Share this page
ka iske maigadi har ya isa yana jiransu a kofar fada. " ga wannan Nutud dubu ɗari kuma bashi ka ja jari zan nemi kuɗi na nan da shekara ɗaya, sannan gobe ka rubuta wasikar ajiye aiki, tsohon ka da kai ka tsaya aikin gadi, nawa ne albashin na ka? Maza ka je ka san abin da zaka fara don rana ita yau shekara mai zuwa in ba ka biya bashi ba, sannan baka ɗauki akalla mutum biyar aiki karkashin ka ba za'a neme ka a rasa" Ya karasa cikin izza da isa. Bai jira yayi godiya ba ya wuce abin shi ya bar tsoho cikin farin ciki. One word for the first chapter Guess our main male protagonist Guess where this story is heading to Thnx alot for the votes and comments pls don't get tired I love u ol. mention a usermention a user Una don start ba, Haba ghosties, pls now, ga ni akan guiwa, pls vote and comment Gabas da Qahɗaanie akwai wata karamar yanki da ake kira Zango. Wanda Amir Al'ansarie ke shugabantar Zangon. Duk wani nau'i na ta'addanci da alkba'ir za ka samu ana aikata shi kai tsaye a wannan yankin amma hakan bai sa a ci zarafin ahlin wannan yanki ko kuma a musguna masu ba. *** Asalin Al'ansarie mutumin Qahɗaanie ne don tare da iyayensa na hamsin da bakwai Sheik jibril ya kafa daular Qahɗaanie. Hakan ya sa ya ga shi ya fi kowa cancantar rike sarautar Daular a wannan lokacin har ya fito takara da sarkin wannan zamani duk da ba'a kallon gidansu a matsayin gidan sarauta. Tun a zagaye na farko aka watsar da shi daga jerin wa'inda kwamitin za su zaɓa, a karshe aka zaɓi sarki AbdulJaleel wanda akasarin al'ummar daula suka aminta ya zama shugaba gare su, ku ma shi ne jinin sarki kwaya ɗaya tilo da yayi saura har mutuwar sarki. wannan zaɓe ne ya tunzura Amir wanda asalin sunansa Saifullahi Alhamzie kafa na shi yankin ya sanya masa Zango saboda wannan yankin ne duk wani wanda zai tsallake Qahɗaanie zuwa fatauci kan tsaya don ya huta. Abu na farko da ya fara yi shine bai wa yan fashi masauki a wannan yankin. Ya basu hannun amana su ka amince su ka amsa sannan ya musu alkawarin kariya, a dalilin haka Larabawa daga cikinsu suka fara kiran sa da Ameer.. Daga nan ya ba dukkan fatake masu yaɗa Zangon hannun aminci tare da alkawari ga duk wanda ya yi rajista da shi cewar babu shi ba wahalar yan fashi don ko ina aka musu a bisa kuskure yayi alkawarin maida musu da dukiyarsu da aka sace, hakan ya sa Larabawa daga cikin su sanya masa Al'ansarie.. Kafin shekara ya zagayo Al'ansarie ya samu cigaba don yankin sa ya habbaka sosai sai kuma aka fara damun al'ummar daula da sata, fashi har ma akan taɓa fyade. "Mai girma Ranka shi daɗe, ranmu fansa a gare ka, binciken da mu ka yi ya nuna mana da sa hannun Saifullahi Alhamzie ake duk Wa'innan miyagun ayyukan.. Ka bamu izini mu zubar da jinin sa kafin ya fi karfin mu" cewar sarki yaki kuma kwamandar sojojin Daular Qahɗaanie. "Ku gayyato mana shi ne, mu ji daga gare shi" cewar sarki a wancan lokacin. Bisa ga yin biyayya ga sarki aka gayyato saifullahi har fada, bayan an karanto masa abin da ake tuhumar sa da shi ne ya ce "Ba ni na sa su sana'ar nan ba, sannan ba na cin ko digo daga haramun, suna min biyayya dai saboda adalci na gare su, zan yi biyayya ga umurninku amma bisa sharadin babu ruwan hukumar daular nan da su, in an kama su da yin laifi a sanar da ni, karkashi na su ke ni na fi kowa cancantar hukunta su" nan take fada ta kaure da hayaniya dogarai da sojoji na jiran umurni don zartar masa da hukuncin da ya dace da shi na yi ma sarki tsaurin ido, amma ga mamakin su sai sarki ya ce "Shi ke nan abin da kake bukata? Ko da wani sharadin, in shike nan ni kuma ina so ka sani duk ranar da ka saɓa alkawari za mu ci ka da yaki, ko kuda aka taɓa a Qahɗaanie zan turo dakarun da za su taho min da kanka ko da gangar jikinka zai cigaba da aiki ko ba zai cigaba ba, babu abin da ya shafe ni. Kada ka yi tunanin zan dubi zumunci kasancewar ka ɗan kawun mahaifiyata, na sallame ka" "Godiya nake" yace yana mai ficewa. Sarki bai ba kowa fuskan korafi akai ba. Kuma tun daga lokacin har yanzu shekaru talatin da biyu kenan ko kaza ba'a ake sata ba a Qahɗaanie haka ko tsakar dare mace ta fita babu wanda zai tunkare ta balle ya cutar da ita. *** Gagarumin Sata aka yi a kasar Ghana inda aka yi fashi a babban bankin Kasar (central bank of Ghana) kuɗi aka sace da in aka juya zuwa dollar zai iya kai dollar biliyan talatin, hankalin gwamnatin Kasar ya tashi ainun nan aka sa bincike ana neman wa'inda su ka yi fashin ta hanyar na'ororin ɗaukan hotuna da ke maqale a bankin. Add Vote Dukkansu sanye su ke da lullubin fuska, dauke su ke da na'ororin buɗe kofofi wanda da gani ba karamin. Masanin fasaha ne ya qera Shi ba. Ba sa magana sai dai yin alamu da idanun su da ke buɗe. Har sifeto janar din yan sandan Kasar zai ce a kashe faifain da aka samo daga bankin sai fuska ta bayyana na shugaban tawagar, nan take ya sa aka tsayar aka dauki fuskan hoto haɗe da tsayar da faifan bidiyon. Binciken farko da su ka yi nan su ka gano mammalakin fuskan ta hanyar yanar gizo "Adjetey Tetteh" shine sunan da ya fito da duk wani shafi da ya bayyana sunansa. Bincike ya nuna ɗan unguwar Zango ne da ke Kasar Ghana (zango community). Nan take a ka baza hotunan sa a ko ina da sunan a kawo ma gwamnati shi ko a mace ko a raye. "Nii Adjetey ka ga hotunan ka a ko ina ana nema a mace ko a raye, ya kamata ka aiwatar da wani abu in ba haka ba za'a kashe ka ne a banza" cewar ɗaya daga cikin yan tawagar sa, duk da ya san ba wai zai tsorata bane don duk duniya Adjetey ya kasance mara tsoron komi da kowa. Sai dai abin da ba su sani ba duniya ba wanda yake so da kauna sai Amir Al'ansarie. "Babu damuwa Armah, zuwa gobe maganar zai zama tarihi, yanzu dai ku tabbata kun bar yankin nan, zan kula da kaina, abu ɗaya za ku sa a ranki shi ne Amana, sannan abokantaka na da hakki fiye da jini, in dai kuna tare da ni, babu abin da za'a mana" da haka ya juya baya alamun ya sallami Armah. Bayan fitar Armah, wayar sa ya ɗauka ya latsa wasu lambobi, kara na biyu aka ɗaga daga wancan ɓangaren. "Yau ɗa na ya ni me ni, ina fatan bai yi girman da ya fi karfin taimakon uban sa ba" suka sauka a kan kunnen sa "ina neman afuwa Amir, ba zan taba yin girman da zan fi karfin albarkan uba ba, yanzu haka rai na ake nema ido rufe a Ghana, kuma na san ba ka shirya birne ɗan ka ba" Ya fadi yana mai cike da imanin matsalar sa ta kawo karshe. "Gobe da safe ka shirya wani zai zo ka sammasu wani abu cikin abin da kuka samu, da yamma kuma duk runtsi ka iso nan waje na" Ya ce masa kai tsaye ba tare da ya ja zancen da tsawo ba. Godiya Adjetey yayi ya ajiye wayar. Amir na ajiye wayar Adjetey ya nemi sifeto a waya bayan doguwar gaisuwa da ke nuna alamar sanayya ya ce "Wannan aiki na kasan rai ne shi ya sa na neme ka in ba haka ba gobe iwar haka Kasar Ghana za ta kasance cikin kunci da tashin hankali, na ji yaranka na neman raina" Ya faɗi kai tsaye "Ranka kuma Amir, da taimakon ka na dane kujerar nan, ka taimaka ka min bayani yanda zan gane" "Adjetey yarona ne na kasan rai, ka je gidansa ka amshi abin da za mu iya baka a ciki maganar nan ya zama tarihi. In kuma ka ki, toh tabbas ran Adjetey daidai yake da na kusan duk wanda Ajali yayi kiran sa. Adjetey na gidansa na zango community, kana iya zuwa yanzu" Amir ya karasa yana mai katse wayar. Hankalin sifeto ya tashi, ga koshi ga kwanar yunwa. Bayan ya zauna yayi tunani mai zurfi can dai ya yanke shawarar karɓan rabon sa ya kara gaba. A cikin daren ya shirya fita ofireshon inda yayi nasaran kashe wani mashayi, aka ɗauke hotunan sa cikin jini da sunan shi ne Adjetey. Sannan ba'a samu kuɗin ba don a inda aka same shi bindiga kawai aka Samu sai kwalaban giya. Wannan labari ya kara ma sifeto daraja a idon al'ummar Kasar Ghana don ganin da shi aka fita ofireshon. Shi kuma Adjetey ya isa Zangon Qahɗaanie kamar Yanda Amir ya umurce shi. *** Wanka ta fito cikin sauri kasancewar ta yi latti, tana yi tana kallon agogo hakan ya sa ta zira doguwar riga baki mai filawowi a jikinsa. Karamin hijab ta sa wanda iyakarsa hannunta ruwan ganye wanda ya shiga da wasu daga cikin filawowin jikin rigar. Tsaraban Mahaifin ta ne daga zaria ɗinkin hazikin ma ɗinkin hijabi baban sadiya mijin sadiya. Duk ta sanya hijabin nan sai an faɗa mata yanda hijabin ya fito da ita ya bayyana kyawunta, hakan ya sa ta aika masa da kuɗi ya ɗin ko mata kaloli daban daban har guda goma. Bayan ta gama ne ta tsaya gaban doguwar Madubin ta da ya kai tsawon ta, duk da kasancewar ta doguwa, doguwa da ta kasance doguwa don ita mace ce. Fara ce tas, saboda jinin Fulani da Larabawa da ke yawo jikinta, kirjinta a cike yake sannan tumbin ta a shafe yake, tana da mazauna daidai misali duk da cewa siririya ce sosai. Gashin kanta a dunkule yake yayi tuntu, hakan ya sa hijabin ya ɗan dage ta keyarta ya zama wani nau'i ma. Kwalliya. "Abie na shirya ka min addu'a" Ta faɗi yayin da ta iske iyayenta na yin kalaci "Kin yi kyau sosai yar albarka, Allah shiga tsakanin ki da magauta, ki dawo cike da aminci kinji" yace yana mai yin musabaha da ita. "Ummie! Mamie!! Ammie!!! Na wuce, se na dawo" Ta ce tana mai shirin fita "Yaya Fatima ki dawo da wuri don Allah, za a zo gaisuwa daga gidan su Sufyan, ba zan so a zo ba ki ba" cewar zubaida kanwar ta na wajen biyar sannan babban yar Ammie. "MaashaAllah, ana gama meeting zan dawo Insha'Allah. Ki ce za mu sha biki" tace tana mai cike da murna. "Ai kam de, tun da manya su yafe girman su gara kanne su yi su yi, kannenki uku na ɗakunan su amma ke ko kunya ba kyaji" cewar Mamie kai tsaye, fatima ba ta tanka ba ta sa kai ta wuce makaranta abin ta. Assalamu Alaikum warahmatullah Da fatan kuna lafiya. Exams time table is out, 2 more posts before the date Insha'Allah. Se kuma 13th December da zan gama Insha'Allah from then daily updates if my thesis permit. Don't forget to vote, comment and share ﺃﺣﺒﻜﻢ ﻳﺠﺮﻱ ﻓﻲ ﺩﻣﻲ 😘😍💞💕 Bin ta su ka yi da kallo har ta ɓace ma ganin su. Nan su ka ji karan tashin motar ta kirar vibe, sannan Alhaji Yahuza ya maida kallon shi ga matansa "Duk wata wacce ta sake goranta ma ɗaya daga cikin ya'ya na gorin aure toh a bakin aurenta da ni, ko da kuwa ita ta haifi yar, ko da kuwa a bayan ido na ne, in ta rufe ta kwashi zunubin zaman zina ita kaɗai. Rawa ake ma Allah ya sa mutum yayi aure? Na tabbata da rawa ake da dukkanku na gidajen iyayenku ba aure. Kun fi ta son taga tayi aure ne? Ba Za ku sa ma yata damuwa ba, in ba zaku bi ta da addu'a da fatan alkhairi ba toh ku kyale min ita" yace rai a ɓace "Amma Alhaji haka za'a sa mata ido tana haɗa kafadu da mu" mahaifiyarta tace tana mai jin haushin yanda yake ɗaure ba karya kugu "A'a, sa ta zamu yi a gaba ta bi duk samari da mazan aure da suka bata sha'awa tana rokon su arzikin zuwa neman aurenta. Ko so kuke in ɗauki hoton ta ina yawo masallaci mai so ya zo ya ɗauka. Ko yau ta rasu bata ci baya ba, ba haka aka so ba amma kuma alkhairi ne gareta don ina da tabbacin ba ta taɓa zina ba. Wasu ma sun haifa sun yar an kuma aure su balle nawa kintsatssa" Ya ce yana mikewa haɗe da kakkabe riga "Alhaji toh wa ye yayi haihuwan gaba da Fatiha, ni dai na san duk a ledan mu ka auro mu balle ka saki magana" waigowa yayi duk da ya san ita kaɗai ce zata iya maida masa amsa ta kwana lafiya shi ya sa a hali irin haka take shigar ma abokan zamanta fada ko da kuwa ita aka cuta. Sai da ya kare ma dukkansu kallo sannan yace; "Ke dai kin san kan ki, ko da yake kila ma ba ki san kanki ba bare saura" Nan ya fita ya barsu duka kamar ruwa ya cinye su. Kowannensu da abin da yake sakawa a rai. Makarantar su fatima ya isa nan ya iske sun shiga taron,jira yayi har su ka kammala. Tana fitowa tayi arba da shi, nan ta nemi duk wani damuwa ta rasa, fuska yalawace da fara'a ta iske shi "Abie Allah ya bar min kai" Ta faɗi cikin farin ciki. "Aminin kwarai ke saurin isa ga amini lokacin da wata damuwa ta samu amininsa, a ina zamu zauna ko mu karasa wajen cin abinci ne" Ya ce yana daga mata gira "A'a mu je lambun fada" tace tana jin farin ciki na wanke bakin cikin da ta fito gida dashi. Tafiyar minti ashirin ya sada su da lambun fada, suna yi suna tsere tsakanin su don kowannensu a cikin motarsa yake. Lambun fada babban waje ne da ya kunshi ababen shakatawa tun daga furanni, tsuntsaye da saiwa kala kala. Lambun ya kasance daya daga cikin abin da Daular ke samun kuɗin shiga don in zaka shiga wajen sau ɗari a rana duk shiga sai ka yanki tikiti na nutud hamsin. Sannan duk wani abin lashe baki da ake siyarwa a waje daga aljihun masarauta ne don haka riban na amfanin al'umma ne. Bayan sun zauna aka kawo musu abin taɓa ka lashe ne ya kalle ta yace Add " Faɗa min damuwar ki, na san kina ta tunanin wacce za ki kai m kukan ki ne ko" Ya faɗi yana dariya "Abbie aure nake so, babu wanda ya ke so na yanzu, duk masu zuwa min da an kwana biyu sai su nemi yin zina da ni, Abbie kallon wata mai nakasa ake min saboda rashin aure" Ta ce tana hawaye "Toh fatima kina da karfin chanza kaddaranki ne, ko masu miki magana da habaici suna da ikon chanza kaddaranki ne? Damuwa ba abin da yake sawa sai cuta ba ya biyan bukata. Ina so ki sa a ranki duk abin da yake rabon ki ba zai wuce ki ba, abin da ba rabon ki ba ko kinyi zina ko kinyi tsafi ko me za kiyi in dai ba rabon ki bane ba zai zo miki ba. Ki yi hakuri" Ya ce yana lallashin ta "Abbie shi ne aka ce ko zan samu masu ruqya ne su min ko a amso min rubutu saboda aljanu na hana aure" Ta sake faɗin haka cikin marairaicewa "Subhanallah! Fatima kada ki ɓa ta imaninki, su za su sa Allah ya aurar da ke in bai so ba? Shi faFA'ALLUN LIMA YURID ne, kada ki yarda a maida ki hanyar yin kuɗi, garin haka a yayimo miki muguwar fata. Ba kya yin azkar ɗinki ne? " Abbie ina yi kullum,safe, maraice, bayan sallah farali, na barci, na tashi daga barci duk ina yi" "Toh kenan kina yi ne ma fashion ba wai da imani ba, don in kina yi da imani kin san kin fi karfin duk wani mai sharri don kariyan Allah ke tattare da ke, in haka ne babu wani dan 419 da zai ci kuɗin ki. Kwantar da hankalinki babu jinkirin da ba alkhairi ba, kuma ana yin auren masu gulman kin ki aure za su fara hassadan jin daɗin da kika iske a gidan auren. Almuhim ki tsare mutuncin ki, wanda bai aure ki ba don baki ba shi jikinki ba toh ko kin bashi ba auren ki zai ba" yace yana mai kara mata kuzari "Abin ne yana damu na, tun ba in naga yara da ya'yan su ba" tace cikin karaya "su kuma suna sha'awar ki ba, abin da baki sani ba wasu sun yi Dana sanin aurensu sau Bila adadi, ke dai kawai ki roki Alkhairi Insha'Allah zaki manta anyi wannan. Ki kara hakuri kinji, Allah ya miki albarka ya sa ki dace kin ji" yace nan su ka zauna jugum "kin san kafin na auri Ummie sai da na yi soyayyar shekara biyar da Ammie. Soyayyar in ba ke ba sai rijiya ɗin nan" Ya faɗi yana dariya. Itama dariyan ta yi tare da maida hankali gare shi cike da son jin labarin "zan iya cewa ita ce masoyiyar farko, in kika ganta lokacin kamar kada kuda ya taɓa. Hakan ya sa mu ka buga gasa da manyan mutane ciki har da Saifullahi Alhamze" "wanene Saifullahi ɗin" "Au Amir Alnasarie, kwatsam sai ya aiko ma Marigayi alhaji da sakon in har yana son ya sake haihuwan wani Yahuza toh in cigaba da neman Amina. Nayi kunci kamar ba zan rayu ba can dai na hakura don dole, hakan ya sa ido na ya gano ummi, cikin ikon Allah a cikin wata uku mu ka yi aure. In kika sa ma ranki dole-dole sai miji iri kaza, toh ba za ki buɗe zuciya ki karbi zaɓin Allah ba, ki maida zuciyar ki ba kowa se abin da Allah ya azurta ki dashi" haka ya cigaba da mata nasiha har sai sai da aka kira azahar. Sannan su ka shirya su ka tafi gida zukatansu fal da farin ciki. *** Sai bayan isha'i sannan Adjetey ya isa Zangon Qahɗanie. Hankalinsa bai kwanta ba sai da ya ganshi gaban Amir. Tsugunawa yayi ya gaida Amir cike da ladabi. Maimakon ya amsa sai dagewa yayi ya kwashe shi da mari, bai farfado ya sake jin saukan wani marin, sai da yayi masa sau biyar sannan ya ɗago ya rungume shi. "Ba ka jin magana, ɗa na, me ya kaika? Yaushe rabon ka da ganin shugaba a wajen sana'a? Sanda na so ka da aikin lawyer ki kayi. Shi lawyer in de yana rike da bakin jakarsa zai yi fashin kuɗin da yan fashi ɗari da bindigogi ba zasu iya samu ba, lokacin ka tsallake ni kace kaji ka gani. Zan ba ka uzuri, amma dole ka bi umurni na a karo na karshe, za ka zauna anan har ka yi aure kuma za ka koma makaranta. "Abin da ka zartar Shine daidai gare ni, ba zan musa maka ba., zan ci gaba maka Biyayya matukar ina da sauran rai a jiki na" yace yana mai kara rusunawa. Take soyayyar sa ya cika masa da yana son mutum mai biyayya kamar yanda yake son mai gaskiya. A titi ya tsinci Adjetey lokacin bai wuce shekara takwas ba, kishiyar uwa ta sako shi gaba da duka duk ta farfasa masa jiki da igiyar rediyo. Tausayin sa kwarai ya shige shi lokacin da ya samu labarin rasuwan mahaifiyarsa da kuma ukuban da ya ke sha hannun kishiyar uwar. Hakan ya sa ya sallama ma mahaifinsa ya ce da shi cikin ɓacin rai "Ai duk kiyayyar da ke tsakanin ka da uwar yaron nan, tun da ta mutu ya ci a birne ta da kiyayyar amma wannan ba ka tsoron ya girma ya zama ajalinka" shiru yayi yana kallon karfin halin Amir, mutumin da bai sani ba har yake da karfin halin bin sa da muguwar fata. "Ka bani shi in baka so, yanzu in kai ma matata shi dama zaman garin nan kewa na damunta" Ya kara yana sakin fuskarsa. Malam kofi Mahaifin Adjetey bai amsa ba iya ya koma cikin gida sai ganin sa yayi da kayan Adjetey su ka yi ya watso musu "Ban taɓa ganin ɗan da zai tona asirin uban sa ba se tsinanne, ka tafi da shi la'ana biye da ku" Ya faɗi a tsiyace "Alhamdulillah! Amma sai ka zo da kukanka kana neman ya dawo gidanka nan ne kuma baka isa ba" Ya fadi yana rike hannun yaron da kaunarsa ke shiga zuciyar sa kaɗan kaɗan. Maimakon ya kai shi gidansa kamar yanda ya alkawura sai ya kai shi makarantar kwana a jihar iko na Nijeriya, nan kuma ya sa masu kula da shi cikin wa'inda hurdan arziki ya haɗa su. Hakan bai hana masa zuwa duba shi ba duk bayan wata uku kuma duk su ka haɗu sai ya tuna masa da mahaifinsa da ce masa "ka dinga sa mahaifiyarka a addu'a ta rasu lokacin da ta fi sonka, sannan mahaifinka Allah kare shi daga sharrin asiri don farraqu aka muku" tun baya iya gane mai kalmomin su ke nufi har ya fahimta. Bayan ya kammala karatun sakandire ya nema masa jami'a anan ne ya ki karatun ya ce sana'a zai yi, Aamir yayi yayi amma Sam bai bi ta kansa ba, wajen neman sana'ar ne ya zaɓi sata don a cewarsa yafi komai kawo kuɗi sannan ya fi komai sauki. Za'a iya cewa ya faɗa harkan a sa'a don ba'a daɗe ba ya gina gida mai kyau a kasar sa na gado a kuma shiyar da aka birne mahaifansa, uban sa kuwa ya zama bai da bukatar komai don dan sa ya kudanye. "Zan tura ka Kasar Masar ka karanto shari'a, don ina ji a jiki na saura Kiris daula ta dawo hannun mu. Sannan zan nema maka aure tare da matar ka za ka wuce" Aamir ya ce kai tsaye bayan ya gama tuna haɗuwar su "Allah kara girma, ina godiya" faɗin Adjetey, a haka ya bar Amir da tunanin yanda zai fara abin. *** Tun bayan dawowarsu yau kwana goma kenan ba su samu damar kebancewa da uwayensu ba sai daren yau, shima ba su shigo gidan a tare bane kamar yanda su ka saba sai kowannensu ya fara da ɗakin mahaifiyarsa. Ummou Hafsah (suna kiran su da Ummou ne don matan shugaba uwaye ne ga al'umma) ta hakince zaune ko da ya shiga, da ido ta yi ma masu mata hidima alamun su ba ta waje don ta daɗe tana so ta kebe da ɗan ta. "Kai na rasa gane maka, Sam ba ka da wayau, shi ya sa mai martaba ke kokonton ɗaura ka a matsayin mai jiran gado duk da kasancewar kai ne jinin sarauta gaba da baya" tace tana aika masa da harara ganin ya fara canza fuska "Ummou kin san dai AbdoulHalim bai da amini sama da ni, son da ya ke min ya sa bai taɓa yafe abin da aka min na ɓacin rai, ni ma ina son ɗan uwa na" yace yana zumburo baki "Toh tunda haka ne ka je wajen Mai girma ka ce ka yafe ma AbdoulHalim sarautan" tace tana gyara zama tana mai jingina a jikin filo da aka sa mata. "Ai ni na fi cancanta in zama Sarki, ke ce fa uwargida, kawai dai ya riga ni zuwa ne amma ai ni ya kamata na zama babba, kuma.. Kai! Ba ma zai iya mulki ba, ni na san rauninsa" yace yana jan tsaki, "Ai naji labarin kyautan kuɗi kake don talakawa su so ka, abin da baka sani ba, babu butulu azzalumi kamar talaka kana masa arziki ne yana neman nakasa ka. Zan tura ka wajen Baffanmu, kawu mahaifi na ne kamar yanda yake ɗan uwar mahaifiyar mai girma. Can yankin zango ka nemi Aamir Al'ansarie shi kaɗai zai cika maka buri AbdoulHaseeb. Ina sane na ce ka karanta military science, don na san za ka koyo dabarun mulki da yaki, shi ma wannan din shawarar Aamir ne. Kuma bakinka alaikum, tun ba shegen nan dan mabarata AbdulBari, wallahi shima kujerar yake hari" a haka ta cigaba da kintsa masa son mulki tare da cusa masa kalolin makirci da zai iya amfani ya ci

Chapter 2 of 14