Share this page
kuwa a idanun Gwaggo. "La'ilaha ilallahu Muhammadur rasulullahi salallahu alaihi wasallam kallon uwar me kake mata haka?wato kada ta fad'a ki?to kada ka damu sai nayi maganinka wallahi da mi kake zancen." Daga Nan ta ja hannun Inteesar suka shiga d'aki don ta k'udurata niyyar sak ta gano tsakanins,dafe goshi Muhdeen ya yi yana ta addu'ar Allah yasa Inteesar kada ta fad'awa Gwaggo komai,muryar Mummy ce ta dawo dashi tunanin da yake. "Son maganar Gwaggo fa gaskiya ne nima na gani kuma nasan ba auren aoyayya kuka yi ba,kana can kana k'untawa 'yar mutane da ba ruwanta fa." Dady ya d'ora da cewa Muhammad Inteesar amanace awuri ka indan kaci amama amana zata cika. *LONDON* Kwance ta ke tana kallon Pics d'in Muhdeen tana kuka,ita kad'ai take magana "Baby me yasa kayi Mani haka?me yasa aka aura maka wannan tsinanniyar yarinyar ne mun tsaka da cin amarci?kasan irin son da nake bazan iya had'a soyyayar ka da wata 'ya mace ba." K'arar shigowar sak'one ya shigo tana dubawa ta ga Shila ce bud'ewa yayi taga Muhdeen da Inteesar a gaban motarsa a bakin super market,wani gigitaccen k'ara ta saki Wanda ya ja hankalin Mum nata da Da wayar take kallo tabbas shine tare da Inteesar sun ci ado ya d'aukota a motarsa,jifa ta yi da wayar ta bugata da bango dai-dai lokacin da iyayen nata suka shigo d'akin,numfashinta ne ke barazanar d'aukewa tayi luuu zata fad'i cikin zafin nama Dad d'inta ya tare ta ta fad'a jikinsa. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) DON K'ARIN BAYANI 09065327995 Love u oll😍😘 Comment and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ki hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page4️⃣1️⃣ Numfashinta ne ke barazanar d'aukewa tayi luuu zata fad'i cikin zafin nama Dad d'inta ya tare ta ta fad'a jikinsa,Mum d'inta ce ta saki kuka tana fad'in "Shikenan mun shiga uku 'yar da muke da ita k'wara d'aya ce muke neman rasa ta akan d'a namiji." "Kinga ba kuma Zaki zauna kinayi mana ba,ki kawo mani ruwa." Fridge d'in da ke cikin d'akin ta nufa ta d'auko robar ruwa ta 'balle murfin ta mik'a masa ya kar'ba ya watsa mata a fuska sau biyu,sai ga ta ta farfad'o da ajiyar zuciya tana cewa. "Wallahi bazai yuwu ba Ni Muhdeen zai ci amana ta Ina nan ina tunanin yarinyar nan ba sonta ya ke ba ashe yana can tare da ita ya manta dani ko?" Ajiyar zuciya Dad ya sauke tare da cewa "Kada ki damu da kansa zaizo har nan da kansa ya same ki." Cikin muryar kuka ta fara magana "Dad wallahi yanzun aka turo Mani pic d'insa ya tafi shopping da wannan matsiyaciyar yarinyar Inteesar,Dad ban ta'ba kisan Kai ba amma Inteesar d'innan matuk'ar tana raye bazan ta'ba samun kwanciyar hankali ba,I will kill her matuk'ar ban kashe ta... "Shut up kinyi hauka ne ko kuma kishi hauka ne? kada na sake jin wannan maganar ko makamancinta a bakinki,dole ne sai kinyi rayuwa da Muhdeen? Cikin d'aga murya ta maida ma Dad d'inta da martani "Yas dole ne!na ce maka dole sai nayi rayiwa da Muhdeen shine mahad'in rayuwa ta bazan ta'ba iya rayuwa babu shi ba da na rasa shi gara a ce na rasa komai a duniyarnan Dad Kai da kanka kayi mani alk'awarin duk abunda nake so a duniyar nan zaka yi mani shi, kuma nima shira ne tunda na tashi naga duk abunda nake so shi kake mani ban ta'ba neman abu na rasa ba duk abunda nake so shi kake so kuma shi kake mani,amma karon farko a rayuwa ta na samu abunda nake son amma yana barazanar su'buce mani." Mum d'inta ce ta yi ajiyar zuciya sannan ta fara magana "Tunda haka abun ya kasance da kake cewa ya za'bi d'aya ko'yarka ko wacce suka aura masa kasan dai yana wa iyayensa biyayya bazai ta'ba tsallake maganar iyayensa ya bi na wasu ba kaima kasan da hakan kuma kaji maganganun da kakarsa ta fad'a maka lokacin da ka kira mahaifinsa kake masa magana,indai zaka bi shawara ta tunda basu suka kori Sumayya ba kuma mijinta bai sake ta ba kuma bai wulak'anta ta ba da k'afarta ta bar gidan ta taho nan,to idan zaka bi magana ta ta koma d'akin mijinta tunda ba zata iya rabuwa da shi ba." "Mum ke da kanki kike fad'in na koma da kaina na zubar da aji na a idonsa da danginsa?da wannan yarinyar da ya aura?." Fashewa da kuka ta yi fad'aj ikin Dad d'inta tana cewa "Wallahi Mum ba inda zan koma wato ma na fahimci baki so na baki k'auna ta baki kishi na,tunda har kike son na zauna da kishiya ke me yasa kike zaune ke kad'ai Dad bai k'ara aure ba?ai da Dad ya k'ara aure kika San zafin kishi ba Zaki ce na koma na zauna da kishiya ba." Da mamaki Mum d'inta ke kallonta "Sumayya ni kike fad'awa haka?" Tura baki ta yi tare da cewa "Ai gaskiya na fad'a kinsan zafin kishin ne?" Mummy ta yi kanta da niyyar marinta Dad ya daka mata tsawa "Ke dakata!" Sumayya k'ara shiga jikin Dad ta yi don ta tsorata da 'bacin ran da ta gani a fuskar Mun nata. "Kada ki kuskura ki ta'ba mai ita don wallahi kika mareta sai kinyi mamakin abunda zaki maki,k'arya ta fad'a ba gaskiya bane?sabida ance gaskiya d'aci ne da ita,da wanne zata ji da 'bacin ran mijinta ko da naki?kinzo Zaki saka yarinya gaba kamar ba kece kika haifeta ba,ke kanki kin sani bani k'aunar ki 'batawa yarinyar nan rai tun tana k'arama ballantana yanzun da tasan me yakamata tasan dai-dai da akasin haka,da ki ta'bata gwanda ki ta'ba ni,idan kuma kina musu da haka ne to ki ta'bata kisha mamaki." Mum bata sake cewa komai ba girgiza kai kawai ta yi ta fice ta bar masu d'akin. A nan k'asa ta kuwa bayan Gwaggo ta ja Inteesar sun shiga d'aki ta zuba mata ido bayan sun zauna ta kalleta ta ce, "'Yar albarka ki fad'a mani gaskiya ya yanayin zamanki da Muhammadu ya ke?" Shiru Inteesar ta yi tana nazari kafin ta ce, "Ba komai Gwaggo muna zaune lafiya" Kai Gwaggo ta girgiza tare da cewa "Ba lafiya ba 'yar albarka akwai abunda kike 'boyewa,kina nufin baya cutarki baya zalintarki yana kyautata maki duk wani hakkinki baya tauyewa?" Shiru Inteesar ta yi ba tare da ta ce komaiba,hakan yasa Gwaggo cewa "Kiyi mani magana mana abunda yasa kika ji na ce ki fad'a mani ya zamantakewarku ta ke shine kinsan ba auren soyayya kuka yi ba,auren had'i ne kuma bawai yana sonki bane kada ya je ya dinga k'untata maki ba. "Shiru Inteesar ta yi tana tunanin zamanta da shi Sam baya mata adalci burinshi kawai ya ganta tana wahal,amma Bata son ta zama sanasiyar 'batawansa da iyayensa don matuk'ar ta ce zata sanar da Gwaggo to tabbas zata sanar da su Mummy da Dady kuma zasuyi fushi da shi, hakan yasa ta ja bakinta ta yi shiru ta k'udiri niyyar hak'uri da juriyar zama da shi,dan haka kallon Gwaggo ta yi tare da cewa "Kada kisa tunananin komai a ranki muna zaune lafiya ba abunda kike tunani bane." "Shine duk kika rame kika lalace?ba komai tunda kink'i fad'a,koma dai mene ne zan gano Allah ya kaimu jibi zanzo na gaishe ku,tashi to muje." Mik'ewa Inteesar ta yi inda suka nufi falo,zaune suka tarar da su kamar yadda suka barsu, Mummy ce ta zubawa Inteesar ido tana karantar yanayinta,adai zaman da sukayi tare da Inteesar barci ke raba Inteesar da gidanta a tsawon shekaru uku zuwa hud'u kenan amma tabbasa yanayin Inteesar ya canza da ganinta kasan akwai abunda ke damunta. "Gwaggo ta sanar da ke ko akwai wata matsala?" Kai Gwaggo ta girgiza yayin da take zama a kan kujera "Ba abunda ta fad'a itama 'yar nema tayi shiru tana rufa masa asiri badai namiji ba ki cigaba da rufa masa asiri shi zai tona naki ne,ba'a goyon bayan namiji don ba d'an goyo bane kuma tunda na tambayeki kika mani shiru to duk ranar da kika zo kika ce ga abunda ya maki na cutarwa ba abunda zance masa sai dai nayi maki dariya." "Mummy ce ta yi ajiyar zuciya "Son Inteesar amana ce aka baka don Allah kada ka cutar da ita kaga k'aramar yarinya ce ita sai kayi hak'uri da ita,idan ta yi abu ba dai-dai ba ka nusar da ita ta lallami da hikima ka yi hak'uri da ita kada ka zaince ta." Kai ya jinjina tare da cewa "To Mummy kada ki damu insha Allah ba zakiji komai na rash... Gwaggo ta yi saurin katse sa da cewa "Ai dole ka ce ba za'aji ba tunda ka hanata fad'a kayi mata barazana me kuwa zamuji?amma ni ba iya ji ba har gani sai na yi dani kake zance." Kallon Gwaggon ya yi tare da fad'in "Me kum zaki gani rigimammiyar tsohuwa?ai ba abunda zaki gani,zancen da kike ma na cewa zaki zo gidana kiyi wata d'aya ban gayyaceki ba kiyi zamanki,ko na wuni d'aya bana buk'atarki ballantana na wata d'aya ki yi zamanki mu zamu zo ki ganmu idan kina buk'atar ganinmu." "Wallahi baka Isa ba sai nazo" Murmushin gefen baki ya yi "Aiko duka ranar da kika zo sai kinyi jinya kin gwammaci da baki zo ba." Da mamaki take kallonsa "To me zaka yi mani" "Ba abunda zan maki amma ina Mai tabbatar making da cewa kika zo gida na sai karen gida na ya yayyaga maki fatar jikinki." Salati Gwaggo ta saki tana tafa hannu tana ceqa "Oh ni Kuluwa yanzun kare ka ajiye a gidanka?saboda me?" "Saboda ke na ajiye duk randa kika saka k'afa gida na sunanki sorry." "Muhammadu haka zamuyi da kai d'an jakkar uba?" Mi'kewa ya yi tare da cewa "Ni zan d'an fita anjima zan dawo na d'auke ta mu koma gida." Mummy ce ta amsa masa da "Adawo lafiya" Dady ya kalli Inteesar ya ce "Daughter ba wani matsala ko? Kai ta girgiza tare da cewa "Bakomai Dady" "Ba wani abunda kike buk'ata ?" "Ba komai Dady" Mi'kewa ya bar wajen. Wunin ranar Inteesar a gidan ta yi shi Mummy ta Kira ta har d'akinta ta yi mata dabara da lallami, ko zata fad'a mata wani abu na rashin kyautatawa da Muhdeen ke mata amma sam tak'i yarda ta sanar da su haka suka hak'ura suka k'yale ta, Mufida ta ji dad'in zuwan Inteesar sun yini suna fira. Bayan sallar isha'i ne Muhdeen ya dawo gidan don d'aukar Inteesar su tafi gida,bayan ya ci abinci ne Mummy ke sanar da shi cewa ya je tana d'akin Gwaggo,da sallama ya shiga d'akin Gwaggo da kezaune kan sallaya tana jan carbi ta amsa masa,kwance ya samu Inteesar ganin Gwaggo ya sa ya fara magana mai dad'i "Sweet heart har kinyi barci kenan tun yanzun?"ashe daren yau ba zamuyi fira ba kenan?" Ita kuma Inteesar cikin barcinta da yanzun ta saba aikin wahala safe da yamma, kuma yaune bata yi ba sai ta mafarkin wai yana mata hukunci me yasa ba tayi ayyukan da ya ce ta dinga yi kowa ne yamma ba?a cikin mafarkin ta wai gata kwance tana barci shi kuma yana tsaye kanta zai dake ta ne ta fara magana,daga shi har Gwaggo suna kallonta tana mutsu-mutsu sai suka ji ta fashe da kuka tana cewa. "Yaya dan Allah ka yi hak'uri wallahi narci ne ya d'auke ni banyi ayyukan da kake sani ba,dan Allah kada ka dake ni wallahi bazan k'ara b... Dafe goshi Muhdeen ya yi tare da sauri ya k'arasa bakin gadon yana jijjiga ta tare da kiran sunanta. "Baby lafiyarki kuwa wani irin mafarki kike yi ne ai mafarki ba gaskiya ba ce." Tana bud'e ido ta ganshi a gabanta sai ta k'ara rikicewa tana girgiza kai tana ja baya idanunta na zubda hawaye,goshinsa ya dafe cikin takaicin abunda ya ke 'boyewa yarinyar nan na fiddo da shi,Muryar Gwaggo da Inteesar ta ji ne yasa ta dawo hayyacinta ta gane ashe mafarki take. "Ba shakka! Ni tunda na kalle ki nasan baki cikin kwanciyar hankali,idan ba haka ba ace barcin mintuna Ashirin ne zaisa ki rikice haka?wannan tsoron da na gani a cikin idanunki da maganar ayyukan da ya ke saka ki kina kuka kina bashi hak'uri kad'ai na fahimci halin da kike ciki saboda abinda mutum yasa a ransa ne ya ke mafarkinsa,don haka tashi kibi mijinki ku tafi." Mi'kewa ta yi tare da d'aukar posanta da wayarta suka nufi k'ofar fita tana gaba yana binta a baya,bayan fitar Inteesar Muhdeen na k'ok'arin fita ne ya jiyo muryar Gwaggo tana cewa "Idan baka kashe ta ba to ba sunanka Muhammadu ba." Kamar ya yi mata magana sai kuma ya fasa ya fice tare da buga k'ofar da k'arfi." "Ai da ka dawo ka 'balle k'ofar gaba d'aya,mutumin banza." A falo suka tarar da Mummy sallama suka mata suka fice. Yana driving ransa a 'bace saboda yasan cewa Gwaggo ta gano halin da suke ciki. "Wato ke bakijin magana ko?duk gargad'i da nayi maki sai da kika bari suka gane halin da muke ciki dake ko?." Kai ya jinjina "Zaki gane kuranki wallahi" Hawaye ne ya fara fita daga idanunta cikin muryar kuka ta fara magana "Wallahi ban fad'awa kowa ba duk yadda suka lalla'bani ban fad'a ba." "Ni zaki raina ma hankali?kina magana a gaban Gwaggo har da kuka kina rok'ona Wai ayyukan da na saki ko?." "Wallahi bansan na fad'a ba mafarki nayi." "Kada ki damu mafarkin zai zama gaskiya idan muka k'arasa gida,bana buk'atata na sake Jin muryarki." Daga nan ba Wanda ya sake magana har suka k'arasa gida,bayan Mai gadi ya wangale masa gate ya shiga ya yi parking need suka fito,yana gaba tana binsa a baya,suna shiga yaga tana k'ok'arin nufar d'akinta ya ce, "Dakata Tsayawa tayi tare da kallonsa,ya cigaba da magana. "Yanzunan ki tabbatar da cewa duka falon gidannan kin goge share su kin goge,sannan duka d'akuna guda takwas dake gidannan ki tabbatar a daren nan kin sharesu kin goge su,duka toilets guda takwas ki wankesu a daren nan toilet na falon nan ma shima haka duka kitchen d'in ma haka fatan kin gana?" Shiru tayi ta kalli time a wayarta ta ce, "Yaya kafin na wuce da safe sai da suka ayyukan nan da ka lissafa na yi su,ba wanda banyi ba a cikinsu,bayan na gama ne muka rufe gidan muka tafi ba wani datti bamu zauna gidan ba kuma kaga yanzun k'arfe goma na dare ya kusa don Allah ka barni da safe sai nayi ba datti suka yi ba wallahi barci nake ji." "Umarni na baki ba shawara na nemi ki bani ba, sannan bari na fad'a maki daga yau bana son uzuri." Yana fad'in haka ya nufi parta d'in Sumayya,ita kuma ta nufi d'akinta idanunta tab da k'walla na tausayin kanta canja kayan jikinta ta yi zuwa kananun kaya yadda zata ji dad'in yin aikin. Da paart d'inta ta soma daga nan bayan ta gama ta nufi part d'in Sumayya,haka ta dinga bin falon da d'akunan da toilets na kowane da kitchen duka biyu dinnan area ko ina sai da ta goge su tas. Dama can ba wani datti sukayi ba fes suke kuma ba amfani ake dasu ba ba kowa a ciki,amma don mugunta sai ya sata ta yi safe da yamma. Bata gama ayyukan da ya saka ta ba sai k'arfe d'aya na dare,duk ta gaji sai hawaye ne kawai ke tsiyaya masu d'umi daga idanunta.wanka ta yi tare da yin addu'ar kwanciya barci ta kwanta, lokacin k'arfe d'aya da rabi na dare. K'arfe hud'u da rabi na asuba ta farka wanka ta yi ta d'auro alwala,ta yi nafila da addu'a ta samun sassauci a rayuwarta, har aka Kira assalatu ta yi sallah da azkar tana son ta tashi ta yi ayyukan safe ne barci mai nauyi ya yi awon gaba da ita ba tare da ta shiryawa yin barcin ba. Misalin k'arfe tara na safe ya fito daga bedroom d'insa ganin bai ganta a kitchen ba kuma bata shigo ta gyara masa d'aki ba yasa ya nufi d'akinta. Tura k'ofar ya yi ya ganta kwance saman sallaya da hijab a jikinta,alamun daga sallah ta yi barcin,fridge ya bud'e ya d'auko ruwa mai sanyi sosai ya 'balle murfin robr ya tsiyaya mata ruwa tun daga Kan fuskarta har zuwa jikinta, a firgice ta farka tare da fad'in "Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Jikinta ne ya soma rawa don ruwan ya yi sanyi da yawa,gashi dama bata son ruwan sanyi ko wanka dashi batayi Amma yau ruwa mai sanyi kamar K'ank'ara aka kwarara mata a jiki,kuka ta fashe da shi mai cin rai,yatsarsa ya sa a baki tare da furta "Shhhhhhp" Ba shiri ta had'ye kukan hawaye na tsiyaya a idanunta. "K'arfe nawa yanzun?" Kallon agogon da ke manne a d'akin ta yi "K'arfe tara da minti biyar" "Shine kike kwance kina barci?" "Wallahi bansan lokacin da barci ya d'auke ni ba." "Tashi kije ki yi ayyukan da kika San ya wajaba a kanki." Mi'kewa ta yi zata shiga toilet taji muryarsa yana cewa "Ina zaki je?" "Zan shiga toilet ne na cire kayan nan sun jik'e da ruwan sanyi, idan na ce zan barsu a jikina sanyi zai kamani ne." "Ya kamaki mana sai me?ba sanyi ba ko k'ank'ara zai kamaki ya kamaki ba matsalata bace,don haka fita ki fara ayyukan da na saka ki." Haka ta fita kamar kazar da k'wai ya fashewa a ciki ta fita ya bita da kallon banza. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love you oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa,idan suna ki hali yaso d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi t,arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page4️⃣2️⃣ Haka ta fita kamar kazar da k'wai ya fashewa a ciki,ta fita ya bita da kallon banza. A haka ta da jik'akkun kayan ta dinga aiki da su a jikinta,har suka bushe a jikinta ga sanyin da take ji ba yadda ta iya ahaka ta gama ayyukan gidan. Kasancewar ba ya cin abincinta ya sa bata yi wani girki ba ta ruwan shayi kawai ta dafa ta sha,ta koma d'akinta lokacin rana ta riga da ta yi, wanka ta yi ta Sanya soguwar riga na atamfa wayarta ta soma ringing dubawa ta yi Usman ne daon haka Bata d'aga kiran ba har ya tsinke,wani tunani ta yi kodai ta d'aga ne tunda wannan auren ba mai d'orewa bane shi da kansa ya fad'a mata idan Sumayya ta dawo zai rabu da ita,don ba sonta ya ke ba tunanin hakan ne ya sa ta cewa bari ta d'aga kafin matarsa ta dawo ya ce zai sallame ta,d'aga wayar ta yi ta Kara a kunnenta. "Assalamu Alaikum" Daga can 'bangaren Usman da ke zaune a office d'insa ya saki ajiyar zuciya tare da furta. "Wa'alaiki salam, har naji sanyi a Raina Inteesar azabtar da ni da kike ya yi yawa,baki san rashin ganinki da rashin jin muryarka ya hanani sukuni ba kullun da tunaninki nake kwana nake tashi,tunda muka had'u a sau uku nazo gidanku amma kika hana wai Abba ya hanaki,hakan ya sa na yi tunanin zuwa neman izinin zuwa zance a wurinsa." Da sauri ta katse shi da cewa "Kadai bari zuwa nan gaba kad'an amma ko ka same shi yanzun zai ce ka bari zuwa gaba kad'an ba jimawa,saboda haka idan olkaci ya yi da kaina zan sanar dake." Hira suka ta'ba sosai na kusan mintuna talatinl,sai da ya ji ana knocking sannan ya mata sallama ya ajiye wayar,sannan ya bada izinin shigowa. Ita kuma sanin cewa jiya abokan mijinta suka ce yau zasuzo ne ya sa ta mi'ke ta nufi kitchen don d'aura masu girki. Jallop d'in cuscus ta da white rice and stew da ta ji naman rago,sai pepper chicken da tayi masu da farfesun d'anyar kifi da ta yi masu ga lafiyayyan juice na kwakwa da madara,ta had'a masu girkuna masu gidan ya cika da k'amshin girkinta ya cika gidan. Komawa d'akinta tayi ta fad'a toilet ta sake sabon wanka sake ta shirya cikin doguwar riga na less d'inki bubu ya kar'bi jikinta,dama ita bata damu da kwalliya ba,don haka bayan ta shafa man shafawarta na wajen Hajiya Bilkisu, powder kawai ta shafa sai man baki,ta saka sark'a da d'an kunne,gasjin kanta ta tufke shi a tsakiyar kanta,zama ta yi baki gadon tare da d'aukar wayarta tana buga game. Gidansu Inteesar kuwa koda Abbanta ya dawo kasuwa yammaci ne lik'is hannunsa d'auke da leda mai layin yellow da bak'i, Dankalin hausa ne a cikin ledan da sallama ya shigo gidan , Umma da ke zaune gaban murhun itace tana tuk'a tuwo ne ta amsa masa sallamar,sakin muciyar ta yi da niyyar tashi ta kar'bo ledar,hannu ya d'aga mata alamar ta barshi . "Zauna ki cigaba da aikinki Umman Inteesar" Murmushi ta yi tare da cewa "Sannu da zuwa ya kasuwar?" "Alhamdulillah an godewa Allah." Zama ya yi kan tabarman da ke shimfid'e a k'ofar d'akinsa. Bayan Umman Inteesar ta gama tuk'a tuwon ne ta tashi ta d'auki kofin silver da murfinsa ta d'ebo masa ruwa,a cikin randar k'andar k'asa me sanyi gabnsa ta ajiye tare da k'ara masa sannu da zuwa,bayan yasha ruwan ne ya mi'ke tare da cewa "Bari na tashi nayi wanka na tafi masallaci, lokacin salla ya k'arato. Mi'kewa ya yi yayin da Umma dama ta ajiye masa ruwan wanka a cikin tukunyar da suke dafa ruwan zafi,juyewa ta yi a cikin bokinti ta surkar masa da ruwan sanyi ta kai masa bad'aki ya fito daga cikin d'akinsa ya shiga band'akin Bayan sallar isha'i ne bayan ta dawo daga masallaci yana zaune a Kan tabarma Umma ta kawo masa tuwo,ya ci ya gama ta ce , "Mallam Inteesar sunzo da mijinta d'azun da rana kana kasuwa." Zuba ma Umma ido yayi fuskarsa d'auke da murna duk da bai ganta ba amma ya ji dad'in zuwanta gidan. "Masha Allah da nasan zata zo da na bari sai na ganta kafin na tafi,suna dai lafiya ba wata matsala ko?" "Wannan ne kuma ban sani ba mallam" "Kamar ya baki sani ba da tazo me yasa baki tambaye ta ba ko awai wata damuwa." Shiru Umma ta yi tana tunanin yanayin da taga Inteesar,ita ta haifeta tafi kowa saninta a duniyarnan,amma ganin yanayin da ta ganta ko shakka babu akwai abunda ke damunta,dalilin da yasa bata d'aga hankali ba tasan cewa wasu lokutan auren had'i idan har basa son junansu sukan sawa kansu damuwa da tunani saboda ba wannan ne a zuciyarsa ba,wannan dalilin yasa Mummy kauda ido. "Mallam ta ce mani suna zaune lafiya." Jinjina kai yayi "Masha Allah" Umma ta mik'e ta shiga d'aki ta fito hannunta d'auke da kud'in da Muhdeen ya bata mik'a masa tare da cewa "Mijinta ne ya kawo muna kayan abinci masu yawa tare da kud'in nan." Kallon kud'in Abba ya yi sannan ya kalli Umma ya ce, "Harda d'awainiya haka?da baki kar'bi kod'insa ba" "Nima banso kar'ba ba ajiyewa ya yi" Yana zaune akan kujera Yana jiran isowar abokansa,wayarsa ta fara ruri,dubawa ya yi yaga Dadynsa ne,d'aga wayar ya yi tare da cewa "Assalamu Alaikum" Daga d'aya 'bangaren "Wa'alaika salam Muhammad kana gida ne?" "Eh Dady ina gida ina jiran su Jabeer ne zasu zo." "Okay to ga Gwaggo nan ta shirya kayanta ta ce lallai sai dai na kira ka kazo ka d'auke ta zuwa gidanka." Gaba d'aya hankalin Muhdeen ya tashi,don yasan zuwa sa masa ido kawai Gwaggo zata yi ba wai don ziyara ba,yanzun ya zaiyi da wannan tsohuwar ba,ta zame masa matsala,yana cikin tunani ya jiyo muryar Dady na cewa "Ya kayi shiru lafiya kuwa?" Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Gani nan zuwa Dady" Tsuki ya ja tare da d'aukar wayarsa kamar ya ba Direba ya d'auko ta,ya tuna kira Mahaifinsa ne don haka ya ta fi da kansa. Yana driving akan hanyarsa ta zuwa d'aukota ne wayarsa ta soma ruri dubawa ya yi yaga Sumayya ce, ba shiri yayi parking a gefen titi ya amsa wayar cikin farin ciki. "Hello Baby sai yau kika Kira ni tunda kika

Chapter 17 of 38