Share this page
na ba kawai umarni suka bani inaji Ina gani aka d'aura auren.Jabeer wallahi bana son auren nan ba yadda zanyi ne." Shiru Jabeer yayi yana nazarin maganar shikam baiji takaicin wannan auren da aka d'aurawa Muhdeen ba,don yasan cewa iyayen nasau sun lura da rashin tarbiyar Sumayya ce shiyasa aka nema masa masa wata matar.A cikin zuciyarsa yaji dad'in zancen don dama ba yadda baiyi dashi ba akan kada ya auri Sumayya amma soyayyarta ta riga da ta rufe masa ido ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Wace ce matar da aka aura maka?" Cikin takaici ya fad'i sunanta "INTEESAR" Gaban Jabeer ya fad'i Jin sunan Inteesar,take yaji wani Abu zuciyarsa har sai da wayar hannunsa ta su'buce masa ta fad'i k'asa.Sunanta ya ambata da k'arfi "INTEESAR?" Kai Muhdeen ya jinjina masa alamar eh Shiru yayi na d'an lokaci kafin ya saki murmushi ya ce, "Indai Inteesar ce na Taya ka murna samunta a matsayin mata,duk da na fahimci baka son aurenta amma Ina da yak'inin cewa zuwa gaba zakayi alfahari da ita." Tsuki Muhdeen yayi "Allah ya kiyaye kaima fa na lura da cewa a 'bangaren su Gwaggo kake." Gajeren murmushi Jabeer yayi tare da cewa "Ba zaka gane gata akayi maka ba sai nan gaba." "Ba wani gata ni ba wannan yasa na kiraka ba,tunda my Sumy taji Ina fad'a maka zancen auren Inteesar har suma tayi Kai a rak'aice dai gata can a d'aki dai fashe-fashe takeyi." Da mamaki Jabeer ya saki baki yana kallonsa "Yanzu tana ina Wai?" Tana d'akinta Kai tsaye suka nufi d'akin,k'wank'wasawa suka dingayi suna bata baki amma ina bata saurare su ba.Haka suka hak'ura inda Jabeer ya nuna masa cewa ya barta zuwa anjima idan ta d'an sauko sai suyi magana. Daga haka ne Muhdeen yaja Jabeer zuwa d'akinsa inda Muhdeen ya shiga bathroom room don yin wanka inda yabar Jabeer zaune saman sofa yana jiransa. Daga can d'akin Sumayyay kuwa tunda ta gaji taga bazata iya cigaba da yayyaga kayan ba.Hakan yasa sauran akwatunan kayan lefen auren ta dinga jansu tana kaiwa harabar gidan tana jibgesu,a haka har ta gama jidar kayan lefen auren bayan ta gama jibgasu waje guda ne ta d'aga kai ta hango Mai gadin gidan tare da Zayyanu Direban gidan suna kallonta,harara ta watsa masu tare da yi wa Zayyanu Direban alamun yazo manuniya,gabasa ne ya fad'i ganin ta kirasa don kallon mahaukaciya sukayi mata ganin yadda takeyi tsoro da fargaba ya hana Zayyanu k'arasawa wajenta sai da mai gadin yayi masa da alamar yaje,cikin tsoro ya k'arasa wajenta.magana tayi masa a kausashe ta ce, "Kaje ka kawo mani fetur yanzun nan." Da mamaki ya tsaya yana kallonta, Tsawar da ta daka masa ne yasa yaba r wajen cikin rawar jiki,ba jimawa sai gashi ya dawo da fetur a cikin galan,amsa tayi tare da ce masa ya kawo mata ashana.k'arasawa yayi wajen mai gadin gidan ya amso mata ashana ya kawo mata. Ga mamakinsu gani sukayi ta bud'e robar fetur d'in ta tsiyaya shi duka a jikin akwatunan kayan lefenta,sanan ta kyasta ashana ta jefa kai tsaye cikin gidan ta koma. Jabeer dake zaune saman sofa ne ya hango bak'i ta jikin gilashin windows, mi'kewa yayi tare da d'an zuge gilashin window d'in,ganin hayak'in da ya turnik'e gidan ne yasa shi sakin salati dai-dai lokacin da Muhdeen ya fito daga wanka ganin hakan yasa cikin sauri ya saka Jallabiya suka nufi hanyar fita,don sun d'auka gobara ce. Suna nufar inda suka ga hayak'in na tasowa turus suka tsaya ganin akwatuna da da kaya suna ci da wuta. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Kalmar da Muhdeen ya furta kenan.Jabir ya kalleshi tare da cewa " ta yaya kuma me hakan yake nufi?" Ajiyar zuciya Muhdeen ya sauke tare da cewa "Sumayya ce ta k'ona kayan lefenta " Cikin mamaki Jabeer ya ce, "Kana nufin kayan lefen da kuka je Dubai kuka siyo da akwatunan sune ta bankawa wuta?" Kai Muhdeen ya jinjina masa alamun eh. "Tirk'ashi Shine kalmar da Jabeer ya fad'a,sannan ya d'ora da cewa "Gaskiya duk yadda nake tunananin Sumayya lamarinta ya wuce haka,ta wuce sanin tunanina.wannan ai hauka ne da rashin sanin darajar dukiya.kayan miliyoyin kud'in ne zata bankawa wuta?saboda mahaukacin kishi? Zuba masa ido Muhdeen yayi,kafin ya d'aura da cewa "Haka take duk lokacin da aka 'bata mata rai sai tayi asarar duk abunda ya tari gabanta,amma ban ta'ba tunananin cewa zata iya k'ona kayayyakin lefen nen ba,amma hakan Bai rasa nasaba da cewar kishi ne yasa ta k'ona kayan lefen nata." "Muhdeen zan baka shawara guda d'aya,shawarar kuma ita ce kada ka ajiye Inteesar a cikin gidannan,don idan har ka had'asu gida guda wata rana wannan mahaukaciyar matar taka zata iya kashe Inteesar ko ma ta illata ta,mafita d'aya ce shine ka raba masu gida,ka Kai Inteesar wancan gidan naka." Wani kallon irin Wanda ke nuna alamar bazaiyuba muhdeen ya watsawa Jabeer. "Wani gidan ne zan Kai ta? gidan da na gina da sunan Sumayyata ne zan d'auki waccan kucakar yarinyar na ajiye a ciki?." Da mamaki Jabeer ke binsa da ido jin kalamansa "Kamar ya?me kakae nufi ne?" "Kai nifa wallahi ka daina mani maganar yarinyar nan ba itace a gaba na ba,aure dai an d'aura ko to shikenan tunda haka suka so,amma bazan ta'ba kallon wannan kucakar yarinyar a matsayin mata ba.Yanzun kawai ka sanar dani yadda za'ayi na shawo kan Sumayya." Tsaki Jabeer yayi cikin jin takaicin maganganun da Muhdeen ya fad'a sannan ya ce, "Wannan matsalarka ce ni inada abunyi,nabar aiki a asibiti sakamakon kiranka so zan koma patient na jira na,kaima ka shirya dawowa bakin aiki don ayyuka sun mani yawa." Yana Kai K'arshen zancensa sai ya nufi motarsa ya shige,horn yayi Mai gadi ya bud'e masa ya fice yabar muhdeen yana mamakin me yasa duk 'yan uwansa suka juya masa baya akan Sumayya. Wayarsa ce tayi k'ara sunan Mummy ce ya bayyana a kan fuskar wayar,bayan ya d'aga kiran ne ta shaida masa cewa tana buk'atar ganinsa yanzun a gida.Daga nan ta katse wayar shi kuma ya shiga ciki d'akin Sumayya ya nufa still a kulle k'ofar take hakan yasa ya nufi bedroom d'insa key d'in motarsa ya d'auka ya nufi gidan iyayensa. Koda ya ya isa gidan horn yayi mai gadin gidan ya lek'o ganin motar Muhdeen ne yasa cikin azama ya bud'e masa gate,bayan yayi parking ya fito ne ma'aikatan gidan suka dinga gaishesa amma ko kallonsu baiyi ba hannu kawai ya d'aga masu don ransa yakai k'ololuwa wajen 'baci. Gwaggo ce da Mummy a falon suna tattaunawa sai Mufida dake zaune kan center carpet,don Mufida ma Bata San da zancen auren ba sai yau.Kuma Mummy ta kwa'beta cewar kada ta fad'i ma Inteesar zancen auren,su manya zasu San yadda zasu fad'a mata cikin hikima don kada ta tashi hankalinta. Da sallama ya shigo falon gaba d'ayansu suka amsa masa sallamar, inda ya k'araso ya durk'usa ya gaida Mummy "Ina wuni Mummy" Cikin sakin fuska ta amsa masa "Lafiya lau son ya Sumayya take" Jim ya d'anyi don bazai iya sanar dasu halin da yake ciki da Sumayya ba,cikin sanyin jiki ya ce, "Tana lafiya lau Mummy" Ganin yanayin d'an nata da yanayin maganarsa ta fahimci cewa akwai wata matsala don haka ta d'aura da cewa "Ka sanar da ita zancen auren ne?" Kai ya jinjina "Eh na sanar da ita Mummy" "Masha Allah ina fatan dai ba wata matsala kuma Sumayyar Bata tashi hankalinta ba,duk da nasan kowace mace ce dole zata shiga damuwa kishi kumallon mata ne." Bazai iya yi wa mahaifiyarsa k'arya ba,kuma bazai iya sanar da ita halin da suke ciki ba. Jin muryar Mummy yayi ta cigaba da cewa "Son don Allah ka rarrasheta,ka kwantar mata hankali sosai please." Kai kawai ya jinjina ya kalli goggo cikin jin haushin auren da tasa akayi masa ne ya kauda Kai ciki-ciki can k'asan mak'oshi yayi maganar ya ce, "Ina wuni" Ta'be baki tayi tare da fashewa da dariya tana fad'in "Yaro man kaza,wato fushi kake dani ko?to kaci gaba gausuwarka ma bana so d'an k'wal uba mai zubin sadaka yalla,nayi maka gata amma ba godiya ko?zanyi maganinka ne daga Kai har wannan matar taka gata nan kamar busashshen cry fish." Harara ya galla mata ta ta'be baki tana cewa "Uwarka ka harara gata nan a zaune d'an k'wal uban yaro." Dai-dai lokacin Dady ya sakko ya K'araso wajensu.zama yayin da Muhdeen ya ce, "Dady Ina wuni" "Lafiya lau,sauri nake dama zan fita nace Mummynka ta Kira Mani Kai,kana jina ko?" Kai ya jinjina "Eh Dady" "Abunda nake son na sanar da Kai shine,zancen tarewar Inteesar a ina zaka ajiyeta ne? gida d'aya da Sumayya ko kuma zaka kaita d'ayan gidanka ne?" "A'a Dady gida d'aya zasu zauna." Kai Dady ya jinjina tare da fad'in " Masha Allah" "Zancen tarewarta kuma Nan da sati d'aya zata tare." Kai kawai ya jinjina ba tare da yayi magana ba. Zancen kayan lefe kuma Ni da kaina zan bada kud'i a had Kafin yakai k'arshen zancen Gwaggo tayi saurin cewa "Sani akan me zaka bada kud'in kayan kefe?ai bazai yi wu ba,ita waccan Kai ka bada kud'in kayan lefenta?shi da kansa ya siya,to haka ma Inteesar shi ne da kansa zai siya saboda hakan zaisa ya san mahimmancinta a gare shi." Daga alkalamin ✍️ Maman Ihsan Don K'arin bayani 09065327995 Love U oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa shi ta kowace siga. Wannan kagaggen labari banyi tunanin rubutashi shi dan cinzarafi kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to ku garface ni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa. Page3️⃣1️⃣ "Sani akan me zaka bada kud'in kayan kaya lefe? bazaiyuwu ba,ita waccan Kai ka bada kud'in kayan lefenta ta?shi da kansa ya siyo,to haka ma Inteesar shine da kansa zai siya,saboda hakan zaisa yasan mahimmancinta a gare shi." Kallon takaici Muhdeen ke yi wa Gwaggo sai da ta Kai K'arshen maganarta sannan ya ce, "Banda kud'in da zan siya mata wani kayan lefe yanzu,dududu Yaushe nayi auren?sati biyu kenan fa kinsan miliyoyin da na kashe a lokacin auren nan kuwa?banda wani kud'in lefe yanzun keda kika had'a auren sai ki siya mata kayan lefen." "Dan k'aniyarka ba gata nayi maka ba?" Bud'e baki yayi da niyyar maida Mata da martani Dady ya daka masa tsawa. "Kai Muhammad ka shiga hankainka , Mahifiyar tawa ce kake maidawa magana a gabana?" Sunkuyar da kansa yayi k'asa yayin da Gwaggo ta d'ora da cewa "A'a Sani ba ruwanka da shi ai wannan tsakanin kaka da jika ne ka kyalemu kawai." Jinjina kai Dady yayi tare da kallon Muhdeen ya ce, "To na dai sanar dakai sati mai zuwa Zata tare a gidanka,sannan batun kayan lefe Kai da kanka zaka had'o mata ne ko kuma kud'i zaka bayar?" Hannu ya saka cikin aljihun wandonsa ya ciro A.T.M card d'insa ya mik'awa Mummy. "Ga shinan duk abunda kuka siye sai ku cire ku biya tunda kinsan pin d'in." Amsar A.T.M card d'in tayi tare da sa masa albarka.Dady ya mik'e don dama Shirin fita yayi,daga nan yayi masu sallama ya fita.Mummy ce ta ce, "Bari na shiga ciki na d'auko waya ta na kira Aunty Abla ta shirya gobe zamu je mu had'o kayan lefen." Daga nan Mummy ta mi'ke ta nufi d'akinta,Gwaggo ce ta kalle Mufida ta ce, "Ke 'yar nan tashi ki d'auko Mani magani na nasha don anjima zamuje mu d'auko Inteesar" Cikin zumud'i Mufda ta Fara magana "Gwaggo anjima za'a d'aukota?" "K'warai kuwa anjima za'a d'aukota mu kawota gidannan idan sati d'ayan yazo sai a kaita gidan mijinta." Cikin farin ciki ta nufi d'akin Gwaggo yayin da Muhdeen ya mik'e ya fice, Gwaggo na ce masa "Asauka lafiya" Ko kallonta baiyi ba ya daka Kai ya fice. Inteesar ce zaune a gaban Abba da Umma a tsakar gidansu,Abba ya kalleta cikin nutsuwa ya ce, "Inteesar" Jin yadda yadda Kira sunanta cikin wata irin murya yasa ta zuba mada ido tana jiran Mai zaice. "Kiyi hak'uri na yanke shawara akanki ba tare da na tuntu'be ki ba,banyi shawara dake ba naji r'ayinki ba kiyi hak'u..." Idonta ne ya ciko da k'walla cikin rawar murya ta fara magana "Abba don Allah ka daina bani hak'uri akan koma meye,nice ya kamata na baka hak'uri ba Kai ba,duk shawar ko hukuncin da ka ga ya dace ka yanke akaina dai-dai ne Abba.Ni Mai biyayya a gare ka na ka daina bani hak'uri idan kana bani hak'uri ji nake kamar ban cika 'ya Mai biyayya a gare ka ba." Shiru yayi cikin alfahari da 'yar tasa ya fara magama "Na aurar da ke" Da sauri ta d'aga ido tana kallonsa da mamaki,ganin irin kallon mamamkin da takeasa ne ya sashi fad'in "Kiyi hak'uri" Sunkuyar da kanta tayi k'asa hawayen da suka taru mata ne suka samu nasarar zubowa,cikin rawar murya ta ce, "To Abba " Hawaye ne suka cika idanun Umma Don bata ta'ba kowa wa a ranta cewa Nan kusa zata rabu da 'yarta tilo ba,Amma gashi k'addara tasa lokaci guda ba zato ba tsammani zasu rabu ba,ita da ganinta sai ranar da tazo gaishesu.Abba ya cigaba da cewa "Ki kasance Mai biyayya ga mijinki yi nayi bari na bari duk abunda ya umarce ki da kiyi masa to kiyi masa matuk'ar bai sa'bawa addinin musulunci ba.sannan ki zauna lafiya da abokiyar zamanki ki bata girmanta a matsayinta na wacce take gaba dake,ki zama mai kauda kai akan al'amarin mijinki da abokiyar zamanki,kiji kik'i ji ki gani kik'i gani ki zama Mai kyautatawa ga kowa mijinki da danginsa da kowa da kowa.Ki zama Mai nutsuwa da kamun kai a duk inda kike,ki girmama mijinki kibi shi sau da k'afa kindai ga irin zaman da mukeyi da Mahifiyarki a cikin gidan nan kiyi koyi da ita." Nan dai ya cigaba da Mata nasiha masu ratsa jiki Umma ma ta d'aura da nata, Inteesar dai kanta a sunkuye yake sai kuka da takeyi.Ganin kukan nata yayi yawa ne yasa Abba ya Umarce ta da ta tashi ta shiga d'akinta. Bayan shigar ta d'akin ne,Abba ta kalli Unma ya ce, "Dama kinsan munyi maganar kayan d'akinta akan zan siyar da dabbobi na a siya Mata kayan d'aki tunda auren ba shiyawa akayi ba." "Eh na sani haka ne" Cewar Umma dake goge hawayent,Abba ya d'aura da cewa "Naje na samu kadintan nan dake bakin titi muna maganar kayan d'akin ne sai naga Alh.sani ,wato mahaifin Muhdeen ya tsaya da motarsa Yana horn,juyawa sai naganshi na k'arasa muka gaisa nan yake sanar Dani cewa kada muce zamu siye ki cokali domin su day kansu zasuyi Mata komai.Shi ya d'auki naiyin kayan d'aki komai zai siya matarsa kuma Hajiya Fatima zata siya Mata kayan kitchen,da na nuna cewa yayi yawa shine yake ce Mani Wai na manta cewa Inteesar 'yarsu ce?ko da ace ba d'ansu ne zai aure ta ba zasuyi Mata kayan d'aki ballantana tuwo na maina." Cikin jindad'i Umma ta sanya masu albarka. 'Bangaren Muhdeen kuwa yana komawa gida Kai tsaye ya nufi d'akin Sumayya,yana Isa k'ofar d'akin kuwa ya samu K'ofar a wangale,Kai tsaye ya tura Kai cikin d'akin amma bata nan ga 'barnar da tayi kaca-kaca.Closet d'in ta ya duba kayayyakin da ta yayyaga kawai ke ciki, toilet ya nufa k'ofar toilet d'in ma a bud'e take,yana makin ina Sumayya ta shiga don dai bata shiga kitchen amma duk da haka ya kutsa Kai a cikin kitchen d'in ya duba bata nan.Gaba d'aya haka ya bincike gidan nan ko wane d'aki lungu da sak'o ba Sumayya ba alamarta,sai yayi dabarar tambayar Mai gadin ko yaga fitarta nan mai gadin ya sanar dashi cewa ta fita bayan fitarsa ba dad'ewa.Nan hankalinsa yayi masifar tashi har ya rufe mai gadin gidan da fad'a kamar zai rufe shi da duka shi dai hak'uri kawai yake bashi,don yasan bashida laifi amma yasa shi gaba da fad'a alhalin shi a matsayinsa na mai gadi ya isa ya hana matar gida fita?haka ya k'araci fad'arsa ya fice. Gurin ajiye motocinsa ya nufa ya figi motar a guje Mai gadin ya wangale masa gate ya fice ya fice daga gidan.Parking yayi a gefen titi yana ta sak'e-sak'e ina Sumayya zata tafi?gashi Dad d'inta da Mum d'inta basa nan sun koma London,dama can suka fi zama ko sunzo Nigeria basa jimawa zasu koma.yanzun ta Yaya kuma ta Ina zai fara? Kai tsaye gidan k'awarta Jumy ya nufa a k'ofar gidansu ya sameta tana zance da saurayinta a cikin mota,bayan yayi parking ne kasancewar Jumy ta hangi motarsa yasa ta fito,bayan sun gaisa ne ya tambayeta k'awar ta sanar dashi bata ga Sumayya ba ya sanar da ita cewa bata gida kuma wayoyinta duka basa shiga,daga Nan dai ya yi Mata sallama ya tafi,gidan Shila ya nufa nan ma bata nan k'arshe dai haka ya hak'ura ya nufi gidan Abokinsa Salisu,daga waje ya tsaya ya kira Salisu a waya ya sanar dashi cewaa yana gida ya shigo ciki. Bayan ya shiga cikin gidan ne ya samu Salisu a fall da matarsa Saliha sai 'yarsu k'arama 'yar shekara d'aya mai suna Hidaya da sallama ya shigo falon. "Assalamu Alaikum" "Wa'alaika salam" Salisu ya fad'a yana mik'ewa tsaye ya k'arasa wurin Muhdeen ya bashi hannu sukayi musabaha tare da janyo shi ya zauna kan kujera. "Abokina da alama yau dai kayi 'batan hanya ne ko?" Murmushi kawai Muhdeen yayi tare da cewa "Bari kawai" Saliha matar Salisu ne ta gaida Muhdeen "Ina wuni ango?" Murmushin yak'e yayi tare da cewa "Lafiya lau Saliha" "Ya amarya?da Safen nan muka gama zancen zuwa gidanka naga amarya." Murmushin yak'e kawai yayi tare da d'aukar Hidaya Yana Mata wasa. Saliha ce ta nufi kitchen take ta kawo masa abun ta'awa,duk d yunwar da yake ji baya tunanin zai iya kai want abu a bakinsa.ganin Saliha na zaune ne kum ga shi magariba ta kusa yasa ya mi'ke yayi Mata Sallama ya nufi k'ofar fita inda Salisu yabi bayansa suka fice. A Harabar gidan suka tsaya Salisu ya zuba masa idanu ganin yadda yadda gaba d'aya ya canza lokaci guda. "Lafiya kuwa?naga gaba d'aya ka sauya me ya faru ne?" Ajiyar zuciya Muhdeen ya sauke,sannan ya bawa Salisu labarin duk abunda ya faru.A jiyar zuciya Salisu ya sauke. "Lallai kana cikin yanzun abuda za'ayi shine mu bari muyani Ko Sumayya zata dawo idan har takai dare bata dawo ba zuwa gobe da sassafe sai mu san abunyi." Nan dai suka cigaba tattaunawa kafin sukayi Sallama ya tafi. Washe gari ne ya kama ranar da za'aje a had'o ma Inteesar kayan lefe,kuma a ranar ne za'a d'auko ta a kawo ta gidan su Mummy.Da misalin k'arfe goma na safe ne Aunty Abla k'anwar Mummy da kuma k'awar Mummy Hajiya Ameera suka zo don siyowa Inteesar kayan lefe.su uku suka tafi Mummy da Aunty Abla da Aunty Ameera ne suka tafi,aka bar Gwaggo da Mufida a gida. 'Bangaren Inteesar kuwa kwana sukayi ita da Ummanta tana tayi mata nasiha Inteesar tasha kuka kamar ba gobe har idanunta sun kumbura,ita dai bata san waye mijinta ba abunda ta sani kawai ance mata an aurar da ita, kuma an sanar da ita cewa yau zata koma gidan Mummy da zama kafin ranar juma'a akaita gidan mijinta.Bayan wannan bata san komai ba.Haka dai dai tayi ta Addu'a tana Kai kukanta ga Allah akan auren nan yasa ya zama alkhairi a rayuwarta. Da misalin k'arfe biyu na rana Mummy da su Aunty Abla suka dawo nik'i -nik'i da akwatunan da kayyaki a ciki akwatunan guda takwas ne da kayan da duk ake had'awa a cikin lefe,komai yayi kyau masha Allah.Nan dai aka bajewa Gwaggo kayan tana dubawa tana Sanya alkhairi da Addu'a Allah yasa shekara Mai zuwa ta Muhdeen da Inteesar. 'Bangaren Muhdeen kuwa ya yi neman Sumayya har ya gaji,ya Kira layin wayarta bila adadin shida Salisu tun safe suke ta nemanta Amma ba Sumayya ba labarinta,duk inda yasan tana da alak'a da mutanen wajen sun tafi wajen amma basu sameta ba. a cikin kwana d'aya muhdeen yabi ya zabge ya fita hayyacinsa domin hankain Muhdeen yafi jirgin sama tashi. Daga alk'amin ✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DOMIN K'ARIN BAYANI* 09065327995 Love u oll🥰😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne mai kashe auren wawa. Page3️⃣2️⃣ A cikin kwana d'aya muhdeen yabi ya zabge ya fita hayyacinsa, domin hankalin Muhdeen yafi jirgin sama tashi. A yammacin ranar ne Gwaggo da Aunty Abla da Hajiya Ameera suka je gidansu Inteesar dan d'auko ta.Umma ce da k'anwar ta Huraira sai k'awayenta su biyo da kuma mak'ota da suka shigo Umma ta sanar dasu,duk da ba taron biki akayi ba amma za'ayi taron biki ranar juma'a a gidan Mummy.Mama Huraira k'anwar Umma ce ta shirya Inteesar cikin atamfa riga da zani da Ummanta ta d'nika mata sai mayafi fari da aka yafa mata ta lullu'be fuskarta da shi,idan ka ganta sai ka tausaya Mata idanunta duk sun kumbara sunyi jazir hatta fuskarta ma duk tayi ja ta kumbura saboda tsabar kuka.Ita dai gata zata rabu da Abbanta da Ummanta,zata je can wani gida inda zata shirya sabuwar rayuwa gashi ita kanta ba'a fad'a mata waye mikinta ba kuma itama bata tambaya ba, tambayar da taketayiwa kanta shine,shin shima mijin bai santa ba kamar yadda itama bata sanshi ba?shin wace irin rayuwa zata yi?yanzun shikenan ta rabu da Ummanta da Abbanta kenan sai randa yazo gaishe su? Kuka ne yaci k'arfinta dakyar mama Huraira ta rarrasheta tayi shiru ta dakatar da kukan da takeyi.Nasiha sukayi mata Mai ratsa jiki sannan aka ja hannunta don tafiya,nan fa ta coge ta ri'ke hannun Umma tana kuka dakyar aka 'ban'bare hannun Umma daga nata,hakan yasa Umma itama hawayen da ta rik'e suka samu nasarar zubowa.A haka tana kuka suka nufi hanyar fita inda Mama Huraira ta tsaya da ita zauren gidan wajen Abba,shima ya d'ora da nasa nasihar sai kuka Inteesar take yi,haka dai aka ja hannunta suka nufi hanyar fita, inda aka jera motoncin.Motoci guda uku ne aka shiga da Amarya d'aya inda Mama Huraira da k'awayen Ummin suka shiga mota d'a ma'kotansu ma d'aya,yayinda su Gwaggo da Aunty Abla ma suka shiga d'aya.duk da cewar unguwa d'aya ce basu da nisa minti kad'an suka isa gidan,bayan Mai gadi ya wangale masu gate ne suka shiga nan aka firfito Mama Huraira ce ta rungume Inteesar ta gefen kafad'arta suka shiga cikin gidan. Part d'in Muhdeen da ya zauna kafin ya auri Sumayya nan aka ajiyeta,duk da cewar ba dad'ewa yayi da barin d'akin ba sati biyu kenan,ba wani k'ura sosai dama Mummy ta sanya Mufida ta gyara part d'in.Da sallama suka shiga falon ba kowa sai k'amshi ke tashi,har bedroom aka shiga da ita inda aka zaunar da ita bakin gado.kasncewar lokacin sallar magariba ne yasa sukayi Mata sallama akan cewa zasu dawo ranar juma'a,waro ranar da za'a kaita gidan mijinta. Har yanzun Inteesar Bata san waye mijinta ba ta d'auka saboda shak'uwar da ke tsakaninta da 'yar gidan su Mummy yasa aka ce ta zauna nan gidan kafi akaita gidan mijinta. Bayan kowa ya watse ne ita kad'ai ta ragae a d'akin,ido ta zubawa d'akin tana k'are masa kallo a zuciyarta tana cewa d'akin wannan mugun aka kawo ni,mutum sai mugunta da da bak'in hali a haka dai ta nufi toilet ta d'auro alwala tazo ta shimfid'a sallaya ta tada sallah. A can aibitin Muhdeen kuwa Salisu ne ya fito daga d'akin tiyata hankalinnsa a tashe, wayarsa ya ciro Number Muhdeen yayi dialing, Muhdeen na kwance a samam gadonsa ya lumshe idonsa kamar mai bacci tunanin Sumayya kawai yakeyi,ya rasa ina zai same ta faga k'arshe dai ya yanke shawarar zuwa London wata kila can take tafi wajen iyayenta,yana cikin wannan tunanin ne wayarsa ta fara ruri da sauri ya bud'e idonsa don kullun baya cire rai akan Sumayya zata kira sa,ganin Jabeer ne yasa shi sakin tsuki don dama haushin Jabeer ya ke ji akan bai goyi bayansa ba ya juya masa baya.Yana gani wayar ta katse bai d'aga ba,har aka k'ara kira still bai d'aga ba sai da Jabeer ya kira sau biyar sannan ya d'aga don yasan idan Jabeer ya matsa da kira akwai abu mai mahimmanci da yasa shi yawaita Kiran.Daga wayar yayi ba tare da yayi magana ba,ganin ya d'aga yasa Jabeer ajiyar zuciya

Chapter 12 of 38