Share this page
Kai,daure fuska yayi ba Alamar rahama,da hannu yayi Mata nuni da ta biyo shi. Haka ta Mike ba musu Tana gaba Yana binta a baya har suka karasa part din sa cogewa tayi a bakin kofar dakin Tana tsoron shiga sanin cewa ba kowa a dakin kuma Ummanta ta Hana ta ke'bewa tare da namijin da ba muharramin ta ba. Ganin Bata da niyyar shiga ya watsa Mata harara tare da cewa, "Ba Zaki shiga ba?" Kai ta girgiza cikin rawar murya tace, "Ummana ta hanani ke'bewa da namiji mu biyu idan ba kowa" Dariyar raining hankali yayi Mata yana Kare Mata kallo yace , "Dalla shiga uban me zanyi dake ko ina neman Mata bazan bazan taba iya hada jiki da kucaka irin ki ba ke har kinkai macen da Zan kalla naji wani Abu akan ki?" Tsaki yaja sannan yace, "Shiga muje" Ba musu tabi bayan sa har toilet suka shiga,kayan da ya cire Wanda ta watsawa Miyau ya nuna Mata yace, Kindan kudin shaddar Nan da kika 'bata kuwa?kinsan nawa na siye ta?kinsan anko mukayi nida Mai sumy kuwa?kinsan yau ne na Fara saka ta da niyar zuwa wurin masoyiya ta kuwa?kinsan zamuje yawan sha'katawa zamuje muyi photo da kayan Nan kuwa?" Cikin rawar murya tace , "Kayi hakuri" Tabe baki yayi Yana cewa, "Wannan kayan sun fita a Raina bazan iya saka su ba,yunusa Mai bawa fulawa ruwa zanba su,yanzun ki Duka ki wanke su tas ki fita ki shanya su a Rana,kiyi gadin su sai sun bushe kafin kizo ki goge sau" *YAWAN COMMENT DIN KU YAWAN READ MORE*🤷‍♀️Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Wannan kirkirerren labari ne banyi tunanin Rubuta ta shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to kuyi Hakuri bada niyyar yin Hakan nayi ba, arashi ne Mai kashe Auren Wawa. Page 1️⃣3️⃣ "Yanzun ki d'auki kayan nan ki je ki wanke su tas ki fita kije ki shanya su a rana, kiyi gadin su sai sun bushe karin kizo ki goge su" Karasawa tayi gaban washing machine Don dake cikin tangamemen Toilet din, ganin hakan yasa shi dakatar da ita cikin tsawa ya ce, "Keee" Da sauri ta juyo ta kalleshi, "Ina kike kokarin zuwa? Hannun ki zaki sa ki wanke su ba warshing machine za ki yi amfani dashi ba" Yana kallon ta har ta gama wanke kayan da ba datti ne dasu ba,ta d'auraye kumfar sabulun ta fito, ganinan zata bi ta hanyar babban falon gidan ya dakatar da ita. ya nuna wata kofar da bata san da ita ba,koface wacce take cikin part din sa wanda idan kabi direct zai sadaka da garden din gidan.cikin bada umarni ya ce, "Idan kika shanya kayan a garden din ki jira su bushe kafin ki kawo su ki goge su, sannan wannan kofar da kika gani ita zakibi ki dawo" Yana gama fad'ar haka ya koma ciki, direct babban falo ya nufa zaman sa keda wuya sai ga Gwaggo ta karaso falon, ganin babu Inteesar yasa ta Fara waige-waigen neman ta ganin Bata Nan yasa ta Harare shi tare da fadin "Kai ina Inteesar take ne? Nan na barta ita kadai?" Ko kallon ta bai yi ba ya cigaba da danna wayarsa. Cikin daga murya ta ce, "Tambayar ka nake, ina yarinyar da kaci zalinta take?" Still shiru ya mata kamar bai ji ta ba don dama akufule yake da ita yadda a gaban Inteesar ta dinga zagin say Wai salon ta Raina shi, a hasale ta sake tamayarsa a karo na uku sannan ya ce, "Ajiyar ta kika bani ko zaman gadinta na ke yi?" A hasale ta ce, "Haka kace ko?yanzun tsabar balagar rashin kunyar taka takai ka kalli tsabar ido na ka fada mani haka?" Ina mahaifiyar Uban ka? Nina haifi wanda yayi sanadiyar zuwan ka duniya da har ya d'an banza Mai suffar sadaka yalla, dama ance wanda kafi so shi yafi kuntata maka, duk cikin jikokina nafi kaunar ka da son ka Amma kafi kuntatamani da bakanta mani rai. Tunda kace ban Isa ba to bari na Kira mahaifiyar ka ai ita na isa da ita" Daga murya tayi Tana kwalawa Mummy kira "Fatima! Fatima!! Fatima!!!" Da sauri Mummy ta fito daga kitchen d'in da sauri jin yadda Gwaggo ki kwala mata kira tasan ba na lapiya bane,bayan ta karaso ta kalle ta cikin girmamawa ta ce, "Gwaggo lafiya kuwa?" Kallaon ta Gwaggo tayi ta ce, "Ina fa lafiya banga baiwar Allah da nasa aka kirata tun daga gidansu tazo wannan bakin mugun yayi mata dukan kawo ruwa, nan ba barta wance" Ta nuna kujera mai zaman mutum uku "Shine yanzun na dawo ban ganta ba, ina tambaye sa Ina take yana fada mani maganar banza, amma yanzun tunda ke uwarsa ce zai fada maki" Kallonsa Mummy tayi na dan lokaci tana karantar yanayinsa ta ce, "Son ina yarinyar nan take?" Kallon ta yayi cikin kwabe fuska ya ce, "Mummy nima yanzun na fito daga d'aki banga kowa anan ba, wata kila ta shiga dakin Mufida ta kwanta" Mummy ta kalli hijabin Inteesar tare da wayarta akan kujera yasa ta kalli Gwaggo ta ce, "Kin ga Hijabin Inteesar da wayarta ba inda taje ina ganin ta shiga ta kwanta ne" K'ai Gwaggo ta gyada ya yin da Mummy ta koma cikin kitchen d'in, Gwaggo ta ci je lebe tare da ce wa, "Wayyo ciwon kafata ta soma yi mun ciwo" Ta karasa maganar da 'kyar ta zauna Kan kujera tana kallon Muhdeen da kallo daya ya Mata ya dauke kansa ta ce, "To yauwa d'an albarka dama magunguna na sun Kare ka taimakawa tsohuwar nan mana" Kamar bai ji ta ba haka yayi mata shiru "Magana nake maka shalele na" Dariya ce taso kufce masa amma sai ya dake tare da cewa, "To waye kuma shalelen naki a yau?" "Kai mana d'an Albarka likita bokan turai, ai ba ni da shalele bayan kai" Murmushi yayi "Ada ne nake shalelen ki, amma yanzun bani ba ne waccen yarinyar mai kama da Aljana ita ce shalelen ki yanzun, don na lura zaki iya batawa dani in dai akanta ne" Ya Karasa maganar ba tare da ya kalle ta ba, rike baki Gwaggo tayi tare da ce wa, "Waya fada maka ba kaine shalele na ba? Ka ta'ba ganin inda aka canzawa tuwo suna?" Dariyar raining wayo yayi mata sannan ya ce, "Ana ki canzawa tuwo suna sai dai idan bai kwana ba, amma idan ya kwana ya zama d'umame" Gwaggo ta kalle shi "Shalele na ka manta cewa da tsohuwar zuma ake magani?" Murmushi yayi tare da ce wa, "Sanin da ki ka yi na cewa da tsohuwar zuma ake magani Amma yanzun anayi da sabuwa Dan neman karin sinadari" Kallon mamaki tayi masa "Wai kai komai aka fada maka sai ka samu amsar maidawa? to naji don Allah ka kawo mani irin magungunan da saka aika mani dasu nasa da na shafawa" "Babu wani maganin da zan baki wannan karon allaura za ni yi maki" Kallonsa tayi da sauri ta ce, "Ai me za ka yi mani?" Mi'kewa yayi tare da bar mata falon. Bangaren Inteesar kuwa tana nan zaune ta tasa kayan a gaba tana jiran bushewar su, kasancewar akwai Rana har sun kusa bushewa, magana takeyi a fili. "Insha Allah na bar masa gidansu kenan, lokaci yayi da zan nisance su tunda har tsanar da yayi Mani yakai haka, dama dole tasa nake zuwa gidan su bawai son kaina ba ne, mahaifiyarsa ce take sani zuwa sshe lokacin da mahaifiyar sa taje ta samu Umma da maganar cewa na dawo gidanta gaba d'aya da zama Umma da Abba suka Hana Ashe da sun amince da na kad'e a hannun sa in banda su da suke matsa Mani aiba killin zan zo ba, ko ban zo ba zasu kirani a waya ne wai dan Allah nazo wata Rana Mufida ce zata zo tace wai Mummy tace nazo.amma yanzun duk abunda zai faru ya faru ya faru zan dauke kafa ta a gidan nan, ki zuwa school din da nake shiryawa da wuri na biyowa Mufida zan daina shiryawa da wuri ne har sai na tabbatar sun bar gida sannan na fito mu had'u a hanya, duk da cewar Mummy, Dady, Gwaggo, ga kuma Mufida da muka shaku ba za su so hakan da zanyi ba Amma shine mafita a gareni.Yaya Muhdeen kayi hakuri na kusa bar maka gidan ka zuba ruwa kasa kasha, mugu a gaban mutane baya nunamin hantara da kyara Amma da zaran ba idon kuwa kare ma narishi daraja a idonsa" Tana ta magana ita ka dai kamar tanayi da wani ga zazabi naso rufe ta ga azababben ciwon Kai da yasa ta gaba,Tana Nan zaune kayan suka bushe ta kwaso su tabi ta yanda ta fito,har Bedroom din sa ta wuce ta fara goge kayan. Can fall kuwa bayan angama girki Anjera a Dinning table kowa ya hallara Mummy, Muhdeen da Gwaggo ya yin da Dady ne kadai baya nan.Mufida ce ta fito cikin tashin hankali tana fadin "Mummy gaba daya na duba ko Ina banga Inteesar ba Ina ta shiga?" Dai-dai lokacin Inteesar ta fito daga part din Muhdeen dafe da kanta, jin alamar tohuwar mutum yasa suka waiga dukkan su sauka zuba mata ido suna kallonta da mamaki, ya yin da Mummy tayi saurin mikewa ta rike hannunta cikin mamaki tace, "Daga ina kika fito?Mai ya kaiki part d'in son?" Mummy ta kara rungume ta tana fad'in "Subhanallahi jiki yayi zafi, zazza'bi ne ya rufe ta" Janyo hannunta tayi suka karasa dinning room dinta zaunar da ita kan kujerar dake kusa da ita.Ba yadda Mummy batayi ba akan Inteesar taci abinci taki da kyar tasha lemon da Mummy ta tsiyaya mata a cup, Mummy ta kalli Muhdeen ta ce, "Son" D'agowa yayi ya kalleta tare da cewa, "Na'am" "Ka d'auko kayan aikin ka sannan ka dauki Inteesar a motarka ka kaita gida kayi Mata treatment din da ya dace kafin ka dawo,sannan kafin KU nufi gidan su ka biya ka siye mata fruit saboda bata ci abinci ba" Cikin bada umarni tayi maganar, kallonta yayi ganin yanayin fuskar ta ba sauki yasa yace, "To Mummy yadda kika ce haka za'a yi" Kallonta ta maida ga Inteesar ta ce, "Inteesar ga yayanki zai kaiki gida yayi maki abunda ya dace kafin nima na zo" Kai Inteesar ta gyada ba ya yin da gabanta ya ci gaba da fad'uwa.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Wannan kirkirerren labari ne banyi tunanin Rubuta ta shi Dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHEEM* Page1️⃣4️⃣ Kai Inteesar ta gyd'a yayin da gabanta gaba da fad'uwa. "Uhm wannan marukan da tasha ba dole tayi rashin lapiya ba? Yanzun haka ba Wanda ya ta'ba Mata wannan Marin,ko uwar ta ubanta nasan bazasu yiwa wannan nitsatsiyar yarinya Marin nan ba Amma Rana tsaka wani katon banza ya more ta." Gwaggo ce tayi maganar yayin da karasa bayan Inteesar Tana shafa kyakkywar fuskar Inteesar. Muhdeen ko kallonta baiyi ba yayinda ya Mike ya nafi part dinsa fuskar Nan a muturke.Mufida ce to janyo hannun Inteesar tare da cewa, "Muje na rakaki mota,idan na dawo daga gidan Yaya Jabeer matar sa Bata da lapiya ne zamuje da Mummy mu gaishe ta,idan muka dawo zan biyo gidan naku Allah ya baki lapiya" Inteesar tace , "Ameen " yayin da suka nufi hanyar fita,Kai tsaye parking lot suka nufa Inda Mufida ta bude Mata murfin gidan gabar motar.kai Inteesar ta girgiza tare da cewa, "Baya zan zauna" Ba musu Mufida ta bude Mata bayan motar ta ahiga,zamanta keda wuya sai ga shi Shima ya karaso hannun sa rike da akwatin magunguna,murfin motar ya bude yashiga ganin Bata gefen sa yasa Kai idon sa baya,ganin ta dukunkune yasa yace Mata. "Niba direbanki bane ki tashi ki dawo gaba" Mufida ce tace "Ya Ina ga kamar zatafi yin Balanced a baya tunda nac... " Had'iye sauran maganar tayi ganin irin kallon da yake Mata ne yasa tayi shiru.bude bayan motar tayi ta kama hannun Inteesar Dan ta taimaka ta fito,a hankali ta fito da taimakon Mufida Dan har jiri take ji Yana neman dauke ta.Bayan ta zauna gaban motar ne ya figi motar suka bar gidan. Sai da ya biya ya siye Mata fruits kamar yadda umma ta Umarce shi.Tundaga Kan lemo,kankana,Apple, Abarba inibi da ayaba sannan ya kama hanyar gidan su Inteesar din kasancewar yasan gidan ya ta'ba Kai Mummy. Dai-dai lokacin da ya Isa kofar gidan ya juya ya kalli Inteesar,ganin idon ta a lumshe kamar Mai bacci.Dai -dai lokacin ne kuma Kira Sumayya ya shigo wayar Video call ne.daga Kiran yayi ganinta sanye da shaddar da suka shirya sawa sunyi anko su tafi uawan shakatawa.lumshe kyawawan idanun sa yayi tare da bude su yace, "Mai Baby kinyi kyau sosai" Murmushi tayi tare da cewa, "Thanks Amma ya bangan ka da naka a jikin Ka ba?kayi lettin zuwa waje na yakamata ace minti talatin da suka wuce ka iso Amma shiru" Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace, "Ki bani minti talatin zan karaso yanzun Nan insha Allah" Turn baki tayi sannan tace, "Kana Ina ne yanzun?" "Ina kofar gidan su Inteesar" Rasss Gaban ta ya dadi tace, "Wace Inteesar" Saita secreen din wayar yayi dai dai yanda Inteesar ke zaune gefen sa idonta alumshe. Take Sumayya Gaban Sumayya ya Fadi ganin Inteesar a cikin motar Muhdeen yayin da ita Tana can Tana jiran sa Amma shi Yana can wurin wannan yarinyar. Take taji wasu zafafan Hawayen kishi suna kwaranya a idanun ta muryar kuka tace, "Nagode da abunda kayi Mani " Tana kokarin kashe wayar ne yayi saurin cewa, "Kinga dakata ki saurare Ni nayi maki bayanin abunda ya daru" "Want bayanin zakayi Mani?cewa Inteesar tafi Ni mahimmanci a wirin ka ne da yasa ka shanyani kusan awa d'aya Ina jiranka yayin da Kai kake can wajenta" "Kinga ki tsaya nayi maki bayanin yadda akayi" Kara fashewa tayi da kuka,Don dama Tana da zafin kishi Bata tsaya sauraren sa ba ta katse kiran. Juyawa yayi ya kalli Inteesar da ta lumshe ido kamar Mai bacci yayinda duk Tana Jin maganar da suke. "Fita" Ya fada Mata a takaice,yayin da Shima ya fito ya rufe marfin motar.da'kyar ta iya bude marfin motar ta fito jiri ne ya d'ebe ta tayi luuu zata fad'i. a guje Muhdeen ya Karasa gare ta ya tare ta ta fad'a jikin sa. Cikin wata iriyar kasalar da ta dorar masa lokaci guda yace, "Kiyi a hankali" Same jikinta tayi ta jingina da motar saboda ganin takeyi komai na jujjuya Mata. Karasawa yayi bakin kofar gidan tare da yin sallama,Yana Nan tsaye Umma ta fito sanye da Hijab.zubawa kyakkywan saurayin Mai kwarjini da haiba ido, Muhdeen kyautatawa ne ajin farko dogo ne fari fuskar sa zagaye da kwantaccen saje da yayi luf a fuskar sa Gashin kansa ma haka yake kamar ba na bakin fata ba ga madaidaitan idanun sa Mai masu kyau da kwarjini. Durkusawa yayi cikin girmamawa ya gaida Umma. "Ina wuni Umma?" "Lapiya qalau" Ta amsa masa cikin sakin fuska 'Dan Jim yayi Don ya gane cewa Umma Bata sanshiba yasa yace, "Dama Inteesar ce bataji dad'i ba shine Mummy tace na na kawo ta nayi treating d'inta kafin su karaso" Jin haka yasa Umma ta fahimci cewa shine Muhdeen din da ake fadi.nuna mata Inteesar da ta jingina da jikin motar yayi tare da cewa, "Umma jiri takeji shiyasa nayi sallama Don azo a taimaka Mata" Da sauri Umma ta karasa ta tallabota tare da had'a ta da jikin ta suka nufi cikin gidan. Acikin d'akin Inteesar din ta kaita yayin da ta koma tare da bawa Muhdeen izinin shigowa.Har dakin tayi masa jagora hannun sa dauke da akwatin magunguna sai ledar fruit din da ya siya Mata. Tana kwance akan katifar ta ya kalle ta tare da cewa "Tashi zaune Kisha fruits din kafin nayi maki allura ,Kinga ba komai a cikinki da kikaci" Shiru tayi masa tare da tura baki Tana kunkuni .Umma CE to daka Mata tsawa Tana fadin "Wai lapiyar ki Yana maki magana kinyi banza dashi ba taimakon ki zaiyi ba" Hawaye ne ya cika Mata ido tace, "Umaa kiyi hakuri indai taimako ne daga wurin say bana bukata ya tashi kawai ya tafi" Umma shiru tayi ta zuba Mata idanu Don ita a tunanin ta allura ce bata so shiyasa take fad'in hakan. Sake magana yayi a karo na biyu yace, "Dakin daure kinci wani abun ko kadan ne* Cikin tsiwar da Bata San Tana da ita ba ta Fara magana Tana fad'in "Dalla mallam ka tashi ka dauki tarkacen ka bana bukatr ganin ka a rayuwa ta,ko a hanya bana fatan sake had'uwa da Kai.Kuma gidan KU bazan sake zuwa ba idan kaga kafata duk wulakancin da kaga dama kayi Mani Ni na jawowa kaina " Shiru yayi ya zuba Mata ido Yana mamakin yadda har ta iya bud'e baki tayi masa magana gatsai haka... Bai karasa tunani da yakeyi ba ya sake Jin murayar ta Tana cewa. "Ka tashi ka fita bana kaunar ganin ka a rayuwa ta,na tsane ka irin tsanar da ba ta'ba yiwa 'Dan Adam shi ba.Ba zaka sake gani na a gidan KU ba ballantana..." Bata Kai aya ba taji Umma ta daka Mata tsawa Wanda yasa Inteesar fashewa da kuka Tana fad'in " Umma Don Allah ya fita wlh idan na kalleshi zuciyata tafasa takeyi" Numfashi taja alamun maganar ma karfin hali ne,sannan tace, "Da ace Kaine likitan da zakayi Mani treatment na samu lapiya gara nayi ta zama da ciwo" Ledan fruits din da ya siyo ta dauko ta watsa masa su a jikin sa.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Wannan kagaggen labari ne ban Rubuta shi Dan cin zarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba Arashi ne Mai kashe Auren Wawa. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHEEM* Page1️⃣5️⃣ Ledan fruits d'in da ya siyo ta d'auko ta watsa masa su a jikin sa. Umma da ranta ya gama 'baci ne ta fita waje,ba jimawa sai gata ta shigo da zabgegiyar bulala,ta nufi Inteesar da niyyar za ga Mata bulalar Amma cikin zafin nama Muhdeen ya shiga tsakani Yana ba wa Ummi hak'uri. "Ka bar ni da ita yanzun nan taji a jikin ta" Girgiza Kai Muhdeen yayi tare da cewa "Kiyi Ha'kuri Umma zafin ciwo ne yasa haka" "Ba wani zafin ciwo da zai sa ta haka?Bata cikin hayyacin ta ne?ka daina kokarin Kare ta " Ta karasa maganar Tana jifa da bulalar ta fita d'akin ranta a 'bace,Don Bata taba tsammanin Inteesar za ta yi abunda tayi a yanzun ba. Bayan fitar Ummin ne ya juyo ya kalle Inteesar cikin 'bacin Rai ya soma magana. "Wace ce ke?me kike dashi ?me kike ta'kama dashi? Kyawu? Ilimi? Daraja?Dukiya ?ko me?" Haka ya jera Mata wad'annan tambayoyin,ita Kam ko kallon sa ba ta yi ba zuciyar ta cike da fargabar hukuncin da zata d'auka akanta,Don rabon da ta ga irin wannan 'bacin ran a wurin Ummi har ta manta. Muryar Muhdeen ce ta ji Yana cewa, "Kalle ni da kyau ni Muhammad Muhdeen na fi karfin wulakanci wallahi,ke har kin Isa ki wulakantani ?ban da yi wa mahaifiya biyayya da ta umarceni nazo nan meye zai kawo ni wajenki. Wallahi kinci arzikin Mai daraja da na baki mamaki wallahi. Bai sake magana ba Fara had'a Alluran da zai Mata yayi,Tana ganin haka ta Fara kuka ita wallahi Ba ta son Allura magani take so, dariyar mugunta yayi tare da cewa, "Yauwa na ji dad'in sanin haka kasancewar kina masifar tsoron Allura ,da haka zan yi maganin ki" Fashewa tayi da kuka Don A Rayuwarta Tana masifar Jin tsoron Allura fiye da komai,cikin muryar kuka da tsoro tace, "Yaya Don Allah ka yi hakuri wallahi bana son kayi Mani Alluran Nan Don mutuwa zanyi kuma nikad'aice Umma na ta Haifa ka tausayawa Umma na kada ta rasa 'yar ta gudaliya" Dariya ce ta so su'buce masa Amma sai ya Danne yace, 'karamar mara kunya ba Ni kika gamawa yiwa wula'kancin da Tunda nake a rayuwa ta Ba'a ta'ba yi Mani kwatankwacin sa ba,Don Haka dole na hukunta ki" Fashewa tayi da kuka sosai Tana ihun Kiran Umma "Umma ki zo za'a kashe maki 'yarki guda d'aya da Allah ya baki,Umma na kizo wallahi fansa yake da niyyar dauka akaina,Umma kinsan bana son Allura ballanta shi da biyu zaiyi Mani Alluran Nan" Bai kalle ta ba ya ci gaba da abunda yake yi saida ya gama sannan ya kalle ta yace, "Ki d'aga rigar ki sama" Cikin muryar kuka tace, "Wallahi bazan d'aga ba tunda baka da imani" Tana fad'ar haka ta Mike cikin rashin 'karfin jiki ha jire dake d'ibarta ta nufi hanyar fita daga d'akin cikin jirin dake d'ibarta tayi luu zata fad'i Don ganin duhu takeyi,cikin zafin nama ya Karasa ya ri'keta da hannu d'aya,yayin da d'aya hannun yayi amfani dashi wajen soka Mata allurar ba tare ya d'aga rigar ba, yayi Mata Allurar.Gigitaccen Kara ta saki tare da sakar masa jiki taci gaba da ihu Tana Kiran Umma a haka ya yi Mata allurai biyu sannan ta kwanta Tana kuka kamar 'karamar yarinya son Sai ta ji zafin Alluran na daban ne,yasha Bambam da Wanda ta Saba ji.nan ya ajiye Mata magunguna ya Rubuta yadda za ta yi amfani dashi ya tattara kayan say ya fito daga d'akin,a tsakar gida ya samu Umma yayi Mata sallama tare da shaida mata gobe zai dawo.Bayan fitarsa Umma ta shiga ta samu Inteesar inda tayi Mata fad'a sosai akan abunda ta yi wa muhdeen,ita dai shiru tayi tare da bawa Umma hak'uri,fad'a ya sake Mata tare da nuna Mata cewa wannan mummunar d'abi'ar Bata son shi, Inteesar din kuwa hakuri kawai take bawa Umma tare Mata al'kawarin ba za ta sake ba. Lalla'bata umma tayi ta d'aci Abinci kad'a kafin ta kwanta. Muhdeen kuwa Koda ya 'karasa gida Bai samu sun Umma ba sun tafi gidan jabeer gaida matarsa Maryam da tayi rashin lafiya. Wanka yayi ya canza Kaya cikin hanzari ya nufi gidan su Sumayya,Bayan yayi horn Mai gadi ya bud'e masa ne ya shige cikin gidan, Yana zaune a motarsa ya Kira layin Sumayya Yana ta ringing Bata d'aga ba. Sumayya kuwa Tana zaune a d'akin ta da tayi kaca-kaca dashi ta hargitsa sa gashin attached din da akayi Mata Kari ta barbaza shi kamar mahaukaciya sintiri takeyi a d'akin Tana ta suratai ita kad'ai,duk abunda ya tari gaban ta sai tayi jifa dashi gaba d'aya ta yay bedsheet din gadon tayi jifa dashi pillows din ma gaba d'aya tayi watsi dasu a cikin d'akin kayan makeup dinta duk tayi watsi dasu da turarruka,wad'anda suke cikin kwalabe kuwa duk sun farfashe suk abunda tayi tozali dashi sai ta hargitsa sa,hatta sidedrawer sai da ta d'auke sa tayi jifa dashi, Dama ita haka take tun Tana yarinya Iyayenta basa tsawatar Mata sai abunda taga dama take yi basu Hana ta.indai ranta yayi masifar 'baci to duk abunda ya tari gabnta sai taga bayansa,hatta T.v dake kunne Yana aiki Tana kallon wani series a tashar zee word idon ta na sauka Kan T.V ta d'auki 'karfen da handbags dinta suke rataye gadan-gadan ta nufi wurin karfen Bayan ta dauki 'karfen Kai tsaye plasma T.Vn ta nufa ta Fara kwalawa T.V 'karfen har sai da taga seecreen d'in T.V ya ragargaje idonta ne suka sauka Kan dressing mirror jifa tayi da 'karfen ta nufi gaban mirror Hannunta tasa ta naushi mirror d'in take ya ragargaje Hannunta sai zubar da jini yake. Mum d'inta dake ta bubbuga kofar Tana ro'konta ta bud'e dakin kada ta ji wa kanta ciwo Amma Ina Bata ma San tana yi ba,gashi Dad d'inta baya Nan ya tafi kasar Dubai,gaba d'aya mum hankalinta yakai 'kololuwar tashi gashi key din d'akin Sumayyar na jikin kofa ta cikin ballantana ta Nemo spare key ta bud'e Muhdeen da ke cikin mota ya gaji da Kiran layin Sumayya Yana ta ringing Bata d'auka ba,dama wayar na falo ta bar shi lokacin da ta kirashi video call ta gansa tare Inteesar cikin motarsa a guje ta shige d'akin Tana kuka ta saka key karar fashe -fashe ne yasa Iya Ggaje Mai Mata gyaran d'aki ta nufi d'akin

Chapter 5 of 38