Share this page
bazata iya sauka ta gansu ba saboda duk tsaurin idonta mahaifin Abu Zaid tamkar takobi ne mai tsananin kaifi a idanuwanta, da ko ganinshi bata burin ta ƙarayi. Tunanin abunda yafi ƙarfinta da kaf zuri'arta ne ya rinjayi zuciyarta har Aunty ta shigo bata sani ba. "Huda! Tunanin mai kikeyi haka? ina ta sallama shiru." Aunty ta faɗa tana kallonta da farin cikin ganin sauyin da Hudayyan ta samu. "Ohh sannunku da zuwa Aunty banji shigowar ku ba ne." Ta faɗa da sanyi murya tana ƙaƙalo murmushi. "Karki kisa damuwa a ranki fa Huda, baki da matsala da komai yanzu kinji ko?" Aunty ta faɗa ta na dafata haɗe da yi mata murmushinta mai nuna ƙarfafa guiwa. Nodding kanta tayi ƙwalla na taruwa a cikin idanuwanta. "Ina Aunty Zainab da Babyna?" "Zainab ta koma can ƙasar da take aure, amma Huda mai yasa kika yiwa Abu Zaid ƙarya da Gwarzo bayan ke kanki ba taɓa zuwa kikayi da wayonkin ba?" Aunty ta tambayeta tana tsareta da kallo. Kuka ta fashe da shi. "Aunty idan nace daga Abuja na ke bazai yarda da ni ba, kuma nazo Zaria ne tunda naji Mama ( Ramatu) tace anan gidanki yake, kuma nasan bazaki hanani abinci ba idan na ganki, sannan kuma bazaki na dukana kamar Maman ba." Ƙarfin kukanta ne ya ƙaru ta share hawayenta da bayan hannunta sai sauke ajiyar zuciya takeyi. "Kiyi shiru Hudayya komai yanzu ai ya wuce, munyi magana da Abu Zaid yace zai ɗauki nauyin karatunki kinji. In Sha Allah kukan ki ya ƙare tunda kinzo nan. Bari naje gurin su Alhaji ki daina kuka kinji ko?" Aunty ta faɗa haɗe da miƙewa ta tafi. Bayanta Hudayya ta bi da wani irin kallo irin na ƙasan idanuwa tana wani irin taune lips ɗinta. Siyayyan kaya designer ma su kyau da tsada Abu Zaid yabawa Aunty ta yiwa Hudayya da duk wani abubuwa na buƙatar ƴa mace. Wannan dalilin ya ƙara haɓɓaka abinda Hudayya takeji a zuciyarta, a ganinta idan har bayajin wani abu a kanta bazai taɓa ɓata waɗannan manyan kuɗaɗen wajen yi mata siyayya mai yawa haka ba. Hudayya tana ta zuba idanuwan shigowar Abu Zaid sashen Aunty, amma har tsahon kwanaki biyu shiru bataga gilmawarsa ba, kuma bata da damar yin Breakfast, lunch, ko dinner tare da su, sai dai kullum tayi na ta a ɗaki ita kaɗai. Daga nan sai Hudayya ta koma leƙen window duk lokacin da ta tashi daga barci ko Allah zai sa ta hangoshi amma ba ta taɓa samun ganinshi ba. Sai wata rana da damuwa ya hanata runtsawa ta dinga leƙa window duk bayan wasu mintuna tana so taga ko zata hangoshi. Ƙarfe bakwai da rabi Allah ya bata sa'ar ganin nashi kuwa, cikin ƙananun kayan da suka amshi fatarshi da ginannan jikinshi ya yi adonshi mai matukar birgewa, gibgegen Saint Laurent jacket ne asaman ƙananun kayan jikinshi saboda sanyin safiyar ranar da yafi na kullum. Window ta zuge gaba ɗaya tana ƙare mai kallo da iya ganinta amma har lokacin bataga wani abu ɗaya na su daya dace da juna ba, amma ita dukka ba wannan ne matsalarta ba ko shi ya kawo iya ado kuma yafi kowa kyau da kuɗi a duniya sai ta cika muraɗinta a kanshi wannan alƙawari ne ta yiwa kanta. A kan idanuwanta Abu Zaid ya bar gidan gaba ɗaya tana jin kamar ta ƙwala mai kira. Tunani takeyi mai yasa tun ranar daya kawota gidan su bai ƙara neman ganinta ko da fuskarta ba ne? Ta tambayi kanta bayan ta zube a kan gado ta na dafe haɓarta. Kafaɗunta ta ɗaga alamun ko a jikinta. Daga wannan ranar ne kuma sai Hudayya ta mayar da tashin ta a irin wannan lokacin kamar ibada har Alarm ta sa, sau biyu Aunty na kamata amma batasan mai take kallo ba. Har shuɗewar sati ɗaya basu haɗu ido da ido dashi ba. Wata ranar Friday wanda yayi dai-dai da sauran kwana biyu ayi resuming school ɗin da Abu Zaid ya ɗauki nauyin biya mata. Gaba ɗaya Hudayya ta kasa jurewa da sanɗa ta sauko down stairs ɗin ta fita daga sashen gaba ɗaya duk da tsoron da ke mamaye a cikin zuciyarta. Ma'aikatan gidan ne ke ta aikace-aikacen su babu wanda yabi ta kan ta. Turare mai daɗin ƙamshi daya sauya iskar wajen ne yaketa busowa yana bugar mata cikin hancinta, kamar kullum da ƙananun kayan da sukafi yi mishi kyau yayi ado. Da sauri ta ƙarasa kusa da shi tana gaishe shi. Bai ganeta ba don haka ya amsa mata kamar yanda yake amsawa kowa. Alamar hakan da ta gani ne yasa ta cewa. "Yaya nice Hudayya." Ta faɗa tana binshi a baya. A tunaninta zai tsaya ko ya nuna wani alamu na farin cikin ganinta, amma sai taga saɓanin haka. Maimakon ya bawa ganin na ta muhimmanci sai ya ɓige da amsa kiran dake shigowa wayarshi. Har ya shiga mota yabar harabar gidan bai katse kiran ba bare ta sa ran zai kulata sai waving hannu da yayi mata lokacin da ya rufe murfin motar. Wani abu ta haɗiye mai tsananin ɗaci a wuyarta tana shanye ƙwallar dake shirin taruwa a cikin idanuwanta. Aunty dake kallon komai ta ɗakin Hudayya idanuwanta ta runtse, tsoron abinda Hudayya ke neman bijirowa da shi na shigarta. Fitowa ƙaramin living room ɗinta ta yi tana jiran shigowarta. Kamar yanda ta fita da sanɗa haka ta koma cikin sanɗa, amma wannan karon sai ta tarar da Aunty tsaye kan ƙafafuwanta ranta a ɓace. "Mai yasa kike bibiyar Abu Zaid duk safiya Hudayya? banaso na ƙara ganin haka kina jina?" Kai Hudayya ta ɗaga mata baƙin cikinta na nunkuwa a cikin zuciyarta. Daga haka ta juya tabar Hudayya da bin bayanta da Kallo. Jajayen iduwanta ta rintse tana kama kanta da dukka hannayenta. Da jan ƙafa ta nufi ɗakin ta tana jin kamar ta saki ihu. A wannan ranar Hudayya batayi ko da Breakfast ba kuma duk Aunty na sane da ita amma bata kulata ba sai da dare yayi. Ta kai minti biyar tana kallon Hudayya da ke barcin ƙarya. Ta buɗe baki tace da ita, "Banason ki bani kunya Hudayya, idan zuciyarki na kitsa miki don wata manufa Abu Zaid ya taimakeki to ki cirewa zuciyarki wannan tunanin don haka halinshi yake ga duk wani mai neman taimakonsa. Hudayya baki da banbanci da duk wani ma'aikacin da kika gani a cikin gidan nan, don a kan haka Abu Zaid ya taimakeki kamar yanda kika roƙa tun a farkon haɗuwarku, shin a wane dalili zai sa ki hana cikinki abinci? ko kina son yin kokawa da abinda yafi ƙarfinki ne Hudayya? Abu Zaid bazai taɓa amsarki amatsayin da kikeson zuwar mishi ba, saboda ke kanki idan kikaga matar da take amatsayin mallakinshi zaki gasgata zancena, kuma har abada Alhaji bazai sauya ra'ayinshi a kanki ba." A zabure Hudayya ta miƙe tana dafe kanta da ke sara ma ta. Kafin ta fara magana a hankali. "Aunty ba fa abinda kike tunanin ba ne, kawai inason mu ƙara gaisawa ne, abinci kuma naƙi ci ne saboda ciwon kan dake damuna." Hudayya ta faɗa tana danne duk wani gobarar da ke cin zuciyarta. Zama Aunty ta yi tana sassauta muryarta tana cewa. "Hudayya ki mayar da hankali kan karatunki kinji? karki ɓata gobenki wajen son abinda bazaki taɓa samu ba Hudayya." Ba ta ƙara cewa Aunty komai ba har ta bar ɗakin. Ta jima tana kallon waje ɗaya kamin ta lumshe idanuwanta ƙwallar da ta cika a idanunta su na biyowa saman ƙuncinta, tana kuma sawa ranta wannan ne kukanta na farko kuma na ƙarshe a kan abinda take ji dangane da Abu Zaid. A jikin window ta wuni har Abu Zaid ya dawo a kan idanuwanta. Don babu nasihar Aunty ɗaya da ya shige ta sai na furucin Abu Zaid yana da mata, to idan yana da ita tana ina? Kuma mai yasa yake rayuwa a gidan iyayenshi tunda ya na da aure? Waɗannan tambayoyin da ta yiwa kanta ne yaƙara mata ƙarfin gwiwar kawai Aunty na son rabata ne da cikar muradinta ne. Ranar Sunday daya rage saura kwana ɗaya a koma makaranta a bakin window ta zauna har wajan 11am ta wuce amma Abu Zaid bai fito ba. Motar da take baƙuwa a idon Hudayya ce a danno cikin harabar gidan... [9/21, 3:51 PM] Novel: ABU ZAID By Nafisa Sasaal Chapter 4 Sosai ta buɗe dukka idanuwanta ta na jiran wanda zai fito daga baƙuwar motar zuciyarta na wani irin bugun daya sata miƙewa daga kan kujeran da take zaune, har ƙanƙance idanuwanta takeyi saboda ta samu ganin abinda takeso da kyau. Matashiya ce kyakkyawar gaske wanda duk da nisan tazarar da ke tsakanin idanuwan Hudayya da inda take bai hanata ganin tsananin kamanceceniyar da matashiyar keyi da Abu Zaid ba. Haka kawai taji tana son sanin wacece ita. Kwalin chips ɗin da take ci ta jefar a kan gado ta nufi ɗakin Aunty da sassarfa, ba tare da tuna kashe din ta a kan bibiyar rayuwar Abu Zaid ba ta riƙe handle ɗin tana knocking. Har lokacin Aunty bata farka ba tana ta baccin gajiyar hidimar breakfast ɗin da ya zama wajibi a kanta duk safiya, don Mijinta baya cin abincin masu aiki sai na nata ko na SIYAA. Gashi da tsarfar son abinci kala-kala musamman na gargajiya. Bugun Hudayya ne ya tashi Aunty da ga baccin gajiyar da bai gama sakinta ba, ta buɗe ma ta ƙofar tana bin ta da kallo. "Lafiya Hudayya?" Aunty ta tambaya tana kallon Hudayyan da kamar ba a cikin nutsuwarta take ba. Gaishe da ita ta fara yi tana sosa ƙeyarta kafin tace. "Dama Aunty baƙuwa na ga kunyi ne shi ne nace bari na sanar dake, Aunty dama Yaaya na da ƙanwa ne? na ga suna kama." Ta faɗa still tana sosa ƙeyarta. Numfashi Aunty ta sauke haushin Hudayya na rashin son tsayawa a matsayinta yana kamata. Sai da ta gama ƙare mata kallon takaicin matacciyar zuciyarta sannan tace. "Hudayya sau nawa kikeson na jamiki kunne kan cire idanuwanki a kan al'amuran gidan nan eh? Idan bazaki daina leƙe-leƙen nan ba gaskiya zamu samu babban matsala da ke, ta shi ki fitar min daga ɗaki." Aunty ta faɗa ranta a ɗan ɓace. Da sanyin jiki Hudayya ta bar ɗakin, maimakon ta koma ɗakinta sai ta zauna a Living room ɗin Aunty ko Allah zai shigo da baƙuwar gaishe da Aunty daganan ita sai ta tambayeta da kanta don bazata iya haƙurewa zuciyarta ba batare da tasan wacece wannan wacce tazo ba. Kai tsaye ɓangaren da yake mallakinta da Abu Zaid ɓakuwar da Hudayya ta gani ta nufa. Doguwa ce sosai amma kallo ɗaya zakayi mata ka hango yarintarta. Tafi minti biyar tana knocking kafin ya buɗe mata fuskar shi a ɗaure saboda baya buƙatar ganin kowa. Wani irin rungumar da ke nuna tsananin ƙewarta da yayi, yai mata yana shaƙar ƙamshin turaren da suke amfani da shi tare. Dariyar nishaɗi ta sa bayan sun zube a kan kujera. "Siyaa ƙauyen Tofa duk ya mayar min dake ƴar ƙauye, dubi duk kinyi duhu." Ya faɗa don ya tsokaneta. "Yaaya! Uhm uhmm! duhu fa kace? Ni da Kaaka tace nama yi fari tace nayi kyau. To ni dai kai kayi duhu ka rame bani ba." Ta faɗa don dagaske ɗin ya rame amma bai yi duhun ba. "Na ɗauka bazaki dawo ba don naga sam baki yi missing ɗina ba." Tana karya wuya gefe tace, "Tayaya zanƙi dawowa bayan komai nawa yana nan?" Da sauri yace. "Kamar me da me?" Abu Zaid ya faɗa ya na kallon fuskarta mai tsananin kamanceceniya da ta shi fuskar. "Kamar Aunty, Daddy da kuma Mijina." Ta faɗa tana ɓoye fuskarta a tafukan hannayenta. "Allah?! Ashe kin yarda ni ɗin mijinki ne ban sani ba?" Abu Zaid ya faɗa da sigar wasa. Dasauri ta tashi zata dugu yace. "Karki gudu Siyaa, come nd make me something to eat I'm starving." Ya faɗa da ɗan ɗaga murya yanda zata ji shi. "Ba guduwa zanyi ba ai Bedroom zanje na dawo." Ta faɗa dai-dai lokacin da ta fita daga living room ɗin gaba ɗaya. Ƙofar ɗakinta dake kallon na shi ƙofar tasa key ta buɗe. Komai na ƙaramin Parlon pink ne hakama wadataccen Bedroom ɗinta shima komai pink aka ƙawata shi dashi ko'ina a gyare tsaf. Wanka ta farayi da ruwa mai zafi sosai sannan ta kimtsa cikin Varley Tracksuit mai taushi da kauri. Brown Veil ta yane kwataccen sumar kanta da shi wanda ya ƙara fito da kyawun fuskarta. Kitchen ɗin dake tsakanin ƙofofin su ta shiga, a gurguje ta dafa mishi noodle da sunny side up, sai coffee saboda ta na son shiga wajen Daddy da Aunty. Da sallama ta murɗa handle ɗin kafin ta fara tafiya cikin sanɗa. Har lokacin yana kwance hannunshi dafe da kanshi. "Siyaa." Ya faɗa da murmushi yana miƙewa zaune. Turo siraran laɓɓanta ta yi alamun bataji daɗin ganewar da yai mata ba. Maimakon ta kawo gefen shi kamar yanda tayi niyya sai ta wuce dining still tana turo baki. Tana shirin juyowa taji mutum a bayanta, ihu ta saki don taji tsoro sosai. Ƙaramin dariya ya saki yana shafa ƙasumbarshi haɗe da kashe mata ido ɗaya alamun ya mata 1-0. Tana zaune a kujerar dake opposite da na shi har ya gama ci. Yana goge bakinshi ya furta kalmar da duk duniya shine kalmar da yafi ƙona mata zuciya. "Allah ya kawo Miji nagari ƴammata na." Ya faɗa yana ƙoƙarin jarumtar haɗiye ƙwallar dake ƙoƙarin cin galaba a kanshi. Kamar kullum ba tace mai komai ba tayi hanyar fita. "Siy.." Bata jira ya ƙarasa kiranta ba tai saurin tarar shi da cewa. "Zanje gaishe dasu Daddy ne." Ta tari numfashin shi itama tana ƙoƙarin haɗiye nata kukan. "Ki jirani kinji?" "Okay." Kawai tace tana komawa da baya ta zauna kan kujera. Yana shiga Bedroom ta fashe da wani irin kuka mai sanyi. Jin alamun fitowar shi yasa ta faɗa wash room ɗin dake parlon. Yana zuwa itama ta fito suka fita daga sashin nasu tare. Bakin Alhaji Ɗalhatu kamar zai yage saboda dariya, duk girman ɓacin ran da yake ciki idan yaga Siyama da Abu Zaid a tare sai farin ciki ya maye gurbin wannan ɓacin ran. Suna tare dashi suna ta hira yana jin daɗi suka fara ƙoƙarin tashi. Ɗakyar ya bar su suka tafi gaishe da Aunty da sunan za su dawo idan sun gaida ita. Har izuwa wannan lokacin kuma Hudayya na kwance a living room ɗin Aunty kamar mai barci. Ta kuma yi sa'ar har lokacin Aunty bata fito ba. Tana ji ana knocking ta miƙe da sauri ta nufi ƙofar wanda yayi dai-dai da fitowar Aunty cikin adonta mai birgewa. "Wa nake gani kamar Abu Zaid da Siyama Zaid?" Aunty ta faɗa da sigar tsokanar da ta saba yi mu su. Da sauri Siyaa ta saki hannun Abu Zaid ta rungume Aunty da dariyar ta tana murna. Har suka zauna Aunty ba ta daina tsokanar su ba. A iya maganganun Aunty kaɗai Hudayya ta ɗan ɗauki hasken wacece Siyama (Siyaa). "Aunty baƙuwa kikayi?" Siyaa ta faɗa tana kallon Hudayya da murmushin yaƙe ke kwance a kan fuskarta. "Eh sunanta Hudayya ƴar ƙanwata ce." "Hudayya ga matar Abu Zaid nan, kuma ƙanwar shi." Aunty ta faɗa tana kallon Hudayya. Kamar sukar ƙarfe haka taji maganar Aunty a zuciyarta, banda zuciyarta kafaffece da babu abinda zai hanata sakin kuka mai ƙarfi. Ƙara gaishe da su tayi ta na mamakin Abu Zaid da har lokacin bai nuna ya santa ba. To ai dagasken bai sanki ba Hudayya tunda a ranar daya taimakeki ko cikakken kamannin ki bai sani ba ya ɗamkaƙi a hannun Yayar mahaifiyarka, taimako ne dama ya haɗa ku, kuma ya yi miki. Amma fa lokaci bai ƙure miki ba kina da damar zana masa sunanki a cikin zuciyarshi wanda har abada bai isa ya manta ba. To amma taimakon da yayi min fa bai kamata na saka mai da sharri ba ko? To ai kuwa saiki zauna ciwon zuciya ya kashe ki. Hudayya nayin waɗannan shawarwarin ne da gurɓatacciyar zuciyarta mai tsananin son kanta. Koda da sakan ɗaya ne takasa ɗauke idanuwanta daga kallon Siyaa da Abu Zaid, dai-dai da yatsun ƙafarsu dake kusa da na juna iri ɗaya ne, haka siraran laɓɓansu baƙi da sirkin ja suma iri ɗaya ne. Kanta mara cikkakken gashi ta shafa lokacin da ganinta yakai kan kwantaccen gashin dake gaban goshin Siyaa. Yanayin maganar Siyaa mai haɗe da murmushi da ɗan zare ido yafi komai tsayawa Hudayya a rai, ga shi ta lura Siyaa macece mai tsananin kunya don bata hirar minti ɗaya bata rufe fuskarta ba. Gaba ɗaya sai zuciyar Hudayya ya fara saƙa mata ya ya zata gusar da wannan murmushin na Siyaa zuwa kuka mai tsananin raɗaɗi da ciwo? Dole akwai hanya kuma sai ta nemo. Kiraye-kirayen sallar azahar ne ya tashi su Abu Zaid zuwa sashen su. Da wani irin kallo mai ma'anoni da yawa Hudayya ta bi bayan su, kafin ta miƙe zuwa na ta ɗakinta.... [9/23, 1:18 PM] Novel: ABU ZAID By Nafisat Aliyu Sasaal Page 5 A wannan dare sam Hudayya ba ta samu nutsuwar yin baccin arziƙi ba, kyakkyawar fuskar Siyaa, murmushinta da kunyarta su suka maƙalewa idanuwa da zuciyar Hudayya, zumu ɗin son zuwanta makaranta duk sai ya kau a cikin ranta. Kamar yanda Hudayya bata runtsa ba haka itama Siyaa bata runtsa ba, sai dai matsalarta dana Hudayya sun sha ban-ban duk da dai sunyi tarayya ne akan abu ɗaya. Duk lokacin da ta yiwa mijinta hidimar girki, haɗa ruwan wanka da sauransu sai yayi mata addu'ar da sai ya hanata bacci a wannan rana. Shin yaushe ne mafarkinta zai zama gaske? Bata jin akwai wani sila da zuciyarta zai zaɓi rabuwa da Abu Zaid duk tsanani duk wuya. Yaushe zai daina tuna mata abinda tajimay da sani? Kwantacciya kuma cikakkiyar sumar kanta dake ƙunshe cikin hula ta birkita, tsabar kukan da takeyi jikinta har rawa yakeyi. Kamar daga sama taji ana knocking. Da sauri ta goge fuskarta ta shiga Bathroom ta ƙara wankewa da ruwa, ƙaramin hijab ta ɗora akan Pyjamas ɗin jikinta. Hannuwanshi ya harɗe a lafiyayyen chest ɗin shi yana kallonta da rinannun idanuwanshi da tsabar shan cigarette ɗin da yake sha ne ya kaɗasu. "Zo." Ya faɗa yana mata alama da hannu. Jiki a sanyaye taƙara matsawa kusa da shi. Har lokacin kallonta yake yi ta cikin farin tabaran dake maƙale a jajayen idanuwanshi, cikin tsananin tausayi da sonta mara gushewa aranshi har abada yake ƙare mata kallo. Su na shaƙar ƙamshin juna duk da na shi ƙamshin ya surke da warin cigarette ɗin da yasha. Bayan ta zo daf da shi sai ya mayar da ita abun kallo da iya ganinshi ya na kuma tantance damuwar dake kwance akan fuskarta mai tsananin kamanceceniya da tashi fuskar kafin ya furta. "Yaushe zaki fahimci kalamaina har su daina damunki Siyaa? Ko da kin amince da yi min alƙawari a irin wannan lokacin wata rana zaki ƙalubalanceni. Na san bazaki jure ba nan gaba." Ya faɗa ƙwalla na taruwa a cikin jajayen idanuwanshi. Kamar ba dare ba haka Siyaa ta buɗe muryarta cike da raɗaɗin wutar dake cin zuciyarta tace. "Yaushe zaka daina furta min irin waɗannan munanan kalaman ne? Ashe a kwai wani sauyi da zai sa kayi tunanin mallakawa wani namiji ni kai ka rabu dani? yaushe zaka daina shan abinda zai ƙarasa nakasa lafiyarka duk da alƙawarin dainawa da kayi min? Bazan gujeka ba, kuma bazan sauyawa soyayyarka daga cikin zuciyata ba har ƙarshen numfashina, sai dai idan kaine ka sauya komai da kanka." Ta ƙarasa faɗa kuka mai raɗaɗi da ciwo na ƙwace mata. "Siyaa." Ya faɗa shima yana fashewa da kukan zafin da yake ji a ransa. Maimakon ta tsaya ta saurareshi sai ta koma ɗaki haɗe da bugo ƙofar da ƙarfi ta murza key. A jikin ƙofar ta jingina ita da shi duk suna jin yanda sautin kukan kowannen su ke fita. Kafin kuma tabar jikin ƙofar da sauri. Ya saba yi mata kuka da alƙawarin ya daina shan abinda yake sha tun wa su shekarun baya, amma har yanzu bai daina ɗin ba, shin da wanne zasuji? Tabbacin tabar wajen ƙofar ne yasa Abu Zaid komawa nashi ɗakin ya na cire tabaran fuskarshi haɗe da goge hawayen daya cika mai fuska. Da kuɗi da mace tagari ne kaɗai farin cikin rayuwa, tabbas da yafi kowa farin ciki a cikin duniyar nan, amma dole sai da cikakkiyar lafiya komai zai tabbata. Sai yaji ya matsu gari ya waye ya ƙara ganin fuskarta da kuma addu'ar Allah yasa ta haƙura. ★Da sassafe Hudayya ta shirya cikin uniform ɗin da suka haska ta haɗe ta fito da kyawunta dai-dai misali, amma ita a yanda takejin kanta sai take ganin kamar tafi kowa kyau a cikin duniyar nan. A gurguje ta fito harabar gidan ta kuma yi sa'ar samun Abu Zaid yana jingine da motarshi yana bankawa cikinshi hayaƙin da Siyaar tashi ta tsana. Ba ƙaramin kyau yayi mata ba cikin off white shirt da jeans. Tayi tunanin da ta matsa kusa dashi zai ji nauyinta ya ɓoye abinda yake sha amma sai taga sama-sama ya amsa mata, sai tayi tunanin ganeta ne baiyi ba sai da taji yace ta matsa wajen motar Drivern da zai kaita Makaranta. Jiki a saɓule ta koma ta tsaya duk da haka a saitin da zata dinga hango shi ta tsaya. Kallo take ƙare mai sosai, duk da sanyin da ake yi jikinshi babu rigar sanyi, maimakon takalmin gayun da ya saba ado da shi wannan karon slippers ne a fararen ƙafafuwarshi da suka yi fururu saboda rashin mai. Gaba ɗaya ma kamar ba'a nutse yake ba a yadda take ganin shi. Da zafin nama ta ga ya yarda da abinda yake sha ya sa kafa ya mitsitsike, sannan yayi sauri ya ciro turare da ruwa ya kuskure bakin shi ya fesa turare ta ko ina ƙamshin shi har inda take tsaye, sannan ya dai-daita tsayuwar shi kamar wanda yaga tahowar uban gidan shi. Inda Abu Zaid yake kallo da dukkanin nutsuwarshi Hudayya ta bi da kallo. Irin Uniform ɗinta ne a jikin Siyaa sai dai tsadar yadin da tsananin kyan da yayi wa Siyaa sai ya tashi kamar ba iri ɗaya ba. Jiya ba a sarariya ta ga Siyaa ba, sai ganinta na yanzu, da kuma abinda Abu Zaid yayi duk don kar Siyaa tayi fushi sai taji ya gusar da duk wani nutsuwa ta Hudayya. Tsanar Siyaa mai girma ta mamaye zuciyarta har duhu-duhu take gani. Siyama kuwa rashin baccin da bata samu bane ya haddasa mata wani irin ciwo kai, sai tafiyarta ya sauya salo kamar mai rangwaɗa. Bata lura da tsayuwar Hudayya ba balle ta lura da irin kallon da takebinta da shi. Kafin ya zagayo ya buɗe mata ta buɗe da kanta ta zauna tana runtse idanuwanta saboda warin cigarette ɗin da yake hawa kanta, tsabar ɓacin rai hannunta har rawa yake yi zuciyarta na zafi. Shin yaushe mijinta zai sauya ya dawo yanda take buri? Kamar marar gaskiya haka ya shigo motar yana marairace kyakkyawar fuskar shi. "Good morning Yaaya." Ta furta muryarta na rawar tana jin tsoron amsa gaisuwarta da zai yi saboda warin dazai ƙara buso mata. Bata san yaushe zai daina shan abinda ta tsana ɗin nan ba. Maimakon ya amsa gaisuwarta sai ya fara bata haƙuri. "Ki yi haƙuri Siyaa Allah daga yau na daina sha kwata-kwata kinji. I promise you." "A gida ko?" Ta ƙarasa mishi da kuka. Shiru yayi yana ɗage tabaran shi haɗe da ɗauke ƙwallar daya tararwa na shi idon shima. Magana zai ƙara yi ta tari numfashin shi ta hanyar toshe bakinta da hancinta da tafin hannunta. Da sauri ta fita daga motar tayi ta kwara amai, ɗan abinda ta cusawa cikinta duk ya fice. Sai da tayi amai kamar abubuwan cikinta zasu fita sannan ta tsaya. Bayan ya bata ruwa ta wanke bakinta sai yayi sauri ya nufi sashen su kamar zai kifa. Har lokacin Siyaa na tsugunne dafe da kanta tana jin yana juya mata. Wani irin baƙin ciki ne ya mamaye zuciyar Hudayya wanda yasa tsayuwar gurin ma gagararta, dole itama ƙasa ta tsugunna tana jiran ganin abinda ya je yi ciki. Bathroom ya faɗa kai tsaye ya watsa ruwa a gurguje ya sake yin wani brush ɗin da sanya wa su kayan. Tsaf ya fito yana zura takalminshi mai kyau turaren daya fesa har yawa

Chapter 2 of 11