Share this page
yayi masa. Tunda ya fito Hudayya da taƙi is tashi tabi driver su tafi ta kafeshi da ido zuciyarta na ƙara ɗaukar zafi, wai duk a kan yasha cigarette ne matarshi tayi aman gulma shi ne yasa ya je yasake yin wanka? Bata gama wannan saƙe-saƙen ba taga har sabuwar mota ya canza. "I'm sorry Siyaaa." Ya faɗa kamar zai yi kuka dai-dai lokacin da yazo inda ta ke. Ba ta ce mai komai ba ta miƙe ta shiga motar jikinta a sanyaye. Banda ta yi missing ɗin ƙawayenta a school da bazata je ba yau. Har sukaje School bai daina yi mata magiyar ya daina ba har sai da tace ta yarda sannan yayi shiru. Bayan tafiyar su kuwa kuka Hudayya ta fashe da shi, banda tasan Aunty bazata yarda da komarwata cikin gidan ba, da wallahi komawa zatayi tafasa ma yin karatun gaba ɗaya. Shima Driver sai da yaƙara ɓata mata lokaci sannan yace ta taho su tafi. Tayi tunanin zata ga kowa na rububinta da nuna ita ɗin wata ce, sai ta ga zaren ba kalar yadin ba ne, don har lokacin fatarta baiyi gogewa irin na ƴaƴan ma su kuɗin da take gani ba, sai duk taji ta raina kanta. Zamanta a aji bai fi na awa biyu ba, Siyaa da ƙawarta suka shigo duba sistern ƙawarta ta. "Siyaama Zaid!,Siyaama Zaid!" Shi ne furucin mafi yawan ɗaliban da Siyaa ta bawa aji ɗaya,tana da masoya da ƙawayen da batasan adadin su ba,wa su na sonta don kyawunta,wa su don ƙoƙarinta wa su kuma don kuɗin Mahaifinta,wa su kuma don kyawawan halayyarta da sauƙin kanta. Tun tana Junior section take da wannan farin jinin har kawo lokacin da ta shiga ajin ƙarshe. Dogayen hannunta take ɗaga mu su fuskarta da yalwataccen murmushin da ya sirka da damuwa. A sit ɗin da ke gaba da na Hudayya su Siyaa su ka tsaya,wanda hakan ya bata damar ƙarewa Siyaa kallo yanda take so. Siyaa na ɗagowa idanuwanta suka faɗa kan Hudayya,dariya da mamakinta ne ya bayya a fili. " Hudayya right? " Ta faɗa bayan ta ƙaraso sit ɗin Hudayya. Daƙyar ta haɗiye baƙin cikin daya toshe ma ta maƙoshi ta amsa da murmushin yaƙe a fuskarta. Hannunta ta miƙe mata alamun su gaisa,taushi da danshin hannun Siyaa ya sa Hudayya runtse idanuwanta tanaji kamar ta ɓalla hannun. Siyaa ba gwanar surutu da tambaye-tambaye ba ce don haka bayan sun gaisa ta juya domin barin ajin. Ƴammata kyawawa zuƙa-zuƙan da dacan ba su ko kalleta ba ne suka marmatso kusa da ita. "Don Allah dama kinsan Siyaama Zaid? Ƴar uwar ku ce?" Kanta ta gyaɗa mu su don a take zuciyarta ta yanke mata sai ta so Siyaa sannan dukka muradanta za su cika. Siyaa ce makaminta a cikin kuduriin dake zuciyarta. Hannayensu suke ta miƙa mata ta na gaisawa da su, amma har ta gama gaisawa da dukka hannayen su bataji hannu mai taushi da danshi irin na Siyaa ba. Wacce ta fi liƙe mata a cikin su sunanta Ramlat, ga mai nutsuwa da saurin karantar mutane da fuskarta su kamar Hudayya zai gano itama ba ƴar ma su kuɗi ba ce alfarma ne ya kawota makarantar. Wannan dalilin ne ya karfafawa Hudayya sakin jiki da ita ko zata ƙaru da ita wajen cikar muradinta. Lokacin da suka fita short break sai Hudayya ta saki jiki da ita don ta lura ta na da surutu. "Kema Siyaa ƙawarki ce?" Hudayya ta tambaya. "Siyaa kuma? wacece Siyaa?" Ramlat ta tambaya ta na fari da manyan idanuwanta. "Siyaama nake nufi." Ya cewar Hudayya. "Wow ki ce Siyaama Zaid, ai ina matuƙar sonta sai dai tayi min nisa a komai." Ramlah ta faɗa da iya gaskiyarta. "To amma mai yasa mutane suke sonta haka?" Hudayya ta tambaya ta na ƙoƙarin danne azababben kishin da ke cin zuciyarta. "Ko ke kanki zaki so Siyaama Zaid in dai kina cikin makarantar nan, kin san kuma halayya nagari da sauƙin kai na ƙara maka farin jini da soyayyar jama'a." A lokuta da dama sai naji baƙin cikin da ma tuntuni nasan Siyaama da babu abinda zai shigo da cutar wani cikin zuciyata. Ki tayi Ramlah taci gaba da cewa. "Siyaama na da kyau kuma Mahaifinta da ya rasu mai kuɗin gaske ne kamar yanda na samu labari. Sannan Siyaama ta sha cin gasar kyau idan aka yi a makarantar nan. Mahaifinta ya taimaki mutane da dama, amma duk da haka Siyaama bata taɓa wulaƙanta wani ba. Lokuta da dama sai naji baƙin cikin da ma tuntuni nasan Siyaama da babu abinda zai shigo da cutar wani cikin zuciyata. Saboda kyawawan halinta. Amma mai yasa kike min waɗannan tambayoyin bayan kincewa ƴan aji ke ƴar uwarta ce?" Hudayya ta samu kanta da cewa. "A gida ba mu santa da wannan farin jinin ba shi yasa." Hudayya ta faɗa tana sunkuyar da kanta don samun damar shanye ƙwallar baƙin cikin da ya fara lulluɓe ganinta. "Gaskiya ke baƙuwa ce a gidan su Siyaaa, amma babu wanda bai san Siyaa ƴar baiwa ba ce ba, domin kamar yanda muke sonta, haka mijinta da dukka danginta suke ji da ita." Ramlat ta faɗa ko a jikinta. "Hakane Ramla ni baƙuwa ce ban jima da zuwa ba." Hudayya ta faɗa da son taƙaita hirar ta su, duk da tana da tarin tambayoyin da takeson sani amma halin da zuciyarta yake ciki bazai bata haɗin kai ba. "Bari ina zuwa." Ramlat ta faɗa ta na miƙewa. Bayanta Hudayya tabi da wani irin kallo mai ban tsoro. Dole ta na buƙatar sanin mafarin su Siyaa da sanin tushen su kafin komai nata yayi yanda take so. NAFISA SASAAL ABU ZAID NAFISAT SASAAL Chapter 6 Maimakon Hudayya ta mayar da hankali kan abinda ya kaita makaranta sai ta ɓige da saƙe-saƙen yanda zata yiwa Aunty dabarar jin labarin tushen su Abu Zaid a bakinta, don tasan duk wanda zata tambaya a bayan Aunty yake. Har suka tashi Hudayya bata fuskanci komai a darussan da aka koya mu su ba na ranar. Da headache sama-sama Siyaa ta wuni a makaranta har suka tashi bai daina ba. Dalilin haka yasa Abu Zaid da yazo ɗaukarta ya kasa samun sukuni sai ya ke ganin kamar haƙura ne batayi ba, ko ta fuskanci ya ƙara shan wani kafin zuwanshi. Ya na parking ta bar motar da hanzari saboda warin cigarette ɗin da take ji sama-sama a motar wanda take kyautata zaton wani ya ƙara sha kafin zuwanshi ɗaukarta. Kanshi ya kifa kan steering motar yana jin komai na juya mishi, kafin ya ɗago a hankali yana tsuke cikakken girarshi haɗe da shafa Beard ɗin fuskar shi. Kanshi ya yi nodding yana murmushin zancen zucin da yake yi. Bai wahalar da kanshi wajen bin bayanta ba don yasan bazata kulashi ba. Office ya koma ranshi duk ba daɗi. 6:00pm ya dawo gida duk ya faɗa saboda stress da weary. Saɓani irin haka bai saba shiga tsakanin shi da ita ba, domin tana da haƙuri da juriya akan duk wani abu da zai aikata saɓanin ra'ayinta, amma bata taɓa tanka mishi ba sai a wannan karon. A gajiye ya yi wanka ya shirya cikin Polo RL shorts da suka ƙara fito da ƙuruciyarshi. Jiki a sanyaye ya nufi ɗakinta. A hankali yake knocking amma bata buɗe ba har sai da yayi knocking ɗin kusan five minutes sannan yaji ta buɗe ƙofar. "Ina wuni Yaaya?" Ta faɗa haɗe da barin bakin ƙofar. "Siyaaa." Ya furta da muryar da yasa dole taji duk wani haushin shi da takeji ya na bin iska. A gefenta ya zauna kafaɗar su na gogar na juna yace. "Yaushe zaki daina fushi dani?" Ya faɗa yana kallon gefen fuskarta. Waiwayo wa tayi tana kallon cikin idanuwanshi da suka ƙara girma ta cikin medical glasses ɗin dake manne a fuskarshi. "Ba ina fushi bane ba, a'a ina jin ciwon yanda kakeson kashe rayuwar mu ne gaba ɗaya." Ta faɗa still tana kallon idanuwanshi. "Wata rana zan daina Siyaa kinji? ki tayani da addu'a nima ina son dai nawa, yau banga murmushinki ba balle dariyarki. Dan Allah kiyi ko da kaɗan ne na gani kinji?" Bata san sanda murmushin ya ƙwacewa laɓɓanta ba, juya idanuwanta tayi kafin ta runtse su still tana murmushin. "Bari na cire gilashina don na ga wannan murmushin naki da kyau." Ya faɗa yana zame Medical glasses ɗin nashi. "Tayaya zaka ganni dakyau bayan ka cire ƙarfin ganin naka?" "Idan babu shi zuciyata ta fi ganinki dakyau Siyaa, ko da idanuwana sun makance wata rana, to zuciyata bazata daina haska musu ke ba." Ya faɗa da yalwataccen murmushi a kan kyakkyawar fuskar shi. Idanuwanshi da suka rage girma bayan cire medical glasses ɗin take kallo. Yawan Cigarette ɗin da yake sha kullum duk ya sauya kalarsu zuwa jajaye. "Idanuwanka sun daina haske, tafin hannuwanka sun rage haske suma, sannan lips ɗinka suma duk sun disashe, shin kana so ka cire kamanni a fuskarka?" Ta faɗa muryarta na rawa "Zan daina Siyaa wallahi zan daina kinji." Kai ta ɗaga mai kawai tana wiping tears ɗin da ya ɓata mata fuska da bayan hannunta. Miƙewa ta yi yabi bayanta, kitchen suka shiga tare tana aiki yana tayata har suka haɗa dinner mai sauƙi su ka wuce living room ɗin shi. Sai dare sosai Siyaa ta dawo daƙinta zuciyarta har lokacin babu daɗi. Abu Zaid mutum ne mai tsananin rauni ta zahiri a idon jama'a haka ta baɗini a wajen Iyalinshi. Ba shi da taurin zuciya ko kaɗan, abubuwan da ba su da wani tsauri ko tsananin tausayi ne suke saka shi kuka, dan da yawan abokanan shi cutar shi sukeyi su gudu, da wahala mutum ya biyo ta sanadin Abu Zaid bai cuce shi ba. Ɓarawan bacci ne ya sa ce Siyaa saboda tunani da damuwar da take ciki. Fara'a da goge-gogen da sam basu shafeta ba take ta yiwa Aunty, hakan kuwa ba ƙaramin daɗi ya yiwa Aunty ba har take tunanin duk farin cikin fara zuwanta makaranta ne ya janyo hakan. Ƙarfe bakwai da rabi Hudayya ta samu Aunty a ɗakinta. Yanayin yanda ta zauna shiru yasa Aunty tambayar mai yake damunta? Cikin dabara da wayon da ko wani babban ba shi da shi take tambayar Aunty labarin tushen su Abu Zaid. Labarin rayuwar Aunty da na tushen su Abu Zaid abu ɗaya ne wanda kullum da shi take kwana kuma take tashi da shi. Tarihin rayuwar su bazai bayu ba batare da nata tarihin ya shigo ciki ba, sai dai kuma dole Hudayya tasan komai ko don taƙara jajircewa tayi ilimi ta kuma fuskanci Abu Zaid yayi mata nisan, nisan da har abada ba za su dai-daita guri ɗaya ba. WAIWAYE Jami'ar Ahmadu Bello itace sanadiyar abotar Ɗalhatu da Kuma Zayyad ɗan asalin ƙaramar hukumar Giwa mazaunin Chika da ahalinshi. Ɗalhatu kuwa ɗan asalin ƙaramar Hukumar Leren jahar Kaduna ne. Iyayenshi sun jima da rasuwa kuma tun suna raye talakawa ne wannan yasa Ɗalhatu faɗawa neman kuɗi da ilimi har Allah ya bashi sa'ar shiga jami'ar Ahmadu Bello. Zayyad da Zainab ƴan biyu ne ma su tsananin kamanceceniya da juna. Mahaifin su ya jima da rasuwa sai Mahaifiyarsu kawai da suka rayu da ita. Shaƙuwa da yardar dake tsakanin Zayyad da Ɗalhatu ne yasa ya yarje mishi dawowa cikin gidan su da zama. A nan ne kuma Ɗalhatu ya faɗa soyayyar Zainab da idan kika cire tudun ƙirji dana baya da yalwataccen gashin kai babu abinda ya rabata da Zayyad. Su Zayyad mahaifinsu mai kuɗi ne a zamanin shi, haka ko bayan ranshi Zayyad ya ɗora daga kasuwanci da ya tsaya. Mahaifiyar su kuma ma'aikaciyar lafiya da itama ba a haka take zaune ba. Tun mahaifinsu yana da rai take aikin ta. Dalilin rasuwar mahaifiyar su Zayyad ne, sai Zayyad ƴa yanke shawarar aurawa Ɗalhatu Zainab a kan dai ta koma hannun dangin mahaifin su. Zainab macece mai yarda da tsananin tausayi. Rashin cikakken aikin yi ga nauyin iyali yasa Zayyad jan Ɗalhatu Cikin harkar kasuwancin shi dan ya samu abinda zai rufawa kanshi da ilalinshi asiri. Ni kuma kora da ƙyamar mahaifiyata ba musulma ba ce yasa bayan rasuwar mahaifina ɗan asalin ƙauyen Gwarzo danginshi koreta, itama kishiyar mahaifiyata mai ƴaƴa biyu Wato Ramatu da shamsiyya korata tayi saboda kishin mahaifiyata da ta jima da rasuwa tuntuni. Da haka na samu aikatau a gidan Zainab. A shekarar da naje gidan Zainab a lokacin ta haifi ɗanta mai tsananin kama da Ita, suna san shi suna kaunar ɗan nan da suka samu. Ranar suna kuwa yaro yaci sunan mahaifinta wato Ibrahim. Zayyad da kanshi ya yiwa Ibrahim alkunya yana kiran shi da Abu Zaid har sunan ya bishi. Ɗalhatu mutum ne mai ƙyama da nuna ƙoƙon Usul. Tunda ya samu rufin asiri sai ya yiwa kanshi katanga da duk wani ɗan uwan shi, babu ruwan shi dasu, kuma shi mutum ne marowaci saɓanin su Zayyad da Zainab. Abu Zaid na da shekaru uku blood Cancer ya tisa Zainab a gaba kuma dama shi yayi ajalin dukka mahaifan su. Shekarar Abu Zaid huɗu a duniya Allah ya yiwa Zainab mahaifiyarsa rasuwa. Shaƙuwa da ƙaunar da nake nunawa Abu Zaid yasa Zayyad bawa Ɗalhatu shawarar ƴa aureni. Har Gwarzo sukaje neman aurena aka wulaƙanta ƴan uwan mahaifinshi da suka je neman auran, tare da basu tabbacin su basu san wata Salima ba a dangin su. Ƙarshe a nan Zaria aka ɗaura min aure, Zayyad ya zama wakilina. Bansan ina suka samu labarin mijin dana aura mai kuɗi bane sai ga su har cikin gidana. Ɗalhatu yana ganin su yayi musu korar kare yace baya buƙatar ganin su, kuma yace su cire ni a cikin su kamar yadda suka furta tun a baya. Wannan dalilin ya ƙara rura wutar tsanata a ransu. Shekarata ta farko da aure na haifi ƴa mace mai suna Zainab wato takwarar marigayiya Zainab tsohuwar matar mai gidana. Har Zainab ta fara zama ƴar budurwa ban taɓa kaita dangina ba don kullum idan naje gurin su korata sukeyi. Haka dangin Ɗalhatu sam ba sa sona sai iya ƙannenshi mata guda biyu. Har shurewar tsawon shekarun nan Sannan ne Zayyad ya sararawa kasuwanci yazo ya nemi auren ƴar uwar abokin kasuwancinshi mazauna garin Abuja amma ƴan asalin ƙauyen Tofa. Shekarar su ta farko da aure Ziyaada ta haifi makwafin Zayyad. Wato mai kama da Zayyad. Ranar suna yarinya taci sunan kakarta wato Safiyya suna yi mata alkunya da Siyaam. A wannan lokacin ne kuma na tafi ƙauyen Abuja yiwa Ramatu da ita kaɗai take kulani gaisuwar rasuwar Shamsiyya, wacce ta rasa ranta ta dalilin haihuwarki saboda fyaɗen da Shitu yayi mata. Lokacin da tana raye bai musa ba amma bayan ranta sai ya musanta cewa ba shi bane ya yi, dole haka Ramatu ta karɓeki ta tafi dake Abuja. Kamar yanda kamanceceniyar Zayyad da Zainab yake haka na Abu Zaid da Siyaam yake. Kamar su ta ɓaci kana ganin su kasan jini ɗaya ne. Yawan zama a jikin Abu Zaid nacin sai ta kwana ɗaki ɗaya da shi yasa Zayyad yanke shawarar daya tada husuma mai zafi, ƙarshe wannan daliline ya raba auren shi da mahaifiyar Siyaa. Don yayi rantsuwar ɗaura auren Siyaa da Abu Zaid a shekarunta da ba su fi goma ba. A cewar ta asiri Ɗalhatu yake yi mai don ya gaje dukiyar shi da dabara. A rana ɗaya kuwa a ka ɗaura auren Zainab da Siyaa. Bayan wa su shekaru dukiya mai yawa suka tararwa Zayyd kuma har lokacin bai ƙara wani auren ba don Ziyaada ta jima da yin wani auren da wani a wajen ƙasar nan. Siyaa ƴar gata ce a wajen mahaifinta, kama daga wajan kakarta da ke zaune a Tofa, Abu Zaid, Ɗalhatu da kuma ni kaina. Duk wanda yasan Siyaa to sai yasan mahaifinta da mijinta. Soyayyar Siyaa da Abu Zaid soyayya ce ta jini ɗaya wanda bazai rabu ba har abada. Siyaa na aji huɗun secondry shekara ɗaya da rabi baya Allah ya yiwa Zayyd rasuwa sanadiyyar gajeriyar jinya da ya yi." Auntyn ta faɗa da hawaye da majina a fuskarta. Taci gaba da cewa. "Na baki wannan labarin ne don ki cire duk wani shakku ko tunanin Abu Zaid a cikin ranki. Zan kuma roƙeƙi a karon farko Hudayya dan Allah ki cire komai a ranki ki rungumi karatunki, ki bar soyayyar da baki san ma farin shi ba balle ƙarshenshi. Iliminki shine ruwan da zai wanke duk wani ɓakin tabo dake jikinki Hudayya." Aunty ta ƙarasa faɗa cikin kuka maitsanani haɗe da haɗa hannayenta alamar roƙo. Kai Hudayya ta gyaɗa mata ta tashi tabar ɗakin kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki. Tana shiga jikin ta har wani rawa yake saboda jin labarin nan. Kayan kwalliyar dake gaban mudubin ɗakinta tayi watsi da su gaba ɗaya suka yi nasu wajen. Cikin ɗacin rai da mugun zafin zuciya ta furta, "Wallahi sai na cika muradi na." Ta faɗa haɗe da cije haƙwaranta, ba tun yau ake goranta mata rashin asali ba, sai dai batasan asalin tushen zancen ba sai yau ɗin nan. Toh ba fyaɗe ba wallahi ko da son ran mahaifiyarta taje tayi zina ta haife ta, kota yaya ne wallahi sai ta yi rayuwar aure da Abu Zaid...✍️ NAFISA SASAAL [9/26, 5:56 PM] Hajja Ce: ABU ZAID Chapter 7 BY SASAAL Har gari yayi haske sosai Abu Zaid na kan Prayer mat yana tasbihi idanuwanshi a lumshe kamar mai barci. A hankali yaji an buɗe door ɗin living room ɗinshi amma bai motsa ba sai ajiyar zuciyar da ya sauke saboda scent ɗin daya cika lafiyayyan bedroom ɗin shi. Gaba ɗaya sai ya matsu ya ga cute face ɗinta a cikin idanunsa. Cikin sanɗa ta shigo bedroom ɗin da take kyautata zaton yana ciki. "Assalamu alaikum Yaya." Ta faɗa tana kama hannayenshi bayan ta zauna kusa da shi. Gaba ɗaya bayason buɗe red eyes ɗin shi bare ta ganshi saboda gudun ƙorafinta. Idanunsa still a rufe yake amsa mata sallamar da takeyi da cewa. "Amin wa'alaikum salam Wifey, I hope you had a nice night?" Ya faɗa yana matsa soft hand ɗinta. Still idanuwanshi a kulle suke. Matso da cute face ɗinta ta yi right up to his face. "U smell nice." Ya furta a ƙasan moƙoshin shi saboda sassanyar scent ɗin Delina da ke shiga ƙofofin madaidaitan straight nose ɗinshi. "Yaaya mana, please ka buɗe idanuwanka nagani kaji?" Ta faɗa tana matsa hannayen shi da ƙarfi. "Ba ki bani amsa ba Siyaa, ina fatan kinyi barci mai daɗi?" "Saika buɗe ido zan amsa maka." Ta faɗa tana bin duk wani halittar fuskarshi da kallo. "Idan na buɗe zakiyi min faɗa Siyaa." Ya faɗa yana ƙara matse idon nashi. Murmushin da ya tsaya iya kan cute face ɗinta tayi tana jinjina kai. "Sunyi jaa ko? Dan shine iyakacin ƙorafin dazan iya yi maƙa korafi akai Yaaya." Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa. Da sauri ya buɗe su gaba ɗaya yana ƙara kama hannayenta don yasan guduwa zatayi. "When will you s...?" "Karki ce komai Siyaa I swear bansha komai ba." Ya yi saurin tarar numfashin ta. Toshe mai baki tayi tana kwanciya a jikin shi don batason yana yawan yi mata ƙarya. Sumbata mai sanyi yai mata a forehead ɗinta kafin ya zagayeta da hannayenshi. Sai da ta samu nutsuwar zuciyarta sosai sannan ta tashi tana gyara zaman hijjab ɗin kanta. Hanyar fita tayi walking sluggish saboda sauyin da takeji ajikinta. Fararen ƙafafuwanta yabi da kallo kafin ya saki ajiyar zuciya shima yana miƙewa tsaye. Kai tsaye kitchen ta shiga. Roasted Beef Sandwich ɗin da tasan yake so ta yi mishi sai coffee. Sannan ta dafa noddle da Sunnyside up da zata ci. Bedroom ɗinta ta koma tayi wanka ta shirya. A shirye ta sa mesh cikin LP shirt da jeans. Bai yi mata addu'ar daya saba ba balle ƙorafin ɗan noddle ɗin datakeci da sunan Breakfast ta kasa cin ta ba. A ranar ma akan idanun Hudayya suka bar gidan ba tare da su sun lura da ita ba. Tun daga lokacin Hudayya ta sauya har ajinsu Siyaa ta nema, kullum sai taje da sunan gaishe ta duk da ta ɗan girmewa Siyaa ɗin da ƴan watanni. A hankali Hudayya ta fara shiga ran Siyaa har hankalinta ya fara karkata kan mai zai hana Itama Hudayya tayi exam su tafi University tare? Bayan sun koma gida ne ta samu Abu Zaid da zancen duk da Daddyn su taso fara yiwa magana don ita batasan ba shi bane yake biyawa Hudayya kuɗin makarantar ba. "Hudayya? Who is she?" Abu Zaid ya tambaya yana ƙoƙarin tuna ina ya taɓa jin sunan nan. "Yaaya ƴar uwar Aunty fa da muke School ɗaya." "Exactly sai yanzu na tuna." Ya faɗa da murmushin yadda yake takaicin saurin mantuwarshi. "Duk abinda kika yanke shi zanyi Siyaa." Ya faɗa yana kallon kyakkyawar fuskarta. Nan suka sanar da Aunty. Aikuwa Auntyn ba ƙaramin farin cikin yin jarabawar da Hudayya zata zana tayiba tai, saɓanin Hudayya da ita har lokacin burinta Abu Zaid yasan da zamanta a rayuwar duniyar nan, ya kuma nuna kulawarshi a kanta sai dai ina bashi da wannan lokacin. ****** Hakane ta kasance suka fara ƙoƙarin zana jarabawar JAM, Sai dai kuma tun a JAM ɗin Siyaa da Hudayya suka raba hanya saboda Hudayya bata ci jarabawar ba. A kan idanuwan Hudayya Siyaa ta tafi University ita kuma ta tafi College bisa hukuncin da Aunty ta yanke don sam ta lura babu maganar karatu a zuciyar Hudayya, don ko sau ɗaya bata taɓa ganinta tana karatu da sunan zatayi exam ba, sai dai tunani da ta san bai wuce na Abu Zaid ba. A shekarar da Siyaa ta shiga University kyawunta da tsananin kamanceceniyar su da Abu Zaid ya ƙara bayyana. Komai na jikinta ya ƙara fasali da kyawun gani. Sai dai kullum Abu Zaid ya yi ta binta da kallo idan ya rasa ya zaiyi sai ya bar gidan yaje yayi ta bankawa cikinshi hayaƙi. Bai ƙara susucewa ba sai da Hudayya ta saci wayar Siyaa ta ɗauki numbern shi ta tura mishi saƙon cewa Siyaa na zuwa Asibiti kullum wajen wani saurayinta. Tunda ta taɓa rakata sau ɗaya daga ranar take ta bibiyar duk ranar zuwanta. Abu Zaid kuwa baya cikin mutane ma su gaggawa da rashin saurin fahimta, don haka ya bi diddigin komai a nutse har ya gano abinda yake kaita asibiti ta hanyar Likitan da take zuwa gani. Hudayya na ta zuba idon dan ganin gagarumar rigima ta faru tsakanin miji da matar amma sai taji shiru, ƙarshe kasa jurewa tayi sai da ta tambayi Siyaa cewa wai ita kam kwana biyu bata ganin Yaaya yana ina? Siyaa da ba son yin hirar Abu Zaid takeyi ba ko da a cikin ƙawayenta, fuska tayi kamar bata jita ba taƙi bata amsa. Hararar tsana Hudayya ta raka bayanta da shi ganin ta bar mata wajan. Siyaa ta na 200level Alhaji Ɗalhatu ya kasa jurewa ya tunkari Siyaa kai tsaye da suje Asibiti a duba menene matsalar su dan yaji shiru har lokacin babu ciki bayan har wata ƙasar ya tura su hutu don su samu sakewa. Da farko Abu Zaid Alhaji Ɗalhatu yaso tara da zancen amma yasan indai Siyaa bata amince ba, to ba zuwa zai yi ba shima. A wannan ranar da Daddy yai mata magana Siyaa tayi kuka tun Abu Zaid na lallashinta har shima ya fara taya ta yin kukan. "Please Siyaa kiyi min bayani zuciyata bazata jurewa wannan kukan naki ba." Ya faɗa yana kamo fuskarta. Sai da ta haɗiye kukanta tukunna ta buɗe siraran laɓɓanta da sukayi ja tace. "Daddy yace muje Asibiti a duba menene matsalar da yasa ba mu haihu ba har yanzu." Ta faɗa tana kallon idanuwanshi dake bayyana tsakanin raunin dake cikin zuciyarshi. "Yaushe zaki gaya musu gaskiya dan su sa na sawwaƙe miki Siyaa? Ko kina son tarihin mu ya shafe duk ranar da Allah ya ɗauki rayukan mu? Shin yaushe zaki fuskanci abinda nake nuna miki?!!" Ya faɗa da wani irin fushin da batasan shi da shi ba. "Babu rana Yaaya, har yanzu ban karaya ba, kuma ko da kabarni ni bazan iya barin kaba ka tuna alƙawarin mu ABU ZAID, wallahi ko ba na raye ka karya ban yafe maka ba." Ta faɗa da wani irin kuka da ya kwace mata. "Siyaa kina so ki kashe min kanki bayan kinsan bazan jure ba? Ko kina kwana da sha'awa kina tashi da shi kina zuwa ganin likita duk don kiyi survive? Siyaa ko ba da ni ba idan kika haifi yara a wani gidan ina son su saboda suma ƴaƴa na ne, dan Allah karki kashe min

Chapter 3 of 11