Share this page
karasa hada breakfast tajira mufida tayi breakfast sannan su tafi. A bangaren Muhdeen kuwa sai K'ara tsanr yarinyar yakeyi a cikin zuciyar sa.har ita kanta Inteesar din ta fahimci hakan.cewa baya kaunar ta Wanda ita kanta ta rasa dalilin da yasa haka.don ko had a ido sukayi zai galla Mata harara ko ta gaishe sa sai dai idan a gaban mutanen gidan ne yake amsawa idan basu nan kuwa ki ta gaishe say sai yayi tsaki ko ya harare ta Kwanci tashi asarar Mai rai.har muhdeen ya kammala karatun sa na likitanci ya dawo Nigeria inda Dady ya gina masa Babban Asibiti a nan cikin garin Minna.inda Jabir wato d'an yayan Dady zasu dinga tafiyar da asibitin a tare,don Shima abunda ya karanta kenan. Bayan an zuba kayan aiki an d'auki kwararrun ma'aikata sun fara aiki ba dadewa ne Muhdeen Ya tafi kasar Egypt bikin Abokin saWanda sukayi karatu a tare. *CIGABA LABARIN* Washe gari Monday ne Muhdeen ya shirya da sassafe zai tafi asibiti,kai tsaye ya nufi kitchen,don a tunanin sa Mummy na cikin kitchen din.ya nufi kofar kitchen d'in Yana cewa "Muummy da wuri yau zan fita a hada m"ani breakfast di..." Kasa karasa maganar yayi sakamokon tozali da yayi da Inteesar dake kokarin zuba ruwan shayi a cikin flask.bayan ta gama soya dankalin da kwai. Jin muryar muhdeen yasa ta juyo ta kalle shi tare da sunkuyar da kanta kasa tace "Barka da safiya Yaya" Tsuki yayi tare da niyar barin kitchen din Dai-dai lokacin Mummy ta shigo,ganin ta yasa ya k'ak'aro murmushn dole ya kalli Inteesar din cikin sakin fuska yace "Yauwa k'anwata kin tashi lapiya ko?" Daga kai tayi ta kalle shi ciki mamaki,ganin Mummy ne ta shigo kitchen din yasa tasan dalilin amsa gaisuwar ta da yayi. Don dama mummy tace ya dauke ta kamar Asiya da Mufida itama kanwar sa ce.murmushi mummy tayi tace "Yau da wuri zaka tafi asibitin kenan" Kai ya gyada tare da cewa "Eh kinsan sati daya kenan banje ba saboda tadiyar da nayi,Ga aiki sunyiwa Jabeer yawa" Kai Mummy ta jinjina tare da cewa Hakane, Inteesar had'a masa breakfast ya tafi Da sauri ya girgiza Kai tare da cewa "No ta barshi kawai sauri nake idan naje can zanyi." Ya fita daga kitchen din ransa a bace,Don yayi niyyar yin breakfast a gida ganin cewa Inteesar zata hada breakfast yasa ya fasa haka yayi masu sallama fita. Mufida ce ta fito daga dakin ta cikin hanzari ta shiga kitchen din,ta d'ebi ruwan tea kawai sai slice bread da ta dauki guda biyu.a kichen din ta zauna tayi breakfast din suka tafi suna sallamar mummy don'ton dama yanzun already sunyi late. Bangaren Muhdeen kuwa a office yasa aka kawo masa coffee,Yana zaune akan kujerar office dinsa ga tarin file a gaban say Yana shan coffee din a hankali wayar sa ce dake ajiye akan table din gaban sa ta Soma ruri duban yayi tare da murmushi Don yasan ita ce ke Kiran sa dai-dai wannan lokcin,murmushi yayi acikin zuciyar sa ya furta my Sumy daga wayar yayi ba tare da ya furta komai ba. *LONDON* Tana kwance saman gadon ta Jin yayi picking tace "Morning sweet" Daga can bangaren sa "Kina lapiya"? Lumshe idanu tayi sakamakon Jin muryar sa,sannan tace "Lapiya qalau wlh kana inane yanxun?" "Ina office ne,yasu Mum da Dad?" Ya tambaye ta Amsa masa tayi tare da cewa " suna lapiya yanxun haka ma sune suka sa na Kira ka akan maganar da mukayi dakai kan cewa ka turo magabantan ka ayi maganar auren mu Cikin Jin dadi yace Are you serious?Kai Amma naji dadin Jin hakan daga gare ki. Kinyimun albishir mai dadi da safen nan.ina komawa gida zan sanar da su Dady tunda dad dinki ya amince." Murmushi tayi kafin tace, "Kaima kasan duk abunda nace Ina so shi akaeyi mani,ban taba cewa Ina son Abu Mum da Dad suka ki mincewa ba Koda basa son Abu zasuyi mani don su faranta mani Rai." Jinjina Kai yayi kafin yace "Ai ke 'yar gata ce" Knocking k'ofar akayi sannan yace mata " Kinga I will call you when I'm done." Bata fuska tayi tace, "Oh Allah yanxun ba zaka iya Bari mucigaba da hirar mu cikin jindadi ba." Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace, "Karki damu zamuyi magana," Bai jira cewae ta ba ya katse kiran,sannan ya kalli k'ofar da ake knocking ya bada izinin shigowa. Jabeer ne ya shigo tare da Mika masa hannu sukayi musabaha ya zauna kan kujerar dake facing din muhdeen. Jabeer ne ya ce "Wato ka shigo ko ka sanar dani ko? dan banda nurse Hauwa da take sanar sani." Murmushi yayi tare da cewa "Wallahi nabar gida banyi breakfast ba,Ina shigowa nasa aka kawo mani coffee Ina jiran idan na kammala na Kira ka ne sai kuma na samu labari mai dadi." Ya Karasa maganar Yana sakin murmushi,Shima jabeer dtin yayi murmushi tare da cewa "To Masha Allah wani abun farin ciki muka samu da safen nan?" Fara'ar sa ce ta karu yacigaba da cewa "Sumy ce take sanar Dani cewar mahaifin ta yace na turo magabata na a sa Mana ranar aure" Take fara'ar dake Kan fuskar jabeer ya dauke,ya shiga damuwa nan take.domin yasan sumy sosai tunda dukkan su tare sukayi karatu a America tare,Sam bata da tarbiyya bata San darajar dan aadam ba.yadda kasan ba 'yar musulma ba idan kayi la'akari da shigar ta da dabi'un ta sallah ma Bata Dame ta ba,sunan ta kawai zakaji kasan cewa musulma ce. Ido muhdeen ya zuba masa Yana karantar yanayin sa.kafinya ce "Yadai bro lapiya?" Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.NT (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wanna kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa. Page0️⃣8️⃣ Ajiyar zuciya Jabeer yayi tare da kallon Muhdeen cikin kwantar damurya ya ce, "Amma da zaka bi shawara ta daka rabu da Sumy baby domin bata dace da Kai ba" Wani irin kallo Muhdeen ya watsawa jabeer tare da cewa "Meye dalilin ka?" Jinjina Kai jabeer yayi tare da cewa, "Dalilai da yawa ma kuwa, Na farko, yarinyar Nan bata da kamun Kai Na biyu,Bata da tarbiyya Na uku yarinyar bata San darajar d'an Adam Shigar ta da dabi'un ta sunsha ban-ban da ta 'ya'ya masu mutun..." Muhdeen ya daga masa hannu ta alamun dakatarwa cikin bacin rai ya nuna masa hanyar kofa tare da cewa, "Fice mun da ga office" Kallon mamaki jabeer yayi masa yace "Dan na fadi gaskiya shine kake korata?" Cikin daure fuska muhdeen ya furta "Dama na Dad'e da sanin baka k'auna ta da sSumayya,bansan me tayi maka da yasa ka tsane ta na lura da hakan tunda dadewa.kuma Bari kaji aure na da sumayya babu fashi baka Isa ka hanani auren ta ba." Gajeren murmushi Jabeer yayi tare da cewa, "To meye zaisa na tsane ta hakanan kawai?i ba ita na tsana ba halayyar ta ne kawai na tsana." Tsaki muhdeen yayi "Yaushe ka zauna da ita da har zaka fahimci halayyar ta?don kunyi karatu kasa daya makaranta d'aya shine har zaka fahimci halayyar ta?" Cikin takaici jabeer yace, "Ai ba sai ka zauna da mutum ba,kamannin mutum da halayyar sa da ayyukan da yake aikatawa ma yakan say ka fahimce shi ko wane irin mutumi ne." Cikin Dan d'aga murya ya ce "To koma dai manene abunda na sani kawai shine Tana masifar sona.kuma bazata aikata abunda zai 'bata mani rai ba." Jabeer na ya daga kafad'a alamun bandamu ba,sannan ya furta "Shikenan tunda haka kace,sai dai ina baka shawar ka nemawa 'ya'yan ka uwa tagari wacce zakayi alfahari da it...." Cikin daga tsawa yace "I said out" Kai tsaye ya nufi kofar fita ya fice,yana mamakin abokin nasa da ya makance akan soyayyar Sumayya,tunsa yake da muhdeen bai taba d'aga masa murya ba sai akan sumayya.Bashi da Babban abokin da wuce Muhdeen ko shawara ya bashi yana karba amma yau Karan farko ya 'bata dashi akan mace.haka ya nufi office din sa ransa ba dad'i. Shima muhdeen aikin da baiyi ba kenan,haka ya rufe office din nasa yabar jabeer da tulun aiki. Ya nufi parking space ya tada motar say yabar asibitin. Kai tsaye gida ya nufa. ya tarar da Dady a falo yayin da Mummy ta tsiyaya masa ruwa a kofi ta mik'a masa,da sallama ya Isa da mamaki suke kallon sa ganin lokacin da ya dawo ba lokacin dawowar sa ba. Amsa sallamar sukayi yayin da ya karaso zauna a gaban su bisa center carpet. tare da cewa, "Barka da warhaka Dady." Kallonsa Dady yayi bayan ya ajiye Glass cup din da yasha ruwa a saman center table d'in dake gaban sa. "Yauwa barka dai Muhammad,lapiya Naga ka dawo dai-dai wannan lokacin?" Sunkuyar da Kai yayi tare da Sosa keya "Eh lapiya Dady,dama am... " Sai yayi shiru ya kasa karasa maganar Dady ya tattaro dukkan hankain sa ya maida Kan muhdeen sannan yace, "Kayi magana Mana Muhammad Ina Jin ka." Sunkuyar da Kai Muhdeen yayi tare da Fara magana. "Dma akwai yarinyar da muka dai-daita da ita ne,shine ta kirani Wai mahaifin ta yace na turo magabata na suyi magana." Cikin Jin dadi Dady ya furta "Kai Masha Allah,naji dadin Jin wannan maganar daga bakin ka.don dama buri na kenan naga auren ku." Juyawa yayi ya kalli Mummy tare da cewa. "Bakiji abunda danki ya fada ba?" Jinjina Kai tayi tare da cewa "Naji,Amma ka tambaye sa ya tarbiyya yarinyar take?tana da dabi'u masu kyau da addini? Idan ba mantawa nayi ba akwai ranar da Asiya ta nuna mani photon yarinyar a wayar sa,kuma gaskiya nikam bat..." Abba ne yayi saurin cewa "A'a kada kice komai tunda baki taba ganin ta ba, photo kawai bazaisa ki fassara 'yar mutane ta wace siga ba.baki da hujja,kedai kawai fatan alkhairi zakiyi masu tunda suna son juna." Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "Shikenan.Allah ya tabbatar Muna da alkhairi." Ameen Abba yace Sannan ya kalli muhdeen da ya sunkuyar dakai kasa yace "Ita yarinyar 'yar gidan waye kuma a Ina suke?" Cikin Jin dadi yace, "Dady suna zaune ne agarin Abuja sunan mahaifin ta Alh. Tanimu Dan kasuwa ne,kasuwancin Gwal-gwalai yakeyi daga kasar dubai.amma dai yanxun haka suna zaune a London ita da iyayen nata.sai dai ta sanar dani ta hanyar text message Wai gobe zasu dawo Nigeria." Kai Abba ya jinjina alamun gamsuwa Sanan yace, "Zanyi bincike akai,idan yaso sai na Kira Yaya Adam da minina Alh.kabir sai muyi abunda ya dace." Haka kuwa akayi a cikin sati daya aka saka ranar Auren Muhdeen da sumayya nan da watanni biyu masu zuwa.farin ciki a wurin masoyan guda biyu baya misaltuwa,domin abunda suke buri kenan. Wata ranar Asabar ne Muhdeen ya sanar da Mummy cewar zai kawo Mata sSumayya ta gaishe a.mummy taji dadin hakan sosai. Da misalin karfe biyar na yamma sumayya ta gama Shirin ta tsaf da kananun Kaya tasaka saboda dasu ta Saba, mom din ta ce tace ta cire su saboda gidan surukanta zataje tayi shiga na mutunci,zasufi ganin mutuncin ta.dakyar ta yarda ta saka wasu matsatstsun Riga da siket na leshi sun matse ta sosai kamar zatayi numfashi su yage,wayar ta ne tayi ringing Jin ringing din wayar yasa ta sakin murmushi,domin tasan waye ke kiranta ringing d'in sa na musamman ne tasa masada sauri ta daga wayar. "Hello sweet ganinan fitowa" Muhdeen dake zaune a motar say Yana jiran ditowar ta ne ya ce, "Please Baby kiyi shigar mutunci da Kamala,na hanaki saka irin kayayyakin da kike sawa kinki ji ko?" Tura baki tayi tace, "To ni fa kasan dasu nasaba." Muhdeen ya ce, "Ai zance ya kusan karewa da zaran mumyi aure manyan Kaya da manyan hijabai Zaki dinga sakawa,idan kinda kananun Kaya sai dai idan ni zakiyiwa kwalliya" Murmushi tayi sannan ta ce "Ganinan fitowa gashin attached din da akayi Mata Kari ta sake shi baya,tayi daurin Dan kwalin nan da ake cewa ture kaga tsiya,siririn mayafi ta rataya shi a gefen kafad'arta ta tare da rataya handbag dama tayi kwalliya fuska tun daga Kan powder har janbaki ta fesa turarurruka kala uku tasa takalmin ta mai tsini ta dauki wayoyin ta ta rike a hannu.ta nufi kofar fita.Afalo ta samu mahaifiyar ta,sallama tayi Mata ta fice. A cikin mota ta same shi Yana jiranta,bude murfin motar tayi ta shiga ido ya zuba mata yana kallon ta sai sakin murmushi takeyi ta jujjuya ido takeyi tare da cewa. "Baby ya kaga shigar manyan kayan nawa?yayi ko?" Zuba Mata ido yayi tare da cewa "Ba laifi" Zuba masa ido tayi "Cewa zakayi ba laifi? Bayan Kai da mummy ne kuka ce nasa kayan mutunci Amma ki ka Yana Mani?" Murmushi yayi tare da cewa "Sorry my Baby kinyi kyau Amma kike kisaka Koda irin 'dan abayar nan ne da mayafi da mata ke sakawa" Kallon mamaki tayi masa tace, "Tab wlh bazan iya kayan wahala ba duk nauyi ya dameni ga zari ba yanda isaka zai shiga ." Jinjina Kai yayi Taci gaba da cewa "Ni bana ma da abayar ballantana nasaka." Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Ba damuwa zamu siya a hanya sai ki saka mu karasa gidan" "Yakamata ka gane zansha wahala idan na saka" Yace, "Shikenan mu tafi" Baiso haka ba amma ba yadda yadda iya,baiso hakan ba. Horn sukayi Mai gadi ya wangale masu kofa suka fita,basu same ki Ina ba sai gidan su Muhdeen.Bayan yayi horn mai gadin gidan ya bude masa kofa ne ya shiga yayi parking. Atare suka bud'e marfin motar suka fito,Tana tafiya cikin takunta na yanga har suka karasa falo,ba kowa sai Mufida dake zaune a Kan kujera ,ganin su ne yasa ta mike cikin farin ciki ta ce "Sannu da zuwa Aunty Sumayya oyoyo matar Yayan mu" Sumayya ma murmushi tayi tare da cewa "Yauwa Mufida ya karatu "Alhamdulillah" Kasancewar Sumayya tasan kowa a gidan Muhdeen ya tura Mata photon su tun daga kan Dady da Mummy da Asiya da Mufida duk tasansu a photo. Inteesar ce ta fito daga dakin Mummy sanye da Hijab ganin Inteesar sai da gaban Sumayya ya fad'i Inteesar cikin fara'a ta kalle su tare da cewa "Sannu da zuwa,Ina wuni?" Yamutse fuska Sumayya tayi tare da cewa "Wace ce wannan?" Mufida tace kamar 'yar uwa take a wurin mu kullun Muna nan gidan a tare sunanta Inteesar" Sumayya ta Kare Mata kallo ganin irin kyawun da Allah ya mata,gata kamar wata balarabiya Fara ce doguwa mai dara-daran idanu,ga hancin ta dogo sai dan karamin pink lips din ta duk da ta saka hijab Amma Ana ganin yala-yalan gashin kanta da ya kwanta luf a goshin ta take sai taji tsanar Inteesar a cikin zuciyar ta. Dai-dai lokacin Mummy ta k'araso falon,turus ta tsaya tana karewa summaya kallo, Cikin wani irin murya ta ce "Son wannan ce matar da zaka aura?" Muhdeen ya zamo daga Kan kujera ya durkusa akan center carpet din falon Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love you oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman ihsa) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa Page0️⃣9️⃣ Muhdeen ya zamo daga Kan kujera,ya durkusa akan center carpet din falon.cikin far gaba ya ce "Mummy itace, na kawo ta ta gaishe ki." Jinjina Kai mummy tayi tana karewa Summaya kallo,gani tayi sam bata dace da Rayuwar Dan ta ba,dan daga gani bata samu tarbiyya mai kyau ba do daga gida ba,kallon Karin gashin da akayi mata ne ya zubo har tsakiyar bayan ta ga uban make up har yayi yawa,suturar jikin ta ya bayyana surorin jikin ta a bayyane, girgiza Kai tayi ta karaso ta zauna kan kujera. Muhdeen idon sa nakan mahaifiyar sa yana karantar yanayin ta. Sumayya daga yanda take zaune Kan kujera ta gaida mummy ta ce, "Barka da fitowa mummy" Cikin sakin fuska Mummy ta ce, "Yauwa sannu da zuwa" Sumayya ce daga yanda take zaune Kan kujera ta Kara da cewa, "Ina wuni Mummy" Ba yabo ba fallasa Mummy ta amsa Mata da, "Lapiya qalau Sumayya,ya mutanen gidan?" Amsawa tayi da duk suna lafiya Dai-dai lokacin ne Inteesar da Mufida suka loda Mata kayan ciye-ciye da lemu da ruwa a gaban ta. Shidai Muhdeen yana zaune a kasa saman carpet,don dama shi idan iyayen say suna zaune a kujera shi yana k'asa a zaune.koda kuwa daga baya suka zo suka tarar da shi akan kujera da zaran su zauna zai sauka kasa.Haka ma sauran kannen sa, Inteesar ma dabi'ar ta ce wannan tun fil'azal. Sumayya ruwa kawai tasha Wanda mufida ta kawo tata,kayan ciye-ciyen da Inteesar ta kawo mata kuwa ko kallon su batayi ba ballantana ta taba. don haka kawai sai taji kishin yarinyar musamman yanda taga Allah yayi mata sura Mai kyau gata Tana zaune a gidan su Muhdeen,kuma tasan dole zai dinga yawan ganin ta.sai tsanar Inteesar ya sake nunkuwa a cikin zuciyar summaya,don tasan tafita komai,abu d'aya zata fita dashi shinec tsayi Don sumayya doguwa ce tafi Inteesar tsayi.bayan nan ba abunda zata n mata,ko hasken fata ma idan Kika kalli Inteesar da sumayya zaki ga Sumayyar ta fita hasken fata.don ita tana karawa da mai maisa hasken fata shiyasa farin nata ya zarce na inteesar.amma da badon mai ba Inteesar tafita hasken fata Ido ta zubawa Inteesar sai taji k'irjin ta na dukan uku-uku,ta juya ta kalli Muhdeen dake zaune kasa saman carpet tace, "Baby mu tafi ko"? Kallon juna sukayi mufida da Inteesar yayinda mufida dariyar da take 'boyewa ne ya kufce mata. Ganin kowa ita yake kallo yasa taja hannun Inteesar suka shige dakin ta da sauri. Mummy ce ta kalli sumayya ta ce, "Tun yanzun gashi komai baki ci ba?" Yamutse fuska Sumayya tayi yayinda ta kalli kayan ciye-ciyen da Inteesar ta ajiye Mata tare da cewa "Mummy am okay" Mummy ce ta Mike tare da cewa "Ina zuwa" Kai tsaye dakin ta ta nufa,ba jimawa ta fito dauke da Leda a hannun ta.d'an kunne da sarka ce sai Turarruka a ciki. Karasawa tayi ta mikawa Summaya karba tayi tare da yin godiya mata sallama suka fita ita da muhdeen Mummy k'arasawa tayi d'akinta zuciyar ta cike da sake-sake ,tana ganin Sam batayi sa'ar suruka ba,ta dad'e tunanin hakan lokutan da take ganin pics d'in ta da Mufida ta nuna mata wasu ka ganta ba dankwali sai tulun Karin gashin wasu ba suturu. Kirki gasu nan dai da sauran su. Tumawa tayi da maganar da Dady yayi mata na cewar tayi masu fatan alkhairi kawai kada tayi tunanin komai,hakan yasa a cikin xuciyar ta tace Allah ya Sanya alkhairi. A bangaren Muhdeen da Sumayya kuwa suna tafiya a mota ne sumayyay ta kalle shi tare da cewa, "Baby na Wai meye alakarku da yarinyar nan ne?" Ba tare da ya kalle ta ba idanun sa nakan tuk'in da yakeyi ya ce , "Wata yarinya kenan?" Yamutse fuska tayi ta ce, "Wadda suka shiga daki da Mufida,Mai sanye da Hijabin nan Mana" "Okay Inteesar kike nufi ko?" "Eh" Ta amsa masa a takaice Dan Jim yayi kafin yace "Bamu da wata dangantaka ta jini da ita" Gaban ta ne ya tsananta bugawa,ta kalle shi tare da cewa "To zaman me takeyi a gidan ku?" Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Nima kaina ba son zaman yarinyar nan nakeyi ba,hakanan kawai naji na tsane ta a cikin zuciya ta,wallahi bana kaunar zaman ta agidan nan.ke intakaice maki Zaki zance ban taba Jin tsanar wani mahaluki a duniyar nan kamar yadda na tsani ganin yarinyar nan ba. Sumayya wani irin murmushi tayi wanda sai da hak'oranta suka bayyana,cikin jin dad'in kalaman sa ta ce "Ai da kasa an Kore ta a gidan" Da sauri ya kalle ta tare da cewa "Ke! Kinsan yadda Mummy take k'aunar yarinyar Nan kuwa?To bari kiji zata iya 'batawa dani akan yarinyar nan,don ba k'aramin son ta takeyi ba wallahi,ke ba ma ita ba hatta Dady da Mufida suna matakar son ta nida Asiya ce kawai bamu k'aunarta don ma yanzun Asiya bata k'asar tana can kasar Turkey tana karatu." Shiru tayi tana sauraron sa kafin daga bisani tace, "To ya akayi tazo gidan?" Muhdeen ya ce "Mummy ce zata fita unguwa Direbanta yad'an kad'e ta, mummy ta bita gidan su a bayan layin mu daga nan dai ta janyo yariyar a jikin ta,da taso iyayen yarinyar su bata ita taci gaba da zama a hannunta gaba d'aya,so sai iyayen suka ce a'a ita kad'ai Allah ya basu bazasu iya rabuwa da ita ba.amma fa kwana ne kad'ai batayi a gidan amma nan take ko wane lokaci." Juyawa yayi yana kallonta kafin ya maida hankain sa Kan tukyin da yakeyi sannan ya ce, "Wai me yasa kika damu da sanin ko wace ce it's?" Girgiza Kai tayi tare da cewa , "Bakomai ,kawai dai na tambayar ne dan naganta kuma bansan ta cikin 'yan gidan kuba." Daga ita har shi ba wanda ya cewa kowa komai har suka karasa gidan su Sumayya sallam su kayi inda ya shaida Mata gobe zai shigo.sannan yaja motar yabar gidan Ranar monaday da misalin karfe tara na safe Yana zaune a office din sa yana duba mara sa lapiya, yayin da yake ma wani dattijo tambayoyi yana bashi amsa shi kuma yana rubutu a file d'in da ke gaban sa ne jabeer ne ya turo kofar office din ya shigo,don dama shi kadai ne yake shigo masa office Kai tsaye.zama yayi Kan sofa din dake cikin office din ya zauna,bayan ya sallami dattijon tare da sanar dashi inda zaije ya mik'a file din. Karasowa yayi ya zauna kusa da Jabir tare da mik'awa Jabeer hannu Murmushi jabeer yayi ya ce "Angon Sumayya mai jiran gado, har ka Fara kamshin angonci tun yanzun." Kallon shi Muhdeen yayi tare da cewa "Ai kallon ka kawai nakeyi duk yadda muke dakai banida aminin da ya wuce ka kuma dan uwa a gare Ni dan wan mahaifina amma ace tunda sumayya suka dawo garin nan baka taba zuwa kun gaisa ba har tambayar ka tayi." Rik'e baki Jabber yayi yana dariya yace afuwan aboki yau zamuje tare inasha Allah. yauwa na manta ban fad'a maka ba wannan rigimammitar tsohuwar na kira ta jiya tana ta zagin ka ashe dama baka kiranta ka gaishe ta?tana matsayin mahaifiyar Dadyn ka?" Tabe baki baki Muhdeen yayi tare da cewa "Mahifiyar Dady kace ai ba mahifiya ta ba,matar da duk mutum yayi waya da ita sai ta 'bata masa Rai shiyasa na daina Kiran ta." Dariya yayi tare da cewa "Ai ciwon Kai Kam yaxun zaka Fara don tace jibi tace zata so,kuma kasan idan tazo gidan Dadyn ka take sauka." Had'e fuska yayi tare da cewa "Dama duk cikin jikokin ta tafi saka mani ido wallahi." Jabeer ne yace "Ko kuma tafi kowa kaunar ka ba don wallahi tafi sonka fiye da kowa a cikin jikokin ta." Fira suka 'dana taba kafin ya tashi ya koma office din sa. Bayan kwana biyu kuwa sai Gwaggo ta baro garin Kontagora ta iso garin Minna tun ana bikin Muhdeen da Sumayya saura wata biyu tazo.murna a wurin Mummy da Mufida ba'a magana. Waya ta d'auka ta Kira mu6hdeen tace kada ya dawo gidan nan ba tare da yazo mata da amaryar da zai aura yau d'innan idan ba haka ba ko ruwa bazata bari yasha a gidan nan ba. Sanin rigimamar Gwaggo ne yasa baida wani zabi dole ya Kira Sumayya yace ta shirya zaizo ya dauke ta ta gaishe da kakar sa da tazo. Misalin karfe biyar na yamma Mummy ce zaune a falo yayin da Mufida ke zaune Kan carpet,Gwaggo ta shiga ta watsa ruwa. INTEESAR ce ta turo k'ofar karamin gate din gidan ta shigo gaisawa tayi da Mallam Ibrahim mai gadi sannan ta shige cikin gidan. Bakin ta d'auke da sallama ta shiga falon durk'usawa tayi har k'asa ta gaida Mummy sannan ta kalli Mufida ta ce, "Yauwa Mufida Ina Gwaggon take?kinsan ban ta'ba ganin ta ba,wallahi na k'osa na ganta ba." Mummy ce tayi murmushi tare da cewa, "Karki damu Inteesar yanzun zata fito Zaki ganta" Dai-dai lokacin ne Muhdeen ya shigo da sallama sumayya na biye dashi a baya suka karaso yayin da Muhdeen ya zauna a k'asan carpet ganin Mummy akan kujera, s6umayya ta zauna kan 1 seater dake facing din mummy gaida mummy tayi ba yabo ba fallasa ta amsa Mata, Mufida ta nufi d'akin da Gwaggon

Chapter 3 of 38