bugu kowa ba motar ce dai ta kufce masa take da daki wata bishiya."
Mummy ce ƙwalla ya cika mata ido ta kalli Jabeer ta ce,
"Yanzun wani hali yake ciki."
"Da sauƙi za'a ce amma yana can baisan wa ke kansa ba"
Inteesar ce ta fashe da kuka ganin cewa duk alhakin faruwar abun akanta yake ita ce silar komai da ya same shi,Jabeer ne ya kalli hannunta dake zubar da jini ya nufi ɗakin Muhdeen ya fito da kayan aiki yazo yayi mata treatment na hannunta sannan ya kalli Gwaggo ya ce,
"Dawa zamuje ne? tun ina asibitin na kira Dady na sanar da shi."
Mummy ce ta kalli Inteesar ta ce,
"Daughter ki tsaya muje mu dawo ke da Mufida ku tsaya a gida ita tana barci."
Kai Inteesar ta girgiza tana kuka ta ce,
"Mummy wallahi bazan iya tsaya ba zan biku mu tafi domin naga halin da yake ciki."
Tana magana tana kuka, kafin ma Mummy tayi magana har ta shiga ɗauki ta ɗauko hijabinta don zuwa Asibitin, dole suka ƙyale ta suka tafi da ita inda aka bar Mufida tana kwance a ɗakinta tana barci.
Ko a cikin motar ma kuka take Jabeer dake driving Ya ɗan juyo ya kalle ta ya ce,
"Please kibar kukan nan haka insha Allahu zai warware anyi masa alluran barci ne, saboda yaƙi yarda a duba sa da kyau ga rauni a jikinsa amma amma sai cewa yake a barshi ya tafi wanda hakan yasa dole muka yi masa allurar."
Kasancewar Mummy ce a gaba gefen Jabeer Gwaggo da Inteesar suna baya, Gwaggo ce ta kalli Inteesar ta ce,
"Ke nifa bani son damuwa, duk kinbi kin cikawa mutane kunne da hayaniyar kuka."
Jabeer ne ya ce,
"Ba dole tayi kuka ba mijinta na cikin wani hali."
Taɓa baki tayi tare da cewa
"Ni ban gane kukan da take yi ba, mijin da ba wai sonsa take ba neye na ɗaga hankali? sai da na tambaye ta tana sonsa zata koma gidansa ta ce bata sonsa ba zata koma ba, to yanzun daga jin yayi hatsari tabi ta rikice har tana yanke hannunta da wuƙa bata damu da ciwon hannunta ba ta shi kawai take, ni gaba ɗaya na kasa gane inda yarinyar nan ta dosa, wato ke sawun keke ce ba'a gane gabanki ba'a gane bayanki, sonsa kike ko tausayin halin da yake ciki ne ban sani ba."
Tura baki tayi tace,
"Nifa kwai tausayinsa nake ji, gani nake nice silar komai shiyasa nake kuka ba don komai ba, kuma ko waye zan iya masa kuka indai ya shiga wani hali saboda ni."
Daga nan ba wanda ya sake magana har suka ƙarasa Asibitin, bayan Jabeer yayi parking suka fito suka bi bayansa.
*Daga alk'alamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*DON NEMAN ƘARIN BAYANI*
09065327995
Love you oll😍😘
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Idan kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na buɗe wannan duk abu ɗaya ne, sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group don ko kinshiga idan baki comments zan fitar da ke ne.
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinin na ba
*SANARWAR*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi da cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce Ni bada niyyar yin hakan nayi ba, rashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page6️⃣9️⃣
Daga nan ba wanda ya sake magana har suka ƙarasa Asibitin, bayan Jabeer yayi parking suka fito suka bi bayansa.
Yana kwance yana barci sai rauni da ya ji a kansa, Jabeer ne ya turo ƙofar sai Inteesar da ke bayansa sai Mummy da Gwaggo, a guje Inteesar ta ƙarasa jikin gadon bata san lokacin da ta riƙo hannunsa ba tana kuka, Jabeer ne ya kalle ta ya ce,
"Kada ki tayar da shi ana son ya samu isashshen barci kada ki damu zai tashi, zuba masa ido tayi tana tuna lokacin da ya riƙe ƙasar rigarta yana roƙonta da cewa, Inteesar kada ki rabu dani wallahi yanzun sonki nakeyi da gaskiya, bazan cutar da ke ba tunda nake a rayuwata ban taɓa jin tsananin soyayyar wata ƴa mace kamar yadda nake jinki a cikin zuciya ta ba, kada ku rabu dani ki bini muje mu gina sabuwar rayuwa mai cike da jin daɗi da kwanciyar hankali.
Haka ta dinga tuna kalamansa da a cikin zuciyarta tana jin tausayinsa har cikin ranta.
Mummy kuwa ita kaɗai tasan yadda take ji a zuciyarta tana tausayin halin da ya ke ciki akan mace, dan yanzun da daina jin haushinsa akan ƙuntatawar da yayiwa Inteesar a baya, dan yanzun ta fahimci cewa yayi nadama.
Ɓangaren Gwaggo ma bata ji daɗin faruwar hakan ba duk da ita ce ta tunzura shi, amma tayi haka ne dan ta ƙwayar wa Inteesar ƴancinta a wajensa Sakamakon azabar da uƙuba da ya nuna mata a gidansa, duk da ya sauya amma yana da kyau ya gane kuskure da ya aikata kuma yasan mahimmancin da take da shi a wajensa.
Nan dai Jabeer ya kwantar masu da hankali sannan ya nufi office ɗinsa, zama yayi ya ɗauki wayarsa tare da cewa
"Bari na kira abokanmu na sanar da su halin da abokinsu yake ciki."
Bayan yayi dialing number Salisu ya sanar da shi ne, sai ya lalubo ma Biliyaminu shima ya kira sa ya sanar da shi sannan ya lalubo number Bashir shima ya danna masa kira.
Kwance suke a ɗakin hotel ɗin ba kaya a jikinsu suna kulluɓe cikin bargo, ta kwantar da kanta a ƙirjinsa kallonta yayi yana murmushi ya ce,
"Yakamata ki tashi kiyi wanka ki koma gida kafin mijinki ya dawo ya tarar baki gida."
Yamutshe fuska tayi tare da cewa
"Ba yanzun ba don na gaji wallahi sai na huta"
Wayarsa ce tayi ringing ya duba tare ɗagawa ya ƙara a kunne da ya ce,
"Hello Jabeer yau ka tuno da ni ne?"
Ajiyar zuciya Jabeer ya sauke tare da cewa
"Abokinka fa ba lafiya yayi accident?"
"Subhanallahi wane daga ciki Muhdeen ki Salisu ko..."
Kafin yakai ƙarsen zancensa ne yaji muryar Jabeer na cewa
"Muhdeen"
Ita dake kwance a saman ƙirjinsa kasancewar ta ji muryar Jabeer cikin wayan ya ambaci Muhdeen da sauri ta miƙe zaune tare da cewa
"Na shiga uku nala..."
Kafin takai ƙarshen zancenta Bashir yayi saurin rufe mata baki da hannunsa ya ce,
"Asibitinsa yake kwance?"
"Eh"
Ya bashi amsa a taƙaice daga nan ya aje wayar.
Bashir ne ya kalli Sumayya sannan ya cire hannunsa daga bakinta ya ce,
"Meye haka daga magana kina neman tona muna asiri idan ya gane muryarki fa?"
"Kasan yadda naji ne?mijina fa aka ce yayi accident ya bazan ruɗe ba?"
"Bari nayi sauri na tafi Asibitin"
Ta ƙarasa magana tana sauka daga kan gadon, kallonta yayi tare da cewa
Tunda basu kira ki suna sanar da ke ba yanzun idan kika je aka tambaye ki waya sanar dake me zaki ce? ni zaki ce ?idan suka tambaye ki ina muka haɗu na sanar da ke fa?
Sai a lokacin ta tuna ta dawo ta ɗauki wayoyinta tare da kunna su ta ce,
"Na mance na kashe wayoyi na duka kila ma ya kira ni bai samu ba"
Tana kunnah wayar kuwa sai ga kiran Jabeer ya shigo kamar jira yake da sauri ta ɗaga tare da karawa kunnenta duk da cewar da wayar Muhdeen ya kira ta don baida number ta, ko ranar da ta kira shi ya roƙi Muhdeen ya barta akan ta cigaba da zama a gidansa baiyi served number ta ba, kallon Bashir tayi da ya zuba mata ido ta ce,
"Da number Mijina ya kira Ni wayar na hannunsa ne."
Ɗagawa tayi tare da cewa
"Hello my sweet"
Da sauri Jabeer ya ce
"Bashi bane bani da number ki ne yasa na duba wayarsa na kira ki."
"To Allah dai yasa lafiya da naga ka Kira da wayarsa hankali manya tashi."
"Kina ina ne?"
Gabanta ne ya faɗi kada dai ace yahe gidansu bai gabata bane, kafin tayi magana ta ji ya ce,
"Kizo Asibitinsa muna nan"
"Lafiya me ya faru da shi ne?"
"Kada ki damu kizo kawai"
Daga nan ya katse kiran yana girgiza kai.
Suna nan zaune a ɗakin Dady ya shigo don duba halin da Muhdeen ke ciki, daga nan ya je office na Jabeer inda ya nemi jin ƙarin bayani daga bakinsa nan Jabeer ya kwantar masa da hankali cewa ba komai zai warware insha Allahu, sai dai akwai damuwa. zuciyarsa kuma samuwar akan Inteesar ce don haka ya dinga sambatu yana kiran sunanta kafin barcin yaɗauke sa, nan Jabeer ya ƙara jaddada wa Dady cewa su basa matarsa don gaskiya Muhdeen yabcanza, yanzun son Inteesar yakeyi da gaskiya ya kamu da matsancin soyayyar Inteesar, bazai taɓa cutar da ita ba ko ya bari wani ya cutar da ita, nan dai ya cigaba da masa bayani kuma Dady ya gamsu da bayanin Jabeer sannan sukayi sallama ya fita.
Suna nan zaune a ɗakin sa aka kwantar da Muhdeen bayan tafiyar Dady sai ga Sumayya ta faɗo ɗakin kamar wacce aka jefo, ganin su Mummy da Gwaggo yasa ta shan jinin jikinta kunya ce ta dabaibaye ta, don tunda ta auri Muhdeen bata taɓa zuwa ta gaida su ba, lokacin da idonta suka sauka akan na Inteesar sai da gabanta ya tsananta faɗuwa, taji ƙiyayyar da take wa Inteesar ce ta dawo sabuwa a cikin zuciyarta, musamman da taga idanunta alamar tayi kuka kuma tana riƙe da hannun Muhdeen ta zauna a gefen gadon, take sai taji kishin mijinta ya taso mata, ga kuma kunya tana ji na abunda ta aikata na yunƙurin kashe Inteesar kallon Gwaggo tayi ta ce,
"Ina wuni Gwaggo?"
Kauda kai Gwaggo tayi tare da cewa
"Bari na fita ɗakin nan kada Allah ya tashi turo ma wata bala'i ya shafe ni."
Ta ƙara maganar tana kallon Mummy da Mufida tana masu alamar da suzo su tafi, Sumayya ta ƙalli Mummya ta ce,
"Ina wuni Mummy?"
Ba yabo ba fallasa ta amsa mata da
"Lafiya lau ya gidan?"
"Alhamdulillah"
Gwaggo ce tayi saurin sawa gadon taja hannun Inteesar suka tafi zuwa waje, wani wuri suka samu suka zauna saman kujeru dake ajiye a wajen.
A can cikin ɗakin kuwa turo ƙofar akayi tare da yin sallama, Salisu ne da Biliyaminu, sai Bashir, durƙusawa sukayi suka gaida Mummy tare da tamabar ta ya mai kiki, ta amsa da Alhamdulillah sannan Sumayya ta gaishe su suka amsa mata inda Bashir ya kashe mata ido ɗaya da sauri ta kauda kanta daga kallon sa don ta lura Bashir ba kunya ne da shi ba, yanzun sai ya nemi tona masu asiri bayan 'yan mintuna sai ga Gwaggo da Inteesar sun shigo ɗakin, yayin da Bashir ya kafe Inteesar da wani kallon ƙurilla ba wanda ya lura da hakan sai Sumayya da idanunta ke kansa, gyaran murya tayi ya kalle ta ta galla masa harara sosai kai yayi tare da gaida Gwaggo ta amsa suma sauran suka gaishe ta amsa masu.
Bayan kamar mintuna goma ne Bashir ya miƙe ya ce
"Bari naje na ɗauko abu a mota."
"Salisu ya ce
"Okay"
Yana ƙoƙarin fita ne sukayi kiciɓis da Jabeer suka ƙara gaisawa sukayi sannan sannan ya fice, bayan fitar da da mintuna biyar Sumayya ta tashi ta fice,
Yana zaune a cikin motarsa gani kawai yayi an buɗe murfin motar kafin yayi magana har ta shigo ta rufe murfin motar, da mamaki ya kalle ta ya ce,
"Sumy! lafiya kuwa?"
Kauda kai tayi tana taunar cingum ta ce
"Ƙalau"
"To me zaisa ki biyo NI har cikin mota idan wani ya hannu fa akwai matsala."
"Yaushe kasan yarinyar can da naga kana binta da wani mayataccen kallo?"
"Wata yarinya?"
Kauda kai tayi bata ce komai ba sai a lokacin ya tuna cewa lokacin da yake kallon Inteesar Sumayya ce kaɗai ta kula da hakan, dan haka ya ce,
"Oh Inteesar?"
Taɓe baki tayi ba tare da ta ce komai ba
"Ai Inteesar ta daɗe da shiga raina, ranar da akayi reception na aurenki da Muhdeen ne na fara ganinta ita da Jabeer wai daga tashi reception matarsa ta kira sa tana son agwaluma suka kai mata, to bayan sun dawo ne na ganta har na cewa Jabeer zan aure ta don banga maccen da ta haɗa abubuwan da nake so kamar Inteesar ba, gani na na biyu da ita munje gidan baki nan lokacin kina London tana amarya munje cin girkin amarya, munta ta santin daɗin girkinta sai Salisu ke bani labarin wai da kike amarya sunzo cin girkin ki wai kinyi masu daɗɗaɗan girki irin taki ba, wai taki ta musamman ne basu taɓa cin girki mai daɗinsa ba, sanin cewa tsokanarta yake yasa ta ɗaga hannayenta biyu tana kai masa dukan wasa riƙe hannunta yayi, kamar daga sama suka ji ana knocking glass ɗin motar da sauri suka juya cikin fargaba dan ganin waye.
*Daga alk'alamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*DIN NEMAN ƘARIN BAYANI*
09065327995
Love u oll😍😘
Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Idan har kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na buɗe wannan duk abu ɗaya ne, sannan idan kisan cewa bazakyi comments ba kada ki shigar mani group, don ko kin shiga idan baki comments zan fitar da ke ne.
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*SANARWA*
Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page7️⃣0️⃣
Kamar daga sama suka ji ana knocking glass ɗin motar, da sauri suka juya cikin fargaba dan ganin waye.
Sauke glass ɗin motar yayi sai yaga ɗaya daga cikin security na Asibitin ne ya a tsaye, kallonsa Bashir yayi tare da cewa
"Lafiya?"
"Yallaɓai dan Allah ka gayara parking ɗin motarka."
Jinjina kai yayi tare da cewa
"Okay"
Sai a lokacin ya lura da inda yayi parking ashe ya a hanaya ne, kuma motocin da ke gabansa dole sai ya bada hanya kafin su wuce, don haka ya gyara parking ɗin motar sannan ya juya ya kalli Sumayya.
"Waya ta na manta a motar shine na fito ɗauka yakamata ki fita ki koma kiyi jinyar mijinki ko?"
"Ni wallahi tunda na ƙyallara ido naga yarinyar nan a Asibitin nan sai naji gaba ɗaya raina ya ɓaci, musamman da ta haɗu da waccan jarababbiyar tsohuwar Gwaggo, Wallahi na tsane su a rayuwa ta."
"Me sukayi maku da kika tsane su?"
Yamutshe fuska tayi tare da cewa
"Ita wannan tsohuwar tun lokacin da na fahimci baya ƙauna ta ne, ita kuma waccan yarinyar haka nan kawai tun ranar da na fara ganinta a gidansu Muhdeen na tsane ta, Ni dama na tsani kyakkyawar mace,idan har naga mace ta haɗu ta ko ina bata da cikas wallahi sai naji na tsane ta musamman idan na fahimci ta fini ko akan hanya ne bana son ganinta ballantana wannan da ta aure mani miji."
Dariya Bashir yake ta ƙyaƙyatawa har Sumayya ta fara jin haushinsa, dan haka ta buɗe murfin motar ta fice ranta a ɓace.
Komawa tayi ɗakin ta tarar Salisu da Biliyaminu ne sai Mummy, zama tayi gefen gadon da Muhdeen yake tana cewa
"Allah sarki Allah ya tasarmun da kai ya baka lafiya."
Ta ƙarasa maganar idanunta na tara ƙwalla, gaba ɗayansu suka amsa mata da Ameen inda Mummy ta ce,
"Dan Allah ku daina masa kuka haka, jikinsa fa da sauƙi insha Allahu zai miƙe kamar baiyi ba."
Kuka ta sake rusawa tana cewa
"Mummy ta yaya hankali na zai kwanta? mijina yana cikin wani hali l."
A'a kinga wannan ba abunda tada hankali bane addu'a kawai zamuyi masa Allah zai bashi lafiya, nan dai Umma ta dinga kwantar mata da hankali akan ta cire samuwar dake cikin zuciyarta, ana haka ne Bashir ya shigo ko kallon inda yake bata yi ba, daga bisani suka fita zuwa wajen Jabeer, ɗakin ya rage daga Mummy sai Inteesar.
Shiyoyin sallar magariba ne, Mufida ta shigo hannunta ɗauke da basket da aka jera kayan abinci a ciki.
"Assalamu alaikum"
Mummy da Sumayya suka amsa mata
"Wa'alaiki salam"
"Mummy ya jikinsa?"
"Jiki da sauƙi Mufida"
"Allah ya bashi lafiya."
Suka amsa da Ameen, Mummy ce ta kalle ta ta ce,
"Baki ga Auntynki bace?"
Yamutshe fuska tayi tare da cewa
"Mummy ni banga Aunty na anan ba gaskiya."
Kallon gargaɗi Mummy tayi mata ba tare da ta ce komai ba, sanin dalilin kallon ne yasa ta kalli Sumayya murya ciki ciki ta ce,
"Ina wuni?"
Itama kanta Sumayya taji zafin abinda Mufida tayi mata, amma sai ta dake ta nuna hakan bai dame ta ba kasancewar a gaban Mummy suke,
"Lafiya lau Mufida ya kike?
Kauda kanta gefe tayi tare da cewa
"Lafiya"
Dan tunda suka je gidan Muhdeen da Gwaggo lokacin Sumayya na Amarya har tayiwa Gwaggo rashin kunya, tun daga wannan lokacin Sumayya ta fice daga zuciyar Mufida, ganin lokacin salla yayi ne yasa Mummy cewa zata tafi tayi sallah, Mufida ma tabi bayanta suka fice, sai a lokacin Sumayya ta samu dama ta kira Jumy take sanar da ita halin da ake ciki na hatsarin Muhdeen, daga can ɓangaren Jumy ta ce
"Anya ƙawa ta babu sa hannunki a hatsarin nan kuwa?"
"Na san halinki nasan abunda zaki iya aikatawa ."
"Dariya Sumayya tare da cewa
"Tabbas kinyi gaskiya ba abunda bazan iya aikatawa ba, amma ki sani wannan hatsarin masa ba saka hannuna a ciki, ai kinsan idan in son mutum bazan iya cutar da shi ba matuƙar kuwa kika ga na cutar da mutumin dake ƙaunata to haƙiƙa ya kainii bango ne wanda hakan shine masalaha."
Taɓe baki Jumy tayi tare da cewa
"Ba wata masalaha da sai an halaka wani, nifa nan da kika ganni duk iya shige da isakanci na wallahi bazan iya yin kisan kai ba."
"Hmmm ba'a kaiki bango bane wallahi da ankaiki bango da ba zaki daɗi haka ba, sannan lokacin da zaki aikata hakan ma ba zaki sani ba, nayi yunƙurin kashe Inteesar a baya ta tsallake rijiya da baya, amma matukar ta kaimu bango to fa wallahi bazata sha ba, don idan raina ya ɓaci ko zuciyata bana saurara duk abinda yazo gaba na aikata shi nake."
"To ki guji ranar da zakiyi nadama kuwa wanda lokacin nadamar ba zata maki amfani ba."
Maganganun Jumy ba suyi mata ba dan haka ta katse kiran tare da kiran lamabar wayar shila, bugu biyu shila ta ɗauka suka gaisa zancen da yayiwa Jumy ita tayiwa Shila, sai dai shila tunzura ta ta dingyi akan duk abinda ta ce zata yi, a haka sukayi sallama ta kashe wayar .
Sai da akayi sallar isha'i ne su Mummy suka dawo bayan sunyi sallar isha'i, Sumayya tana nan zaune bata tashi ta je sallah ba.
Da sallma suka shigo ɗakin ta amsa masu, a tunanin Mummy Sumayya bata je. sallah bane saboda kada a bar Muhdeen a ɗaki ba kowa dan haka ta kalli Sumayya ta ce,
"Sumayya tunda mun dawo idan zakiyi sallah ki tashi kije kiyi ko."
Dai lokacin Gwaggo da Inteesar ta suka shigo ɗakin, Sumayya ta miƙe tare da cewa
"Bari na tashi naje nayi sallah to."
Kai Mummy ta jinjina tare da cewa
"To sai kin dawo."
Daga nan ta fice Gwaggo ta raka ta da harara, Mummy tayi magana cikin sigar lallashi ta ce,
"Gwaggo don Allah ki fita harkar yarinyar nan, tunda yanzun dai bata sake wani laifi ba."
Gwaggo ta nuna Mummy da yatsarta manuniya ta ce
"Fatima ki kiyaye ni fa ki fita a ido na na rufe, saboda ba ke tayiwa na mi tayiwa rashin kunya da fitsara, ai idan mayar ya manta ai uwar ɗa bai ci ta manta ba, kina cewa wai bata sake wani laifin ba sannunki kenan, amma wannan yarinya duk inda kike neman kaba'ira takai."
Ita dai Mummy bata ce komai ba har Gwaggo ta ƙaraci sababinta tayi shiru.
Jabeer ne ya shigo da sallama gaishe da su Mummy da Gwaggo yayi yayinda Mufida ta gaishe sa,zama kusa da Gwaggo ya ce,
"Ke wannan tsohuwar ba zaki tafi gida ki huta ba?"
Kai ta girgiza
"Ina naga tafiya ga miji kwance ko motsi baiyi ba."
"Kada ku damu ina sa ran insha Allahu ya kusa farkawa"
Mummy ce ta kalli Mufida ta ce,
"Ki dubawa yayanki abinci mana"
Mufida ta tashi da niyyar zuba masa abincin yayi saurin cewa
"Am okay"
Dan haka Mufida ta koma ta zauna inda Jabeer ya cigaba da cewa
"Yanzun magana cin abinci Mummy."
Sumayya kuwa tunda ta fita da sunan zatayi sallah sallah ta zauna gefen masallacin, tana tunanin ta ina zata fara, dan ko sallar asuba barayi na ballantana azahar da la'asar, wayarta ta ciro ta kira number Bashir bugu biyu ya ɗaya
"Hello Sumy ya akayi ya farka ne?"
"Tukunnah dai bai farka ba tukunnah"
"Okay nan zaki kwana Asibitin ne?"
"Wace ni da kwana a Asibitin alhalin wannan fitina miyar tsohuwar na nan ai ba mu zama inuwa ɗaya, gida zan koma da safe na dawo."
"Okay ko nazo na taya ki kwana ne"
Da sauri ta furta
"What's"
Dariya yayi tare da cewa
"Wai sai na maye gurbinsu tunda baya nan ko?"
"Kasan me kake faɗa kuwa? kazo gida na ka kwana bayan ga mai gadin gidan da sauran ma'aikatan gidan zasu ganka ka kwana bayan abokinka baya nan? me zasauyi zato?"
Taɓa baki yayi tare da cewa
"To ke kizo mana ki same ni idan har ba nan zakai kwana ba ba wanda zai san inda kika kwana, su a nan zasu ɗauka gida kika je kika kwana su can ma gidan zasu ɗauka asibiti kika kwana ba wanda zai sani."
Shiru tayi tana nazari kafin ta ce,
"Shikenan sai nayi tunani amma idan kaji ni shiru to ka tabbatar a Asibitin zan kwana tare da mijina."
"Hmm ai naga dole zaki fi buƙatata saboda zanyi maki amfani a daren yau shi kuma fa meye zai tsinana maku?"
"Kaga kada fa ka zaƙe da yawa dan zaka iya fuskantar tirjiya daga gare ni, kuma duk son da nakeyi maka baikai wanda nake masa ba, i love him more than everything dan haka kada ma kayi tunanin haɗa kanka da shi dan ya fika ta kowace fuska."
"Kada ki nemi gaya mun maganar da zuciyata ba zata iya ɗauka ba."
Tsuki tayi tare da kashe wayar
Tashi tayi ta je ta jero dalilin da ake binta tun daga asuba har isha'i.
Bayan ta idar ne ta koma ɗakin ta samu suna cin abinci, Mummy ta kalle ta ta ce,
"Sumayya kin idar da sallar ko?"
"Eh Mummy"
Zama tayi ta fara daddanna wayar ta, Mummy ta kalli Mufida ta ce,
"Ki zubawa Sumayya abinci mana"
"To Mummy"
Daga nan ta janyo Basket d'in da aka jera abincin tare da ciro plate ta zuba mata abincin, ta haɗa mata da ruwan sha, karɓar tayi don dama yunwa take ji sosai.
Suna gama cin abincin ne Inteesar wacce rabin hankalinta na wajen Muhdeen ta lura da ya fara motsi yana juya kai tare da yamutshe fuska.
Cikin tsananin farin ciki ta ce
"Ya farka"
Gaba ɗaynsu suka maida hankalinsu ga Muhdeen, gani sukayi yana juya kai amma idanunsa a rufe, da sauri suka ƙara da wajen gadon Jabeer ya riƙo hannunsa tare da kiran Sunansa.
"Muhdeen sannu ko"
Ba tare da ya buɗe idanunsa ba ya amsa da yauwa, Sumayya ta ce
"Sannu ya jikinka?"
Ba tare da ya buɗe idanunsa ba ya ce,
"Yauwa"
Sai a lokacin Inteesar tayi magana ta ce,
"Sannu yaya ya jikin?"
Jin saukar muryarta a cikin dodon kunne da yasa ya buɗe idanunsa da sauri dan tabbatar da abinda kunne da ya jiyo masa, idanunsa ne suka sauka akan nata yaga tana sakar masa murmushi, zuba mata ido yayi don tunda yake da ita bata taɓa yi masa murmushi ba sai yau, gani yake kamar ba gaskiya bane mafarki yakeyi dan haka sai ya miƙa hannunsa ya riƙo nata hannun, cikin muryarar da bata fita ya furta
"Inteesar kece?"
Kai kawai ta gyaɗa masa tana murmushi ba tare da tayi magana ba, sun kai mintuna biyu zuwa uku suna kallon juna suna sakarwa juna murmushi, kowa kallonsu yake yana murmushi saɓanin Sumayya wacce baƙin ciki da takaici duk ya ishe ta, ta gaishe sa amsawa yayi ba tare ba tare da ya ko kalle ta ba, amma daga jin muryar Inteesar ya buɗe ido ba shiri sai kallon juna suke kamar zasu haɗiye junansu,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 38