Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ABU ZAID By Nafisat Aliyu Sasaal 09132403788 [9/21, 3:51 PM] Novel: Sunana Safeera Yazeed, ni mazauniyar garin Abuja ce, kuma ma'abociyar karance-karance, hakan ya samo asali ne daga rayuwar kaɗaicin da muke ciki ni da ƙannena maza guda biyu, sai mahaifiyar mu da ciwon damuwa yayi mata illah mai girma. Mahaifin mu Allah Yayi mishi rasuwa tun muna yara, bamu rasa komai na wadatatciyar rayuwa ba, sai rashin sanin asalina, kuma duk lokacin dana buƙaci sani sai ciwon Mahaifiyata yaƙara tsanani. Ambaton sunan HUDAYYA SHITU GWARZO da mahaifiyata take yawan yi duk lokacin da ciwonta yayi tsanani, shi yasa nafara bin duk wani hanyar da nasan zan sameta, amma har shuɗewar shekara ina ziyartar duk wasu ƙauyuka na cikin garin Gwarzo, amma bansamu wani labari a kanta ba. Kwatsam wata rana na ci karo da littafi a wajen da nake siyan litattafai mallakin HUDAYYA SHITU GWARZO. Jikina yana rawa na siya ina murna. Bayan na dawo gida sai na keɓance kai na saboda sunan littafin na bani tabbacin yana da alaƙa da mahaifiyata, kuma inasa ran samun dukkanin amsoshina a ciki. Hannuna yana rawa na buɗe shafin farko. *ABU ZAID* ```CHAPTER 1``` RAILWAY STATION. Ƙarar girjin ƙasan ne yake ta ƙaruwa alamun girjin yana daf da ƙarasowa. Ƙasa yayi da tinted glass ɗin motar ya jefar da guntun cigarette ɗin hannunshi sannan ya jefa alewa mai ƙamshi a cikin bakin shi. Ƙofar motar ɗaya ya buɗe saboda hayaƙin daya cika motar ya samu damar fita, sannan ya feshe jikinshi da turare mai tsananin ƙamshi yana ƙara gyara zaman wuyar rigar tsadadden yadin dake jikinshi. Fitowa ya yi ya tsaya a kan ƙafafuwanshi yana mitsitsike guntun cigarette ɗin da bai ƙarasa mutuwa ba. IBRAHIM ƊALHAT ABU ZAID kenan matashin da Allah ya yiwa baiwar tsananin kyan dake jefa dubban jama'a cikin halaka saboda kambabashi da suke yi. Murmushin da ya ƙarawa fuskarshi kyawun gaske yake ta saki lokacin daya hango abokin shi da iyalanshi na ƙara kusanto shi kowannen su fuskar shi na nuna alamun gajiya. Da tsananin farin ciki suka rungume juna. Driver dake maƙale agefe tuntuni ya matso yana ƙoƙarin kwasar manyan luggage ɗin su don zubawa abayan mota. "Ya hanya? naga Madam da yara duk sun gaji." Abu Zaid ya faɗa cikin muryar shi mai tsananin sanyi kamar ba ta namiji ba. "Ka bari kawai Ibrahim yaran nan sun wahalar damu wallahi." Nazeer abokinshi ya faɗa agajiye. Murmushi Abu Zaid ya saki yana gaisawa da dukka yaran abokin nashi da suke gaishe shi. Ya na tsaye kowannen su ya zauna a mazauni shi suna ta faman lumshe gajiyayyun idanuwan su masu cike da bacci. Sannan ya zagaya don zama anashi mazaunin. Da sauri matashiyar da bata wuce shekaru 17 ba ta ƙaraso gefen Abu Zaid dake ƙoƙarin shiga mota da baƙar Abayar da tayi tsananin datti a jikinta, fuskarta gaba ɗaya tayi zuru-zuru saboda yunwar da ya gama rarake mata cikinta. "Dan Allah ka taimaka min koda da aikatau ne na roƙeƙa dan Allah! Dan Allah! Dan Allah! karka ce a'a na roƙeka ka taimaka min fisabillahi." Ta faɗa cikin kuka mai tsanani tana share hawayenta da gefen mayafin dake yane a kanta da ba ɗankwali. Girarshi ɗaya ya ɗage yana waiwayowa kanta da kyau ranshi a ɗan ɓace saboda bai cika son takura irin haka ba. Bayan ya ƙare mata kallo sai ya sassauta fuskar shi don shi ba gwanin ɗaure-ɗauren fuska ba ne ba. "Wa kike nema? ɓata kika yi?" Ya faɗa har lokacin da annuri akan fuskarshi. "Iyayena sun mutu kuma matar Mahaifina ta koreni tace bata da abun ciyar dani kar na ƙara dawowa, kuma ni bansan garin da ƴan uwan Mamana suke ba, naje wajen ƴan uwan Mahaifina sun koreni, ka taimakeni don Allah ko wani irin aiki ne zan iya yi." Ta faɗa da sakin wani sabon kukan mai ban tausayi jikinta har rawa yake yi. "Tashi karki damu kinji, menene sunanki da garin ku?" Ya faɗa yana tattare cikakkiyar girarshi da yanayi na yamutsa goshi. "Sunana Hudayya, ƴar ƙauyen Gwarzo ce ni." Ta faɗa da rawar murya. "Ƙauyen Gwarzo?" Ya maimaita a cikin zuciyarshi yana ƙare mata kallo. Duk da tana cikin datti da wahala bata yi mishi kala da wacce ta fito daga ƙauyen Gwarzon ba. "Hudayya ko?" Ya tamabaya yana kallon fuskarta. Da sauri ta amsa da. "Eh." "Banason ƙara, idan na kamaki da ƙarya zan dawo dake inda na ɗauke ki kinji ko?." Ya faɗa da daddaɗar muryarshi mai tsananin sanyin daya haɗe da yanayin shi na mutum marar hayaniya. Kafin ta ba shi amsa Nazeer da ya kasa jurewa gangancin da aminin nashi ke shirin tafkawa a nashi ganin, yai saurin saukowa daga motar yana magana furiously yana cewa. "Abu Zaid ka ba ta iyakacin sadakar da kayi niya amma mutane irin waɗannan ba abun yarda ba ne. A wane dalili zaka kai mace kamar wannan gidanku parents ɗinka su yarda dakai?" Nazeer ya faɗa kamar zai mari matashiyar da ke tsugunne har lokacin. "Calm down my G-I just want to help kawai fa." Abu Zaid ya faɗa da sanyin shi. "Naji amma wata rana karka nemi shawara ta a kan haka, saboda sam ban yarda da wannan yarinyar ba. Idan har fisabilillahi takeson taimakon why not mu bata kuɗi ta koma gida wajen step Mom ɗinta? Shin mai yasa dole sai tafiya da ita gidan ku? Tukunna ma tun daga ƙauyen Gwarzo taimako ya kawota har garin Zariya? mai yasa bata nemi taimako a kaf faɗin garin Kano ba sai nan?" Cikin yanayi na kosawa da mitar da Nazeer keyi Abu Zad yace, "Nazeer dukka wannan zafin na menene? Ko kasanta ne kake ɓoye min? Gurin iyayena fa zan kaita idan su ka ƙi amincewa zamanta tare da su dole bani da zaɓi Nazeer sai ta dawo nan inda muka ganta. Kuna buƙatar hutu Nazeer zamu tattauna matsalar daga baya." Ya faɗa yana ɗan dukan kafaɗar Nazeer ɗin alamar ƴa basar kawai. "Amma kasan bazan shiga mota ɗaya da stranger ba ko?" Nazeer ya faɗa yana hararar inda ta ke rakaɓe a gefe ɗaya. "Kasan ba na iya driving a irin wannan lokacin Nazeer da nasa Driver ya taho da ita." Abu Zaid ya faɗa yana gyara zaman tabaran fuskarshi. "Wallahi Abu Zaid bazan hau mota ɗaya da stranger ba kaji na rantse. Ni fa nafi san ka bata kuɗi takoma gidan step Mom ɗin nata kawai." Ya faɗa yana ƙafe Hudayya dake tsugunne har lokacin da jajayen idanuwanshi da ɓacin rai da gajiya suka sauya su. Da nazari sosai Abu Zaid yake kallon Nazeer yana kuma tantance ina ya dosa, bai san mai yasa yake jin kamar ya zame mishi dole ya taimaki yarinya ba, duk da shi ba gwanin tsayawa sauraron matsalolin wa su bane, don ko almajirai dazarar sun fara bara haɗe da bayanin abinda yake faruwa da su, baya tsayawa sauraren su yake ba su sadaka mai tsoka su wuce. Amma Hudayya daban yake jin tausayinta a ranshi. Matar Nazeer dake mamakin zafin da mijinta ya ɗauka a kan taimakon matashiyar da ba ma shi zai yi ba ta sakko da zargi kala-kala a cikin zuciyarta wanda ya kasa ɓoyuwa har saman fuskarta. Huci mai zafi Nazeer ɗin da yayi ido huɗu da ita ya fesar saboda tsaf ya karanci damuwar ta, kuma shima tun farko ko don matar ta shi ya kamata ya yiwa Hudayya uzuri ya kuma ba wa Abu Zaid damar taimakonta. Amma haka kawai yake jin tsanar Hudayya a ranshi besan dalili ba. "Bansan mai yasa kake gudun Abu Zaid yayi irin taimakon da kayi a baya ba, ko dai nayi maka wani laifi ne dakake ganin duk wani mai neman taimako bai cancanci a taimake shi ba? Ko jirgin ƙasan da muka saka ka biyo ne ya ɓata maka rai?" Matarshi Surayya ta faɗa a dai-dai saitin kunnenshi da rawar murya saboda ƙaramin kukan daya taho mata. Bai bata amsa ba, sai hannunta da ya damƙa a cikin na shi haɗe da sumbatar hannun, sannan yaja ta zuwa mota ya zaunar da ita shi kuma ya zagaya mazaunin Driver alamun ya yarda a tafi da Hudayya amma ba a mota ɗaya ba. Murmushi mai sanyi Abu Zaid yayi yana ƙara gyara zaman tabaran fuskarshi, wato Nazeer duk gajiyar dayayi ya gwammace ya ja mota da dai Hudayya ta bisu a mota ɗaya. Ragowar kuɗin dake jikinshi yabawa Driver sannan yayi mishi bayanin tahowa da Hudayya da zai yi. Driver ɗin ya karɓa yasa a aljihu, shi kuma Abu Zad ya nufi mota. A kan zurmammun idanuwan Hudayya da kamar za su zazzago wajen bin sabuwa dal kuma fari ƙal ɗin Sienna XLE da Nazeer ya ja da mugun speed su ka bar wajen gaba ɗaya kamar ɗaukewar wuta, idanunta na kai har sai da ta daina hango motar gaba ɗaya sannan ta lumshe su tana sauke ajjiyar zuciya. Shi kanshi Drivern wani irin kallo yake mata kamar ɓarauniya, shima har cikin ranshi bai yarda da Hudayya ba dan ƙarara ya nuna ƙyanƙyaminta da kuma tsanarta ta hanyar hantararta yana cewa. "Wuce muje." Hudayya bakin ciki ya kamata sai dai ta daure. Har suka hau abun hawa Hudayya na cikin fargabar da wani irin fuskar iyayen Abu Zaid zasu karɓe ta? Ko dai suma korarta zasuyi tunda kowa tsanarta da ƙyanƙyaminta yake nunawa....? ✍🏻 _⚠️Idan har kinsan zuciyarki mai tsananin rauni ce karki bibiyi labarin nan don zai hanaki fuskantar darasin dake ƙunshe a ciki, ƙarshe ki ƙasa yi min Uzuri._ [9/21, 3:51 PM] Novel: ```ABU ZAID``` ```BY SASAAL``` ```CHAPTER 2``` Har parking lot ɗin gidan su Nazeer ya shiga da motar, har lokacin fuskarshi babu annuri. Bayan ya yi parking shi ya fara fita kafin yaran su rufama mai baya suna cewa Abu Zaid. "Take care Uncle." Kai yake gyaɗa mu su yana ƙaƙalo murmushin dole kan amintacciyar fuskarshi. Surayya da ta kasa jurewa, matsawa ta yi kusa da shi lokacin da yake ƙoƙarin neman number Drivern. Haƙuri ta bashi akan ɗan musayar yawun daya shiga tsakaninshi da mijinta. Murmushi shi ya ƙara faɗaɗawa ya nuna mata komai ya wuce. Bayan duk sunyi hanyar shiga gidan Abu Zaid ya matsa kusa da Nazeer dake tsaye sukayi sallama har lokacin Nazeer bai saki Fuskarshi ba. "Hit me up when you're free." Abu Zaid ya faɗa yana juyawa ba tare da jiran amsar da Nazeer ɗin zai ba shi ba. Bayan Abu Zaid Nazeer ya bi da kallo, tausayin shi na ƙara kamashi, sai yake jin kamar bai kyauta mai ba. Kasa jurewa yayi har ya kai Ƙofar da zai sadashi da living room ɗin gidan ya juyo, dai-dai lokacin da Abu Zaid ya tashi motar zuwa bakin gate ɗin da Driver da Hudayya suke jiranshi. Sanyin raɓa da lafiyayyen Unguwar da Hudayya bata taɓa kawowa ko kusa ko nesa cewa akwai irinshi a cikin garin Zaria ba nan suka shiga. A waje gidan su Abu Zaid ba shi da wani kyale-kyale, amma cikin shi abun kallo ne mussamman ga baƙauyen mutum. Dariyar muryoyi daban-daban ne ke tashi a cikin ƙaton living room ɗin gidan, dalilin da yasa gaban Hudayya dake biye da shi a baya faɗuwa, tsoron da tun barowarta gida bai shigeta ba ne yake shigarta ta ko'ina. Kyawawa masu tsananin kamanceceniya da Abu Zaid ne a living room ɗin a zazzaune, Mahaifinshi, ƙannen Mahaifinshi, sai ƙanwar Abu Zaid Mlmace da suke Uba ɗaya da ƴar ƙaramar ƴarta, sai kuma Mahaifiyar ƙanwar tashi. Babu wanda ya lura da Hudayya dake laɓe a bayan Abu Zaid har sai da ya samu waje ya zauna sannan ta bayyana gaba ɗayan ta tana ta faman zare idanuwa. "Subahanallahi menene wannan?" Dukka ƙannen mahaifinshi mata suka haɗa baki wajen faɗa. Ƙasa Hudayya ta zube jikinta na rawa tana ƙudundune fuskarta da ɗan Veil ɗin dake ƙanta. Da sanyinshi na halitta ya ce. "A railway station na ganta tana neman iyayen ta, kuma tace ita ƴar Gwarzo ce, shine sai nayi tunanin Aunty (matar Mahaifinshi) ƴar garin ce nace ban sani ba ko zata iya sanin garin su idan tayi mata bayani, idan kuma bata sani ba sai ta na ɗan taimakawa Aunty da aiki kafin bayyanar iyayen ta." Abu Zaid ya faɗa da kyakkyawar niya. Fuskar Abbanshi a tsananin ɗaure zuciyar shi kamar ana hura mata wuta, domin Alhaji Ɗalhatu mutum ne mafaɗaci mai tsananin ƙin jinin bare ya zauna mai a gida, indai banashi dangin bane baya buƙatar kowa a muhallinsa, ko a nashi dangin ma sai iya ƙannenshi mata da suka rage mai da ƴaƴan su kawai yake buƙata. Bai san yaushe zuciyar Abu Zaid zai zama irin yanda ya jima yana buri ba, har tayaya ma zai kula da ɗimbin dukiyar su bayan duk ƙanƙantar abu sai yace yana ba shi tausayi? Hudayya jin akwai wanda yasan Gwarzo a gidan yasa gabanta faɗuwa tana ɗago idanuwanta a ki ɗi me, ba su sauka a ko ina ba sai cikin na Aunty. "Huda!" Aunty ta faɗa da ƙarfi tana dafe ƙirji haɗe da miƙewa tsaye. A zafafe Abbanshi ya miƙe shi ma haɗe da faɗin. "Fitar min da wannan trash ɗin daga Parlo sannan kamay..." "Alhaji wallahi na santa wallahi ƴar..." "I'm not done talking Salima! Ina ruwana da ƴar wacece naki? Kai kaga na baka five minutes ka fitar min da wannan abun daga gidana gaba ɗaya." Ya faɗa yana barin Parlon kamar zai tashi sama. Kuka mai ƙarfi Aunty tasa, Aunty's ɗin Abu Zaid na lallashinta, sosai suke sonta saboda amanarta da kirkinta. "Maman Zainab kiyi shiru kiyi mana bayani yanda zamu shawo kan matsalar." Suka haɗa baki wajen faɗa da sigar lallashi. "Ƴar ƙanwata ce, kwananta uku ana nemanta" ta faɗa tana istigifari a ranta,don Ramatu ta sanar da ita guduwa Huda ta yi daga gida da sunan gara tayi yawon banza da dai tayi zaman bauta a gidan ƙanwar Mahaifiyarta da suke uwa ɗaya Uba ɗaya. "Subahanallahi yanzu sai ki kira Iyayenta ki sanar da su don hankalin su ya kwanta". "Bata da iyaye ai marainiya ce a wajen ƙanwata take, don Allah ku roƙeshi ya barta ta zauna da ni." Abu Zaid dama ya jima da barin living room ɗin zuwa sashen shi, hayaƙin da baya iya shaƙawa cikin shi a gidan ya soma bankawa cikin shi. Zainab kallon Hudayya takeyi da tsananin mamaki, dama Mahaifiyarta ƴar Gwarzo ce? to mai yasa ba su taɓa zuwa ba? Duk da akaron farko ta ga wani tsage daga dangin mahaifiyarta sai taji sam Hudayya bata kwanta mata a rai ba. Aunty's ɗin Abu Zaid wajen Yayan su suka tafi don shawo kanshi. Da wannan damar Aunty ta ja hannun Hudayya zuwa sashenta Zainab ta rufa mu su baya da tarin tambayoyi kala-kala a ranta. Kai tsaye Bathroom Aunty ta tura Hudayya don yin wanka, sannan ta dawo Bedroom ɗinta ta sa mukulli gudun kar Zainab ta shigo. Ringing ɗaya aka ɗaga kiran da sallama. Cikin farin ciki Aunty take bayyanawa Ramatu ƙanwarta kuma mariƙiyar Hudayya ta bayyanar mata da komai na ganinta a gidan. "Hmm." Kawai ta ce daga haka tayi shiru kamar bata kan layi. Bayanin abinda ya faru da wanda ya ke kan faruwa ta bata tana cewa. "Salame karki kuskura ki bar Hudayya a gidanki ko da mijinki ya amince da zaman nata, idan ba haka ba Salame wata rana zaki yi kuka da idanuwanki. Karki manta mijinki shine Uwa kuma uba da dangin daya rage miki, sai kuma ɗiyarki da jikokinki, wallahi ki rungumi ƙaddararki ta tsaya a iya haka Salame. Amma zaman Hudayya a gidanki tamkar kin rura wutar daya jima da mutuwa ne a gareki. Kuma hakan na nufin lalacewar komai." Cikin yanayin mai cike da rauni Salame ke cewa. "Haba Ramatu ba wannan furucin ya kamata kiyi ba, ƙwarin gwiwa ya kamata ki bani kinji na samu nayi wani abun koda Allah zai bani lada a ciki." Ta jinjina kai tare da girgiza wa. Salame ba zata fahimce ta ba, ba zata gane abinda takeso ta gane ɗin ba. Daƙyar Ramatu ta sauko kan zata tayata da addu'ar su rabu lafiya da Hudayya ba tare da ta gane cewa san zama da ita ne batayi ba. Knocking ɗin da Zainab takeyi ne ya katse hirar ta su. Aunty taje ta buɗe mata ta shiga. Bayan Zainab ta zauna, Safeera ƴarta ƴar shekara huɗu ta ɗane kan cinyar Kakarta. Zainab ce take kallan mahaifiyar ta tace, "Mommy dama kinada dangi shi ne ban taɓa sani ba? mai yasa bakya kai ni wajan su?" Aunty da jikinta yai sanyi ne tace. "Zainab labarin mai tsaho ne kuma marar daɗin saurare, ki tayani da addu'a Allah yasa Abban ku ya amince min na riƙe Hudayya nasan komai zai dawo dai-dai." Aunty ta faɗa tana share hawayenta da suka zubo ba tare da ta sani ba. Kai Zainab ta gyaɗa ma ta haɗe da sakin murmushin da yafi kama dana yaƙe. Daga can ɓangaren su Daddy kuwa. Taƙaddama mai zafin gaske ne ya ɓarke tsakanin ƴan uwan nan guda uku. Ƙwararan hujjojin da suka fi na shi tasiri sukai ta kawo mai sai jikinshi yayi sanyi. Saboda dalilin irin wannan mummunar ɗabi'ar ta shi ne Salima tarasa danginta gaba ɗaya suka tsaneta. Bayan ya amince sai ya kafa sharaɗin bazai ɗauki nauyin komai na Hudayya ba sai dai abincin cin ta kaɗai. Amma suturarta kuɗin Makarantar da duk wasu buƙatunta babu ruwanshi da su ba zai yi ba. A kan wannan ma zazzafan mahawara ne ya ƙara ɓarkewa tsakanin su wanda daga ƙarshe dole suka gaji suka haƙura suka kyale shi don ya kafe babu canji. Lokacin da Hudayya ta tuɓe kayanta ta kalli yanda fuskarta ta koma ajikin madubin banɗakin, murmushi ta saki tana lasar leɓenta da yake a bushe. Ruwa mai ɗumi da daɗin wanka ne yake sauka a jikinta, malalacin murmushin dake kan fuskarta na ƙara faɗaɗa. Bata taɓa sanya abu a gaba ba, ba tare da ta ga ƙarshen shi ba, haka halinta yake kuma batajin zata sauya har gaban abadan. Aunty tayi farin ciki sosai lokacin da taji amincewar mijinta akan zaman Hudayya a wajen ta, har da kukanta wajen yi mishi godiya, duk da yace bazai ɗauki nauyin komai na ta ba. Bata damu ba dama fatan ta kawai ya amince dan kuwa su dangi abun alfahari ne musamman idan kayi da ce da nagari. Har sukayi dinner babu wanda yaga shigowar Abu Zaid wajan. Abu Zaid yana da haƙuri amma bai iya fushi ba, a lokuta da dama suna yawan samun banbanci ra'ayi shi da mahaifinshi akan tausayin na ƙasa da shi. ★Washe gari dukkan su ya kasance zasu tattara su bar gidan dan zuwa garin Kaduna yin bikin da suka daɗe suna jira. Sai a lokacin suka ga Abu Zaid fuskarshi a sake kamar komai bai faru ba. Bai tambayi Hudayya ba tunda abinda ya ɗaukota dan shi ta samu, to maganar su da ita ya ƙare. A shirye yake ya yi kyau dashi kasancewar shi wanda ya iya ɗaukar wanka. Daga Hudayya sai Maids (Masu aiki) aka bari a gidan. A kan jajayen idanuwan Hudayya lafiyayyun motocin su Abu Zaid su ka bar gidan. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi na cikar muradinta, tana kuma tuno ƙiyayyarta da take hangowa a idanuwan Zainab ɗin gidan. Mai yasa tunda tazo ta kasa samun soyayya da yardar kowa a gidan? ko dai suna ganin zuciyarta ne duk da a lulluɓe yake a cikin ƙirjinta....? ✍🏻 _Gaskiya rashin comment da like ɗinku zai kashe min ƙwarin gwiwa_ 🥺 [9/21, 3:51 PM] Novel: ABU ZAID By SASAAL74 CHAPTER 3 A ranar sam Hudayya ba ta runtsa ba saboda saƙa da warwarar da ta kwana tana yi. Bata jin zata ji daɗin zaman a gidan nan kamar yanda tayi hasashe kafin zuwan ta, amma duk da haka yafiye mata inda ta baro. Wani ɓangaren na zuciyarta kuma na ƙulla mata yanda zatayi rayuwar ƴanci a gidan duk da tana ganin kamar hakan ba mai yiwuwa ba ne ba. Breakfast mai rai da motsi ta saki jikinta ta yi zuciyarta fari fes. Bayan taci ta ƙoshi sai zuciyarta ta cigaba da kitsa mata hanyoyin samowa kanta mafita da cikar dukkanin muradanta. Mafitar da ta ke ganin ta samu ne yasa gaba ɗaya ta matsu su dawo saboda akwai abubuwa da dama da takeson sa ni dangane da ahalin gidan kafin tafara aikata abinda ta saƙa. Da wannan ƙaguwar Hudayya ta yi kwana uku a gidan, kafin dawowar su baƙinta mai haske yaƙara kyau da ɗaukar ido kamar ba waccen Hudayyar ba. Ranar Sunday da yammaci lafiyayyun motocin da su Aunty suka yi tafiya da su suka fara shigowa harabar gidan, horn ɗin motocin ne ya ankarar da Hudayya dawowar su. Da iya gudunta tayi saman Aunty don bawa idonta abinci. Lafiyayyen curtain ɗin ɗakin da Aunty ta bata amatsayin na kwananta taje ta yaye tana leƙawa window, fes take kallon motocin har su ka dai-daita parking a inda ya dace. Aunty da Alhajin su Abu Zaid ne suka fara fitowa, ragowar motocin kuma duk baƙin fuska ne babu Zainab da ragowan matan da ta gani farkon zuwanta. Abu Zaid ne fitowar ƙarshe a motar da take kyautata zaton shi kaɗai ne a ciki. Lokacin sanyi ne sosai don haka shigarshi ba ƙaramin kyau yayi ma ta ba, tsinin hancinshi kawai take iya hangowa da kyau a fuskarshi sai shigar ƙananun kayan jikinshi da yayi matuƙar burgeta. Duk da yana nesa sosai da idanuwanta, amma a haka take tantance duk wani siffar kyau da Allah ya yi mishi wanda a baya bata samu damar tantancewa ba, wutar abinda take dannewa na ƙoƙarin rura kanshi a cikin zuciyarta. Zubewa ta yi a kan gado ta na rintse idanuwanta, ga shi

Chapter 1 of 11