Share this page
batun cikin ba, tunda Siya bata gaya mata ba sai kuka da takeyi kuma tasan Saleem likita ne bazai yi mata ƙarya ba. ★ Washe gari Mommynta ta taho Zuwa Nigeria, a Lagos ta sauka washe gari ta biyo jirgin Kano. Da magiya da roƙo Siyaa ta yarda ta bi Mommynta suka koma Coventry amma da sharaɗin idan ta haihu zata dawo, shima Muhammad da aka kira a waya ya nuna ya yarda, musamman da yaji Siya tana da juna biyu. Muhammad kam har ƙwarya-ƙwaryar Walima mai ƙayatarwa ya shirya shi da abokanan kasuwancinsa a gidan hutawarshi, har lokacin Zayad baya ƙasar sai a waya da suka sanar da shi. Daidai da tari idan Siyaa tayi sai Muhammad ya tambayeta menene matsala? haka Mahaifinsu duk zuwa sai ya tambayeta ko ta na buƙatar wani abun? Sai tayi bacci suke dena tambayar ta. A ranar da tayi Sati da dawowa Zayad ya dawo amma bai zo gidansu ba sai da yayi kwanaki saboda hutun da yake buƙata. Batason kallon fuskar Zayad saboda dalilan da ita kaɗai ta barwa ranta, a zahiri yana nuna kulawarsa a kanta, amma wasu lokutan tana hango kamar rashin yarda da ita a cikin idanuwansa. Sai bayan sati ɗaya da dawowar Zayad ya kawo musu ziyara, shima bai jima ba ya ja ɗan uwansa suka bar gidan, harara Siya ta raka bin bayansu da shi tana jan ƙaramin tsaki. A ɓangaren Hudayya kuwa irin zaƙewar da ta nuna ne yafi komai birgesa bayan ya keɓance da ita, duk da yana sane da matar abokinsa ce. Daga ranar da ta bawa Taufiq haɗin kai, sai ta janyewa zuwa Makaranta kullum tana guest house ɗin Taufiq suna lalatarsu. Abu Zaid kuwa bai gajiya ba duk ƙarshen wata sai ya tura Hudayya da uban siyayya da zata kai Tofa ta kaiwa Siyaa amma sai ta wuce ƙauyen Gwarzo da shi. Ciwon ƙafarsa bayayin baya kullum sai gaba duk da maganin da yake shafa mai. Taufiq yayi niyar kaisa Asibiti mai kyau amma Hudayya ta hana da salon makirci irin nata, da yake kuma bayason abinda zai ɓata ranta sai ya haƙura. A ɓangaren Aunty kuwa damuwa da rayuwar kaɗaici ce ta fara taɓa lafiyarta itama, a hankali ciwo yafara danneta cikin watanni biyu jikinta yayi tsanani domin ƙiri-ƙiri har Zainab Dangin Alhaji Ɗalhatu sun hanata ganin mahaifinta. Gida ma suka mayar da shi sunata banka mai maganin gargajiya. A ɓangaren Abu Zaid kuwa da Lokacin biyan kuɗin makarantar Hudayya yayi sai yagaza saboda baya ajjiye kuɗi kullum cikin yin siyayya yake yana tarawa duk ƙarshen wata Hudayya takaiwa Siyaa ita kuma sai ta wuce Gwarzo da shi wajen ƴan uwanta ta kai musu suji daɗi. Hudayya kishin inda Abu Zaid yake ƙarar da kuɗinsa har ya gaza biya mata kuɗin makaranta da kuma samun damar da ta yi ne yasa tace Taufiq ya zaɓa ko jikinta ko sallamar Abu Zaid daga aikin da ya bashi. Ba su taɓa samun saɓani ba sai a wannan lokacin don ɗauke mata wuta Taufiq ɗin yayi. Itama sai ta ɗauke masa ta share shi. Amma da yake shaiɗanci da kwaɗayin son jikinta na addabar zuciyarsa sai ya gwammacewa korar Abu Zaid ɗin daga aiki ya kuma cigaba da cin amanar shi. Kira yafi miss called goma Taufiq ya yiwa Hudayya amma bata ɗaga ba tana ƙunshe a ɗaki ranta duk ba daɗi, sai a kira na wajen goma sha ɗaya ta ɗaga cikin yauƙi da salon ƙara siye zuciyarshi tace "Mai yasa kake kirana bayan duk wulaƙancin da Abu Zaid yake min kana gani yasan ba shi da abinda zai gamsar da ni ya ajjiyeni a matsayin matarsa, kuma sannan ya dinga aikani wajen matar da tayi sanadiyar barin shi daga gidan iyayensa. Nifa yake aike duk ƙarshen wata da kaya amma banyi fushi ba shine kuma duk da haka zaice bazai iya biya min kuɗin Makarantar ba? Da me zanji? Haba Dear anya kuwa kana sona? Bafa ina nufin shi da wani abun bane kawai don ya hankalta ne ya daina yin irin wannan siyayyar shirmen dayake yi yana cewa nakai inda ba shida hurumi." Hudayya ta ƙasa faɗa kamar zata saki kuka. Taufiq cikin wutar da shaiɗan yake rura mai na son kasancewa da Hudayya ba don tafi Iyalinshi da komai ba yace; "Naji na amince shikenan yanzu ki fito ina jiranki." Cikin ta Hudayya ta shafa tana sakin murmushin dayasa Taufiq yin ajiyar zuciya... ✍🏻 [10/29, 9:59 PM] Hajja Ce: ABU ZAID Page 13 BY SASAAL Taufiq ajiyar zuciya ya sauke bayan ya katse kiransa da Hudayya. Tunanin shi tayaya zai iya koran Abu Zaid daga aiki bayan yasan shine madafarsa? amma garaɓasar da yake kwasa a jikin Hudayya na neman sashi makantar da zuciyarsa kan ya sauya ra'ayinsa akan taimaka shi da ya yi. Bayan mintuna bakwai da wayar su da Hudayya kiran Abu Zaid ya shigo mai. A mutunce su ka gaisa sannan cikin ƙanƙantar da murya a karo na biyu da yake roƙonshi kuɗi yace. "Kayi min haƙuri Taufiq zanƙara neman alfarma a wajenka, please ka taimaka min da kuɗi na biya kuɗin makarantar Hudayya dan Allah." Wani irin sanyi jikin Taufiq yaji yanajin Abu Zaid bai cancanci ya juya mishi baya ba domin zuciyarshi mai kyau ce. Amma abinda sheɗan yake kitsa mai a kan Hudayya ya girmi tausayin Abu Zaid dayakeji a ranshi. Abu Zaid cikin sanyi murya da yake tunanin haushin tambayar kuɗin da yayi Taufiq yaji yace. "Kayi haƙuri da takurata Taufiq, nasan kayi min halacci, ka rufa min asiri a lokacin da nake buƙata." Cikin kame-kamen tunanin da yake yi Taufiq yace "No.. No.. No! Karka damu, In sha Allah anjima zansa a kawo maka." Godiyar daya ƙara jefa wasi-wasi mai girma a cikin zuciyar Taufiq Abu Zaid yayita yi mai. Bayan Abu Zaid ya katse kiran Taufiq tambayar kansa ya yi; "Mai Abu Zaid yake samu a zamansa da Hudayya da har yake jin ta cancanci ya kyautata rayuwarta har haka? Tana nan tana cin amanarsa, yana can yana tunanin yadda zai kyautata rayuwarta." Ya runtsa ido yana cije lebe. Kuma a take yaji bazai iya korarshi daga aiki ba, zai bashi hutu kawai don kawar da idon Hudayya ya samu abinda yake so. Hudayya Cikin shigar daya fitar da surar jikinta gabaki ɗaya ta shirya sannan ta ɗora Abaya a sama ta yafa mayafin Abayar. Tayi sa'ar Abu Zaid baya parlorn don haka ta siɗaɗe ta gudu bayan ta gama hararar ƙofar ɗakinsa. Abu Zaid kuwa bayan gama wayarsu da Taufiq ajiyar zuciya ya sauke yana shafa ƙafar da yake jin ciwo a cikita gaba ɗaya, ba kamar daa ba da iya ɗan yatsansa ne kawai yake yi mai ciwo, bayaso Hudayya taji wani iri tunda ko ba komai ta taimakeshi ta ɓangaren kaiwa Siyaa saƙo duk da ƙorafin kyara da take yi masa akan Siyaa ta nayi mata amma ta jure, wannan dalilin yasa yake ganin ta cancanci ya kyautatamata.. Bai taɓa zargi ko kawo tunanin Hudayya bazata taɓa yi misa irin wannan alfarmar ba, a tunaninsa dagaske ta sauya kamar yadda take nunawa, har kullum yana ganin yadda zuciyarsa take mai kyau haka na kowa na yake. A hankali ya fito parlorn ya zauna yana jiran zuwan Yaron Taufiq. **** A ɓangaren Siya kuwa. Duk kulawar da Muhammad yake bata amma bata gani kullum tunaninta na kan ɗan uwanta Abu Zaid. Taƙi ta saki jiki suyi irin rayuwar wayayyun da yake buri, babu inda baya kaita don ta samu farin ciki amma bata nuna jin daɗinta balle ta tabashi haɗin kai suyi irin zaman dayake so. Muhammad bai iya riƙe damuwa ba kamar ɗan uwanshi,zai iya cewa akan Siyaa ne kawai yakasa samun irin soyayyar dayake so. Wasu lokutan haka zata wuni tana ƙunci har da su kuka kuma duk tambayar da zai yi mata babu amsa sai kuka, har wajen Mommynta ya kai ƙorafin ta tuntuɓi Siyaa menene damuwarta, maimakon ta tambayeta menene damuwarta ta, sai batayi ba sai faɗan da yasata ƙin kula Muhammad ɗin bayan ya kaita gida ya ɗaukota. Damuwa irin wanda bai san akwai shi ba ya shiga da ya kasa jurewa sai ya wuce gidan Zayad. Babu shamaki tsakaninsa da gidan Zayad amma a ranar sai aka yi misa iyaka da shiga, kuma yakira wayarsa bai ɗaga ba, da wannan baƙin cikin ya wuce gidan Mahaifinsu, yana zuwa na ya fita. Ba ya wahalar da kansa wajen kai wa Mahaifinsa ƙorafin Siyaa don baya ganin laifinta, komai tayi dai-dai ne. Daa ya tashi tafiya maimakon ya wuce gida sai ya tafi mashaya yasha giyan da ya jima da daina sha tun kafin auren su, sai da ya bugu barci ya ɗaukesa anan. Sai tsakar dare ya farka. Baiji wani nauyi ko ya aikata wani laifi na musamman ba. Jiki a mace ya wuce gida abinda ya ƙara ƙona mai rai Bedroom ɗin Siyaa ma a kulle yake haka na nufin batasan ma bai kwana a gidan ba. Da tafiyar mayen abinda yasha da bai gama sakin sa ba ya wuce ɗakinsa da fushi. Siyaa kuwa bayan ta farka simple make-up da shiga mai sauƙin nauyi tayi tana jiran Muhammad ya fito su karya. Tana zaune ya fito fuskarshi a kumbure, kusa da ita ya zauna yana kama dukka hannayenta haɗe da marairaice idanuwanshi, da muryarsa mai daɗin sauraro yake mata ƙorafin bata damu da shi ba. Ko har yanzu ɗan uwanta takeso ba shi ba? Kai ta girgiza tana ƙoƙarin shanye hawayen da yake son zubu mata, hannunta na cikin nashi yake faɗin "Toh me kike so Siya?" A hankali cikin rawar muryar tace; "Bana jin daɗi, komai baya mun daɗi." Da nazari sosai Muhammad yake kallonta yanason tantance menene ainihin matsalarta amma yakasa ganowa. Ya na manne da ita suka karya. Bayan sun gama karyawa ya miƙe ya na yi mata raɗar cikin kunne ce ta shirya su je gidan Zayad. A take yanayin fuskarta ya canza, ta na bin bayansa da kallo. Daa tana da zaɓi da babu abinda zai sa ta bishi. Sun kusa minti ashirin da biyar a zaune sannan sukaji alamun tahowarsa saboda ƙamshinsa dayake ƙara kusanto su. Cikin tafiyarshi data tsana sama da komai na izza da alfaharin da ko bai faɗa ba tasan yana ji da tarin baiwar da Allah yayi mai. Bayyanarsa a parlorn yasa ta ɗauke kanta daga saitinsa Zayad bai ɗauki sauƙin kai a matsayin abu mai kyau ba balle ya kwatanta yi, tayaya ma zai yi sauƙin kai mutane su rainasa bayan yana da komai. Yanda suka gaisa da ɗanuwansa da yanda suka rungume juna ne yasa Siyaa jan ƙaramin tsakin da ita kaɗai taji kayanta. Siya bayan sun gaisa da Zayad Irin kallon da kullum take hangowa idan sun haɗa ido taƙara ganin a cikin idanuwansa sai dai na rana ƙarara ya bayyana kallon ƙasƙanci yake mata, kanta ta sunkuyar ƙasa tana jin takaicin dama bata biyo Muhammad ba, amma komai ya yi mata ba laifinsa ba ne laifin Mahaifiyarta da take kambabasu. Da rawar murya kukan da yake son ƙwace mata ba tare da ta ɗago fuskantata ba ta ke amsa mai tambayarta lafiyar Baby da yayi. Har suka gama hirarsu Siya ba ta motsa balle ta tofa Zayad ya gwaleta, domin tun guduwarta Tofa bai ƙara kiranta ko ya ce ɗan uwansa ya bata waya su gaisa ba kamar yadda ya saba. Zayad da ma can Siya tana burgishi ne saboda yana ganin tana son ɗan uwansa, amma tunda ta gudu ya gano ba son Muhammad takeyi ba kuɗinsu da shahararsu suke so. A ɓangaren Hudayya Suturarta take mayarwa bayan sun gama abinda ya haɗasu, tana sawa tana murmushi har da kashewa Taufiq da yake kwance a gefenta ido ɗaya. Murmushi Taufiq ɗin ya mayar mata, yana mamakin yarinya ƙaramar kamar Hudayya da iya bariki tamkar wata babba. Bayan ta gama sakawa sai ta faɗo kanshi, cikin yauƙi da kisisina tace. "Ya ya zancen mu ka sallamen shin kuwa?" Sai da Taufiq ya tattaro nutsuwarsa sannan yace; "Hudayya bai da ce na kori Abu Zaid a irin wannan lokacin da bashi da kowa ba, amma zan bashi hutu kafin ya ji sauƙi sai na maye gurbinsa da wani ina fatan hakan yayi miki?" Baki ta turo tana miƙewa a zafafe haɗe cewa; "Ta yaya zan baka jikina kuma ka ƙiyi min abinda nake so Taufiq? duk ranar daka cire tausayinsa a cikin zuciyarka ka shirya yin adalci tsakanina da shi sai ka dawo mu cigaba da maga.." Ƙofar da ake ƙwanƙwasawa kamar za'a ɓalla ne ya katse zancen Hudayya, da rawar jiki ta ɓuya a bayan Taufiq. Cikin ƙarfin hali Taufiq yace "Relax Baby bari na duba naga waye shiga can ki jirani." Ɗakin da ya nuna nuna mata ta faɗa a guje ta murza key. Taufiq kam ya na zargin cewa matarsa ce tazo, saboda ta daɗe tana zargin yana kawo matan banza gidan, yasan ma ita kaɗaice maigadi zai bari tayi irin wannan bugun. Mukullin Motarsa ya ɗauka sannan ya nufi ƙofar. Yana buɗewa yayi ido huɗu da matarsa idanuwanta sunyi jajir alamun tasha kuka, gudun tonuwar asirinsa yasa ya fara janta da iya ƙarfinsa tana turjewa har ya samu damar turata cikin mota. Kafin su kai duk da ta yakushe mai fuska da hannu saboda ƙoƙarin ƙwace motar da takeyi a hannunshi. "Ki saurareni nayi miki bayani." Cikin kuka mai raɗaɗin da babu wanda zai gane ɗacinsa sai macen da mijinta baya iya kame kanshi daga matan banza ta ce. "Menene babu a jikina Taufiq? Duk wahalhalu da abubuwa da nake yi wajen gyara jikina duk domin na burgeka ace kana neman Matan banza? Matan banza ma da ba su kaini komai ba? mai zakaso a jikin Macen da ta zaɓi cin amanar Mijinta duk da kyakkyawar zuciyar dayake da shi? wallahi baka yiwa Abu Zaid adalci ba, nasan da shi ne wallahi ko babu sutura naje mai bazai taɓa haɗa shimfiɗa dani ba, amma zanyi maganin Hudayya dan wallahi daga kaina ta daina cin amanar kowa." Cikin bazarana Taufiq ya ce; "Ke wai yaushe zakiyi hankali ne eh? me zanyi da Matar Abu Zaid? Ki daina yi min sharri wallahi, idan ba haka ba zan ɗauki mummunar mataki a kanki." Ɗaya wayarsa da ya manta a gida ta ɗauko ta buga mai a fuskarsa tana masifa.. Wani abu mai ɗaci Taufiq ya haɗiye batayi ƙarya ba don babu wani abu na jikinta da baifi na Hudayya kyau ba, hatta a shifiɗar da shaidan yai masa kida har yaje ga Hudayyan. Sai dai yanda Hudayya take fitsare mai da batsa kala-kala da karairaya iri-iri kamar wanda ta taɓa sana'ar karuwanci ne ya fi komai burgesa sai sheɗain dayake ƙara ƙawata masa ita. *** Hudayya kuwa bayan ta tabbatar su Taufiq sun bar gidan da sanɗa ta fito, ko gefen da Maigadi yake bata kalla ba ta bar gidan. A firgice Hudayya ta shigo Parlorn ko sallama babu kamar an korota. Abu Zaid ta samu a zaune, wani irin wari na ɗan tashi sama-sama a cikin parlon, duk ya rame sama da watannin baya. Komawa tayi da baya tayi sallama tana saita nutsuwarta. Da sakin fuska ya amsa sallamarta kafin ta shige ɗakinta bayan ta gaishesu ya ce; "Gobe ki shirya zuwa Makaranta na roƙi Taufiq kuɗi kuma ya bani banason wannan yawon kinji?" Kukan tausayinsa ne ya taho mata don haka ta ɗaga mai kai alamar ta ji, sannan ta wuce ta ƙarasa shigewa ɗakinta da sauri. Kan katifarta ta zube tana kuka mai sauti. "Mai yasa na yiwa Abu Zaid haka? Shin mai yasa?" Ta tambayi kanta. Tuno dalili da ya sa tayi hakan da kuma sonta da bayayi har lokacin sai shaiɗan ya fara gusar da tausayinsa a ranta, tunani kala-kala na addabar zuciyarta. **** A cikin sati biyu da suka biyo baya ita da Taufiq ba su ƙara waya ba saboda matarshi zinare ce mai daraja a wajensa ba zai yarda ita ya ɗauki azurfa ba, gara ya haƙura da Hudayyan kawai. Domin ita Zina sai ka sawa ranka zaka daina kake iya dainawa da taimakon Allah. Amma ga wanda shaiɗan yasamu galaba a kanshi tubarsa na wani lokaci ne. Sai dai lokaci zuwa lokaci zantukan batsan da kunnuwan Taufiq suka sabaji daga bakin Hudayya ne suke ta azalzalarsa, yana jin kamar ya yi shekara bai ganta ba. Yau dai ƙasa haƙuri yayi ya shirya da sunan zuwa duba Abu Zaid bayan hutun daya bashi don ƙafarsa baya iya tafiyar arziƙi da shi. Warin dake tashi sama-sama mara daɗi ne yatashi hankalin Taufiq ga ƙafar ya kumbura sosai don maganin gargajiya Abu Zaid yake shafa mata tunda aka ce masa Cancer ne yasan yasan ya na zuwa babban Asibiti za su ce yankew zasuyi. "Sannu Abu Zaid dama haka ƙafar taƙara komawa? YA Subahanallahi." Taufiq ya faɗa yana kallon yanda Abu Zaid ya canza kamanni. A take Taufiq ya kira wata Cousin Sister ɗin sa da abokin Mijinta yake maganin gargajiya a Minna. Ba a ɗauki lokaci ba aka ƙara kiran Taufiq dake zaune kusa da Abu Zaid suka ce zai iya tahowa kowani lokaci. Har Taufiq ya bar gidan Hudayya bata dawo daga Makaranta ba. Tun a daren Abu Zaid ya yi sallama da Hudayya, bai nemi taimakonta ba ya haɗa kayansa da kanshi. ★ Washe gari da safe, Abu Zaid Cikin tausayin kanshi ya dai-daita zamanshi a bayan motar da Taufiq ya bayar Driver ya kaishi har garin Minna. A waya suka yi bankwana da Taufiq, Hudayya kuwa tana ɗaki a maƙale wai bata lafiya. Hudayya bayan tafiyar Abu Zaid sai gidan gabaki ɗaya ya gundurenta, ko ba komai motsin Abu Zaid yana rage mata kaɗaici. Ranar wata Weekend tana zauna taji ƙwanƙwasa ƙofa, gabanta ne ya faɗi don Maryam ƙawarta batasan gidan su ba, Taufiq kuma ya daina nemanta. A ɗan tsorace ta buɗe ƙofar. Taufiq ne a tsaye cikin kwalliyar shaddar da ya yi masa kyau, Kamar wani tsohon maye haka furta. "I miss You baby." Ranta ta ɗan ɓata tana juya idanuwan da su kaɗai ne suka taimaki fuskarta yake da ɗan kyawun gani. Da salon ƙara siye zuciyarsa ta ce; "Babu ruwana da kai Taufiq." "Haba mana Hudayya kinsan fa ke ta mussamman ce a waje na." Taufiq ya faɗa yana shigowa ciki. Da musayar kalmomin ƙewar junansu da sukayi suka shiririce a gidan Abu Zaid yayin da shi kuma yake can garin Minna cikin azabar ciwo.....✍🏻 [11/2, 11:13 AM] Hajja Ce: ABU ZAID 14 BY NAFISA SASAAL Shashancin da ido bazai so gani ba Taufiq da Hudayya suka tafka a gidan nan dan sai wajen karfe goma da rabi taga yana ƙoƙarin kimtsa kanshi don tafiya gida. Cikin ƙwarewar da ta karantar da kanta Hudayya tace; "Tafiya kuma? gaskiya ni tsoro nakeji kuma ƙewarka zai hanani barci, ni dai gaskiya ka kwana anan." Ido Taufiq ya buɗe da kyau yana kallonta kamar wani tsohon maye na wasu daƙiƙu kafin yace. "Haba Hudayya kinsan banaso matata ta ƙara zargin komai akan mu, kuma kinsan soyayyar mu na sirri ne, kinga kenan babu buƙatar na kwana a nan, ko kinason labari yaje wajen Abu Zaid ne?" Hudayya da takaici ya gama kamawa cikin fushi ta ba shi amsa da. "Sai me? ina da right ɗin yin irin rayuwar da nakeso saboda ba shi da abinda zai gamsar dani a matsayina na Matarsa, kawai kace kana tsoron matarka shine kawai." Rungumeta yayi yana lallashinta da kalaman yaudara cewa. "Ohh My Dayya bai da ce na kwana anan kin gane? Kwana na anan bazai yiwuba ki yi haƙuri." Da fushin da yafi na baya ta ce; "Ka tafi mana wanene ya damu? Mtwsss." Ya ji haushin tsakin da tayi mai, banda ya wulaƙanta kanshi akan Hudayya bata kai matsayin da zata yi masa tsaki mai tsaho irin wannan ba. Bai ƙara kulata ba ya zura kayanshi yabar gidan, bayajin zai iya ƙuntata ran Iyalinshi a kan Hudayya duk da kai tsaye bazai ce baya sonta ba amma sha'awarta ce tafi ƙarfi a ranshi. Bayan fitar Taufiq tayi tsaki yafi ba adadi, dole Taufiq ma ya rabu da matarsa don bazata juri ace kowanni namiji sai tayi sharing ɗin shi da wata macen ba, itama tana buƙatar na ta ita kaɗai. Har ta kwanta barci bata tuna Abu Zaid ba balle tayi mishi addu'a, tunaninta gaba ɗaya ya ƙare ne akan yadda zata ƙara zage damtse wajen juyewa Taufiq kai gaba ɗaya dan ya sake narkewa akan ta. A ɓangaren su Aunty kuwa; An raba gadon Yazid mijin Zainab, tsinke ƴan uwansa basu samu ba, Zainab da ƴaƴanta ne suka gaje komai. Lamarin da bai yiwa dangin Yazeed ɗaɗi ba. Daga ƙarshe suka buƙaci Zainab ta kawo wannan dukiya su juya musu kafin su Safeera su girma. Amma taƙi yadda tace itama tayi wayon da zata iya. Aikuwa rashin amincewar nan nata ya rura ƙiyayyarta a cikin zuciyarsu ƙarshe suka barranta kan su da ƴaƴanta da ita kanta. Ta yi kuka kuma tayi magiyar su tausayawa ƴaƴanta saboda su kaɗai su Safeera zasuyi alfahari da su idan sun girma a matsayin dangi don ita ba ta da kowa daga mahaifiyarta sai mahaifinta da ko ganinshi yafi ƙarfin ta suka rage mata. Gashi dukkansu babu lafiya. Amma sukai biris da ita, ƙarshe tsangwamarsu ya sa Zainab tattara kan ƴaƴanta da mahaifiyarta da take tare da su tana jinya suka dawo Abuja. Bayan sun dawo Zainab ta fara aiki tana haɗawa da kasuwanci, bata taɓa tunanin yin wani yunƙuri na nemo Abu Zaid ba, a tunanin Abu Zaid yana cikin ƙoshin lafiya. Rayuwar su Zainab babu nishaɗi kwata-kwata domin ko Mommyn Siyaa da suke ɗan kira su yi hira bata son ɗaga kiransu, haka Siya itama sai taga dama take amsa wayar su idan sun kirata. Daga ƙarshe da Zainab ta matsa da kira, ƙiri-ƙiri Mommyn Siya ta sanar da ita su daina kiran Siya saboda kiransu yana tuna mata da Abu Zaid, kuma ita ba ta so, dama Abu Zaid ne ya haɗa kuma ya raba. A ɓangaren Abu Zaid; Azaba mai raɗaɗi da ciwo yakeji a ƙafarsa gashi bashi da wani nashi mai kula da shi da kyau sai ma'aikatan malamin da ya ke jinya wajensa. Bashi da mai kiransa sai Taufiq da kullum sai ya kira yaji lafiyar sa. Hudayya kam bata taɓa kiransa ba. Kuma kai taɓa yiwa Taufiq ƙorafin halin da yake ciki ba na rashin samun kulawa gudun kar Taufiq ɗin yaga rashin haƙurinsa da gazawarshi, har sai ranar daya tambaya da kanshi. Ranar da Taufiq ya tambayesa game da cigaban da ake samu, kuka mai sanyi da bakowa bane zaiji ba Abu Zaid ya fashe da shi yana roƙon Taufiq ya sa adawo da shi gida a yanke ƙafar azaba zai kashe shi. Cikin tausayin da ya mamaye zuciyar Taufiq na cin amanar da yake mai yace. "Abu Zaid ka ƙara haƙuri zuwa ƙarshen wata kaji?" Da wani irin dauriya Abu Zaid yace "Ba komai Taufiq zan jure Allah yasa na rayu zuwa lokacin." Muryar Taufiq cike da rauni ya ce "In Sha Allahu zaka rayu har ka tsufa Ibrahim, kayi hakuri aci gaba da duba ka." Murmushi mai ciwo Abu Zaid yasaki yana runtse idanuwansa da haka sukayi sallama. Taufiq kansa ya shafa yana sakin ajiyar zuciya, bayan sun gama waya da Abu Zaid yana jin tausayin sa amma son kasancewa da Hudayya yafi tasirantuwa a cikin zuciyarsa, bakomai yasa yace ya bari sai ƙarshen wata ba sai dan yafi samun kwanciyar hankalin hutawa da Hudayya da kyau a gidan Abu Zaid ɗin. Yana so kafin ƙarshen wata zai samo musu mafita shida ita. Abu Zaid kuwa duk dare baya barci sai kuka da kiran sunan Siyaa, ita kaɗai yake tunawa domin tuni dangin mahaifinsa sukayi masa sihirin daya daɗe da goge masa sunan mahaifinsa acikin kanshi. Tausayi ya farawa bawa waɗanda suke jinya a ɗan madaidaicin gidan tare, har Allah ya kawo wani a cikin ƴan uwansu ɗan asalin Kano ya zo duba shi. Abu Zaid yana kuka yake roƙon su da su tafi da shi Kano ya gaji. Anata kiran number Taufiq amma bai ɗaga ba. Malamin da Abu Zaid yake jinya a gidan ya kira Taufiq ɗin amma shima bai ɗaga ba, ya kuma yi yunƙurin dakatar da Abu Zaid kan ya ƙara haƙuri zai warke, amma Abu Zaid ya nuna sam ya haƙura da ƙafar gwara kawai a yanke masa ita zai fi samun rahama akan tana haka tana cin azaba. ★ Washe gari da safe Abu Zaid ya sa aka ciro

Chapter 7 of 11