Share this page
da yake yi. Koda ya k'arasa k'ofar gidaan Salisu ya same sa yana jiransa, Salisu me ya k'araso ya bud'e murfin motar Muhdeen ya shiga ciki, hannu ya mik'a masa suka gaisa kafin ya ce, "Mutumi na lafiya kake kuwa? naga kayi wani zuru-zauru?" Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, Ba dole kaga na rame ba?Salisu ina cikin tashin hankali?wallahi akwai damuwa sosai a tattare da ni, banga Inteesar ba tun jiya da safe rabo na da ita, tunda aka kira ni da sassafe a Asibiti akayi mani kiran gaggawa na tafi na barta tana barci, koda na dawo gida da rana banganta ba, abu kamar wasa har yau ba ita ba labarinta." "Inalillahi wa'inna ilaihi raji'un,kunyi fad'a da ita ne? yasa ta tafi ta barka?sannan yakamata ka je gidan iyayenta dan ba zata wuce can ba." "Salisu bata gidan iyayenta kuma bata gidan iyayae na, nasa Mufida ta kira dukkan k'awayensu ta tambaye su ko ta je can, nan ma sun tabbatar da cewa bata gidansu, duk inda yakamata ace ta je bata nan." "Kuma bansan inda ta shiga ba, kuma ni fargabar da nake kada ya kasance ta fad'a mugun hannu, idan wani abu ya same ta bazan iya jurewa ba." Ajiyar zuciya Salisu yayi tare da cewa "To yanzun neye mafita?" "Ko zamuje police station ne da gidan redo ko Allah zaisa a dace." Take Muhdeen yayiwa motar key suka tafi police station, sukayi report daga nan suka nufi gidan redio ,bayan sunbar gidan redio ne suna tafiya akan hanyarsu ne yayi parking a gefen hanya, Salisu ya kalle sa ya ce, "Lafiya ka tsaya ko akwai wata matsalar ne?" Girgiza kansa yayi cikin yanayi na damuwa da yake ciki ne ya kalle shi ya ce, "Wane lafiya kuma zaka tambaye ni? bayan kasan halin da nake ciki ai ba lafiya, har sai ranar da naga mata ta sannan hankali na zai kwanta." "Kada ka damu ka kwantar da hankalinka addu'a ce kawai mafita a gare ka, duk abunda yayi tsanani sauk'i na zuwa, insha Allah zamu same ta cikin k'oshin lafiya Allah zai bayyana muna ita aduk inda take, nasan yadda kake ji a zuciyarka amma amma ka daure kayi ta addu'a har Allah ya bayyana mata." Murmushi Muhdeen yayi tare da cewa "Naji dad'in kalamanka Salisu har cikin raina, hak'ik'a tunda wannan abun ya faru ba wanda ya ta'ba fad'a mani magana mai dad'i kwatankwacin wanda ka fad'a mani, ba wanda ya nuna damuwarsa akan lamari na sai kai, hatta aminina Jabeer bai damu da halin da nake ciki ba, babbar abunda zai baka mamaki ma Mummy da Dady cewa sukayi wai na nemo ta duk inda ta ke." Haka Salisu yayi ta bashi baki yana kwantar masa da hankali, sai da ya tabbatar ya d'an saki ransa kafin suka cigaba da tafiya, sauke shi yayi a k'ofar gida inda ya ajiyae shi kafin yaja motarsa ya nufi gidansa. Koda ya shiga ba kowa a falo don ko motsin Sumayya bai ji ba, da alama bata gidan ta fita kenan, kai tsaye d'akinsa ya nufa, lokacin k'arfe d'aya na rana komai baici ba bai sha ba, rabonsa da abinci tun jiya da yasha yoghurt bai sake saka ko da ruwa a cikinsa ba, gashi wani masifaffen yunwa yake ji na addabarsa amma baya jin zai iya cin abincin duk da yunwar da ta addabe shi, toilet ya shiga yayi wanka ya fito ya saka kaya ya nufi masallaci, bayan an idar da sallah ne yayi addu'a sosai akan Allah ya bayyana masa Inteesar. Daga masallaci gida ya dawo a falo ya d'an kishingid'a, ba abuda yake tunani sai Inteesar, tuna yadda ya dinga wahalar da ita da azabtar da ita tun kafin aurensu har ya zuwa bayan aurensu, ya tuna irin biyayyar da take masa duk k'untatawa da yake mata bata ta'ba tsallake maganarsa ba, duk abunda ya umarce ta da tayi sai tayi shi koda hakan zai zama bak'in cikinta ne, zata yi masa indai zai faranta ransa, bata damu da halin da zata shiga ba. Nadama ce ta kama sa tare da danasanin abunda yayi mata a baya, tabbasa da zai ganata yanzun zai gyara kura kuransa ne, ya nuna mata kulawa da k'aunar da yake mata, yana nan zaune ya shagala da tunani bai ankara ba sai jin Kiran sallar la'asar yayi, mik'ewa yayi ya d'auro alwala ya nufi masallaci, kuma har lokacin baici komai ba a cikinsa, bayan idar da sallar ne ya d'auki motarsa ya koma gidan iyayensa. Da sallama ya shiga falon Mummy ce zaune a falo, amsa sallama tayi masa tare da kallonsa, ganin yadda ya rame cikin k'ank'anin lokaci yiyi zuru-zauru kamar ba shi ba, mamaki ne ya kamata ganin ramar da yayi, a tunaninta baya son Inteesar kamar yadda ta sani, amma yanzun ganin yadda ya koma ne yasa ta shakku akan abunda ta sani, domin kuwa don idan baya sonta bai kamata a ce ya shiga damuwa har haka ba, kenan yana sonta? to me yasa ya wulak'anta ta alhalin ya damu da ita har haka, uwa uwa ce duk da tana fushi da shi amma bata ji dad'in ganinsa haka ba. K'arasowa yayi ya durk'usa a gabanta "Ina wuni Mummy?" Ba yabo ba fallasa ta amsa masa "Lafiya lau" Zama yayi a saman center carpet dake falon, daga shi har Mummy ba wanda yayi magana, ganinsa tayi da alamar yunwa a tattare da shi, dan haka ta kalle shi ta ce, "Ka zo ka ci abinci" Bata jira cewarsa ba ta nufi dinning area, bin bayanta yayi duk da ba jin cin abincin yake ba amma yaji dad'i, ganin Mummy wannan karon ta d'an kula da shi, zama yayi a d'aya daga cikin dinning d'in tayi serving d'insa, white rice and stew ne da ya ji naman kaza, kunun aya da ta zuba masa a cup ya fara sha, take gabansa ya fad'i, don tabbas idan har Inteesar tayi masa kunun aya haka yake jin d'and'anonsa, abincin ya d'eba da cokali yakai bakinsa ya tauna a zabure ya mik'a tsaye, kallonsa Mummy tayi tare da cewa "Lafiya kuwa?" "Mummy ina take?" Da mamaki ta kalle shi ta ce, "Wake nen?" "Mummy Inteesar tana gidan nan, me yasa aka mani haka?" "Waye ya ce maka tana gidan nan?" "Mummy ba wanda ya fad'i mani amma tana gidan nan, don wannan abincin da na ci tabbas ita ta dafa shi, wannan kunun aya ma ita ce ta had'a shi, tunda na d'and'ana abincin nan nasan ita ta girka shi wannan d'and'anon girkinta ne, nasan d'and'anon girkinta nasan naki wallahi Umma ita ce ta girka shi, kuma tana cikin gidan nan." Mik'ewa yayi ya nufi falo yana k'wala mata kira da k'arfi "INTEESAR! INTEESAR!! INTEESAR!!!" Inteesar dake zaune a akan sallaya sanye da hijab, tunda ta idar da sallar la'asar bata tashi ba ta zauna tana azkar, gabanta ne ya fad'i jin muryarsa yana k'wala mata Kira yasa gabanta ya fad'i ta furta kalmar "Inalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Dama ita kad'ai ce a d'akin Mufida ta fita Mummy ta aike ta gidan Aunty Abla, Gwaggo dake d'akinta ta fito tana cewa "Wannan kuma haukar me yake mana a gida ne? Kazo kana d'agawa mutane murya ." Ranasa a 'bace yake kallon Gwaggo, yana shirin bata amsa ne sai idonsa ya sauka akan dady dake saukowa, kallon fusakar Dadyn yayi a murtuk'e ya ce, "Muhammad fitar mani a gida." Da ya ke kallon Dady jin kalmar bakinsa, bud'e baki yayi da niyyar magana Dady ya d'aga masa hannu alamun dakatarwa ya ce, "Get out in my house" Yadda yayi maganaar a tsawa ce, da ganin irin 'bacin ran da ya gani a fuskar Dady yasa ya nufi hanyar fita. A harabar gidan ya had'u da Mufida da suka dawo da Direb, ganinsa ta tasan akwai damuwa, da har zai wuce sai ya tamabaye ta "Da Inteesar tazo gidan nan mai ta sanar da su Dady da Mummy ne?" "Nima ban sani ba" "Kada kiyi mani k'arya ki sanar da ni gaskiya, me ke faruwa da kowa ya d'auki zafi da ni." "Yaya ai dole kowa ya d'auki zafi da kai, da badon Allah yasa munje gidanka ba kuma Allah yasa tana da sauran numfashi ai da wani zancen ake ba wannan ba." Kallon rashin fahimta yake mata kafin ya sake tambayarta "Kamar ya please ki sanar dani abunda ya shige Mani duhu." Ajiyar zuciya ta sauke sanan ta bashi labarin yadda suka tafi gidansa ita da Mummy, suka tarar da Inteesar kwance bata numfashi, kanta na fitar da jini, ta kuma tabbatar masa da cewa Sumayya ce tayi yunk'urin kashe Inteesar, take idanunsa suka kad'a zuwa ja jikinsa gar rawa yake, ya. nufi motarsa cikin k'unar rai da fusata ya shiga motarsa, key yayi mata ya dinga danna horn sai da kiwa ya firgita da yadda ya dinga horn, Mallam Ibrahim mai gadi ya wangale masa gate ya fita a guje zuciyarsana masa zugi, Mallam Ibrahim ya kalli bayan motar ya ce, "Allah dai ya kiyaye hanya amma wannan tuk'in akwai hatsari a cikinsa." *DAGA ALK'ALAMIN*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Don k'arin bayani* 09065327995 Love you oll😍😘 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page6️⃣4️⃣ "Allah dai ya kiyaye hanya, amma wannan tuk'in akwai hatsari a cikinsa. Driving yake kamar zai tashi sama, gaba d'aya Allah kawai ne zai kaishi gida lafiya, gudu kawai yake akan titi kamar zai tashi sama. Sumayya kuwa tana cikin bedroom d'inta zaune saman gado, waya ne kare a kunnenta, tana magana tana cewa "Ba haka bane shila har yanzun mutumin a sama yake, tunda waccan 'yar matsiyata aka rasa inda take gaba d'aya hankalinsa na kanta, ko damuwa dani baya yi, ina naga sakin fuska a wajensa daga na fad'i magana akanta kinga yadda ya hauni da fad'a kamar zai cinye ni d'anya?" Banko k'ofara d'akin yayi da k'arfi, a firgice ta mik'e tsaye tana kallonsa ganin fuskarsa ba alamun rahama be yasa zuciyarta tsinkewa, ganin yadda yanayinsa da fuskarsa suka canza ne yasa ta fara ja baya, cikin k'arfin hali ta bud'e baki ta fara magana "Baby lafiya kuw..." Kafin ta kai k'arshen zancenta taji ya sauke mata tagwayen maruka biyu a kumatunta, d'ayan kumatun ma haka ya sake sauke mata tagwayen maruka biyu, jiri ne ya fara d'ibanta, don tunda take a rayuwarta ba'a ta'ba marinta ba sai yau, yau d'in ma maruka hud'u lokaci guda, k'eyarta ya rik'e ya buga goshinta a bango take sai goshinta ya fashe jini ya fara fita, wuyanta ya shak'e wajen mak'ogoronta ya rike take ta fara kakari idanunta suka fito waje miyau ya fara dalala daga bakinta, cikin kakkausar murya ya fara magana. "Zaki kashe ta ko? to kafin ki kashe ta ni zan fara kashe ki, a kin had'ani da iyaye na suna fushi dani duk ta sanadiyarki, baiwar Allah da bata maki laifin komai ba kike neman kashe ta, dama Gwaggo ta fad'a mani cewa ke ba matar aure bace amma na dinga k'alubalantarta, amma gashi naga gaskiyarta a yanzun." Jifa da ita yayi gefe sannan ya nufi hanyar fita yana huci, ita kuma yanda yayi jifa da ita ta zube wajen ko numfashi bata yi. A can gidansu Mummy kuwa bayan fitarsa ne da Dady ya kalli Mummy ya ce, "Waye ya sanar da shi cewa tana gidan nan?" Mummy ce ta kalle shi tare da cewa "Ba wanda ya fad'a masa , daga ya ci abinci shine fa ya ce wai ita ta dafa abincin nan wannan d'and'anon girkinta ne, daga nan ya dinga k'wala mata kira." Shiru Dady yayi yana nazari, tabbas ya gane cewa Inteesar ce ta dafa masu abincin, don shi dama haka ya ke tun yana yaro indai ya d'and'ana abincin da ba mahaifiyasa ce ta dafa ba ya sani, yana ganewa Dan a lokacin Dadynsa har yana mamakinsa sai yanzunn ya ke tunowa da wani abun, wato har girkin Inteesar ma yana ganewa, gajeren murmushi Dady yayi tare da komawa ciki, Mummy ce ta kalle Gwaggo ta ce, "Lamarin nan fa ya fara d'aure mani kai." Dariya irin ta su ta manya Gwaggo tayi tare da cewa "Ba abunda ke d'aure mani kai a lamarin su, ki zuba ido kawai kada ki ce komai." Da misalin k'arfe takwas na dare ne Sumayya ta soma tari a hankali, dak'yar ya iya tashi zaune saboda tana rik'e da mak'ogoronta da ke mata zafi, goshinta dake mata rad'ad'i ta kai hannu ta shafo shi,jin yadda ya fashe ya kumbura ga jini da ta shafo, kuka ta sake da shi mai cike da tsantsar bak'in ciki da takaici, jikinta gaba d'aya ji tayi yana mata ciwo, dak'yar ta lalla'ba ta shiga toilet, tana kuka tana wanka har ta gasa jikinta, har zuwa wannan lokacin mak'oshinta na mata ciwa ga goshinta sai zugi yake mata, raki da son jiki bai bari ta gasa wurin ba. Haka ta ta fito ta zube a Kan gado, don dama sallah bai dame ta ba ko da kafiyarta ballantana yanzun da ba lafiyar,kuka ta cigaba da yi, wayarta ta kalla inda ta fad'i k'asa lokacin da Muhdeen ya mare ta, tashi tayi ta d'auko wayar tare da lalubo number Dad dinta, sau uku tana jaraba Kira amma bai shiga ba, kuma ba zata iya kiran Mum d'inta ta sanar da ita ba, dan tunda ta lura Mum ta daina goyon bayanta ta daina sanar da ita halin da take ciki, kwanciya tayi a kan gadon har barci ya d'auke ta. A 'bangaren Muhdeen kuwa shima haka ta kasance a gare shi, ya kwana cikin bak'in cikin abunda Sumayya ta aikata, wanda a dalilin haka kowa na fushi da shi, duk da cewar shima da nasa laifin amma nata ya janyo wannan matsalar har aka kawo wannan matakin, dan shi yanzun yayi niyyar gyara zamantakewarsa da matarsa, ya mantar da ita rayuwarsu na baya. A haka dai bai samu isashshen barci ba har k'arfe hud'u na asuba, toilet ya shiga yayi wanka ya nufi masallaci. Daga masallaci ya zauna yayi azkar da karatun al'qur'ani mai girma, sai k'arfe bakwai sannan ya dawo gidan, yana tafiya yana tunanin yadda zai fuskanci Dady da Mummy da Gwaggo akan Inteesar, amma ko ba komai ya samu sassauci a cikin zuciyarsa, kaso hamsin ciki d'ari na damuwar da yake ciki ya ragu, domin yanzun yasan cewa Inteesar bata mugun hannu, duk da dai akwai babban aiki a gabansa. A falo ya had'u da Sumayya tana zaune kan kujera tana cin snacks da yogurt, don dama aikinta kenan tunda bata iya girki ba sai dai tayi ta fama da kayan su biscuits cake da sauransu, tana zaune tana tsaka da cin snacks ne ya shigo, sai da gabanta ya fad'i dan wani tsoronsa ne ya shige ta, ko kallonta baiyi ba har ya wuce ta zai nufi d'akinsa ya tsaya ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "Kada ki sake kwana mani a gida, ki tattara naki ya naki kibar mani gida na." Daga nan ya shige d'akinsa, kuka ta saki tana cewa "Dan Allah kayi hak'uri ka gafarce ni wallahi bazan sake ba, kayi mani alk'awari na zamu rayu har k'arshen rayuwarmu ba zamu rabu da juna ba, wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba dan Allah kayi hak'uri, soyayyar da nake maka ne ya saka ni cikin wannan halin. Bai saurare ta ba ya shigewarsa d'akinsa. A guje ta ruga d'akinta wayarta ta d'auka tana kuka, lamabar Jumy ta kira bugu d'aya ta d'auka, tana d'auka Sumayya ta fashe da kuka ta fara magana "Jumy na shiga uku, Muhdeen ya kore ni ya ce nabar masa gidansa." Cikin mamaki ta ce, "What! akan me ya kore ki?" Cikin muryar kuka ta fara magana "Jumy ya gano gaskiya cewa nayi yunk'urin kashe Inteesar." "Me kika ce? ta yaya ya gano gaskiya? ko dai bata mutu bane?" Jinjina kai tayi kamar tana ganinta ta ce "Ina tunanin bata mutu ba, kuma ta sanar cewa nice nayi mata wannan aiki." "To yanzun ina ita yarinyar take?" "Nima ban sani ba, amma da alamar ya sani tunda har yasan nayi yunk'urin kashe ta, kinga ta sanar da wani kenan, Jumy wallahi jiya na d'and'ani k'amshin mutuwa, kwana na ne kawai a gaba." "To yanzun da ya ce kibar masa gidansa Ina zaki je? London zaki koma?" "Ba inda zanje Wallahi, bazan ta'ba rabuwa da shi ba, ni da shi takalmin kaza mutu ka raba." "Kada fa yazo ya wulak'anta ki." "A shirye nake da na fuskanci ko wane irin wulak'anci daga gare shi, amma bazan tabu da shi ba." Ajiyar zuciya Jumy ta sauke ta ce "Shikenan, Allah ya bada sa'a." Daga nan ta katse kiran ." Tana nan zaune har tsawon mintuna talatin, turo k'ofar yaayi ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "Kada na dawo gidan nan na tarar da ke, don wallahi zaki sha mamaki a waje na." Daga nan ya fice tare da buga k'ofar da k'arfi,. kuka tan saki, domin Alah ya sani ba zata iya rabuwa da, gaba d'ya hankalin ta yatashi. Wayar ce ta k'ara d'auka tare da Kiran shila a waya, labarin abunda ya faru tabbata, sannan ta cigaba da cewa "Wallahi bana son rabuwa da shi, ya zanyi ya hak'ura ya barni, so nake mu cigaba da zaman mu, meye mafita? "Ajiyar zuciya shila ta sauke tare da dogon tunani ta ce, "Ina zuwa k'awa ta zan kira ki" Katse kiran tayi ta nufi k'ofar d'akinta da taji ana knocking. Acan gida kuwa tunda Gwaggo ta shiga d'akinta Inteesar ta bita a baya, Gwaggo na zama Inteesar ta fad'a jikinta tare da sakin kuka, cikin tashin hankali Gwaggo ta d'ago ta tana cewa "Yar albarka me ya faru kuma kike kuka?" Cikin kuka ta fara magana "Gwaggo kada ki mayar dani" Kada mu mayar da ke Ina?" "Gidan Yaya" Murmushi Gwaggo tayi tare da cewa "Akan wannan shine kike kuka? to ki kwantar da hankalinki tunda baki so ba zaki koma ba." Cikin kwantar da murya tayi magana "To kiyi mani alk'awari" Dariya Gwaggo ta sake yi sosai ta ce,. "Nayi maki alk'awari sai dai idan kece kika nuna kina kina son cigaba da zama da shi, idan ba haka ba ki d'auka aurenku ya rabu." Dariya tayi sosai tare da cewa "Ni ba abunda zaisa nayi sha'awar komawa gidansa, daga shi har matarsa basu da imani, kashe ni zasuyi idan na cigaba da zama da su." "Ba zasu kashe ki ba sai dai idan kwananki ne suka k'are." "Gwaggo kenan haka zancenki yake, amma ni kad'ai nasan wahalar da nake sha a gidansa." "Dalla matsa ki bani waje, kinsan da haka shine na je gidanku tsawon wata d'aya baki sanar da ni halin da kike ciki ba? " "Gwaggo yadda yake nuna mani so da kulawa, da nace zan fad'a maki ba zaki yarda dani ba, saboda wayau ne da shi,yasan me yakeyi shiyasa ya ya dinga mani abubuwan da yake dan ki yarda da shi " "Shikenan yanzundai ba inda zaki koma." Cikin jindad'i ta jinjina kanta alamar gamsuwa da maganar Gwaggon . Sumayya na zaune tana jiran Kiran wayar sha ta shigo wayarta, sai kuwa ga Kiran nan ya shigo, da saurinta ta d'aga tare da cewa "Yauwa k'awa ta naji kince mafita d'aya ce zaisa na cigaba da zama da Muhdeen me ne ne?" Ajiyar zuciya shila ta sauke tare da cewa "Nasan ko na fad'a maki ba zaki amince kiyi ba, amma nasan hakan ne kawai mafitar da zaisa ku cigaba da mallakar juna, idan kuma baki amince kinyi abunda nasa ki ba to lallai ba ke ba Muhdeen yafi k'arfinki kina ji kina gani." "Kinga kada kiyi shakka akan komai don ba abunda bazan iya aikawa ba akan na cigaba da mallakarsa." *DAGA ALK'ALAMIN*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Don neman k'arin bayani* 09065327995 Love you oll😘😍 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Idan har kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na bud'e wannan, duk abu d'aya, sannan idan har kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group don ko kin shiga indai baki comments zan fitar da ke ne. *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. Page6️⃣5️⃣ "Kinga kada kiyi shakka akan komai, don ba abunda bazan iya aikatawa ba akan na cigaba da mallakarsa." 'Dan jim Shila tayi kafin ta ce, "Ki shirya ki tafi gidan Dadynsa da Mummynsa ki nuna nadamarki, sannan ki rok'e su gafara kin tuba ba zaki sake aikata abunda kika aikata ba, nasan suna da mutunci da karamci, ba zasu banzatar da ke ba, musamman idan suka ga abunda d'ansu ya aikata maki, nasan zasu kar'be ki hakan zaisa suyi masa maga..." Tun kafin takai k'arshen maganar da zata yi Sumayya ta katse ta tare da cewa "Bazan iya ba." Sakin baki Shila tayi cike da mamaki ta ce, "Lallai kuwa baki shirya zama da mijinki bane, kuma baki da wani za'bi da ya wuce ki nemi wad'anda zasuyi masa magana ya hak'ura, kinga sai ku cigaba da zama tare da shi, amma idan ba haka ba yadda ya zuciya da ke bazai saurare ki ba." Nidai ki bani wata shawarar amma ba wannan ba, dan gaskiya bazan iya zuwa gidansu na sanar da su ba, dan ba k'aunata suke ba, musamman wannan kakarsa ta tsane ni sosai wallahi, dan haka nima na tsane ta." Dariya shila tayi tare cewa "Idan 'bera na da sata daddawa ma tana da wari, haka nan kawai ba yadda za'ayi dangin mijinki su tsane ki, sai dai idan halinki ne zai sa su tsane ki, nasan halinki fa kuma dangin mijinki suna da mutunci haka nan kawai ba zasu tsane ki ba, idan kika girmama su kika d'auke su iyaye suma zasu d'auke ki 'yarsu." "Kingama? to shawarki bata yi aiki ba ki kawo wata." "To kije ki nemi abokinsa Wanda kika san yana d'aukar shawaransa ki sanar da shi, kuma ki rok'e sa ya taya ki bashi hak'uri ya yafe maki." Jinjina kai tayi alamar gamsuwa da shawar shila ta ce, "Yanzun kikayi magana mai kyau, zan nemi abokinsa Jabeer duk da shima ba wai jini na ya had'u da shi bane, amma zanyi amfani da shi wajen cikar buri na." Sallama sukayi ta katse kiran. Number wayar Jabeer ta lalubo zata danna masa kira, lokacin ya fito zai shiga motarsa ya fita kenan ya ji wayarsa na ruri, ciro wayar yayi daga cikin aljihunsa ya duba, mamaki ne ya kama shi ganin mai kiransa a bayyane ya furta "Sumayya?" Zuba ma wayar ido yayi yana mamakin ya akayi ta kira sa, har wayar ta katse bai d'aga ba sai da ta sake kiransa a ya d'aga, yana d'agawa yaji muryarta ta fashe da kuka, gabansa ne ya fad'i dan shi a tunaninsa wani abun ne ya samu Muhdeen, cikin tashin hankali ya ce, "Subhanallahi Sumayya me ke faruwa? wani abu ne ya samu Muhdeen?" Kai ta girgiza kamar yana ganinta ba tare da tayi magana ba "Me ke faruwa ki sanar da ni mana." "Jabeer kana ina ne?" "Ina gida yanzun nake shirin zuwa Asibiti, akwai matsala ne?" "Dan Allah ka jira ni gani nan zuwa." "Okay ki hanzarta dan ina sauri." Daga nan ya katse kiran ya koma cikin gidan zuciyarsa cike da tarin tambayoyi, Maryam da ke zaune a dinning room tana breakfast, ta kalle shi ta ce, "Kayi mantuwa ne?" "A'a Sumayya ce ta kira ni wai tana son ganina, shine na dawo na jira ta." "Lafiya take son ganinka?" "Yadda naji tana kuka kam ba lafiya, akwai wani abun da ya faru." Ta'be baki Maryam tayi tare da cewa "Allah ya kyauta" "Ameen ya rabbi" Bayan ta kammala ta dawo ta zauna kusa da shi, suna d'an ta'ba hira. Bayan kimanin mintuna talatin aka turo k'ofara aka shigo da sallama, dukkansu a zabure suka mik'e suka Zuba mata ido cikin mamaki, ganin yadda fuskarta a kumbure, ga goshinta ya ffashe ya

Chapter 29 of 38