Share this page
su. A hankali ya furta. "Love at first sight." Yana shafa tarin sumar dake kanshi. Saitin kunnen Mommynta dake zaune a gefenta ta kai bakinta tace. "I'm tired Mommy ina buƙatar hutu." Kama hannunta tayi alamun ta miƙe don batason wani abu dazai ɓata walwawalar da take ciki yanzu. Paul na ganin sun miƙe shima ya miƙe. A bakin Mota ya samu Mommy tana ƙoƙarin shiga bayan Siyaa ta shiga ta zauna, dukka guards ɗin shi na bayanshi har lokacin kuma wasu basu daina ɗaukarshi a hoto ba. Da British accent ɗin daya kama mishi harshe dakyau yace "Excuse me Ma'am." Da wani irin farin ciki Mommyn Siyaa ta karɓeshi bakinta kamar zai ƙara faɗi saboda dariya duk da ƙoƙarin kame kanta da takeyi. Card ya miƙa mata ba tare da dogon magana ba ya juya saboda yawan mutane da suka fara zagaye su suna ɗaukar su hotuna. Fuskarshi ya shafa yana jin wata nutsuwa na shigar shi dan har ya zauna murmushi bai ɗaukewa fuskarshi ba. Kallon Mummynta da ta shigo da farinciki takeyi kafin a hankali ta furta "Who is he?" Da wani irin ƙwarin gwiwa mai surke da farin cikin da take ciki Mom tace. "Siyaa! The greatest Basketballer Brother ya bani Card ɗin shi, can you imagine? Ohhh my God, Allah yasa yace sonki yakeyi Siyaa da nafi kowa farin ciki in dai zai musulunta." Kamar saukar hammer haka taji saukar zancen Mahaifiyarta ta a cikin kunnanta, bata ƙara magana ko tankawa surutan Mommyn na ta ban saboda yanayin zuciyarta da ya canza, a ranta take mitar ba ma shi kanshi Basketballer ba a'a his Brother shine take wannan murnar, anya Mommynta tasan girman Soyayyar Abu Zaid a ranta kuwa? A haka suka koma gida ba wanda ya sake yin maganar saurayin. Momyn Siyaa kam saboda ta kame kanta da mutuncin ƴarta yasa bata kirashi a ranar ba sai after two days. Paul bai huta da bawa Zayad mai zafin kan tsiya labarin Siyaa ba har sai da yabawa zancenta muhimmanci, ga shi har lokacin Mommyn Siyaa bata kira ba. Da mamaki Zayad yake kallon Paul da ko zancen budurwa bayaso sai dai idan sha'awarshi ta dameshi ya nemi na rage zafi, kuma asanin dayayi mishi ba mutum bane mai son Musulunci don dalilin bin addinin Mahaifiyarsu kenan duk da bata raye, may be tunda ya haukace a kan Soyayyar musulma ya musulunta nan gaba. Daƙyar yayi controlling kanshi lokacin da Mommyn Siyaa takira ta kwatanta masa kanta, kuma batare dogon magana ba ya roƙi alfarmar zuwa gidanta idan ba damuwa. Mommy cikin aminci ta yarje masa. Dinner mai rai da lafiya Mommyn Siyaa suka shirya masa ita da Maigidanta. Lokacin da ya iso gidan ba ƙaramin cika unguwar tasu tayi ba. Yana shiga suka nuna masa gurin zama ya zauna. Ƙamshin shi kaɗai ya isa ya shaida maka how wealthy he is. Bata buƙaci fitowar Siyaa ba don batason ta kunya ta su a agaban shahararren baƙon na su. ********* Hudayya kuwa ba ta daina gwada sa'ar ta ba nayin ado da kwalliya da tsaftace ko'ina kullum ba, amma babu alamun zatayi nasara sai komai da yake ƙara dawowa baya. Da sallama ta shigo a gajiyenta, with surprise take kallon shi bayan ya amsa sallamarta don ba lokacin dawowa daga aiki bane. Cikin ɗari-ɗari ta zauna a gefenshi saitin ƙafarshi daya ɗan miƙe. Cikin salo da yanga tace. "Barka da yamma Yayaa." Bata yi tunanin samun amsar shi ba as usual, amma sai taji ya amsa mata ba tare da ya kalli gefenta ba. Da ƙwarin gwiwar amsa matan dayayi tace "Yayaa wani abu na damunka ne?" Tana maganar tana kuma mai hannunta kan ƙafafuwanshi dake kusa da ita. Da zafin muryar da bata sanshi da shi ba taji ya ce. "Get your filthy hands off me." Da sauri ta cire hannunta tana miƙewa ta tashi daga gurin zuwa bedroom ɗinta cikin sanyin jiki. Bayanta yabi da kallo ƙwalla na cika idanuwanshi. Mai yasa ta zaɓi yi mishi irin wannan budulcin bayan halaccin da yayi mata? Idanuwansa ya runtse ciwon da ya fara ji a babban ɗan yatsan kafarsa kwanaki biyu da suka wuce na ƙaruwa da yi masa zafi da zugi. A ɓangaren Hudayya kuwa bata sake fitowa ba har sai da ya tafi masallaci sallar magriba. ********* A ɓangaren Siya kuwa daɗi ne yasa Mummynta rungume mijinta bayan gama tattaunawarsu da Paul ya bar gidan. Ta na jin farin cikin abinda Paul ya zo mu su da shi a cikin zuciyarta, domin yayi alƙawarin musulunta kamar yanda suka buƙata kafin su bashi auren Siya. A hankali ta nemi waje ta zauna saboda sanyin da jikinta yayi lokaci ɗaya, ba lallai Siyaa tabasu haɗin kai ba domin har lokacin akwai raɗaɗin rabuwarsu da Abu Zaid a cikin ranta. Ɗakinta ta nufa da Addu'ar Allah yasa ta amince acikin ranta. A zaune ta sameta tana sana'ar da ta saba na tunani. Da wani irin tsoro da mamaki take kallon fuskar Mommynta bayan ta gama koro mata bayanin Paul ƙanin shahararren mai buga wasan ƙwallon wandon nan wato Zayad yace yana sonta kuma a shirye yake ya aureta idan ta amince. Mommyn siya da sigar lallashin da tasan dole jikin Siyaa yayi sanyi ta ce; "Siyaama kina buƙatar abokin rayuwa ko don lafiyar ki, nasan Abu Zaid shima zai yi farin ciki idan ya ji kinyi aure kin kwantar da hankalin ki, kuma zaki samu lada mai girma na zama sanadiyyar musuluntar Paul. Bazan takura miki ba, amma idan kikayi min biyayya zanji daɗi na kuma ƙara sa miki albarka da fatan rayuwar farin ciki mai ɗorewa a tare dake." Zugum Mommy tayi tana jiran amsar Siya tare da addu'ar Allah yasa ta amince da Paul suyi biki na alfarma. Siya kuka mai raɗaɗi dake ƙara tabbatar mata da ta rabu da Abu Zaid ta fashe da shi hannayenta na rawa ta kamo na Mahaifiyarta tana cewa "Na amince Mommy, na amince." Kuka sukasa dukkansu kafin su rungume juna. A zuciyar Mommyn Siya ba laifi ta ɗan ji datasani da tausayin cutar da Abu Zaid da tayi a cikin zuciyarta. Itama Siyaa tausayin Abu Zaid ne yaƙara tsarga mata, tana jin kamar bai dace tayi aure ta haihu ba bayan mahaifiyarta ta nakasa tasa rayuwar ba. ****** Zayad ɗan uwan Paul da Mahaifinsu ba ƙaramin farin cikin karɓa musuluncinsa sukayi ba. Ko da Siyaa bata amincewa aurensa ba, iyakacin musuluntarsa wani babban nasara ne a wajen su. Babu inda labarin musuluntar Paul daya koma Muhammad bai zaga ba a cikin ƙasar har ma da wajen ƙasar ba. Har shuɗewar wata biyu Paul da ya koma Muhammad baya samun sakin fuskar Siyaa duk da haka bai da muba balle yaji raguwar sonta a cikin zuciyarsa, burinsa kawai su yi aure su zauna tare. Yasan da labarin Abu Zaid a bakin Mommynta don bata ɓoye masa ba gudun faruwar matsala a gaba. Kyaututtuka masu nauyin kuɗin dake ƙara ruɗar da Mommyn Siyaa Muhammad da Zayad suke aikowa da Siyaa da shi wasu lokutan kuma Muhammad ya kawo mata da kanshi. Muhammad bashi da ciwon kai da kowa nasa kan maganar auren su da Siyaa, domin rayuwar ƴanci da zaɓin kai sukeyi balle kuma yasamu amincewar mahaifinsa da ɗan uwansa. Siya kuwa har lokacin bata son auren haka dangin su rabi da kwata duk basaso amma banda Kakarta, Mahaifiyarta da kuma Yayan mahaifiyarta wato Alhaji Sunusi. Mommyn Siya har su Aunty da Zainab ta kira kan su lallashi Siya tun da taga a gidansu ta taso wataƙila ta ji nasu lallashin ta fara sakarwa Muhammad fuska. Da lallashin Aunty da Zainab da Kakar Siyaan ta ƙauyen Tofa da mijin mahaifiyarta Siyaan ta amincewa aurenta da Muhammad. Siya bata wani ji alfahari ko jinta ta musamman dan zata auri Muhammad ɗan uwan Zayad da duniya take damawa da shi ba, tunaninta da zuciyarta gaba ɗaya na wajen ɗan uwanta Abu Zaid. Babu wani masoyin Ziyaada da Siyaa da bai tayasu murnar mallakar Muhammad a matsayin siriki ba, don kowa shaharar ɗan uwansa da dukiyar shi suke kallo bawai asalinshi da tushenshi ko addininshi ba. ***** A ɓangaren Abu Zaid kuwa ya daina samun barci ko kaɗan saboda ciwon ɗan yatsan da ya tisa shi a gaba da zafi da zugi da raɗaɗi. Ko wajen aiki ma a daddafe yake zuwa ya dawo. ****** A ɓangaren Siya kuwa nacin da akayi mata ƙiri-ƙiri ta nuna ita bazata yi taron komai ba na kanta, tace dai idan su zasu yi ita bata hana ba. Domin nuna isa a Lagos gidan Yayanta Mommyn Siyaan ta shirya yin bikin auran na bugawa a jarida, saboda irin kuɗin da Muhammad yake sakar mu su. Lokacin da komai na bikin Siya ya kammala aka ɗaura aure, Siyaa tayi kuka irin wanda batasan iyakarsa ba Zainab tana tayata saboda kishin da take taya ɗan uwanta da har lokacin basu san a duniyar da yake ba. Daga Siya sai Mommynta da matar Yayan mahaifiyarta wato Alhaji Sunusi suka tafi Coventry kaita gidan Muhammad. A ranar da aka tafi da Siya Coventry Aunty da Zainab suka bar Lagos, lokacin Safeera babbar ƴar Zainab ta na da shekaru bakwai da ɗoriya a duniya, ƙannenta Mmza ma duk sunyi wayo. Ango Muhammad bayan an kawo masa Siya gidan shi bai ga alamun zata karɓi soyayyarsa ta daɗin rai ba, wannan dalilin yasa daren tarewarta ya sa mata ƙwaya a cikin lemo dan gaba ɗaya ya gama narkewa a kanta. Siya kuwa bayan ta farka washe gari taga abinda Muhammad ya yi mata tsanarsa da danasanin aurensa ne suka mamayeta. Duk yadda Muhammad yake tarairayarta da lallashinta taƙi ta daina kukan da takeyi balle ta saurareshi. A kwanakin da suka biyo baya ta fara gane matsawar zata zauna da Muhammad waje ɗaya to fa dole sai ta so shi wata rana. Saboda Muhammad kyakkyawa ne irin asalin kyan da ya haɗe da hutu, ga kulawa kamar zai lasheta ga sauƙin kai da yake dashi. Haka ɗan Uwansa Zayad, shima yana ƙoƙarin nuna kulawarsa akanta, haka Mahaifinsu shima kamar zai goyata saboda so, dukkan su kulawarsu akanta na musamman ne. A ɓangaren Mommynta da su Aunty har da Kakarta kusan kullum suma sai sun kirata sunji lafiyarta. Watan Siyaa biyu a gidan Muhammad ta tabbatar da shigar ciki a jikinta. Kayanta ta haɗa a ɓoye bayan sun yi sallama da Muhammad ya fita office, ta nufi Airport ko gidan Mahaifiyarta bata biya ba. Cikin sa'a ta samu jirgi da sa'ar rashin nemanta da kowa bai yi ba tabar ƙasar. Bata tsaya a Lagos ba kai tsaye gidan Kakarta na ƙauyen Tofa ta nufa, domin ta roƙeta su haɗa kai su zubar da cikin ita bazata haihu da Muhammad ba. ****** A ɓangaren Abu Zaid kuwa wajen masu sayar da kayan marmari ya sauka lokacin da yake dawowa daga wajen aiki, tun safe ya kasa cin komai saboda zazzaɓin daya ɗauke masa appetite. Kafin ya miƙawa mai kayan marmarin canjin da ya rage masa ya hango ƙanin mahaifiyar Siyaa yana ƙoƙarin tarar Taxi. Daga ɗan nesa da tsallake titin da yake. Da ƙarfi Abu Zaid ya ƙwala masa kira yana ambatar sunansa. "Saleem!" Yana barin wajen mai kayan marmarin zuwa inda Saleem ɗin yake tsaye. Saleem a ɗan firgice ya kai dubansa inda ya ji ankira sunansa, kallon mamaki yake bin Abu Zaid da ke ƙoƙarin tsallakowa titi dashi don har ga Allah bai ganeshi ba domin wannan wani Abu Zaid ɗin ne daban ba wanda ya sani ba. Sai da ya matso kusa da shi sosai sannan Saleem ya ɗan ganeshi amma duk da haka yakasa yarda da gaske shi ɗin ne. Tambayar da ya fara zuwa bakin Abu Zaid bayan ya ƙaraso kusa da Saleem sun gaisa shi ne; "Saleem ina Siyaa ta haƙura tayi aure ko?" Saleem raunin da ya hango a idon Abu Zaid da yanda Abu Zaid ɗin ya koma kamar mai matsalar kai yasa yace "A'a yanzu haka tana gida taƙi yarda ta zauna a can." "Subhanallah ku lallasheta ku bata haƙuri kaji? bari na siya mata kayan daɗi ka kai mata, amma karka gaya mata ka ganni kaji?" Abu Zaid ya faɗa yana komawa wajen mai saida kayan Marmarin daya baro. Wani irin abu mai ɗaci Saleem ya haɗiye tare da ƙwallar daya taho mai a hankali ya furta. "Allah Karka jarabbaceni da son abinda bazan samu ba." Duka kuɗin jikin Abu Zaid ya tattara ya siyi fresh fruits ma su kyau a ido sannan da sauri ya ƙara nufowa gurin Saleem. Daga sama har ƙasa Saleem yake kallon Abu Zaid kafin ya ƙaraso. "Wai dagaske Abu Zaid ne wannan?" Ya tambayi kansa, Ya tsinewa Hudayya a cikin zuciyarsa babu adadi. Numfashi Abu Zaid yake saukewa yana ƙoƙarin shanye raɗaɗin da ɗan yatsansa yake mai, bayan ya ƙaraso kusa da Saleem a hankali ya furta. "Ga shi ka kai mata amma kayi min alƙawarin bazaka gaya mata ka ganni ba?" Kai kwai Saleem ya ɗaga mai alamun ya ji saboda idan yayi magana kuka ne zai biyo baya. Abu Zaid yana tsaye har Saleem ya hau Taxi yabar wajen. Bayan Taxin ɗin ya bi da kallo kafin ya ɗauke Ƙwallarsa da ta kwararo kan kuncinsa yana kife tafukan hannayensa a kan fuskarsa, kuka mai sanyi ya fashe da shi har da shesheƙa tamkar wani ƙaramin yaro. Ya daɗe a tsaye yana kuka kafin ya fara tafiya domin ba shi da kuɗin siyan wani kayan marmarin kuma ba shi da na Mota, tsakanin wajen da gidan su akwai ɗan tazara sosai. Dole haka yafara takawa da ƙafa yana hutawa idan raɗaɗin ɗan yatsan ya ishe sa, a haka ya ƙarasa gida a gajiye ....✍🏻 [10/29, 9:59 PM] Hajja Ce: ABU ZAID By Nafisa Sasaal 12 A parlor ya samu Hudayya tana kallon tv harda kyalkyala dariya. Bai ce mata komai ba bayan sallamar da ya yi. Dariyarta ce ta ɗauke lokaci ɗaya, cikin sanyin hali da na muryar da take ƙoƙarin nuna tana da shi tun bayan barowar su Zaria ta amsa sallamarsa kafin ta ɗora da. "Sannu da zuwa Yayaa." Kai kawai Abu Zaid ya ɗaga mata ya wuce ɗakinsa. Bayansa tabi da kallo, sai take ganin kamar akwai abinda yake damunsa yake ɓoyewa, amma koma dai menene a hankali zata sani. Kallonta ta tacigaba dayi ranta fari fes tana ci gaba da kyalkyala dariyarta. Abu Zaid kuwa bayan ya isa daƙinsa numfashi mai ɗumi ya sauke lokacin da ya fito daga wanka, raɗaɗin abu biyu na haɗe mai wato labarin Siyaa tana gari ɗaya da shi da kuma ciwon ɗan yatsan nan nasa da yakeji a duk sassan jikinsa. Kullum sai dare ya raba idan Allah ya taimakesa yake iya barci, amma daren ranar sai yafi na kowani daren muni saboda tunani da ciwon da ya addabesa. Hudayya kam washe gari da wuri ta bar gidan zuwa Makaranta ba tare sun haɗu da Abu Zaid ba. Bata da ƙawa sai Mutum ɗaya mai suna Maryam kuma itama ba sa hirar personal issues a tsakaninsu, sai hirar karatu da hirar daba'a rasa ba. Ranar dai kasa jurewa tayi ta gutsurowa Maryam labarin iyakar inda zata wanke kanta batare taga aibunta ba. Bayan Maryam ta gama sauraran labarin Hudayya baki ta riƙe kafin ta kwashe da dariya, ta ɗan ɗauki daƙiƙu ta na yi sannan ta tsagaita tana cewa; "Hmm Hudayya baki iya neman soyayyar ɗa namiji ba, ai da hirar Siya zaki dinga jansa ko da yanuna bayaso, idan zaki iya ma kice masa zakije har wajen Kakarta ki tambayeta ko Siya tananan lafiya tunda kin ce can wajen zuwanta ne, wallahi ina gaya miki dole ya fara sakar miki fuska saboda kina taɓa masa inda yake masa ƙaiƙayi." Hudayya da tantama tace, "Dagaske Maryam kina ganin hakan zai janyo min hankalinsa kuwa?" Da ƙarfin gwiwa Maryam ta ce; "Ƙwarai kuwa da kanki zaki bani labari." Ta ƙarasa faɗa tana juya idanuwanta. Hudayya gaba ɗaya sai ta matsu ta koma gida dan ta aiwatar da shawarar da aka bata. Su na tashi kuwa bata tsaya surutan da ta saba ba ta nufi gida. Lokacin da ta isa gida, a parlor ta samu Abu Zaid yana kwance kan doguwar kujera kamar ma bai fita aiki ba, da tsoron abinda yake ranta ta gaisheshi, bata jira amsawarshi ba tayi gyaran murya da addu'ar Allah yasa ya karɓi zancenta. Sannan ta ce; "Yaaya ina son zuwa Tofa wajen Kakar Siyaaa na ji ya ya lafiyar Siyaan, don Allah kabani addireshin gidan nasan zaka so sanin yadda take." Abu Zaid miƙewa ya yi ya zauna da mamaki kwance a saman fuskar sa. Da a waya yayi magana da Saleem jiya da sai yace laɓewa Hudayya tayi ta ji tattaunawarsu. Murmushin da bata taɓa samu daga garesa ba yasakar mata, don kamar tasan hanyar da zai ƙara samun wani labari akan Siyaa yake nema. Da sanyin muryar daya haɗe da ciwon dayake ji yace "Yaushe zakije Hudayya?" Cikin zumuɗi Hudayya tace; "Ko gobe Yaaya a shirye nake." Kai ya jinjina mata yana miƙa mata farar shinkafar daya girka yakasa ci. Kamar babu komai a ranta haka ta tashi ta nufi ɗakinta da abincin daya bata a hannunta, wata irin wutar tsanar Siyaa nacin zuciyarta. Abu Zaid kuwa, Maula ko roƙo ba halinshi bane don baima taɓayi ba, amma a karon farko ya ɗaga waya ya kira Taufiq ya roƙesa kuɗi. Cikin ƙasa da hour biyu sai ga Taufiq ya turo yaronsa da kuɗin. Da lallaɓawa Abu Zaid yabar gidan. Siyayyan kayan sawa dana ciye-ciye da yasan Siya tanaso yayi mata. Bayan ya dawo gida a sabon ƙaramin jakar daya siyo ya jera mata komai yana jin wani irin farin ciki. ★ Washe gari bayan Hudayya ta shirya, kuɗin mota wadatacce Abu Zaid ya bata tare da kafa mata sharaɗin kar tace tasan inda yake. Hudayya wani mugun kallo tabi bayansa da shi ta cikin liƙabin dake manne akan fuskarta. Bayan Hudayya ta isa Tofa tana sauka a tasha ta haɗu da Hajjo riƙaƙƙiyar maƙiyar zuri'ar su Siyaa duk da alaƙar jini da suka haɗa. "Don Allah tambaya nake yi, gidan Habu Sarki." Hudayya ta tambayi Hajjo dake tsaye a gefenta. Dasauri Hajjo ta karɓe da cewa. "Zo in rakaki nima gidan na nufa." Gaisheta Hudayya tayi Hajjo ta amsa tana ƙare mata kallo sannan ta ce; "Ƴar nan badai wajen Siyaama kika zo ba Ko?" Da salon bugar ciki ƙiyayyar su Siyaa daya bayyana a maganar Hajjo Hudayya ta ce; "A'a ni mai ya haɗani da wannan uwar girman kan." Shewa da guɗa Hajjo tasa kamar mara kamun kai sannan ta ce; "Yo ai jiji da kai yaƙare tunda ta kasa zama da baturen da suka aura mata, kuma dai Ibrahim ɗin da takeso zalamar uwarta yasa sun turan mai aljanu sun kashemai al'aurar to mai ya rage da zata yiwa mutane jiji da kai ga ciki ta kwaso tazo dashi." Gaban Hudayya ne faɗi tsoro da kishi mai zafi na shigar ta. Hajjo da yake mai surutu ce ga kuma hassada daya makatar da ita ba tare da tantace daga ina ma Hudayya take ba, tunda har lokacin fuskarta manne yake da liƙabi tayita sakar zance Hudayya na janta da hira har suka rabu a hanya bayan ta nuna mata gidan daga nesa tace bari taje ta dawo. Wadataccen fili ne a gaban gidan an kewaye shi da wayan ƙarfe har sai da ya haɗe da ƙofar shiga ainihin cikin gidan. Shuke-shuken kayan marmari ne a yalwataccen filin don haka gurin yake da sauƙin zafi. Siya tana zaune akan plastic chair fari idanuwanta a lumshe kyawawan dogayen yatsunta dake bayyane na zube kan wayarta mai tsadar da sai shahararrun ma su kuɗi ne suke iya riƙewa a waccan lokacin, daga nesa Hudayya take kallonta kishinta kamar zai kassarata, ta sani babu wani labarin da zai wanzar da murmushi a saman fuskar Siyaa sama da wanda tazo dashi amma batajin zata bata wannan labarin, maimakon ta shiga filin kamar yadda tayi niyya sai ta juya a zagaye ta koma tasha, kai tsaye motar Gwarzo ta nema ta tafi. Su Baba Ilu bakinsu kamar zai yage don kaf abinda Abu Zaid yabawa Hudayya su taje ta rabawa. ***** Abu Zaid kuwa tun bayan tafiyar Hudayya yake zaune a parlor sallah ce kawai take tayar dashi, har bayan Magriba yana zaune zaman jiran dawowar Hudayya ƴa ƙagu yaji labarin Siyaa. Hudayya bayan ta bar Gwarzo Kukan Abu Zaid bashi da amfani a wajen ta ta tsaya tasha a hanya dan bata taɓa zato ko tsammanin bashi da amfani a wajan auratayya ba. Wannan dalilin yasa idanuwanta yin jajir. Sai dare ta iso gidan. Da damuwa sosai Abu Zaid yake tambayarta mai ya samu Siyaan? Ta samu ganinta kuwa? Cikin kuka Hudayya ta ce; "Siyaa tayi aure tana ma da ciki kuma tace karka ƙara nemanta tunda kaci amanarta, nayi mata bayanin sharrin su Baba Ilu ne amma taƙi yarda ƙarshe tasa aka koreni." Murmushi mai tafe da ƙwalla ne ya tahowa Abu Zaid cikin sanyin muryarsa dake rawa yace. "Banyi fushi ba, duka da haka ina mutunta Siyaa, ina Kuma ganin darajarta, kuma laifi nane tun farko, amma ai dai tana lafiya ko?" Baki hanci ido Hudayya tasaki tana kallonshi kafin ta girgiza kai alamun a'a. Murmushi Ya ƙara yi amma na wannan karon hawaye ne kwance a kan fuskar sa yace. "Na sani wata rana zata haƙura ta kuma fuskanceni tasan da cewa banci amanarta ba. Yanzu dai kije ki huta Hudayya na gode kinji." Kai ta ɗaga mai saboda ta kasa yin magana. Hudayya bayan ta koma ɗaki tausayinsa ne yake neman bijiro mata amma baƙin halinta sai ya danne tausayin na shi. Kwanan neman mafita Hudayya tayi sai a lokacin ta gano dalilin da yasa baya jin komai a kanta na shauƙi ko burgewa. Ashe dalili ne yasa duk abinda zatayi masa don ta burgesa ko ta ja ra'ayinsa baya nuna yasan tana yi. Ta jinjina kai tana cizon yatsa tare da lashe busasshen lebenta da ya bushe sosai. ★ Washe gari kamar yanda Abu Zaid ya kwanta bai ci abincin dare ba haka ya tafi wajen aiki bai karya ba. Daga wajen aiki ƙaramin private hospital mai sauƙin kuɗi ya wuce. Batare da sanin makamar aiki ko gwaje-gwaje ba, Likitan ya danƙara masa magunguna har da na shafawa a ƙafa. Hudayya kuwa a hankali ta fara mayar da gidan Taufiq wajen zuwanta bayan ta gina shaƙuwa a tsakaninta da Matarsa mai son mutane da sauƙin kai. A cikin watanni ukun da suka biyo baya sau biyu Abu Zaid yana aikar Hudayya wajen Siyaa da uban siyayya, amma Hudayya ko biyawa Tofa ma batayi take wucewa Gwarzo da kayan ta kai musu. A hankali a hankali yawan zuwa gidan Taufiq da yadda Hudayya take tallata masa Jikinta ta hanyar saka matsatstsun kaya yafara jan ra'ayin Taufeeq ɗin, har ya kasa haƙuri ranar da ya ɗauketa zai mayar da ita gida ya karɓi lambar wayarta. Tun kafin ta baro Motarsa suka saka ranar haɗuwa da juna a keɓantaccen waje ba tare da sanin iyalinsa ba. A ɓangaren Muhammad kuwa, sai dare ya dawo gidan yaga babu Siyaa, kuma dama tun da rana yake kiran layinta baya samu. Hankalinsa dana mahaifinsu da suke ƙasa ɗaya ne ya tashi. Itama Mommyn Siyaan da Muhammad ya sanar mata ruɗewa tayi gashi ko sun kirata baya shiga. Bayan Muhammad yasa an zurfafa bincike sai ya samu labarin tafiyarta zuwa Nigeria. A gidan Mommyn Siya Muhammad ya tare saboda ƙuruciya da sangartar da suka haɗe mai. Duk magiyar da Mommyn Siya ta yiwa Kaaka a waya kan su tilastawa Siyaa ta dawo bata saurare ta ba, don cewa ma tayi Siyaa bazata koma ba sai dai idan Nigeria Muhammad ɗin zai dawo su zauna tare. A ɓangaren Kaka tasan batun Muhammad ya dawo Nigeria, abu ne mai wahala shi yasa ta faɗi haka don tasan rabuwa zai yi da Siya kowa ya huta tunda Siyaa ta ce bata son shi. Numfashi Saleem dake zaune kusa da Kaka ya sauke har lokacin fuskar Abu Zaid nayi mishi yawo a ido, da damuwa ya ce; "Nenne kibar Siyaa ta tafi don Allah." Cikin faɗa Kaka ta bashi amsa da. "Akan wani dalili Saleem? Menene hujjarka Eh? Yarinya ta ce bata so dole ne?!" "Nenne kamar fa Siyaa ciki gareta gara ki barta ta tafi, domin idan kika biye mata baturen mijinta ne zai ɗaureki." Saleem ya faɗa da iya gaskiyarsa Jikin Kaaka sanyi yayi don ita batasan da wani

Chapter 6 of 11