ragowar kuɗin da ke cikin Account ɗinsa sukayi kuɗin mota dasu, shatar Motar suka ɗauka saboda warin da ƙafarsa take yi ba kowa zai iya zama tare da shi ba sai mai karfin imani.
Taufiq kuwa ya na ganin kiran Malamin da Abu Zaid yake wajensa amma yaƙi ɗauka saboda yasan ba zai wuce matsalar Abu Zaid ɗin ba, shi kuma baya son dawowarsa a lokacin.
Da sassafe ya shirya zai tafi aiki dan ya samu ya dinga karyar sunan aiki ya mishi yawa a office.
Ko tashi daga aiki beyi ba ya fito daga office ya nufi hanyar gidan Abu Zaid, ya na kaiwa gidan tun a parlor suka fara shashancinsu shida Hudayya, anan suka ƙare bidirin su kafin barcin nishaɗi ya kwashe su.
Su Abu Zaid da misalin ƙarfe biyar suka shigo garin Kano. Har compound ɗin gidan Deeni da ya taimaka ya taho da Abu Zaid ya ce Driver ya kawo su, bayan ya sauka ya kalli Drivern da Deeni cikin taushin harshe da azabar dayake ji yace
"Allah ya biya ku da mafificin alkhairinsa ya faranta muku kamar yanda kuka yi min. Na gode na gode sosai." Hawayen da keson zubowa Deeni yai sauri ya share da gaggawa , sannan shi da Drivern suka amsa da.
"Amin." Deeni ne ya taimaka mai har bakin ƙofa sannan ya juya bayan sun ƙara yi mai sallama. Baya tunanin Hudayya tana gida saboda ranar makaranta ne, don haka ya zaro mukullan dake gefen aljihun jakarsa ya zura jikin ƙofar ya buɗe.
Hudayya tana jikin Taufiq babu kayan arziƙi sai wata ƴar guntuwar riga da take jikinta, barcin su sukeyi hankali kwance tamkar a gidan auran su.
A hankali ya ɗingisa ya ƙarasa ciki yana cije lebe ya zauna akan one seater yana juya mu su baya don bayason kallon su a karo na biyu. Baiji haushi ko kishi ba sai na rainin hankali da rashin imanin da Taufiq ya nuna mai saboda zai ci amanarsa ya zaɓi barin shi cikin azabar ciwo.
Warin da ke shiga cikin hancin kowannen su ne ya farkar da su daga baccin, dukkan su ihun daya amsa gidan suka saki suna ƙanƙame juna kamar zasu shige cikin junan su. Cikin rawar murya Abu Zaid yace;
"Tsoron me kukeji bayan bakuji na Ubangijin ku ba? Taufiq mai zakayi da mace marar darajar da ta siyar da darajarta don kawai ta ƙulla sharri? bayan kanada Zinariyar macen auren da ka biya sadaki ka aura da daraja?"
Shiru Taufiq ya yi kamar ruwa ya cinyesa.
Hudayya da tasan maganganun Abu Zaid a buɗe suke gareta, ba ƙaramin ciwo sukayi mata ba, domin dagaske ɗin kanta tabayar aka haɗa mata hotunan da take turawa mahaifin Abu Zaid, da yake akwai ruɗu da rashin haƙuri a halayyar Alhaji Ɗalhatu ga kuma tabbacin daya samu a na fitowa daga ɗakin Abu Zaid ɗin, da kuma shaida wajen Nazeer sai ya yarda.
Taufiq gaba ɗaya kunya da muzantar da bai san akwai irin shi bane ya kamasa, da rarrafe ya ƙarasa kusa da Abu Zaid yana ba shi haƙuri. Abu Zaid a take ya shaida mai idan yana son Hudayya ya shirya aurenta don shi ya daɗe da sakinta tun ranar da aka ce an aura masa ita. Ya zaɓi yin shiru ne saboda ba ya son sanar da ita taje ta kuma yi masa wani sharrin da bazai iya wanke kansa ba. Kai Taufiq ya girgiza alamun bazai iya aurenta ba saboda Iyayensa bazasu lamunce mai ba.
Hudayya najin haka kuka mai ƙarfi ta fasa tana shigewa ɗakinta da gudu.
A daren ranar Taufiq yakai Abu Zaid asibiti, da hanzari ya ƙara dawowa gidan saboda gangar da sheɗan yake bugamai a kan Hudayya kamar ana janshi haka yake jinsa akan ta.
Hudayya bayan fitarsu Asibiti kuwa taci kuka idanuwanta duk sun kumbura, tana cikin haɗa kayanta Taufiq ya sameta da taushin murya yace.
"Hudayya ina zaki je?" Da kaushin murya Hudayya ta ce;
"Gwarzo zan tafi don bazan zauna yakashe ni da warin ƙafarsa ba, tukunna ma menene ya dawo da kai tunda ka ce bazaka iya aure na ba eh?" Wani irin fargaba ne ya ziyarci zuciyar Taufiq tayaya zai bar garaɓasar dayake kwasa ya wuce shi? Da ya barta gara ko aurenta na wani lokaci ne yayi daga baya ya sake ta shima. Ɗan gyaran murya ya yi kafin ya ce.
"Haba Hudayya ki daure ki zauna, In Sha Allahu zuwa next three months zamuyi aure kuma ai yanke ƙafar tashi za'a yi. Don haka dan Allah ki cigaba da lallaɓawa kinji?" Fasa saka kayanta tayi a jaka ta tsaya tana kallon shi. Kusa da shi ta ƙara matsowa tana fashewa da kukan makirci kafin ta ce;
"Dagaske Taufiq zaka aure ni, bayan da bakin naji kace bazaka iya aure na ba?" Ido Taufiq ya runtse sannan ya ce;
"Hudayya ina jin tsoron iyayena da dangina ba lallai su amince ba, amma In Sha Allahu zan lallaɓa su zasu amince tunda bana san rabuwa dake." Rungumesa tayi da tsananin farin ciki ta na dariya.
A wannan dare a gidan suka kwana ya bar Abu Zaid shi kaɗai a Asibiti bayan ya yiwa matarsa ƙaryar a Asibiti zai kwana tare da Abu Zaid.
Taufiq shi kanshi bayajin daɗin abubuwan da yake aikatawa amma rabon ƙaddara da shaiɗan da yake bugamai ganga yasa ya kasa yaƙar zuciyarshi
★
Abu Zaid kuwa washe gari barci mai daɗi yakeyi bayan an yanke ƙafarsa, irin barcin da rabon da yayi irinsa har ya manta.
Sai dab da azahar ya farka, lokacin da ya farka ya tabbatar da dagaske bashi da ƙafa ɗaya a jikinsa, hannu ya ɗaga cikin jarumta yana yiwa Allah godiya da raƙon neman mafita. Yana cikin addu'a yakasa jurewa ya fashe da kuka. Sai da yayi kukan da ya ƙara sauya halittar fuskarsa saboda kumburin da ya yi sannan ya yi shiru.
A kwanakin da suka biyo bayan jinyarsa a Asibiti sau ɗaya Hudayya tazo asibitin dubashi. Matar Taufiq da Taufiq ɗin da wasu abokanan aikinsa ne suke ta zarya har zuwa ranar da aka sallamesa.
Tun da aka sallamosa ya dawo gida, sannu ne kawai ya ke haɗasa da Hudayya, ko fitowa parlon bata son yi kullum tana ɗaki acewarta har lokacin Abu Zaid wari yake yi, tana jin warinsa a cikin hancinta.
Duk yasan manufarta amma bai damu ba saboda yasan zata aikata fiye da haka, dole sai ka na da Imani kake zama mai tausayi ita kuma tayi hannu riga da Imani balle kuma yasa rai zataji tausayin shi. Ko abincin gidan bataci sai ta ce kayan abincin ma wari suke yi.
Bai taɓa ganin mugun ɗan Adam a rayuwarsa ba irin Hudayya, mutane sun sha cin amanarsa da salo daban-daban saboda saurin yardarsa da tausayinsa amma ba'a taɓa zaluntarsa kwatankwacin wanda Hudayya tayi ba.
Suna cikin wannan yanayin ne batare da sanin kowa na Taufiq ba, Taufeeq ɗin yaje ya nemi Iyayen bogi suka tafi Gwarzo nema masa auren Hadayya. Hudayya tun kafin zuwan Iyayen Taufiq ɗin dama ta tattara ta tafi Gwarzo. Murya ciki-ciki tayiwa Abu Zaid sallama shi kuma ya yi mata fatan alkhairi.
A gidan su Baba Ilu ake gudanar da taron da Taufiq ya saki kuɗi Hudayya ta yi bushasha ita da danginta. Babu wanda ya damu da bincikar gaskiyar abinda ya faru da aurenta na farko da kuma gaskiyar inda ta samo Taufiq balle suyi bincike akansa.
Ranar juma'a da ya kama ranar ɗaurin aure su Baba Ilu sai washe baki sukeyi, saboda ganin uban kuɗin da Iyaye biyun Taufiq suka kawo a matsayin sadaki.
Cikin iyayi da salo kala-kala Hudayya take haɗa kayanta. Ƴan matan gidan su suna kallonta suna jin dama sune sukayi sa'ar da tayi. Babu Mama Ramatu ƙanwar Mahaifiyarta kuma mariƙiyarta a shekarun baya, ba ita su kaɗai suke kiɗan su suke rawar su.
***
A ɓangaren Mama Ramatun kuwa dalilin rashin zuwanta bikin Hudayya shine zuwanta gidan Zainab, kamar yadda Zainab ɗin ta kwatanta mata ranar da suka haɗu a kasuwa.
Bayan Mama Ramatu ta huta ta samu keɓancewa da ƴar uwarta Aunty da har lokacin take kan jinya sai ta fara zubo labarai ba tare da la'akari da halin da Aunty take ciki ba, labarin sabon auren da Hudayya zatayi ta fara bata kafin ta ɗora da cewa. Wai Hudayya ta gayawa su Baba Ilu cewar Abu Zaid yasaketa bayannan ya tattara kayansa ya gudu, shine ta haɗu da Taufiq ya taimaka mata.
Tun kafin ta ƙarasa jikin Aunty ya fara ɗan yin rawa, amma daɗin labari yasa bata ankara ba, bayan ta ɗisa aya a labarin nata sai taga Aunty ta sansanƙame idanuwanta sun juye, ihun kiran sunan Zainab Mama Ramatu ta dinga yi. Da kuka Zainab ta mayar da mahaifiyarta Asibiti.
Bayan an bawa Aunty gado Zainab ta fito harabar Asibitin inda Ramatu take zaryar tashin hankalin da take ci. Kashedi Zainab ta yi mata na karta ƙara zuwa inda suke dama tazo ne don ta ƙarasa mata Uwa? banda haka tayaya zata bawa matar da take halin ciwo irin wannan labarin da tasan zai dame ta? Mama Ramatu bataji haushin Zainab ba don da gaskiyarta itama baƙin cikin abin ne ya isheta shi yasa ta fito dashi.
Cikin Asibiti Zainab ta koma ta bar Mama Ramatu a tsaye kanta a ƙasa. Jiki a sanyaye ta juya ta koma gida tana yiwa ƴar uwarta addu'ar samun sauƙi. Baƙin cikin wannan ne ya hanata halartar bikin Hudayya.
A can Gwarzo...
Bayan an ɗaura aure Iyayen bogin Taufiq sun komo gida suka barsa a can shi kaɗai tunda dama bai gayyaci abokansa ko ɗaya ba. Hotuna suka yi ta ɗauka da dangin Hudayya da ita kanta, bayan sun gama ɗauka aka kai Taufiq ɗaya daga cikin ɗakunan ƴaƴan Baba Ilu maza ya huta ya ci abinci.
Hudayya ɗakin da aka kai Taufiq kafin tafiyarsa ta shiga tun da bata da mafaɗi, ta na cika kamar zata fashe tayi sallama, a tsume take da magungunan mata na sihiri kala-kala duk don ta samu abinda takeso. Cikin rashin aji da burin cikar muradinta ta ƙara bawa Taufiq kanta tunda dama sun daɗe ba su koma ruwa ba. Cikin iyayin da take tunanin ta riga ta gama ta gama da Taufiq a wannan lokacin tace.
"Ni fa ba zan tare ba gaskiya sai ka kori Abu Zaid daga aiki don bana son alaƙar komai a tsakaninku, idan kuma har ba haka ba to na haƙura da auren." Ta ƙarasa faɗa cikin raɗaɗin kalaman Abu Zaid da ya ce ita mace ce mara daraja. Matar Taufiq kuma Zinariyar Mai daraja, bazata taɓa yafe masa wannan cin zarafin da ya yi ma ta ba.
Taufiq gumin da ya tsatsafo masa a goshi ya sharce baisan wani irin girman laifi Abu Zaid ya yiwa Hudayya ba amma🤔.....✍🏻
Arewabooks@sasaal74ABU
[11/2, 12:59 PM] Hajja Ce: ABU ZAID
BY
NAFISA ALIYU SASAAL
15
Amma yasan yanda zai ɓullowa lamarin duk da yasan ba abu bane mai sauƙi ya cire mutum mai muhimmanci a rayuwarsa kamar Abu Zaid ba, to amma ba shi da zaɓi tunda Hudayya ta kafe. Ita kuma Hudayya tana ganin kamar har lokacin Taufiq yana kokwanton korar Abu Zaid daga aikin da ya bashi, sai ta miƙe tana girgiza jikinta haɗe cewa;
"Ka yi yadda na ce idan ba haka ba wallahi bazan bika ba Taufiq, a gabanka ya zage ni ya kirani da mace marar daraja dan kawai na biye maka kuma kayi shiru, sannan yanzu ya cigaba da zama a cikin rayuwarmu yanacin arzikin mu? wallahi bazan yarda ba dole sai ka rabu dashi." Ta ƙarasa faɗa tana fashewa da kukan makircin daya gama bin jiki da jininta.
Numfashi Taufiq ya furzar yana murza tafukan hannayensa waje ɗaya, ya ɗan ɗauki lokaci sannan ya ce
"Ya isa Hudayya In Sha Allah da kaina zan kai mishi takardar sallamarshi idan yaso gobe sai ki tare, hakan ya yi miki?" Da kai tayi masa alamar yayi tana ɓoye fuskarta.
Bayan barin Taufiq daga gidansu Baba Ilu, tun kafin ya isa gida yake saƙawa yana kwancewa akan lamarin Zaid. Dole bazai sallami Abu Zaid gaba ɗaya ba, lokaci kawai zai bashi da sunan sallama da zarar ya gama siɗe Hudayya zai mayar da shi bakin aikinsa ita kuma ya sake ta dan ba zai zauna da ita ba, yana da matarsa mai rufa masa asiri.
Kafin Taufiq ya shiga gida sai da ya biya ya yiwa matarsa siyayyar kuɗi ma su nauyin da bai taɓa yiwa Hudayya ba, saboda yana ganin matarshi ƴar gata ce tun bai aureta ba take da kima da darajar da zai iya mallaka mata komai. Ba kamar Hudayya ba da kuɗi kaɗan suke ruɗawa ta dinga zumuɗi akan su ba. Shi kam duk bama wannan ba ji yakeyi kamar asara ne ya kashe mata irin wannan kuɗin tunda ba daga gidan arziƙi ta fito ba. Yana zuwa gida ya samu matarsa ta ci kukanta, siyayyar hannunsa ya ajjiye ya fara zubo mata daɗin baki da ƙarairayi kala-kala, daƙyar ya samu ta haƙura.
A ɓangaren Abu Zaid kuwa. Washe garin ɗaurin Auren Hudayya a Gwarzo da zazzaɓi ya tashi sama-sama. Da rashin kuzari yake shirya kanshi cikin shiga mai sauƙi. Yana cikin saka shirt yaji kamar ana ƙwanƙwasa ƙofa. Kamar yadda yayi tunani Taufiq ne a tsaye fuskarshi babu fara'a ya harɗe hannunsa a ƙirji. Gaishesa Abu Zaid ya yi da fara'a kwance a saman fuskar sa tamkar komai bai faru ba. Taufiq a daƙile ya amsa gaisuwar Abu Zaid, duk da shi kanshi a cikin zuciyarsa yanajin babu ɗaɗi, amma ba shi da zaɓi sama da zaɓin Hudayya a wannan gaɓar. Kamar baƙo haka ya shigo Parlorn Abu Zaid dake gyare fes, ƙamshi mai daɗi na tashi. Cikin dakiya yafara magana;
"Ehm dafarko dai zance karka tambayeni dalili saboda ni kaina bansani ba, amma zaka dakata da zuwa aiki har sai sanda na nemeka. Kuma dan Allah banason bada haƙurinka Abu Zaid iya wanda nayi ma ka ma ya isa."
Abu Zaid a shekaru bai taɓa Aboki sa'ansa ba dukkan sun girme mai a shekaru har Nazeer, ko aure banda Siyaa ƴar uwarsa ce da sai yace yayi yarinta da aure a matsayinsa na mazaunin birni wanda ya taso cikin gata. Amma arziƙin daya gada ne ya kaishi matsayin yin abota da su. Duk da wannan tazarar shekarun dake tsakanin su sai yake ganin kamar Taufiq bai kyauta masa ba ya kalli cikin idonsa kai tsaye yace ya koresa daga aiki a wannan yanayin da yake ciki na rashin kafa. Ya lura ƙarfi da yaji mutane so sukeyi sai sun mayar da shi mugu mara imani, dan haka yake jin zuciyarsa na san komawa. Cikin taushin harshen da ya haɗe da rawar murya Abu Zaid yace;
"Bansan girman laifina ba Taufiq, amma na roƙeƙa karka koreni kabani lokaci tukunna saboda bani da wanda zai bani abinci, sannan ni gurgu ne yanzu marar ƙafa ɗaya. Dan Allah kaji tausayina kaji ƙaina nasan kayi ƙoƙari amma dan Allah ka ƙara bani lokaci zan nemi sana'a wacce zan riƙe kai na dan Allah."
Taufiq ba ƙaramin karaya zuciyarsa tayi ba amma da ya tuno da Hudayya da banzar da yake kwasa sai yaji bazai iya mayar da shi aikin ba. Cikin ko inkula da ya tsaya a iya harshensa yace;
"Duk wanda nayi maka a baya bai isheka ba eh? Kai ba zaka tashi ka yi gwagwarmaya ka nemi naka ba dole sai ka ci a ƙarƙashin wani? Ka tashi ka nemi aiki Ibrahim amma ba a ƙarƙashina ba, nayi iya yadda zan iya." Abu Zaid cikin kuka mai tsananin da yake ganin komai na shirin juya mai baya a lokaci ɗaya yace
"Taufiq ka dubi maraicina da nakasa ta, tayaya zan nemi wani aikin su ɗaukeni da ƙafa ɗaya? Dan Allah ka taimaka min dan Allah idan laifi nayi maka ka yafe min." Da zafin murya Taufiq ya ce;
"Babu ruwana Abu Zaid ka je can kayi rayuwarka na gaya ma." Yana ƙarasa faɗa ya ajiye masa envelope ɗin sallamarshi da cash ɗin 100k. Taufiq yana tafiya Abu Zaid yana binsa a baya yana ba shi haƙuri har compound ɗin gidan amma yaƙi sauraronsa.
Abu Zaid parlornsa ya dawo yana wani irin kuka har lokacin tunanin nahaifinsa ko neman su Aunty bai taɓa zuwa ransa ba. A cikin abinda bai kai shekaru uku ba Ubangiji ya sauya rayuwarsa daga nishaɗi da kwanciyar hankali zuwa tsanani da tashin hankali.
Hannayenshi ya ɗaga ya yiwa Allah godiya tare da roƙonsa neman mafita. Ya sani a rayuwar duk wani shahararren mutumin da yayi nasara akwai wani ɓoyayyen labari mai tsanani, zai jure kuma zaiyi gwagwarmayar da Taufiq yayi masa gori akai. Amma tayaya? kuka ya ƙara fashewa da shi don har lokacin zuciyarshi mai rauni ce.
"Allah Ka bani mafita Allah, Kayi riƙo da hannayena ka fitar dani." Abu Zaid yayi ta maimaitawa da sunayen Allah har barci mai nutsuwa ya ɗauke sa.
****
Taufiq kan iyayen bogin da ya bawa kuɗi ne suka ɗauko masa Hudayya daga Gwarzo tare da danginta da suketa ƙus-ƙus ɗin da Taufiq yasan asalinta da bazai aure ta ba, ba su san cin amana da cin amana bane suka haɗu.
Ƙaryar tafiya Taufiq ya yiwa Iyalinsa da danginsa kafin ya tafi gidan Amarya ƙafarshi na rawa.
****
A ɓangaren su Zainab da Aunty kuwa. Kwanan Aunty biyu a Asibiti Allah ya ɗauki ranta. A wannan rana Zainab ta ga tashin hankalin da bata taɓa gani ba. Mahaifiyar Siyaa Zainab ta fara kira amma ƙiri-ƙiri ta nuna mata bata jinta, su ma ɓangaren dangin Mahaifinta data kirasu babu wanda ya nuna alamun jimamin babban rashin datayi balle su zo mata gaisuwa.
Daga ita sai ƙawayenta da danginsu, duk da suma ba don Allah suke raɓarta ba sai don dukiyarta. Abokannan aikinta maza da na kasuwancinta ne suka yi mata karar zaman makokin yini ɗaya.
Zainab tayi kuka irin wanda baki bazai iya furtawa ba. Sai rayuwarta ta rage daga ita sai ƴaƴanta da mahaifinta da sam danginsa basa bari ma ta gansa sai ankai ruwa rana. Faɗan da suke yi duk lokacin da taje kan hanata ganinsa ne yasa bata zuwa da ƴaƴanta.
A ɓangaren Siya
Lokaci da Zainab ta kira Mommyn Siyaa su na Asibiti za'a yiwa Siyaa aiki. Cikin muryar karayar da Siyaa ta farayi da rayuwa tace.
"Mommy naji kamar Aunty Zainab ce ta kiraki tana kuka kuma kince bakya jinta." Da fargabar halin da Siyaa zata iya shiga idan taji Aunty ce ta rasu Mommynta tace.
"A'a Aunty ta rasu, kawai banason ɗaga wayan kowa ne, amma idan mun koma gida zan kirata da kaina." Siyaa taji tashin hankali sosai musamman da itama take ta ganin kamar mutuwar zatayi.
Muhammad mijinta tun zuwan sa Asibitin da Siya take fuskarsa ta canza, bayan sanar da shi shekarun Siya, bai taɓa sanin Siyaa ko shekara 19 bata kai ba sai ranar, amma Mommynta ta takura mata sai ta aurensa, tayaya zata haifar masa yaro mai lafiya? Ohh ashe shi yasa Mommynta take nacin kaita Asibiti awo da kanta? Haka ya karaci zamansa ya gaji ya tafi. Da ƙunci ya tafi gidan Zayad.
Zayad da kallonsa na rainin hankali yake bin Muhammad bayan ya gama sauraron sa, sai ya ɗan ja fasali sannan ya ce.
"Idan ta haihu ta baka babynka ka saketa idan ba haka ba wanna muguwar Uwartata ta son kuɗinta sai yasa ta kasheka da ƴartata gaba ɗaya, dama kai ne ka dage sai ka aure ta na rasa me ka gani, saboda na lura kuɗi ne kawai a gaban uwarta."
Muhammad da nazari sosai yake jujuya maganar Zayad bayajin akwai ƙarya a ciki don yasha kai mata ƙarar ta lallashi Siyaa su zauna lafiya amma sai tayi mata faɗa har sai Siyaa ta daina kulasa. Ya ma rantse indai wani matsala ya samu ɗanshi sai yayi Shari'a da Mommynta.
Asibiti kuwa a daren da aka ciro jaririn Siyaa bai fi minti arba'in ba ya rasu tamkar uban ya san mutuwar zai yi.
Muhammad a zabure ya miƙe ya zauna bayan ya gama waya da likitan da ya ciro jaririn Siya, idonsa da hawaye yake shirin biyowa ya shafa yana miƙewa don zuwa Asibitin.
Tunda Muhammad ya leƙo Asibitin sau ɗaya bai ƙara ba sai Mahaifinsu dake zaryar zuwa duba Siyan. Shima Zayad tunda suka zo Asibitin suka ɗauki gawar jaririn bai ƙara dawowa ba. Mommyn Siya da damuwa ta bar Asibitin zuwa gida.
Nenne ta kira a waya cikin damuwa, bayan ta gama koro mata bayanin ƙorafin da Mijin Siyaa ya yi na tayi ƙanƙanta da aurensa balle ɗaukar cikinsa. Nenne ta sa dariya tace.
"Toh Ziyaada kefa kika ƙulla kayanki, banda haka yarinya na auren ɗan Uwanta ke da mahaifinsa son duniya yasa kukayi abinda kukayi toh ai saiki rungumi haƙuri ko ki ƙara sasanta su kamar yadda kika saba." Da rawar muryar baƙin cikin da Mommyn Siya take ji a ranta ta ce;
"Nenne wani irin magana ne wannan? ba don son zuciya na haɗa Siyaama da Muhammad aure ba, kuma ki daina haɗani da Ɗalhatu banda son zuciyarsa guda nawa Siyaa da shi kansa Abu Zaid ɗin suke amma yake tura su ƙasa-ƙasa neman maganin haihuwa? ba don duk ya kanainaye dukiyarsu ba ne? ai Ina Sha Allahu Ɗalhatu bai ga komai ba, yanzu zai fara gani."
Nenne kashe wayar tayi domin batasan zuciyar wa Ziyaada ta ɗauko ba na kafiya da riƙo ba.
Muhammad kuwa yaso ya haƙura da Siya ya saketa amma Mahaifinsa ya ce yabari ya yanke shawara bayan ya bincika menene ainihin gaskiyar halin Mommyn Siyaan da suke zargi.
****
A ɓangaren Abu Zaid kam. Bayan sati uku da korarsa daga wajen aiki da Taufiq ya yi, kuɗin hayar gidan da yake ciki ya ƙare, baiyi shawara da kowa ba ya nemi masu siyan motoci suka suyi motar da Taufiq ya siya mai. Bayan kuɗin sun shigo hannunsa ya sa a bincika masa gidan haya mai sauƙin kuɗi da shagon yin sana'a. Yana samu kuwa ya koma yaci gaba da rayuwar sa, bai bari rashin ƙafar ya zame masa nakasa a zuciyarsa ba. Kayan provision ya cika a madaidaicin shagon.
Da farko Abu Zaid yanata ciniki kuma zai ci yasha sau uku a rana, amma daga baya sai mutanen Unguwar suka fara amfanin da tausayinsa da rauninsa wajen cin bashin kayan provision ɗinsa kuma suƙi biyan sa. Tun yana daurewa har sai da suka fara kaishi ƙasa, a hankali-a hankali komai yayita ƙarewa ba kuɗin siyan sabo don da zarar sun zo sunyi magiya musamman matan dake yin kamar suna cikin walahar rayuwa sai ya ba su. A hankali yafara fuskartar yaudararsa sukeyi idan suna da kuɗi wani shagon suke tafiya daban suyi siyayyarsu.
Sai daga baya Abu Zaid yake samun labarin ashe har suna mutanen Unguwar suka sawa shagon nasa, idan zasu ci bashi sai su ce zasu je shagon Ibrahim Gurgu mai Rahusa. Bayan wani Lokaci komai na shagon Abu Zaid yaƙare abinci ci ya fara gagararsa wannan dalilin ya fara bin kamfani-kamfani neman aiki maimakon su ɗaukesa, sai foreigners ɗin da suke giftawa a manyan motoci suna ba shi sadaka kamar ragowar mabarata.
Da farko bai fuskanta ba sai daga baya yagane dalilin rashin ƙafarsa ɗaya ne yasa suke mai haka, duk lokacin da suka miƙo mai sadaka ya kai hannu zai karɓa sai yaji kunya da wani irin zafin zuciya na shigarsa,
"Ya zama mabaraci kenan? ko dai gaskiyar Taufiq da yace bazai iya yin gwagwarmaya ya nemi nasa ba sai dai yaci a ƙarƙashin wa su tunda ga shi har yana karɓar sadaka da sunan mabaraci?" Abu Zaid ya faɗa yana sharce hawayensa
★
Washe gari duk da zafin zazzaɓin dake jikinshi haka ya fito yana tafiya zuwa inda ya saba zuwa. Ya yi kansa alƙawarin bazai karɓi sadaka ba aiki yakeso su ɗaukesa, bazai gajiya ba. Wasa-wasa sai abincin ci yafara gagarar Abu Zaid saboda daina karɓar sadakar da ya yi, ga shi kuma sunƙi ɗaukarsa aikin da yake ganin shine mafitarsa.
Wani iri rama mai fitar da ƙasusuwan dukka sassan jikin Mlmutum Abu Zaid ɗin ya yi sai manyan idanuwanshi da suka zama marasa kyan gani saboda jan da sukayi na rashin abinci da wahalar rayuwa ga shi bashi da kuɗin sabonta gilashinsa, shi yasa gani ma ba sosai yake yi ba, sai dai kuma baya jin zai karaya ko da zai makance gaba ɗaya.
Wani sabon Company ya ƙara komawa ya tsaya bayan sun gaisa da Securities sannan ya koro