Share this page
mu su bayanin cewa aiki yake nema. Securities ɗin sun so gumtse dariyar su amma sai suka kasa don haka suka shiga ƙyaƙyatawa domin kuwa yau sunga ikon Allah wai gurgu da neman aiki, masu ƙafa ma yaya suka ƙare bare shi. Motar da ido bazai iya wassafa tsadar ta ba ne ta ƙaraso daf da inda Abu Zaid ɗin yake tsaye. Wani farin Baturen da kuɗi da hutu suka yiwa kamu mai kyau ne a ciki a zaune, farin hannunsa ya ziro ya miƙowa Abu Zaid sadaka. Maimaikon Abu Zaid ya karɓi iya kuɗin da Baturen ya miƙo mai sai ya damki hannunsa da nashi hannun mai zafin zazzaɓin yunwa da taurin talauci suka kama, jikinsa babu inda baya rawa. Drivern da yake jan Baturen bai lura da hannun Abu Zaid ba ya fizgi motar bayan an buɗe mu su gate ɗin, dalilin haka yasa Abu Zaid zubewa ƙasa bayan ya saki hannun Baturen yana wani irin kuka, da iya girman muryarsa da yunwa ta yiwa raga-raga yake cewa; "Ku taimakeni ku bani aiki banason sadaka, ni ba mabaraci ba ne na roƙeƙu." Baturen dake cikin motar ne ya dakatar da drivern daya ke tuƙasa. Masu gadi jikinsu ya na tsuma suka nufi Abu Zaid don kawar da shi daga gurin gaba ɗaya saboda kar su rasa aikinsu, saboda Baturen ba ƙone ziyara ya kawo wajen MD ɗin Companyn. ***** A ɓangaren Hudayya kuwa. Ta ɗauka saduwa ne kawai aure da kuma jin daɗinsa wannan dalili yasa take ganin kamar ta gama da Taufiq. Abinda ya fara bata tsoro shine satin su ɗaya da tarewa Taufiq ya daina kwanan gidan gaba ɗaya sai dai yazo da safe yayi abinda yaga dama da jikinta ya wuce office. Sai ya zamana ita ba ta da wani daraja sai na bukatar kasancewa da ita. Matar Taufiq sauyin Taufiq na rashin nutsuwa ne yafara hawa kanta, a ɓangaren hidimarta dana ɗan su Taufiq bai sauya ba sai sai dai kwata-kwata baya bata haƙƙinta na auratayya. Macece ita mai juriya da jajircewa wajen kai ƙarar komai wajen ubangijinta don haka ta dage duk dare sai ta gayawa Allah tunda ya rantse mata baya tare da Hudayya. Cikin iko Allah Ubangiji ya amsa addu'arta ya nufi Taufiq da zuwa bikin buɗe kamfanin abokinsa Nazeer da ya sani sanadiyyar Abu Zaid da za'ayi a Lagos. Hudayya da Taufiq yazo yi mata sallama ta yi magiya da kisisinar kar ya je Lagos zatayi ƙewarsa da yawa. Taufiq kansa ya girgiza yana shaida mata muhimmancin gayyatar da Nazeer ya yi mai bayan shekarun da suka kwashe ba su haɗu ba. Hudayya bata san Nazeer abokin Abu Zaid Taufiq yake nufi ba, don haka sukayi sallama ranta babu damuwar komai. N SASAAL [11/6, 12:20 PM] Hajja Ce: ABU ZAID BY NAFISAT ALIYU SASAAL 16 A ɓangarensu Siya kuwa. Bayan kwana shida a asibiti aka sallamota daga asibitin, maimakon a wuce gidan Muhammad kai tsaye, a'a kawai gidan Mommynta su ka wuce da ita. Kwata-kwata babu wani kuzari a jikinta saboda Muhammad ya sauya mata gaba ɗaya. Kwatakwata baya zuwa asibiti kuma baya kiranta a waya yayi banza da ita tamkar bai san da ita ba. Mahaifinsu ne kawai yake kula da ita har aka sallamota bai daina zuwa dubata ba. Bayan kwana biyu Yayan Mommynta Alhaji Sunusi ya kawo musu ziyara, yana sauka ko hutuwa bai yi ba yaji abinda yake faruwa ya nufi gidansu Muhammad don jin menene matsalar da yasa Muhammad ya ɗauke ƙafarsa daga Asibiti kuma babu kira babu komai. Sai dare sosai sannan ya dawo gidan Mommy, tun da ga yanayin rashin sakin fuskarsa Siya tasan ransa a ɓace yake, bayan ta yi masa sannu da dawowa, yunƙurawa tayi zata koma ɗakinta ya dakatar da ita. Sai da ya gama ƙare mata kallo Mommynta na gefensa tana banka mata harara kamar dukka idanuwanta zasu zazzago, sannan yace. "Safiyya menene tsakaninki da mijinki ko yake yi miki mara daɗi da har yanzu bakya son sa bakya son ɗan uwansa? Yace kullum yana lura dake idan ya ce kuje gidan ɗan uwansa sai ki haɗe rai, yayi ƙorafi daban-daban a kanki amma wannan ne yafi bani mamaki don bansan menene dalilinki na ƙin ɗan uwansa da suke jini ɗaya ba." Da sanyin muryar fargaban yadda zasu fassara maganarta Siya ta ce; "Kawu wani irin kallo Zayad ɗin yake min na ƙasƙanci, na rasa me nayi masa." Da sauri Mommynta ta tari numfashinta gudun kar ta faɗi wani abun da zai sosai zuciyar Yayanta akan Muhammad har ya ce kawai a haƙura da auren, ta ce. "Ƙarya kikeyi Siyaama, ina Zayad yaga lokacin ki ma bare har ya yi miki kallan da zai sa kiji kin tsane shi? wallahi idan baki faɗi gaskiya ba zan baki mamaki yanzun nan." Cikin tsoro da yanda za su ƙara fassara maganarta tace. "Bana son ganinsa saboda Basketball ɗin da yake yi, kuma wallahi dagaske nake kallon ƙasƙanci yake min idan muka haɗu dashi." Da mamaki kwance a muryoyinsu Mommynta da Alhaji Sunusi suka haɗa baki wajen faɗin. "Basketball kuma? Hassada kikeyi da ɗaukakarsa?" Da sauri Siya tace. "A'a wallahi ai ba ɗaya muke ba taya zan yi masa hassada." Cikin barazana Mummynta tace. "Siyaa kiyi mana bayani menene dalilinki kafin na yi miki abinda bazaki ji daɗi." Da kame-kamen da tasan bayaninta bazai yi musu daɗi ba tace "Na tsani wasan ne saboda shine dalilin fara shan sigarin Yaya Abu Zaid, amma kallon da yake min ne yasa na ƙara tsanarsa kuma ko na gayawa Muhammad ba zai yarda da ni ba." Kamar ta faɗi mugun abu haka Alhaji Sunusi ya yamutse fuska ransa fal tsanar Ɗalhatu da zuri'arsa. Numfashi Mummynta ta sauke haɗe da ƙura mata ido alamun ta cigaba suna jinta. Cigaba tayi da cewa. "Abu Zaid yana son Basketball, amma Daddy ya hanashi bayan ya gama wahala yakai matakin ƙasa amma Daddy yace shi Business yake so yayi ba aikin wahala da tsalle-tsalle ba." Siya ta ƙarasa faɗa komai daya faru a waccen lokacin na dawo mata. Cikin ɗacin zuciya da kuma tsanar Abu Zaid da Mummynta takeji a ranta tace; "Amma Siyaama kanki ya samu matsala ko? Haka kawai saboda wannan dalilin sai yasa ki tsani Zayad? kinsan waye Zayad kuwa? sau nawa kikeso na ja miki kunne a kan Ibrahim ne? Tayaya Ɗalhatu zai barshi ya zama ɗan wasan ƙwallon kwando tunda burin mallakar dukiyar da ba nasa ba ne a ranshi. Yayaa ina ganin maganar nan ba anan ya dace muyi sa ba ina buƙatar ganin Nenne." Mommy ta ƙarasa faɗa tana kallon Alhaji Sunusi. Kai Alhaji Sunusi ya ɗaga mata don yagane so takeyi su je Tofa a gogewa Siyaa tunanin Abu Zaid. A daren ranar Alhaji Sunusi ya kira Muhammad ya naimi alfarmar tafiya da Siyaa. Muhammad bai ce a'a ba fatan dawowa lafiya yayi musu. ***** A can Legos wajen taron buɗe sabuwar Ma'aikar Nazeer. Taro ya shirya na gani na faɗan daya tara wayayyun mutanen da mafi akasarinsu abokanan kasuwancinsa ne, da yawan su sun san Abu Zaid saboda kasuwanci ya taɓa haɗasu, wasun su sunyi farin cikin rashin hallattar Abu Zaid, saboda yawanci sun damfararshi dan haka suka ɓoyewa ganinshi. Nazeer ya ɗan rame saboda damuwar ɓacewar Abu Zaid, rashin Abu Zaid a cikin rayuwarsa wani giɓi ne da bashi da abin maye gurbinsa da shi. Abu Zaid bai taɓa cutarsa ko cin amanarsa ba, amma sai gashi shi ya zama ɗaya daga cikin waɗan da sukayi silar rugujewar rayuwarsa, yasan da bai bada shedar da gaske Abu Zaid yana neman Hudayya ba da Mahaifinsa bazai amince da zancen Hudayya da na ƴan uwanta ba. Bayan angama taro kafin mutane su watse Nazeer ya nemi alfarmar ayiwa Abu Zaid abokinsa kuma ɗan uwansa addu'a Allah ya bayyanashi ya kuma kareshi a duk inda yake. Dukka waɗanda suka sanshi idan aka cire Taufiq sai a lokacin suka san Abu Zaid ɓata yayi ba ƙin zuwa taron ya yi ba, a take sai jikin su yayi sanyi. Taufiq kuwa wani irin gumi mai tahowa tun daga cikin gashin kai har ƙirjinsa ne yake tsatsafo mai. Da wani irin sauri ya bi bayan Nazeer dake ƙoƙarin shiga mota. Da rawar murya yace. "Nazeer ina buƙatar yin magana dakai yanzu Please." Nazeer ya fasa shiga motar kawai ya bi bayan Taufiq suka nemi waje suka zauna. Bayan sun zauna Taufiq ya roƙi Nazeer ya sanar da shi yaya akayi Abu Zaid ya bar gida, ɓata ya yi kome? Nazeer ƙwallarsa ya sharce yana jin kamar idan ya bawa Taufiq labari zai ɗan samu sauƙi a cikin ransa. Don haka ya gyara zama ya fara ba shi labarin komai. Kuka da ba kasafai namiji mai jin daɗin duniya yake iya yiba Taufiq yakeyi bayan ya ji labarin taimakon da Abu Zaid yayiwa Hudayya har tayi masa haka. Nazeer yana taya shi. Kenan da baiji asalin labarin ba haka zata rabashi da ƴar Aljanar Matarsa? Cikin tunanin irin muguwar sakayyar da yayi wa Abu Zaid yace; "Shekaru biyu da ɗoriya da suka wuce Abu Zaid ya zo tare da Hudayya, Hudayya tayi min ƙarya mai girma Nazeer saboda bansan komai akan ahalin Ibrahim ba, Ibrahim ya rasa ƙafa ɗaya amma duk da haka banji tausayinshi ba na koresa daga aiki, yanzu haka bansan ina yake rayuwa ba, ko yana gidan da na kama mai ko ya tafi wani wajen bansani ba." Kamar hoto haka Nazeer yake kallon Taufiq na tsahon wasu mintoci, kafin ya miƙe batare da ya ce mai komai ba yabar wajen, shi bai ga ma amfanin labarin Taufiq ɗin ba tunda ya fita ya kori Abu Zaid daga rayuwarsa to manene ya rage? Har Motar Nazeer ta bar wajen Taufiq na zaune bai motsa ba saboda takaici. Sha'awar Hudayya da yake ji kamar ba zai daina ba a baya duk sai yaji ta bi ruwa nan take. Baya jin sakin Hudayya kaɗai zai wadatar da shi wajen hukuntata dole sai ya yi mata wani abinda sha'awar ƙarya ko cutar wani zai fice daga a ranta. *** A ɓangaren Abu Zaid kuwa. Drivern dayake jan Baturen ne ya dakatar da securities ɗin dake ƙoƙarin janye Abu Zaid daga bakin Ma'aikatar. Baturen da shekarunsa zasu bawa arba'in baya ne ya sauko, da turancinsa da basa fahimta da kyau yace su taimaki Abu Zaid ya miƙe su daina jansa a ƙasa. Rawar da jikin Abu Zai yake yi ne yasa ya kasa tsayuwa da kyau. Mota Baturen yace a shigo da shi don yana tsoron shiga Ma'aikatar da shi don bai san wanene shi ba. Kallo irin na ƙurilla Baturen mai suna John yake yiwa Abu Zaid kafin ya tambayesa yanajin turanci? Abu Zaid ya amsa masa da turancin da yasa Mr John ƙara kallon cikin Idanuwansa da har lokacin rauni ne lulluɓe cikin su. Murmushi Mr John ya yi kafin ya ce; "Ina da muhimmin abinda zanyi yanzu amma zan haɗaka da driver ya kaika gidan ku idan iyayenka sun amince nayi alƙawarin taimakon ka, ina ne garin ku?" Kai Abu Zaid ya dafe sunan ƙauyen su Siyaa da address ɗin gidan su ne kawai ya rage a kanshi don haka kai tsaye yace "Tofa." Mr John yasa aka siyawa Abu Zaid abincin da ya tsakuri kaɗan saboda bakinsa da ya jima bai wanke ba, sannan suka ɗauki hanyar Tofa shi da Driver. **** A washe garin ranar da su Siyaa suka sauka Tofa Motar Mallam Sa'adu Driver da ya ɗakko Abu Zaid yayi parking a dai-dai bakin bishiyoyin dake ƙofar gidan. A mota Mallam Sa'adu yabar Abu Zaid shi kuma ya sauko ya matsa kusa. Yaro ya tura ayi masa sallama da mutanen gidan. Jin sallama yaro kuma yace Abu Zaid aka kawo yasa suka yo waje dukkan su Nanne, Alhaji Sunusi, Siyaa da Mommynta. Da ƙwarin gwiwa Abu Zaid ya ɗoraga sandarsa ya sauko ganin sun fito gaba ɗaya har da Siyaamar shi. Sai dai irin kallon da kowannen su yake bin ɗan uwanshi da shi ne yasa jikinshi yayi sanyi, domin Siyaarshi ta ƙara zama ƴar gayun matashiyar budurwa duk da yaji ance tayi aure amma gani ya yi tamkar batayi ba. cikin rawar murya bayan ya ɗogaro sandarsa ya matso kusa da su yace. "Siyaa." Siya daga yadda ya kira sunanta tasan dagaske Abu Zaid ne, sai dai har cikin ranta ƙyanƙyami da mamakin rasa ƙafarsa ɗaya takeyi da kuma irin ramar dayayi. Jiki a sanyaye taƙara matsowa kusa da shi cikin ɗari-ɗari da ƙyanƙyamin dake kwance asaman fuskarta ta ce; "Yayaa kai ne ka koma haka? mai ya sa meka ka koma haka? ina Daddy mai yasamu ƙafarka ɗaya ya guntule?" Abu Zaid bai bata amsa ba sai Kukan da ya fashe da shi don bai yi tunani akwai yanayin da zai shiga ya hango ƙyamarsa a idanuwan Siyaa ba. Da sanyi muryarsa dake rawa yace. "Siyaa bakiyi farin cikin ganina ba ko? saboda banzo a yanda kike so na ba a baya ko siya?" Siya da sauri ta toshe hanci tana komawa baya haɗe da zare iduwanta. Gefe ta matsa ta shiga tana ta kwara amai saboda ɗan warin ranar dake tashi a jikinshi da kuma bakinshi dake ɗan bugawa. Hakan da Siyaa tayi ba ƙaramin faranta ran Mummynta da na Alhaji Sunusi yayi ba, saɓanin Drivern daya kawoshi da Nenne dake tsaye suna kallon ikon Allah. Abu Zaid kansa ya sunkuyar ƙasa hawayensa na ɗiga akan ƙasa. Daa labari a ka bashi da ya ƙaryata, har wane irin wari yake yi da Siyaa zata toshe hancinta tana amai? Dama kenan a baya kyansa, tsaftarsa da gayunsa takeso? to manene ya rage mai kuma? Tabbas yanzu jam yasan tashi ta riga ta ƙare masa. Cikin isa da rashin tunanin mai gobe zata haifar Mummynta ta matso ɗan nesa da shi alamun kar itama taji warin dayake yi sannan ta ce "Ibrahim zuwa yanzu ya kamata ka nemi gobenka don ƴata tafi ƙarfinka kai da annamimin Ubanka, kasan wa take aure yanzu kuwa? Toh Siya wani hamshaƙi mai arziƙin da baya zalama da sanya ido akan na wa su ta ke aure. Da haka ka riƙe maganganuna ko Allah zai taimakeka ka zabura ka nemi gobenka domin na lura ƙwaƙwalwarka da ta Ubanka ta jima da toshe wa. Karka ƙara neman Siyaa domin Siya tafi ƙarfinka, shin mai zatayi dakai a da ma bare kuna a yanzu? Gurgu da kai mai warin baki da na jik.." Marin da Nenne ta saukewa Mommyn Siya ne ya hanata ƙarasa abinda tayi niyyar faɗa. Da faɗa sosai Nenne take cewa; "Ya isheki haka Ziyaada wani irin zuciya gareku fisabillahi? Ɗalhatu Mahaifinsa ne kike haɗawa dashi kina ci musu fuskar nan. Kuma da Zaid ya rasa samun mai taimakonsa kai tsaye saboda soyayyar ƴarki ya taho garinku, yaro duk ya rame ya lalace ga ƙafa ɗaya a gutsure amma ku kasa tausaya masa? Itama waccen munafukar har da aman gulma ashe son da kike ikirarin kina yi mai na ƙarya ne? Maza wata rana naji kina kiran sunansa sai na fasa bakinki sha-sha-shai kawai. Kuma wallahi duk wanda ya ƙaracin zarafin yaron nan bada yawuna ba idan bazaku taimakesa ba ku barshi mana haka yaji da abinda yake damunsa." Mallam Sa'adu Driver kuwa bai taɓa ganin rashin tausayi irin wanda suka yiwa Abu Zaid ba, ba su bashi wajen zama ba, ba su ba shi ruwan sha ba balle abinci ba su tambayi dalilin da yasa ya zama haka ba don daga shigarsu kasan ma su wadatar rayuwa ne, shine a ƙarshe suka tozartashi duk da tsananin taimakon dayake buƙata a lokacin nan. Har lokacin Abu Zaid bai ɗago ba sai yake jin jikinsa kamar ba nasa ba, yanajin takun su har na Siyaa suka koma cikin gida sai Nenne kawai ta tsaye a gurin, bata ɓoyewa Mallam Sa'adu dalilin barin Abu Zaid gida ba. Tas ta kwashe ta gaya masa. Sai dai sun gano ainihin gaskiyar abinda ya faru a ƙuraren lokaci, domin ita kanta batasan ina Mahaifin Abu Zaid ɗin yake ba yanzu kuma tana kyautata zaton baya Zaria, amma su matsawa Abu Zaid da tambaya wataƙila ya tuno ya gaya musu. Ba tare da ƙyanƙyami ba Nenne ta kamo hannayen Abu Zaid da suke a yamushe cikin rawar muryar kuka ta ce; "Karka ɗauki nakasar ka amatsayin kasawarka Ibrahim, kayi gwagwarmaya kuma ka roƙi Allah wata rana komai zai zama labari." Kai kawai ya ɗaga mata saboda tsoron magana ma yakeyi. Har su Abu Zaid suka shiga mota Nanne bata tafi ba har sai da suka ɓacewa ganinta. Da haka Abu Zaid yabar ƙauyen Tofa Soyayya da tausayin mutanen duniya na barin cikin ranshi. Bayan su Abu Zaid sun dawo, Tafinta aka nemo yake sauraren Mallam Sa'adu ya kuma fassarawa Mr John abinda ya faɗa. Ran Mr John ba ƙaramin ɓaci yayi ba cikin ɗacin zuciya ya tambayi Abu Zaid ina Mahaifinsa yake? Kai Abu Zaid ya dafe haɗe da girgizarwa kamar wanda a ka tambaya mugun abu. Dakatar da shi John yayi saboda gudun matsala. Masauƙi mai kyau Mr John ya kai Abu Zaid dan ya samu nutsuwa. Da dare yayi bayan Abu Zaid yayi wanka anyi misa aski yayi brush. Likita Mr John ya kira ya duba masa shi saboda zazzaɓin da ya rufe shi, Allura likita ya yiwa Abu Zaid haɗe da basa magani. Bayan wani lokaci barci mai daɗin daya jima baiyi ba ya ɗaukesa. ★ Washe gari bayan Abu Zaid ya karya John ya tura a kirawo masa shi. A ladabbace Abu Zaid ya gaishe shi, Mr John ya amsa yanajin Soyayyarsa a ranshi. Takaitaccen labarin shi ya so ji. Iyakacin abinda Abu Zaid ya iya tunawa kawai ya bashi labari. Kai Mr John ya jinjina kafin ya tambayesa mai yake burin zama a rayuwa tunda da ƙuruciyarsa har yanzu? Murmushin tuna marafin shaye-shayensa ya yi kafin Allah ya tsayar mai iya kan sigari, sannan ya cewa Mr John burinsa na baya shine ya zama Basketball player, har mataƙin ƙasa yakai amma daga baya mahaifinsa ya hana. Shi yanzu ba shi da wani buri tunda ya rasa ƙafa ɗaya waccen burin nasa ya ƙarasa rushewa gabaki ɗaya, sai dai yanzu ya zama ɗan kasuwa idan zai taimakamai da jari. Kai Mr John ya girgiza sannan ya fara magana da salon ƙarawa Abu Zaid ƙwarin gwiwa. "Rasa ƙafarka ɗaya bashi ke nufin mafarkinka ya rushe ba Ibrahim, kasawa ranka da zuciyarka zaka buga kuma zakayi nasara, idan har da gaske kana da ƙwarewa ni nayi maka alƙawarin cika maka burinka wanene yayi maka horon?" Nan ma Abu Zaid kansa ya dafe na tsahon lokaci Mr John ya na kallonsa kamar ya fizgo maganar daga bakinsa. Da kame-kame Abu Zaid ya ambaci sunansa da lambar waya. *** A ɓangaren Hudayya Maganin mata namanyan kuɗin da aka kawo mata tun daga Gwarzo kafin dawowar Taufiq take ta ɗurawa cikinta, cikin shiga mai jan hankali tayi ado tana jiran isowar Taufiq ɗin sai rawar jiki takeyi. Da Taufiq ya dawo, gidan Uwargidansa ya fara biyawa. Kamar mahaukaci haka ya ɗauki Matarsa da ɗansa zuwa shopping mall siyayya na fitar hayyaci ya yi mu su. Bini-bini sai ya sumbaci goshin matarsa yana ƙanƙame hannunta, ita dai batayi mamaki ba don Allah ta roƙa kuma babu abinda ya gagare sa. Bayan sun dawo gida, shiryawa ya yi ya wuce gidan Abu Zaid. Bai samu Abu Zaid ɗin ba, da ya tambayi mutanen gidan sai aka sanar da shi ai ya jima da barin gidan tuntuni. Taufiq bai sha wahalar samun Unguwar da Abu Zaid ɗin yakoma ba ta hanyar dillalin daya nema mai gidan da ya zauna a ciki. Nan ma bai sameshi ba, daya tambaya sai aka sanar da shi labarin sana'ar dayayi ƴan unguwa suka karyashi a lokaci kaɗan da cin bashi, ƙarshe ya koma bara a bakin kamfanonuwa su dai ba su san ina ya tafi ba yanzu don kwanansa uku bai dawo ba kuma sunje bakin Companyn da ya saba zuwa ance bai zo ba. Zafin da zuciyar Taufiq ya ɗauka ne ya sa kai tsaye ya wuce Gwarzo yasa aka kama su Baba Ilu gaba ɗayan su, ƙauye kakaf inda suka ji labari sai dariya akeyi mu su. ★ Washe gari Hudayya tana jin an ƙwanƙwasa ƙofa ta taso ta ƙara zazzago da wuyan shara-sharan rigar dake jikinta haɗe shagwaɓe fuskarta. Ta riga ta kitsa makircin da zata yiwa matarsa don tasan tun a jiyan ya dawo ya wuce wajen ta. Da salo ta buɗe ƙofar idanunta akan...... [11/6, 3:36 PM] Hajja Ce: ABU ZAID BY NAFISAT ALIYU SASAAL 17 A can Tofa wajensu Siya kuwa. Da ɓacin rai Nenne ta shigo gidan. A sitting room ta same su amma banda Siyaa da ta wuce ɗaki. Cikin faɗa da takaicin abinda suka aikata tace, "Yanzu kai abinda ka goyi bayan Ziyaada tayi dai-dai ne a wajenka? kun san me gobe za ta haifar ne?" Da salon son su kwantar mata da hankali Alhaji Sunusi yace; "Zuwan yaron nan zai iya kashe auren Siyaama don hure ma ta kunne zai yi, gara yaje can ya ƙarat.." Bai samun damar ƙarasawa ba saboda masifar da Nenne ta rufe su da shi, da tafiyarta mara sauri ta faɗa ɗakin da Siyaa taje ta fara janyota da iya ƙarfinta tana faɗin. "Fita ku bar mun gida tunda ba uban wani ne ya gina mun ba. Kuma babu gadon uban kowa a ciki marasa kirki kawai." Da murya kuka Siyaa tace. "Nenne ki fahimceni mana. Wallahi Yaaya wari yakeyi sosai, sannan ki ganshi fa ƙafa ɗaya babu wallahi tsoro ma ya bani amma ai ban ce na daina son shi ba kawai dai wani irin wari yake yi da ban taɓa ji ba." Dai na janta Nenne tayi ta tsaya kallon fuskarta da wani irin kallon ashe haka kike? Cikin fushin dayafi na baya Nenne tace; "Ashe baki da imani ban sani ba Safiyyah? fita ki bar min gida kije ki samu mijinki mai ƙamshi da rashin warin baki. Wallahi naa kuma ganin wannan sili-silin ƙafafuwan naki sai na sa anyi miki dukkan tsiya a garin nan." Duk magiya da roƙon Nenne da sukayi bata saurare su ba sai da tabbatar sun bar gidan sannan hankalinta ya kwanta bayan ta kafawa Ziyaada sharaɗin ko ta koma ta nemo Abu Zaid ko taje su warware asirin da suka yi mai idan ba haka ba wallahi ko bayan ranta bata yafe mata ba. Bayan sun bar gidan ajiyar zuciya Mommyn Siyaa ta sauke bata da buƙatar naiman taimakon da Siyaa zata manta da Abu Zaid iyakacin abinda Siyaa ta yi masa yau ya isheta amsar ta daina son shi. Kuma da ta nemosa kamar yadda Nenne ta kafa mata sharaɗi ya dawo cikin su gara ta bada ko million nawa ne a warware asirin da suka yi mai yaje can ya ƙarata. Jirgin Lagos suka bi zuwa gidan Alhaji Sunusi. A ɓangaren Hudayya kuwa. Cikin shanye sakayayyun idanuwata ta take kallon Taufiq haɗe da cije ƙasar leɓenta irin na ƴan duniyan nan. Fuskar Taufiq sam babu wani walwala balle ya nuna zumuɗin ganinta. Cikin hayaniyar zafin da ya taho da shi yace. "Bani hanya Mallama." Gabanta ne ya faɗi zuciyarta na bugawa kamar zai fito. Taufiq bai taɓa yi mata tsawa irin haka ba. Shi mai yake shirin faruwa? Bayanshi ta bi zuwa ɗakin daya shiga tana ƙara zazzago da wuyar rigarta. A tsaye ta sameshi yana zarya a ɗakin da sabon belt ɗin wandonsa a hannunshi. Gabanta na ci gaba da faɗuwa ta tsaya daga bakin ƙofa har lokacin mamakin sauyinsa bai gama sakinta ba. "Mai zai yi da belt kuma?" Ta tambayi kanta kafin da gama saƙa da warwara ya fincikota da zafin namanshi yafaray lafta ma ta belt ɗin da iya ƙarfinka. Tunda uwarta ta haifeta ba'a taɓa yi mata irin wannan dukan da ya yi mata ba. Da ƙarfi Taufiq yake faɗin; "Ni zaki yaudara ki cuceni? wacece ke? nayi miki kama da sakarai da zakiyi wasa da hankalinsa? wallahi yau sai kin yi da kin sanin auren." Sai da yaga bata motsi da kyau sannan ya ƙyaleta ya faɗa washroom yana nurfarfashi. Tana gani ya shiga washroom ta miƙe da ɗan ƙarfin daya rage mata, ta ɗauki wayarta ta bar gidan gaba ɗaya kafin ya rabata da ranta. Gidan Abu Zaid marainin wayonta ta nufa tasan raunin zuciyarsa bazai barsa yaƙi karɓarta ba. Amma sai ta tarar wani ne a ɗakin ba Abu Zaid ba, da taimakon maƙotan shi ta samu gidan dillalin da ya raka

Chapter 9 of 11