Share this page
mai dad'in k'amshi, k'aramar riga ya saka da wando 3 quarter. Shikad'ai yake magana kamar yanayi da wani yana cewa "Bansan yaushe ne ki kuma wani lokaci bane na kamu da sonki, bani da burin da ya wuce na ganni gani gaki, ina jinki tamkar wani sashe na jiki na idan na kasance tare da ke har farin ciki nake ji a cikin raina." Haka ya dinga magana shi kad'ai har ya gama shirinsa ya fito don zuwa d'akinta, yana fitowa ne yayi kici'bis da Sumayya tana dawowa daga waje, kallo d'aya yayi mata ya kauda kansa ya nufi d'akin Inteesar, ganin haka yasa Sumayya ta k'arasa da sauri ta rungume sa ta baya tare da d'ora ha'barta a kafad'arsa cikin kirsa ta fara magana tana cewa "Washh baby nagaji wallahi tun jiya da na fita ban dawo ba sai yanzun duk a gajiye nake baby yunwa ya addabe ni me yarinyar nan ta girka muna ne?" Baice da ita komai ba illa ya janye ta daga jikinsa yayi tafiyarsa, murmushin mugunta tayi ta nufi d'akinta, shi kuma ya nufi d'akin Inteesar. *Daga alk'alamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love you oll😘😍 Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by ✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page5️⃣9️⃣ Baice da ita komai ba illa ya janye ta daga jikinsa yayi tafiyarsa, murmushin mugunta tayi ta nufi d'akinta, shi kuma ya nufi d'akin Inteesar. Da sallama ya shiga d'akin bayan ya tura k'ofar, bata cikin d'akin dan haka sai ya zauna a bakin gadon yana jiranta don a tunaninsa tana toilet ne, har tsawon mintuna goma bata fito ba kuma baiji alamun motsin mutum ba, dan haka ya tashi ya k'arasa k'ofar toilet d'in bata ciki tsayawa yayi ya k'arewa d'akin kallo komai tsaf abun sha'awa sai k'amshi ke tashi, murmushi yayi sannan ya fita d'akin. Kai tsaye kitchen ya nufa nan ma bata ciki har store ya duba bata nan, mamaki ne ya kama sa ina zata je ita da bata zuwa ko ina kullun tana gida to ina ta shiga ne? Haka ya dinga duba cikin gidan nan duka d'akunan gidan lungu da sak'o ba inda bai neme ta ba amma bai ganta ba, haka ya bincike gidan nan gaba d'aya ba Inteesar ba alamarta, fita harabar gidan yayi ya samu mai gadi da Ishaq Direba da mai bawa filawa ruwa suna fira. "Cikinku akwai wanda yaga fitar matar gidan nan?" Girgiza kai mai gadin yayi tare da cewa "Hajiya Babba dai tun jiya da ta fita yanzun ta dawo, amma Hajiya k'arama banga fitarta ba gaskiya." Shiru Muhdeen yayi yana nazari duk ya bincike gidan nan amma bata nan, kuma mai gadi baiga fitarta ba, juyawa yayi ya kalli sauran ma'aikatan gidan ya tambaya su ko akwai Wanda yaga fitarta kowa ya ce bai gani ba, dubansa ya maida wajen mai gadin ya ce, "Kuma ba wanda yazo gidan nan yau?" "Eh to Mahaifiyarka tazo ita da k'anwar ka da safe." "Akan idonka suka fita?" "K'warai kuwa akan Ido na suka fita." "Basu fita tare da ita ba?" Nan sauran ma'aikatan gidan suka tabbatar da suna dawowa Mummy zata fita kuma ita kad'aice suka hangeta a bayan motar, sai Mufida dake gefen Direban. Haka ya juya ya koma cikin gidan, kai tsaye d'akinsa ya nufa ya shige tare da zama a bakin gadon, zamansa kenan sai ga Sumayya ta turo k'ofar ta shigo, zama tayi gefensa tare da rik'o hannunsa cikin nata ta fara magana "Ya naganka haka kamar kana cikin damuwa?" Ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "Wani lokaci kika dawo gidan nan?" Kwantar da kanta tayi a gefen kafad'arsa ta zagayo da hannunta d'aya ta bayansa ta rungume sa d'ayan hannun kuma tana rik'e da hannunsa ta fara magana "Dawowa ta fa kenan naganka kana k'ok'arin shiga d'akin Amaryarka, gashi naga bata girka muna komai ba yau kuma yunwa nake ji." Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Nima tunda na dawo nake nemanta bansan ina ta shiga ba." Gaban Sumayya ne ya fad'i jin maganarsa don ita dai ta san da cewa ta barta kwance matacciya kodai bata mutu bane? ko kuma dai ta rayu ne, to idan bata mutu ba ai da anganta a cikin gidannan amma shiru? meke faruwa ne? haka take ta tunani tare da anyyana abubuwa dayawa a cikin zuciyarta, ganin yadda ta fad'a duniyar tunani ya tambaya ta "Tunanin me kike yi ne?" Murmushi tayi tare da k'ara narkewa a jikinsa ta ce "Bakomai, kada ka damu maybe wani uzurin ne yasa ta fita." Girgiza kai yayi tare da cewa "Ba uzirin da zaisa ta fita kai tsaye ba tare da sani na ba." "Ok to Allah ya dawo da ita lafiya." "Ameen" "Baby nayi missing naka fa, amma kai naga kamar ba kayi missing d'ina ba, ada baka iya kwana biyu baka neme ni ba amma yanzun kwana biyu shiru baka ma damu da ni ba, ko a jikinka ni gani nake ma kamar ba kai ba wallahi, ka canza mun." Zura hannayenta tayi cikin rigarshi ta fara shafar kwantaccen gashin k'irjinsa tana shafawa, wani yarrr yake ji a jikinsa take yanayinsa ya sauya, ganin hakan yasa ta saki wani shu'umin murmushi, ganin tana son sashi cikin wani yanayi ne yasa ya ce mata, "Pls ki bari, bana cikin yanayin a yanzun so nake nasan halin da Inteesar take ciki." "Kada ka damu ita ba k'aramar yarinya bace, duk inda ta je zata dawo mana cikin k'oshin lafiya." Ya bud'e baki da niyyar magana kenan tayi saurin saka bakinta cikin nasa ta fara tsotsa kamar ta samu sweet, hannunta na cikin rigarsa tana masa tafiyar tsutsa, baisan lokacin da ya fara maida mata da martanin abunda take masa ba,dama ba wata rigar arziki ce a jikinta ba, nan danan ya raba ta da kayan jikinta anan ya k'ara tabbatar wa da kansa cewa lallai mata suna suka da kafin ya fara ganin surar jikin Inteesar idan yaga jikin Sumayya burge shi take amma tunda yaga suffar jikin Inteesar sai yaga yanzu jikin Sumayya ba komai bane, dan fatarta bai kai na Inteesar laushi da shek'i da santsi ba, haka breast d'inta ma bai kai na Inteesar girma da laushi ba uwa uba tsayuwa don breast d'in Inteesar a cike suke kamar an hura balon-balon kuma a tsaye kem basu rankwafa ba bare su zube, ita kuma Sumayya nonuwanta k'ananu ne irin masu tsawon nan dan har sun d'an rankwafa. Haka suka dinga wasanni da junansu daga nan suka afka duniyar ma'aurata, ya d'an samu gamsuwa d ita amma bai kai gamsuwar da ya samu da Inteesar ba, dan ko baiyi sex da Inteesar ba iya wasa kawai yana samun gamsuwar da ko yayi sex da Sumayya baya samunta, lallai Allah ya mata baiwar ni'ima. Bayan sun samu nutsuwa ne ya tashi ya shiga toilet ya tsarkake jikinsa. Ita ko kwanciyarta tayi don dama sai yayi fama da ita kafin tayi wanka kullun haka suke ya zama jiki. Bayana ya canza kaya ne ya kalle ta tare da cewa "Ki tashi kije kiyi wanka lokacin sallar la'asar tayi, daga masallaci zan tafi asibiti naji ki ta tafi wajen Ummanta ne, idan kuma bata nan zanje gida ko ta tafi wajen Mummy da Gwaggo." Bayan an idar da sallar la'asar daga masallaci asibiti ya koma, kai tsaye ya nufi word d'in da aka kwantar da Umma a can, Jabeer na k'ok'arin fitowa daga d'akin shi kuma yana k'ok'arin shuga ciki, komawa baya yayi don yana son magana da Jabeer d'in, kallonsa Jabeer yayi tare da cewa "Har ka dawo ne angon Sumy?" Kauda kansa yayi kamar baiji shi ba, Jabeer ya cigaba da cewa "Kazo ganin surukanka ne ko? jikin nata da sauk'i insha Allah gobe za'a sallame ta." "Ni duk ba wannan ba, a cikin nan da ka fito kaga Inteesar a ciki ne?" Kallonsa Jabeer yayi tare da cewa "Wata Inteesar d'in?" "Ya ina tambayarka kana dawo mani da tambayar rainin wayo, wace Inteesar kasan zan tambaya bayan matata." "Au haba dama kana da mata Inteesar ce?ai na d'auka Sumayya ce kawai matarka Inteesar kuwa 'yar aiki ce a wajenku." Baida lokacin jurara maganganun Jabeer d'in don haka sai ya shige cikin d'akin dan bazai iya jurar maganganunsa ba. B'angaren Mummy kuwa koda tabar Mufida a Asibiti gidan ta nufa, inda ta tarar da Dady da Gwaggo suna zaman jiran dawowarta, koda Gwaggo ta ganta ta fara sababi tana cewa "Wannan wani irin mugun hali ne kike so ki d'auko Fatima? kibar gidan nan tun sassafe ko abinci na baki bani ba kin tashi kin tadiyarki ko a jikinki ko? wato idan ma yunwa ta illata ni ba damuwarki bane ko Fatima? kuma kinsan ina da gyambon ciki bana iya jurar yunwa yanzun nan jiki na sai ya soma rawa ko akwai abunda na tare maki a cikin gidan ne da kika fara gajiya da ni? nan fa gidan d'ana ne ni na haife shi kafin ki ganshi ya aure ki, don haka baza ki hora ni da yunwa ba abincin da d'ana ne yake nemowa." Girgiza kai Mummy tayi tare da murmushin takaici, don inda sabo ta saba da halin Gwaggo haka take dam, shiyasa hakan bai dame ta ce, "Don Allah kiyi hak'uri Gwaggo, wallahi nima tafiyar a ba shiri tazo mani dole ce tasa na fita." "Au dole ne fitar shiysa amma ni ba dole bane bani abinci ko?" "Allah ya huci zuciyarki Gwaggo, na kammala had'a breakfast sannan na tafi sha'afa nayi ne shiyasa, kuma Gwaggo ai da kika ji shiru da sai ki shiga kitchen ki d'ebi kici ." "Da nina saba shiga kitchen na d'ibi abincin naci?" Dady ne ya kalli Gwaggo ya ce, "Kiyi hak'uri Gwaggo insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba." Kallon Mummy yayi tare da cewa "Wai yau sammakon gaida Umman Inteesar kikayi haka? Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin ta sanar da shi ne ki kada ta sanar da shi? Idan ta sanar da shi dole Gwaggo zata sani kuma Gwaggo ba zata iya bata matsala akan shawara da ta yanke musamman idan akayi la'akari da soyayyar da take yiwa Muhdeen. Daga alk'alamin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don neman k'arin bayani 09065327995 Love you oll🥰😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Page6️⃣0️⃣ Idan ta sanar dashi dole Gwaggo zata sani, kuma Gwaggo zata iya bata matsala akan shawara da ta yanke, musamman idan akayi la'akari da soyayyar da yiwa Muhdeen. "Eh Asbiti naje tare da Mufida na barta a can zuwa anjima zata dawo." Daga nan kitchen ta nufa dan ta kawo masu breakfast nasu, jin muryar Gwaggo tayi tana cewa "A'a idan saboda mu zaki shiga dawo ki huta, don nariga na cika ciki na ban tsaya jiranki ba nida Sani muka ci." Daga nan Mummy komawa d'akinta tayi, duk da tana jin yunwar amma ji take ma ba zata iya cin komai ba. Koda Muhdeen ya shiga d'akin Umma ya samu zaune a bakin gadon, sai Mama Huraira ce a gefenta sai wasu mata guda uku mak'otan Umma da suka zo dubiya. "Assalamu alaikum" Gaba d'ayansu suka amsa sallama, ya k'araso ya durk'usa ya gaishe su cikin girmamawa tare da k'ara tambayar Umma da jiki, suka amsa masa da sauk'i. Dube-dube yake kamar mai neman wani abu, ya kasa magana da dukkan alamu Inteesar bata cikin d'akin, tamabayar kansa yake ko ina take ko tana toilet ki kuma ta fita tayi sallah ne, to ai kuma ga d'akin yau akwai wajen sallah bai cika ba irin na wancan ranar, Mama Huraira ce ta lura kamar akwai abunda take nema ta kalle shi ta ce, "Muhammad akwai abunda kake nema ne?" Murmushi yayi tare da cewa "Bakomai na d'auka Inteesar tazo ne." Girgiza kai tayi tare da cewa "Gaskiya yau bata zo ba, ka barta a gida bata nan ne?" Ya rasa ma ta ian zai fara mata bayani,magana ya fara yana cewa "Dama munyi zata zo ne, to na d'auka ta iso ne ashe bata zo ba" Girgiza kai tayi "Bata zo nan ba gaskiya." Sallama yayi masu tare da cewa bari ya koma gidan kila bata samu fitowa bane. Mummy tana zaune kan sallaya tana azkar na yammaci, tana ta rok'awa Inteesar sauk'i a wajen Allah, bayan ta idar ne tana cire hijabin taji ana knocking a k'ofar bedroom nata, tasan Dady baya gida Mufida na asibiti Gwaggo na barci a d'akinta, mamaki ne ya kamata waye zai shigo har bedroom bak'o dai iya karsa falo,bada izinin shigowa tayi ta zubawa k'ofar idanu, ganin Muhdeen ne yasa ta tamke fuska dan ranta ya 'baci idan ta tuna da abunda yayiwa Inteesar. "Assalamu alaikum" Wa'alaika salam" Ya k'araso ya durk'usa k'asa ya gaishe ta "Ina wuni Mummy?" "Lafiya lau" Shiru yayi na tsawon mintuna biyar ba wanda yayi magana, d'agowa tayi ta kalle shi taga ya sunkuyar da kai kuma yana durk'she be zauna ba, kauda kanta tayi tare da cewa "Ya dai ina fatan dai lafiya?" "Lafiya lau Mummy, dama na d'auka tazo nan ne?" Kallonsa tayi tare da cewa "Wace ce ta zo nan?" "Inteesar nake nufi." "Ce maka tayi nan zata zo? to nidai banganta tazo ba, amma ka shiga d'akin kakarku ka tambaye ta ko tazo nan tana d'akinta kafin ta k'araso nan." Jinjina kai yayi tare da cewa "To bari naje na gani ko tana can" Mik'ewa yayi ta bisa da kallo ya fice don zuwa d'akin Gwaggo. Gwaggo na zaune a bakin gadonta tana cin goro Muhdeen ya shigo d'akin ba tare da yayi mata sallama ba, kaallon mamaki take masa tare da cewa "Yau naga ja'irin yaro d'akin kafura ka shigo da ba zakayi mani sallama ba? d'an banza mai suffan yahudu da nasara, ko nayi kama da kaba'ira ce da ba zakayi mani sallama ba." Bai tanka ta ba ita kuma bata fasa fad'a da take ba, kallonta yayi tare da cewa "Ba wannan ya kawo ni ba, Ina mata ta take?" Kallonsa take shek'ek'e take kafin ta ce, "Ka d'auke ta inda ka ajiye ta." Kauda kanta tayi ta cigaba da taunan goronta, ganin ta share sa ne yasa ya k'ara mata magana yana cewa "Bata gida kuma bata wajen Ummanta ba inda nake tunanin zata je da ya wuce nan." "Kai ka fita a Ido na, ka kiyaye ni na fad'a maka dan tsabar ka raina ni idan uwarka ce zaka shiga mata d'aki haka ne? ko kuma zakayi mata magana haka? Bansan inda matarka take ba ko ce maka tayi waje na zara zo da zaka titsiye ni da tambayar inda take? wata kila ma ba nisa tayi ba ta koma gida kazo kana damu na, ka fitar mani a d'aki ko yanzun nan na kira ubanka a waya yazo yayi mani iyaka da kai." "Ank'i a fata daga d'akin naki" "Haka ka ce?" "Eh haka na fad'a kuma haka kika ji." Wayarta ta ciro daga k'asan filo tana cewa "Yanzun ubanka zai mani katanga da kai." Tana shirin kiran wayar Dady bayan ta lalaubo number dak'yar tana kashe ido dan bata gane wayar sosai, tana kara wayar a kunnenta. Cikin zafin nama ya fisge wayar, tare da sakawa a aljihu ya kalle ta ya ce "In banda masifa da kika saba da shi daga tambaya ina mata ta sai bak'ar magana?" "Ka bani waya ta kuma kaje can gida matarka nasan tana gida ba inda zata tafi ba saninka." Jefa mata wayar yayi sannan ya nufi k'ofar fita, jin muryarta yayi tana cewa "Ka jefi uwarka Fatima amma ba ni Kulu ba" Har ya tsaya zai bata amsa ya kuma yi ficewarsa ya barta tana ta masifa ita kad'ai. A can gida kuwa Sumayya da taji yunwa na neman illata, ta sai ta kira Ishaq Direba ta aike sa yayo mata takeaway, tana zaune tana ci ya turo k'ofa ya shigo, dube-dube yake ganin bata falon ne yasa ya nufi d'akinta nan ma bata nan, kallon Sumayya yayi tare da cewa "Har yanzun Wai bata dawo ba?" Ta'be baki tayi tare da cewa "Dama ka daina wahalar da kanka akan nemanta." Wani banzan kallo ya mata "Akan me kika ce haka?" Gani nayi akan me kake wahalar da kanka bayan ta fita bata sanar da kai ba, ka fita harkarta kawai "Karki sake mani magana makamancin wannan, ke idan zaki fita sanar dani kike yi? ba gara ma ita da ke ba, nasan dai ba zata ta'ba fita gidan nan ba tare da izini na ba, sai dai idan wani abu daban ne, ke tunda na aure ki dai-dai da rana d'aya baki ta'ba bin magana ta ba, ko kibi abunda nake so bakiyi, kina mani biyayya a matsayi na na mijinki wanda mukayi auren soyayya da ita, ita Inteesar ba auren soyayya muka yi ba, hasali ma na tsane ta bana son ganinta, koda aka aura mani ita haka na dinga wahalar da ita da bautar da ita da ayyukan wahala, bana barin ta huta haka zan dinga wahalar da ita ba tausayawa, hakanayyukan da ba sai tayi ba haka zan saka ta yi bana bari ta huta, amma duk da haka tana kallo na a matsayin mijinta bata ta'ba nuna mani 'bacin ranta ba, kwanakin baya Mahaifiyar k'awarta ta rasu Mufida ta biyo mata su tafi, haka tasa Gwaggo ta Kira waya ta har na bada izini sannan ta tafi, shekaranjiya na same ki d'aki kina shirin zuwa oarty, na nuna maki kada ki tafi, ina da buk'atarki haka kikayi fatali da buk'ata na mijinki kika fita ba tare da izinin mijiki ba, ina cikin halin buk'atar mace kika tadi kika barni, Allah da ikonsa sai ya turo mani ita a dai-dai lokacin da ya dace, gashi bata cikin kwanciyar hankali kuma ga mahaifiyarta kwance ba lafiya, a haka na nuna mata buk'ata ta kuma ba gardama ta amince mani saboda tasan girman hakkin mijinta kan wuyanta tasan laifin bijirwa miji masifa ce, amma ke baki San hakan ba, matar da akan rashin lafiyar Umma bata tafi ba sai da ta nemi izini na sannan ta tafi, wani uzurin kuma zaisa ta fita ba izini na." Kallon mamaki take masa har ya gama maganarsa, sannan ta ce "Kana nufin ta ta fini kenan ?" "Kee Sumayya wallahi ki kiyaye ni, a halin yanzun raina a 'bace yake kada ki tunzura ni, dan idan kika tunzura ni zan aikata abunda daga ni har ke bazai muna dadi ba, Dan haka ki kiyaye ni kafin yanzun nan Kisha mamaki, dan zan aikata abunda daga ni har ke bazai muna dad'i ba, karki manta da wannan." Daga nan ya fice ya barta zuciyarta na tafarfasa, tana mamakin wai yau ita Muhdeen ke fad'awa haka. Mummy na zaune a d'akinta tana tunanin halin da Inteesar ke ciki, wayarta ce ta fara ringing ganin Mufida ce tasa ta d'aga ta rawar jiki kafin tayi magana Mufida ta ce, "Mummy Albishirinki." Murmushin farin ciki tayi ta ce "Goro ta farfad'o ne?" Mufida ta kalli Inteesar dake zaune ta jinjina bayanta da filo ta ce, "Eh Mummy gata nan zaune wallahi na tambaye ta me ya same ta muka same ta kwance cikin jini da kwalabe, tayi mani shiru bata bani amsa ba, amma idan kika zo kila tayi maki magana, duk maganar da nake mata bata ce komai ba kallona kwai take kamar wata kurma." Shiru Mummy tayi tana nazari kafin tace, "Ina Doctor take?" "Yana office nasa" "Yasan ta farfad'o?" "A'a bai sani ba." "To kiyi sauri ki sanar dashi yanzun nan, nima gani nan zuwa." Daga nan ta katse kiran ta d'auki mayafinta da handbag ta nufi hanyar fita. *Daga alk'alamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love you oll😍😘 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. *SADAUKARWA* Wannnan shafin naki ne Faty mannir ina jin dad'in comment naki, don haka na sadaukar da wannan shafin a gare ki naki ne, kiyi yadda kike so da shi, sauran members na INTEESAR ma ina godiya da da comments had'i da add'ar da kuke mani Allah yabar k'auna. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page6️⃣1️⃣ Daga nan ta katse kiran ta d'auki mayafinta da handbag ta nufi hanyar fita. Kici'bis suka yi da Dady wanda shigowarsa kenan daga waje, ganin yadda take sauri yasa ya ce, "Ina kuma zuwa haka?" Shiru tayi tana nazari kafin ta ce "Asibiti" "Waye kuma baida lafiya" Jim tayi kafin ta ce, "Inteesar" A kid'eme ya kalle tare da cewa "Subhanallahi me ya same ta?" A juyar zuciya ta sauke "Alhji dogon labari ne ba lokaci muje kawai." Kallon k'ofar d'akin Gwaggo yayi tare da cewa "Ina Gwaggo" "Tana d'akinta barci take" Fita sukayi inda ta umarci Direbanta ya kaisu asibitin da Inteesar take, shiga sukayi bayan motar aka jasu zuwa Asibiti. Zaune take akan gadon marasa lafiya kanta an nad'e shi da bandeji,Mufida na zaune a gefenta Doctor yana tambayarta yadda take ji ko akwai abunda ke damunta, kai kawai ta girgiza alamar ba komai. Mummy ce ta turo k'ofar ta shigo Dady na biye a bayanta, k'arasawa tayi kusa da Inteesar ta rungume ta hawaye tab a idanunta ta fara magana "Sannu Daughter ya jikin naki?" Take hawaye suka dinga ambaliya daga fuskarta kamr an bud'e famfo, Mummy tasa hannayenta tana goge mata hawayen tana cewa "Ki daina kuka Daughter zaki samu lafiya, insha Allah komai zaizo k'arshe da yardar Allah." Jabeer ne ya turo k'ofar ya shigo, ganin Inteesar zaune yass ya saki murmushi tare da cewa "Alhamdulillah" Kallonta yake yana cewa "Ashe ta farfad'o" Dady dai baisan me ya faru ba kuma baisan dalilin kwanciyarta Asibiti ba, kallon Mummy yayi tare da cewa "Accident ta samu ne?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "Sai dai idan mun koma gida muji daga bakinta amma yanzun kam bansani ba." Kallon Doctor yayi tare da cewa "Yaushe za'a iya sallamarta?" "Dama ba wani abu da zamuyi mata tunda ta farfad'o, sai dai ciwon kai da ba'a rasa ba, kuma zamu bata magungunan da zata dinga sha." Fita yayi tare da sanar dasu yana zuwa "Inteesar ce ta fashe da kuka tana cewa, "Mummy dan Allah kada ku mayar dani gidan Yaya wallahi bazan iya jurar zaman gidansa ba." Ta k'arasa maganar tana mai sake fashewa da wani sabon kukan, rungume ta Mummy tayi tana cewa "Daina kukan haka nan ba zaki koma gidansa ba kinji? ki kwantar da hankalinki ba zaki koma can ba, haka Mummy ta dinga rarrashinta saosai har tsagaita da kukan da take, shi dai Dady abun ya d'aure masa kai, don baisan me ke faruwa ba, ganin yadda Inteesar ta rikice yasa yayi shiru yana jiran su koma gida. A cikin mintuna talatin aka sallame su suka koma gida inda Jabeer ma ya bisu. Da sallama suka shiga cikin falon Gwaggo tana zaune kan kujera tana kallon T.V Africa Tv3 inda suka saka wa'azin Shekh Jabeer Sani mai hula. Amsa masu sallama tayi tare da zuba masu ido, ganin Inteesar yasa ta mik'a ta sauri tana salati "Inalillahi wa'inna ilaihi raji'un, na shiga uku ni kuluwa me ya same ki 'yar albarka naga anbi an nannad'e maki kai da bandeji?" Ba wanda ya iya magana cikinsu k'arasowa sukayi suka zauna yayin da Inteesar ta k'arasa wajen Gwaggo ta zauna a saman center carpet kusa da kujerar da Gwaggo take zaune, kallonta Gwaggo tayi tare da cewa "Kada dai zargin da nake akanki ya tabbata, mijinki yazo nemanki ya ce baki gida kin fita kada dai a ce hakkinsa ne ya kamaki da kika fita ba tare da saninsa ba kika samu hatsarin mota naga an wani yi maki rawani da bandeji." "Bayan sun zauna ne Dady ya kalli Mummy ya ce wai me ya same ta kuma ina mijinta?" Mummy ce ta kalli Mufida ta ce, "Ki fad'a masu abunda

Chapter 27 of 38