Share this page
gida lafiya lau. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" ta faɗi dan da kyar. Tunawa da tayi da kalaman AbdulHaseeb ya sa ta barkewa da kuka, ta ina za ta fara? "Ummu ki tuba tun kafin Dana sani ya zo miki a kurarraren lokaci, babu abin da zai daga masarautanmu yanzu sai ni da AbdulHaleem, haɗin kanmu shine zaman lafiyan mu da al'umma gaba ɗaya, a da mun bi kururuwan iblis amma ina ga lokacin tuba bai kure mana ba ko" ya fadi yana fice mata daga dakin saboda irin kallon da ta ke jifan shi da shi. 'kaico na' ta faɗi tana mai kara sakin hawaye kamar famfo a zaria. "Ummu Laa tahzan, innallaha ma'ana" cewar matar Galadima tana mai share mata hawaye. Can cikin daji aka kaisu, ginin tenti ne da tamfolin aka yi du bukka bukka, cikin daya aka cusa su sannan ana sanya wasu kiran samudawa su ka kewaye su ta yanda ko suna da karfin gudu ba za su iya ba. *** Ko da sakon batan su ya iske masarauta hankula ya tashi, don ganin an sace uwar gidan mai martaba ai kowa ma bai cikin tsaro. Ganin an kwana an tashi an sake kwana an tashi babu bayanin su ya kara tayar da hankalin mutane, duk in da ka shiga zancen kenan, mutane na kara ɓuya a cikin gidajen su, masallatai su ka ɗauki qunuti da sauran addu'oi don samun agaji daga mai duka. Sai da aka yi kwana huɗu sannan mai martaba ya tara yan jarida don ya aika ma mutanen sa kalaman sa duk da kuwa kasancewar sa cikin rudu da tashin hankali. "Yaa ku al'ummata, ina muku gaisuwa irin ta yan aljanna Assalamu Alaikum warahmatullah..." Ya fara faɗi bayan ya zauna, sannan yai shiru yana haska duk wani mai kallon sa da murmushi. "Hakika na san muna cikin rudani saboda bacewan iyayen gari guda biyu kwana hudu da su ka wuce, ni rudani na ba don bacewan su bane, halin da kuke neman jefa kawunan ku ne tashin hankali na, rayuwar al'umma ta ya fi min mahimmanci akan na daya daga cikin iyali na, sannan tsoro ke sa a ci galaba akan gwani. Abin da nake so da ku shine mu haɗa karfi da karfe mu ga mun yaki ɓata gari ma su son ganin karshen daular mu, mu tona asirin duk wani mugu da ke ɓoye a cikin mu sannan mu cigaba da addu'a tare da gyara halayyanmu. Allah na tare da mai hakuri mai yawan bauta masa" ya fadi a karshe yana mai yi musu sallama. Kalaman mai martaba ya dawo ma da yawa da suka yanke kauna kuzarinsu da kuma wani karfin son ganin sun samu nasara. Sai da akayi sati da sace su labarin ya iske AbdulHaleem yana Mauritius lokacin, tun da ya ji yake kokarin san kamo inda suke ta hanyar tauraron dan adam da yanar gizo. "Wai mun zo nan ɗin ma ba zan mori miji na ba, ka aje kwamfutar nan ka saurare ni" fatima ta ce tana jan kafafunsa. Add Vote ohhh Azeezaty, nourie" yace yana jan hancin ta ganin ya fara samo abin da yake nema. Zama tayi gefen sa tana kallon yanda y a ke abu se kace wasan aljanu. 'wai wannan da kwamfutar ya karanta ba gina makamashin nukiliya ba da se Allah' ta faɗi tana murmushi ganin baiwan da Allah ya ma mijinta. Ya kai gaf dazai kai wajen da ya tabbatar da nan ne sansanin yan ta'addan ne sakon ya rufe sai wata wasika da ya shigo. Cikin jin haushi ya buɗe yana tsaki 'Shiga wannan don yin hiran bidiyo da wakilin mu" ya gani rubuce, bai yi kasa a guiwa ba ya shiga link ɗin inda cikin kankanin lokaci ya iske shi a shafin. Turawa uku ne su ka bayyana kowannensu sanye da tufafin kare hakkin bil adama. "Muna maka barka da maraice, muna godiya da amsa gayyatar mu" su ka faɗi, girgiza kansa yayi don ya matsu ya ji rainin hankalin da su ke shirin karanto masa. "Muna daga cikin masu kare hakkin dan adam ne na majalisan dinkin duniya, mun yaba da kokarin ka na son fitar da ta'addanci daga yankin Qahɗaanie, amma ka san dai su ma mutane ne kuma su na da ikon yin rayuwa kamar kowane ɗan Adam, akwai kudade da majalisa zata dinga biyan Qahɗaanie duk shekara matukar za ku kauda kanku daga harkan ta'addancin da ake a yankin ku, da wannan kudin za ku iya kai daular ku zuwa ga wata mataki mai dorewa tare da samun taimako daga wajen mu. Sai dai rashin ɗaukan shawara zai iya sa ka cikin matsalan cin zarafi ɗan Adam" su ka faɗi suna saurarensa. "Su kuma al'ummanmu da ake kashewa kullum fa su kuma ba su da gata kenan" ya tambaya a kufule "Ai su ɗin ba kungiya bace, sannan kowa baya wuce wa'adinsa, saboda haka nake shawartan ka da tsaya a matsayin ka kar ka zaqe da yawa" su na gama faɗi su ka ɗauke. Ko da ya koma ya cigaba da tracking waincan nan ya iske komi wayam. "Dama an faɗi, turawan nan na da hannu a ta'addancin da ake da sunan Musulunci" ya faɗi cikin tashin hankali. Se a lokacin ya tuna Fatima ta shigo ko a yaushe ta fita bai ma sani ba. Ji yayi zaman Mauritius din ya fice masa a rai, babu abin da ya ke so. Kamar ya koma Kasar sa ta gado, ya fito ya yaki yan ta'adda har sai sun zama tarihi. *** Washe garin wayar AbdulHaleem aka sako duk wani da yan Ismaalie su ka sace, maza da mata wasu da ciki wasu a nakashe abin dai babu daɗin ji. Sarki yai murna da dawowarsu su sannan ya kara bada shela duk wani dan ta'adda ya aje makami sa ya zo masarauta zata ba shi aikin yi don in ya bari masarauta ta kamo shi toh ya sani hukuncin sa kisa ne. Wannan hukuncin ya zama kanun labarin duk wani kamfanin rediyo ko jarida, wasu na jinjina masa yayin da wasu ke ganin ya tsaurara amma shi bai bi ta kan kowannensu ba ya cigaba da hidimominsa. *** An shafe wata shida babu wani tarzoma da ya sake tashi a daular Musulunci Qahɗaanie, mutane sun cigaba da lamuran su kamar ba'a yi ba, an manta da wasu Ismaalie saboda tunanin sun zama tarihi, kwatsam sai aka wayi gari da tashin bomb a masallacin kusa da jami'a. Inda aka samu rashin rayuka da dama. Hankalin mai martaba ya tashi don bai taɓa tunanin mutanen nan na nan ba. An sallaci mamata an kai su gidajen su na gaskiya sannan aka yi makokin kwana uku. Ana cikin makokin ne AbdulHaleem ya sauka da iyalinsa da Ramlat da Ahmad dinta. Sun iso mutane na ta farin ciki saboda a bayyane su ka dawo. "MaashaAllah, AbdulHaleem ne da yara biyar, kai ya kamata mu yunkura munyi aure muma" cewan AbdulBaar yana mai rike da yaran da Fatima ta haifa a Mauritius yan biyu masu kama da mahaifinsu. Haka su kai ta santinsu tun bayan isowarsu. "Ai se hamdala kam, ka san duk abin da aka ce maka ba yin mutum bane na Allah ne shi ya ke yin sa a lokacin da ya so ga wanda ya so. Dubi auren nan nasu da irin sheɗancin da muka saka kanmu a ciki amma da ya ke Allah ya riga ya tsara hakan zai faru ba gashi nan ka ji su tsit ba, sai albarka da su ke tayi" AbdulHaseeb ya fadi yana mai jin Dana sani a tattare da shi. Baya gajiya da nadaman abin da ya faru a baya, sannan baya gajiya da ba kanshi laifi akan duk wani tashin hankali da su ka fuskanta a daular Qahɗaanie. *** AbdulHaleem da shirin sa ya dawo, bai faɗi ma kowa ba cikin dare ya je ya birne duk abin da ya kunso ya dawo da shi. Sannan ya koma gida abin sa. "Ai duk wanda ya taimaka wajen rufa ma mai ɓarnar asiri toh shima yana daga cikin masu ɓarnar" ya ke ta faɗi ma kanshi duk lokacin da tunanin wa'inda ba su da hannu da abin zai shafa ya faɗo ma sa a rai. *** Tun bayan da ya tabbatar da mabuyar yan ta'adda a Qahɗaanie ya zauna ya shirya ma su yanda zai karar da manyan su yanda hakan zai ɓatar da kananan. Da haka ya kulla abota da daya daga cikin su ta hanyar shafin Twitter. Anan ya dinga sanin sirrin su har ya san shirin da su ke da niyyar yi na kona sarauta sai a koma damurkadiyya a Qahɗaanie. Tun daga lokacin ya kara kaimi a shirin sa cikin sirri har ya kai ga shuka nukiliya a yau da ya tabbatar da suna cikin shirin yin taro da mutanen su zasu hallara ciki kuwa har da Saifullahi Alhamzie. *** Karfe sha biyu na dare nakiyar da ya shuka su ka fashe, nan gaba daya gari ya dauka. Mutane sun rufe kunnuwansu don a tunanin su girgizan kasa ne ya faru a Qahɗaanie. Hayaki da kara ke karade ko ina yayin da ɗakin taron Ismaalie ya banke kurmus ba tare da ko ɗaya daga cikin su ya fita ba. Sai da garin Allah ya waye sannan aka ga in da aka samu tashin nakiya, nan take masarauta ta fitar da sun shigo da nakiyoyi ne don su hallaka Al'umman Qahɗaanie sai abin ya tashi musu. AbdulHaleem ya bayar da shedu cikin wa'inda ya biya kudi akan suna cikin Ismaalie amma su an tura su gadin matan su ne. Duniya kwarai ta girgiza da wannan balle da aka samu kusoshin wasu kasashe a cikin mamata. Salam Ku kara hakuri da ni pls, ba haka na so ba amma kuma haka abin ya zo. Please ku sanya ni a cikin addu'aoi ku. Ina son ku ina kaunar ku fi SABILILLAH... Kila na baku wani Anjima Bayan wasu shekaru masu tsawo... "Papa ka ganta ko, wai nace zan zani wajen Ummu tana cewa princess ba sa fita, ni de a kaini ko wajen Ummu ko wajen Abbie" faɗin yarinya yar shekara huɗu. "kin manta alkawarin ki da abbun ki, ɗazu fa su ka zo da ummi ko kin manta" yace yana gyara gilashin idon sa. Shiru tayi kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta sa kuka. Ya rasa me zai mata ta yi shiru, rigiman ta ya fi na sauran ya'yan da Allah ya musu ga shi ta faɗo gidan farfesa ina ka fito littafi ina za ki littafi. Safiyyah kenan er su ta takwas, bayan yan uku Allah ya azurta su da biyu maza Muhammad da Mahmood, Fatima ta sake yan biyu kuma maza Mus'ab da Musayyib sai auta Safiyyah. Tun bayan dawowarsu Qahɗaanie abubuwa su ka cigaba da lafawa, tsiararun yan ta'adda da su ka yi saura su ka tsere daga yankin saboda hukunci mai tsauri da ake ɗaukan masu. A cikin wannan ne Zubaida ta samu ta tsero gida bayan duk ya'yan da ta haifa sun rasu a dalilin tashin nakiya. Da fari Abbie ya ki amsar ta saboda a cewan sa itama er ta'adda ce, haka aka dauke ta zuwa fada bayan kuka babu abin da take yi ita da ammi. "Ban san miji na dan ta'adda bane sai bayan sa su ka kwace fada, sun kasance suna karanta Ayoyin qur'ani da fassara da yayi daidai da ra'ayin su tare da alkawarin ni'ima ga wa'inda su ka yi taaddanci. Tun da ya fahimci na fara d'ago shi ya yanke min fita, duk yanda na so da na gudu na kasa da ga karshe ya min alkawarin in na yi yunkurin guduwa sai ya kashe Abbie" ta faɗi cikin shessheka lokacin da mai martaba ya tsareta da tambaya. "ban ki ko wane hukunci daga gare ku ba, yin gaggawa a al'amura ko da yaushe tudun Dana sani ya ke sauke mutum. Ban nemi zaɓin Allah ba a aure a tunani na wayau da dabara ke kai mutum ga aure wanda bai yi ba kuma yin kansa ne ba wai lokaci bane. Sai da lokaci ya kure min sannan na san BA GIRIN-GIRIN BA ne abin tayi mai. Ga ukhty Fatima wa zai ce ta taɓa dadewa ba aure, duk wani jin daɗi da mace ke nema a gidan miji ta samu fiye da haka, kaico na" ta faɗi tana fashewa da wani sabon kuka. Jikin wa'inda ke wajen duk yayi sanyi, wasu na tausayin ta wasu na tunanin na su makoman. "BA komai ke kai mutane ga gaggawa akan abin da ya jibinci aure ba sai daukansa da ake gasa ba ibada ba, don kowa da na shi tsarin rayuwa, sannan hassada ba abin da ya ke karawa se ci baya. In ka ce baka yi aure ba, saoinka sun yi, saoinka nawa ke gadajen asibiti sannan nawa ke gidan mahaukata? In ka ce baka da kuɗi kannen ka na dashi wasu suna can suna kokuwa da numfashi don su samu su rayu kamar kai. In kana tunanin kai ka fi wani kayi aure shi bai yi ba, kila kullum sai ka zubar da hawaye saboda bakin ciki da kake samu a gidan auren shi yana can hankalin sa kwance. In kana ganin ka fi wani dukiya ne kake masa dagawa toh a duniyar nan ma mutane nawa su ka san da kai. In kuwa ka ce hassada da kyashi da bakin ciki ne zaka sa a gaba toh tabbas kyashin nan, hassadan nan ko bakin cikin nan shi zai zama. Ajalin ka. A rayuwar nan fa yanzu kawai kake da shi, jiya ya wuce babu amfanin dawo da shi, sannan ba ka da tabbas din kaiwa anjima balle ka tsaya fada akan gobe" mai martaba ya fadi yana mai sallaman kowa. *** Rayuwar su ta cigaba da tafiya sannu a hankali, komi na tafiya daidai misali, Fatima ta koma bakin aikin ta, Ramlat ta koma makaranta inda AbdulHaseeb ya kasa kai da kafa bai da mata sai Ramlat. Zubaida kuma ta koma gida gaban su Abbie. Nasarori su ka dinga samun su tun bayan auren AbdulHaseeb da Ramlat. Sannu a hankali Fatima ta taka matakin farfesa duk yanda masarauta ta so ta aje aikin ta ki don a cewar ta Mafarkin Mahaifin ta ne dole ta cika masa shi. *** Daular Musulunci Qahɗaanie ta kara samun cigaba, in da komai nata na tafiya daidai da zamani. Kwanciyar hankali da zaman lafiya ya wanzu sosai a daular. Ilimin kimiyya da kere-kere ya zama abin da ke kara ɗaga daular. Mulkin daular ta koma hannun yarima AbdulHaleem duk da mai martaba na nan a matsayin sa na sarkin Qahɗaanie. AbdulHaseeb na kula da rundunar sojin Qahɗaanie. AbdulBaar ya koma neman ilimin addini har ya taka matakin malanta saboda ganin sa hidiman da zai ma addini ne kawai zai jawo masa Rahma wajen Ubangiji. *** Kukan da Safiyyah ta saki ne ya dawo da AbdulHaleem daga duniyar tunanin da ya shiga. Cikin masu yi musu hidima ya kira aka ɗauke ta don ya san ba zata barshi ya natsu ya gama shirya cigaban da ya samo na amfani da karan masara wajen fitar da takin noma da yake so a gwada a damina mai zuwa. Ana fita da ita farfesa Fatima ta shigo tana mai rungume mijinta ta baya. "o'ooo ina ta mamakin inda Safiyyah ta koyo rigima ashe dai..." bata bari ya kai karshe ba ta mantar da shi duniyar da su ke ciki Alhamdulillah.... Banso ya kare anan ba but wani dalili ya sa dole na cire more than 5 chapters don kawai mu kammala a yau. Ba a son raina bane but may b a gaba in da rai da lafiya kuma Allah Ya so zan dawo na gyara. In kun lura ko comments bana bi yanzu kun ga hakan kadai ya isa sheda cewa ina wani yanayi.. Kun san ina sonku ko💞💕 wannan na har abada ne. Tana iya yiwuwa ba zaku kara ji na ba har se wata shekara, tana iya yiwuwa kuma ku ji ni bayan Ramadan. Amma ko ma dai menene ina rokon duk wanda na ɓata ma wa da ta/ya yafe min. Allah sada mu da alkhairi Safiyyah Ummu-Abdoul Safiyyahjibril@gmail.com 08157284163 Add Vote An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 14 of 14