Share this page
ke damunta? Tambayar .da taiwa kanta kenan' wadda bata da mai amsa mata ita. Tai saurin' zabura ta mike lokacin da maganganunsa ke dawo mata. wallahi akan matata zan iya jirkita miki halitta in barki a kwance kinji na rantse miki kuma don wannan qatuwar da kikai bazai hanini dinga jibgarki kamar allah ya aikoni ba Rukayya ta maimaita, "Katuwa kuma‘!" A sanyaye ta nufi gaban dogon madubin dake tsaye a gefen gado ta soma bin kanta da ,idanuwa. Ita kanta sai da gabanta ya fadi, ta sa hannu tana shafa wuyanta wanda ya ciko duk wasu rami' da gurbi ya cike ldanuwanta suka dira saman kirjinta wanda ya qara cika tamkar zai fasa rigar ya' filo. lol Gabanta ya fadi, to tun yaushe ta zama haka? Ta dan karkata yana kallon kugunta da cinyoyinta wanda suka qara budewa, sai dai har yau bakin nan na nan kamar baqin zunubi Rukayya ta koma tanara sharar hawayenta, tabbas samun cima mai ' kyau yana gyara jiki fiye da shan wasu kwayoyin magani. Ko ina Kaka take yanzu? Idan ba zata manta ba yau satin su shida rabon da su hadu tun ran data kawota gidan gashi jin dadin da take mata kwadayinsa amma ba a sameshiba, ‘ kullum tana cikin zubar da hawaye amma gashi har wata kiba take, kota mece ce Oho. Ta bawa kanta amsa. Ga dukkan alamu Rukayya ta shiga shekarar cikar ‘yan matancinta, saboda ga jikinta nan ya nuna, sannan ga tunaninta ya soma canjawa daga na quruciya zuwa na masu hankali. Tasa hannu ta share hawayenta sannan ta laluba ta kwanta tana maida ajiyar zuciya, a haka bacci barawo ya lallaBo ya sureta. A kwana as tashi ba wuya wurin Allah, yau watan RuKayya biyu a’gidan Abubakar, babu wani abinda ta samu na cigaba illa wata irin natsuwa da tazo mata, da raahin son magana, ga wani irin hakuri. In zaka sa yatsa a bakinta ba zata iya cizawa ba. gurin qazanta kuWa sai abinda yai gaba, ~ ' ita kanta tsamin jikinta ya takura mata ga atamfar dake jikinta har ta soma yayyagewa don dama can taji jiki shiyasa ko aiki take ta shiga kare-kare kenan, kada wani yaga tsiraicinta. - Yanzu haka aikin take ita da kuku suna girki, shi ne ta dauki tawul din da suke goge~ goge ta daura a kugunta a saman zanin jikinta, tana aikinta. ‘ Suhailat ta leko kicin din, "Da Allah ku saki wannan aikin, ina da baqi maza a hada masu abin motsa baki, (just 10 minute) na baku". . , ‘ bata saurari abinda zasu cc ba ta juya ta. ' fice Kuku ya dubi Rukayya cike da damuwa a yanayinsa,kafin ya ce "Gaskiya Hajiya tana da matsala, yanzu maimakon ta bari mu qarasa abinda, muka dora, a'a sai .dai mu sauke mu dora wani‘ Rukayya ta tabe baki ba tare data tanka ba,taci gaba da abinda‘ take. Shima ganin hakan yasa ya juya ya soma abinda ke gabanshi, don yasan in ya biyeta sai ya wuni yana maga’na bata bashi amsa guda ba, don haja yaja bakinshi ya tsuke Suka hadawa baqin kayan kwalama irin su (snaks) kusan kala hudu, sai dambun naman kaji, sannan farfesun da sukayi na naman zabi suka hada masu dashi, Rukayya ta dauka ta fito musu ‘ dash Kallo ,’daya taiwa bakin ta janye idanuwanta a qasa ta ajiye kayan abincin ta yunkura ta mike ta nufi (fridge) ta Ciro musu lemuka da robobin swan water. Muryar wata daga cikin qawayen ta daki dodon kunnen Rukayya. "Kai Suhailat, yanzu ki rasa wadda xaki dauka aiki sai wannan. qazamar bakauyar? Haba! Ni wallahi k0 cokalin data taba ba zan iya cin abinci dashi ba Dubrta fa don Allah ' sai tsami take". * Suhaiiat tace, "Haba Rahma, yar gayu kikeso in dauka wadda zata kwace min mijin cikin qan kanin Iokaci k0?" Wata daga cikinsu ta ce, "Ah! Ai daga, baya kenan , in banda sakarcin ki Suhailat ki rasa wadda za ki dauka aiki sai mai coca Cola sharp? Aike da gani wannan k0 bata samu gyara ba sai ta dauki hankalin 'yan maxa. Ke baki ga yanda take ba a dire, ga tsawo ga sharp? Ai wannan ita ce bature yaiwa laqabi da Coca-cola , don haka tun wuri ki sake shawara, don kada wata rana tazo ta tsokale maki ido har yai ruwa, don kin san dan hakin daka raina...”. Rukayya da ta ajiye musu lemuka saman tebir tai sauri ta juya ta bar wurin, gabanta na faman faduwa, saboda tsoron matakin da Suhailal din zata iya dauka akanta yanzu kuma. Yau sunyi daren girki, ba su suka kammala abincin dare ba sai bayan sallar magariba,. saboda Bata Iokacin da sukai wurin hadawa baKin Suhai'lat abin motsa baki. Suna kammala girkin kuku ya fice daga kicin din, Rukayya ta dauki farfesun naman zabin ta zauna ta ci da ruwan tca mai zafi tana gamawa ta mike ta share kicin din ta gage, ana kiran sallar isha'i ta filo daga kicin din a lokacin Abubakar ya fito shima daga sashinshi yana daurA agogon hannu, da alama alwalar sallar isha'i ya dauro. Sukai ido hudu da Rukayya tana Rokarin gaida shi, ya daga maya hannu. "Rike gaisuwar ki"._ .Ya kare mata kallo cikevda kyama yace' "Yanzu dama a haka kuke mana girkin da muke ci da wannan tsinanniyar qazantar? Dubeki Rukayya sai kace ba 'yar mutum ba‘? Shin wai k0 dai aljanu garc ki wadanda sukesa ki qazanta ne iye?" Shiru ya dan ratsa wurin kadan, yaja yar gajeren tsaki. ' .“Mtsw!". _ Ya dubi Suhailat dake can zaune saman ( daya daga cicin kujerun dake baje a Cikin falon, ya ce‘ . "(My love) don Allah ki dan tsintsinto mata wasu daga kicin kayan da kika gama dasu, wallahi ban .qaunar qazantar nan k0 ’kadan". ‘ Suhailat ta mike tana fadar, "Wah! Ni zan bawa 'yar aiki kayana ta saka" Wallahi ba dai niba, a koma qauye kenan aji dadin kullo mani wani 'mugun abin'? Ai ni bani 'daga cikin matan dake bawa yar aiki kayan da suka gama ashema Na kwashe kayana, a sami wurin jera nata kenan. Abubakar ya ce. 'a"a Yar uwar tawa?" Suhailat ta ce. "Koma wacece inda har tana nan . a matsayin 'yar aiki to fa haka nake son ganinta". Abubakar ya ce "Ba zan iya ba, ai tsafta tana daga cikon addinin Musulunci, kuma ke kanki za ki iya rantsuwar kayan Rukayya ba za ' suyi sallah ba. Dubi yanda take yawo da kaya a yayyage". Suhailat ta ta tabe baki, "Matsalarta ce wannan Dear, wa yace ta yayyaga in bata son yawo dasu haka?" Abubakar ya Juya ya dubi rukayya cike da bacin rai, yai gaba yana fadar. "Z0 muje Rukayya". . Ta bi bayasa a tsorace, kai tsaye gidan suka fita, yana gaba tana baya. . Gidan dake jikin nasu suka shiga, shima qatone sosai,mai gadi yana sallah don haka kai kai tsaye suka wuce ciki. haduwar gidan ya ninka na Abubakar sosai, kai da gani 'gidan wani babban hamshaki ni . Salda ya danna (bell) sannan aka bude suka shiga matar gidan ce tsaye a bakin kofar da murmushi a "fuskarta. "A'a dan duniya, kaineka dawo? Ka gama yi min tsiyar taka?" Matar gidan ta fada tana murmushi. Abubakar ya ce, "Yanzun ma ba zama ‘nazo ba, Kanwata na kawo miki don Allah ki bata' kaya kala guda ta canza wanda ke'jikinta kafin zuwa gobe in san yanda za'ai". ,Matar ta mai da kallonta akan Rukayya tana fadan . "Wayyo Allah, ina ka samo ta ,kuma Abbakar kai ko baka gajiya da rakice-rakici Abbakar ya ce "Na'ce miki qanwata ce, baki , yarda bane?" ’ Dariya tayi ta janyo Rukayya jikinta tana "fadar. matar tace”Ai qaryarka ba sallah take ba ”yan mata ya sunanki‘!” "Rukayya". Ta bata amsa a taqaice. Matar ta kada kai uhm tace "Nice name“. _ Abubakar ya ce, "Bari injr masallaci in dawo. Ta ce "Sai ka dawo". Ya juya ya fita sannan matar taja hannun Rukayya suka nufi cikin gidan tana murmushi Saman bene suka hau kai tsaye suka shiga wani qaton falo sannan ta jata suka shiga cikin dakin dake gefe qaton (bedroom) ne wanda ya gaji da haduwa Rukayya tabi wani hoto da kallo wanda aka girke a falon matar gidance da wani magidanci suna mngume da juna sunsa wasu yara a gabansu To wai dama haka rayuwar birni take Mace tai ta rungumar namiji ba kunya koko ya abin yake ne? _ Duk zuciyar Rukayya ce ke raya mata hakan, bata ankara ba, sai dai taji matar ta ambaci sunanta. Tai saurin waigowa ta ga ta bude mata wata qatuwar (wardrop) bango guda, babu abinda ke danqare a cikinta sai suturu, tsoro ya kama Rukayya, ta ce. "A'a, ki bani k0 wanne Hajiya”. Matar ta ce,‘ "A'a, kar muyi haka dake kizo kawai kizaba idan kuma kina ganin sun miki girma bari na kawo miki wasu dogayen riguna ki zaba wadda kike so jiya maigidana ya dawo daga Dubai yaxo min dasu guda hudu, ne naga duk sunmin yawa, daya ce kawai tai mini Ina zuwa, bari na dauko miki su". . RuKayya bata ce komai ba, matar ta fice daga dakin, bataci minti biyar ba sai gata‘ ta .dawo rungume da kaya a hannunta ta zubesu gaban Rukayya tace lol mu tara donjin ci gaba naku har kullum A,I,S KE cewa asha karatu lfysa zallah RIKON KAKA CHAPTER17 'Gashi, ki dudduba'. Rukayyya tasha jinin jikinta matuka, harta kasa bincika kayan, sai saidai ta zari guda. ~ Mata tace 'To ga (toilet) can ki shiga ki wanka kisa kayan ga kayan kwalliya a gaban (mirrow) sai ki shirya'. . Rukayya tace 'To'. Ta mike ta nufi (toilet) cike take da mamakin yanda matar ke janta a jiki haka, ba tare da nuna tsana ko kyama ba. Wanka tayi sosai a(toilct) ta, fito sannan Matar _bata nan don haka rigar kawai ta dauka ta saka, ta rataya dan sirin gyalen rigar saman kanta ta daure shi a wuya. Tana cikin tattara kayanta matar ta shigo da sallamana riKe da wasu takalma ruwan kalar rigar ta nunawa rukayya. “tace mahadin rigar, ne ai sun hau ko?‘ Rukayya bata iya magana ba amsa kawai ta bata tace “Nagode'. Ta saka lakalmin mai mutuqar tsini ita ita kanta tasan ta yaudari kanta idan tace zata iya tafiya da takalmin, don haka ta dan dubi matar a kunyace ta ce "Anya zan iya tafiya dasu? Ba zan iya ba, sunyi tsini". Matar tai murmushi, "Sister kenan, ai takalmi mai tsini yana daya daga abinda ke fitowa mace sharp dinta. Karki damu da ‘tsawon ki, ki daure za ki iya tafiya da su, kije ki danyi (makeup) kafin yazo k0?” Shiru tai don k0 za'a dora mata bakin bindiga bata san k0 meye haka ba. Ganin ta‘. danyi dam yasa matar ta fahimta, don haka ta dafa kafadar RuKayyar tana murmushi, tace. "Ina nufin ki danyi kwalliya ko yaya". . Rukayya ta girgiza kai, alamar a'a, matar ta ce. ' ”A'a, kar muyi haka dake ‘yar uwa, tunda kika ga Abubakar ya kawo ki nan to ki saki jikinki, mu da shi tamkar 'yan uwa muke, abokin aikin maigidana ne, mijina shi ne babban su a (office) din da suke aiki, don haka ki saki jikinki. Muje in taya ki kwalliyar ma da kaina". Ta kama hannunta suka nufi gaban madubi, ta zaunar da, ita saman kujera, ta mika mata mai ta shafa a jikinta, sannan ta dauko (foundation) ta shafa mata, ta dauki ta gari ta shafa mata, sannan ta shafa mata wata kalar kuma. Sannan ta zane mata girra da (brown air pencil) ta zana mata a qasan ido tai‘ mata line a , labba sannan ta shafa mata jambaki (24hours), ta‘koma ta dora mata (pink) a sama. (Eye shadow) shima (brown) ta shafa mata a saman ido, sannan ta zana mata (cyc leaner) sannan ta sharce mata girar ido da mascara ta shafa mata bakin kwalli, sannan ta gyara mata mayafin, ta nada mata shi irin yanda larabawa ke yi. Sannan ta feffesa mata turare ta k0 ina a jikinta,‘ ta riqe hannunta. tace to dubi kanki a madubi yanxuu Rukayya, har kin flto a macer ki sak”. Rukayya ta bi kanta da kallo, ita kanta tasan tayi kyau matuqa," amma yanda ri gar tabi jikinta shi yafi komi birgeta. Ashe haka take dama? Ashe ba wani kyau ne aka fita ba kawai an flta iya fito da kyan ne. ? .Matar tace, ”T0 amma me yasa ba ki gyarakanki? Baki ga yanda kitson kanki ya dankareba Ga faratan ki sunyi zaqo-zako, . na qafarkima tayi kina macen ki me yasa haka? ‘ , Haba Rukayya, ai ita, mace 'yar gyara ce sai da gyara. Na tabbatar Abubakar bai kai ki gidansa kai, tsaye ba sai ‘don kar matarsa ta . ganki a yamutse haka, kin san mata ’yan rainin wayo ne, yanzu data ganki haka wani sabon (page) din rainin wayo ne zai bude Don haka gobe "da kin gama abinda kike ki dawo zan tsin-tsintar miki kaya k0 kala goma ne aba tela ya gyara miki ki rinka dan sauyawa kinji?" Rukayya ta amsa da, ”To". . Matar tace "Yauwa, haka" nake so, kinga idan kika gyara kanki matar bata isa ta raina miki ba ballantana yayan naki Muje qasan don nasan wata qila ya dawo Sannu a hankali Rukayya ke taflya sai kace 'yar koyo, abin har ya bawa Hajiya malar gitan), ta rinqa gwada_ mata yanda ake taflyar har suka isa qasa. ' A zaune suka samu Abubakar da mutumin da Rukayya ta gani a hoto suna cin abinci, Abubakar ya kafe su da wani irin kallo tun daga nesa. Ba wai kwalliyar da Rukayyar tai ya dauki hankalinsa ba, saboda idan maganar kyau ne Suhailat ta ninka ta, gaban rigar-shi yafl komi daukar hankalinsa, 'saboda duk tsawon rigar babu inda akaiwa ado sai a' Kirji, aka kuma qara ciko gaban rigar da soso (breas cup) mai da tsohuwa yarinya kenan, ko na ce a cuci maza. ’ To ila wannah dama yarinyar ce kuma . mai kayan ya abin zai' ba da kenan? Abuhakar ya sauko da kallonshi har saman kugunta Wanda yai wata Irin budewa tare da cinyoyinta, a take kuma ya dauke kansa daga kallonsu saboda yanda yaji kirjinsa ya buga da karfi Yai gaggawar kawar da abinda ya zunguri zuciyarshi, don haka bai san qarasowar su ba sai dai yaji maganar‘ Hajiya Maimuna na ' fandar. "Kai Yallabai, abin har ba’a ganin masu shigowa, anya ba zamu ware maka kwano a gidan na ba?" ' Abubakar yai dariya kafin ya ce, "Magori wasa kanka da kanka, idan maciyan abincin kike nema ai kisha kurumin ki, don na fada miki, . Oga Mahmud nan zai santalo maki tsala~tsalan 'yan mata har guda biyu, kinga sai kiji dadin .girkin".Dariya tayi sosai kafin ta ce "Ai k0 da kun gwammace ku tari (transformer) da ruwa a jikinku da kuce za kuyi wannan gangancin, don duk dan da ya hana uwarsa barci wallahi shima ba zai runtsa ba, kaji in fada maka".' -_Abubakar ya ce"Yo araduma tayi ta gama kuma walqiya kawai akai aka dauke". 'Ta ja numfashi, "Hum! 'to ai sai ku tanadi manyan na' urori don shirya sabon (film) din Dakin Amarya (one to four). Dukkan su suka kwashe da dariya banda Rukayya da Hajiyar, Abubakar ya mike yana dariyarsa. "Ke tashi muje kinji, idan muka biyewa wannan sai mu kwana anan". Ya maida kallonsa wurin Hajiya Maimuna. "To ranki shi dade, godiya marar adadi, sai na ce Allah Ya sada mu da alkhairi,'d0n gobe zamu wuce Atlantic insha Allahu ni da madam, saboda Wani (course) da zanyi na shekara daya da rabi, sai ai mana addu' a". _ Ta ce, "Kai don Allah Abbakar da gaske?" Ya ce "Gaskcn gaske" . Ta ce"To ita wannan baiwar Allan fa ya . zakai da ita? Ba zaka maida ita gida ba har zuwa lokacin da zaku dawo?" Abubakar ya ce "Nan zata zauna tunda akwai' maigadi,kuma kema zaki rinka. shiga tana shigowa itama, saboda zaman kadaici naiwa Oga Mahmud magana“; Haj. Maimuna ta ce, "To shi kenan, Allah Ya kiyaye, Ya tsare Yasa a aje a sa' a a dawo a sa‘ Abubakar ya ce, "Amin, kuma don Allah duk abinda ke nan Zan rinqa kiran waya sai ki fada mana k0 da bukatata kudi k0 ta wani abu sai a turo Haj. Maimuna ta ce "Ba komi, Allah Ya kaiku lafiya". . ‘ Ya amsa da, "Amin". Har bakin kofa ta rako su tana zabga musu addu'a, sannan ta koma su kuma suka fice. . . A tare suke tafiyar, sai dai ba wanda ke tankawa wani a tsakaninsu har suka shi'go cikin gidan. Abubakar yabi ta baya ita kuma ta shiga ta falon da sallamarta ' Kallon-kallo suka shiga yi tsakanin Rukayya da Suhailat, Suhailat ta zabura ta mike a sukwane tayo kan Rukayya tana fadar. "Kaza-kazan uba! Uban wa za aiwa ‘ wannan shigar a gida? Bala‘ il". Kafin Rukayya ta ankara har ta shiga kai mata duka ta k0 ina, tsoro da fargabar abinda zai iya faruwa shi ya hana Rukayya kwatar kanta Dukanta take kamar mahaukaciya, ta rinqa keta rigar, saida taga tabbalar ta yagalgala rigar . ta yanda bata Kara sanyuwa sannan ta hankada ta waje, tana. fadar.’ "Yau sai' kin bar gidannan 'yar iskar banza inko ba hakaba wallahi sai na 'tsugunar dake". ta hankadota tamaida kofar ta rufe, Rukayya tai duke a gurin-tana .faman dibar kuka kamar ranta zai fita gaba'daya Wata irin iska mai qarfi ta taso mai hade da guguwa irin mai Balle kwanikan Jama' ar nan. _ Hankalin Rukayy’a yai masifar tashi, tsoro da fargaba suka Kara shigarta, ta rasa mafita, To ina zata nufa? Kafin 'ta gama tunanin ruwan sama mai. Rarfi ya sauko tare da faukewar wutar lantarki a tare.-Tsoron ne ya dabaibaye ‘zuciyarta don saboda ko danyatsanta bata iya gani saboda duhu. Ta dunkule a gurin. ruwa‘ na sauka a jikinta da karfi, kuka take sosai irin wanda bata taba yi ba tudna Allah Ya halicceta. ' Abubakar dake nashi Bangarcn kwance saman duguwar kujerar dake gefen gado yana latselatse a laptop ya ga an dauke wuta, cikin takaici yaja tsaki a zuciyarsa yana takaicin halin wutar Nigeria. Ya yunkura ya mike ya jawo rigar ruwa. ya saka, ya dauki lema da (tourch light) sannan ya fito daga falon don kunna (generator). Ya bude falon yana faman haske-haske, tun kafin ya fita kamar kar ya fitan saboda yanda yaga ruwan na sauka da qartinsa, sai dai ya zama wajibi ya fitan saboda sanin halin 'yar mulkin tasa, yasan ba zata iya kwana ba wuta ba. ‘ Ya runtse ido yai waje ya nufi inda injin yake, ya sa makulli ya tayar sannan ya wuto . gabansa yai wata mummunar faduwa, hatta (toureh light) din hannunsa ta nemi suBucewa saboda razana. Ya Kara ware ido, tabbas mutum ne a dunkule a wajen. Cikin dakiya irin ta mazan jiya ya daga 'murya. ~ "Waye nan?" Rukayva ta dago a galabaice saboda dukan da ruwan yai mata ba na wasa bane. "Subhanallahi! Rukayya meye haka?" Ya nufeta da sassarfa, ya kamo ta gaba daya ya dagata tsaye. "Subhanallahi! Inna lillahi! Wa yai miki ' haka?" Shiru ba amsa sai dai kyarmar haqoran da take. ' . . Abubakar ya riqota sosai a jikinsa ya nufl falon da ita, kai tsayr falonta ya nufa ya direta kan kafet, ya mike da sauri ya fita bai jimaba ya dawo da tawul da jallabiyya a hannunsa, ya kamata ya tsane mata jikinta da tawul din, sannan ya mika mata jallabiyyar. "Amshi ki sanya, za ki iya?" Rukayya ta daga mashi kai, ya-mika mata farar jallabiyyar sannan ya juya ya fita. Ta lallaBa ta mike ta cire rigar jikinta da ta yayyage sannan ta saka jallabiyyar, sabuwa ce qal irin ta mazan nan mai hade da hula, ta lallaba ta koma kan kujera ta kwanta. . Bata jima da kwanciya ba Abubakar ya dawo riKe da (Cup) a hannunsa ya miKa mata tare da Ballin magani, ta karba ta shanye sannan ta miqa mashi kofin Abubakar ya amsa yana kallonta, haka kawai yake jin wani abu na masa yawo a zuciyarsa game da yariyar, to meye? Shi dai yasan ba so bane, sai dai wani abu mai kama da sha'awa. "Na gode. Rukayya ta fada da sanyin muryar da bai san tana da ita ba, abubakar ya dawo dashi ‘cikin hankalinsa, don haka yai saurin (contoling)din zuciyarsa. "Okay, ba matSala". Ya fice da saurinsa sai kace wanda aka kora, ya fice daga falon yaja mata Kofar. Rukayya ta raka shi da idanuwanta wanda suka ciko da hawaye, ita kanta ba zata iya ccwa ga k0 kukan meye take ba ‘ Abubakar ya koma sashinsaya cire jallabiyyar jikinsa, daga shi sai dan qaramin (short nickcr) 'sai .dai ' ya 'gaza’ kwanciya, ‘ qirjinshi yai mashi nauyi matuka. Ya jingina LOL akwai rikici fa naku har kullum A,I,S ke cewa asha karatu lafiya CHAPTER18 bayansa jikin (wardrop) din dake like a‘ bango, idanuwansa a rufe. Surarta ce kawai ke faman kai komo a idanuwansa, shi kanshi bai san tsawon loakcin‘ da ya dauka ba, sai dai yaji muryar Suhailat na fadar. "Da kyau, dama nasan wannan ranar , tananan zuwa Abbakar, nasan k0 ba dadade k0 ba jima sai kazo kana son yarinyar nan" Abubakar ya bude idanuwansa ya kafe su akanta yana maimaita. "So... So fa kika ce Suhailat?" Ta daga murya, "So na ce Abbakar! Ka ‘ soma son Rukayya, karya na fada?" * Shiru ya danyi, shin k0 abinda yake ji game da yarinyar nan shi ne son? Kai gaskiya a'a ba‘ so bane; To meye? Ya tambayi kansa kai ' tsaye tambayar dabata da amsa. D0n haka ya girgiza kansa yana fadar. "Ki yarda dani Suhailat, abinda yakr cikin zuciyata ba so bane. ' Cikin daga murya ta'ce, "Rufe min baki munafiki, idan ba so bane mene ‘ne? Sha' awa ? ce ? tunda' .ka kalleta a tsirara Allah dau yai wadan irin wannan zuciyar taka Abubakar, wadda ba zata iya kare kanta daga fadawa sharrin shaidan ba. Kuma idan ma ka soma sonta Abubakar . ka sani wallahi'tallahi ba zan taBa yarda wata mace a matsayin kishiya ba ballantana wannan sokuwar yarinyar, ballagaza, jaka, akuya, 'yar matsiyata. Wallahi ba zan yi kishi da ita ba, sai dai kwarya tabi kwarya, 'don haka ina gargadinka da kada ka ballo wutar da zai kasheka Abubakar ya ce, "Ki dawo hayyacinki Suhailat, kada ki yanke hukuncin da zuciyar ki ba zata iya dauka ba, alhalin kin san zuciyata bata tanadi dakarun da zasu kareta daga kamuwa da son wata ba .. idan kuma kin aikata abinda kika ' so don ki salwantar da rayuwarta saboda kina tunanin bata da gata to ki sani ni nine gatanta daga yau kuma daga yanxu inason ki sani abinda nakeji a zuciyata gameda ita baso bane bane kuma ba Sha'awa bace, sai dai wani abu mai kama da sha,awar". Suhailat ta fasa wata uwar Kara . "Wayyo na shiga uku! Inna lillahi Wa'inna ilaihi raji un Ta zube Kasa ta fashe da wani irin kuka mai Kairfi. Abubakar ya duKa gabanta, "Kiyi a hankali, kinga dare ne, idan da kuma za ki dauki shawara da kin adana haWayen tun yanzu, don wata qila akwai ranar zubarsu". Ya yunkura ya mike. Suhailat tai saurin riqo hannunsa, "Kar kai min haka Abbakar, don Allah don Annabi kada ka zamo sanadiyyar rugujewar farin,cikin rayuwata, ,don Allah Abbakar don Allah, wallahi ba zan‘iya kallon ka ‘da wata macc a duniya ba idan kace kai. min kishiya Abbakar mutUWa zanyi, wallahi mutuwa zanyi. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Yau‘ 'na shiga uku". ‘ ta hada kanta da hannunsa ta cigaba da rera kukanta mai ban tausayi, Abubakar ya ja wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya ce. "Me yasa kike dauka cewa isarki da tinkahon ki da zamantowar ki wata zai iya samar miki abinda kike so da arziqi k0 da tsiya? Me yasa kika dauka kudi zai iya samar miki duk abinda kike so a duniya? Me yasa kike zaton don ina qarkashin mahaifinki zan iya kwantawa ki takani yanda ranki yakeso? Kinyi kuskure Suhailat, zuciyar ‘ Abubakar tamkar dutse take, dutscn ma na ‘ niqa wanda k0 nakiya ba zata iya masa ba. ‘ ‘Suhailat ina sonki son da ba zan iya misalta miki irinshi ba, a duniya babu abinda 'zaki‘nema a wurina ki rasa, sai dai in in raina ne‘shima don ban iya cire shi daga jikina in bayar.ne Amma ke sai kike ganin kamar wata isarki ko da arziki yasa nake miki abninda nake yi.~ Kinyi kuskure Suhailat, dOn. har yau ba ai dukiyar da zata sa in yima mace bauta ba, kuma” "Kayi haquri don Allah Dear, Wallahi ba zan Kara ba. Ni dai don Allah kai min alkawarin ba zakai min kishiya ba, wallahi zuciyata ba zata iya daukar wannan tashin hahkalin ba".Suhailat ta katse shi. . , , Abubakar ya danyi. jim yana jinjina girman lamarin,” Suhailat ta‘mike ta kwanta a jikinsa', Cikin muryar kuka ta Ce. ' "Ba don halina ba, don Allah Abbakar, ni kuma nai maka alKawarin zan zame maka . daya tamkar da dudu. Nai maka alkawarin babu abinda zaka nrma ka rasa na daga zamantakewar . aure da kyautatawa da soyayyah Ta lalubo hannunsa ta rike tana matsawa. "Kai nake saurare my Dcar". Abubakar ya ja Wata ajiyar zuCiya mai qarfi kain yace."Nai miki alkawari Suhailat" ta qara makalkale shi tana sumbatarshi ta k0 ina. "Na gode my Dear, Allah Ya saka da alkhairi". Murmushi kawui yayi saboda nauyin jinjina girman alkawari da zuciyarshi tayi. Misalin qarfe tara na safe Rukayya da kuku suka kammala abin karyawa, sannan ita ’ ta dawo falon tana gyarawa, bayan ta gama gyaran 'kicin din, Abubakar' da Suhailat suka fito‘daga falo‘ suna 'janye da akwatina, Rukayya ta sadda kanta tare da gaishe su cikin girmamawa. Abubakar ne . dai ya amsa banda Suhailat da ta juye idonsa ta watsa mata harara « Abubakar yaCe, ”Yauwa Rukayya, dama sallama zamuyi za muyi tafiya sai idan mun dawo. na sallami kuku saboda gidan yanzu ke kadai ce akwai kayan abinci sai ki rinqa dafa duk abinda kike so Sai har Allah Yai mana dawowa". Ya zaro kudi masu yawa cikin aljihu ya ajiye mata "T0 sai Allah Yai mana dawowa". Muryar Rukayya na rawa tace "Allah Ya kiyaye Ya amsa da, "amin". Sannan suka fice . RuKayya ta raka Su da idanuwanta ‘wadanda suka ciko da hawaye, haka kawai takejin tana kewar su,‘ to me kenan? Ta ajiye tsintsiyar hannunta ta zauna saman hannun kujera tana kallon Rofar da suka fita 'sharar da hata idar ba kenan ta lallaba ta miqeta nufi sashinta ta kwanta. ‘ Da yamma liqis Rukayya ta fIto falon ta ida shararta ta dazu, sannan Ia nufi kicin ta dora Indomic saboda yunwar da ta soma ji sama-sama ta rinka jiyo sallama. Ta dan tadan sauarara kadan, sallama ce kuma muryar mace. Rukayya ta ajiye wukar da take yanka albasa ta fito tana amsa sallamar. . "Lah Aunty. Maimuna, sunnu da zuwa". . ’ Ta nufeta da murmushi a fuskarta, "Don Allah zauna ga kujera, bisimillah". ‘ Haj. Maimuna ta zauna itama da fara'a ‘ a fuskarta ta ce. ‘ "Rukayya kenan, ya zaman kadaici‘. ’" Murmushi kawai tayi, Haj. Maimuna ta ce. "A'a ban gane ba, 'sai. dariya ba magana?’Rukayya ta bar murmusawa kafin tace. ‘ "Alhamdulillahi". _ Aunty Maimuna tace, "Haka nake so ki saki jikinki duk maganar da zanyi ki maido mani amsa, "To, bari na kawo miki ruwa ’ ‘Tace "A'a sha zaman ki. na hutasshe ki 'Yar raihin wayo, kika'ce min kanwar Abubakar: ceke, ashe Shara min ita ku kai jiya. Ogana (mijina) yake-fada min

Chapter 7 of 13