Share this page
ƙoƙarin tashi zaune yayi yana cije leɓe har lokacin hannunsu na riƙe da juna, Gwaggo ce ta ce, "Muhammadu ya jikinka?" Kai ya jinjina tare da cewa "Da sauƙi Gwaggo" Nan ma Mummy da Mufida suka gaishe su ya amsa masu, Jabeer ne ya fita ba jimawa sai gashi ya dawo da kofin shafi ya bashi daƙyar yasha sannan Jabeer ya bashi magani yasha. Haka farin ciki ya lulluɓe zuƙatansu Ganin ƙarfe goma tayi ne yasa yasa Jabeer ya ce su tafi gida shi yana tare da shi, hakan yasa suka tafi Gwaggo, Mummy, Mufida da Inteesar sukayi masa sallama zasu tafi, maraice fuska yayi alamar baiso tafiyarsu ba kuma duk saboda Inteesar ne, Mummy ce ta kalle shi tayi murmushi "Son kada ka damu da sassafe zamu dawo." Kai ya jinjina alamar gamsuwa daga nan sukayi masa sallama suka tafi, Jabeer ne ya kalli Sumayya ya ce, "Ke fa ba zaki tafi bane yanzun dare yayi." Fuskarta ba walwala ta ƙarasa wajen gadon Muhdeen ta ce, "Baby baka ganni bane?" Murmushi yayi ya tare da cewa "Ba kece kika fara mani magana bayan Jabeer ba? mun gaisa ai." Cikin ƙunar rai ta fara magana "Shine ko kallo ban ishe ma ka ba ko? amma daga jin muryar waccan bagidajiyar kucakar yarinyar ka maida hanakalinka akanta saboda tafini a wajenka ko?" Girgiza kai yayi tare da cewa "Bakwai ta fiki a wajena bane a'a matsayinku ɗaya ne ba wacce tafi wata" "Ba haka bane ka fifita ta a kaina mana, ki ta kaina ma baka bi ba sai da ta fita sannan ka kalle ni ka kuma kama hannunta ka riƙe kana kallon fuskarta kamar ka samu farin wata, me ta fini da shi da ka maida hankalinka akanta ka amsa mani." Dade kansa yayi jin yana sara masa don baya son hayaniya, lura da hakan yasa Jabeer ya ce, "Sumayya meye haka? mutumin da yake cikin wannan halin ne zaki saka a gaba kina damunsa da hayaniya? wannan ba dai-dai bane." "Yanzun ne kasan ba dai-dai ba? lokacin da nayi masa magana bai kalle ni ba ya zubawa waccan 'yar matsiyatar ido me yasa baka faɗa masa wannan ba dai-dai bane?." Muhdeen kam rintse idanunsa yayi tare da riƙe kansa dan maganar Sumayya ma ciwon kai yake saka sa. Fita tayi fuuu kamar wacce zata tashi sama, wajen motarta ta nufa ranta a matuƙar ɓaci ga zafin kishin da take ji akan Inteesar ɗin, kai tsaye wayar ta ciro a handbag ɗinta number Bashir ta Kira, bugu biyu ya ɗaga kafin yayi magana ta ce "Kana ina ne gidanka ko hotel?" Yana kwance a kan kujerar mai zaman mutum uku ya ce, "Ina gida ne ya akayi?" "Lahira zatayi baƙuwa" Cikin rashin fahimtar inda zancenta ya dosa ya ce, "Ban fahimci inda zancenki ya dosa ba." "Am on my way" "Till you come?" Daga nan ta katse kiran ta tayar da motar tana ayyana yadda zata aiwatar da shirinta, tayar da motar tayi ranar Asibitin ta ɗauki hanyar gidan Bashir. *Saura pages guda 10 na kammala book 1 insha Allahu, zamu shiga book 2 amma book 2 paid book ne idan kin siya ki karanta* Daga alƙalamin ✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DON NEMAN ƘARIN BAYANI* 09065327995 Love you oll😍😘 Comments & shara Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Idan kinsan cewa kina cikin group ɗin Inteesar to kada kiyi joining wannan, duk abu ɗaya ne Sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group dan ko kin shiga idan baki comments zan fitar da ke ne. *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page7️⃣1️⃣ Daga nan ta katse kiran ta tayar da motar tana ayyana yadda zata aiwatar da shirinta,tayar da motar tayi ta ɗauki hanyar gidan Bashir. Horn yayi mai gadin gidan ya leƙo ganin ita ce yasa ya wangale mata gare ɗin gidan ta shiga, bata ma tsaya yin parking da kyau ba ta fito ta nufi hanyar da zata sada ta da falon, tura ƙofar tayi ba tare da tayi sallama ba, ƙamshin turarenta ne ya tabbatar wa da Bashir ta iso,miƙewa yayi daga kwance da yake ya tashi zaune tare da ware hannayensa duka biyu, alamun tazo gare shi, ƙara sawa tayi tare da faɗawa jikinsa ya rungume ta, ajiyar zuciya ta sauke. "Waye ya taɓa ki? ki kwantar da hankalin..." Kafin ya kai ƙarshen zancenta ta katse shi da cewa "Hankali na bazai taɓa kwanciya ba matuƙar tana raye, mutuwarta shine kwanciyar hankaalina." "Wace ce?" Wani tunani tayi dan haka bata amsa masa tambaya da yayi mata ba. "Nace wace ce, mutuwarta ne kwanciyar hankali a gare ki?" Ƙara tsuke fuska tayi "Bai shafe ka ba." "Ki faɗa mani wata kila ma akwai amfanin da zanyi maki." "Babu wani amfanin da zaka mani a matsayinka na abokin miji na." "Domin ina da yaƙinin zaka iya taimakonsa ta wata fuskar" "Badai Inteesar kike ƙoƙarin kashewa ba?" "Ba matsalarka bace" "Idan ma ita ce tun yanzun ki fidda abunda ke cikin ranki, domin Inteesar she is innocent.." "Me ye matsalarka da ita ce, naga matar abokinka ce, bayan haka nana tunanin akwai wata alaƙa a tsakanin ku" Jinjina kai yayi tare da cewa "Tabbas ba wata alaƙa a tsakanina da ita bayan ta matar aboki a gare ni, kuma ita ce matar da na fara tunanin mallaka a matsayin uwar ƴaƴa a gare ni." Da sauri Sumayya ta miƙa daga jikinsa tana masa kallon mamaki, ya cigaba da cewa "Tun kafin Muhdeen ya fara sonta nake sonta duk ƴan mata da nake da su da kuma waɗanda nake gani banaga wacce ta ta mallaki duk abinda make so a wuri ƴa mace ba sai ta, ita ce ta cika 💯 irin zaɓi na." Taɓa baki tayi tare da jan tsuki, jin taja tsuki ne ya kalle ta ya ce, "Kishi kike ne?" "Allah ya sauwaƙe, akan mijina da make so kamar raina zanyi kishi, shi kaɗai ne nake kishi akansa saboda shine wanda nake haukar so, bayan shi banga namijin da ya isa nayi kishi akansa ba." Dariya yayi tare da cewa "Kina kishinsa har haka amma kika kasa killace masa kanki, kike fita kina waufantar da kanki ga wasu mazan da ba baki ba?" Murmushin takaici tayi tare da cewa "Ba laifinka bane laifi na ne da na baka kaina dole kayi mani duk cin kashin da kaga dama." Ƙoƙarin tashi daga jikinsa tayi yayi saurin janyo ta jikinsa ya ƙara katse ta "Am sorry" Bata ce komai ba ta cigaba da ƙoƙarin ƙwatar kanta yayinda shi kuma bai sake ta b. "Don Allah kiyi hak'uri Allah ya huci zuciyarki sarauniyar mata, banyi niyyar ɓata maki rai ba, ke ai baƙuwa ta ce dole na girmama ki, kuma na fahimci matsalarki Inteesar ce ko? to kiyi tunanin hanyar raba da Muhdeen yadda zai sake ta Ni kuma na aure ta, kinga Shikenan ke kin samu damar mallakarsa ke kaɗai Ni kuma na samu mallakar macen da nake mafarkin samunta a rayuwata." Shiru tayi tana nazarin kalamansa, tabbas ba zata iya jure ganin Muhdeen da kowace mace na raɓarsa ba kuma tasan raba Muhdeen da Inteesar wani abu ne mai wahalar gaske, don ta lura da yadda yake tsaninin son Inteesar yanzun, ga danginsa suna sonta ba zasu taɓa yarda ya rabu da ita ba, mafita ɗaya ce mutuwar Inteesar, bata san lokacin da murmushi ya suɓuce nata ba har sai da Bashir yaji saurin murmushin nata, kallonta yayi yana murmushi. "Kin amince wane shawara kika yanke?" "Ka zuba ido kawai kayi jallo" Daga nan ta tashi ta shiga bedroom ɗinsa kai tsaye toilet ta nufa, wanka tayi ta fito ɗaure da towel zama tayi ta shafa lotion nasa mai ƙamshi bayan ta gama ta juyo ta kalle shi taga yana kallonta yana mata murmushi yayin da ya haye saman gadon tare da jan bargo, ya rufe jikinsa, bayan ta gama ne ya ƙarasa jikin gadon tare da hayewa saman gadon ya shige cikin barhon itama, janyota yayi jikinsa tare da warware towel ɗin da ta ɗaura shima ya cire kayan jikinsa suka soma saɓon Allah kamar yadda suka saba yi. Washe gari Inteesar na idar da sallar asuba tayi azkar ta nufi kitchen don haɗa breakfast. Farfesun kayan ciki tayi wanda yaji kayan ƙamshi kamar yadda ta lura Muhdeen yana son shan farfesun kayan ciki da safe, don haka tayi shi Musamman saboda shi ta fere dankalin turawa da plantain ta soya da ƙwai sai ruwan shayi da yaji kayan ƙamshi, tayi kunun gyaɗa da bayan ta jiƙa wake ta wanke ta zuba tattatasai da albasa tayi blendin tayi ƙosai. Koda Mummy ta fito ƙarfe bakwai ta tarar da Inteesar a kitcheen har ta gama komai, murmushi tayi "Daughter yau da sammakon aiki kika tashi? baki gajiya ne?" Murmushin tayi tare da sunkuyawa ta gaida Mummy, ta amsa mata cikin farin ciki buɗewa ta fara yi tana mamakin yadda cikin ƙanƙanin lokaci Inteesar ta gama ayyukan nan. "Sannu da ƙoƙari Allah yiyi maki albarka" Murmushi kawai tayi inda ta ɗauko basket ta fara shirya wanda za'a tafi Asibitin dasu, kallonta Mummy tayi tare da cewa "Waɗannan da?" "Mummy na yaya ne da za'a kai masa Asibiti." Murmushin jin daɗi Mummy tayi don taji daɗin jin hakan har cikin ranta, don yanzun ta lura tun lokacin da Muhdeen ya durƙusa a gaban Inteesar yana kuka yana riƙe rigarta tare da roƙonta tayi haƙuri ta koma gidansa, tun a lokacin Mummy ta hango soyayyar Muhdeen acikin idanunta, amma duk da haka zata gwada ta dan ta tabbatar da abinda zuciyarta ke faɗa mata, kallon Inteesar tayi tare da cewa "Oh yanzun abincin nasa ne kika haɗa? saboda shi kikayi wannan sammakon?" Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana wasa da yatsun hannunta, ba tare da ta ce komai ba Mummy ta cigaba da cewa "Idan kin kammala ki bawa Direba ya kai masa kiyi zamanki ki huta, ba wanda zai je." Da sauri ta kalli Mummy tana so tayi magana kuma tana jin nauyin Mummy dan haka ta nufi ɗakin Gwaggo, kallo ɗaya Gwaggo tayi mata taga yanayinta ya sauya, dan haka ta ce, "Lafiya kuwa?" Girgiza kai tayi ba tare da ta ce komai ba, Gwaggo ta ce "Akwai abunda ya faru naga duskarki ba walwala, daga ina kike? A takaice ta ce, "Kitcheen" Miƙewa Gwaggo tayi tare ta nufi kitchen, ta samu Mummy ta ce, "Fatima lafiya naga Inteesar ta fito daga nan kitcheen duk yanayinta ya sauya?" Dariya Mummy tayi tare da cewa "Dama ina son na tabbatar da hasashe na ne, yarinyar nan sammakon zuwa kitcheen tayi tana girkawa mijinta abinci, kuma inda zaki tabbatar saboda shi tayi duk abincin da yafi so shi ta girka masa, saboda na ce, Direba ne zai kai ba wanda zai je shine fa ta shiga wannan halin, nima na faɗa ne kawai dan naga yadda zatayi." Murmushin kawai Gwaggo tayi ta fita daga kitchen ɗin zuwa ɗakinta kallon Inteesar tayi tare da cewa "Kiyi wanka kiyi breakfast sai kibi Direban ku tafi ko?" Bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba,tayi saurin rufe fuskarta da tafin hannunta, Gwaggo dariya itama tayi tare da cewa "Wato dama can kina son mijinki kike nuna baki sonsa ko? to anyi walƙiya na ganki kina so kina kaiwa kasuwa, har kina roƙo kina kuka akan cewa baki sonsa a raba auren, to yanzun da an raba auren wa kika cuta idan ba kanki ba? don nima nasan cewa idan kika rasa miji irin jikana Muhammadu kinyi babban rashi, samun miji kamarsa sai mai Sa'a irinsa basu da yawa a wannan duniya, bawai ina faɗa maki haka a matsayin yana jikana bane a'a ina baki shawara ne a matsayi na na babba a gare ki wacce ta hango abinda ke baki hango shi ba, ki riƙe mijinki hannu biyu da kyau, kinga har kusan kashe kansa yayi a dalilin an hana sa ke yana masifar sonki fiye da yadda nake zato, don banyi tunanin cewa yana sonki har haka ba, shiyasa nima na sauko daga dokin fushin da na hau da shi, dan na fahimci irin son da yake maki, yanzun mahaifiyarsa ma tasan da hakan, mutum ɗaya ne nake tunanin zaku fusƙanci ƙalubale daga wurinsa wato Mahaifinsa, dan naga yadda ya ɗauki abun da zafi sosai, ni kuma bazan ce masa komai ba duk shawara da ya yanke akai Shikenan." Da sauri Inteesar ta kalli Gwaggo ta ce, "Idan bai amince ba fa?" "Sai kuyi haƙuri bana son nayi saurin saka masa baki, wannan karon zan barshi yayi iko akan ɗansa, ba kamar kwanakin baya ba da nake masa katsalandan na hana shi aiwatar da hukuncin da yayi niyya, amma idan naga abun yayi yawa zan taka nasa birki ne." Cikin sanyin jiki ta nufi toilet don yin wanka, Mufida ce ta shigo take tambaya ina Inteesar Gwaggo ta sanar da ita yadda sukayi tun daga kan girki har zuwa wankanta zata je Asibiti, dariya Mufida tayi tare da cewa "Lallai kuwa bari nayi mata kwalliya ta musamman, ina zuwa." Ta fita zuwa ɗakinta kasancewar Inteesar da ta farfaɗo daga Asibiti aka taho da ita nan, so ba kayanya ko ɗaya a nan kayan Mufida take sakawa tunda kusan jikinsu ɗaya duk da cewar akasarin ɗinkunan Mufida suna matse ta cif ita kuma bata cika son ɗinkuna da suka matse mata jikinta ba. Sai da Mufida ta zaƙulo wani wani leshi milk colour da broun yana da ratsin golding color, sai ta fito mata da mayafi golding colour sai hakka da takalmi broun ta kwashe su tare da kayan kwalliya ta nufi ɗakin Gwaggo, lokacin Inteesar har ta fito daga wanka tana shirin zuwa ɗakin Mufida sukayi karo da juna, komawa baya Inteesar tayi Mufida ta kalle ta ta ce "Kayan da zaki saka na kawo maku, dan so nake ki burge mijinki fiye da waccan matar tasa, dan naga juya da ta ganki kamar zata haɗiye zuciya ta mutu dan baƙin ciki, yau so nake ki kece raini ki fito kamar wata Amarya." "Kinga Mufida meye abun wani kwalliya a cikin zuwa asibita?ni ba shi zai kaini ba kibarshi kawai." "Wallahi sai kin saka." Bata jira sawarta ba kawai sai ta fara ƙoƙarin zura mata kayan, ganin haka yasa Inteesar ta karbi kayan tare da cewa "Bari nasa da kaina." Bayan ta saka kayan ganin yadda siket ɗin kayan ya matse ta tam a jikinta hatta hips nata sai da suka bayyana, kallon Mufida tayi tare da kwaɓe fuska kamar zata yi kuka ta ce, "Bazan iya fita da kayan nan ba." Dariya tayi tana kallon Inteesar ta ce, "Wow gaskiya Allah yayi halitta a nan kinga yadda kikayi kyau kuwa?" Yamutshe fuska Inteesar tayi "Kinga ni ban damu ba nafi son saka abaya gaskiya, wannan kayan takura Ni zaiyi baki ga yadda suffar jiki na suka bayyana ba?" "To meye?" Girgiza kai tayi "Nidai gaskiya bazan iya ba." "Wajen mijinki fa zaki" Bata saurare ta ba ta fara mata makeup duk da ta ce bata so amma sai da akayi mata na dole, sarƙa da ɗan kunne na gold ta saka mata duk yadda Inteesar tayi sai da Mufida tayi mata kwalliya ta fito kamar ba ita ba, wani kyau da kwarjini ta ƙara sai fitar da annuri take, kallon Gwaggo tayi tare da cewa "Gwaggo ni da zan tafi Asibiti meye na mani kwalliya kamar wacce zata je gidan bikin?" Taɓe baki Gwaggo tayi tare da cewa "Kunfi kusa Ni bani da lokacinku bari naje na cika ciki na." Daga nan ta fita Inteesar ma tabi bayanta, suka nufi dinning table, ruwan tea kawai Inteesar ta sha sannan ta ce, ta ƙoshi, hakan yasa ta miƙe ta kalli Mufida ta ce, "Ki bani hijabi na tafi." "Gyale na ɗauko maki ki saka?" "Haba kema kinsan bana son saka gyale" " To ni bani da hijabi gyale nake da su hijabi na guda biyu ne na sallah kuma yanzun na saka su cikin washing machine na zuba ruwa da sabulu zan wanke." Kallon ta kawai Inteesar tayi ta nufi ɗakin Mufida, kai tsaye toilet ta wuce ta duba cikin washing machine taga duka hijaban ta saka su ta jiƙa, daga gani tasan da gan gan Mufida tayi haka dan yasan dole zata nema ita kuma ba zata so ta saka ba, takaici ne ya ishe ta dole ta ɗauki mayafin ta saka ta zura takalmi da ɗauki hand bag ta fito, kallo ɗaya idan kayi mata sai ka sake sha'awar kallonta, tayi kyau sosai, ɗakin Mummy ta shiga ta sallame ta itama ta yaba da kyaun da Inteesar tayi, sannan ta nufi kitchen ta ɗauki basket ɗin ta nufi harabar gidan dan ta sanar da Direba ya Kaita Asibiti. Direban Mummy ya buɗe mata bayan motar ta shiga bayan ya saka abincin, sannan ya zagayo ya shiga mazauninsa ya tada motar suka bar gidan *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DON NEMAN ƘARIN BAYANI* 09065327995 Love you oll😍😘 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Idan kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, duk abu ɗaya ne, sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group, dan ko kin shiga idan baki comments zan fitar da ke ne. *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce, bada niyyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page7️⃣2️⃣ Direban Mummy ya buɗe mata bayan motar ya shiga, bayan ya saka abincin sannan ya zagayo ya shiga mazauninsa ya tada motar suka bar gidan. Ɓangaren Sumayya kuwa bayan sun gama abuda sukayi ne suka kwanta rungume da juna a haka barci ya ɗauke su, kiran sallar asuba ne ya tada Bashir ya janye ta daga jikinsa don yasa ko ya ce, ta tashi tayi sallah ba tashi zatayi ba, sai ta gama barcinta, buɗe ido tayi jin ya janye ta daga jikinsa ta ce, "Ina zaka je?" "masallaci zanje, tashi muyi wanka lokaci na tafiya" Gyara kwanciyarta tayi tare da cewa "Idan na tashi da safe zanyi wanka da sallar." Girgiza kai kawai yayi ya nufi toilet don yin wanka, bayan ya fito ne ya saka kaya ya nufi masallaci. Ana idar da sallar ya dawo ya kwanta ya cigaba da barcinsa, ƙarfe bakwai ta farka ta tayar da Bashir ya tashi zaune tare da kallonta "Lafiya Summy?" "Ka fita ka nemo Mani kayan da zansa idan nayi wanka, kasan banzo da niyyar kwana ba kuma ban ɗauki komai ba so kane ka siyo man.." Kafin ta kai ƙarshen zancenta ya ce, "Kwantar da hankalinki Baby akwai kaya ana sababbin waɗanda na tanada saboda irin haka, ke dai kawai kije kiyi wanka." Tashi tayi ta nufi toilet bayan kamar mintuna ashirin sai ta fito kanta na ɗaure da towel, ba tare da jin komai a ranta ba ta warware towel d'in ta shafa mai shaf-shaf t gama shiryawa ta ɗauki doguwar riga ta material da Bashir ya ajiye mata ta saka ɗan ƙaramin mayafinsa ta saka ta kwashi wayoyinta da jakarta ta nufi hanyar fita, har ta kai bakin ƙofa ta jiyo muryarsa yana cewa "Bako sallama?" "Sorry Dear may be na dawo ta nan, amma ba tabbas ko na koma gida sai shawarar da na yanke." "Okay sai munyi waya kenan?" "No kada ka kira waya ta idan ba nice na kira ka ba kada ka kira ni, idan ma akwai wani abu ne to kayi mani text message idan da yiwar nayi magana zanyi maka magana ta waya, idan babu kuma zaka ga text message ɗin a." Daga nan bata jira amsar da zai bata ba tayi ficewarta har ta kai tsakiyar falo ta ji ya ce, "Ba zaki tsaya muyi breakfast?" "Kai ta girgiza tare da ɗaga hannunta na hagu tana kaɗai yatsarta manuniya alamar a'a." Daga nan tayi ficewarta gurin motarta, shigewa tayi tare da tada motar ta bar gidan. Kwance yake bayan Jabeer ya taimaka masa yayi wanka, ya dawo ya zauna, Jabeer ne ya shigo hannunsa ɗauke da kayan Muhdeen, kasancewar dama a cikin office ɗin Muhdeen akwai bedroom da toilet don haka ya je ya bedroom nasa cikin wardrobe na kayan Muhdeen ya ɗauko masa wasu ƙananan kaya ya kawo masa ya saka, yana gama sakawa Jabeer ya fita da waɗanda ya cire shi kuma ya kishingiɗa, idanunsa ya lumshe kamar mai barci alhalin ba barci yake ba. Sumayya ce ta turo ƙofar ta shigo, shi dai ya ji motsin shigowar mutum amma baisan ko wace ce ba, kuma bai buɗe idanunsa ba, ƙamshin turaren da ya ji ne yasa ya yayi magana ba tare da ya buɗe idanunsa ba ya ce, "Bashir kaine da sassafe haka?" Gaban Sumayya ne ya faɗi jin abunda Muhdeen ke faɗa, cikin rawar murya ta ce, "Nice kuma Bashir yau?" Da sauri ya buɗe idanunsa ya sauke a kanta, ganin ita kaɗai e yasa ya ce, "Bashir kaɗai nasan yana amfani da wannan turaren shiyasa nayi zaton ko shine, don naji ƙanshin turarensa ne, amma ke me ya haɗaki da irin turaren nan?" Murmushi tayi tare da zama dab da shi inda yake kishingiɗe, tashi zaune yayi ta ƙara matsawa dab da shi, tana shirin yin magana ne sai ga Inteesar ta turo ƙofar bakinta ɗauke da sallama "Assalamu alaikum" Jin muryarta yasa ya zubawa ƙofar ido idanunsa suka sauka akanta, subhanallahi, ai mutuwar zaune yayi sakamakon wani ƙayataccen kyau da yaga tayi, din tunda yake a rayuwarsa bai taɓa ganin tayi nasa kyau irin na yau ba, ko lokacin aurensa da Sumayya da aka mata kwalliya a lokacin kallon arziki bata ishe shi ba, ko lokacin aurenta da shi ma bai ko kalli fuskarta ba, tabarakallu ahsanal khaliqin, shine kalmar da ya furta a zuciyarsa, ita kanta Sumayya sai da gabanta ya faɗi ganin irin kyau da kwarjini da cikar haiba irin ta Inteesar, don ko mace ƴar uwarta ta kalle ta sai ta sake kallonta ballantana namiji, tsananin kishi ne da baƙin ciki suka cika mata zuciya. Ita kuma Inteesar ganin basu amsa mata sallama bane yasa ta sake cewa "Assalamu alaikum" Daƙyar Muhdeen ya iya amsawa da "Wa'alaiki salam" Shigowa tayi hannunta ɗauke da Basket da aka jera abincin a jiyewa tayi a gefe ta sunkuya ƙasa ta gaida Muhdeen. "Ina kwana yaya?" Tsayawa yayi yana kallonta, don tun da yake a rayuwarsa ba mahaluƙin da ya taɓa durƙusawa har ƙasa ya gaishe sa sai ita, farin ciki ne ya lulluɓe masa zuciyarsa don haka ya ce "Kin tashi lafiya" "Lafiya lau ya ƙarfin jiki?" "Alhamdulillah" Miƙewa tsaye tayi tare da cewa "Allah ya ƙara sauƙi" Ya amsa da "Ameen" Kallon Sumayya tayi tare da cewa "Aunty Sumayya ina kwana?" Ganin Muhdeen ne yasa ta amsa mata da "Lafiya lau ya kike?" "Alhamdulillah" Zama tayi a ɗaya daga cikin kujeru da ke cikin room ɗin, Sumayya ganin Inteesar zaune yasa ta ƙara shigewa jikin Muhdeen musamman da ta lura ya mida hankalinsa ga Inteesar ita kawai yake kallo, sajensa ta shafa da hannayenta cikin kirsa ta ce "Nayi missing ɗinka sosai wallahi" Gajeren murmushi yayi tare da cewa "Nima haka". "Da gaske" Kai kawai ya ɗaga mata alamar eh, amma gaba ɗaya hankalinsa na ga Inteesar, ya mace a kallonta abubuwa dayawa yake ayyanawa a zuciyarsa game da ita, lura da hakan yasa Sumayya tayi ƙoƙarin ɗauke hankalinsa dan ya manta da Inteesar dake wajen. Bakinsu ta daɗe wuri guda ta tsotsansa, zaro ido yayi yana kallonta da mamaki, sanin cewa Inteesar na wajen ne yasa ya fara ƙoƙarin zame jikinsa daga nata amma ina sai ƙara ƙanƙamesa tayi a jikinta, hannu tasa cikin sumar kansa kamar maiyi masa susa. Inteesar tana ganin haka ta miƙe ta nufi ƙofar fita da sauri ta fice. Fitarta daga ɗakin ta nemi wani waje da aka tare kujeru ta zauna a harabar wajen, akwai 'yar tafiya tsakani, tagumi tayi tana tuna yanayin da ta barsu take taji wani ɗaci a zuciyarta ƙwalla ne suka taru a idanunta sai tayi saurin mayar da su, tsuki tayi tare da furtawa a fili. "To me yasa ma naji haushin abunda suka yi? ina ruwa na da su? me yasa nake jin kishinsa a raina?." Ita kaɗai take magana sanin

Chapter 33 of 38