai su ka dinga tashi, mutanena ta kus kus wasu na faɗin ba'a daura ba wasu na faɗin an daura ba dangin ango ko ɗaya. Sai cikin dare aka mika amarya fada, ɗakin ta kusa da na Ummu Maryam, kafin a yi budan kai a kaita gidanta da ke can gaba da fada. *** Washegari wajen buden kai amarya da ango sun ci kaya kalar shuɗi, musamman Alhaji Muhammadu ya je jihar Kaduna na Kasar Nijeriya ya ɗauko fitattun mawaka sha'irai masu daɗin murya wato Saadatu Isa vocal, Jamil Nafseen da MD Asnanic. Tun bayan da ya ci karo da wakar aure da su ka yi ya yaba da aikin su,lambarsu kawai ya kira. Nan su ka turo masa sakon tallansu kamar haka; <> Qungiya ce ta zaratan mawaqa samari masu kaifin qwaqwalwa gami da jini a jika, a shirye suke don sadaukar da lokutansu wajen yin amfani da baiwar da Allah ya ba su domin sanya ku nishad'i da dad'ad'an waqoqinsu cikin dad'ad'an muryoyinsu. Add Vote Wannan qungiya d'auke take da qwararrun mawaqa a fanoni da ban da ban, kamar :- Waqar Biki, Waqar Suna, Waqar Sarauta, Wakar Siyasa, Waqar Candy, Waqar Taya Murna, Waqar Passing Out, Waqar Masoya Biyu Waqar Film, Kai, har ma kai da kanka za mu iya waqewa idan kana buqata. Duk irin waqar da kuke buqata daga cikin wad'anda muka zayyano muna da mawaqin da za mu had'a ku da shi daga cikin 'ya'yan wannan qungiya ta AREWA sound RECORD, sannan za mu iya bin ku har gida mu gabatar da wasanni bayan mun buga waqar (Life performance), duka wannan muna yi ne Cikin RAHUSA matuqa. Don yin Booking za a iya tuntu6ar mu a lambobin waya kamar haka :- 08037191788 08032125326 Email:-arewasound@gmail.com WhatsApp :-07063828558 Facebook :- Arewa Sound Record Instagram:-md_asnanic Tsara talla : MD Asnanic . Saboda ya tura ma wa'inda su ka ji daɗin aikin su kuma su ka yi sha'awar gayyatar su. Bayan an zauna an gabatar da abubuwa da yake al'adan gidan sarautan Qahɗaanie aka ba sha'irai Daman baje basirarsu don gabatar da basiransu. Nan su ka fara Amshi:- Auren soyayya dadi ne da shi, Yarima Abdulhaleem ka kula da Fatima Zama mai daďi zama na aure, Aljannar masoya a gansu a tare, Ďadi ko wuya kam dukansu su jure, Suna a tare masoyan juna babu faďa balle ka ji kokawa. Fati mai karamci, mai babban suna, Inai miki nuni ki zam mai amana, Gwanar iya girki na saki da kaina, Kalamai na soyayya ki yi mai, hakan yana qara danqo na qauna. Abdulhaleem kaima, ba zan barka ba. Fatima yau taka ce, haqqinta ka duba, Tabar danginta duk, uwa har da uba, Ta yarda da kai za tai rayuwa, ka riqe amana banda kyara. Iyaye na ango ina gaishe ku, Iyayen amarya kuma na sa ku, Anties sai ku jiya ku yo rawa da taku, Qannai da yayye suna cikin tsare dole ne na sa ku cikin waqata. Kiɗan kaɗai ya ɗauki hankalin mai saurare, yan uwa sunyi rawa sun yi ɓarna kuɗi kamar ba gobe. Anan wajen budan kai ne Khuder da matarsa su ka san wa AbdulHaleem ya aura don tun da sarki ya ba da umurni a sallame ta daga tsare ta da aka yi suka je Dubai ita da Khuder bikin ya dawo da su. Nan duk su ka cika da bakin ciki don kuwa sun san ta zarce ma tunanin su. Sarki ya mata marhabin da mata kyautan sarka mai kyau da tsada. Nan aka ci aka sha, yan uwa su ka yi hotuna, kannenta da kawayen ta ma duk aka kyalla su. Kanen amarya Surayya da Najaatu Assalamu Alaikum warahmatullah Da fatan kuna lafiya, ya kuka ji da hakuri da Safiyyah, ku dai cigaba da hakuri har zuwa lokacin da uzurorin zasu daidaita, ku sa ka ni a addu'a kuma don shine kawai kaunarku gare ni bayan kun gama voting da commenting su kuma ghosties 👊👊👊 a idanun kanne daga cikin su 😢😢😢 yayyi da iyaye a tausaya kafin hawaye na ya shanye garin Kano. Yan uwa kun kula da yanda mutuwa ke ɗaukan mutane ba notice, mu gyara halayenmu musamman ga yan uwa musulmi har ga wanda ba musulmi ba, Ahlaq zai kai mutum wuta/Aljanna depending on yanda mu ka yi amfani da shi duk kuwa da yawan ibadanka.. Mu kiyaye kalaman ɓatanci ga duk wane kunne mai saurare ko idanu mai karantawa. Mu kyautata kalamanmu akan mutane sannan mu kiyaye zaqulo aibunsu. Khalifa Aliyu bn Abie ɗalib ya ce duk wanda ya fara tunanin ya fi wani mai ɓarna (alfasha) a wajen Allah toh tabbas ya ɗauko hanyar ɓata. Matukar mutum musulmi ne, ba mushriki ba ina ruwanka da zunubin sa da ke tsakanin sa da Allah, in dai ba tunkarar sa za kayi ka gyara ɓarnar da hannayenka ko bakinka ba, in kuwa yaɗa shi ne hanyar gyara to ka sani shi Allah mai yalwan Gafara ne kuma mai jin kai ne. Yan uwa muna da sauran lokacin tuba kafin kofofin tuban mu su kulle, mu gyara tsakanin mu da mutane, mu mu'amalance mutane ba tare da cutar da su da halshen mu ba ko idanunmu. Sannan mu yawaita istigfari, ibada kaɗai ba zai tsiratar da mu gobe qiyama ba. Safiyyah Ummu-Abdoul 16/01/2018 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 Ummie da kannen Fatima Sai da aka kwashi sati ana bukukuwa da shagali har abin ya gunduri Fatima, Sam ba ta taɓa son budaddan biki ba don yawan shagali a biki in shagali ya haɗa da saɓon Allah ya kan kai ga raguwa a albarkan da ke cikin aure. Amma ya ta iya, sai hakuri. Duk da shagulgula aka yi mai tsafta, talakawa sun ci sun sha, don duk wani mabukaci ya samu wadata a wannan kwanakin. Bayan kwana bakwai ɗin ne aka sada ta da gidan ta da aka keɓe ma su. Ta yaba kwarai da zubin gidan. An zuba kaya ta alfarma sannan ga kuyangi da ma'aikata da aka zuba mata bayan na'urori na zamani da ke saukaka aiki. Ta bayan gidansu kuma dawakai ne guda biyar da suka samu kyauta daga fada. An sakaye gidan da furanni don samun ingantacciyar rayuwar aure. *** A kwana a tashi satin su biyu ba tare da sun fito ko kofar gida ba. Rayuwa su ke gudanarwa cikin kauna da girmama juna, in sun zauna baya gajiya da bata labarin Kasar Amerika inda ya yi rayuwar kuruciyarsa a can, yakan nuna mata hotuna ya mata bayani. Anan ta fahimci shi mutum ne mai saukin hali amma mai wuyan gane hali. "Rayuwa babu abin darajawa kamar mace don uwata macece kuma ita ce gatana. Amma kuma babu abin da nake kyama kamar mace duk da ina son su. Ni ba wani kyau ba amma mata sun zubar da kimar su a gare ni har ya sa na dauke su kawai abin da su ka bayyana min su ɗin ne" ya ce da ita suna zaune a wajen dawakai. Kallon shi take zuciya na ayyana mata abubuwa marasa daɗi, nan ta hango darussan da ya koyar da ita a Yan zaman su ya riga ya koyar da wasunta, wasunma kazamai tambadaddu. Take zuciyar ta tayi kunci murmushin fuskar ta ya ɓace. Shi kuwa ido ya sa mata yana ganin yanda Yanayin ta ya canza kamar a shirin fim. Daga ta yayi ya ɗaura Saman doki sanin da yayi tsoron su ta ke, aiko take ta kamkame shi tana ihu, shi kuma ya sauko da ita. Rungume ta yayi su na jin saukar numfashin junansu, sai da ta samu daidaito sannan ya riko hannunta yana kallon ta cikin ido ya ce. "matsoraciya! Kin san kuwa kin fi kyau in kaka firgita" ya ce yana kyafta mata idanu. Duka ta kai masa duka a qirji nan take ya gauce yana dariya yace "Ke! Sarkin gobe za ki duka. Hmmmn ba ruwa na in hannunki ya kumbura" nan duk su ka sa dariya. Kamo ta yayi bai sauke ba sai gefen da korama ke gudana, an samar da matakala da mutum zai bi ya kai ga koraman, a nan su ka zauna, ya kunna wayarsa su na kallon video da aka turo masa ta hanyar WhatsApp. "Wow Sauti safiril bulbuli kenan, wani soja ɗan asalin Nijeriya da ya zo jami'ar mu ɗaukan kwas ne ya turo min, kuma ina son wakar" yace mata bayan ta buɗe wani video ta na kallon sa alamun neman karin bayani. "Ina son yan Nijeriya ance mutane ne masu son addini, Kaga duk kusan hijabai na a zaria Abbie ke siyo min su" tace tana murmushi "Major Abubakar Abdullahi kenan, bawan Allah mai kiyaye dokokin sa, in faɗa miki shima dai haka, in na faɗa miki tarihin wakar sai kin ci dariya" yace yana kara jinjina maganar ta na son addinin yan Nijeriya "Haba Azeezie sai na ce ka bani yanzu" Ta ce tana kashe shi da ido. " A kasar larabawa ne aka yi wani sarki lokacin jahiliyya, sannan suke ji da maaurar fasaha. To shi wannan Sarkin marowaci ne na gaske. Idan ya ji abu sau d'aya duk yawansa zai haddace, shi kuma wazirinsa idan Ya ji abu sau biyu duk yawansa zai haddace, yana da wata kuyanga a bayan lalube ita kuma duk abinda ta j i sau uku duk yawansa za ta haddace.Hakan ya ba shi dama duk mawaqin da yazo Ya biya masa waqa da sunan shi ya rera wa, sai Ya ce ai wannan waqar na santa tun tuni, bari ma ka ji in rera maka. Sai ya rera waqar, saboda dama yana da baiwar hadda in ya ji abu sau d'aya, in ya gama sai ya ce, in ma baka yarda ba ga wazirinsa nan ya san wakar, bari ka ji ya rera maka, shi kuma waziri dama ya ji sau biyu kenan sai ya rera. Sai sarkin Ya kara cewa, ai hatta kuyangina ma a cikin gida sun iya, bari in kira kuyanga ďaya ta yi maka ka ji, sai Ya kira wannan kuyangar tashi ta bayan lalube, ita ta ji sau uku Kenan, sai ta rera. STORY CONTINUES BELOW Sai kiga mawaqi yana dabur-dabur, yana tunanin anya kuwa aljanu ba su shafe shi ba, Ya akai haka. Daga nan sai sarkin Ya ce "ku amshi takardar ku auna ta a sikeli, ku ba shi zinari iya nauyin awon Takardar. Wata rana da mai Safirul Bulbuli ya ji labari, sai ya je wa da wannan Sarkin da wakar Safirul bulbuli, ai kuwa sarki Ya rasa ta ina aka fara balle Ya maimaita, shi kuma waziri dama sai ya ji sau biyu ne zai iya, ballantana kuyanga dai sai ta ji sau uku. A ranar dai aka qure Sarki, sai Ya ce to kawo takardar da ka rubuta wakar a ba ka kyauta iya nauyinta, sai mai Safirul bulbuli ya ce "ranka Ya dade sanda na rubuta ta ina daji ne ba takarda kusa da ni" Sai Ya ce "to kawo ganyen da ka yi rubutu a kai" Sai Ya ce "ranka Ya dade ba ganye ba ne" Sai Sarki ya ce kawo ko ma meye za a auna maka da shi. Ashe ďan malaminka a jikin 6angori Ya rubuta. Yana sauke mangalar jakinsa sai aka ga manyanyan 6angorai na tukunyar qasa a jiki ya yi, a ranar dai sarki sai da ya yi kyautar zinari mai nauyin gaske. Ai yana karewa ta sa dariya har da kwanto masa, rabon da ita kanta tayi dariya irin haka har ta manta. 'ashe dai yana magana sosai, amma duk haɗuwar mu kafin aure ba ya ko yarda mu yi hira balle ta ga fara'arsa' ta ce a zuciyar ta, ganin ta yi nisa a duniyar tunani ne ya ce da ita "Ba ki ji ba" Sai ta ɗaga kai tana kallon sa hi kuma ya yi amfani da wannan damar ya aika mata da sakonni da ta gagara ɗauka. Ganin ta na neman yin yaushi sai kawai ya sa mata dariya. A nan su ka yini, sai yamma su ka koma gida shi kuma ya shirya ya je Fada don ganawa da sarki. Ta raka shi har inda zai shiga motarsa, bakinta na masa addu'ar dawowa lafiya da samun nasara duk kuwa da ba ya faɗa mata abin da zai je yi fada bane. Yana tafiya ta dauki waya ta kira Abbie wanda kullum sai ta kira shi don su gaisa amma yau so take su yi hira. "Abbie, am in love" tace masa bayan sun gaisa Add Vote "Ahhhh lallai Er Abbie aure daɗi ko" yace yana dariya, ya san halin da take ciki neman wanda za ta faɗa mawa take kuma kasancewar sa amininta ya sa ta tunkare shi da zancen. "Abbie zamu ɗaure a haka ko, kar ya yi disappointing ɗina, ya zanyi? Yana da kirki kuma ga sanyin hali a ɗan iya fahimtar da na masa" Ta ce kai tsaye. "Amarsu har yanzu ba ki san mijinki ba, addu'a ce kawai babban ingredient ɗin da kike bukata, daga nan se ki rike biyayya. Banda gardama kin san maza ba sa son gardama ballantana jinin sarauta, jinin sarautar ma sarki mai jiran gado. Ki rike Allah fiye da yanda kike yi a gida, sannan kada ki dinga kallon laifi ki kalli alkhairi, hakan zai kara muku zaman lafiya." " Insha'Allah Abbie zan kiyaye, ina Ramla ne ni kuwa, na ga da ita aka yi dukkan bukukuwan da aka yi mana na fada, an kai ta kuwa " " Hmmmn! Mijin bai zo ba kuma bai turo ba, ni dai ban ɗaura mata aure ba, gata nan daga ita har uwarta fita na gagarar su" yace yana mai jin daci a ransa, don duk ya tuna sai ya ji haushi. "Amma abu bai yi daɗi ba, sai ta koma makaranta kawai don zamanta haka ba zai yiwu ba Abbie" tace tana tausayin mahaifinta. "Fatima ta ki zuwa tace za'a mata dariya don duk ta ce musu aure za ta yi" ya ce yana tsaki "Abbie ka sa mata ido, ai gara ta koma, darasi ne gareta da mu kanmu, wanda yacce ruwan wani ba zai tafasa ba Abbie na shi ko zafi ba zai yi ba, ban ga abin gaggawa a aure ba kwata kwata shekarunta nawa ne, bana take sha biyar fa, Abbie ka yi hakuri amma in har ɗaukan mataki zai sanyaya maka rai Abbie ka ɗauka kawai, na san kana cikin damuwa" Ta faɗi cikin shagwaba. "Mataki kuwa ai za ɗauka, lokacin zartarwa kawai na ke jira, kar ki damu ki kula da kanki ga Mamie ta zo ta tsare ni da ido ta ji me muke faɗi" ya ce yana dariya, mikawa Mamie wayar yayi su ka gaisa da fatima sannan su ka yi sallama. *** AbdulHaleem yana isa Fada AbdulHaseeb ya fara nema don yana cikin kewar ɗan uwansa. Tare da AbdulBaar ya gansu duk da yayi mamakin ganin su tare bai nuna ba " Haba yan uwa, kun barni cikin kewa, don Allah inji duminku" yace yana buɗe musu hannu. Ba musu su ka rungume shi zukatan su na quna. "Haseeb ka dawo sashi na don Allah, rashin ka na taɓa ni" ya sake faɗi yana rungume ɗan uwansa. Ganin hawaye idanun AbdulHaseeb ya tayar masa hankali. "Na sani, ba sai ka faɗi ba. Ka dawo mu cigaba da zaman mu tare, kai ma in ka yi aure mu zauna dukkanmu kamar yanda Ummu ta tarbiyyantar da mu" AbdulHaleem ya faɗi yana share kwalla. Zuciyar sa cike da kewan ɗan uwansa, yana tunano rayuwar da su ka yi tare. "AbdulBaar bamu waje don Allah" AbdulHaleem ya faɗi ganin ɗan uwansa ya gagara magana yana share hawaye. Bayan ya fita ne ya ja AbdulHaseeb quryar ðaki ya ce "Son mulki wai hauka ne? Na san duk abin da ke faruwa, da kuma shirin da kuke yi akan kujerar nan. Ka sani duk wani tarbiyya da zaka samo bayan na Ummu Maryam to ba zai ɓulla ba, ka tattaro ka dawo gida na mu cigaba da rayuwar mu hankali kwance, but in ka ce za ka zama matsala ba zan duba alakarta jini da ke tsakanin mu zan hukunta ka. Babu wanda zai so ka sama da AbdulHaleem Abdul-Jabbar" yana cewa ya fice ta kofar da ya shigar da su cikin gida ya je dakunan iyayensu. Dakin ummansa ya shiga karshe, kamar yanda Ummu hafsa tayi bakin cikin kiban da yayi haka Ummu Maryam ta yi farin ciki sosai, har ta kasa ɓoyewa, sun yi hira sosai su ka yi anan ya ke faɗa mata abubuwan da ya lura dangane da AbdulHaseeb da Ummu Hafsa "A'a tilona bana son ka sa zargi a zuciyar ka, don bai zo gidan ka ba shi ne wani abu ko don ya ganka yana hawaye shine na bakin ciki, kai ɗin ba hawayen ka ce kayi ba" Ta faɗi tana shashantar da sauran abubuwa da ya faɗi wanda ya ke daga bincikensa ya samo. STORY CONTINUES BELOW "shike nan nayi shiru, bari in je wajen mai Qahɗaanie" yace yana mai Mike wa don babu abin da zai faɗi ta yarda da shi sai m in ya nace ta ce shi ke son su da rigima. *** Bayan ya isa Fada, nan ya nemi izini sarki da yan majalisa su ka masa iso, fadawa su ka mika gaisuwa shi kuma ya gaida manyansa. Bayan gaisuwa ya nemi a bashi izini zai yi magana babu gardama aka bashi ya mike yana godiya. "A wannan qarni da muke ciki qarni ta ashirin da ɗaya, an samu cigaba da dama a duniya musamman duniyar kimiyya. Ina bakin ciki idan na kalli daular mu na ga muna can baya ta wannan fannin duk samun matasa masu jini jiki da ke da ilimin fasaha da kere-kere Ina so a bani dama, mu maida komai ta masarautar mu da yanar gizo, a sanya kyamarori a ko ina a cikin masarauta wacce za'a alakanta shi da rundunar sojin Qahɗaanie, a tura sojojin da su ke ɓangaren yanar gizo da satellite wato (signals) su ko you kwas da dabarun amfani da wannan na'ura. Sannan a sauya kofofin da su ke sadar da mutane ga maɓuyar bango na cikin masarauta a saka mai lambobin sirri wanda ahlin masarauta kaɗai zai mallaka." Ya ce yana mai dukar da kansa alamun godiya tare da zama. Gaba ɗaya majalisa ta yi na'am da tunaninsa, har su ka kai ga jinjina masa tare da yaba ma sarki na zaɓansa a matsayin mai jiran gado. " ka faɗa mana abin da kake so a yi ba ka faɗi tanadin da ka ma shirin" sarki ya faɗi yana gyara zama. Take ya sa aka haɗa kwamfutar majalisa ya haɗa da wayar sa nan komai ya bayyana (projector) "Nan za'a sa na'ura, kun ga ai a ɗan ɓoye ta ke, nan ma za'a saka kyamara wacce za ta dinga ɗauko abin da aka yi a nan da chan, ba za'a sa a dakunan barci da bandaki ba saboda sirri ne amma ko wace taga da kofa za ta ɗauko mai shiga da fita dakunan. Nan zai dinga ɗaukan na fada, tun daga wanda ya shigo kofar har zuwa nan, daga nan wannan zai ɗauko na daga wannan kusurwa zuwa nan" haka ya dinga nuna musu tsarin ɗin da ya zauna ya haɗa akan wannan shiri. "Muna bukatar kuɗi, don kamfanin da za su yi aikin a cikin kwanaki biyu za'a yi gudun samun matsala, ni zan ɗauko su toh in aka ji matsala ni za'a tunkara" Nan ya kammala

Chapter 8 of 14