Share this page
zan fad'a maki Abu d'aya saboda Yaya Muhdeen na d'auke k'afata da zuwa gidan ku,Amma kukayi bina keda Gwaggo har kuka gaji,Amma yanzun tunda ya kusa aure da zaran yayi aure ya tare da matarsa a sabon gidan sa zaku cigaba da ganina a gidan KU,Amma gaskiya yayan ki ya azabtar dani a baya bana k'aunar ma mu had'a inuwa d'aya dashi." Allah sarki bansan meye ya maki ba,kuma baki fad'a Mani ba Amma inaji a jikina kece matar da Yaya na zaiyi rayuwa da ita. *KUYI HAKURI DA WANNAN KILA KUJINI ANJIMA*Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi ( Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa. Page2️⃣1️⃣ "Allah sarki bansan meye yayi maki ba,kuma baki fad'a Mani ba amma inaji a jikina kece matar da yayan mu zaiyi rayuwa da ita. Wani kallo ta watsawa Mufida ba tare da ta sake cewa komai ba ta kanyo ledar da Mufida ta shigo da ita,kayan ta fito dasu wad'anda suka Kai d'inki ranar da Usman ya kad'e ta da mota,duka d'inkin iri d'aya akayi masu tun daga Kan atamfa da material da less d'in duk dinkunan iri d'aya akayi masu, tundaga Kan ankon yinin biki har zuwa na dinner da lunching.harda wani shadda da Mummy ta siye masu su biyu kawai zasuyi ankon , Inteesar taji dad'in ganin kayan sosai tsabar farin ciki rungume Mufida tayi tana godiya.Mufida ta kalle ta tare da zame jikinta daga nata tace, "Nidai sake ni don naga alamar k'arfi ya ishe ki,kuma da kike mani godiya ai ba nice zakiyi wa godiya ba, Mummy ce,don ita ta siye Mana kayan kuma kuma ta biya kud'in d'inkin.Kuma tace tasa akawo mana gyalulluka da takalma jakka wad'anda zasu shiga da kayan." Murmushi Inteesar tayi tana fad'in , "To sai dai kece zaki saka gyale,amma banda ni don kinsan cewa Hijab nake sakawa." Ta janyo less d'in purple colour ne wanda yake da ratsin milk colour tana fad'in, "Kinga Hijab d'in da Mummy ta siye mani last month Milk colour ne dama ban ta'ba Sanya shi ba,kinga zai shiga da less d'in." Harara Mufida ta watsa mata. "Wane irin Hijab kuma?kinsan Allah ba Hijab d'in da zaki saka gyale zamu saka iri d'aya,duk da nasan baki saba ba amma lokacin bikin nan kam dole kiyi hak'uri .Don Wallahi so nake komai namu ba ban banci komai ya kasance iri d'aya zamu saka,Don so nake mu kece raini a bikin nan.Sannan kuma gsky dole ki koma gidanmu da zama har a gama sabgar bikin nan." Da sauri Inteesar ta kalleta da niyyar bud'ar baki tayi magana,amma sai taga Mufida ta had'e fuska ta ajiye Mata kayan ta nufi hanyar fita. Tana jin sanda Mufida ke yiwa Umma magiya akan tabar Inteesar tayi kwana biyu a gidansu kuma Umma ta amince da hakan. cikin farin ciki Mufida tabar gidan. 'Bangaren Muhdeen kuwa Shima sai shirye-shirye yakeyi da abokan sa,dama babban abokinsa d'an uwan sa ne jabir sai kuma abokan su guda biyu Salisu da Bilyaminu,suna ta sabgogin bikin abokin nasu ba kama hannun yaro. Yau ne suka shirya inda zasu had'u da k'awayen Amarya ,don suji abubuwan da suke buk'ata na hidimar biki. Su Hajiya Gwaggo kuwa,gatanan dai ba yabo ba fallasa,ita bata farin ciki da auren kuma bata bak'in ciki.Yayinda bak'i da suka zo daga garuruwa musamman mutanen garin Kontagora da Abuja duk sun iso,k'anwar Dady wato Hajiya Maryam tazo da 'ya'yanta tagwayen'yan mata Azeeza da Azeema suma bazasu wuce sa'annin Mufida da Inteesar ba Asiya ma tazo don bikin yayi dai-dai da hutunta .Hajiya saudat matar Alhaji Adam wato mahaifiyar Jabeer ma ta iso da suran dangi da suke garuruwa duk sun iso. Mufida ce ta janyo tagwayen k'anwar Dady Azeema da Azeeza suka nufi gidansu Inteesar,dama tunda suka iso suke tambayarta ina Inteesar,don sun saba ganin Pic d'inta idan Mifida ta d'ora a status ko a dp don akasari tare suke d'aukar photo,suna kuma k'aunar Inteesar har cikin ransu. 'Bangaren amarya kuwa nan ma shiri sukeyi ba kama hannun yaro, k'awayen ta kuwa sai santin ango sukeyi duk da yawancin su basu ta'ba ganin Muhdeen a zahiri ba sai photo da suke ganin sa, k'awayenta biyu ne kawai suka San Muhdeen a zahiri Jummy da shila, kasancewar sune manyan k'awayenta kuma akasari suna yawan zuwa gidansu Sumayya wata rana su tarar da Muhdeen yazo suna tare,wata rana kuma shine zaizo ya tarar dasu sunso wurinta. Koda Su Mufida da Azeema da Azeeza suka k'arasa gidansu Inteesar sun tarar da ita ta gama wanke kwanukan wanke-wanke ta shiga dasu kichen d'insu dake tsakar gidan tana fitowa suka had'a ido,sallama suka shigo cikin gidan, Inteesar ta amsa masu tare da tunanin ina tasan wad'annan Tagwayen masu matuk'ar kama da juna,take ta tuna cewa a wayar Mufida ce take ganin pic d'in Tagwayen.Murmushi suka sakar Mata yayinda itama ta mayar masu da marttanin Murmushin tace, "Oyoyo manayan bak'i ne mukayi yau a gidan namu haka?" rungume ta sukayi Azeema ta rungumeta ta ta gabanta yayinda Azeeza ta rungumeta ta bayanta tamkar ba yau suka fara ganinta ba.Lokaci d'aya suka saketa fuskokinsu d'auke da murmushi, Azeema tace, "Inteesar mun same ku lafiya?" Cikin farin ciki da jindad'in ganin su ta bata amsa. "Lapiya qalau wallahi,sai dai bansan dawa nake magana cikinku ba Azeeza ce ko Azeema?" Murmushi Mufida tayi kafin ta bata amsar cewa "Kina magana ne da Azeema" "Ayyah Masha Allah sannu da zuwa Azeema" Ta maida dubanta ga Azeeza wacce ke karanta message a wayar ta. "Sannu da zuwa Azeeza fatan kun iso lafiya?" "Lafiya lau wallahi Inteesar,ai muna d'an hutawa kad'an mukazo don muganki" "Aiba Wai saboda ganin ta kad'ai mukazo ba,munzo d'aukarta ne yau zamu tafi da ita gidanmu can zatayi ta kwana sai bayan biki sannan zata dawo gidansu" Murmushi Azeema da Azeeza suka sake tare da cewa " hakan yayi" Inteesar ta fara magana tana fad'in "Ba inda zanje yau sai dai gobe idan za'ayi lunching sai ku biyo tanan mutafi" Harararta Mufida tayi sama da kasa. "Ai baki isa ba,dama na nemi izinin Umma tun wancan ranar,kuma ta amince muje sai bayan biki ki dawo,bayan haka jiya da na shigo na k'ara tuntu'bar ta da maganar tace ba komai har Abba ma ta sanar dashi.Don haka ki tattaro muna d'inkunan bikin mu kizo mu tafi. Shiru Inteesar tayi tana nazari don ba haka taso ba,don kwata-kwata batayi niyar komawa gidan ba,saboda alwashin do da taci Kan cewa ba zata je gidan ba sai bayan Muhdeen yabar gidan,amma yanzun kam ba yadda zatayi don Mufida ta d'aure ta da jijiyoyin jikinta.Mufida ce taja hannun Azeema da Azeeza. "Kuzo mu shiga mu gaida Umma" Binta sukayi harda Inteesar,bakunan su d'auke da sallama,bayan ta amsa masu ne suka shiga,tana kwance kan gadonta dama duk maganar da sukeyi a tsakar gidan a cikin kunnenta yake,zama sukayi kan tabarmar suka gaishe ta cikin girmamawa.Ta amsa masu fuskarta a sake Mufida ta fara magana tana fad'in. "Umma wad'annan 'yan uwa na ne,yaran k'anwar Dady ce,'yan biyu ne Azeema da Azeeza" "To Masha Allah,kunzo lafiya ya hanya?" Dukkan su biyu suka amsa da "Alhamdulillah" "Umma dama munzo zamu tafi da Inteesar" Cewar Mufida yayin da take kallon fuskar Umma, "Badamuwa ku tafi Allah yasa a watse taro lafiya yasanya alkhairi" Ameen suk amsa yayinda Inteesar tayiwa mahifiyarta sallama suka mik'e suka nufi hanyar fita su duka. 'Dakin Inteesar suka shiga inda ta kwaso d'imkunan bikin zata d'aiki kayan sawarta Mufida ta hana Wai tayi amfani da nata,daga nan suka nufi gidansu Mufida. A yammacin ranar bayan suk sunyi wanka sun canza kayan jikin su, Azeema da Azeeza wani material pink colour suka saka riga da siket, yayinda Mufida ta saka doguwar Riga na atamafa, Inteesar kuwa rigar Mufida ta abya ta saka Green wanda Muhdeen ya siyo ma Mufida a Dubai lokacin da suka je siyen kayan lefe,kayan sun burgeshi Matuka amma Sumayya tace bata son kayan,hakan ne yasa ya siyewa K'annen sa Mummy ta raba masu kayan su uku Asiya,Mufida,da kuma Inteesar.Suna zaune akan gado suna suna fira ne Inteesar ta mik'e ta bud'e fridge din d'akin ganin ba ruwa sai lemuka ne yasa Kai tsaye ta fita d'akin Don zuwa kitchen ta d'auko ruwan da zata sha.Dai-dai tana k'ok'arin shiga kitchen d'in Dai-dai Muhdeen ya shigo zai wuce part d'insa Yana rik'e da waya a kunnensa Koda yaga Inteesar zata shiga kitchen a tunananin sa Mufida ce,hakan yasa ya janyo hannunta ba tare da ya kalleta ba yace, "Yauwa Muje ki gyara Mani part d'ina,duk da ba wani iya gyara kikayi ba yafi babu,zanyi manaji hakanan" Bai kalli fuskarta ba yaja hannunta suka nufi part d'insa ,sai da suka shiga falon ya saki hannunta yana cewa, "Ki fara gyara falon" Daga nan ya wuce cikin bedroom d'insa,binsa tayi da kallon mamaki. Daga nan sai ta fara k'ok'arin gyaran falon,cikin k'ank'anen lokaci ta gama gyara falon fess ta kunna turaren wuta take falon ya d'auki k'amshi.Dai-dai lokacin ya fito har wannan lokacin ya fito hannunsa rik'ke da waya yana danne-danne a wayar kallon falon yayi sannan ya maida idonsa akan wayar yace, "Dama kin iya gyara waje iskancine kesa idan an sakaki bakiyi dakyau sai yau da kikaga damako?To shiga ciki ki gyara bedroom d'in" Har yakai K'arshen maganar bai d'aga ido ya kalleta ba.kwatsam sai yaji saukar muryarta a kunnensa sa tana cewa, "Nikam wallahi bazan shiga ba" Da sauri ya d'ago Kai yana kallonta da mamaki,domin shi a zatosa Mufidace ganin kayan da ya siyo Mata a Dubai ne a jikin Inteesar yasa yayi tunanin Mufida ce a she ba ita bace Inteesar ce tasa kayan Mufida.Had'e fuska yayi yana cewa "Kee ubanwa ya kawoki d'akina?" Kallon mamaki take masa don gani take ya raina mata hankali. "Tukunna ma dai ba kince idan na sake ganinki a gidan nan duk abunda naga dama nayi maki ba?ke ga mara kunya fitsararriya ko?to yau zakiga kuwa abunda zanyi maki" Gaban Inteesar ne ya fad'i ganin ya nufota gadan-gadan fuskar nan a murtuk'e ba sassauci a tare da shi.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi ( Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa. *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. Page2️⃣2️⃣ Gaban Inteesar ne ya fad'i ganin ya nufota gadan-gadan fuskar nan a murtuk'e ba sassauci a tare da shi. Tattare k'asar rigarta tayi da nufin guduwa,kunsan abu ga dogon mutum ai taku biyu yayi ya isa gare ta, kafin ta ankare ganinsa kawai tayi a gabanta yayi mata dirar mikiya.Hannayenta duka biyu yasa ya murd'e mata hannayenta tare da maidasu baya,hakan yasa ta bud'e baki ta saki k'arar azaba da sauri yasa hannunsa d'aya ya toshe mata bakii, yayin da d'aya hannun yana rik'e hannayenta da ya murd'e.Girgiza kai kawai take yi na azaba yayinda Idanuwanta suke tsiyayar da hawaye.girgiza kai taci gaba da yi idanunta na cigaba da zubar da hawaye.Girgiza masa Kai tacigaba da yi amma ko a jikinsa baiji tausayinta ba. Suna cikin wannan halin ne Jabeer ya turo k'ofar falon ya shigo,turus ya tsaya yana kallon Muhdeen cikin tsananin mamaki ya ce "Meye haka?wanna wani irin rashin imani ne?" K'arasawa yayi ya cire hannun Muhdeen daga rik'on da yayi wa Inteesar.yana sakinta ta zube a wurin ta samu damar fitar da kukan zucin da takey.Jabeer harara ya watsa masa . "Yanzun meye kake aikatawa haka? Zaka kama 'yar mutane kana azabtar da ita akan meye?" "Ba azabtar da ita nayi ba tarbiya nake koya mata." "Eh k'warai kuwa tarbiyya kake koya mata irin tarbiyuar da kake koyawa Asiya da Mufida,idan Asiya da Mufida sukayiwa laifi haka kake ladabtar dasu?" Ya k'arasa maganar yayin da yake kallon Muhdeen. "Ai idan sune basasu yi mani irin abunda yarinyar nan tayi Mani ba ballantana har na d'auki irin wannan hukuncin akan su." Girgiza kai Jabeer yayi tare da ce wa, "Duk da bansan me tayi maka ba kuma nansan alak'ar dake tsakanin ku ba,amma da dukkan alamu yarinyar nan bata da rashin tarbiyya ko rashin kunya.Ni nasan halinka fa idan ka d'aurawa mutum karan tsana,wata kila ka kure ta ne shiyasa har takaiga tayi maka haka." Don't tell me that,how dare you gaban yarinya kana gaya mun maganganu tare da bani laifi?salon ta k'ara raina ni ko?." Ba tare da Jabeer ya sake wata magana ba ya durk'usa gaban Inteesar dake ta k'ok'arin mik'ar da hannayen ta amma ta kasa,har lokacin kuka take,cikin tausayawa ya kalleta ya ce, "Sannu ko?" Kai ta gyad'a masa alamun yauwa ba tare da ta yi magana ba. "Cikin tausasawa ya ce, "Me kikayi masa ne?" Cikin muryar kuk ta fara magana. "Nidai haka nan kawai ya tsaneni banyi masa laifin komai ba, shiyasa ma nace bazan sake zuwa gidan nan ba sai yayi aure yabar gidan su Mufida suka matsa nazo." Cikin tausasawa ya girgiza kai. "Kenan ke k'awar Mufida ce?" Kai ta jinjina masa alamar eh,da ya ke shi Jabeer baisan Inteesar ba kasancewar duk lokacin da yake zuwa bayan sallar isaha'i ne,kuma lokacin Inteesar ta riga tabar gidan. "To amma me kikazo yi a d'akin sa?" "Shi ne ya janyoni wai nazo nayi masa gyaran falo" Kai Jabeer ya jinjina. "Okay.yanzun ki tashi ki tafi,sannan ina mai matuk'ar baki hak'uri a madadinsa" Tashi ta yi dak'yar ta dafa hannayen ta mik'e tsaye, ta nufi hanyar fita ta fice Jabeer yabi ta da kallon tausayi.Gwaggo ne ke zaune a falo su day wasu Mata k'awayen Mummy su uku,ganin Inteesar ta fito daga part d'in Muhdeen idanunta sunyi ja alamun kuka yasa ta mik'e dakyar,ta nufi Inteesar ta ce, "Subhanallahi 'yar albarka me ya same ki?me kikayi je yi d'akin Muhammadu?me yayi maki? " Murmushin k'arfin hali tayi tare da ce wa, "Bakomai Gwaggo kada ki damu" Ta k'arasa maganar tana mai nufar k'ofar kitchen,bayan ta shiga kitchen d'in fridge ta nufa ta d'auko goran robar ruwa tare da tsiyayawa a kofi tasha.Sai da ta k'ara koge fuskar ta inda hawaye ya gangaro da bayan yatsunta sannan ta nufi da'akin Mufida. Da sallama d'auke a bakinta ta shiga,kallo d'aya Mufida tayi mata da sauri ta mi'ke ta isa gare ta tare da dafa kafad'arta. "Inteesar lafiya kuwa me ya same ki naga idon ki alamun kinsha kuke?" Murmushin k'arfin hali tayi tana kallon Mufida ta ce, "Kada ki damu kaina ne ke Mani ciwo yanzun zan d'an kwanta,idan na tashi zuwa anjima zai sake ni" Azeeza ce ta ce. Ikon Allah daga fitar ki zuwa kisha ruwa shiru baki dawo ba sai yanzun kika shigo kanki na ciwo.Dama kina kukan ciwo ne kamar k'aramar yarinya?" Ta k'arasa maganar cikin yanyin zolaya.Azeema ce ta d'aura da ce wa. Ni da naga shiru-shiru Bata dawo ba na tambayi Mufida cewa ga Inteesar shiru,take cewa kila ta tsaya wajen mutumiyarta Gwaggo" Mufida ta girgiza Kai tare da cewa, "Nidai nasan bakiyin kukan ciwo sai dai idan 'boye mana zakiyi" Asiya dake tsaye bakin k'kofar hannunta na rik'e da handle d'in k'ofa ce tayi tsuki tare da fad'in "Amma kuma da naci kuke,tace bakomai ta a tafi a hakan mana haba da Allah.yauwa ni ba wannan ya kawoni ba,wace ce ta d'auki chargern wayata? Azeeza ta ce Nice Aunty Asiya na mance da tawa ce,na shiga ban ganki ba shine na d'auko" Ta k'arasa maganar tana nuna socket d'in da tasaka charging. "Okay badamuwa idan kin gama ki kawo mani" Daga nan ta juya ta fice, Inteesar kwanciya tayi akan gadon ta juya masu baya. 'Bangaren Gwaggo kuwa ganin Inteesar ta fito 'bangaren Muhdeen Tana kuka yasa ta nufi 'bangaren nasa.ko sallama batayi ba ta tura k'ofar ta shiga. "To shugaban mugaye na Africa,uban me kayiwa 'yar mutane ta fito tana kuka?" Shiru yayi bai kalleta ballantana ya amsa Mata,bada Kai nake magana ba ka yi mani shiru?nasan dai yarinyar nan bazata ta'ba aikata wani abu da zaisa kayi mata azaba ba,sai dai idan kuskure aka samu,haka ranar ka akan ta watsa maka yayu a rashin sani ka kamata kahau yarfa mata maruka kamar Allah ne ya aiko ka,yanzun ma ka kamata kana jibga to a kunnen ubanka d'an banza mai k'irar yahudawa." Ba tare da ya kalleta ba ya fara magana. "A halin yanzun Ina cikin farin ciki,saboda haka kada ki ruguza farin mani cikin da nake ciki.karki manta nifa ango ne" Harararsa tayi ta ce, Dalla rufe mani baki ina angon yake,sai dai muna angon don ni banga cikakken ango anan ba,wata kila idan zakayi auren da ake kira aure zan ganka cikakken ango Amma yanzun angogo na gani.Dan zaka auri wananna tambad'ad'd'yar yarinyar zaka kira kanka ango. Take ya murtuk'e fuskar sa don ya tsani a fad'i kalma mara dad'i akan Sumayyarsa. Zata bud'e baki da niyyar tayi magana,yayi saurin dakatar da ita da fad'in. "Gwaggo a halin yanzun kin riga da kin 'bata mani rai saboda haka kada ki tunzurani." Ri'ke baki tayi tana kallosa. Muhammadu duka na za ka yi ko me?na tunzura kan d'in,ko uwarka da ubanka za su ce kada na tunzura su ballantana kai.?" Jabeer ne ya k'arasa gaban Gwaggo cikin sigar rarrashi ya fara magana. "Allah ya huci zuciyarki Gwaggo kiyi hak'uri ki tafi kada ki biyewa Muhdeen don Allah kinsan halinsa." "Halinsa na banza ba,yanzun ka fad'a mani gaskiya me yayiwa yarinyar nan?"don nasan ba abunda zatayi masa bak'ar zuciyarsa ce da mugun halinsa ne kawai." Ahljiyar zuciya Jabeer ya sauke tare da cewa, Gwaggo idan har nace ga abunda tayi masa nayi k'arya,nadai zo na tarar ya murd'e mata hannaye ya lan'kwasa mata su baya tare da toshe Mata baki wallahi iya abunda na sani kenan." Jinjina Kai tayi "To Allah yayi maka Albarka ya sauke matar ka lafiya ta Haifa maka d'anka namiji, mai sanin darajar mutane da neman albarka irinka." Murmushi yayi tare da cewa, "Ameen Gwaggo." "Ni banma tambayeka ya jikin matar taka ba ko?anya ma zata iya zuwa bikin nan kuwa?" Girgiza kai Jabeer yayi yana dariya ya ce, "Ba zata iya zuwa ba Gwaggo saboda cikin nan yana wahalar da ita." Kai ta jinjina tare da ake tambayar sa. "Cikin nan nata wata nawa ne?" "Wata biyar kenan Gwaggo" "Auren KU watanni biyar kenan ko" Kai ta jinjina tana dariya ta ce, "Dakyau namijin gaske,ashe dai jikan nawa ba rago bane,aure wata biyar ciki ma wata biyar lokacin da kukayi watanni tara da aure lokacin cikinta watanni tara sai haihuwa kenan. Wato baka da wasa kana jefa k'wallo kenan ta shige raga lallai yaron nan ka cika namiji ba lusari bane kai.Ai dam..." Muhdeen ne ya katseta ta hanyar cewa. Ba'a irin wad'annan maganganun a gaba na,don na dad'e da sanin cewa baki san alkunya ba." Kallon shek'ek'e Gwaggo tayi masa ta ce, "Ubanwa yace dole sai ka saurare mu ka fita mana." "Kuzo har cikin d'aki na sannan ku ce na fita? ai ba zamanin mulkin mallaka muke ciki ba.Koda yake dama ke nasan haka kike shine ma da ya biye maki." Juyawa yayi ya kalli Jabeer ya nuna sa da hannu ya ce, "Kai baka san waye Gwaggo ba ko? shiyasa har take tambayarka sirrin gidanka kake fad'a mata,sai ta dinga terere da sirrin gidan ka.Idan ka biye Mata cewa zatayi ka fad'a mata me ya faru a first night d'in ku,kaga jata ku tafi can d'akinta ku karasa zancen ku ba'a nan ba." ya k'arasa maganar yana shigewa bedroom.Ta bishi da harara tana cewa, "Ai sai dai ka shiga ciki,kuma saura kuma naga naka k'wazon jarumi ne ko kuma lusari." Daga Nan ta fice daga d'akin tana sababi,Kai tsaye d'akin Mufida ta nufa nufa ganin Inteesar kwance tana barci yasa ta fita ko gaisuwar da su Azeema suke mata Bata amsa ba ta fice. Washe gari gidan ya cika da jama'a 'yan uwa da abokan arziki ana ta shagulan biki.inda kowa yake cin abincin da ransa yake so yasa abunda ransa ke so. Da misalin karfe hud'u na yamma ana ta Shirin zuwa reception kowa ya saka ankon material d'in da aka fitar saboda reception d'in kowacce tana shiga mitoci ana waucewa dasu.Su Inteesar kuwa suna cikin d'akin Mufida su hud'u. Mufida, Inteesar,Azeema da Azeeza.Sunci anko inda Azeeza ta tsantsara masu kwalliya sunyi matuk'ar kyawu sosai sai shek'i da k'amshi suke inda suka inda suka dinga fama da Inteesar akan ta dage lallai dole sai ta saka hijabi ita kuma ta dage,dakyar suka shawo kanta ta har ta amince zata saka gyalen.Gashi kayan sun bayyana tsantsar kyawun surar jikinta kowacce ta d'auki wayarta da posa d'inta suka fito. Koda suka k'araso harabar gidan duka motocin gidan ba ko d'aya duk an tafi dasu tundaga Kan motar Mummy har Motocin Muhdeen ba ko d'aya .Domin duk an tafi wajen reception motar Jabeer kawai suka gani sai motar Asiya wacce fitowarta kenan daga cikin gidan ita da k'awayenta guda biyu,tana k'arasowa ta kallesu tace, "Au kuma baku tafi ba?" Mufida ce ta kalleta tace, "Wallahi bamu tafi ba tunda gaki sai mu biki" girgiza Kai tayi tare da cewa, "Sai dai dukkanku motar ba zata d'uke mu duka ba,don ga friends d'ina guda biyu sannan ga ku hud'u kinga sai dai mutum d'aya ta hak'ura ta hau keke napep" Mufida ta kallesu ta ce, "Badamuwa ni zan hau napep ku ku shiga motar." Kai Asiya ta girgiza "A'a sai dai Inteesar ta hau napep don bazaiyuwu ba kibar su Azeeza baku tare." "Gaskiya Inteesar ba zata hau napep ba." 'Daga kafada Asiya tayi alamun I don't care d'innan sannan ta kalli Mufida ta ce, "Shikenan sai ku tafi daga ke har ita kuhau napep d'in." Dai -dai lokacin Muhdeen ya fito tare da Jabeer,Jin abunda suke fad'a yasa Jabeer tambayarsu. "Wace ce zata shiga napep?" Mufida ta ce "Motar ce bazata d'auke mu duka ba saura mutum d'aya." Idanun Jabeer ne suka akan Inteesar ya zuba Mata idanu ba ko k'yaftawa,gaba d'aya ta tafi da hankalin sa ya kasa d'auke idanunsa akan kyakkywan surar jikinta.Muhdeen ya lura da kallon da Jabeer ke mata hakan yasa ya buge masa hannu Wanda yasa shi dawowa hayyacinsa.Muhdeen ya baibi ta kansa ba ya wuce ya shige bayan motar ya zauna. Jabeer ya kalli Inteesar ya ce, "Inteesar kizo mu tafi a motata" Kallon Mufida tayi,sai Mufida tayi mata alamun taje ta shiga.Hakan yasa tabi baynsa inda ya bud'e Mata marfin gabar motar ta shiga ta zauna.Mufida kuwa suka shiga na Asiya.Cikin sanyi murya ta ce, "Nagode" Murmushi Jabeer ya sakar mata tare da cewa "Bakomai Inteesar." Muhdeen ne ya had'e fusaka ya ce, "Motar da zaka d'auki Amarya da Ango ne zaka d'auki wannan kucakar yarinyar to aiko sai dai ta fita." Jabeer ne yayi masa irin kallon nan na kayi kad'an sannan yace, "Wallahi bazata fita daga motar Nan ba sai dai Kai ka fita." 09065327995Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi ( Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa. *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. Page2️⃣3️⃣ "Wallahi ba zata fita daga motar nan ba sai dai Kai ka fita." Kallon mamaki Muhdeen yayiwa Jabeer don Bai ta'ba tunananin jin wannan maganar daga bakin Jabeer ba. "Yanzun akan wannan yarinyar kake fad'a Mani magana?don kaga friends d'ina sau d'auki motacina zasuyi amfani dashi basoda nace zanbi naka kai ka isa ka fad'a mani mota?kaima kasan motocin da nake hawa sunfi naka, ballantana ka fad'a Mani magana" Murmushi Jabeer ya ce "Bakomai ai zakaranka rak'uminka,kardai ka 'bata ranka a banza a wofi don yanzun zamuje mu d'auko maka amaryarka tana zaune gefenka yayin da ni kuma Inteesar tana zaune a gefe na." Banza dashi Muhdeen yayi bai tanka masa ba, yayinda Jabeer kan d'an ja Inteesar da fira,duk da ba wani biyeshi yakeyi ba idan daga eh sai A'a, a hakan har suka k'araso k'ofar gidan su Sumayya amarya nan suka tarar da d'aya daga cikin motocin Muhdeen a k'ofar Get d'in gidan,wanda abokin ango Bilyaminu ne ya tukota don d'aukar 'kawayen amarya.Bayan ansaka amarya cikin motar da ango ke ciki ne sauran k'awayenta suka shiga motar da

Chapter 8 of 38