Share this page
nasara step by step har Allah ya amsa roƙonshi. Ranar da yayi signing ɗin professional contract yayi kukan abubuwa da yawa da suke ta dawo mai ɗaya bayan ɗaya. Rashin son raɓar mutane da ƙaunar su na ƙara mamaye zuciyarshi da yin girma mai tsananin tasiri a komai na shi. Bayan wani lokaci kaɗan Abu Zaid ya zama ɗan ƙwalisa, ya tara gashi mai yawa har ana iya kitsa masa shi kamar Mace, ya yi wani irin kyau mai birgewa da ɗaukar hankalin duk wata Mace mai son rayuwar hutu da wayewa. Bai cika saka short ba sai dogayen da zasu rufe ƙafarsa indai ba Basketball zai buga ba. Yayi suna kuma yayi kuɗi irin kuɗin da duk kuɗin su na baya bai taɓa ganin irin su ba. Ba iya ado ba hatta kyawun siffa Abu Zaid yafi Leo Zayad da duniyar wasan ƙwallon kwando take ji dashi, sai dai shi ƙafafuwanshi biyu ne, saɓanin Abu Zaid dayake da ƙafa ɗaya. Shahara da sunan Abu Zaid da yake neman take na Leo Zayad ne Allah ya ƙaddara ganawarsu, bayan Leo Zayad ya tabbatar Abu Zaid ya taki matsayin da ganawar su wani abin alfahari ne a wajen sa. Abu Zaid yaji haɗuwarsa da Leo Zayad kamar a mafarki saboda abu ne da bai taɓa kawowa zai tabbata ba a rayuwarsa. Ranar daya shirya tarbar Leo Zayad, cikin ƙananun ƙayan da suka haɗiyi manyan kuɗade ya shirya. A lokacin Zainab da Iyalanta suka samu alfarmar isowa ƙarsar da yake, har ƙofar tangamemen gidansa aka kai su. A ɓagaren su Zainab, baki, hanci da ido suka saki ita da ƴaƴanta suna kallon ƙaton gidan da aka ba su tabbacin na Abu Zaid ne. Cikin sa'ar da suka taka bayan sun koro jawabin da ya ɗaukesu wajen minti arba'in, masu tsaron gidan suka ba su damar zama a harabar gidan. Baƙaƙen ƙosassun matoci ne suka fara fitowa don zuwa gidan hutawarsa saboda Leo Zayad da iyalansa na daf da isowa. Abu Zaid kamar ance ya ɗago idanuwasa, katari ya yi da fuskar da take matuƙar yi masa kama dana Zainab duk da duhun gilashin motar da yake ciki. Fuskar Zainab fuska ce mai daraja a rayuwarsa irin darajar da bai san ta yaya zai misaltashi ba. Tsaayuwar motocin ne yasa Zainab ƙara gyara zaman mayafin Abayar dake nannaɗe akan kwantacciyar sumar kanta. A hankali ya sauko daga Mota ya na takowa inda suke turarren jan rigar jikinsa daya taimaka wajen fitar da aihinin kyawunsa na haske mu su ido, jelar kitson kansa na reto a gefe da gefen farar fatar wuyarsa. Idanuwanshi ya ƙara lumshewa hakan yasa girman su raguwa. Memoryn abubuwan da suka wuce na dawo mai. Yana ƙara motsowa ganinsa naƙara gasgata mishi Zainab ce da ta rage mai bayan labarin rasuwar Aunty da na Mahaifinshi daya samu. Su Zainab miƙewa suka yi dukkan su, tsayayyen dogon namijin da dogon wandon jikinsa ya ɓoye waccen ƙafar ƙarfen da ta gani ne yake tunkaro su, idan ta cire tsaho ba shi da wani haɗin siffar halitta da Yayanta. Fuskarshi sakaye da baƙin nose mask. Cikakkiyar girarsa take kallo har ya matso kusa da su. Tsadadden ƙamshin shi na ƙara narkar da zuƙatansu, ko kamanni sun ɓace idan jininka ya matso kusa dakai dole kaji wani alama. An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 11 of 11