Share this page
account ɗin* *2242538358 Zainab Abdullahi U B A nagode* *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *_Albishir! Albishir!! Albishir!!!_* *_Jama'ar Annabi inayi muku Albishir da cewa nakawo muku wannan shahararre Kuma ingantaccen gida, gidan da suka darje suka rairaye suke kawo Muku kayiyyaki masu dankaren kyau da Kuma inganci abisa farashi dai dai da Aljihun ku_* *_Hajiyata, kanwata, Aunty na, kinaso kisamu kaya Wadanda ba kamarasu? Kayanda idan kika shirya kika fito kizama abin kallo a wurin Yan uwanki?_* *_dama wadanda zasu ganki ahanya?_* *_sbd yadda Zaki fita daban da saura?_* *_Kinaso Idan kikayi shiri arinka tambayanki a ina kika saye wannan kayan?_* *_Zakije gidan biki ko gidan suna Amma kina tunanin kayan dazaki saka saboda kiyi fita ta Alfarma ta kece raini?_* ```ARZUQLANA GALLERY``` *_sunkawo muku duk Wani abu Wanda zakuna bukata kama daga:_* ```Laces Atampha Shadda Abayas Materials Gyale Takalma Jaka Kayan Kitchen Bangles n jewelries``` *And many more* ```GIDAN KYAU, GIDAN QUALITY, GIDAN SAUKI, GIDAN KWALISA, DA ADO``` *_Wani abin sedai kunbiyomu zaku Gani da idanunku_* *_sunayin kasuwancinsu bisa gaskia da Amana, ba cuta ba cutarwa_* *_koda bakida kudin Siya Muna gayyatarki dan ki tallata kema kisamu naki_* *_Yar uwa kasance a gidan, da abaki labari gwanda ki bayar_* https://chat.whatsapp.com/FRJAnQZXm0t7rAroZWlMnQ *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a giji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page8️⃣0️⃣ Jabeer me yayi driving nasu bayan sunyi sallama da su Mummy da Gwaggo, Muhdeen bai sanar da Sumayya zancen tafiyar ba dan ya ji tana cewa zata bishi, kuma bazai so tafiya da ita ba a wannan yanayin da suke ciki, dan haka bai sanar da ita ba daga shi sai Jabeer suka kama hanyar zuwa Gombe. Bayan ya dawo daga masallaci yana kishingiɗe a ɗakin Dr Abdulkarim, yayin da Dr Abdulkarim yake daga gefensa. Wayarsa ce ta fara ruri, ko kallon wayar baiyi ba ballantana yayi niyyar ɗauka, har ta katse bai ɗaga ba, kallonsa Dr Abdulkarim yayi tare da cewa "Wayar ma sai kaga dama kake ɗagawa?" Bai ce da Abdulkarim komai ba kuma bai ɗaga wayar, har sai da aka kira wayar sau uku sannan ya ɗaga. Gimbiya Anisa ce ta kira shi video call, kara wayar yayi a gabansa ya ajiye ta, tare da zubawa wayar idanunsa. Zaune take ta ɗaura ƙafa daya kan ɗaya, yana sanye da alkyabba irin ta 'ya'yan sarakai, masu mata hidima na zagaye da ita, yayinda wata take ƙara gyara mata hullar alkyabbar, ɗaya wata tana durƙushe a gabanta tana bata fruit a baki, tana taunawa cikin yana kamar bata son ci. Murmushi ta sakarwa Yarima Areef tare da cewa "Barka da safiya my prince, fatan ka tashi lafiya." "Alhamdulillah" "Yarimana tun jiya nake jiran dawowarka na ji shiru, sai kuma nake jin labari wajen Fulani cewa ka tsaya ne saboda wata yarinya, gaskiya ba girmanka bane wannan, duk da nasan cewa kai mutum ne mai taimako da tausayi, amma hakan bai dace ba kana ɗan sarki guda ka tare a asibiti kawai dan ka tsinci yarinya a gefen titi." "Ni waye da nafi ƙarfin taimako, ba wanda yafi wani a wurin Allah sai wanda yafi shi tsoronsa, shi Allah baya duba zuwa ga surar jikinmu da dukiyarmu sai dai yana duba ne zuwa ga zuciyoyinmu da ayyukanmu." Shiru kawai tayi ya zuba ma pink lips ɗinsa da ke matukar burge ta ido, inda ya cigaba da cewa "Ina nan tare da ita, har sai ta farka sannan zamu taho da ita." A zabure ta miƙe tsaye tare da cewa "Ku tafi ina." "Masarautarmu kina da matsala da hakan ne?" "Komawa tayi ta zauna, ba tare da ta sake magana ba, ta ce, "Yanzun yaushe zaka dawo na ganka?" "Maybe gobe ko jibi insha Allahu." Datsar tufa tayi tare da cewa "Gaskiya bazan iya haƙurin zuwa jibi ban ganka ba, idan har ba zaka samu dawowa yau ko gobe gaskiya sai dai kaga na zo nan." "Kizo ina wai?" "Gombe" "Koda wasa kada kiyi Wannan gangancin, ba hali na sanyi tafiya na kwana biyu ki ce zaki biyo NI?" Dariya tayi tare da cewa "Ai a hakan ma nayi ƙoƙarin n daure dan naga ba aure mukayi ba, amma idan mukayi aure su inda zaka je ƙafata ƙafarka, Allah dai ya kaimu ranar aurenmu. Ta ƙarasa magana tana murmushi. Kallonta yayi tare da cewa "Bissalam" Daga nan ya katse wayar, Dr Abdulkarim ne ya kalle shi tare da cewa "Gimbiya Anisa na masifar sonka sosai, gashi kun dace da juna dukanku jinin sarauta ne gaba da baya, Allah ya kaimu ranar aurenku" "Ka daina tunanin cewa zan auri Gimbiya Anisa, dan gaskiya bata da ce da irin macen da make da burin aure ba, tana da gadara ta taƙama, tana da sin mulki da sarauta, Ni kuma duk Waɗan nan abubuwa basu dame ni ba, kullun maganarta zata zama matar sarki, wai nine sarkin gobe, yayin da Ni kuma bana son sarautar nan." Jinjina kai Abdulkarim yayi tare da cewa "Sarauta kam ko kana so ko baka so dole ka karɓe shi, dan mahaifinsa bashi da wani burin da ya wuce yaga ka gaji kujerar sarauyarsa. domin kai ne mafi mafi soyuwa a gare shi." Daga nan ya mike tare da cewa "Pls muje mu duba yarinyar nan mana." "kada ka damu nurse zasu yi mata duk abinda ya dace." Daga nan ya miƙa shima Dr Abdulkarim ɗin tashi yayi yabi bayansa Masu tsaron Yarima Areef ne suka take masa baya, dakata yayi na tare da ya kalle su na ya daga masu hannu dakatarwa., sanin me yake nufi me yasa suka koma inda suka tsaya, dan dama sun saba da wannan idan suka fita yakan dakatar da su,amma idan a masarautarsu ne bai hana su dan ya laura mai Martaba baya son yana dakatar da su. Koda suka iso Gombe basu sha wahalar gane gidan ba, dan haka, autar su Umma ne yayi masu jagora, har cikin gidan Da sallama suka shiga gidan, inda suka gaida da kowa na gidan tare da tambayarsu ya mai jiki, aka masu jagora har ɗakin kakan Inteesar suka gaishe ta tare da yi mata ya jiki. Bayan an kawo masu abinci da ruwa ne Jabeer ne kawai ya iya shan ruwan, amma Muhdeen ko kallon ruwan baiyi ba burinsa kawai yaga Inteesar. Koda suka shiga ɗakin da aka kwantar da ita, har lokacin tana kwance idanunta a lumshe, ƙarasawa Yarima yayi kusa da gadon tare da zuba masa ido. A hankali ta buɗe idanunta ta sauke su akan na Yarima, kallon juna suka dingayi na na lokaci, kafin ta cire ƙwayar idanunta daga nasa, ta maida su ga sauran nursess guda uku da ke ɗakin. Yarima ya kalle ta tare da cewa "Sannu ya jikinki?" Shiru kawai tayi tare da zuba masa ido, ya ƙara cefa mata wata tambaya ya ce "Ya jikinki? Nan ma shiru tayi ba tare da ta ce komai ba, Kallon Dr Abdulkarim Yarima yayi tare da cewa "Wuni ɗaya da kwana ɗaya tana kwance ba abunda ta ci, yakamata a nemo mata Abinci. Murmushi Abdulkarim yayi tare da cewa "Kada ka damu an je kawo mata." Kallonta Yarima yayi tare da cewa "Zaki iya tashi ki shiga toilet ki wanke baki?" Kallonsa tayi kamar mai kiyon magana ta ce, "Toilet baki?" Dr Abdulkarim ya kalli daya daga cikin nursess ɗin ya ce, Ta raka ta ta nuna mata yadda zatayi, dan haka ta ja hannun Inteesar suka nufi toilet, sabon brush ta ɗauko tasa tooth paste ta miƙawa Inteesar, sannan ya sake saka wani a wani brush ɗin, ta ƙara da jikin tap tana riƙe da hannun Inteesar, ta dinga nunawa Inteesar yadda ake yi ta hanyar yiwa kanta, haka kuwa akayi duk yadda tayi sai Inteesar ta yi itama. Har suka kammala suka fito, dai-dai lokcin da aka kawo mata kofin tea, aka bata ta shanye tass. A ranar nan sai da Muhdeen da Inteesar suka dinga zagaye Gombe, suka kai report police station aka tabbatar masu akwai motar da tayi accident jiya amm mutanen da ke cikin motar sun ƙone kurkusa hankali tashe Muhdeen ya ce sune amma baya tunanin sune, kuma aka sana cikin tamabaya ne ko akwai wadanda sukayi accident, jagorancin autar su Umma da Mallam Habu, nan dai suka gano motar da Inteesar yayi hatsari, hankalin Muhdeen yayi matuƙar tashi ganin motarsa da Inteesar suka tafi da ita ta koma, ya tsaya yayi mutuwar tsaye sai jin muryar Mallam Habu na cewa "Innalillahi wa'inna ilaihir, duk sun ƙone ƙurmus." Ji sukayi tim Muhdeen ya daɗi wajen sumamme, a guje Jabeer ya ƙarasa gare shi tare da ɗago shi yana kiran sunansa. Autan su Umma ne ya kalli Malam Habu ya ce, "Haba mallam Habu ba haka ake magana ba, ta yaya zaka ce sun ƙone kurmus? ba wanda ya mutu a cikin motar nan, dan banga alamar ƙashin mutum a cikin motar ba." Jabeer ya ɗauko robar ruwa a mota ya yayyafawa Muhdeen a karo na uku ya farfaɗo, koda ya farfaɗo kuka ya ke yana cewa "Kada ka ce mani Inteesar ta rasu, dan idan ta tafi nima zan bita ne." Autar su Umma ne ya dafa kafad'arsa tare da cewa "Ka kwantar da hanklinka, ba alamar mutum ya ƙone a cikin motar nan, dan haka muje asibitoci mu duba ko Allah zaisa an samu waɗanda suka ceci rayuwarsu, suka kaisu asibitin, daƙyar suka lallaɓa shi ya shiga mota inda suka dinga zagaye asibitoci sun tambayar ko an kawo wasu mace da namiji da sukayi accident, ko ina sukayi tamabaya za'a ce masu ba nan bane. Yarima ne ya tara jama'arsa inda yake sanar da su cewa da zaran an idar da sallar la'asar zasu kama hanya komawa Yola, dan ya ce daga masallacin zasu tafi. Inteesar kuwa an shirya ta cikin Abaya blue tayi kyau sosai, Yarima ne yasa da Galadima dai Dr Abdulkarim suka cikin ɗakin da take, yayin da Yarima ke hanta da magana yana murmushi, yayin da Galadima kuwa zuciyarsa baƙa sai kallon Yarima yake yana kwafa a cikin zuciyarsa. Haka su Muhdeen suka dinga zagaye asibitoci amma shiru basu da ce ba, inda Jabeer ya kalli Mallam Habu ya ce, "Ba wani asibitin da kuka sani na kuɗi ko na gwamnatin?" "Jinjina kai kawai Mallam Habu yayi tare da cewa "Gaskiya waɗannan kawai na sani." Autar su Umma ne ya ce "Akwai dai wani asibitin kaɗai sanya taga bamu je can ba." Jabeer ya ce wa "Ina ne?" "Autarsu Umma ya ce can ne ta farkon shigowa gari, shine ma yakamta mun fara zuwa, dan yafi kusa da inda maka baro wajen accident ɗin." Kiran sallar la'asar akayi wanda Mallam Babu ya ce "Bari suyi sallar la'asar sai su tafi can Asibitin Dr Abdulkarim ko can aka kai su, da wannan tunanin sukayi sallah suka tafi masallaci dan yin sallar la'asar sai su je asibitin Dr Abdulkarim. Acan ɓangaren Yarima kuwa yada an ajiye komi da zasu tafi da shi a cikin mota, yayin da suke jiran a idar da sallar la'asar suja motocinsu ya ɗaga zuwa Yola. *Shin ya kuke gani Muhdeen zasu ƙara so asibitin nan su haɗu da Inteesar?;idan sun koma da ita ashirin Sumayya ya tonu ya makomarta a wajen Muhdeen? Wani irin hukunci zai ɗauka akanta?shin ina direban da ya ɗauki Inteesar yake? Bashir zai faɗa wa Muhdeen kamar yadda yayi wa Ikirarari? idan kuma Yarima ya tafi da ita Yola ya rayuwarta zata kasance a cikin gidan sarauta?kunsan dai gidan sarauta da makirci waye Yarima Areef wace ce gimbiya Anisa?meye makomar Sumayya*? *Dan cigaba da karanta littafin Inteesar book 2 ki biya kuɗinki naira ɗari uku kacal # 300 ɗan jin ƙarahen labarin, zaki tura kuɗi ki ta wannan account ɗin* 2242538358 *Zainab Abdullahi U B A bank sai ki turo shaidar biya ta wannan lambar 09065327995* *Don neman ƙarin bayani* 09065327995 Love you oll😍😘 Love you oll😍😘 An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 38 of 38