Share this page
kanki baza...." Rugumar da tayi mishi ta baya ne yasa yakasa ƙarasa maganar da ya ɗakko. Cikin kuka take cewa, "Yaaya karka rabu dani dan Allah kaji?" Fizge jikinshi yayi yabar ɗakin da sauri. Zubewa tayi kan gwiwoyinta tare da yin addu'ar da duk yazo cikin bakinta. Abu Zaid kuwa yasha cigarette ɗin da bai san iya adadin da ya sha ba, kafin baccin azaba ya ɗaukeshi. Sai midnight ya farka, abinda ya fara zuwa ranshi shine Siyaar shi tana ina? Tashi ya ya fito, bai tsaya yin knocking ba ya buɗe da key ɗin wajenshi. Tana kan Prayer Mat idanuwanta duk sun koɗe saboda kuka. Da sauri ya tsugunna a kusa da ita yana kamo fuskarta, bakinta yake kallo kafin a hankali ya ɗora nashi akan natan, duk da warin Cigarette ɗin da yake yi bata tureshi ba. Sai ta ya tabbatar duk wata gaɓa ta jikinta ta narke sannan ya zare bakin nashi daga cikin mata yana maida numfashi. A ɗakin ya kwana suna ƙanƙanme da juna kamar za'a raba su. Ringing ɗin wayarta ne ya tashe shi daga baccin da suke yi. A hankali ya shimfiɗe ta saman gadon ya miƙe tsaye dan ɗaukar wayar. Sunan Aunty daya gani ne yasa shi response. Kalmar Innalillahi da yake ta maimaitawa ne ya tashi Siyaa daga bacci. Sauke wayar yai yana jin jikinsa yana rawa. Kallansa takeyi tana neman ƙarin bayani taji yace. "Mijin Zainab ne Yazeed Allah yayi masa rasuwa." Siyaa ta sakko a gigice itama ta shiga furta Innalillahi Wainna ilaihir raji'un ɗin. A gurguje Siyaa take shiryawa saboda su Aunty dake jiranta. Da sallama Hudayya ta shigo take sanar da Siyaa ɗin cewa Aunty tace tayi sauri. Bunch ɗin keys dake hannun Couch Hudayya ta faki idon Siyaa ta ɗauka ta zura a hijjab sannan tabar living room ɗin daya ƙara rura wutar kishin daya dabaibaye zuciyarta. Sai da Siyaa ta zo kulle ƙofa kawai ta nemi keys ɗin tarasa ga shi Abu Zaid ya fita zuwa parking lot tuntuni. A waje ta same su dukka har Hudayya dake rakuɓe a gefe don bada ita zasu tafi ba. Wajan da yake tsaye Siyaa ta ƙarasa. Kafin tayi mai magana ya kama fuskarta yana gyara mata zaman hijjab ɗin da bai zaunawa fuskarta da kyau ba. Kamar mai raɗa ta gaya mishi ya kulle ma ta ɗaki bataga keys ɗinta ba. Gaba ɗaya hankalin Hudayya na kansu saɓanin su Aunty dake ta ƙoƙarin shiga mota. Daga mota har jirgi Siyaa na kwance a jikin Abu Zaid saboda fever dake damunta. Har suka kai Ghana asalin mahaifar Yazeed hannun su na cikin na juna. Shi dai Daddy burinshi ace wannan zazzaɓin da Siyaa takeyi na ciki ne. A haka suka samu Zainab da yaranta uku Safeera ƴar shekara Shida da rabi sai ƙannenta ƴan biyu maza da bata daɗe da haihuwarsu ba. Tunda suka je garin Zainab na lura da yawan kukan Siyaa musamman idan suna waya da Abu Zaid ko kuma idan ya shigo duba ta, gaba ɗaya duk ta rame yawan fara'arta duk ya ɗauke. Sai da tabari Abu Zaid ɗin ya shigo ta titsiyesu da tambayoyi har Abu Zaid Ya gaya mata asalin matsalarsu da kuma hukuncin da ya yanke. "Wannan ba mafita bace Yaaya, akwai likitan ɗaya yi min dashen cikinsu Al-hussain a Poland zan haɗaku da shi kuje ya duba ku dan ya duba yaga menene ainihin matsalar." Da farin ciki Siyaa ta rungume Aunty Zainab, sai take ganin kamar Abu Zaid ya riga ma ya warke. Ashe ƴar uwar Yazeed na laɓe tana jin su. Kwana biyu bayannan Abu Zaid da Siyaa suka bar Ghana da addu'ar fatan dacewa. Daga Daddy har Aunty babu wanda ya kawo ga ainihin matsalar Abu Zaid tunda basu ji labarin ba. Kai tsaya Poland suka wuce, Doctors suka shiga gudanar da aikin su cike da hikima da ubangiji Allah ya basu. Babu wata matsala a jijiyoyin al'aurar Abu Zaid komai na shi lafiya ƙalau amma al'aurarshi bata tashi balle ya iya saduwa da iyalinshi. Duk iya bincike su basu ga matsalar komai ba. Da suka koma masauki Abu Zaid yayi kuka irin wanda bai taɓa yi ba, ya kuma sha cigarette kamar zai kashe kanshi. Da Siyaa ta matso domin hanashi mari mai zafin gaske ya sauke mata cikin rashin sanin ina hankalinsa yake, yake ta ke kallansa ne tana buɗe idanu jikinta yana rawa yasa shi saurin yi mata wata irin wawuyar rungumar daya kusa ɓallata saboda matse tan dayayi yana surutai. Yadda ya yi mata ne yasa ta sassauta jin zafin da zuciyarta tayi na marin da yai mata. A wannan rana basuyi bacci ba. Kafin gari ya waye ya fita daga hayyacinsa gaba ɗaya. Tashin hankalin Abu Zaid ɗin shine rabuwa da Siyaa, tunda yasan ita ɗin macece ita mai ƙarfin sha'awa idan ya biyewa soyayyar su zai kashe mata rayuwa ne kawai ba tare da ya samu hanyar da shi ɗin zai iya faranta mata ba. A daren da aka kwantar da Abu Zaid saboda gabaki ɗaya ya rikice ciwo sosai ya kamashi. Cikin wannan yanayin ta samu kiran Mommynta wato (mahaifiyarta) akan tazo da gaggawa tana nemanta. Uzurin sai Abu Zaid yaji sauƙi ta bata, ba dan taso ba ta haƙura. Kwanan su biyu aka sallamoshi saboda ya ɗan dawo hayyacinsa duk da cewa ba duka ba. Nan fa kowanne su ya shiga haɗa kayanshi tsaf, shi zai dawo Nigeria ita kuma zata wuce Coventry. Hannunta ya ɗamka yana kuka komai na jikinshi na rawa ɗakyar yayi jarumtar furta mata. "Siyaa dan Allah ki dawo da wuri kinji? karki daɗe ina nan ina jiranki dan Allah." Ya faɗa still yana kukan dake karairaya mata zuciya don ya jima da sanin ƙiyayyar da Mommynta take yi mishi. Toshe bakinta tayi saboda wani irin kuka daya taho mata. Sai da tayi jarumtar haɗiye shi sannan ta furta. "Da wuri zan dawo Yaaya dan Allah ka dinga cin abinci kaji? kuma kayi min alƙawarin bazaka sha cigarette ba har na dawo kaji?" Ta faɗa da wani irin murya kamar ba nata ba. "I promise u." Ya faɗa da sauri. A hankali hannayen su ya rabe da juna tana waiwayenshi shi kuma har lokacin yana tsaye yana kallon foot step ɗinta. Zazzaɓin daya kusan zautar dashi kafin yakai gida ne yasa ya tsaya a Lagos gidan Nazeer. Kafin washe gari duk yayi wani irin rama saboda rashin samun layin Siyaa da bai yi ba. Jikinshi a mace yake ƙoƙarin fita don Nazeer ya kaishi airport kiran Daddy ya shigo. Da murya kamar ana tashin duniya Daddy yake tambayarshi. "Abu Zaid kazo kayi min bayani menene tsakaninka da wannan yarinyar Hudayya?" "Hudayya kuma?" Ya tambayi kanshi jinin jikinshi na tsinkewar da yasa dole ya nemi waje ya zauna a gefen Couch ɗin da Nazeer yake....✍🏻 _Yanzu zamu shiga cikin ainihin labarin In sha Allah_ NAFISA SASAAL. [9/26, 5:57 PM] Hajja Ce: ABU ZAID Page 8 By Nafisat Aliyu Sasaal Kafin ya ƙara magana Daddy ya kashe kiran. "Meye matsalar?" Nazeer ya tambaya yana kallonshi. "Nothing serious." Abu Zaid ya faɗa yana saita yanayin da yake ciki. "Really? bayan naji kafaɗi sunan filthy girl ɗin da ka kwasowa kanka." Nazeer ya faɗa cike da izgilanci haɗe da haushin ɓoye mishi ainihin matsalar da Abu Zaid ɗin yake ciki. "Har sau nawa zan gaya maka kadaina kiranta da haka?" "Ohh haka ne fa, da alama ta fara baka kana ɗanawa." Nazeer Ya ƙarasa faɗa don huce haushin da yake ji duk da yasan Abu Zaid bashi da makamanciyar halayyarshi. "Ni ba irin ka bane, idan taimako ba shi da rana da may be har yanzu kananan kana bin club ɗin daka saba, ban taimaki Hudayya don tana da abin bani ba kamar yanda kayi naka taimako." Abu Zaid ya faɗa yana jin zafin kalaman Nazeer har lokacin. Sa'insar kalamai ma su zafi ne ya ɓarke tsakanin su ƙarshe sukayi faɗan daya kusa kai su ga yin dambe, don zuciyar Abu Zaid akusa yake, shima kuma ta Nazeer ɗin haka saboda matarshi daya hango alamun taji komai. A fusace Abu Zaid ya fice daga gidan yana jin nadamar zuwa gidan Nazeer ɗin tana shigarsa. A motar haya Abu Zaid ya tafi airport, zuciyarshi a ƙuntace yana jin abotarsu da Nazeer ɗin ta zo ƙarshe. ******* Sai dare ya ƙarasa gida wajen 9:30. Bai nemi Daddy ba don har lokacin bai bawa tambayar menene tsakaninshi da Hudayya da yayi muhimmanci ba. A kan idanuwan Hudayya dake manne jikin window Abu Zaid ɗin ya dawo. Shi kuwa apartment ɗin sa ya kusa. A ranar kusan kwana yayi yana neman layin Siyaa tare da tura mata saƙonni kala-kala har videon kuka da magiya ya tura ma ta amma har midnight Siyaa bata kunna data, gashi kuma wayarta kwata-kwata bata shiga. Yanke shawarar ya bita Coventry ɗin yayi akan indai ya ƙara kiranta gobe bai sameta ba. Bacci marar daɗi ne ya ɗaukeshi cike da mafarkai kala-kala. Bai yi wani baccin hour ɗaya da rabi ba alarm ɗin sallar asubahi ya tashe shi. Alwala ya yi ya fito zuwa masallaci. Tun a masallacin Daddy bai amsa sallamarshi ba balle gaisuwarshi, Abu Zaid kuwa da ya lura da fuskar mahaifin na shi da kyau sai ya ga har rama yayi. Ganin bai kulashi ba har ya shige apartment ɗin su, hakan yasa shima Abu Zaid ya wuce nashi. Duk ƙarfin damuwar da ke ran Abu Zaid ɗin haka ɓarawon bacci ya yi nasarar ɗaukeshi. Duk Hudayya na kallon fitarshi masjid ɗin gidan da dawowarshi. Cikin kayan baccin da ba su da maraba da babu ta shirya, sannan ta ɗora hijjab a kai ta fito daga apartment ɗin Auntyn. Da sanɗa ta buɗe ƙofar corridor ɗin su Abu Zaid ta shige. ****** Aunty kuwa rashin ɗaga wayarta da Alhaji Ɗalhatu ya ƙiyi kwata-kwata ne ya fara damunta, tana cikin wannan zullumin ne text message ɗinsa na cewa ta zo ta ɗauke yarinyar da ta kawo mishi cikin gida ya shigo wayarta. Tashin hankali ya dirar mata ta fara tunanin kodai wani abun Hudayya tayi? A ranar Aunty tabao Ghana duk da tsaka mai wuyan da ƴarta ta take ciki game da fitar zancen dashen da akayi mata cikin dangin mijinta, saboda dukkan su sun juya mata baya daga jin zancen. Dan acewarsu ma don kwaɗayi taje tayi dashen. Dama ana gobe Abu Zaid zai dawo zariya Alhaji Ɗalhat ya turawa Aunty saƙon. Dan haka tun yammacin ranar da Abu Zaid ya dawo itama Aunty ta dawo. Faɗan da yayi tsamarin daya kusa furta mata kalmar saki sukayi tayi a daren yana cewa matsawar bata mayar da Hudayya gaban ubanta ba, tabbas ita da Hudayyan zasu bar masa nashi gidan. Aunty tayi magiya ta tambayeshi dalili da kuma abinda ya faru ya sauya, amma yaƙi sanar mata, ƙarshe kuma korarta ya yi daga ɗakinsa ya kulle ƙofarshi. Bata kawowa ranta Hudayya zata aikata wani mugun abu ba, shi yasa tayi ƙoƙarin shanye dukkan damuwarta don karta fahimci komai kar hankalinta ya tashi. Aunty na ɗaki abun duniya duk ya yi mata yawa taji motsin buɗe ƙofa amma bata kawo fitar Hudayya a irin wannan lokacin ba. A cikin bedroom ɗin Abu Zaid Hudayya tayi ɗai-ɗai har da cire hular dake kanta tana ƙare masa kallo yana ta baccinsa. Cikin dabara ta fara gudanar da mugun nufin dake cikin ranta, tunda har ya gagara bata muhimmanci a cikin rayuwarsa bata jin zata iya barinsa har sai ta ɗanɗana masa zafin da take kunsa akansa. Makamancin saƙon data saba turawa numbern Alhaji Ɗalhatu da ta sato a cikin wayar Aunty, shi ta ƙara turawa Alhaji Ɗalhat ɗin harda haɗawa da number Siyaa. Ta kuma yi sa'ar yana online Alhaji Ɗalhat ɗin dan haka tana turawa ya buɗe saƙon. Dama kuma a wuya yake dan haka ya sake fusata ganin abunda aka turo masa, parlorn Abu Zaid ɗin da yagani ne a cikin sakon ya tabbatar masa da gaskiya ne cikin gidan shi ne. Ya fito a fusace ya yo apartment ɗin Abu Zaid ɗin. Da ƙarfi taji Lokacin da yake knocking ɗin door ɗin farko. Da hanzari ta miƙe tsaye scafe ɗin ta riƙe a hannun da hijjabinta da ta ninke. Gaba ɗaya fin rabin ƙirjinta a waje yake. A haka taje ta buɗe door ɗin tana mitsitsike idanuwanta. Kamar gaske haka ta nuna taji tsoron ganin shi, da gudu ta raɓa ta gefensa tabar wajen zuwa na su sashen mugun murmushin fuskarta yana sake faɗaɗa. Alh Ɗalhatu kan shi ya dafe zuciyarshi na bugawa. Ƙafafuwanshi ne suka kasa ɗaukar gangar jikinshi don haka ya zube a ƙasa kamar wani tsohon gini da yasha ruwan sama lokacin damuna. Hankalin ma'aikan gidan a tashe suka yo kanshi. Cikin ɗaga murya suke kiran Aunty, wacce ta fito da gudu tayo hanyar. Ganin halin da Alhajin nata yake ciki ne yasa tace a shigo dashi ciki. Kai tsaye ɗakin shi aka kaishi ta kira likita hankali a tashe. Shima Abu Zaid da yake cikin ɗaki jin irin yadda ake kiran Hajiya Aunty yasa shi farkawa daga bacci. Kafin ya gama shiryawa ya fito an ɗauke Alhajin an kai shi ɗaki. Sai da likita yazo ya fara duba shi sannan ya fito yana ta mamakin meke faruwa? Me ya samu Daddyn? "Sannu Alhaji." Shine furucin da Aunty take ta maimaitawa bayan likita ya gama dubashi. Bai amsa mata ba kuma bai buɗe idanuwanshi ba har Abu Zaid da yayi wani irin rama ya ƙara shigowa ɗakin. A tunaninsu bacci yake yi don haka suka bar ɗakin don ya samu hutu da kyau. Dukkan tambayar juna suke yi meke faruwa da Daddyn? Sai dai babu wanda ya san taƙaimaimai abinda ya faru. Aunty kuwa sama ko ƙasa ta nemi Hudayya ta rasa a cikin gidan, tana ta mamakin ina Hudayyan ta sani da har zata fita ba tare da ta sanar da ita ba? Ai kuwa har zuwa yamma babu ita babu labari. Tun abun baya damun Aunty har taga tsoron rashin ganinta ya fara damunta. Da tsananin kuka ta kira Ramatu amma ba'a ɗauka ba, dole haka ta haƙura tana fatan Allah yasa ba wai ɓata tayi ba. Har dare yayi Alhaji yaƙi tankawa kowannen su, amma jikinshi da sauƙi tunda har ya ɗan fita. A daren ranar shi kuma Abu Zaid ya haɗa kayansa na bin Siyaa can Coventry. Dan yasan idan ya ƙara wasu kwanakin ba tare da yasan halin da take ciki ba ciwo ne zai danneshi gaba ɗaya. Daddy gaba ɗaya ya sake ɗaure fuska ya damu Aunty da lallai karya sake ganin Hudayya a cikin gidan. A nan ne take sanar dashi cewa bataganta ba. Duk da Alhaji Ɗalhatu yaji daɗin barin Hudayya gidanshi. Still yakasa daina imagine ɗin hotunan da ake tura mai na muraran ɗin al'aurar ɗanshi da yarinyar da bata kai Iyalinshi komai ba. Shi a karan kanshi kunya da tsoron tunkarar Abu Zaid da zancen yakeyi don idan har da gaske ya tabbata shine da Hudayya a waɗannan hotunan, toh wallahi sai ya sakar mishi ɗiyar shi dan Siyaa ba zata zauna dashi ba. Amma a kaf binciken dayayi Abu Zaid baya bin mata sai dai shan cigarette da suka sanshi da shi. Sai dare sosai Aunty ta samu wayar Mama Ramatu. Tana ɗagawa kuwa ta shiga cewa. "Ramatu baku da wajen zuwa gobe ku bar gidanku gaba ɗaya?" Salame ta faɗa da dakushasshiyar muryar kukan datasha bayan sun gaisa. "Ramatu kiyi min bayani ina Huda? mai yake faruwa?" Kit Ramatu ta datse kiran saboda wani irin bakin ciki daya taho mata. A daren ranar babu wanda ya samu ya runtsa, kowannen su da abinda yake zuciyarsa. ****** Ƙarfe 8:00 na safe wata motar dattijai da matasan da talauci ya yiwa kamu mai tsauri tayi parking a ƙofar gidan su Abu Zaid. Hudayya ce kaɗai mace a cikin su. Gaba ɗaya ba su da kyawun gani don ko a ƙauyen ma su masu rangwamen tsafta ne. Hayaniya da Zage-zagen su ne ya fito da Alhaji Ɗalhat da Aunty da dama ba wani bacci suka koma ba, mutanan kuwa tuni Maigadi ya hanasu shiga ciki ganin yanayin su da yai. Abu Zaid kuwa yana can a kwance ya ɗan fara baccin daya samu bayan sallar Asubahi hakan yasa duk baiji abinda yake faruwa ba. Aunty kuwa babu fuskar wanda bata gane ba a cikin su, wani irin fargaba da tsoro ne ya mamaye jinta da ganinta. Duk fargabar da Aunty take ciki ta Alhaji Ɗalhat yafi nata saboda Hudayya da yake kallo kanta a ƙasa bayan ya ba da izinin a barsu su shigo cikin gidan. Cikin rashin daraja da haushin Salame da shi kanshi Alhajin da ya yi mu su korar kare shekarun da suka shuɗe suka daɗe suna neman hanyar fanshe shi ba su samu ba sai yanzu. Ƙanin mahaifin su Aunty ne ya fara wajabi cewa. "Jiya Huda tazo Gwarzo batayi cikakken minti talatin ba ta sume mana. Bayan mun kaita a asibiti likita ya tabbatar mana da cewa ɓarin ciki tayi. Da muka matsa akan ta gaya mana gaskiya, sai ta sanar da mu cewa ɗan wajenku ne yayi mata wayo yake kusantarta da sunan zai dinga biya mata kuɗin Makaranta, ita kuma bata da zaɓi don tana son yin karatu mu kuma gaskiya ba zamu yarda ba don yanzu babu namijin da zai iya aurenta a haka." Baba Ila ya ƙarasa faɗa da kukan makircin da suka shirya yi mu su. Hankalin Aunty ne yai mugun tashi. Da gudu Auntyn da ta kasa jurewa maganganun Baba Ila ta nufi wajan Hudayya da ke rakuɓe a gefe, dukanta ta farayi ta ko'ina da wani irin kuka mai ɗacin gaske. Daƙyar aka ƙwace Hudayyan daga hannunta wacce ko gezau bataji zafin dukan ba. A shirye Abu Zaid ya fito janye da luggage ɗin kayanshi. Hayaniyar ɓakin fuska da ganin Aunty a tsaye Mahaifinshi kuma na daga gefe yana waya ne yasa shi ya taho wajen su da sauri. Tun daga nesa suke ƙare mai kallo zuciyarsu na ƙaryata mu su cewa Abu Zaid bazai iya neman mace kamar Hudayya ba don tazarar su mai ratar gaske ce. Amma ɗaukar fansar dake zuƙatan su bazata barsu su neman yin diddigin komai ba. Kyawawan hannayenshi yake miƙawa Baba Ilu don su gaisa. Kukan kura Aunty tayi ta janye hannun Abu Zaid tana ƙanƙameshi. "Lafiya Aunty mai yake faruwa ne?" Ya faɗa da sassauƙar muryarshi. Batace komai ba sai kuka kamar zata haɗiyi ranta. Alhaji Ɗalhatu kuwa Nazeer ya kira kai tsaye don jin ko yasan wani abu dangane da alaƙar Abu Zaid da Hudayya? Nazeer ya tuna yadda Abu Zaid ɗin ya wulakanta shi duk saboda yarinyar. Dan haka zugar da ya rusa duk wata amana da yadda da mahaifin Abu Zaid ya yiwa Zaid ɗin tare da tabbatar mishi da cewa eh dagaske ne ita Nazeer ya yi. A nashi tunanin Nazeer ɗin korar Hudayya kawai za'a yi dan abokin nashi ya huta. Sai dai bai san zugar dayayi yanzun itace ta zama silar rushe ginin da bazai ƙara ginuwa ba har abada. Weakness ɗin Alhaji Ɗalhatu ne ya bayyana ƙarara wanda ba abu bane mai sauƙi idan ya shiga wannan yanayin, don shi mutum ne mai taurin zuciya da zafin kai. Ƙwallar baƙin cikin daya zubo mai ce ya share zuciyarshi na wani irin bugawa kamar zata faɗo ƙasa. Baba Ilu da sauran Dattijan Alhaji Ɗalhat ya kira gefe suka tattauna kafin ya koma ciki ya ɗauko kuɗi, har lokacin kuma Aunty na riƙe da Hannun Abu Zaid tana kuka. Ciki ya jata suka koma don tunanin shi irin matsalar data saba samu ne da dangin ta. Jikin Aunty har rawa yake yi tana riƙe dashi ɗin yace, "Aunty kiyi shiru mana komai zai dawo dai-dai In sha Allah." Kalaman da Abu Zaid yaketa lallashin Aunty da su kenan amma still taƙi yin shiru. Babu sallama Alhaji Ɗalhatu ya shigo living room ɗin Hudayya na biye da shi a baya wacce ita kanta sai takejin muzantarta da tsantsar butulcinta gare su. Ƙaramin littafi da pen ɗin shi dake soke a gefe Alhaji Ɗalhatu ya bawa Abu Zaid yace. "Yanzun nan ba sai anjima ba ka rubutawa ɗiyata sakinta ka bani. Kai kuma ga mata nan na aura maka ita yanzu nan sai kaje ka cigaba da abinda kuke yi har sai na nemeka. Idan kuma ka dawo min cikin gidan nan wallahi sai na maka ɗaurin da sai ka gwammacewa mutuwarka." Alhaji Ɗalhatu ya faɗa da wani irin fushi a ƙarshen furucinshi. "Daddy! Aunty! Dukka menene wannan yake faruwa? Please kuyi min bayani dan Allah." Abu Zaid ya faɗa yana kallon su both of them. Cikin wani sabon fushin Alhaji Ɗalhat ke cewa. "Har yaushe tarbiyyar da muka gina maka ni da Zayyad yayi rushewar da zaka zaɓi wannan yarinyar a kan Siyaa har kayi mata ciki Ibrahim?! Wallahi baka yi min adalci ba, idan na bar mutum irinka da auren ƴar Zayyad tabbas naci amanar shi. Shin yaushe kayi wannan lalacewar ban sani ba?" A gigice Abu Zaid ɗin yake cewa, "Daddy kuyi min bayani sosai menene wai? Ni dukka wannan ɗin wacece ita da na yiwa cikin? wallahi ƙarya takeyi, karya ne Daddy ban aikata ba!!" Ya faɗa da amon da yasa Aunty ƙara nufar Hudayya tana jibga. Sai a lokacin Abu Zaid ya fara gano bakin zaren maganar ganin yadda Aunty ke dukan Hudayyan. Da sauri yake cewa. "Ni kuma Daddy? Toh me zanyi da Hudayya nikam?" Ya faɗa yana girgiza kanshi. "Waɗannan hotunan uban waye a jiki da zaka karya ta? Sannan mai take zuwa yi cikin sashenka? sannan kuma Nazeer ya tabbatar min da gaskiya ne duk abinda ya faru!!" Ya faɗa yana nuna masa hotunan su marasa kyan gani dake cikin wayarsa. Wani irin kuka wanda ko sautinshi baya fita sosai Abu Zaid ya saki, cikin tashin hankali ya shiga bawa mahaifin shi haƙuri tare da nufar Hudayya da Aunty take duka har a lokacin. Janye Aunty gefe ya yi yana kallon Hudayya da jajayen idanuwanshi yake cewa. "Ki ba su labarin ya kika haɗa abinda kika haɗa karki cuceni kinji? Ina da abubuwan da suke damun rayuwa ta, taimaka miki nayi fisabillahi. Kinganni ko? wajen Siyaa zan tafi tana can tana jirana dan Allah ki gaya musu gaskiya kinji?" Ya faɗa kamar wani ƙaramin yaron dake neman abinci. Hudayya batace komai ba sai kukanta daya ƙaru lokacin da kunnuwanta suka ji yana cewa wajan Siyaa zai je. Duk abinda yake faruwa ba damuwarta bane ba tunda har ya zama mallakinta. Sai dai kalmar wajan Siyaa zai je ta tsaya mata a wuya. Kira ne ya shigo layin Alh Ɗalhatu bai ɗaga ba don yasan mai zata faɗa. Na Aunty ta kira batare da tsayawa tantance mai kiran ba Aunty ta ɗaga. "Kina kusa da Ɗalhatu?" Sai a lokacin Aunty ta gane cewa mahaifiyar Siyaa ce. Bata jira cewar Auntyn ba taci gaba da cewa. "Idan shi bazai ɗaga kiran ba toh kisani a sarari dan yajini saboda shi na kira. Wallahi na rantse indai ɗan shi bai sakar min ƴata ba wallahi sai na tona asirin komai wanda kunyar duniya kaɗai ya ishe shi." Duk suna jinta kuma tunanin su kan hotuna ne yaje gurinta. Saɓanin shi Abu Zaid daya fuskanci abinda take nufi wanda shida Siyaa da Zainab ne kawai suka san komai. A daidai wannan gaɓar ne ya ƙara tuna cewa barin Siyaa dolen shi ne, duk da dai yayi tunanin neman maganin Islamic kamar yanda wani likita yabashi shawara, amma yanzu anzo gaɓar daya riga ya makara abun ba zai yiwu ba. Littafi Daddy ya ƙara jefa mai a fuskar sa yana cewa. "Ka rubuta mata sakin kazo ka bar min gidana. Kuma wallahi ka ɗauki tsinken dana siya da kuɗina ban yafe maka ba." Alhaji Ɗalhatu ya faɗa yana fashewa da wani irin kuka. Ba wani dogon rubutu ba ne zai yi, amma rubutu ne da zai zama dogo a tarihin rayuwar Siyaa na har ƙarshen rayuwarta. A nan ya bata mata labarin halin da yake ciki na sharrin da akai masa. Ya kuma bata labarin girman soyayyarta dake cikin zuciyarsa. Ƙarshe ya rubuta ma ta saki ɗaya yana jin zuciyarsa kamar zata faɗo ƙasa. A gefenshi ya ajjiye wanda zuwa lokacin Alh Ɗalhatu yabar parlon sai Aunty dake wani irin kuka. Hudayya na rakuɓe a gefe amma cikin zuciyarta babu nadama sai na furucin korar Abu Zaid da kuma furucin mahaifinshi na kar ya ɗaukar masa komai na shi. Aunty ya

Chapter 4 of 11