miƙawa littafin bayan ya miƙe hannunshi na rawa take cewa.
"Ka yafe min Abu Zaid, ka yafe min dan Allah. Ni ce silar shigarka cikin wannan halin ta hanyar nuna cewa ita ɗin tawa ce." Kalaman da Aunty take ta maimaitawa tana kukan rusatan da Hudayya ta yi. Kai ya jinjina mata yana barin parlorn ba tare da yace uffan ba.
"Banyi nadamar taimakon ki ba don nasan Allah zai yi min sakayya tsakanina dake. Wallahi bansan irin zuciyar Shamsiyya ce a ƙirjinki ba da bazan karɓe ki ba Hudayya. Amma ki riƙe wannan a ranki wata rana zaki tuna cewa na gaya miki. Kijini da kyau Hudayya Abu Zaid bazai taɓa zama abinda kikeso ba, kuma zaki haɗu da musiba mafi munin musiba a cikin rayuwarki. A ranar ne kalamai na za su dawo kanki dan sai kin nadama mara amfani cikin rayuwarki." Daga haka Aunty ta hau sama don haɗa kayanta saboda tasan ita kanta zamanta ya ƙare da Alhaji Ɗalhatu.
Babu zancen Aunty ɗaya da Hudayya ta ɗauka zai zama gaskiya balle har ya dameta. Tunanin ta kawai ina Abu Zaid zaije? Bata sani ba kuma. Haka dai ta fita ta nufi parking lot ta tsaya.
Alhaji Ɗalhatu kuwa yana kallon ɗan shi mafi soyuwa a zuciyar shi ya fito da jakar da yasan ko kwatan kayanshi bai ɗiba ba, slippers ne ma a ƙafarshi ya cire na gayun da ya gansa da farko. Hudayya na biye da shi a baya da Akwatin kayanta itana, don su Baba Ilu tuni sun daɗe da kasafta kuɗin sadakinta sun bar gidan.
Zubewa yayi ƙasa tim kamar dai ranar daya ganta ta fito daga sashen Abu Zaid ɗin. Sai dai wannan karon yana jin jikinshi kamar ba na shi ba. Kamar yafi buguwa akan na ranar.
A can parking lot kuwa, kamar wasu raƙumi da akala haka takebin Abu Zaid da be tanka mata ba har ya tare abun hawa suka hau. Tayi tunanin anan garin Zariya zai ce su zauna ya kama mu su hayar gidan ƴan gayu ta cigaba da karatunta tana kuma rayuwa tare dashi, amma sai taga sun nufi tasha.
Da wahala Abu Zaid ya gifta mutum bai ƙara juyawa ya kalleshi ba a lokacin, saboda duk yanayin da yake ciki Allah ya yi masa tsarin halittar da ba za'a gushe ba wajan kallansa.
Sai dare suka shiga garin Kano har lokacin kamar kurma bai ce mata komai ba. Taufiq abokin da suka taɓa Business tare ne ya ɗauko su daga tasha. Sai a lokacin Hudayya taji sanyi a ranta ganin irin kyawun motar da Taufiq ɗin yazo ɗaukar su da ita, ko banza tasan ba gidan wahala zasu je ba.
Koda suka isa gidan Taufeeq ɗin, ɗakin masu aiki aka kai Hudayya duk da haka bata damu ba tunda tasan tana tare da Abu Zaid ɗin.
Fitowa suka yi daga ɗakin da suka kai Hudayya, Taufeeq ya kaishi ɗakin da zai zauna. Two bedrooms flat mai kyau Taufiq yakai Abu Zaid ɗin. Dan Taufeeq ɗin babban ɗan kasuwa ne, don har Companyn sarrafa citta ne da su, da na sarrafa robobi. Abu Zaid ya taimakamai a lokutan baya kafin kasuwar tasu ta tashi tai sama har ya kai hakan.
Bayan yayi wanka ya kwanta kuka mai sanyi da wani irin danasanin taimakon Hudayya ya lulluɓe shi. Alƙawari yayi kuma bazai karya ba shi na Siyaa ne ita kaɗai. Ba kuma zai ƙarashan cigarette ba tunda yayi mata alƙawari.
"Kin tafi kin barni, farin ciki yayi kaura daga cikin zuciyata, na sani ba zai dawo ba har sai ranar dana ƙara ganinki Siyaa." Ya faɗa da wani irin kuka mai zafi.
Coventry
"Mommy kiyi haƙuri karki kasheni, please karkiyi tunanin zaki iya raba komai ta sauƙi, ki tausaya mana Mommy Abu Zaid zai damu idan bai ganni ba dan Allah." Sune kawai kalaman Siyaa tun bayan ƙwace Mobile ɗinta da mahaifiyarta tayi....
NAFISA SASAAL
[9/26, 5:58 PM] Hajja Ce: ABU ZAID
Page 9
By NAFISAT SASAAL
"Ki saurareni da kyau Siyaa, mahaifin Abu Zaid baya sonki kawai yana amfani dake ne. Ke ni duk bama wannan ba ta yaya zaki cuci rayuwarki ki zauna da mutumin da ba shi da isasshiyar lafiyar da zata sa kiyi rayuwa mai inganci Siyaa? Kiyi tunani sosai kinji ko?" Mommynta ta faɗa da sigar lallashi.
"Mommy ba wannan ne lokacin da ya dace ki rabani da Yaaya Zaid ba. Tunda na dawo daga Tofa, muna tare dashi, Mommy Yaaya Zaid bazai iya koda cin abinci ba bana gurinsa, ki tausaya mishi Mommy ki bani shi koda a waya muyi magana dan Allah Mommy." Ta faɗa da muryar da yasa jikin Mommynta yin sanyi.
"Ki kwanta ki huta anjima zakuyi maganar." Ta faɗa tana barin ɗakin.
Slim face ɗin ta daya ƙara ramewa ta shafa tana jin yanda ƙashi ya fito a both side ɗin cheeks ɗinta, haka kyawawan idanuwanta duk sun zurma sunyi ciki. Ƙwalla ce ta cika idanuwan ta don tasan Abu Zaid zai shiga damuwa sosai sama da ramar nan da tayi.
Da dabara mahaifiyarta tasa Doctor Hilda ƙawarta dake duba Siyaa yi mata allurar barci mai ƙarfi dan gaba ɗaya bacci ne ya kauracewa idanunta. Baccin da Siyaa bata shiryawa yi bane ya ɗauke daukarta ta dolen dole.
Idan ta tashi kuma bata cin abinci, dan haka alƙawarin sai taci abincin Mommy take yi mata tana cewa zata bata waya suyi magana da Zaid sannan Siyaa take janyo shi gabata.
Kallon mamakin yanda takecin abincin Mommynta takeyi tausayin ƴarta da tsanar Ɗalhatu mai girma na ƙara mamaye mata zuciyarta.
Kafin Siyaa tagama ci Mommynta ta suɗaɗe ta bar gidan. Bata dawowa kuma sai yamma liƙis.
Tana dawowa a rakuɓe ta samu Siyaa tayi kuka fuskarta har yt kumbura. Tana ƙoƙarin yi mata bayanin wanke kanta taje kawai sukaji ana knocking.
Da mamaki Mommyn Siyaa taje ta buɗe ƙofar. Mamaki da tsoro ne suka shigeta lokaci ɗaya. Aunty ce sanye da ƙananun kayan daya ɓoye ainihin shekarunta mussamman ga wanda bai santa ba. Fuskarta har lokacin a kumbure ta ke saboda kukan da taci. Hanya ta bata suka shigo ciki tana binta a baya.
Da sauri Siyaa ta rungume Aunty tana tambayar ta ina Abu Zaid ko tare suka zo? Kai ta girgiza tana ɓoye ƙwallarta da take shirin zubo mata. Siyaa na kwance a jikinta suka zauna Mommynta na kallon su. A nutse suka gaisa da Mommy kowanne da abinda yake cikin ransa.
Sai bayan sunyi dinner da Mommy Wanda Siyaa ce kawai taci na kirki suka zauna tattauna dalilin zuwan Auntyn. Auntyn ce ta gyara murya ta shiga cewa.
"Da farko bansan dalilinki na riƙe Siyaa da manufar kalamanki ba Ziyaada, amma ina roƙon gafararki ke da Siyaa a kan abinda na zo dashi, nasan yanada ɗaci da ciwo ga duk wata Uwa tagari da kuma duk wata Mace tagari, amma wani lokacin idan aka dubu yadda Allah ya riga ya shirya mana rayuwa, za'a ga cewa wani abun ba da san ranka yake faruwa ba." Labari ta ba su cikin kukan dayasa ƙwalla cika idanuwan Mummyn Siyaa. A karon farko tayi nadamar cutar da Abu Zaid da sukayi ita da Mahaifinshi saboda san ran su. Gaba girman tsanar Ɗalhat na ƙara mamaye duk wani sashe na zuciyarta. Shi yafara wasan ita kuma ta mayar da martanin daya rusa komai.
Siyaa ba sosai taciga da gane ragowar bayanan Aunty ba, don batama ji wai Abu Zaid yabar gida ba balle takardar sakin dake hannun Aunty. Cikin tashin hankali take cewa.
"Aunty wallahi ƙarya Hudayya takeyi Yaaya baya iya yin komai da mace shi da lafiya na taya zai kusanceta bar yai mata ciki? Aunty ki gayawa Daddy dan Allah karku yi min haka, koni da muke tare dashi baya iya yi min komai, munje asibiti cikin gida da waje amma har nazo garin nan Yaya bashi da lafiyar da zai yi wannan abun." Siyaa ta faɗa da wani irin kuka mai ban tausayi tana ƙanƙame Aunty.
"Kuyi min bayani Ziyaada bangane ba." Aunty ta faɗa tana rungume Siyaa tare da bubbuga bayanta alamun lallashi.
"Salma labarin gajere ne amma yayi silar lalata komai, danasan wannan ranar zata zo da na haƙura na barwa Allah auran nan da akai musu."
"Menene yake faruwa Ziyaada? dan Allah ki yi min bayani kun sake sani a cikin duhu." Aunty ta faɗa a kiɗime zuciyarta cike da zargi kala-kala.
********
Da sassafe Abu Zaid yabar gidan zuwa Companynin su Taufiq.
Hudayya kuwa sai da tayi wanka sannan ta fito ɗan madaidaicin living room ɗin dake tsakiyar ɗakin. Babu wani kayan abinci balle ta dafa don haka ta zauna zaman jiran shi. Tun Hudayya nasa ran dawowarshi har ta cire rai. Kafin yamma yayi duk ta yi yaushi fuskarta har ramar dole ya yi. Tana jin knocking tai saurin zuwa ta buɗe duk a tunaninta Abu Zaid ne. Sai dai mace ta gani da kayan abinci niƙi-niƙi fuskarta a ɗaure kuma kamar dai halittarta ce haka. Babu ɗigon ɗanyen abinci sai kayan amfani wanda da alama wanda zatai amfani dashi ne a lokacin.
A buɗe tabar ƙofar saboda jikinta daya gama mutuwa gaba ɗaya.
Sai daf da sallar magrib ta ji sallamar shi, da sauri ta gyara zamanta ta na marairace idanuwanta duk don ta siye zuciyarshi.
Bai yi magana ba ya ajjiye ma ta leda ɗaya a cikin wanda ya shigo da shi. Kayan jikinshi take bi da kallo zuwa ƙafafuwanshi, ba irin kayan da ya saba gayu da su bane. Slippers ɗin da a baya ko taɓa ganinshi da shi batayi ba ne a ƙafarshi irin dai wanda marasa ƙarfi suke rayuwarsu da shi a tsakar gida ko fita siyo abu kusa da gida. Shine amma Abu Zaid yake iya fita har wani wajen da shi. Wucewa yai bedroom ɗinsa ba tare da ya kula ta ba. Kauraran laɓɓanta ma su duhu sosai ta ciza tana miƙewa da ledan daya bata. Abinci ne mai kyau dai-dai misali har da lemon jarka.
Wajan karfe 11:30pm taji motsin mutum a kitchen ɗin da yafi kusa da nata ɗakin. Da kayan baccin jikinta ta nufi kitchen ɗin tana ƙara zazzago da wuyan rigarta bayan ta cire bra ɗin daya riƙe manyan halittun ƙirjinta.
LV shorts ɗin da yayi mishi kyau sosai yasa yana juye abinci da baya jin zai iya cin na arziƙi a plate. Hannunsa da karfi ya janye ta daga riƙon da tayi masa. Bata damu ba dan tasan dama hakan zata faru. Tace,
"Yaaya don Allah ka yafe min wallahi su Baba Ilu sharri sukeyi min duk don su ƙullawa Aunty sharri." Ta faɗa da sigar yanda Siyaa take yin magana. Shiru yayi bai tanka mata ba yaci gaba da abinda yake yi.
Matsowa tayi daf da bayanshi a hankali kafin ta manna ƙirginta a bayanshi.
"Yaaya please dan Allah kayi haƙuri ka yafe min kaji? ka kuma roƙar min afuwar Siyaa." Ta faɗa still da salon muryar Siyaa.
"Ban san har haka kika mayar da ni sha-sha ba Hudayya, bansan har mace ƙarama mai ƙarancin shekarunki zata iya mayar dani lusarin namiji ba sai a kanki, yanzu kina jin kina da wani abu da zan kalleki da shi ko na soki dan shi? Karki ƙara wahalar da kanki wajen neman yafiyata balle jin furucin bakina don girman butulcinki ya jima da kurmantar da ni." Ya faɗa yana barinta da sakakken baki.
Ƙirjinta da mazan department ɗin su suke hauka akai ta bi da kallo ganin ko kallansu bai yi ba. Wani irin baƙin cikin mai raɗaɗin gaske na taso mata, zafin kalaman shi na ƙara rura wutar ƙiyayyar Siyaa a zuciyarta. Duk da tayi nasarar auransa amma tana ganin kamar ba zata sha wahalarsa.
Sai dai kuma bazata gajiya ba har sai burinta ya cika, tasan da ga ranar daya shigo hannunta har ya haɗa shimfiɗa da ita to tashi taƙare. Dole ya so ta don ita ɗin macece mai ni'imar gaske kamar yanda take yawan ji saurayinta Abba yana faɗa da koɗata duk ranar daya shawo kanta har ya samu tabashi kanta.
A hankali ya nemi waje ya zauna yana ƙoƙarin har zuƙa zuciyarshi shima ya zama mai fushi da zafin kai, amma sai yaji yakasa, maimakon haka sai yaji wani rauni na ƙara shigarshi.
Kuka yasa yana cire gilashin fuskarshi. Wayar da Siyaa ce kaɗai ke kira a kai ya janyo. Sim Card ɗin ciki ya zare ya karkkarya shi sannan ya mayar da wayar inda take. Runtse jajayen idanuwanshi yayi yana jin idan har Siyaa zata iya samun layinshi to sai ta nemi inda yake wanda hakan ke nufin dawo da hannun agogo baya.
Abincin da bai ci ba kenan haka ya kwanta kan sabuwar katifar dake hargitse da hotunan Siyaa na kati da ya gama gani yana cewa.
"Allah ya baki ikon jure rashina Siyaa, kiyi auranki kawai mu samu Ƴaƴa ma su kama da mu. Nasan zaki yi min kara ke da mijinki ku sawa ɗanku sunana ko da bana raye ku tuna dani ko?." Ya tambaya kamar tana kusa da shi. Kuka mai haɗe da dariya yasa yana cigaba da surutan da ba su da tushe balle makama. A haka wani wahalallan bacci ya ɗauke shi.
*****
A lokuta da dama idan mutum ya fiye kwaɗayin tara dukiya da neman suna sai yazama dalilin faɗawar mafi akasarin wasu halaka da dan asani. Wannan burin shi yaja Ɗalhatu kwaɗaituwar haɗa auren Siyaama da ɗan shi. Sanin tunkarar Zayyad kai tsaye da auren Siyaa da Abu Zaid bazai yiwu ta sauƙi ba yasa ya fara kwaɗaita min kawo Siyaa gidanshi. A haka shaƙuwa da manyan dalilin da zai tunkari Zayyad da shi suka haɗu yanda yake so. Duk da haka sai ya haɗa da sa malamai suyi yi mishi sauka da roƙon Allah yasa Zayyad ɗin ya amince mai. Toh idan har ka shiryawa wani mugunta kuma Allah ya ƙaddaroshi a cikin ƙaddararsa to ba makawa sai yafaru. A bakin matar abokin kasuwancin Ɗalhatu nakejin komai. Duk yanda nayi ƙoƙarin nunawa Zayyad manufar Ɗalhatu ƙarfin ƙaddara ta rufe mishi idanuwa abun bai yi ba.
Baƙin cikin hakan ne yasa na tura matar abokin Ɗalhatun tayiwa Abu Zaid asirin da al'aurarshi bazata ƙara tashi ba har abada don kawai na rama abinda Ɗalhat ɗin yayi min kuma na hanashi cikar muradinshi na mallakar jika ta tsatson su Zayyad gaba da baya.."
Kuka mai ƙarfi Siyaa tasa tana ƙanƙame Aunty kafin idanuwanta ya juye gaba ɗaya...✍
[9/26, 5:58 PM] Hajja Ce: ABU ZAID
Page 10
By Nafisat Sasaal
"Why Mommy? Saboda kuɗi kukayi wannan zalunci? i can't take it anymore, I can't live without him." Siyaa ta faɗa tana fashewa da kuka mai ban tausayi.
"Siyaa ki fuskance ni mana, nayi dukka wannan abun ne saboda son da nake yi miki. Ɗalhatu mugu ne irin wanda bakya tunani, tayaya zai kori Abu Zaid bayan da dukiyarshi yake rayuwa kuma ya hanashi ɗaukar komai? kiyi tunani da kyau mana." Kai Siyaa shiga ɗaga mata saboda weak ɗin da jikinta yayi.
He was not strong enough da zaiyi rayuwa shi ɗaya da Hudayya, cutar shi zatayi. Ta ya ya ma zata fara wani rayuwar da babu Abu Zaid a cikinta? Shigowar Aunty ne ya hana Mommyn Siyaa magana wacce ta tashi daga wajan taje ta amsa waya.
"Mai yake faruwa Salma?"
"Nothing serious, matsalar Alhaji ne Sister's ɗin shi suka kirani. He was admitted to the Hospital." Aunty ta faɗa tana ɓoye tashin hankalin da take ciki. Ba don labarin ya taɓa zuciyar Mommyn Siyaa ba tace.
"Uhmm Allah ya ba shi lafiya."
"Ameen." Cewar Aunty jiki babu karfi.
Har lokacin idon Siyaa na kulle tana jin su. Batasan ya zata misalta ko kwatanta girman abinda take ji a ranta ba. Babu kuma mai iya ganewa sai wanda ya tsinci kanshi a irin condition ɗinta. Wani irin tashin hankali take ciki wanda su kansu abin ya basu tsoro. Yadda jikinta ya rikice ne yasa dole suka ɗauke ta zuwa asibiti dan bata taimakon gaggawa.
★Sai da safe aka sallami Siyaa bayan jikinta yayi sauƙi. Lokaci zuwa lokaci sai ta share hawayen da suka ƙi yankewa daga idanuwanta. Tunda ta shige ɗaki bata fito ba har sai Aunty ta shigo yi mata sallama.
A hankali Aunty ta zauna a gefenta suna facing juna sannan tace.
"Siyaa zan wuce Allah Ya ƙara miki juriya ya kuma kawo miki mijin da yafi Abu Zaid zama alkhairi a gareki. Shi kuma Allah ya kareshi a duk inda yake." Ta faɗa cikin wiping ɗin tears dake bin cheeks ɗinta.
"Meyasa zakice haka Aunty? kema kinaso naso wani bayan Yaaya yana raye? Idan nai haka ai naci amanarshi ko?" Ta tambaya kamar ba a cikin hankalinta take ba. Hannayenta Aunty ta kamo da sigar lallashi tace.
"You have to move on Siyaa, ko da Abu Zaid ya dawo zaman ku bazai yiwu ba, kiyi haƙuri kinji? kiyi ta addu'a Allah zai kawo miki mafita."
"Naji Aunty, naji zan daina amma yanzu dai kam ni kawai nasan me nakeji." Ta faɗa cikin shedding tears da yaƙi yanke mata. Ɗan ƙaramin littafin da Aunty ta taho da shi ta ajjiye a gefenta tana miƙewa. Sumbatarta Aunty tayi a forehead haɗe da faɗin.
"Take care darling."
Kai kawai Siyaa tayi nodding don bazata iya magana ba, gani takeyi kamar tafiyar Aunty na nufin bazata ƙara ganin Abu Zaid ba na har abada. Tare da Mommyn Siyaa Aunty sukabar gidan don yi mata rakiya.
Siyaa kam batasan kuka rahama bane sai da take karanta saƙon masoyinta abun ƙaunarta. Screaming ɗin daya amsa dukkan girman gidan tasa lokacin da ta ƙara tabbatar da dagaske Abu Zaid yasaketa. Sakin aure abune mai raɗaɗi da ciwo mussamman irin na Siyaa da bata shirya masa ba.
Tabbas bai yi ƙarya ba don wannan saƙon nashi shi ya zama abin karatunta safe, rana da kuma dare. Kullum cikin kuka da surutan daya fara damun mahaifinyarta take.
*******
As usual da sabon suturun gwanjon daya siyo ya shirya tafiya wajen aikin da Taufiq ya ɗaukeshi a ma'aikatar su, duk da kayan masu sauƙin kuɗi ne bai hana su yi mishi kyau ba.
Tun waccen lokacin baya mata magana gaisuwarta ma daƙyar yake amsawa. Tayi kwalliya da ado mai ɗaukar hankalin duk wani lafiyayyen ɗa namiji, amma Abu Zaid bai taɓa nuna yasan tana yi ba.
Satin su na biyu kenan a sabon gidan su Taufiq da Iyalinshi suka kawo mu su ziyara.
Sosai Hudayya take kallo da kuma sha'awar yanda Taufiq ɗin ke nuna kulawarshi a kan matarshi da ɗan su ɗan shekara biyu.
Ba ƙaramin daɗin zuwan na su taji ba don Taufiq ya yiwa Abu Zaid maganar nema mata Makaranta ta cigaba da karatun ta, kuma ya nuna amincewa shi tunda dama ba wani abun takeyi masa ba bare ya hana.
Kyautar motar bazatan daya kawowa Abu Zaid ne yasa Hudayya yin tsalle zata rungumeshi da sunan murna, ya matsa dasauri ta faɗi ƙasa tim. Kunya da takaici ne ya mamaye zuciyarta duk da Taufiq ɗin da matarshi ba su nuna alamun sun ga abinda ya faru ba.
Godiya sosai suka ƙara yi da Taufiq ɗin kafin suyi sallama. Abu Zaid bai fito ya gayawa Taufiq matsalar shi kai tsaye ba amma ga duk mai hankalin da yasan shi a baya yasan ba ƙaramin abu bane zai kawo namiji irin Abu Zaid yin rayuwa a gida makamancin irin wanda suke ciki don bawani building bane da Abu Zaid ɗin ya saba rayuwa a cikinsa ba.
Yana tafiya kuzarinshi na raguwa, dariyar fuskarshi na ɗaukewa.
Mai zai yi da motar da ba tare da Siyaa zasu hau ba? Baya son gwasale Taufiq be amma ko kaɗan babu ɗigon farin ciki a cikin zuciyar shi dan ya mallaki mota.
Da sauri Hudayya ta rufa mishi baya, tayi sa'ar samunshi a Living room kafin ya shige Bedroom. Da ƙaramar muryar da take kyautata zaton zai ƙara raunana raunanniyar zuciyarshi tace.
"Yayaa don Allah ka yafe min, kaji tausayina don darajar Allah da manzonsa. Na tuba wallahi dan Allah kai haƙuri." Ta faɗa haɗe da zubewa a kan gwiwoyinta tana haɗa hannayenta alamun roƙo.
Bai yi niyyar bata amsa ba amma ya lura ba ƙaramin mahaukaci ko sha-shasha ta mayar da shi ba. Cikin zafin da ke cin zuciyarshi yace.
"Da kinsan girman abinda kika aikata min da bazaki iya kallona ki ce na yafe miki ba. Kin raba zumuncin waɗannan ƴan uwa guda biyun da suka rayu cikin so da ƙauna bayan ƙasa ta lulluɓe idanuwan wasu. Ko da na yafe miki bazan taɓa kallonki ko mu'amalantarki da fuskar da kikeso ba, bazan kuma daina nanata miki girman butulcinki da ya daɗe da kurmantar da ni ba Hudayya. Zaman lafiyarki shi ne ki nisanta kanki da ni, dama ai a haka kikeson ganina ko? Toh kinyi nasara. Amma dole ki barni a yadda kika ganni, saboda kin zaɓi yi min sharri mafi muni a idon duniya." Ya faɗa yana barin living room ɗin saboda girman tsanar ta da yake ji a cikin zuciyar shi.
Bai sauya daga ƙin kulata ba, sai abinda ya ƙara gaba da yin muni dan bayacin duk wani abu daya fito daga hannunta, baya kallon TV tare da ita kullum idan ya dawo daga wajen aiki yana ɗaki sai zuwa masjid ne kaɗai ke fito da shi. Sam baya dariya da kowa sai dai murmushin yaƙen da idan ya kamashi yi dole. Motar da Taufiq ya siya mishi ma bayason hawanta kullum tana compound ɗin gidan a lulluɓe ya gwammace ya hau Taxi ko express yaje duk inda za shi .
Acikin wata biyu Abu Zaid yayi wani irin rama kamar ba shi ba, kamannin Siyaa da yake dashi duk ya fara barin fuskarshi.
Kamar yanda ya alƙawarta tunda Taufeeq ƴa bashi damar komai, wata Private University da bata taɓa zatan zai affording ba ya kaita, sai jikinta yayi sanyi. Mamaki takeyi shi kam wacce irin kyakkyawar zuciya gareshi mai tsananin rauni da tausayi? Sai takejin ina ma bata wannan hanyar ta biyo ba wajen mallakar shi a matsayin mijinta da take expecting yin rayuwa ta har abada dashi ba. Kullum shi zai bata transport amma bazai yi mata magana ba.
*****
SIYAA kuwa da magiya da roƙo take cin abinci shima ɗan kaɗan kamar abincin da yaro ƙarami zai ci. Magana kaɗan takeyi sai kuka, daga Mommynta har mijin Mommyn nata duk sai abun yafara damun su. Gaba ɗaya slim face ɗin ta ya koma duk ƙashi ne ake gani. A baya ita ma'abociyar kallo da danne-danne a waya ce, amma a wannan lokacin duk ta daina yi dan babu wanda yake burgeta, karshe ma kashe su tayi gaba ɗaya.
Shawarar tafara fita da ita wajajen shaƙatawa Mommy Ziyaada suka yanke da Mijinta.
Dakyar ta shirya cikin ƙananun kayan da suka haska farar fatarta. Duk da zuzutata da Mommynta takeyi batayi dariya ba kamar yanda takeyi a baya. Haka suka fita bata wani farin ciki, ji takeyi ma kamar ta saki kuka, tana jin an takurawa zuciyarta.
Guri ne da manyan masu kuɗin kasashe mabanbanta da celebrities suke zuwa hutawa, nan Mommynta ta kaita duk dan ta kawai mata da tunanin da yake neman kassara rayuwar Siyaan.
Tun shigowar wasu dogayen matansa da samun irin tsahon su a cikin miliyoyin mutane kaɗan ne hankalin mutane da ɗan dama ya koma kan su ana ta yi musu video mussamman ga waɗanda suka san su. Gashi ne akan kowannensu mai yawan da sukayi parking ɗinshi. Paul Maher da Zayad Maher shine sunayensa. Ana ta murna ana ihu wasu na ta kiran sunan Paul wato fans ɗin shi. Yayin da wasu suma suke ta kiran Zayad dalilin da yaja hankalin Siyaa kenan harta waiwayo kan su...
NAFISA SASAAL
[10/29, 9:59 PM] Hajja Ce: ABU ZAID
Page 11
BY SASAAL
A kaikace take kallo da tantace halittar tsayin su, abu ne mai wahala kasamu ma su irin wannan tsayin a cikin mutane mafi akasari tafi sanin Basketballers da shi. Dama babu iddah akan Siyaa kasancewar tunda ta auri Abu Zayd bai taɓa kusantarta ba. Tunda ta ɗago Paul yake kallonta rashin damuwarta da su balle har ta ɗauki hoton su kamar yanda ragowar sukeyi ne ya ja ra'ayinshi duk da ƙaramin Camera da ke gefenta. "Who is she?" ya tambayi kanshi yanajin feelings na daban a kanta. Bata ƙara kallon su ba ta cigaba da sipping drinks ɗin dake hannunta duk da ba wani daɗi yake yi mata ba. Har suka zauna hankalinshi yana kanta saɓanin Zayad mai zafin kan da ko kallon mutane bayayi balle ya tantance su wanene suke ɗaukar su da waɗan da basa ɗaukar