Share this page
Taufiq waccen gidan. Nan ma sun sanar da ita har lokacin Abu Zaid bai dawo ba, kuka ta fashe da shi tana tunanin mafita. Shawarar tafiya Gwarzo ta yanke sai dai kafin tayi yunƙurin miƙewa wayar hannunta ta fara ringing. Babban ɗan Baba Ilu ne, da ta ɗaga batayi magana ba saboda jikinta yana bata ba lafiya ba, zagi masu lanƙwasa yake zubo mata kamar bamaguje da warning ɗin ta sa mugun mijinta ya sakar mu su Iyaye idan ba haka ba wallahi sai ya biyota har birni ya nakasata. Katse kiran tayi ta kashe wayar gaba ɗaya. Jikinta har rawa yakeyi ta ƙara komawa cikin gidan tana roƙon su suyi mata kwatancen Companyn da Abu Zaid yake zuwa. Labarin da Taufiq ya samu itama shi ta samu sai dai ita ta samu ƙarin hasken ai Company ya canza. Kamar mahaukaciya haka ta nufi Companyn da aka kwatanta mata. Sai yamma liƙis ta samu ganin Mallam Sa'adu Driver iyakacin labarin abinda ya sani ya gaya mata ciki har da labarin barin Ibrahim Kano amma bai san ina sukaje ba. Numbersa ta karɓa da sunan idan ya dawo a sanar mata ita ƙanwarshi ce Uwa ɗaya Uba ɗaya. Satin ta biyu tana nemansa saboda labarin da sukaji cewar yana Kano, ba don Mallam Sa'adu ya yarda da dukka maganganunta ba ya bata numbernsa. A bakin titi ta tsaya tana saƙe-saƙe kala-kala batasan kowa ba sai Taufiq da Abu Zaid. Hango motar Taufiq ya sa ta barin titin, da sauri ta nemi jikin wata bishiya ta ɓuya ƙirjinta na bugawa. A ɓangaren Abu Zaid Mr John bai samu matsalar ganawa da Mr Toyosi wanda ya bawa Abu Zaid horo ba, kuma ya samu gamsashen bayanin dayake so akan Abu Zaid ɗin. Address ɗin ƙasar da Mr Toyosi yake ya basu. Jirgin da Abu Zaid ya cire yaƙinin zai ƙara shiga ne ya kai su Washington babu ƙauyanci ko rashin sabo a tattare da shi kamar yanda Mr John yayi tunanin gani. Hakan sai ya ƙara masa ƙarfin gwiwar tunkarar komai da zafinsa saboda alamun nasarar dayake hangowa tattare da Abu Zaid ɗin. Da farko wajen ƙwararrun Opthalmologist (likitocin ido) Mr John ya kai Abu Zaid su ka yi mishi gyara idon da zai gani da kyau ba tare da amfani da gilashi ba. Sannan likitoci suka ɗorashi kan abincin da zai bayar da yanda suke so jikinsa ya koma haɗe da kalolin motsa jikin da zu taimaka wajen bayarda abinda ake so. Ƙafar da idan yasa zai tsaya kamar kowa aka ƙeramai yana koyon tafiya da ita kullum. Mr John da Mr Toyosi da yake tare dasu a lokacin ne su ke ƙarawa Abu Zaid ƙarfin gwiwar ya sawa zuciyarsa cewar shi ba nakashashen da zai ci ko roƙo koyin bara a ƙarƙashin wa su bane, kuma nasararsa zai tabbata ne idan ya jajirce ya cirewa zuciyarsa rauni da manta abubuwan da suka faru a baya. Ko ba su faɗa ba waccan Abu Zaid ɗin da ban wannan ma daban. Duk wani nasara na tare da ƙalubale masu zafi da tsanani ire-iren, su Abu Zaid yayi ta fuskanta ta ɓangaren ƙungiyoyin da za su ɗaukesa, daƙyar da taimakon Allah da na Mr John da Mr Toyosi Abu Zaid yasamu dama. Saura kwana ɗayan daya rage ya je buga wasan da Mr Clinton ya amince da bashi damar da zai yi da ma su ƙafafu duka biyu amma one legged za su yi. Abu Zaid yakasa barci sai sallah da ya yi tayi da karatun Al Qur'ani. Ta ɓangaren horo bashi da matsala saboda yaƙara samun horo mai zafin gasken da ya sashi ƙara ƙwarewa akan ƙwarewarsa na baya. Wajen 11:00 na dare Mr John ya shigo ɗakin da yake. A kan abin sallah ya sameshi fararen idanuwanshi sunyi jajir jijiyoyin goshinsa sunfi fito sun yi ruɗu-ruɗu, alamun yasha kuka ba kaɗan ba. Da muryar ƙarfin gwiwar da Mr John yakeji a kan shi yace. "Leo's suna da ƙwarin guiwa na halitta. Inaso kazama haka Ibrahim Inaso naji alfaharin saninka a rayuwata, iyayenka ba su haifeka don kayi rayuwar ƙasƙanci ba Ibrahim inajin wannan a jikina kuma idan Allah ya yarda nasara a jininka yake." Kai Abu Zaid ya ɗago yana kallon cikin ido Mr John da ƙwalla ke kwance a ciki saboda tsoro da fargaban zuwan gobe. Har Mr John ya bar ɗakin Abu Zaid yakasa furta komai. ★ Washe gari sumar ya dake tarawa ya gyara ya ɗauko ƙafarshi ya maƙala da bismillah sannan yafara zura sabon kayansa da addu'ar sanya sutura a bakin shi. LEO AZ ne manne abayan rigar. Mr John yasan akwai wani leo Zayad daya taɓaji shi yasa ya babban ta nashi da AZ agaban na Abu Zaid. A mabanbanta duniya Abu Zaid da Zayad su ke rayuwa amma waccan Zayad ɗin duniya tasan da zamansa, yana fatan Abu Zaid daya raina yanzu da hannunsa ya kere waccen Leo Zayad ɗin ba ya kamo shi kaɗai ba. Ba ƙaramin kyau baƙaƙen kayan suka yiwa Abu Zaid ba. Zuciyarsa ce take wani irin bugu mai ƙarfi lokacin daya bayyana a filin wasa da abokan bugawarsa su ke. Tausayi da ƙwalla ne ya tararwa idanuwan Mr John lokacin da Abu Zaid ya bayyana jikinsa har karkarwa yakeyi saboda fargabar kar damar da suka samu ta kuɓuce musu wanda hakan na nufin lalacewar komai. Abokanan wasan Abu Zaid dogaye ne sosai wa sun su kuma ma su matsakaitan tsaho, Abu Zaid yana daga cikin dogayen su sai dai akwai waɗanda suka kere mai irin masu tsayin su Leo. Zayad shima ba dai irin sosai ɗinnan su ka fisa ba. Zuciyarsa ce ta cigaba da buguwa tsoro na neman yin tasiri a gangar jikinsa da zuciyarsa har suka fara buga wasan. Da farko sam babu zafin naman a wasan Abu Zaid sai dai tuna kalaman Taufiq da yake cewa; "Kai bazaka tashi kayi gwagwarmaya ka naimi naka ba dole sai ka ci a ƙarƙashin wani?" Da kuma kalaman Mommyn Siyaa da take cewa; _"Ibrahim zuwa yanzu ya kamata ka nemi gobenka don ƴata tafi ƙarfinka kai da annamimin Ubanka. Kasan wa take aure? Hamshaƙi mai arziƙin da baya zalama da sanya ido akan na wasu. Ka riƙe maganganuna ko Allah zai taimakeka ka zabura ka nemi gobenka domin na lura ƙwaƙwalwarka da ta Ubanka ta jima da toshewa, karka ƙara neman Siya domin tafi ƙarfinka, mai zatayi da kai Gurgu mai warin baki."_ Da zafin nama daya manta ƙafarsa ɗaya na ƙarfe ne ya fara buga wasan daya bawa ko wa mamaki. Toshe bakin da Siyaa tayi ya tuna da aman da tayi a gabansa, bakin cikin yasa shi yin wani irin tsalle ya yi ya buga ƙwallon da babu shamaki ya shige cikin raga zururuf. Tuna kalaman Mr John da yai cewa. "Da zuciyarka zaka buga kuma zakai yi nasara." Hakkan yasa ya ƙara jefewa a karo na biyu. Ƙara tuna kalaman Mr Toyosi na kar yasawa zuciyarsa shi nakashashene da zai ci a ƙarƙashin wani, ya sawa zuciyarsa shi cewa lafiyayye ne shi da zai yi gwagwarmaya har wasu su yi rayuwa a ƙarƙashinsa. Amma ba wannan Abu Zaid ɗin na baya ba Gurgu mai raunanniyar zuciya. Nan da nan zafin namansa ya ƙaru, zuciyarsa na ƙara ɗaukar zafi kalaman ɓatanci da girman butulci da mabanbanta mutane sukayi tayi masa da gorika kala-kala ne yaƙara rura wutar samun nasara a cikin zuciyarsa da ƙaimin cimma muradansa. "Muna da damar cimma muradan mu a lokacin da muka shirya, tsufa nakasa ko rashin ilimi mai zurfi ko wani dalili na daban kar mu bari suyi mana shamaki da cikar muradanmu. Mu dage kuma muyi gwagwarmaya wata rana burikan mu zasu zama gaskiya." kalaman da zuciyar Abu Zaid take ta nanata mai kenan har Allah ya bashi nasara.....✍🏻 [11/8, 10:32 PM] Hajja Ce: ABU ZAID BY NAFISAT ALIYU SASAAL 18 A ɓangaren su Siya kuwa. Bayan barin su Tofa kwanan su biyu a Lagos suka koma Coventry. Zaman sulhu mahaifinsu Muhammad da shi kanshi Muhammad da Siyaa da Mommynta sukayi. Cikin yauƙi da son lallai sai auren Siyaa da Muhammad ya tabbata Mommynta ta fara yunƙurin hana Siyaa furta komai. Mahaifinsu Muhammad ya dakatar da ita tare da bawa Siyaa kwana biyu taje tayi tunani a kai dan ba za'a yi mata dole ba. Bayan sun dawo gida ba ta bari Mommynta ta samu damar yi mata faɗa ba ta shige bedroom ɗinta ta kulle kanta a ciki. Kwanan tunanin Siyaa ta yi a ranar dan bata samu ta runtsa ba. Tana son Abu Zaid tasan kuma nemo shi abu ne mai sauƙi a wajenta tunda Nenne tasan sunan Companyn da mutumin daya kawoshi Tofa yake aiki. Amma tayaya zata iya rayuwa da shi haka jikinshi duk datti kuma tasan har yanzu yana shan sigari? Ita kam duk ba ma wannan ba tayaya zata iya yin rayuwa da miji mai ƙafa ɗaya bayan ba shi da kuɗi? da me zai dinga ciyar da ita? kuma tasan babu wanda zai taimaka musu da ko naira ɗaya dan su amfna. Ita gaba ɗaya ta saba da rayuwar hutu, jin daɗi da tsananin tsafta, dan haka gaskiya bazata tura kanta cikin rayuwar wahala ba. Muhammad mijinta ɗan gayu ne kuma kyakkyawan da milliyoyin naira ke bayyane a komai na shi, kuma yana sonta sosai haka mahaifinsa yana bata kulawa, ita kam gaskiya bazata iya komawa Abu Zaid ba, za dai ta tura kuɗi Nenne ta sa a nemo wannan Drivern ya kai mai. A wannan dare Siya ta fara saƙa yadda zata kulle dukkan shafin soyayyarta da Abu Zaid a cikin zuciyarta. ★ Da sassafe Mummynta da ta kasa barci ta fara ƙwanƙwasa mata ƙofar ɗakinta. Bayan ta buɗe ƙofar cikin lallami da burin cikar muradi Mommyn ta ce. "Siyaa bana son wani shirmen tunani ya zo kanki kina jina? Mahaifin Abu Zaid baya sonki saɓanin mahaifin Muhammad. Sannan Abu Zaid ba zai iya ɗaukar nauyin ko da abincin safen ki ba balle a zo kan abubuwan buƙatun ki na rayuwar yau da kullum. Kiyi tunani kinji? na tura kuɗi ma su yawa a warware waccen sihirin ya samu lafiya yaje ya gina rayuwarsa, amma banason ki ƙara damun kanki akan shi, kowa ya yi rayuwarsa." Ta ƙarasa faɗa da salon yaudara a cikin muryarta. Da ire-iren waɗannan huɗubobin Siyaa ta shafe shafin ɗan uwanta kuma tsohon mijinta a cikin rayuwarta. Dama mutuwar Daddyn Abu Zaid bai wani dameta ba don tuni mahaifiyarta ta jima da ya kice duk wani shaƙuwa da tunanin su a ranta ta hanyar kushe su da aibata su kullum. ****** A ɓangaren Hudayya kam. Tafi minti talatin manne a jikin bishiya har aka fara kiran sallar Magriba sannan ta fito bakin titi, ƙirjinta na bugawa tana addu'ar Allah yasa kar Taufiq ya kuma biyowa hanyar. Ta saƙa ta kwance bata samu mafitar da ya wuce zuwa wajen Maryam abokiyar karatunta ba. Taxi ta tara a tsorace tana waige-waigen kar Allah yasa wanda yasan Taufiq ya ganta. Kwatancen da Maryam ta taɓa yi mata ta bi har taje. Gida ne mai kyau da ya dace da kalar unguwar. Kamar ɓarauniya haka ta fito saboda kuɗin da babu a jikinta, da sanyi murya kamar mutuniyar kirki ta ce da mai taxi ɗin. "Mallam dan Allah bari na shiga na karɓo maka kuɗin ka." Tsoho ne kuma mara hayaniya kai kawai ya ɗaga mata alamun yana jiranta. Numbern dake manne a haɗaɗɗen gidan take kallo da sunan unguwar "Dama haka gidan Maryam yake?" Ta faɗa a ranta lokacin da take ƙwanƙwasa gate ɗin gidan. Buzun maigadin su ne ya buɗe mata, cikin kame-kame ta gaishe shi kafin ta sanar da shi Maryam take nema. Kallon anya tana da kusanci da Maryam yake yi mata don Maryam ta jima da komawa Lagos ita da Mijinta. Da Hausarsa da bata fita dakyau ya ce da ita. "Ayya ai tuni Hajiya su ka koma legas sai dai ki kira wayarta." Ya faɗa yana ƙarewa Hudayya dake firgice kallo. Hannunta na rawa ta fara neman layin Maryam,a kira na wajen huɗu ta ɗaga. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauke lokacin da Maryam ta amsa sallamarta. Da muryar tausayin da take yaudarar mutane da shi tace. "Madam ina ƙofar gidanki kuma gateman yace bakya nan." Cikin tsokana Maryam ta ce. "Ai na jima da komawa Lagos Hudayya, ina fatan komai lafiya ƙawata masoyiyar Ibrahim." Kai ta girgiza kamar Maryam na ganinta, sannan ta ce. "Labarin mai tsaho ne please ki sa Maigadi ya bani ɗari biyar zan biya mai taxi." Da jimami Maryam tace ta ba wa gateman waya. A tunanin Hudayya Maryam zata yarda a buɗe mata gidan ta zauna na wani ɗan lokaci, amma sai ta ga akasin haka don ƙememe maigadi ya hanata shiga, ya dai bata dubu ɗaya tayi kuɗin mota kamar yadda Maryam ta kirasa tace ta bashi. Babu kunya Hudayya da ta ƙara kiran Maryam ta gaya mata bukatar ta na samun gurin zama zuwa wani lokacin. Maryam ta shaida mata mijinta ne bai amince ba amma zata bata address ɗin gidan masu aikinta taje can ta kwana. Ba ta da zaɓi haka ta ƙara hawa Taxi zuwa Unguwar da Maryam tayi mata kwatance. Ba laifi gida ne mai kyau dai-dai misali, kuma ta samu tarbar mutunci albarkacin kirkin Maryam da ta ci. A daƙin Firdausi babbar ƴa a gidan aka sauke Hudayya.. _(Ƙarshen littafi na ɗaya kenan, mu haɗu a littafi na gaba. Abinda taga an rubuta a karshen Page ɗin kenan.) Uhmmm masu karatu mun dawo farkon labari yanzu._ SAFEERA Littafin Safeera ta jingine a gefe, idanuwata sunyi jajir kamar an watsa mata yaji saboda kukan da tasha. Kamar zararriya haka ta koma inda ta siyo littafin ba tare da ta daina kukan ba, sai dai duk iya binciken ta babu na biyun littafin. Jiki a sanyaye ta dawo gida, lokaci zuwa lokaci tana share ƙwallar da take ta zubo mata. A zabure ta miƙe saboda tunawa da numbern wayar dake ƙarshen littafin. Hannunta yana rawa ta kwafe number a wayarta, Sai tayi kira na wajen 10 sannan aka ɗaga. Ba tare da Safeera tajira ta yi magana ba tace. "Sunana Safeera Yazeed, dan Allah Hudayya nake nema." Da sanyin muryar da ya haɗe da tsoro wacce ta ɗaga wayar tace. "Ban san me kike nufi ba." Da sigar lallashi Safeera ta ce; "Dan Allah ki taimaka min idan kinsan Marubuciyar da ta rubuta labarin da na karanta saboda na biyunsa nake ma dan Allah." A ɗayan ɓangaren shiru a kayi kafin wacce ta ɗaga wayar ta numfasa sannan ta ce; "Babu littafi na biyu saboda wasu dalilai da ya sa aka dakatar da shi, kiyi haƙuri Hajiya." Safeera kuka ta sanya tana magiyar dan Allah dan Annabi ta ƙarasa mata labarin abinda ya faru ta waya, ko ta kwantanta mata zata zo har gida ta bata labarin. Haƙuri dai aka ƙara bawa Safeera tare da shaida mata fitar labarin na iya ƙara jefa asalin wacce ta rubuta labarin cikin matsala. Magiya Safeera ta cigaba da yi mata da roko sosai amma bata bata dama ba. da dai taga bazata amince mata ba sai ta bata labarin wahalar da mahaifiyarta take sha, wannan dalilin yasa ta keson taji ƙarashen labarin, idan da gaske Abu Zaid ɗin da Mahaifiyarta take nema ne. Ajiyar zuciya wacce take kan layi da Safeera ta sauke, kafin tace Safeera ta bata ƴan mintina tana zuwa. "Toh." Safeera ta amsa mata da shi, sannan ta zauna tana jiran kiran nata, bata damu da wacce ta ɗaga wayarta ba ita dai burinta ta samu jin ƙarshen labarin. Kati ta siya ta banki mai yawa tana jiran aƙara kiranta. Sai da akwashi rabin sa'a sannan aka ƙara kiranta. Katsewa tayi ta kira tana gyara zaman ta. Gyara murya akayi a ɗaya ɓangaren sannan aka ɗora mata da; _"BAYAN ƳAN GIDANSU FIRDAUSI SUN TARBI HUDAYYA SUN BATA MASAUƘI;"_ Da dare ya yi cizon sauro ne ya hanata bacci saboda rashin wutar nepa balle ta samu shan fanka da ma kuma ba su da AC irin na gidan Taufiq. Sai tsaki take yi ta na juye-juye. Har lokacin Firdausi tana zaune ta na rubutu sai cikin dare sosai barci ya ɗauketa. ★ Washe gari bayan sunyi sallar asubahi, Firdausi ta cigaba da rubutun ta, Hudayya kuma kasa jurewa tayi ta matso kusa da ita tana ce wa. "Me kike rubutawa haka tun jiya baki yi bacci ba Firdausi?" Cikin murmushi da alkunyar tarbiyyar da Firdausi take dashi tace. "Ina rubuta labari ne na siyar a buga a takarda." Ido Hudayya ta zaro mafita kala-kala na zuwa ranta lokaci ɗaya. Cikin kame yanayin zumuɗin da ta tsinci kanta a ciki tace "Ina son nima ki koya min na rubutu labarina, kina ganin zan samu kuɗi sosai? kuma yaushe zaki fara koya min." Ɗan jim Firdausi ta yi kamar mai tunani, Hudayya na ganin haka tace. "Firdausi karki damu duk kuɗin da na samu tare zamu raba kinji?" Cikin tsoro da rashin sabon da ke tsakanin su Firdausi tace; "Ki bari nayi shawara da Inna ta." Ɓata fuska Hudayya ta yi alamun bataji daɗi ba tana kwanciya kan abin sallar da take kai. Kallo Firdausi da suke kusan sa'a ɗaya ta bi ta da dashi tanajin kamar bata kyauta mata ba, a hankali ta ce. "Shikenan naji zan koya miki." Da sauri Hudayya ta miƙe tana murmushi, kamo hannunta tayi sannan tace "Nagode Firdausi amma zaki taimaka min zuwa Tofa gin bincike. Nayi miki alƙawarin tare zamu raba duk kuɗin da zan samu kinji?" Shiru Firdausi tayi cikin tunani sai dai tuna zasu raba kuɗi kai ɗaya da ita ya sa ta amince. ★ Da gari yayi haske sosai, Hudayya ta ƙara kiran Maryam da salon yaudararren magiyarta ta ci galaba akan Maryam har ta amincewa zuwanta Lagos amma sai bayan sati saboda muhimmiyar maganar da ta ce za su tattauna. Da zumuɗi Hudayya ta fara shirin tafiya Lagos bayan ta samu nasarar kwashe dukka kuɗaɗenta dake cikin Account. Wajen mai ƙarbar labaran Firdausi ya siya ya buga suka je, da taimakonshi ba tare da sanin Inna Rahima ba sukaje Tofa. Hudayya na bakin tasha tana jiransu. Da dabara suka samu jin ainihin bayanin auren Siyaa da zuwan Abu Zaid da korar su da Nenne ta yi, da yadda duk wasu abubuwa suka faru da Siya a Coventry. Ta bakin Nenne. Tsufa da yarda na wancan lokacin yasa ta yarda da gaske su ƴan uwan Ɗalhatu Mahaifin Abu Zaid ne su, sun nema shi a ko ina amma basu gansa ba, shine suke so suyi rubutu akan tarihinsa da na Siya ko Allah zaisa ya gani ya dawo gida. Shima Mallam Sa'adu da abinda suka yaudari Nenne suka yaudaresa har ya ba su bayanin inda Abu Zaid ya tafi. Hamisu mai bugawa Firdausi littafi shi yayi musu kuɗin Mota har ƙauyen Abuja gidan Mama Ramatu, itama suka yi mata dabara suka samu jin wasu bayanan daga bakinta, ita ta kwatanta musu gidan Zainab. Zainab da damuwa ta yiwa yawa ita taƙara musu da bayanai masu yawa irin wanda suke buƙata, bayan sun yaudareta da su ƴan uwan mahaifiyar Abu Zaid ne. Bayan sun dawo Kano Hamisu ne ya binciko shafukan sada zumuntar Mr John kuma yasamu bayanai da yawa akan Abu Zaid da bayanin da Mr John yayiwa ƴan jarida da kuma burin abinda yakeso Abu Zaid ya zama. Kafin a kammala rubuta labarin Hudayya ta tafi Lagos gidan Maryam. An kammala rubuta labarin Hudayya amma ba'a buga ba. Har zuwa wata ɗaya Hudayya bata ƙara neman kowa ba, dalilin haka yasa kawai Firdausi ta cewa Hamisu ya buga saboda tanasa ran littafin zai kawo kuɗi, ba musu Hamisu ya amince. An buga littafin an shigar da shi kasuwa da sunan Hudayya ce ta rubuta, kuma ya samu karɓuwa sosai, ana jiran Hudayya ta dawo ta bayar da ragowar labari a ɗora, kwatsam sai ga jami'an tsaro har gida sun cafke Firdausi. Kwanan Firdausi uku sannan tasan Hudayya ce tasa aka mata, wai ta buga littafi da sunanta zata ɓata mata Suna. Da ƙyar da suɗin goshi da taimakon Hamisu aka bayar da belin Firdausi, wannan shine abinda ya faru. "A ɓangaren TAUFIQ, SIYAA, DA ABU ZAID DA ITA KANTA HUDAYYA DUK BA MU SAN WANI RAYUWA sukeyi yanzu ba, amma ki bibiyi shafukan sada zumunta na tabbata zaki samu ABU ZAID don a yanzu fitaccen Mutum ne." Godiya Safeera ta fara kwararo mata, sai dai tana cewa; "Dan Allah da wa nake magana Firdausi ce ko ƴar uwarta?" Kit aka katse kiran tare da kashe layin gaba ɗaya. Ido Safeera tabi wayarta da shi, kafin ta miƙe ta shiga washroom. Bayan Safeera ta fito daga washroom shafukan da tasan ake posting ɗin abinda ya danganci wasan ƙwallon kwando tayi ta bi ta na dubawa, amma har tsakiyar dare ta kasa samo shafin Abu Zaid, tasa Leo Az bata samu ba, tasa Abu Zaid bata samu, daga ƙarshe tasa Ibrahim shima duk bata samu ba. Barcin gajiya ne ya ɗauke ta hakan yasa bata ci gaba da bibiya ba. ★ Washe gari bayan tayi sallar Asuba ta roƙi Allah ya sauƙaƙa mata ta samo shafin Abu Zaid. Instagram ta ƙara hawa ta cigaba da bibiyan Videon da suke ɗorawa. Kyan matashin da zanen kitson kansa ne ya birgeta, don haka ta ɗan shagala da kallonsa. Kan sunan AZ da akayi tagging ta shiga. Vidiyoyinsa ne suka bayyana ƙalilan, sai ƴan hotunan da yawanci an ɗaukesa ne bai sani ba. Videon farko ta shiga. Daga bayaninsa da na baturen da ake nunawa, da wasu hotunansu acikin videon na yarda sukayi gwagwarmaya kafin ya samu babban contract ta fahimci Abu Zaid ɗin da ta nema ne. Ihu ta kurma kafin tayi sujada take a gurin. Ɗakin Mahaifiyarta ta nufa a guje tana ƙwala mata kira; "Mommy! Mommy!!" Zainab da duk ta rame ta ɗago kanta a hankali tana amsawa da. "Na'am Safeera wannan ihun na menene?" Safeera tana shigowa ta kai mata wayar saitin fuskarta, da zamuɗi tace; "Mommy Uncle Ibrahim ne kingansa wallahi shine." Kai Zainab ta girgiza don babu inda wannan ƙosasshen namijin ya haɗa hanya da ɗan siririn ƙaninta kuma shiru-shirun da ko magana bai damesa, ba. Sannan wanda Safeera take nuna mata ƙafa ɗaya ne da shi. Nata Ibrahim ɗin kuma tasan da kafafunsa. Safeera da ta fuskanci mahaifiyarta ba ta gamsu ba da sauri ta ƙara nemo wani Videon, tayi sa'ar samun wanda fuskarshi ke kusa sosai, ya na zaune a kan kujera ya na kallon wayarsa da kitso guda shida zane a kan kwantacciyar sumar kansa da matsowar videon kusa ya ba su damar gani da kyau, saɓanin na ragowar hotunan da aka yi masa daga nesa. Lumsassun idanuwansa masu wani irin kyau ya ɗago yana kallon wani wajen, ƙara lumshe su yayi alamun kamar agajiye yake ya ɗan shafa gefen fuskarsa a hankali. Ihu Safeera tasa har da tsalle tana cewa. "Subhanallahi Mommy dan Allah kalli kyau ki gani, gaskiya babu maganar jira Mommy ki shirya dole zamu tafi nemosa a duk inda yake." Zainab nishaɗin da taga Safeera a ciki ne yasa ta ɗan samu dariya duk da bata tabbatar da Abu Zaid ɗin su bane wannan, saboda babu wani abu na su ɗaya da yake iri ɗaya da wanda ta sani. Dan Abu Zaid Yayanta baya gani da kyau, sannan shi yana da ƙafa dukka biyun, kuma matsoraci ne hatta idanuwansu ba iri ɗaya ba ne idanuwan Abu Zaid jajayene ma su tsananin rauni, duk da tasan yana da kyau amma bai kai wannan ba. Karfa Safeera ta ƙara mu su damuwa akan wanda suke ciki, idan har dagaske Abu Zaid ne tayaya ya zama haka? Bata ce komai ba, sai dai ta nuna jin daɗin ta saboda hankalin Safeera ya kwanta. Bayan kwana biyu Safeera da Zainab suka gama cuku-cukun samun ƙasar da yake ta hanyar wani abokin kasuwanci Zainab. Tsaf suka shirya dukkansu, wajan misalin ƙarfe 9 na safe suka bar ƙasar. A ɓangaren Abu Zaid kuwa. Wasan da Mr Clinton ya basa dama ya buga ya bar baya da ƙura, wasu cewa ma suke yi anya mutum ne shi? saboda ƙwarewar da ya nuna a wajan, sai ya zamana a duniyar buga wasan ƙwallon kwando zancesa kawai ake y, babu inda Video clip ɗin sa bai zaga ba, ya buga wasa da yaƙinin nasara a wajen Allah kuma Allah ya ba shi nasara sama da yanda yayi hasashe. Da ga wannan lokacin kuma Abu Zaid ya fara taka matakin

Chapter 10 of 11